ne?" Sheik ya ce
"Ah haba matsala da kanta ƙarya take ta doshi balaraben Malami daga Yemen" Wani sanyi ne
ya ratsa zukatan mutanen wajen.
Sheik ya matsa gaban gawar guda ɗaya, ya buɗe littafin hannunsa, ya shiga dubawa kamar
mai duba qur'ani ki littafin addu',oi ya ji ya kasa komai so yake ya karanta wata addu'a ko sura
amma bakinsa ya ƙi basa haɗin kai, ganin haka ya juya ya kalli jama'a ya ce
"A karanto" Suka kalle shi da rashin fahimta.
"Mai za a karanto?" Mai Gari ya tambaye shi
Sheik ya ce
"Kowa ya karanta karatun da ya iya" Ya faɗa don shi ya kasa saamun kowacce sura ma bare ya
karanta, haka kowa ya buɗe baki yana karatu a nan Sheik ya fisge wata surar ya fara, kowa
yana kaiwa ƙarshe sai aka yi ɗif, matsawa ya yi ya ɗauki shebir ya fara kwashe ƙasar kabarin,
saboda gabaɗaya ƙasar ta koma ta rufe inda za a mayar da mutumin yana cikin kwasowa ya ga
cinyar mutum a ciki, gabansa yana faɗuwa ya juyo zai sanar da mutane tun da su suna can
baya sun bashi wuƙa da nama.
Kafin ya furta komai sai ji ya yi gawar wajen ta saka ƙafa ta tura shi sai ga Sheik ya kusa ya
faɗa ciki, dakyar ya yi nasarar komawa gefe yana haki lokacin mutane duk sun ƙara ja baya,
littafinsa da ya ajiye ya ɗauka tare da maganin nan da ya ɗakko na wajen Malam yana nufo
mutane gabansa yana faɗuwa don ya tabbatar gawar nan ta tura shi gashi tsohuwar gawa.
Yana zuwa ya ce
"Kar ku damu wannan ba wani abu bane, akwai siddabarun aljannu a lamarin, kuma wannan
mayar da gawar kabari ba na mutum ɗaya bane ku matso mu taru mu yi aiki tare" Kowa ya fara
zare ido Sheik ya ga suna masa kallon tuhuma.
Da sauri ya nuna musu robar maganin hannunsa ya ce
"Wannan magani ne daga ƙasar Yemen na taho da shi idan aka yayyafa a bakin kabari aljannu
suna guduwa cikin daƙiƙu" Si ya ga kowa ya ɗan saki jiki.
Bai nuna musu ya ga cinya a cikin ɗaya kabarin ba haka suka mayar da gawarwarkin don sun
yarda da maganin da Sheik ya barbaɗa basu san cewa shi kansa Sheik ɗin bai san maganin
mene ne ba wataƙila ma yana cikin magungunan mallakar da za a ba mata.
Kabarin yaro nan ne kawai ya rage, Sheik ya ce tun da ba gawar garin ba ce a nemo ƴan garin
su zo su binne, don tun da ya ji saurayin nan ya ce an ce gawar ta yi kuka sai ya tsorata dama
gabaɗaya ma ƙarfin hali yake yi.
Mai Gari ya ce ai kawai su binne tun da yana cikin tawagar mutane ai su ma garin namu
ƙarƙashin mulkinsa yake. Kai Sheik ya gyaɗa tana wayincewa, sun kewaye kabarin mutane
damƙam, Sheik tun da shi ne balarabe shi ne yake jagorantar komai.
Hannu ya miƙa zai ɗauki yaron , da ya miƙa hannu ta wajen kan yaron sai ya ga kamar ba shi
ya ɗago kan yaron ba, kamar dai gawar ce ta ɗago da kanta, da sauri ya janye hannayensa ya
ɗago sai ya ga ba a lura da abin da ya gani ba, kamar gawar ta san mai yake tunani kawai sai
ya ga ta fara ɗagowa sai ga yaro a zaune dakaka duk da yana sanye da likkafani, Sheik da ya
tashi a firgice ya tsallake yaron sai ƙafarsa ta maƙale da likkafanin da aka ƙulle ƙafar yaron
yana fisga ya yi tsalle da yake yana ɗaya gefen ne Mai Gari kuma suna ɗaya gefen, sai lokacin
kowa ya lura da abin da yake faruwa, tun da dama gawar yaron daga can gefen kabarin take ba
a dab da kabarin ba, tsalle ɗaya Sheik ya yi ya tsallake ramin kabarin sai gashi a gaban Mai
Gari ya kama rigar Mai Gari, jama'a kowa ya fara kama gabansa da yake dama maƙabarta ba
wani a kewaye take ba sai kowa ya fara kama gabansa wasu gabas waau yamma wasu arewa,
Mai Gari da Sheik suna cikin mutanen da suka fita ta yamma.
Don Mai Gari ya warce riƙon da Sheik ya masa haka suke falla gudu kowa yana ta kai- ta kai.
Babbar rigar Mai Gari sai tashi sama take, rawanin ya kunce yana binsa yaraf, ko takalmi
babu a ƙafarsa ya sille, Sheik ƙafarsa maƙale da dogon tsumman likkafanin da aka ɗaurewa
yaron ƙafa, haka suka ratsa ta cikin gonaki suna sheƙa gudu, Sheik ya tattare jallabiyarsa
saboda gudun samun akasin faɗuwa, suna cikin gudu da yake Mai Gari ne a gaba Sheik yana
take masa baya, jama'a kuwa kowa ya yi tashi hanyar, kamar daga sama sai ganin wannan
yaron da suka baro a maƙabarta zaune a kan makara ya diro a gabansu, Sheik ya taka wani
uban birki shi ma Mai Gari haka, sai Sheik ya juya a guje ya bi wata hanyar sai tafiyar ta
kasance Sheik ne a gaba Mai Gari a baya gawar yaro tana take musu baya.
Da yake Sheik a wuyansa ya rataya carbinsa, littafinsa yana aljihunsa, Mai Gari ganin gawa
tana son cim masa sai ya miƙa hannu ya kamo carbin wuyan Sheik a haka suke gudu, sai da
suka zo dab da shiga gari Sheik ya ja wuyansa sai carbin ya tsinke, a nan Mai Gari ya saki
carbin, kamar an ce su waiwaya bayansu a tare suka hango gawar bagatatan tana binsu,
wanann karon yaron tsirara ya riƙe likkafaninsa a hannu hancinsa toshe da auduga, yana cewa
"Sheik, Mai Gari ku zo ku mayar da ni kabarina ku binne ni" ,Amma bahu wanda ya tsaya bare
ya saurare shi.
Tun daga gidajen farko -farko suke cin karo da gidaje a rurrufe, alama ce ta gabaɗaya
magana ta ratsa gari tun da dama a tsorace ake da maganar tone kabari bare kuma yanzu aka
ce gawar ta tashi zaune, tabbas sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci!.
Sun zo tsakiyar gari suke ganin mutane suna ɓullowa ko ta ina, wani babu takalmi wani hula
a maƙale a hamata wano ya tuɓe rigar ma yana zangaya gudunsa a haka.
Mai Gari maimakon ya yi hanyar gidansa sai kawai ya bi bayan Sheik, Sheik kuwa ganin
gawar yaron tana son cin musu sai ya tura wata ƙofar gida haka Mai Gari ya mara masa baya
suka shige, gidan wata tsohuwa ne wacce kp fita bata iya yi, ɗaki suka bankamu suka rufe suna
mayar da numfashi.
Sheik ya fito da robar magani daga aljihunsa ya buɗe yake tuttulewa a fuskarsa, Mai Gari ma
ya karɓa ya watsa a tashi fuskar sai suka ji da wata muryar yaro an ce
"Ku zo ga likkafaninku, raminku yana can na haƙa muku kabarin" Suna juyawa suka ga yaron
ya ratso ta bango, da rarrafe suka fito Mai Gari yana miƙewa sai gida ya yi, Sheik ma ya yi nasa
gidan yana shiga ya banke ya zauna ya kifa tagumi, carbinsa ɗaya ya ɗauka ya fara ja yana jin
tsoro sosai idan ya tuno wai gawa ce ta tashi da ƙafarta take bin su riƙe da likkafani.
Yana cikin wannan halin ta tuno yadda ya ji wani a maƙabarta ya ce, ya ga wani kabarin yana
motsi tunanin da ya fara kar sai gabaɗaya gawarwakin su fito su bazo gari shi bai san ma abin
da zai ce ba.
Tun da ya shige ɗaki bai fito ba, ranar haka garin ya tsaya cak baka jin motsin kowa hatta
masallaci ma ladan bai kira sallah ba, bare kuma mai gayya mai aiki wato Sheik ya fito ya ja
sallah, to shin wa zai ja sallar ma? Bayan mutanen gari kowa yana gida a ɓame ana tsoron
fitowa a yi arba da gawa.
Salloli dai Mai Gari sai a ɗaki ya samu ya yi alwala a wani kwano ya gabatar sa sallolinsa cikin
tsoro. Ranar dai babu watandar kayan daɗi yo waye zai dafa kayan daɗin.
Ɓangaren Mai Gari ma tun da ya kwasa da gudu ya yi gida, lokacin matarsa ta ji ana cewa
gawa ta bazo gari hakan ya sa ta taho za ta kulle gida, ta tura ƙofar kenan hakan ya yi daidai da
zuwan Mai Gari ya kai kansa ta banko masa ƙofar a goshi, haka suka shiga turarreniyar ƙofar
shi yana turawa yana so ta buɗe masa ya shiga, ita kuma tunaninta gawar da aka ce ta bazamo
gari ce, shi kuma tsoro ma ya hana shi furta komai, saboda ko da ya taho ma ya sha haɗuwa da
mutane kowa yana ta kansa, babu ma wanda ya lura da shi bare a girmama shi, yo shi ina zai
tsaya karɓar girman ma.
Jin yana neman ya ci ƙarfinta sai ta ƙara dagewa ta tura ƙofar, Mai Gari sai cewa ya yi
"Ke buɗe Mai Garin Ƙundu ne" Jin muryar mijinta a rikice sai ta matsa daga ƙofar ko kallonta bai
yi ba ya wuce ta ya shige cikin gida a guje, ganin haka bata tsaya rufe gida ba don abin ya girmi
tunaninta yadda ta ga Mai Gari yana zabgar gudu ta san tabbas akwai lauje cikin naɗi.
Baya ta take masa sai dai kafin ta je ya shige ɗakinsa ya banki sai ƙaran saka sakata ta ji,
nata ɗakin ta nufa, wanda tana shiga ta rufe ƙofar runawa da ta yi sakatar ta cire, sai kujerar
zaman tsakar gida ta mata ta saka a bayan ƙofar ta zauna tana haki tana tunanin to ina
Balaraben Malamin garin nasu da yake yaƙar aljannu.
Washe gari sai da gari ya waye tangararai aka fito sallah, saboda ƙarfin hali irin na Sheik ya
baro wata baƙar rigar jallabiya tana ta sheƙi ta ƙara haska shi, ya sheƙa uban turaren oud, ya
fito yana jan carbi, yana muzurai don kar a kawo masa raini, a haka ya ja sallar, bayan an idar
ya zauna a mazauninsa bayan ya juyo ya fuskanci mutanen masallacin ya ce
" Alal haƙiƙa jiya mun haɗu da wani ibtila'i, wanda aka samu wani aljani marar imani ya shiga
jikina don kawai yana son ya rikita wanann gari ku shiga halin ha,u'la'i, saboda sun san ni kaɗai
ne zan kawo mafita a wanann gari, sun san ni zan magance duk wata matsala da za ta tunkaro
gari, shi ya sa suka tura mini wani ƙasurgumin aljani ya shiga jikina, sai da daddare na ƙure
karatun qur'ani a wayata sanann na hau yi wa kaina da kaina ruƙiyya, a nan ne da ya buɗe baki
ya yi magana na gane ashe ba ni bane aljani ne" Kowa ya yarda da maganar Sheik sai suka ji
dk ya fara basu tausayi don sun yarda da abin da ya faɗa.
Mai Gari da yake da shi suka yi gudun famfalaƙin da Sheik sai ya kalle shi da mamaki ya ce
"Yanzu dama Sheik duk wannan abin da muka yi na gudun ceton rai ba kai bane?" Wani yawu
Sheik ya haɗiye jin kamar dai tambayar ta yi kama da tambayar tuhuma ko rashin yarda.
Cikin son ya kankarowa kansa mutunci ya ce
"Ashsha Mai Gari, haba kai kuwa ni ne zan yi gudu saboda gawa? Ko ana ha maza ha mata ai
ba zan yi gudu ba, sannan kuma ina horar mutane a kan rashin dacewar tuhumar malaman su
musamman malaman larabawa ko abu suka yi ba daidai ba, ba a tambayar mai ya sa" Shiru
Mai Gari ya yi sai ya ce
"Ni ma duk mamaki ne ya cika ni, ni ina ta gudun gawar yaro ashe ina tafe da aljani" Ya faɗa
yana ji babu daɗi.
Haka dai Sheik ya yi ta kawo maganganun da zai kama zuciyarsu, ya ringa faɗar maganganu
masu shiga rai, saboda cewa ya yi ma ko joya da suka ji shiru bai fito ba aljanin ne da bai sake
shi ba shi ya sa bai fito jan sallah ba, basu san abin da ya hana su fitowa ba shi ɗin ma shi ne
ya hana shi fitowa wato tsoro.
A ƙarshe dai ya ce musu wannan yaron ba mutum ba ne, aljannu ne suka ɗauke gawarsa
wanda ya taso ya shigo gari aljani ne ya yi shigar yaron, sai washe bari aka ga gawar yaron a
ƙofar maƙabarta, haka dai Sheik ya ari jarumta aka binne yaron.
Bayan sati uku, komai ya kankama, a inda mata suke tururuwar zuwa wajen Sheik karɓar
magani, gabaɗaya a sati rana biyu ce ta maza amma kwanaki biyar duka mata ne aka warewa
suke ziyartar Sheik ɗin.
Hatta ƴan mata suna layi a wajensa, maganin farin jini, maganin karɓar kuɗi a hannun
saurayi, maganin samun bazawari marar mata, haka suka yi ta zuwa suna karɓar magani,
Sheik kuma kasuwa ta kankama yana ta damƙar kuɗaɗe.
A wata ranar laraba ne Sheik ya yi arba da wata budurwa da iyayenta suka kai masa ita ya
mata ruƙiyya tun da ya ɗora kansa a kan yarinyar nan ya ji ya kamu da son ta, yana so ya aure
ta amma kuma yana tsoron su mutanen gari su zargi wani abu ko ma wani ya harbo jirginsa, a
ga shi yana balarabe ya ce yana son baƙar fata, amma dai ya fara ƙagauta da zama babu mace
ya baro matansa biyu.
Shiru ya yi a fili ya furta
"Ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, in baro mace tana gugar mace har mata biyu amma in zo ina
zaman gwauranci, shi ma Mai Garin ban da sakarai ne ka bar baƙo babu mace haba ko da na
ce ni malami ne ina kwaana sallah da salatin annabi S.A.W ai ni ma ba dutse bane kuma ba
katako bane da zan ƙare kullum a cire aljannu da bayar da magani, ina nan ina zaune da abu
sanƙamƙam a jallabiya" Ya faɗa yana jan wani dogon tsaki.
Bayan kwana biyu da yamma ya ce zai yi lazimi ya dakatar da ba maza magani dama ranar
maza ce, shi kuma ya fi son ranar mata saboda wuni yake yana wadaƙarsa yana kallon su
shegen son mata.
Kuma maza basa bada kuɗin sadaka da yawa, amma ya fi morar kuɗin mata.
Yana kishingiɗe bayan ya gama kallon film a wayarsa, wanda ya sauke a youtube, wayar da
ya cewa su Mai Gari wayar babu komai sai karatun qur'ani.
Ɗan baccin da ya ɗauke shi ne yake mafarkin ya auri budurwar nan da ya ɗora rai. Bugun
ƙofar gidan ne ya falkar da shi, ji yayi ana ta rafka sallama, ya taso ya leƙo, jin ana hayyahayya, wata matashiyar mace ce aka shigo da ita maza ne ƙattai uku sun riƙo ta tana togewa,
dakyar ake janyota sai kamce saniya, da wata mata tana share hawaye da alama mahaifiyarta
ce, sai da Sheik ya kalle ta ya gane ido ɗaya ne da ita.
Aljannunta ne suka tashi, ɗaki aka sakawa Sheik ita duk da yana jin ɗarɗar haka ya shiga
mata ruƙiyya kafin a gama ruƙiyyar ta haɗa shi da ƙasa sau uku, yana cikin bayan ya fitar mata
da aljannun sai ta miƙe ƙafa ta ƙura masa idonta guda ɗaya har sai da ya tsargu, ko kuɗin
sadaka bai karɓa ga burinsa kawai su fitar masa ita.
Da daddare yana zaune ya gama cin abinci sai ga Mai Gari, Liman, da wasu dattijai guda uku,
suka zauna aka sake gaisawa, Mai Gari ya yi gyaran murya ya ce
"Ya Sheik a matsayina na Mai Gari na zo da wata buƙata" Buɗar bakin Sheik sai cewa ya yi
"Haba Mai Gari ai babu abin da za a nema a rasa a wajensa, har da cewa ya yi alƙawari tun bai
ji abin da ake buƙata ba.
Mai Gari ya ce
"Wannan yarinyar da ka yi wa ruƙiyya da yamma mai ido ɗaya... Gaban Sheik ne ya faɗi
tunaninsa ko za a ce aljannun ne suka sake tashi, saboda dama dai ya san lafawa suka yi ba
wai sun bar jikinta bane.
Mai Gari ya cigaba da cewa
"Aljannu sun karɓi ƙarfin jikinta, sun hana ta sakat sun ce sai an ɗaura mata aure da kai, in ba
haka ba wani gagarumin bala,i zai sauka a garin nan sai sun kashe rabi da kwatar jama,ar
gari...
MAMAN AFRAH
09025576222
[7/11, 4:08 PM] Mom mashkur & Afrah: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko
gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture
👳🏻♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 11
*RAHMA*
Tsabar firgici da mamakin furucin Ma'aruf tsaye ta miƙe, shi kuma Ma'aruf ganin Sulaiman sai
hakan ya sanya ya shafawa idanunsa toka, don a yau ya ci alwashin babu gudu babu ja da
baya, dole ya bayyana sirrin zuciyarsa ko ta halin ƙaƙa ko da kuwa hakan zai zama sanadiyyar
afkuwar gagarumar matsala.
Hannu biyu ya saka a aljuhunsa ya yi wata irin tsayuwa ta yaran zamani, in ban da su da
suka san shi kuma suka raina masa hankalin cewa shi baƙauye ne babu wanda zai ce ya taɓa
zama a wani ƙauye, cike yake yau da kwarjini haɗe da haiba kyawunsa ya ƙara bayyana, yana
sakin wani shu'umin murmushi, yana mai kafe masoyiyar tasa Rahma da idanunsa da ta ji sun
zame mata tamkar miki, don yau sai ta ji ya mata wani kwarjini sai dai ba za ta bar kwarjininsa
ya rinjayi zuciyarta ba, dole za ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, saboda ma kar ya yi gigin
furta wata kalma a gare ta.
Mummy kuwa kallon ƙasƙanci da raini ta shiga jifan Ma'aruf da shi, ganin yana tsaye a inda
tilon ƴarta take sannan ga ɗan minista da take fatan ya zama sirikinta wato Sulaiman.
Sulaiman kuwa tun lokacin da ya ji furucin Ma'aruf sai zuciyarsa ta buga, tsanar da ya yi wa
Ma'aruf ɗin ta ƙara linkuwa a zuciyarsa, a gefe ɗaya su duka yana jifansu da kallon tuhuma,
musamman tauraruwar tasa wato Rahma.
Rahma ita ta rasa ma abin cewa don furucin Ma'aruf ya bata ɗimbin mamakin da ta kaaa furta
uffan duk da a ƙoƙarinta na ganin ta masa tatas.
Mummy ce ta katse shirun da ya ratsa wajen, da kuma kallon tuhumar da wasu suke jifan
wasu, sannan da zulumi da taraddadin da zukatan wajen suke ciki ta ce
"Ma'aruf lafiyarka kuwa, wanann wane irin daƙiƙanci ne? Ko an faɗa maka bakin rijiya wajen
wasan makaho ne" Ta faɗa tana masa alama da hannu na tambaya. Amma abin mamaki
maimakon ya girmama ta kamar yadda yake yi a kullum sai ta ga ya ɗan murmusa ya ce
"Mummy ina baki haƙurin furucina sai dai, furucin da zan yi yanzu zai sha gaban wanda kika
saurara, amma sai dai ina so matsayinki na Mummynah ki tayani neman karagar mulki a zuciyar
Rahm... A ƙufule Mummy ta ɗaga masa hannu alamar dakatarwa tana huci kamar kumurcin
zaki ta ce
"Allah wadaran naka ya lalace wai jakin dawa ya ga na gida, an faɗa maka ni ina da wani ɗa a
duniya da ya wuce Rahma? Idan mafarki kake ka falka daga mummunan mafarkin da kake yi,
ka wartsake idanunka ka san da wa kake magana, Rahma ta fi ƙarfin talaka baƙauye irinka ka
taka a sannu in ba haka ba za ka ɗakko ruwan dafa kanka" Rahma ce da ƙwallar takaicin
furucin Ma'aruf ya cika mata ido saboda takaicin cewa yana neman karagar mulkin zuciyarta ta
shiga nuna shi da yatsa ta ce
"Wallahi ahir ɗinka, ko giwa ta faɗi ka sani ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, wallahi, wallahi,
wallahi, idan har baka taka a sannu ba za ka yi da na sani na har abada, rainin ma ya yi yawa,
ni Rahma kake wa wannan furucin? Ina so ka sani matsawar baka dawo cikin hankalinka ba to
za ka taka dakalin da yake ɗauke da ruwan ɗanyar kuɓewa, a ƙarshe ka zame ka karkarye a
banza a wofi" Ta faɗa tana hayayyaƙo masa.
Sulaiman fara takawa ya yi a sannu sai da ya zo har gaban Ma'aruf ya tsaya, kallon kallo aka
shiga yi, tsakanin Ma'aruf da Sulaiman, shi Sulaiman ransa a mugun ɓace shi kuma Ma'aruf
yana sakin wani shu'umin murmushi.
Hannu Sulaiman ya sanya a cire glases ɗin fuskarsa, ya kafe Ma'aruf da idanunsa da takaici
ya sa suka yi jawur, yana masa wani kallo irin na raini, ba komai yake baƙanta masa zuciya ba
sai yadda Ma'aruf ya fi shi kyau da cikar haiba, kai zai iya cewa Ma'aruf ya fi shi komai kuɗi ne
kawai zai Sulaiman zai faɗa masa.
Sai dai inda gizo yake saƙar shi ne, Sulaiman babu ɗigon ko da son Rahma a zuciyarsa, ba
komai bane a zuciyarsa sai yaudara yana so ne kawai ya raba ta da mutuncin ta, shi ya sa ya yi
amfani da zaƙin baki da nuna soyayya da kulawa na ƙarya har ta amince da shi, a halin yanzu
duk ta rabu da samarinta duk da dama su ɗin ma za ni ce ta tarar da muje mu, ma'ana babu
wani na kirki duk ƴan ƙarya ne ƴaƴan manya masu kuɗi.
Baƙincikinsa ɗaya shi ne ya fahimci matsawar Ma'aruf ya furta so ga Rahma to ko da a ce
bata son sa to zai yi iya yinsa ya ga ya hana shi cim ma burinsa, haka ya fahimta saboda ya
lura ko a cikin gidan za su hira, sai yake neman zame musu ƙadangaren bakin tulu, yana hana
su rawar gaban hantsi.
Ba ma wannan ba kawai zuciyarsa ta bashi raina masa hankali suka yi, ma'ana ya fara zargin
Rahma tana son Ma'aruf ne in ba haka ba ya zai zo ya tarar da su a lambu tare ya yi shiga mai
kyau, sannan shi da kansa ya ji Rahmar tana faɗin wasu kalmomi na soyayya ga Ma'aruf shi ma
kuma Ma'aruf ɗin ya mayar da martani, zuciyarsa ma ta bashi cewa zuwan Mummy wajen ne ta
musu alama da cewa ya iso wajen shi yasa suke masa wasa da hankali suke raina masa wayo.
Ya dara tunanin kawai ma amfani ake yi da shi ana cin kuɗinsa.
Hannu Sulaiman ya kai ya dafa gefen kafaɗar Ma'aruf amma sai Ma'aruf ya saka hannu ya
ɗauke hannun Sulaiman daga kafaɗarsa ya warɓar da shi, daga Rahma har Mummy baki suka
saki saboda yau ɗaya Ma'aruf ya sauya musu, ran Sulaiman ne ya ƙara ɓaci a ganinsa wannan
baƙauyen har ya kai ya masa haka? A ƙufule ya nuna shi da yatsa ya ce
"Kai ƙaramin ƙwaro, ƙaramin ɗan iska, ina so ka sani ko da mai ka zo an fika, ruwa ba sa'an
kwando bane kuma ni na fi ƙarfin in yi tarayya da kai a wajen mace ɗaya... Rahma jin wannan
furucin sai ta lumshe idanu, tare da sakin wani murmushi saboda ta lura Sulaiman zai ladabtar
sa Ma'aruf ko da kuwa da kalamai ne, Mummy kuwa jinjina ta hau yi wa Sulaiman a zuciyarta,
tana jin gwara ma a bar shi da Sulaiman ɗin ya nuna masa kudu ba arewa ba ce.
Sai dai me? Sai suka ji saɓanin abin da suke tunanin ji wato Sulaiman ya cigaba da cewa
"Don haka in dai Rahma ce ka je na bar maka" Daga Mummy har Rahma sai da gabansu ya yi
mummunar faɗuwa, suka shiga zare ido jin za su yi babbar asarar ɗan masu kuɗi, duk da suna
da kuɗi amma sun san Sulaima tsani ne a wajensu na cim ma wasu burika a rayuwarsu.
Da sauri Rahma ta matso tana kafe Sulaima da idanu ta ce
"Ka san mai kake faɗa kuwa Baby? Yanzu my love wannan ƙazamin kake yi wa furucin ka bar
masa ni, in ce dai wasa kake ko?" Ta faɗa tana kallonsa don so take ta ga ya wawwanke fuskar
Ma'aruf da kyawawan maruka, don ya zame masa izna kuma darasi a nan gaba, don su basa
so su masa wani abu cibi ya zama ƙari idan Daddy ya dawo.
A zuciye Sulaiman da yake jifan Rahma da kallon tsana ya ce
"Ke dalla malama dakata! An ce miki kowa sakarai ne, ko kin ɗauka ni ɗin ma sakarai ne irin
samarin da kika yaudara saboda kin same ni kika sallame su? To ni da hankalina, na san abin
da nake, ni za ki rainawa hankali, in zo in same ki kuna soyayya amma ki nuna mini bariki, to ni
nan na fiki sanin bariki idanuna a buɗe suke yadda bakya zato" Ya faɗa yana hayayyaƙo mata
tamkar zai kai mata duka.
Ma'aruf ya ji daɗin hakan ya san kuma ko da bai auri Rahma ba to tabbas ya cire mata mugun
iri a rayuwarta, saboda ya san Sulaiman mayaudari ne ba don Allah yake sonta ba, yana
amfani da ita ne saboda cim ma wata dama tashi daga ya samu biyan buƙata ya tabbatar zai
cikawa rigarsa iska, in ma bai barta da guzurin ciki ba.
Mummy ce ta dafe ƙirji ta ce
"Haba Sulaiman ya za ka yanke wannan ɗanyen hukunci marar ma'ana da madafa? Kai kanka
ka san Rahma ta fi ƙarfin wannan bagidajen, kai take so kuma kai za ta aura" Juyowa ya yi
yana yi wa Mummy kallon baki fahimci rayuwa ba.
Ma'aruf ya ce
"Mummy dama fa ba son ta... Kafin ya kai aya Mummy ta ɗaga hannu ta kai masa wani
mummunan marin da ya sa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 14