yi ya saka a gaba yana kallo, a haka matar tasa ta shigo,
ganin haka ta ce
"Mai Gari ya haka, kai da za a kai wa baƙo abu ka zauna ka saka a gaba, kana kallo kamar ka
samu wata sabon kamawa?" Yawun da ya taru a bakinsa ya haɗiye, kamar zai yi kuka ya ce
"Dama ina kallo ne saboda in kore kwaɗayin da nake ji" Ta ce
"Haba dai dama kallon abu yana kore kwaɗayi?" Ya amsa mata da cewa haka ne. Tana fita ya
kasa jurewa, cinyar kaza ya ɗauka guda ɗaya, zafi ne da ita dakyar ya ɗauka, ya kai baki ya
ciri tsokar ya cika baki da ita kamar daga sama sai jin takun matarsa ya yi da sauri ya rasa inda
zai saka cinyar kazar kuma ba ya so ya mayar cikin kwanon a kai balarabe ya gani an ci ko ma
dai ya ce ba zai ci guntun baƙar fata ba, ya san kuwa shi ne a ciki tun da dole a kama wata
kazar a yanka a dafa, in ba haka ba jama'ar gari su yi da shi a ace abu ya gagare shi. Da sauri
ya kai hamatarsa da yake ƴar shara ce a jikinsa sai ya zamana hamatar a buɗe ai kuwa yana
saka naman nan mai zafi ya danne hamatar ya matse ta, ya yi saurin goge hannun a jikin
rigarsa. Bidik Asabe matar Mai Gari ta shigo ɗakin ko sallama babu, muduk Mai Gari ya haɗiye
naman bakinsa da sauri ba tare da ko taunawa ya yi ba, gashi da zafi duk ya ɗane harshe.
Tana shigowa ta ce
"Mai Gari ga Audun ya zo" Idanu ya ɗan runtse jin zafin naman da yake ratsa hamatarsa ya
buɗe idanun cikin ɗan gigicewa ya ce
"Gonar za su tafi yin shuka?" Galala ta saki baki tana kallonsa ta ce
"Haba Mai Gari lafiyarka kuwa? Mu da ba a damuwan muke ba wane irin tafiya gona, kai fa ka
ce a kirawo shi zai kaiwa baƙo abincin" Wata ƴar dariya ya saki yana sosa ƙeya da ɗaya hannun
nasa ya ce
"Allahu akbar ashe fa haka aka yi ina jin mafarki na yi" Ya faɗa yana tura mata kwanon da jug
ɗin gabanta, saboda ya matsu ta fita ya cire naman hamatarsa ko ya samu sauƙin raɗaɗin zafin
yaji da na wutar da suka haɗe masa.
Kallonsa take da mamakin jin furucinsa da sauti ta suri kwanukan ta fito daga turakar tasa,
tana tunanin ko dai aljannun garin Ƙundu sun fara taɓa Mai Gari. Audu ta ba kwanukan ta juya
ta shige ɗakinta gudun tsautsayi ko ɗakin Mai Gari bata koma ba, a yadda ta ga yanayinsa ta
fara tsoron ya mata wani abu.
Mai Gari tana fita fa sauri ya ɗaga hamatarsa, naman faɗowa ya yi, amma tsabar raɗaɗin zafin
barkono da na wutar bai bi ta kan naman ba, illa barin hamatar da ya yi a ɗage ya karkata
bakinsa ya shiga hura iska a hamatar ko ya samu salama. Haka ya dinga yi sai da ya ji sawaba,
sannan ya ɗauke naman ya cinye ya taune ƙashin ya haɗiye, fitowa waje ya yi yana ƙwalawa
matarsa kira, bakam ta fito daga ɗaki tana ɗan ɗari-ɗari da shi, sai cewa ya yi
"Asabe anya baki cika yaji a wanann dahuwar naman ba?" Shiru ta yi tana kallonsa da mamaki
ta ce
"Yaji kuma Mai Gari? Kai da baka ci ba ya aka yi ka sani ko dai baƙon ne ya faɗa ya ce an cika
yajin?" Sai sannan ya fahimci ya yi ɓaran-ɓarama cikin wayincewa ya ce
"A'a fa, kawai dai tun ɗazu nake atishawar yajin da na shaƙa garin jin ƙamshin naman" Baki ta
taɓe ba tare da ta ce masa komai ba, ƙuri ta yi wa ƴar sharar jikinsa ganin wani abu kamar man
miya, fuska ya ɗaurr ganin tana kallonsa gudun kar ta harbo jirginsa, don haushinta ma yake ji
da ta zo ɗakin bai kurɓi shayin nan mai madara ba.
Ruwa ya cika a buta ya wanke hamatarsa da klin, don ita matarsa ɗakinta ta koma.
A ɓangaren Audu tun da ya je gidan da aka sauki Sheik, ya shiga rafka sallama ganin Sheik
ya rufe ɗaki, Sheik kuwa tun daga sallamar ya ji yawunsa ya tsinke don ya gane saƙon
abincinsa ne ya zo.
Sai da ya ɗan yi jim sakamakon mayar da mayukan bilicin ɗinsa da yake shafawa, don dama
yana shafawa da dare sai ya kwana da su, saboda an ce masa man ya fi bin jikin fata in ana
kwana da shi. Ƙofar ya buɗe ya fito yana cewa.
" Man yatahaddas(Waye yake magana?) Ya ce yana ɗan ƙara fitowa . Audu da bai san mai aka
ce ba ya juya da gayya zai koma, tun da ya ga ba hausa zai masa ba shi kuma babu abin da ya
sani na larabci. Cikin sauri Sheik ya fito ko takalmi babu yana faɗin
"Ya za ka koma gani fa ko ba wajena ka zo ba" Audu juyowa ya yi yana mamakin ɗan rikicewar
da malamin ya yi ya ce
"Dama abinci ne Mai Gari ya ce a kawo maka" Karɓa ya yi yana ta wasu zantukan larabci da shi
kansa Sheik ɗin bai san mai yake faɗa ba, Audu kuma sai ya ji abin ya birge shi, saboda a
rayuwa yana spn ya ji yana wani yare da ba hausa ba sai dai bayan hausa bai iya komai ba.
Sai da ya juya zai tafi, malam ya ajiye kwanukan ya bi bayan Audun wannan karon fa hausa
yake zabga godiya, saboda tsabagen rowa so yake Audun yana fita ya rufe ƙofar gida, don kar
wani ma ya zo yana cikin cin naman shi kuwa ba zai bayar ba. Audu sallama ya masa zai tafi
ganin ya kama ƙofa zai rufe Audu ya yi gyaran murya cikin yin ƙasa da murya ya ce
"Malam da kake barin ƙofar gidan nan a buɗe, in son samu ne ma har ƙofar ɗakin da kake ciki,
idan ma ba damuwa da sai ka ce a baka masu tayin kwana..." Tun kan ya kai ƙarshen maganar
Sheik ya katse shi da faɗin
"Ni bana buƙatar kowa ya zo ni kaɗai ma zan zauna" Ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce
'Aikin banza mutane da shegen kwaɗayi da son samu kuke, wato ka ga an haɗo kayan daɗi an
aiko mini shi ne za ka yi dibara don in ce ka zo ka kwana wato duk wani abin daɗi in ke kasawa
ina baka, to alharam giya a gidan liman'
Audu ya ce
"Malam wannan gidan da kake gani gidan kakan Mai Gari ne, mutumin nan ya kashe shekaru
masu yawa a duniya kafin ya mutu, tsabar tsufa da kuma malamin tsubbu ne mai aiki da aljannu
sai da gabaɗaya jikinsa ya yi fari gashi..." Sheik ya kalle shi ya ce
"Audu ni fa ban tambaye ka tarihin Kakan Mai Gari ba" Ya katse masa hanzari. Audu ya ce
"Ba tarihi nake baka ba, abin da nake faɗa maka ya danganci zaman ka a gidan, wato duk
jikinsa sai da ya yi gashi farin gashi, ko da ya mutu aka binne shi kullum sai raminsa kabarinsa
ya buɗe wataran a gan shi a wajen kabarin, to a ƙarshe dai sai rami aka masa a cikin gidan nan
aka binne shi, ka ga wancan zagayen da aka saka langa-langa to kabarinsa ne a ciki, kuma
gidan nan matattarar aljannu ne, tun daga ranar da ya mutu cutuka suka baibaye garin Ƙundu,
aljannu suka addabi jama'a mutane ɗai-ɗai ne basu da aljann... Gaba ɗaya Sheik ya jiƙe
sharkaf da gumi, tsabar ruɗun da ya saukar masa a zuciyarsa, hatta jikinsa ya ɗan fara
karkarwa amma bai bari Audu ya fahimci hakan ba, idanunsa duk sun faɗa tamkar wanda ya yi
sati bai ci abinci ba, bakinsa ya haɗa kalmomi yana shirin faɗin wani abu sai ya tsinkayi
maganar Audu yana faɗin
"Ni zan koma sai da safe"
Tsabar rowa da Sheik yake da ita sai dai ya ji duk da haka ba zai gayyaci kowa a taya shi
kwana ba, musamman ma da ya san ya riga ya cewa Mai Gari shi kaɗai zai kwana ya riƙe
ayoyin qur'ani.
Har Audu ya juya cikin haɗo jarumta ya ce
"Kuma baƙin da ake saukar da su a gidan fa?" Audu ya ce
"Basa yarda su kwana su kaɗai, sannan duk da haka suna faɗawa ƴan garinsu kaima ina ga
abin da ya sa Mai Gari bai maka bayani ba saboda ya ga kai babban malami ne" Kai ya shiga
gyaɗawa kamar ƙadangare, a haka Audu ya tafi ya bar Sheik, dakyar ya iya kara ƙofar kamar
dai ya jinginata amma bai rufe ta da ƙarfi ta rufu ba, bare a yi maganar saka sakata.
Yana juyowa daga zauren idanunsa suka sauka a kan kewayen langa-langar da aka ce
kabarin tsohon nan ne, ƙwiiiiwitttt wata tusa da bai shirya fitowarta ba ta ƙwace masa, tsabar
tsoratar da ya yi amma dai zai yi iya yinsa ya ga bai kunyata kansa ba, wajen cikar burinsa na
zama Malami a garin, tun da neman kuɗi ya fito dole ya jure.
Kwanukan ya ɗauka ya shige ɗaki ya rufo ƙofa, amma bai kulle ba, domin ya tsorata da furucin
Audu na cewa akwai kabari a gidan, sannan akwai aljannu. Duk halin da yake ciki yana buɗe
kwanon kaza sai ya manta komai, romo ya dangwala ya ɗanɗana wani ɗanɗanon farin maggi
da na daddawa ya ziyarci harshensa, tuni ya tashi yana wata rawar larabawa yana juyi a
tsakiyar ɗakin, gijif ya faɗa kan katifa a reran tsabar murna, ya tashi ya dawo gaban kwanon,
ƙuri ya yi wa kazar yana ɗakkowa yana ɗorawa a kan marfin, tsaf ya irga sai ya ga babu cinyar
kaza guda ɗaya, tsaki ya ja a ransa yana ayyana don maita sai da suka taɓa masa, amma dai
zai sanar da su cewa su a ƙasar larabawa idan za a ba malami kaza kai da ƙafa kawai ake
fitarwa amma ba a cire wani sassa ya faɗa saboda ƙarfin hali.
Tas ya cinye ya shanye wannan ruwan shayin mai uban yawa, dam ya ji cikinsa yana sakin
gyatsa, ta window ya miƙo hannunsa ya wanke, da yake akwai ruwa a ɗakin.
Sai da ya gama danne-dannensa a waya, sannan ya cire hularsa da saje haɗe da gemu ya
ajiye, rigarsa ya cire daga shi sai gajeran wando, kan nan sai sheƙi yake, magungun ƙwaya na
bilicin ɗinsa ya sha, ya kwanta, ya yi ɗai-ɗai a kan katifa, a take ƙoshin da ya yi da kuma samun
ɗaki mai iska ya sanya bacci ya yi awon gaba da shi, ko addu'a bai yi ba, shi ya sha'afa ma da
maganar da Audu ya faɗa masa.
Yana cikin bacci ya fara mafarki da ƴan garin a mafarkin suna cewa
"Sheik, wannan gidan... uhm... ka dai dinga karanta ayatul kursiyyu da suratul Jinn a kai -a kai.
Saboda kowa ya san gidan…” Duk a mafarki ne amma sai da gabansa ya faɗi
Cike da ruɗewa ya ce
" Mai gidan yake? Sheik ya tambaya yana jan carbi da azama.
"Dama... Uhmm... Komai lafiya ne. kawai gidan yana da...” Ba a faɗa masa mene ne a gidan ba
ya farka daga nannauyan mafarkin, gabaɗaya ya haɗa gumi gabansa sai faɗuwa yake.
Lalume ya hau yi a jakar kayansa, ya ɗakko wata rigarsa wacce ta fi jallabiyar da ya cire
tsawo, zai saka amma sai ya kasa saawa kasancewar ta wuyan rigar yake ƙoƙarin sakawa,
ganin bashi da nutsuwar sakawa sai ya rataya ta a kafaɗa, ko sallaya bai shimfiɗa ba ya zauna
a ƙasa ya kalli gabas yana karanta “A'uzubillahi”Har sai da numfashinsa ya fara daidaita.
Yana cikin wannan halin sai ya ji ƙara daga ƙofar ɗaki "Gum, gum, gum!"
Sheik ya yi firgigit! Ya miƙe yana ƙoƙarin lalumo wayarsa sai kawai ya kara ta a kunne yana
faɗin
"Wayyo Mai Gari a kawowa Sheik ɗin yemen ɗauki" Ya faɗa cikin raɗa, sai lokacin ma ya tuna
bashi da number Mai Garin ashe.
Wata iska mai sanyi ta fara ɗaga labulan windown, sai ya hangi wani haske kamar walƙiya ya
wulga, sai ya ji ana buga katako.
Sheik ya miƙa hannu ya ɗakko wani littafi da yake yashe a tsakiyar ɗakin, duk tunaninsa ba
qur'ani ne saboda tsabar ruɗun da yake ciki, buɗewa ya yi yana karantawa, kawai yana girgiza
kai yana cewa
“Wallahi ni dai ban taɓa ganin irin wannan ba a ce ba damina ba ana walƙiya Allah mun tuba"
Ya faɗa yana ɓarkewa da kuka marar sauti, sai dai har yanzu bai ji yana da na sani a kan fitowa
harkar maluntar bogi ta cutar mutane ba.
Yana a haka sai ya ji kamar ana tafiya, ma'ana ya fara jin taku a tsakar gidan, bai san lokacin
da ya yi cilli da littafin hannunsa ba, shi da yake kallon gabas sai gashi ya juya zuwa yamma,
bakinsa yana kaiwa da komowa, wannan karon, babu ƙalƙalar larabcin bogin nasa hausa ce
sak yake yi babu lanƙasa, shi kansa bai san mai yake faɗa ba. Yana cikin wannan hali ya ji wani
sauti ana cewa
"Sheeiiiik Ibra mun san kai ba malamin gaske bane na bogi ne, to ka sani muna sane da
zuwanka wannan ƙauye" Shi da yake zaune ya kalli yamma, bai san ya tashi ba sai ganinsa ya
yi a tsaye ya kalli kudu ƙafafunsa, suna barazanar kasa ɗaukansa, saboda karkarwar da suke,
tunaninsa ɗaya wai aljannun ne suka san da haka ko kuma shi tsohon da aka binne ne ya yi
fatalwa? Tun da gashi har sunansa na asali an kira shi da shi wato Ibra.
Wannan yasa Sheik ya buɗe ƙofar ɗaki da sassarfa, ya fito yana kwalalo ido kamar wanda ya yi
fashi aka kama shi. Ya yi gigin barin gidan da sassarfa.
Cikin sanɗa ya fito daga ɗakin daga shi sai gajeran wando, da rigarsa rataye a kafaɗa,
Yana fitowa ya ji gidan ya ruɗe da surutai kamar ana wani gagarumin taro, bai tsaya wata-wata
ba ya durfafi hanyar ƙofar gida, sai lokacin ya tuna lokacin da ya ɗauki wayarsa ta kawo haske
ya ga ƙarfe biyu da rabi na dare, amma da bala'in da ya fara fuskanta a gidan gwara ya fita.
Cike da tsoro ya buɗe ƙofar gidan, shiruuu garin tamkar babu kowa sai carar zakaru da yake
tashi da kukan dabobi lokaci zuwa lokaci.
Yana fitowa ya kalli, gabas da arewa ya ɗaga ƙafa zai fara sheƙa gudu ya tuna kansa babu
hularsa ta gashin larabawa mai haɗe da saje da gemu, sannan ƙafarsa babu takalmi, uwa uba a
tuɓe yake bashi da riga don bashi ma da nutsuwar saka rigar da take rataye a wuyan, amma
dai ya san ba ƙaramin abin kunya bane ya tafi cikin gari a haka a zo a ganshi da kai a
ƙwalƙwale, kai sunan zuwansa a haka mutuwa kusa don batu ne wannan na tonuwar asirinsa,
yana a wannan halin na cewa ko ya koma ya yi shigarsa ta balarabe, in ya so ko gidan ne sai
ya ce a sauya masa, duk da bashi da hujjar da zai faɗa a sauya masa tun da shi dai ba zai ce
yana tsoron aljannu ba, a wannan yanayin ne ya ji an ce
"Sheik, baby nah ina jiranka mu je mu kwanta" Idanu ya zaro yana mai juyawa inda ya ji sautin
wato ƙofar gidan da ya fito, wata budurwa ce tsaleliya riƙe da fitila mai haske, tana sanye da
sari na indiyawa"
Ga birni ga ƙauye, shi dai ba zai koma gida ba tun da ya san dai budurwar nan aljana ce,
sannan ba zai je cikin gari a haka ya bugawa mutane gida ba, tun da gidan kusan shi ne na
ƙarshe a inda yake, ganin ta doso inda yake sai fitsari ya suɓuce masa, ya fara sakin wata tusa
mai ƙara a kai- a kai...
MAMAN AFRAH
09025576222
[6/28, 6:21 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS
👳🏻♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 3
*ƘAUYEN MAI MANGWARO*
Lami matar Sheik tun daga lokacin da ya tafi take cike da tsammanin jiran dawowarsa, tana
son idan ya kawo kuɗin nan ta ɗauki nata ta mayarwa mai saniya nata, shi ma Ibran ta
sammasa wani abu daga ciki saboda ta san shi da idon son naira. Tun bayan sallar la'asar
motocin kasuwa suka fara dawowa, tun daga lokacin take ta sintiri wajen da motocin suke
sauka amma duk motar da ta kawo mutane bata samub mijinta a ciki,duk sai ta shiga damuwa
tana fatan dai ba saniyar ce bata siyu ba, ko kuma ta ƙi yin daraja shi ya sa bai dawo da wuri
ba, duk da ta san ta faɗa masa ya siyar ko ma nawa ne ita ba asarar ta bane indai ta ɗauki
kuɗinta. Dab da magriba tana tsaye riƙe da tsantsa ta rasa mai yake mata daɗi, don zuwa
lokacin hankalinta ya fara tashi, tana tsaye kamar daga sama sai ta ji an fisgi kafaɗarta,
juyowarta ke da wuya idanunta ya sauka a kan Jummai tudun adashe, tana wani muzurai sai
huci take kamar kububuwa.
Rai Lami ta haɗe itama tana aika mata harara, cike da masifa Jummai ta ce
"Lami ashe baki da hankali ashe tunanin yara ne da ke, saniyar marayun kike je kika kunce? Ina
kika kaita, kin san dai tsohon mijina da ya mutu gadon ƴaƴana da aka bani na saya saniyar nan
tun tana ƙanƙanuwa na kiwata musu ita, a kan wani kuɗin adashe ki je ki since mini ita?" Ta
faɗa tana dawowa gaban Lami har zanin Jummai yana neman kuncewa ta gyara. Kallon ko in
kula Lami ta jefe ta da shi ta ce
"Wato kuɗin adashe ba kuɗi bane ko? Saniyar marayu ita ce abun kirki da tattalawa... Katse ta
Jummai ta yi da cewa
"Ni ba wannan ba mu je ki bani saniyar nan tun muna mu biyu kin dan dai ta marayu ce na faɗa
miki" Wata dariyar rainin wayo Lami ta yi ta ce
"To sai su ɗauki na annabawa, ki jira dawowar Ibra mijina daga kasuwa in ya kawo kuɗin
saniyar sai in ɗauki kuɗin adashena in baki ragowar in ya so sai ki sayi wata ƙaramar ki kiw...
Tun kafin Lami ta ƙarasa Jummai ta wani zaro idanu tana dafe ƙirji ta ce.
"Kanki ɗaya kuwa Lami?Saniyar kika bada aka kai kasuwa?" Ta faɗa cike da takaici dama
dawowar ta kenan, aka faɗa mata ko gida bata je ba ta kama hanyar gidan Lamin shi ne ta
hange ta tsaye.
"Ras kuwa, ai da nake kai miki kuɗin zubin adashen kike karɓewa baki taɓa sanin kaina ɗaya
ne ko ba ɗaya ba sai yanzu da na ɗauki saniya" Masifa Jummai ta shiga yi tamkar za ta hau
Lami fa duka, ita ma da ba kanwar lasa ba suka haɗu suna yi har mutane suka fara taruwa ana
basu haƙuri, Jummai tana cewa ko Ibran ya dawo da kuɗin daga kasuwa sai ya koma ita
saniyar ta kawai ta sani.
Wani dattijo yaa basu haƙuri a kan a jira Ibra ya dawo amma har motar ƙarshe ta kasuwa ta
dawo amma babu Ibra a ciki, nan hankalin Lami ya tashi don ta fara wani tunani da ban, sai da
ta samu wani direban motar shanayen da Ibra ya shiga ta tambaye shi, nan yake ce mata suna
sauka a kasuwa ko cikin kasuwa Ibra bai shiga da saniya ba, aka fara tayawa, nan ya samu
wani ya saya ya bashi kuɗin don har la'ada ya bayar.Ya ce wata mota ma Ibra ya shiga, don a
yanayinsa ma bashi da niyyar komawa Mai Mangwaro. Jummai kamar ta yi hauka sai zage-zafe
da tsinuwa take, amma kuma tana riƙe da mayafin Lami a kan cewa ƙafar Lami ƙafarta sai ta
nemo Saniya, magana ya girmama har gaban mai gari.
Bayan an faɗawa mai gari komai, sai ya rasa ma yadda za a yi da Ibra tun da komai dai na
maganar yana hannunsa, don haka sai mai gari ya aika wani yaro ya zo da Tasallah kakar Ibra,
yaron da zuwansa ya samu Inna Tasallah tana kwance a kan tabarma daga yin sallar isha'i ta
ɓingire a kan sallayar. Sallamar da saurayin yake rafkawa ita ta falkar da ita daga ɗan baccin da
ya ɗauke ta.
Bayan ya gaishe ta ya ce
"Inna saƙon kira ne daga fadar mai gari" Inna warai ta ware daga ɗan baccin, tana zaro ido da
mamaki ta ce
"Idirisu Allah sa dai lafiya, ya za a yi a ce mau gari yana kirana da wannan daren?" Idrisu ya ce
"Inna Ibra ne dai yake son tada miki zaune tsaye, ya karɓi saniya a wajen Lami, kuma saniyar ta
Jummai ce, kasuwa Lami ta ce ya kai ya siyar amma har kowa na kasuwa ya dawo amma babu
Ibra, yanzu dai suna can gufane a gaban mai gari Jummau ta ce sai an biyata" Salati Inna
Tasallah ta shiga zabgawa tana tafa hannuwa ta ce
"Wannan yaro an yi taƙadari, yanzu Ibra ina zai je da saniyar mutane, a ce mutum ya girma bai
san ya girma ba, yanzu a ce mutum da iyalinsa shi ba wani yaro ba amma sai jan rigima, ni
yanzu ai ni ya tsunduma a masifa, ni da ko kaza bani da ita, wallahi Ibra albasa bata yi halin
ruwa ba, iyayensa mutanen kirki ne amma tun da suka mutu nake jigila da shi, tun yana yaro
bai barni na huta ba" Ta faɗa tana fashewa da kuka irin na tsofaffi.
Haƙuri Idrisu ya shiga bata, taba goge idanu tana face hanci ta shiga ɗaki jim kaɗan ta fito da
wata roba mai ɗan girma tana riƙe da ita, waje suka fito ta saka mukulli ta kulli gidan, suka farw
tafiya ta shiga faɗin
"Wannan kalwa da barkonon da kuka da suke cikin robar wannan su kaɗai ne mallakina a
duniyar nan, su nake kira suke amsawa, yau ban da cinikin naira ɗari ban yi ciniki ba, ita ma
ɗarin gata nan a cikin robar, idan mun je ko da an buƙaci wani abu daga gareni in biya kuɗin
saniyar sai in juyewa mai gari wanann kayan don su kaɗai ne da ni.
*GIDAN ALHAJI ADNAN JIBO*
Hajiya Nuritya ce zaune a tangameman falon ta da ya gaji da kayan alatu, tana zaune ta harɗe
ƙafafunta hannunta riƙe da waya ƙirar iphone 16 pro mx sai wani ɗan yatsina fuska take lokaci
zuwa lokaci. Shigowar mai aiki falon ɗauke da tire wanda aka ɗora plate da ta yanka kayan
marmari, ko sallamar da ta yi bata amsa ba, haka ta ƙarasa gaban Hajiya Nuriyya ta durƙusa ta
ajiye tiren tana mai cewa
"Barka da hutawa Hajiya, na kammala yankawa" Shiru Hajiya ta yi bata amsa ba, kamar ba za
ta yi magana ba zuwa can ba tare da ta kalli mai aikin ba ta ce
"Ki je ɗakin Rahma ki sanar da ita kin gama yanka mata" Da to ta amsa cike da girmamawa,
sama ta haura ta je ƙofar ɗakin ta tsaya, tana tsoron ta ƙwanƙwasa ta yi laifi, amma haka ta
daure son babu yadda za ta iya tun da in bata sanar da ita ba ɗin ma, laifin ne gwara dai ta
sanar ɗin.
Kamar tana jin tsoro haka ta shiga ƙwanƙwasawa a hankali, duk don gudun laifi" Sau biyu
kawai ta buga sai ta dakata tana jiran jin amsa, tun da ta san dai in har idanun Rahma biyu to
tabbas za ta ji bugun sai dai amsar ce sai an kai ruwa rana.
Sai da ta ɗauki kimanin minti biyu zuwa uku tana jira sannan ne cikin muryar Rahma mai
sanyi ta ce
"Waye?" Cike da girmamawa ta ce
"Ni ce Hajiya ta ce an gama yanka kayan marmarin"
Cike da izza Rahma ta ce
"Na ji" Baki mai aiki ta taɓe tamkar Rahma tana ganinta, juyowa ta yi ta bar ƙofar ɗakin, tana
zuwa ta sanar da Hajia ta fita don zuwa ta cigaba da aikinta.
Sai bayan kamar minti goma sha biyar, sai ga wata kyakkyawar budurwa wacce ba za ta fi
shekaru ashirin ba kuma ba za ta gaza shekara sha tara ba, tana tafiya kamar bata so, sanye
take da fararen kaya tas riga da wando a jikin gaban rigar an yi zanen heart da pink colour, sai
aka rubuta BEAUTY.
Kyakkawa ce ajin farko, sai dai bata da ƙiba, ƙarasowa ta yi ta zauna a kusa da Hajiya
Nuriyya, Hajiya cike da soyayya da son nuna kulawa ga tilon ƴar tata, ta ajiye wayar hannun, ta
mayar da hankalin ta kanta ta ce
"Mai kike so ne eh baby nah?" Ta tamabaya tana kallonta cike da soyayya.
Ɗan yatsina fuska ta yi tana ɗan tura baki ta ce
"Fruit ɗin ne ba zan iya ci ba" Ta faɗa cikin muryar sangartattun yara.
Murmushi Hajia ta yj ta ɗakko ta shiga bata, suna cikin haka sai Alhaji da Yaya Ma'aruf suka yi
sallama suka shigo, Yaya Ma'aruf ɗan gidan yayan Alhajin ne a ƙauye yake shi ne ya zo karatu
birni ya sauka a gida ƙanin mahaifin nasa.
Yaya Ma'aruf mutum mai ibada da kula da addini, yana son ganin mutum yana riƙo da sallah,
sai dai kuma ya sauka a gidan kawunsa inda yake ganin ana wata rayuwa ta da ban.
Da gudu Rahma ta tashi ta je ta rungune mahaifinta tana cewa
"Oyoyo Daddy nah" Yana nuna farin cikinsa ya raba ta da jikinsa yana riƙe da hannunta yake
cewa
"Oyoyo baby fatan kin ci abinci" Ɗan tura baki ta yi ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 14