Share this page
ce "Ban son cin abinci yau Daddy fruit nake ci" Murmushi ya yi yana riƙe da ita suka ƙarasa tsakiyar falon. Yaya Ma'aruf cike da girmamawa ya shiga gaishe da Hajiya, amma ta amsa kamar bata so, don ita har yanzu kallon wanda bai waye ba take masa, kallon baƙauye, ita dama ba don dai ɗan gidan ƙanin mijinta bane kuma mijinta yana jin maganar Yayansa da tuni ta kore shi daga gidan. Ganin Rahma ta tashi tsaye tana wani buga ƙafa alamar ɓaci, wai Daddy ne zai cigaba da bata fruit, da sauri Yaya Ma'aruf ya ɗauke kai, ganin kayan sun kama mata jiki, kuma ya san shi ba muharraminta bane. Sallama ya musu yana shirin juyawa ya ji Rahma tana cewa "Daddy ka ce Yaya Ma'aruf ya miƙo fruit ɗin ka cigaba da bani" Ta faɗa lokacin da Daddy ya zaunar da ita kusa da shi yana lallashin ta yana faɗin zai bata har sai ta ƙoshi. Idanu Yaya Ma'aruf ya runtse jin rainin wayon wannan, ba don yana son ilimi ba, kuma yana da burin ya je garinsu ya kawo musu cigaba daga jahilcin da suke ciki da tuni ya bar gidan nan ya koma ƙauye. Maganar Daddy ce ta katse mata tunani. "Ma'aruf miƙo fruit ɗin can na ƙanwarka" Daddy ya faɗa hankalinsa yana kan Rahma da take ta zuba masa shagwaɓa, yana mugun son ƴar tasa. Haƙori Yaya Ma'aruf ya sanya ya danne leɓensa na ƙasa yana jin takaicin wanann aiken, amma babu yadda zai yi, kasancewarsa mai biyayya, cike da ladabi ya je gaban Hajiya ya ɗauki tiren, Hajiya tana aika masa wani kallo saboda ita kawai bata ƙaunarsa. Sai da ya je zai ajiye amma Rahma ta miƙo hannu ta ce ya bata plate ɗin, ya mayar da tiren kicin. Daddy bai ji daɗin abin da ta yj ba amma babu yadda zai yi don ba ya son abinda zai mata ran Rahma. Haka Yaya Ma'aruf ya danne zuciyarsa ya ɗauki plate ɗin fruit ya miƙa mata ashe dai bata riƙe ba, ai kuwa plate ɗin ya kuɓuce gabaɗaya kayan marmari suka yi masauki a jikin fararen kayan Rahma, duk ruwan kankana ya fito jawur a jiki, tana kallon jikinta ta fashe da wani kukan ɓaci, da sauri Hajiya ta tashi har tana neman yin tuntuɓe, tana zuwa vata yi wata-wata ba ta ɗaga hannu ta saukewa Yaya Ma'aruf yatsunta biyar a kumatunsa, kuncin ya safe cike da mamaki ya ɗago idanu yana kallonta Daddy kuma ya miƙe tsaye, duk da ya ji zafin abin da Ma'aruf ya yi na zubaw Rahma kayan marmarin a jiki amma kuma ya ji haushin marin da Hajiyar ta wanke Yaya Ma'aruf da shi a ganinsa abin da ya yi bai kai a mare shi ba, hakan ya sa Daddy ya ce "Hajiya... *SHEIK* Yana cikin wannan halin wandonsa jargaf da fitsari, ya fara ganin wasu ƙananan yara kamar jarirai amma tsaye suke a kan ƙafafunsu suna doso shi, kusan su goma, da alama daga cikin garin suke, abin da ya tsorashi ma babu wani mai sutura a jikinsa su duka tsirara, bai gama tunanin jinsin mutane ne ko na aljannu ba sai ya ji budurwar nan ta ƙofar gidan da take kiranshi ta ce " Sheik waɗannan ƴaƴanmu ne ni da kai, wanda na haifa maka su daren yau, gasu nan zuwa kowanne ka masa kuɗuba ka raɗa masa suna" Galala yake kallonta, ganin jariran suna dab da zuwa suna faɗin "Baba Sheik" Kawai Sheik ya yanke shawarar ya tsira da rai da lafiyarsa, don da alama wanann yaran suka rafke shi wato suka ɗane jikinsa kowa fisgar inda ya samu zai yi ba lallai su bar shi da fatar jikinsa bama, fakar idanun budurwar yayi kawai sai ya zura da uban gudu, ganin wata kwana sai kawai ya sha kwanar, amma kamar almara sai ya ji ƙarab takun gudu a bayansa, haka ya tabbatar masa da biyo bayansa ake yi, ganin wata bishiya ya yanke shawarar hawa kanta, a nashi tunanin idan ya hau bishiyar in wanda suka biyo shi sun zo sun wuce sai ya sakko in ya so ya gwammace ko gadin gidan wasu ya je ya yi da ya zauna a wannan bala'i da tashin hankali, da shegen kaɗayi da son abin duniyarsa ya kawo shi ciki. Yana hawa bishiyar yana jin wani santsi dakyar ya samu ya haye sai da ya hau can sama, ya samu waje ya zauna, sai ganin jariran nan ya yj sun tasho suna gudu suna kiransa, haɗe da wanann budurwar mai fitila, suka zo suka wuce bishiyar, wata dariya Sheik ya fashe da ita marar sauti a zuciyarsa ya ce. 'Ashe aljannu ma ana iya guje musu, ka ga sakarkaru wato ni ina saman bishiya ku kun wuce kuna kirana, wannan shi ake kira hotiho!' Yana kallonsu har suka yi nisa kifta idanun da zai yi sai ya neme su ya rasa a fili ya ce "Ai indau zan samu cikar burina to da in fallasa kaina a gane MALAMIN BOGI ne gwara kullum in ke kwana a saman bishiya, a to don na ga wajen zama ni sai in ke kwantawa ma a kan bishiyar in kr baro musu gi... Jin an zungure shi daga bayansa shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake, cike da faɗuwar gaba ya ɗan waiwaya, jariran nan ya gani su duka suna kan bishiyar da yake muryar ɗaya mai amo a cikin su ita ta katse shi da faɗin "Baba Sheik muna ta nemanka ashe dai ka zo gidanmu" Jin an ambaci gidansu sai lokacin hankalinsa ya kai ga kallon bishiyar da yake kai a nan ya ga bishiyar kuka ce wato matattarar aljannu" Hawaye ne suka taru a idanunsa, ya tashi dakyar jikinsa yana karkarwa, rigar wuyansa ya ɗakko ya ɗaure tsantsa, bai jira komai ba a fili ya ce "Innal hamda, wal ni'imata laka wal mulk, la sharikala, Allahu akbar! " Yana gama faɗar haka ya yi tsalle ya diro daga saman bishiyar nufinsa sai dai su tsera, da aljannun yaran, amma abin mamaki maimakon ya ji shi a ƙasa sai ya ji shi ya dira a kan hannaye, yana dubawa ya ga wannan jariran ne su duka suka masa ɗaukan makarar mamaci. Babu damar guduwa ya zubawa sarautar Allah ido, don shi kansa ya san riƙon ma ba na jarirai bae, tamkar wanda aka tara ƙattan maza. Suna tafiya suna faɗin "Mama mun ɗakko miki Babanmu" Sheik kuwa sai ruwan ido yake tamkar an buɗe famfo. Suna zuwa ƙofar gidan suka samu wannan dai budurwar, shi bai san wane irin tunani zai yi ba ma. Tana ta musu sannu da kawo Babansu ta matsa gefe suka shige da Sheik yana ji yana gani, suna gama shiga, ta rufe ƙofar gidan ta saka sakata. Ɗakin da Sheik ba a can ya sauka ba can aka nufa da shi, suna shiga suka zaune da shi yana ta kallon ikon Allah, da suka ajiye shi suka fara kama jikinsa kowa yana mamula, guda biyu sun kama breast ɗinsa suna sha wasu kuma jikin fatarsa da babu riga, a zuciyarsa ya ce 'Wai ni Ibra yau ni ɗiyan aljannu suke mamular fatar jikina da bakinsu marar haƙori, har da masu sha mini mama, na ga ta kaina duk tsorona amma yau an ƙure mini gudu' Ya faɗa a zuciyarsa hawaye suna zuba shaaaaa. Yana nan zaune suna ta faman tsotsarsa, idanunsa a rufe don ya lura duk idanunsu babu ƙwayar ido a ciki. Idanun a rufe ya ji kamar daga saman matar nan ta ce "Ka raɗa musu suna ka zo mu kwanta dare ya yi" Cike da faɗuwar gaba ya buɗe, ya ganta zaune a bakin wani gado mai kyau. Haka ya ringa kai bakinsa wajen kunne jariran yana musu gwalan gwalantun larabcin da bai san mai yake faɗa ba bare ya san addu'a ce ko mene ne. Abu ɗaya ya sani duk wanda ya gamawa gwalan gwalantun sai dai ka ji daga ƙarshe ya ce, Mamuda, Lawwali, Amiru a haka ya gama raɗawa kowa suna. Yana gamawa suka tashi suna masa bye-bye suna cewa sai sun dawo, haka budurwar nan ta miƙo masa hannu, wannan karon a zuciyarsa ya ce zai gwada sa'arsa don yadda ya ga za su kaɗaice a gado da aljanna yana tsoron wani abu ya wakana a tsakaninsu ma'ana ta je ta masa cikin gaske, tun da yanzu ma gashi tana cewa ƴaƴan can nasa ne. Ganin ta fara wani abu kamar mai shirin yin dambe sbai san lokacin da zuruf ya tashi tsaye ba, sai kawai ya ga ta fara sawaya ta koma tsohuwa tukuf, a guje ya fito daga ɗakin, ɗakinsa ya shige, yana haki yana shiga ya banke ƙofa ya saka sakata, kan katifa ya faɗa ya ja wani tsohon bargo da ya gani a kan katifar, da gari lafiya ƙalau ne ya san, sai dai ya cewa ƴan garin larabawa basa shiga tsohon bargo, amma yanzu da yake neman mafaka yake gani yake ko cikin kashi aka ce ya shiga babu musu zai shiga kashin in da hali har wanka sai ya yi da kashin.. Tun da ya rufa da bargon nan yake ta faman gumi amma bakinsa sai warto addu'a yake wacce bai san wace iri ba ce shi dai fatansa ya tsira dafa halin wannan, sai ya ji a ransa zai bar garin Ƙundu a gobe amma in ya tuna irin kaji da shayi mai kauri da zai je sha to tabbas sai ya ji zai jure komai. Tun da ya rufa shi ba a kwance ba, shi ba a durƙushe ba kawai dai ya yi goho ya nutsa kansa a katifa, a haka yake ta jin ife-ife da guje-guje wani lokacin ya ji an buga ganga wani lokacin a ƙwala masa kira, fitsari ya yi wajen kala biyar, har sai da aka fara kiran sallar asuba, sannan ya ji komai ya lafa, can kafin shigar masallaci ya fara jin tashin muryoyi a ƙofar gidan, yana ji ana ta bugawa, amma ya ƙi fitowa ma don shi yanzu babu wanda zai kira shi ya je, gani yake aljannu ne, duk da yana ganin rashin fitarsa masallacin asuba barazana ne ga maluntarsa, amma dai a halin da yake duk ya yi wurjanjan, da kuma jiki da fitsari jargaf in ya fita ya buɗe ƙofar abun kunyar sai ya fi na ƙin zuwa masallaci. Sai da ya ga rana ta fito tangararau ya tashi ya fito har lokacin rigarsa tana ƙugunsa a ɗaure, ya since a zuciyarsa yana faɗin 'Wuya in ji tsula, yau malamin balarabe na ƙasar Yemen ya ga ta kansa cikin dare' Ya faɗa yana shafo breast ɗinsa da suka sha damƙa a bakin aljannu. Dakyar yake tafiya haka ya je ya buɗe ƙofar gidan sannan ya shiga ɗaki ya saka hularsa ta gashi da gemunda sajensa, yana gamawa ya shiga bayi ɗaure da towel bayan ya kai ruwa, jikinsa ya shiga sallewa da daddaɗan sabulun bulicin mai ƙamshi, ya gama saɓa jikin bai ɗaureye ba, dib ya ji wani abu ya faɗo daga sama, yana dubawa ya ga kunnen jariri ne. A can ƙofar gida kuwa Liman ne da Mai Gari suka zo da manyan ƙartai za a ɓalle ƙifar gidan a shiga a ga ko lafiya sabon malamin balarabe bai fito sallar asuba ba, kuma an zo an buga masa shiru, sun san dai malamai kamar Sheik ba ya ƙi yin sallar jam'i da gangan ba su da suke ganin an kawowa ƙauyensu waraka daga jahilci, amma har rana ta yi ba a ganshi ba. Ganin kunnen da Sheik ya yi, hakan ya yi daidai da saƙa ƙafa da wani ƙaƙƙarfan saurayi ya yi ya hankaɗa ƙofar gidan, kasancewar Sheik sakatar ya cire bai buɗe ƙofar ba. Buga ƙofar da ta daki bangon bayin shi ya ƙasa assasa tsoro da ruɗanin da Sheik yake ciki, tunaninsa ya bashi aljannun ne suka kawo masa ziyara, don ya san yadda mutanen garin suke girmama shi, babu yadda za a yi su banko masa ƙofa haka har ta gwaru da bango, towel ɗinsa ya fisgo a inda ya rataye ya naɗa a ƙugunsa ko ɗaurewa bai yi ba, ya bazamo da gudu daga banɗakin takalminsa ma ɗaya can ya barshi a bayin, sannan ga jikinsa kumfar da bai wanke ba, fitowarsa a rikice ya nufi ɗaki ko kallon hanyar ƙofar gidan bai yi ba burinsa kawai ya shiga ɗaki ya kulle, Mai Gari da tawagasarsa su Malam Liman ganin abin da yake faruwa sai suka tsorata, sun san duk abin da zai sanya Ya Sheik babban malami balarabe gudu to ba ƙaramin abu bane, ganin shi da ya san qur'ani da ayoyin Allah, da addu'o'i yana gudun ceton rai ina ga su ƙasurguman jahilai. A take aka shiga ƴar tsere zuwa ɗakin Malam inda ya nufa, sai suke ganin nan ne wajen tsira, samari guda biyu sai Malam Liman da kuma Mai Gari aka fara rige-rigen zuwa ɗakin Malam Sheik, shi kuma Sheik sai da yana dab da shiga ɗaki ya lura da tawagar Mai Gari, ganinsu da gudu a kiɗime sun nufo hanyar ɗakinsa alamar kamar an biyo su, sai ya yi tunanin gari ma babu lafiya, tunaninsa su ɗin ma daga waje aka biyo su suka taho wajensa kasacewarsa malami basu san a halin da ya kwana ba, basu san shi bacci ma tun na farkon dare bai runtsa ba haka ya kwana tsakanin waje da cikin gida, yanzu ma yana wanka yana son bayan ya yi wanka ya yi alwala ya yi sallah don yadda jikinsa yake sharkaf da fitsari sai ya yi wanka. To sai kuma aka samu an jefo masa kunnen jariri a banɗakin, bayan ya fito hallaw gashi ya ci karo da su manyan garin su ma sun zo. Da Sheik da Mai Gari aka yi karo wajen shiga ɗaki, shi Mai Gari yana fatan kar Malam ya ƙulla musu salalan tsiya wato ya shige ya banke ƙofar ɗakin, don su tunanin komawa baya ma su fita daga gidan hakan bai zo musu a ƙwaƙwalwar su ba, bare ma sun san tun da aka samu matsala a masaukin malam to garjn ma yana dab da rikicewa, don wani sa'in gabaɗaya aljannu garin suke rikitawa. Karon da suka yi babu wanda ya lura, kowa ta kansa yake, a haka Malam Liman ma ya totsu suka zama su uku a bakin ƙofar suna ƙoƙarin shiga, ƙofar ta musu kaɗan kuma kowanne ya kasa dakatawa wani ya fara shiga. Samarin nan ma suna jira su ma su shige. Malam Liman yana kai kansa suka yi gware da goshin Mai Gari, Sheik ne ya fara nasarar shigewa ɗakin, sai dai da takalmin nan ƙafa ɗaya ya shige santsin ledar tsakar ɗaki ya kwashi Sheik, sai gashi wancakal a gefe, yana ta yaƙi da towel ganin bai masa tsirara ba. Su kuea su Mai Gari basu lura da wani towel ɗinsa ba bare su kawo zai yi wani tsirara, don gani suke tamkar a filin ƙiyama inda ake cewa kows ta kai - ta kai yake. Sheik da rarrafe ya ƙarasa saman katifa, sai Mai Gari da Malam Liman suka mara masa baya, samarin nan ma suna shiga ɗayan ya banka ƙofar, su duka cakuɗe a kan katifar, Sheik ya warto tsohon bargon nan, zai rufa ai kuwa Mai Gari ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da bargon hannun Sheik ba, nan ya shiga yaƙin warta don ya rufa shi ma, haka Malam Liman ma, ya shiga jan bargon da ya gama shan duniyarsa, kasancewar bashi da ƙwari sai ya yage a biyu, Malam Liman ya ɗauki ɓangare ɗaya, Mai Gari da Sheik suka shiga ɗayan, samarin nan suka totsa kawunansu a babbar rigar Liman... 😂😂😂😂😂 Na ba kaina daria yau Allah sa ju dara amma akwai cakwakiya. Mu haɗu next page akwai gwarama, za ku ji yadda Sheik zai kare kansa saboda rainin wayo, su kuma sai su bada kai bori ya hau. MAMAN AFRAH 09025576222 [7/2, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 4 *SHEIK* Suna tunanin samun nutsuwa amma abin ya ci tura!. Abin da yake faruwa shi Sheik ga tsoron kunnen da ya gani a banɗaki ga kuma tunanin yadda ya hango su Mai Gari a sukwane, shi bashi da nutsuwar da za tambaye su ba'asin gudunsu tun da har ya ga suna tseren shiga ɗaki da masu garin to tabbas ya san wataƙila cikin garin yana can a rikice kamar filin yaƙi, kuma ya san kowa shi zai jira, shi ma kuma ga a halin da ya kwana ga kuma a halin da ya falka ko sallah bai yi ba, kenan lamarin garin Ƙundu ba ƙaramin lamari bane in dai a ce aljannu da ranar gari ma sai sun addabi jama'a to lallai akwai sake. Kowa gabansa faɗuwa yake, shi Malam Liman sai yanzu yake jin da na sani da sun juya baya sun koma cikin gari, amma gashi sun shigo wannan gida mai ruɗani bayan sun san cewa wannan gidan shi ne kan gaba wajen matattarar aljannu amma kuma ƙarfin gwiwar tasu shi ne Sheik to shi ma babu yadda yake, sun lura a ruɗe yake ruɗun ma iya ruɗewa, bayan shi suke ganin zai kawo musu ɗauki amma sho ma kamar dai yana neman ɗaukin ne. Mai Gari kasancewar shi kaɗai ne a cikin yankin bargon da ya shiga, duk da a katifa ɗaya suke amma sai yake jin tsoro yana ƙara baibaye shi, ya so a ce bargo ɗaya suke da malam balarabe mai jar fata kuma babban malami wataƙila aljannun sa yi sassauci a lamarin. Samarin nan guda biyu sai numfashi suke ƙasa-ƙasa kwata- kwata a ruɗe suke. Ya Sheik shi idan ya tuna da kunnen da aka jefo masa a banɗaki sai ya ji cikinsa ya murɗa alamar gudawa, yanzu haka yana ta fafutuka wajen danne wata guntuwar tusa da take son ta fito masa wacce yake da tabbacin matsawar ta fito kashi zai iya kuɓuce masa. Wannan dalilin ne ya sa yake ta mutsu-mutsun dannewa, don ya san matsawar ya saki tusar to su Mai Gari za su ji wari kuma hakan kamar zubar da kimarsa ne a matsayinsa na bababan malami, shi ba ma wannn ne matsalar ba yadda suka biyo shi suka cika masa ɗaki, ya san cewa yanzu kowa shi yake son ya kawowa ɗauki bayan shi kansa ta kansa yake. A daidai wannan lokacin kuma ɗaya daga cikin samarin nan ne ya ji ɗayan ya janye masa inda ya rufu don haka ɗan jijjiɓin yaƙi ya kaure a tsakanin su biyun, shi ɗayan so yake ya rufe har ƙafafunsa, shi kuma ɗayan an janye masa don kansa ma yanzu a tantagayyar waje yake, wannan ya sa yake ganin va zai yarda ya ɗauki dala ba gammo ba. Hakan ya sanya suke ta jaye-jaye da rigar Malam Liman wamda fitsari ya cika masa mara, duk fusgar rigarsa ɗaya da suke barazana ne ga mararsa da take cike da fitsari, hakan ya sa ya damƙe baki, a zuciyarsa yana faɗin 'Lahaula wala ƙuwwata, kar ku mini haka ƴan samari, ina zan kai wanann abin kunyar a ce limamin gari guda amma ya yi fitsari a wando, ku taimake ni kar ku kunyata ni' Ya faɗa a zuciyarsa yana wani damƙe idanu tare da haɗe ƙafafunsa waje guda yake fafutukar matse su. Ɗayan ne ya fisge rigar da ƙarfi ya zungura kansa wanda kan nasa yake a saitin mazaunan Malam Liman, Malam liman ana zungurar mazaunansa ya ji guntun fitsari kaɗan ya kufce masa da sauri ya sake haɗe ƙafafun don ya lura in bai yi da gaske ba sai an saka shi ya saki fitsarin nan duka. Hannu ya miƙa ya sakarwar kan wannan saurayin wanda yake kusa da mazaunansa, ya sakar masa ranƙwashi a zuciyarsa yana faɗin 'Shegun yara, kamar da ubanku muka haɗa kuɗi muka sayi rigar, sai ja kuke kamar kun samu guga a rijiya' Ya faɗa a zuciyarsa yana jin da a lafiya ƙalaw ake ko iyayensu ba za su yarda su shiga rigarsa ba saboda yadda yake da kima ana girmama shi, a matsayinsa na Limamin garin. Saurayin nan da Liman ya kaiwa ranƙwashi, zafin ranƙwashin ya saka shi ƙara cukuikuye rigar Liman da gangan, dama shi ne wannan me ƙarfin da aka taho da shi zai buɗe ƙofar gidan, wato ƙaƙƙarfan. Jan rigar da ya yi shi ma ɗaya saurayin yana ta ƙoƙarin ja ya rufe kansa, sai ya zamana gabaɗaya an shaƙewa Liman wuyansa, jin shaƙe wuyan yana barazana ga maƙogwaronsa sai ya lanƙwasa kansa da sauri ya zame kansa daga cikin babbar rigar, hakan ya sa garin ya zame rigar sai kansa ya fita daga cikin bargon da suke tare da Sheik, shi kuma Sheik sai ya ja bargon ya ƙara duƙunƙune kansa, don yana a goho ne duk da yana jin kashin. Samarin nan jin Liman ya sakat musu rigar sai suka cure waje guda suka rufa, tun da yanzu ta ishe su sun rufa tare dama saboda tana jikin Liman ta musu kaɗan. Malam Liman kasancewar a firgice yake kuma a tsorace kansa yana fitowa daga rufar da yake sai idanunsa suka masa gizo da ganin Kakan Mai Gari wanann marigayin da aka binne a gidan, ya tsago jikin ƙofa yana tahowa sanye da likkafaninsa, ya ɗan duƙa kasancewar yana da ƙusumbi. A kiɗime Liman ya nayar sa kansa ya cusa a katifa haɗe da cewa "Wallahi marigayi kakan Mai Gari wato mai ƙusunbi ya tatso ta jikin ƙofa ya shigo ɗakin nan" Ya faɗa yana miƙa hannu a niyyarsa ya samo bargon da ya fito ya shiga, sai ya cafko towel ɗin jikin Sheik, Sheik kuwa jin furucin Liman na cewa Kakan Mai Gari ya shigo ɗaki, hakan ya tuna masa da jawabin da Audu ya masa a daren jiya na cewa Kakan Mai Gari ƙasa ta ƙi karɓarsa da ya mutu, saboda saɓon da yake yi, sai gida aka dawo aka masa kabari aka binne. Kenan wanda ake zuwa maƙabarta ana samun sa yana gefe kabarin da aka saka shi ma a gefe, to ba abin mamaki bane in aja ce yanzu ya taso da ƙafafunsa, wataƙila fatalwa ya yi. Tsabar ruɗanin da Sheik ya shiga yana jin an iska ta fara shiga jikin mazaunansa alamar mazaunan nasa a buɗe suke tantagarya, amma tsoro ba zai bari ya suturta su ba, don shi tunaninsa towel ɗin zamewa ya yi. Samarin nan jin furucin Liman sai suka rungume juna kamar sa zama mutum ɗaya, haka kowanne yake jin bugun zuciyar ɗan uwansa alamar dai ana cikin fargaba da tashin hankali, Malam Liman da ya samu towel ɗin Sheik ya rufe yana ta ƙoƙarin son ya ga ya samu ko da addu'a ɗaya ce cikin wanda ya iya don yake karantawa ko a zuciyarsa ce amma ji ya yi gabaɗaya ya manta komai a halin da yake ciki yanzu gani yake sunansa ne kaɗai zai iya tunawa. Yana wannnn halin ne ya ji saukar hannun Mai Gari a bayansa, wanda hakan ya sa ya ɗauka hannun marigayi mai ƙusumbi ne wanda ya masa gizo, duk tunaninsa a zahiri ya gan shi, hakan ya sa gumi ya shiga zarya a gabaɗaya ilahirin jikinsa tare da kufcewar wannan fitsari da yake ta dannewa, saboda yanzu an zo wajen da ba ta girma da martabarsa ta Liman ake yi ba, ana magana ne ta ceton rai tun da har yana ganin gawa ta taɓa shi, gawar ma ta marigayi mai ƙusumbi. Liman a zuciyarsa yake faɗin 'Allahu akbar! Tamu ta zo (Yana nufin mutuwa) Allah ka bamu ikon amsa tambayar kabari, Allah ni nake jan sallah a garin ƙundu ka bani cikawa da imani' Wannan yake ta maimaitawa a zuciyarsa. Mai Gari kuwa hannun da ya miƙa shi lalumen bargon Sheik yake yi, so yake ya koma cikin bargon Sheik ko ya samu salama a ransa, tun da yana ganin bargon Sheik za a samu tsari kasancewar malamin balarabe ba za a ce ruɗani ya hana shi addu'a ba. Jin ya sauke hannun nasa a jikin riga, kuma ya san dai Sheik bashi da riga suka shigo ɗakin, tun da idanun Mai Garin a rufe suke ba ya so ya buɗe bare ya ga fatalwar kakansa mai ƙusumbi, son ya fara tunanin ma kar dai mai ƙusumbin ya ce ya zo ya tafi da shi ne. Hannun da ya fara matsarwa a jikin Liman kasancewar rigar Liman ta shadda ce ta ci uban duniyar ta da tsinke, domin daga baya a yage take kasancewar ya ɗora babbar riga shi ya sa ba a ganin yagar, yanzu kuma da samarin nan suka sa ya cire babar rigar sai yagar ta bayyana a bayansa. Hannun Mai Gari ne ya shige cikin bayan Liman ta wanann yagar, hakan ya sa ya shafo bayan fatar jikin Liman. Liman mutuwar kwance ya yi don zuwa yanzu ma kawai bakinsa ne yake karkarwa kamar wanda zazzaɓi ya yi wa mugun kamu, haƙoransa suna haɗuwa da juna, saboda ya gama saddaƙarwa cewa fatalwar mai ƙusunbi ce ta dama masa baya take shafa fatarsa, ya san yau babu makawa da shi za ta koma lahira Mai Gari da sauri ya ɗauke hannunsa, saboda fatar da ya taɓa ya ji wani karsansan, alamar fatarsu ce irin ta baƙaƙen fata, ya san ta Sheik tana da laushi da santsi irin na larabawa, shi zai tabbatar da haka tun da jiya ya kama hannun Sheik mai laushi kamar na jarirai, bai san cewa tsabar amfani da allurai da magunguna da kuma sabulai na garan fata ne ya sa take duk a yanayin

Chapter 3 of 14