Share this page
ce yana sana'arsa ta MALAMIN BOGI. Daga nan masallaci suka wuce ya ja su sallar isha'i basu lura da yadda yake ta kare-karen ƙirji ba. Ana gama sallah ya ce zuwa zai yi ya kwana yana lazumi saboda matsalar garin, amma ya faɗa ne kawai don yanzu tashin hankalinsa bai wuce ƙirjinsa ba, so yake ya ce ya ga ta yadda zai yi da breast ɗin ƙirjinsa. Bayan ya je gidan ko ta kan abincin da aka kawo bai yi ba, ɗakin ya bankawa sakata, ya yi saurin cire hirami ya jefar ya kama riga ya cire. A razane yake kallon ƙirjin nasa ganin wani baƙiƙƙirin ɗin breast ne, musamman da suka haɗu da farar fatarsa da ta sha bilicin, sai baƙin su suka ƙaru, kamar a jikinsa suke tun asali haka suka yi, ya rasa ma ya zai yi da su. Ya fara tunanin mafita cewar yake yafa hiraminsa a wuya yana dabara yadda zai ke ɓoyewa ba tare da kowa ya gani ba, har zuwa lokacin da Allah zai yanke masa wahala, don shi bai taɓa jin an ce namiji yana da breast ba in har ba mata maza ba. Ya san mata maza ne suke da breast sannan suna da HQ da kuma mazantakar namiji a jikin su, amma dai bai taɓa jinw wanda shi ba mata maza ba kuma aljannu su fito masa da breast rana tsaka tashin hankalin ya yi yawa. Haka ya kwana ranar da zulumi sai bacci ɓarawo ne yake ɗauke shi. Washe gari aka kawo masa wata mata ƴarnuwar Mai Gari an ce masa bazawara ce sakin wawa, an kawo ta ne a mata magani saboda tun da suka rabu da mijin har yau ta rasa mashinshi ni, shi ne ake tunanin ko mijinta na farko ne ya mata asiri. Sheik tun da ya ƙyalla idanu a kanta ya ji yawunsa ya tsinke, sannan a ransa yana tunanin ina ma a ce wannan ce aka ɗaura masa aure da ita ba waccan mai ido ɗayan ba, yanzu kuma da kunya matsayinsa na balarabe ya ce ya ga baƙar fata yana so, domin ita ma farar bafulatana ce gashi har kafaɗa ga shi tana da cikar halitta wacce ita ce ta sanya Sheik ya rasa nutsuwarsa don sai ya ji ko fatar jikinta ne yana so ya taɓa. Saboda wannan dalilin na ba ya son ya daina kallon ta ya ce maganin na kaana uku za a yi, sai wanda suka kawo ta suka koma garinsu ita aka barta a gidan Mai Gari a kan cewa idan an gama maganin ta koma. Da yamma motar su Rahma ta yi wa garin Ƙundu dirar mikiya, a ƙofar gidan Mai Gari motar ta tsaya, tun kafin ta fito ta hangi Sheik yana tsaye da wasu mutane, gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin wani balarabe fari tasss da shi yana sanye da baƙar jallabiya ga gashin kansa kwance lufff kamar na jarirai. Sajensa da ya ƙara ƙawata fuskarsa shi ne abin da ya ja hankalin ta cikin sauƙi, gemunsa da ya tashi ziyat a habar shi kaɗai ma abin kallo ne. Ta shagala da kallon Sheik bata san lokacin da ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba. Sheik bai ganta ba saboda hankalinsa ba a wajen motar ma yake ba, dakyar ta samu ƙwarin gwiwar fitowa daga motar. Abin yana bata mamaki ya aka yi aka samu balarabe a wannan kwaraɓaɓɓan ƙauyen, ko ita da take bahaushiya ba don wannan damuwar da suke ciki ita da Mummyn ta ba, babu abin da za ta shigo ƙauyen nan ta yi. Direban ne ya bita da akwatin kayanta wanda ta ɗakko kala uku da kuma su madara kwanfiles da sauran abubuwan buƙata saboda ba za ta iya cin cimar garin ba, kuma dai a yadda ta yi fushi da Daddy tana so ta ɗan nesanta kanta da shi, sannan sai ya zo har garin an magance matsalar wannan dalilin ne ya sa ta taho da kaya. Mai Gari ganin Rahma ya cika da murna, har ya kasa zaune da tsaye ganin ƴar ɗan uwansa da ya fi ƙauna. Mutane suna ta mata sannu amma ko kallo basu ishe ta ba, tana ta waiwayen inda za ta ƙara ganin balaraben nan amma bata ga inda ya yi ba. Direban komawa ya yi a cewarta za ta masa waya ya zo ya ɗauke ta, in buƙatar hakan ta taso. Da suka yi sallar isha'i Sheik yake cewa Mai Gari ya fara sha'awar saka kayan hausawa babbar riga da ƴar ciki, Mai Gari ya yi mamaki ganin dai Sheik bai saba da saka kaya in ba na larabawa ba, amma ganin ya ce tana so sai ya ce za a siyo shaddodi da yadika masu tsada a ɗinka masa. Shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda ya fara ɓoye breast ɗin ƙirjinsa, sannan yana so idan ya je wajen malamin da yake karɓo magunguna ya bashi kuɗi a siyo masa bireziya saboda ya fara suturta ƙirjinsa tun da yana ganin bra ɗin za ta sanya ba za a lura da tudun ba kuma musamman idan ya saka kayan hausawa da babbar riga. Rahma ta faɗawa Mai Gari gabaɗaya damuwar da ta kawo ta, Mai Gari dama ya san cewa ɗan uwan nasa ya yi aure amma kuma bai san cewa bai sanar da iyalinsa ba, don haka sai ya nunawa Rahma zai kira shi ya masa magana za a san abin yi a hukunta Daddy, ta ji daɗin furucin shi ma kuma ya mata hakan ne don ta fita daga damuwa. A nan take tambayarsa labarin wani balarabe da ta hanga lokacin da ta iso, Mai Gari ya kwashe komai ya faɗa mata, dangane da Sheik a take ta ji ta kamu da muguwar ƙaunarsa, kuma in dai shi ne ta amince ko a cikin kara ne tw zauna ba wai a ƙauye ba. Ta sa a ranta idan Daddy ya zo garin nan ba za su tafi ba sai ta mallaki Sheik a matsayin miji, dole Daddy ya gina musu gida mai kyau inda za su rayu, ta haifi ƴaƴan larabawa, idan kuma Sheik ɗin yana so sai su tafi Abuja su rayu a can amma dai bata da mijin sai balarabe daga ƙasar Yemen. Bata faɗawa Mai Gari ba ta dai bar maganar a zuciyarta zuwa safiya. Haka ta kwanta cike da shauƙi da ƙaunar Sheik tana fatan ya zo mata a mafarki. *DARE* Darebya tsala, kowa yana bacci sai dai Sheik sa tun da ya ga baƙuwar nan ya kasa sukuni, idanunsa yanzu ma sun hana shi ya runtsa saboda ya sanya tunanin ta a ransa kawai burinsa ya ji matar nan a kusa da shi. Juyi ya yi yana jon tunanin da ya saka a ransa ya hana shi sukuni. A take ya yanke shawara, tsaye ya tashi ya ɗako wani zani da hijabi cikin kayan da yake tsinta idan aka zo aka taru ana karɓar magani, sai a ga hijabi wani lokacin a rasa mai shi ko ɗankwali ko hula ta mata ko zani. Zanin ya ɗaura ya saka hijabin, yana jin cewa yau ko ta halin ƙaƙa sai ya je ya ji ɗumin jikin baƙuwar nan, shaiɗan yana ta zuga shi yana masa linzami. A zuciyarsa ya ce "Ai na lura tana cikin buƙatar kulawa da soyayya, kuma ai ba za ta gane waye ba, buƙatar maje hajji sallah" Ya faɗa yana fitowa waje, yana duba gabas da yamma arewa da kudu ya ga babu kowa sai kukan karnuka kawai. Katangar Mai Gari ya kama ya ɗare, da yake bata da tsawo ya sauka a hankali, yana lashe baki ya shiga ƙarewa ɗakunan gidan kallo yana so ya gano inda zai samu baƙuwar, ko dogon tunani ba ya yi ya fi so kawai ya ganshi a ɗakin. Ɗakin matar Mai Gari ya fara leƙawa amma jin ana sakin munshari kamar an shaƙe raƙumi sai ya zaci ɗakin Mai Gari ne a tunaninsa Mai Garin ne yake munsharin. Wani ɗaki ya shiga yana ji a jikinsa tabbas a nan masoyiyar tasa take, da sanɗa ya ƙarasa ya haye katifar ganin ta lulluɓe ruf da bargo shi na ya bankaɗa ya yi wa kansa masauki a ciki. A hankali ya lallaɓa ya rungumo na bargon, a zuciyarsa yana cewa 'Alhamdulillahi, ƴar fara zo ki ji lallausar fatar balarabe' Bai tsaya a nan ba ya kai baki zai kamo bakin, amma cikin rashin sa'a sai ya cafko hancin, ya manta ma da ƙirjinsa da aljannu suka masa ajiya, jin an cafki hancinsa sai hakan ya hana na cikin bargon shaƙar numfashi da kyau, yana riƙe da hancin a bakinsa yana sauke numfashin cin nasara da cikar burin sa. Fisge-fisge na cikin bargon ya fara, yana son ƙwacewa amma Sheik ya ƙara zage ƙarfinsa ya maƙalƙale. Cikin hargitsi aka ce "Kai wai waye a nan ne, wane shegen ne ya shigo mini bargon yana lasar mini hanci kamar tsohon maye?" Sheik a zuciyarsa ya ce 'La'ilaha ilallahu ba baƙuwa ba ce Mai Gari ne ai!" Gaban Sheik ne ya doka da ƙarfi ya fara janyo salati a zuciyarsa da fatan Allah kuɓutar da shi, a take ya fara ƙoƙarin ficewa daga cikin bargon, Mai Gari jin haka sai ya kai hannu ya riƙo shi, tunanin Mai Gari rigar mutumin ce ya riƙo ashe hijbin ne ya riƙe saitin fuskar, Sheik ya rasa ta ina zai fito da kan nasa ma domin Mai Gari ya cukwikuye, yana faɗin "Wane kwarton ne wai, wato an ga na yi baƙuwa daga birni" *A NAN NA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 MAI SON SHIGA GROUP YA ƘARANTA ZAO BIYA 500, MAI SON CMPLT DOCMENT 800* IDAN KINA SON JIN YA ZA TA KAYA KI BIYA KI KARANTA A NUTSE *MAMAN AFRAH 09025576222* *ZA A BIYA TA FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14