Share this page
a cikin ku yana da laifi, ke Lami bai kamata ki taka har gidan Jummai ki since saniya a turke, ki ba mijinki ya kai kasuwa ba, mene ne amfanina a wannan garin, da kin kawo ƙaranta ai da na san abin yi" Kai Lami ta sunkuyar tana jin haushin Mai Gari ganin zai ɗora mata jakar tsaba kaji su bita. Bai ba kowa damar magana ba ya ce "Yanzu Tasallah kina da kuɗin da za ki biya wanann cakwakiya?" Inna kamar jira take ta sakin wani kuka mai ɗan sauti tana jin ciwo kayan miyarta da za ta bayar ta ce "Ya na iya da abin da ya fi ƙarfina, ai dama faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi, ni nan bani da komai amma ga kayan miyar nan da wannan naira ɗarin da na yi ciniki, su kaɗai ne na mallaka, ta karɓi jingina har zuwa ranar da Ibra zai bayyana, idan ya bata kuɗin saniyarta sai ta bani kayan miyata, amma da sharaɗi ko kalwata ko kuka suka yi ciwon kai ba zan yarda ba yadda zan bata kayan miyar nan salin alin ta ajiye kar ta sake ta taɓa" Ta faɗa tana ɗaga robar ta juye kayan miyar a kan tabarma a gaban Mai Gari. Tsabar takaici Jummai bata yi magana ba, ƴan fadar ne suka shiga danne dariyarsu, Mai Gari cike da takaici ya ce "Haba Tasallah a gabana kike mayar da babbar magana ƙarama, ana batun saniya kina batun kalwa da kuka da barkono?" Ɗan karkata kai Inna ta yi ta ce "To ai kowa da abin hannunsa yake ado, guntun gatarinka ya fi sari ka bani, ita saniya gare ta ni kuma kayan miya ne Allah ya bani" Mai Gari bai sake bi ta kan Inna ba, ya shimfiɗa sharaɗin za a jira daga nan zuwa kwana uku, a ga ta inda Ibra zai dawo, in ya so sai a san abin yi. Haka ya kashe rigimar ba don ta mutu ba, ya ce idan Ibra ya dawo da saniya ko kuɗin saniya sai Jummai ta karɓi kayanta, sannan ta biya Lami kuɗinta. Inna wani irin washe baki ta yi, tamkar ba ita ce wacce take wannan kukan ba, dama kukan takaicin za a raba ta da kayan miyarta ne. Haka ta kwashe ta saka a robar tana jerawa Mia Gari godiya, ta tafi gida a ranta tana Allah wadai da halin Ibra mutum kusan shekara arba'in amma bai san abin da ya kamata ba sai tunani irin na yara. Lami da Jummau kowa a ƙufule da ɗan uwansa ya bar fadar Mai Gari. Lami tana komawa gida ta samu kishiyarta Sa'a a tsakar gida tana riƙe da ƙugu, shigowar Lami ko zaunawa bata yi ba Sa'a ta ce "Sannu Lami wato ke kin iya ɗauki ɗam baki ajoye ba ko? A kan me za ki ɗaukar mini gayan tuwo?" Lami wacce take cike da ɓacin ran rashin dubu ɗari biyun ta, da kuma yaudarar da Ibra ya mata a tsawa ce ta ce "Sa'a hawainiyarki ta kiyayi rama ta, saboda rainin wayo ni da nake da dubu ɗari biyu kuɗin adashe uban me zan yi da gayan tuwo, to Allah tsari gatari da saran shuka" Sa'a hannuwa ta tafa ta ce "Da ba a san asalin barbela ba sai ta ce daga madina take, kuɗin adashen da ko naira biyar bata zo hannunki ba, kika ɗauki saniyar mutane kika ba wanann marar imanin ya tafi to ai kin yi saki na dafe. Sa'a ta ci gaba da cewa "Shi ne za ki ɗauke mini gayan tuwona ki fice da shi, na san a gyalenki kika duƙunƙu ne tuwon kika je maƙota kika yi kwaɗo da mai da yaji kika cinye" Galala Lami take kallonta sai dai takaicin da yake cikin ranta ya fi wannan wanda Sa'a take takalarta faɗa da shi don ta san ita da Sa'a basa jituwo ko kaɗan, haka ta tashi ta shige ɗakinta tana jinta tana jera mata Allah ya isa amma bata ji za ta iya biya ta su yi ba, don ita a halin da take ciki ko yunwa bata ji bare har ta saci gayan tuwo ta san kawai neman masifa ne irin na Sa'a. *WASHE GARI* Sa'a ce a tsakar gida tana shanya kayan wanki, Lami tana bakin ƙofar ɗakinta tana zaune ta kifa uban tagumi, bata da buri illa ta ga Ibra ya dawo da kuɗin wannan ko saniya amma shiru malam ya ci shirwa. Wata uwar sallama ake rafkawa a zauren gidan, da murya wacce hausa bata gama ratsa ta ba, alamar yare ne yake maganar. Wani takaici ne ya turnuƙe Lami ta taso rai a ɓace ta zo bakin zauren ta tsaya ta ce "Tunde sai aka yi yaya kuma? Ya za ka zo da safen nan ka ishi mutane da rafka sallama" (Tunde inyamuri ne da ya zo daga Lagos yana zaune a garin Mai Mangwaro yana da gidansa da matarsa ɗaya da ɗansa, sai kuma shagonsa da yake a ƙofar gidansa nasa). Kallon Lami ya yi ya ce "Ba wajenki na zo ba wajen mijinki na zo" Ya faɗa cikin hausar sa da bata gama kama bakinsa ba. Ambaton mijinta da ya yi ya ƙara sosa mata mikin takaicin Ibra da ta kwana da shi, cikin takaici ta ce "Baya nan ya ɓata, hijira ya yi da saniyar mutane ba a san duniyar da yake ba" Idanu ya zaro ya saka hannu a lajihu ya fito da takarda wacce rubutu ne rututu a jiki ya ce "In na yarda shegiya nake, kalli basukan da mijinki ya ci" Ya faɗa yana nuna mata takardar. Kallon sheƙeƙe ta wa takardar ta ce "To ai ka yi ta banzar ni da ba boko na yi ba ina zan san me aka rubuta" Yana zaro idanu ya ce "Idan ma ɓoye mijinki kika yi ki fito da shi, don yau ba zan bar nan ba sai da kuɗina, shinkafa kwano uku wake rabin kwano, sabulun bilicin da ya sha karɓa, da mayukan bilin har allurai da nake masa na sanya fari bai biya ni ba wallahi ko a ni ko a shi jiya ya ce zai dawo daga kasuwa ya biyani yanzu ki ce wai ya yi hijira" *SHEIK* Kukan zuci ya shiga yi wanda ya fi na fili ciwo, ya san tabbas yau watan tonuwar asirinsa ne ya kama in ba haka ba hular da ita ce kaɗai rufin asirinsa kuma ita ce take fito da asalin kamarsa da larabawa a ce babu ita. Shiru ya yi yana nazarin yadda zai kuɓuta amma iya tunaninsa bai tuno komai ba, don babu mafita, kansa gabaɗaya ya kulle. Ga abin da ya fi ɗaga masa hankali ma shi ne yadda samarin sukemta azalzalarsa a kan ya fito ana jiransa. Cikin ɗaga murya ya ce "Afwan ya shabbab, gani nan ina zuwa, ina yin shirin ko ta kwana ne, saboda aljannu dubu saba'in ne a kan matar nan mai farfaɗiya" Ya faɗa yana ta safa da marwa a ɗakin ya haɗa uban gumi yana ganin yau dai ƙarya nema take ta ƙarewa ɗan kada, saboda ya lura yana cikin tsaka mai wuya. Kamar zai yi kuka a hankali ya ce "Allah ka taimake ni, Allah kar ka bari in kunyata" Ya faɗa yana ciccira ido a ɗakin, fani yake kamar zai ga hular amma babu niyya wai ango ya kwana da wando. Wata dabara ce ta faɗo masa ya buɗe baki ya ce "Gabaɗaya ku fita daga gidan nan, gani nan fitowa saboda maganin aljannun da zan fito da shi yana da ƙarfi, wataƙika idan na fito guguwa ta taso ta haɗe gidan da ƙura... Tun bai kai ƙarshen maganar ba, samarin nan kowa ya yj ta kansa, sai lokacin ya ɗan ji sawaba, kamar ƙiftawar ido da fitar su Sheik ya fara ganin labulen windown ya fara kaɗawa da ƙarfi kamar dai ana iska mai ƙarfi ne, Idanu ya zaro cikin taku biyu ya koma jikin bango ta raɓe, bakinsa yana karkarwa ya fara addu'a, kawai sai ganin hular gashin nasa ya yi tana reto a saman ɗakin, kai ya ɗaga yana ta kallonta, a ransa yana jin daɗi da ya ganta sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba yanzu tunaninsa ɗaya ya za a yi ta zo hannunsa. Bai ankara ba ya ga an wurgo dogom gemun jikin fuskarsa sai kuma sauran sajen da hular gashin suka ɓace, kamar zai yi kuka ya hau faɗin "Ku taimaka mini, ya zan yi da gemu shi kaɗai, damuwata gashin kan nan nawa da babu yadda yake salsal su kuwa sun san Sheik da gashi laɓaɓa na larabawa." Yana rufe bakinsa sai ga sauran ma sun fito sai kuma suka faɗo, duk da yana tsoro haka ya lallaɓa ya je ya ɗauka yana godewa Allah a ransa yana jin daɗin cewa ashe dai da sauran shan ruwansa a garin Ƙundu tun da gashi dai asirinsa bai tonu ba lallai akwai damfara. Shirinsa ya yi tsaf ya ɗauko wani baƙin takalmi sabo a jakarsa ya saka, ya ɗakko turaruka ya shafa ya saka hular gashin ya manna gemun ya saita sajen da yake wani abu ne a jiki da ake ɗayewa mai danƙo daga ya ɗaga wajen sai ya manne kamar a fuskarsa a ka halicce su. Ɗakinsa ya kulle ya fito yana riƙe da wata roba mai ɗauke da ruwa da wani garin magani da aka jiƙa a ciki ya fito daga gidan gabansa yana faɗuwa, yana tunanin yadda za a ƙare da wannan lamari, shi ya sa ko wayarsa bai ɗauko ba gudun masu aljannu su warce ko ma a fasa masa ita. Tun da ya fito yake hangar mutane jefi -jefi suna yin wata hanya sannan kuma sai wani girmama shi ake ana bashi hanya, wanann ya ƙara masa jin kansa ya ƙara girma, duk da yana cikin yanayin tsoro haɗe da fargaba. Sheik haka ya doshi cikin garin ya yi inda mutane suke yi da alama nan ne wajen da su Liman ɗin suke.Duk da idanunsa sun kumbura saboda fargaba da rashin baccin da bai samu jiya ba, kai har da kukan da ya yi ma. Tun kan ya ƙaraso yake jin ana ta yin salati, yana kusa ƙarasowa ya ji ana faɗin "Shikenan ma ga Sheik nan, ga ƙare kukan ka nan, balaraben malami yanzu komai zai zo ƙarshe. Mutanen gari sun taru suna jiran ya fitar da maganin da zai kori aljannu kuma ya kuɓutar da su Liman. Amma Sheik yana cikin firgici har yanzu saboda abin da ya faru da dare. Yana ganin taron mutane sai ya fara rawar baki da hannun yana murza carbi, yana faɗar kalmomin larabci marasa ma'ana, don shi kansa bai san abin da yake faɗa ba yayin da yake karanta addu'a sai wani ƙaramin yaro ya faɗi a gabansa ya fara rawa ɗari tamkar yana shi ma mai farfaɗiyar ne, mutane suka shiga faɗin suna cewa "Aljannu yanzu za ku gane shayi ruwa ne" Shi kuwa Sheik ganin yaro ya zube a ƙasa idanunsa sun kakkafe sai ya sha jinin jikinsa gabansa yana tsanata faɗuwa, ya yi shiru don bai san me ya faru ba, amma ya ci gaba da murza carbi yana ambaton maganganu. Jama'a suka fara mamaki da tsoron Sheik suna ganin tsabar maluntarsa ce ta sa yaron ya zube a ƙasa. Bai bi ta kan yaron ba ya ɗaga kansa sama, mutane uku ne a kan bishiyar kukar da mutane gari suke kira da kukar bulukiya saboda tarin aljannun da suke kanta Hannu ya saka ya kama yaron nan da ya faɗi ya ɗaga shi, ƙirjinsa ya dukan uku-uku ya shiga karanta fatiha da ƙarfin halinsa yana tofawa yaron a fuska, wani gurnani yaron yake, Sheik kuwa ji yake kamar ya sheƙa da gudu amma babu hali. Ɗan ranƙwafowa ya yi yana cigaba da tofa masa karatun idanun yaron a kakkafe ya miƙa hannu bai masa masauki a ko ina ba sai a gemun Sheik. Sheik a zuciyarsa ya ce 'Shikenan asirina ya tono zai fisge min gemun a bainan nasi, kowa ya gane bogi ne' A fili kuma sai ya fara faɗin "Subhanallahi, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, hasbunallahu wa ni'imal wakil" Duk abin nan da ake yaron ya ƙi sakawa, shi kuma Sheik hannunsa ɗaya yana riƙe da carbin da robar maganin nan ɗayan yana riƙe da yaron, ji yake kamar ya yi kuka, bai yi wani yunƙuri ba kawai sai yaron ya naɗe jikin malam yana cewa "Ka kaini saudiyya" Sheik a zuciya ya ce "Ni kaina ko filin jirgi ban taɓa zuwa ba' A zahiri ya ce "Kai mutum huɗu su zo nan" Ya faɗa yana ƙara miƙa haɓarsa jikin yaron don ba ya so ya ja yaron ya ciro gashin gemun. Samari da mata da magidanta da suke wajen sai aka fara darewa jin malam yana kiran mutum huɗu Malam ganin yaron yana miƙa hannu wajen wuyansa gudun kar ya shaƙe shi ya kashe shi a banza, inda Sheik yake riƙe da hannunsa ya nutsawa yaron farce ya shiga tsunkonsa da ƙarfu ba tare da kowa ya lura ba, mutane duk sun koma gefe. Sai aka ji yaro ya fashe sa wani kuka, lokacin ne mahaifiyarsa da ta uso wajen tana kuka ta ƙaraso, kukan da yaron ya fashe da shi sai Sheik ya shiga faɗin "Allahu akbar! Ya dawo hayyacinsa sun fita" Ya faɗa lokacin har jikin yaron ya saki kamar mai jin bacci yana lunshe idanu, babar yaron ce ta karɓe shi da hannu biyu, tana miƙawa Sheik 3k ƴan dubu-dubu tana cewa "Allah saka da alkairi, Malam ga abin sadaka" Ko fulaki bai yi ba ya karɓa yana cewa. "Babu komai ai yi wa kai ne don ma an ce babu kyau mayar da hannun kyauta baya" Mutane ganin Sheik ya warkar da yaro aljannu sun fita daga jikinsa sai girman Sheik ya ƙaru a idanun su, suka shiga yin kabbara. Kuɗin nan ya saka a aljihu yana faɗi a zuciyarsa cewa. 'Allah kawo dubbanku, da a ce za a ke samun abin sadaka mai yawa haka ai da wuri zan cika buhu da kuɗi' Gabansa yana faɗuwa ya matso daga gaban kukar da su Liman suke ka,reshen kukar ne manya guda biyu a can saman amma ba tsililiko ba, ɗaga reshen Liman ne a maƙale kamar ɓeran da aka tsamo daga ruwa, ɗayan kuma Mai Gari, sai wani lanƙwashashshen reshe wannan matar mai farfaɗiya tana zaune a kan, su kuma suna maƙale da hannuwan su a kan reshen. Sheik ya yi shiru jin wajen babu abin da yake tashi sai kabbara, matan gari an taru wasu ma sai yanzu suke ƙarasowa wajen, a baya idan haka ta faru sai dai kowa ya yi ta kansa, a ringa shiga gida ana kullewa, amma yau ganin balaraben malami kowa sai tsoro ya ragu daga zuciyarsa. Sheik ya fara tunanin Malam Manniru, wanda yake zaune a wani ƙauye a daji a can wajensa yake bashi magungunan da ya zo don yon bogin da su, har ruƙiyar ma ya koya masa, sai dai ya san yin magani dace ne ga shi maƙudan kuɗi malamim yake karɓa. Baki ya buɗe ya shiga jan fatila, nasi, falaƙi, yana ta maimaitawa, ya buɗe wannan ruwan ya tsiyaya a marfin ya watsa wajen bishiyar kukar, wata irin kururuwa da su Liman suka ɗauka sai da Sheik ya ja baya kamar zai fita da gudu, sai kuma ya tuna ashe shi ne jagaba a garin. Ya daɗe yana ta karatun nan sai uban gumi yake sharɓawa, ruwan maganin na kuwa sau uku ya watsa, cikin taimakon Allah sai Liman da Mai Gari suka fara atishawa, kawai sai ga su an sakko da su ƙasa, mai fardaɗiyar ce aka sakko ta kamar wanda aka jefo ta, ta zo da rubda ciki, gabaɗaya wajen ya kaure da faɗin "Allahu akbar! Allahu akbar".Wani daɗi ya rufe Sheik yana jin kawai ya warke, shi dai da talauci sai ko ya ga ana yi amma kam sun yi hannun riga da shi da talauci, tun da ga shi har ta ci nasarar warkar da yaro da kuma su Mai Gari, duk da ya san cewa da alama aljanin jikin yaron nan wahala ce ta tsinkon da ya masa ta sanya ya fita. Mai Gari da Malam Liman sai washe baki suke, su kuma jama'a maza da mata sun dunƙule hannu suna jinjinawa Sheik suna faɗin Allahu akbar!. Sun san ba ƙaramin aiki ne a sakko da mutane daga saman kukar bulukiya ba, matar nan wasu mata biyu aka sa suka kinkime ta aka ce a kaita gidan ta. Mai Gari da Liman faɗi suke "Jajirtaccen balaraben malami, garin Ƙundu ya yi babban kamu, sai inda ƙarfinmu ya ƙare dole gari ya kyautatawa Malam kai jama'a ku ce Allahu akbar!" Gabaɗaya wuri ya kaure da kabbara a tare. Sheik bakinsa ya ƙi rufuwa, sai jin kansa yake yana ƙara girma, har ya fara hango yadda zai yi kuɗi a saya kadarori. Yana shafo gemunsa ya ce "Kar ku damu, mu dama taimako ne muke yi, indai aljannu ne ko ido biyu za mu fafata da su bare kuma a jikin ɗan adam, ai na gani duk aljannu ne suka baibaye kukar amma yanzu sun tarwatse" Ya faɗa yana ɗan murmushi, a take mutanen gari suka fara kawo kuɗi suna ba Sheik tun yana zubawa a aljihu har dai aka ara masa fanteka yake sakawa, mutane suna murnar ceton su Liman da ya yi da kuma murnar garin su zai yi lafiya za su rayu babu tsoro. A cikin kunnesa iska take kawo masa maganganun matan sa suke wajen wata tana cewa "Ai mun samu wajen zuwa, mun huta kaiwa malamai da bokaye kuɗaɗenmu suna bamu maganin mallakar miji, da wanda ake yi wa kishiya, shikenan yanzu a wajen balaraben malami za muke baje haja" Wata ta ce "Ai na faɗa miki yanzu malamin nan sai ya rasa lokacin kansa in aka ringa tururuwa" Duk abin da suke faɗa Sheik yana ji har ya fara hango yadda zai ke tsula musu kuɗin aiki. Ana cikin haka kamar an ce Sheik ya ɗaga kai, sai kuwa ya sauke idanunsa a kan kukar bulukiya. Wani kan ƙwarangwal ya hango ajiye a saman kukar, sai ƙaho a jiki, da sauri ya sunkuyar da kansa, yana haɗiye wani yawu muduk. Carbinsa ya shiga ja da sauri-sauri dama robar ruwan maganin tana cikin fantekar kuɗin, gabansa ne ya shiga faɗuwa ya tuno furucinsa da yake cewa ko ido da ido za su fafata. Liman ne ya ce "Ya Sheik ya dai?" Ya faɗa ganin duk ya diririce yana ta faman haɗa gumi" Ya san babu wanda ya lura da abin da ya gani, bai sani ba dai ma ko shi kaɗai aljannun suka buɗewa ido yake ganin kan ƙwarangwal ɗin. Yaƙe ya yi ya ce "Ah babu komai fa dama"Ya faɗa yana ɗan ɗaga kai kaɗan ya hangi saman kukar, dariya ya ga kan yana masa, kafin ka ce kwabo sai aka ga an fara sama da Sheik alamar ƙafafunsa sun fara barin kan ƙasa, idanu ya zare don kafin ƙiftawar ido har ya wuce saman kan mutane shi kaɗai yana shawagi a saman ba tare da ya riƙe ko ina ba, yana riƙe da fantekar kuɗi. Jama'aka shiga faɗin "Subhanallahi!" Ana ta maimaitawa kowa yana ganin ikon Allah, Sheik gabaɗaya ya tsure sai hannu yake miƙawa alamar a kawo masa ɗauki, tun da aka fara sama da shi yake faɗin "Yauma tublar sara'ir, jama'a taimako" Kowa jin Sheik da kansa yana ambatar taimako sai suka fara ja baya, jar su Mai Gari kowa ya koma can nesa, sai da aka kai Sheik saman kuka, wuyan jallabiyarsa da shi aka rataye shi a jikin kuka, yana ji yana gani kan wanann ya ciro hirami daga wuyan Sheik ya masa ɗaurin ɗankwali gwaggwaro a kansa, babu wanda yake ganin kan sai Sheik... MAMAN AFRAH 09025576222 *TALLAH TALLAH TALLAH* 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 ???????????? *KIN KARANTA* ?????????????? *Shin kin karanta littafin nan? Kin ji cakwakiyar da ake yi a ciki? Ta kamu da mugun son sa wanda da shi ta raini zuciyarta tun tana ƙarama, tun bata san mene ne so ba, sai dai tana daf da sanar da shi aka saka aurensa da yayarta da yake ƴan uwa ne, ta ji takaici a hakan take fafutukar jan hankalinsa duk da yana mijin yayarta, mutuwar yayarta shi ya bata damar cin karenta babu babbaka, ta shiga ta fita ta aure shi tun dafin mutuwar matarsa bai barshi ba, sai dai shegen kishin ta, ya sa ta raba mijinta da kowa ciki kwa har da uwar da ta kawo shi duniya, hatta ƙawayenta mararsa aure sai da ta daina hulɗa da su dk don kar a aure mata miji, mai zai faru? Aminiyarta da ta yarda da ita take faɗa mata sirrinta ita ce mafarin komai, kwatsam mijin ya tashi ƙara aure, da aminiyarta suke fafutuka wajen toshe ɓarakar auren da mijin ya ɗakko, ashe dai ita ce ta yi wufff da mijin nata sai a washe garin ranar da ta tare suka yi ido huɗu, shin ya zaman zai kasance? Kin taɓa jin inda kishiya take yin asiri ta rufewa kishiyarta HQ a toshe wurin gabaɗaya a gefe guda a fito mata da mazantakar namiji? To a buk ɗin nan an yi wannan badaƙalar, da 500 kawai zan baki book ɗin har ƙarshe* . 09025576222 [7/5, 6:08 PM] Mom mashkr & Afrah: https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 Mums & mums-to-be! 👶🧺 Adashen washing machine🥳🥳🥳🥳bby & kids’ clothes + accessories ya dawo!🔥 Easy payment, zero stress! Ki shiga kafin a gama! 📥💃 +234 707 753 2253 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 6 *MA'ARUF* Yana dafe da kuncin yana jin zafi da kuma haushin abin da Hajiya ta masa. Daddy ya ce "Haba Hajiya yanzu abin da ya yi har ya ci hukuncin mari haka?" Ya tambaya yana kallon ta Rahma ce ta taɓe baki ta ce "Haba Daddy ko duka aka masa ai hukuncin ya yi kalli fa yadda ya ɓata mini kaya" Shiru Daddy ya yi duk da bai ji daɗin abin da aka yi wa Ma'aruf ɗin ba, amma sai dai son ƴarsa ya rufe maaa ido. Hajiya ce ta ce "Alhaji kai kake sangarta wannan yaron, in ba haka ba har ya ɓatawa tilon ƴar tamu jikinta kake tambayar dalilin dukan da aka masa, kuma har kana ganin hukuncin da aka masa ya yi tsauri" Daddy iska ya furzar mai zafi ya ce "Bai kyauta ba kam amma dai da baki mare shi ba" Ma 'aruf ya danne takaicin da ya ji yana mai sauke hannunsa daga fuskarsa ya ce "Ba komai Daddy ai ita ma mahaifiya ce a gareni, duk abin da ta yi daidai ne... Kafin ya ƙarasa maganar Hajiya ta katse shi da faɗin "Ai indai tsara magana ne kai dai sai ko a samu na biyunka amma babu na ɗayanka, ka iya kalallame mutane wannan da mace ne kai kishiyarka ta shiga uku saboda kissa" Bai ce komai ba ya juya jiki a sanyaye zai fita, Daddy ne ya ce "Ina kuma za ka je" Ya ce "Zan je in ɗan watsa ruwa ne" Amsa masa Daddy ya yi shi kuma ya fita. Hajiya ta taɓe baki tana cewa "Wannan uztazun yaron miskilin gaske yana abu kamar dai bai san me duniya take ciki ba" Ta faɗa tana kama hannun Rahma. Daddy bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa ga danna waya. Sai shagwaɓa take zubawa a haka suka haura sama wai za ta yi wanka ta sauya kayan wanann na jikinta. Ma'aruf yana zuwa ɗakinsa ya mayar da ƙofa ya rufe tare da jinginuwa a jikin ƙofar, ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yana tuna irin yadda Hajiya da Rahma suka ɗora masa karan tsana, ya san kuma ba komai ba ne dalili illa kasancewarsa ɗan ƙauye kai ba ma ƙauyancin kaɗai ba babban abun shi ne bashi da masu gidan rana, ya san da a ce yana da kuɗi ko da kasancewarsa ɗan ƙauyen ne to zai samu sassauci da salama, sai dai ba sa ganin ilimin da yake da shi na addini a nasa ganin da tunanin ilimin addini kamar shi ne zai zama ginshiƙin da za a ƙauna ce ka, ko yaya dai ka fi ƙarfin jahili, amma a hakan suke masa kallon bagidaje saboda addininsa. Goshi ya dafe jin yanayin da ya fara ziyartarsa a ƴan kwanakin nan, wato wasu sababbin abubuwa da suke son ɓullowa daga zuciyarsa, wanda a halin yanzu shi kansa yake yaƙi da xuciyarsa, saboda ya san tabbas tana son ta kai shi ta baro ne, to in ba tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe ba, mene ne yake jin zuciyarsa tana son ta kai shi ta baro shi?. Ya san tabbas ba ya son halayyar Rahma, ko kaɗan baya damu da sallah ba, ga raini da ɓaci a gaban iyaye saboda an sangarta ta, sai dai yanzu yana jin wasu ƴan canje-canje a game da ita, wanda ba ya raba ɗayan biyu wannan kalmar ce da ake kira SO, wannan kalmar dai da bata duba cancanta ko matsayi, tun da ya san so babu ruwansa da ɗaukaka, matsayi, ƙanƙanci, talauci mulki kyau ko muni, idan ba zuciyarsa tana son yaudararsa ba mai ya kaita take son faɗawa tarkon son Rahma. A fili ya furta "Zuciyata karki mini haka, kar ki yaudare ni, kar ki ja mini abin da zai zama da na sani, kar ki saba da abin da ba za ki taɓa samu ba, idan mafarki kike yi ki falka, Rahma ta masu kuɗi da ƴaƴan masu faɗa a ji ne"Ya ƙarasa faɗa yana faɗawa kan katifarsa ya yi rubda ciki. Ya ci gaba da faɗa a zuciyarsa cewa 'Ta yaya ina baƙauye, sannan ni da albarkacin zumunci

Chapter 5 of 14