Share this page
na zo gidan nan cin arziƙi amma kike ɗakko mini dala ba gammo haba zuciyata ki mini lamuni, ki rufa ni ki saya, ki rufa mini asiri kar ki ja mini tozarci, don abin da kike so ba za ki samu ba ni na sani' Ya ƙarasa faɗa a zuciyarsa yana fito da wayarsa, number mahaifinsa Mai Garin Ƙundu wanda yake ɗan uwa ne na jini ga Daddy, ya shiga kiransa, amma bai ɗauka ba, sai da ya kira sau uku ba a ɗauka ba sannan ya mayar da wayar ya akiye a kan katifar yana mai kifa kansa a jikin katifar yana jin yadda son Rahma yake fara huda zuciyarsa a hankali. *LAMI* Kallon Sheƙeƙe ta yi wa Tunde tana riƙe da ƙugu ta ce "Tunde na faɗa maka ba ya nan, ni nan da ka ganni da haushin kuɗin da ya guje mini na kwana, amma in kana ganin kamar yana nan na hana shi fitows ga ƙofa ka zo ka shiga ku fafata, ka ga sai a yi ko a kai ko a shi" Idanu yake zarowa jin furucinta shi dama ya tsani bayar da bashi saboda ba yadda zai yi ne ya ba Ibra amma gashi cibi yana neman zama ƙari. Kamar zai yi kuka ya ce "Ba zan yarda ba sai kin biya ni kuɗin da nake bin mijinki" Wani uban tsaki ta yi ta ce "Da na san lokacin da kuka yi, to ko biyar ba zan bayar ba idan rigima kake ji na dame ka na shanye, ni na fi inyamuri iskanci dan ka ji in faɗa maka" Ta faɗa tana wani zazzare ido. Haushi da takaici ya cika shi ya ce "Ko za ka daure ki ranta masa" Hanci ta yatsina ta ce "Ko naira biyar ɗita ba za ta yi ciwon kai ba, ka kama hanya ka je gidan kakarsa wataƙila tana da abin biyanka" Tana gama faɗar haka ta juya ta bar shi a tsaye yana riƙe da takarda yana sababi cikin gurɓatacciyar Hausar sa . Yana fita bai zame ko ina ba sai gidan Inna Tasallah kafin ya ƙarasa can ya haɗu da wani wanda jiya yana zaune a fadar Mai Gari aka yi wa su Lamu shari'a. Ganin Tunde yana tafiya yana ɗaga takarda yana masifa ya masa magana, bayan sun gaisa da shegen tsegumi sai cewa ya yi "Ah, ah Oga Tunde sai ina kake sauri" ,Kamar jira yake ya ce "Tsausayi mana ya sa na ba wannan Ibra bashi, ya ce zai dawo daga kasuwa jiya ya mini blance amma yanzu na je gidanaa wai ba ya gari yanzu sai cewa ta yi matarsa wai sai dai in je gidan Kakarsa ta biya ni" Buɗar bakin mutumin sai cewa ya yi "To ai kai faɗuwa ta zo daidai da zama" Tunde ya saki baki cike da jin haushin wancan ɗin yace "Wannan wulaƙanci ne, ashe kana mini baƙincikin kasuwancina in ba haka ba ni kake wa fatan faɗuwa?" Ya faɗa yana nuna kansa. Da sauri wancan ɗin ya ce "Haba Oga Tunda ya za a yi in maka fatan faɗuwa a sana'a Hausa ce fa na maka wato karin magana, abin da ya sa ma na faɗa saboda ina sp in jaddada maka cewa wannan Kakar tasa kuɗi gare ta jiyan nan a fadar Mai Gari muna zaune sai da ta biya kuɗin saniyar Jummai... Tun bai gama bashi labarin ba Oga Tunda ya yi gaba yana sauri yana zabga masa godiya, saboda so yake ya je kar kuɗin ya ƙare. Inna Tasallah ce zaune a bakin gadonta ta sha ɗaurin ɗankwali gwaggwaro, tana zaune robar kayan miyarta a ƙasa a gabanta, hannunta kuɗi ne naira ɗari da saba'in dama da safe ta yi cinikin naira ɗari ya zamana tana da 200 shi ne ta saya koko na talatin ta sha a haka ko suga bata saka ba, duk don kar ta saya sugan tun da ita bata ƙaunar abin da zai taɓa mata kuɗi sai dole. Sai maimaita irgen kuɗin take tana ta washe baki a fili ta ce "Kai jama'a wato a jikin kuɗi akwai wani maganaɗisu wanda idan kana irgawa duk ɓacin ran da kake ciki sai ka ji ya washe, Allah ka ƙarawa kuɗi daraja" Ta faɗa yana gyara naira ashirin ɗin, da yake ɗari ce guda, sai hamsin sai ashirin ɗin. Tana cikin wannan yanayi na nishaɗi kamar daga sama ta fara jin ana rafka mata sallama, abin mamakin ma yadda ta ji muryar ba ta bahaushe ba ce, da sauri ta ɗaga filo ta cusa kuɗin a cikin rigar filon ta gyarawa rigar filon wajen ta gyara ta ja robar kayan miyarta ta tura ƙasan gado a zuciyata tana faɗin "Yanzu na shirya ko tashin bob(Bomb) Za a yi na ɓoye kayan sana'a ta kadarata, haka kawai ka ji inyamuri yana rafka sallama, har ta buɗe baki za ta amsa sai ta fasa, fitowa ta yi daga ɗakin, wani tsohon gatari ta ɗauka ta nufi ƙofae gidan a ganinta koyaushe gwara ka zauna cikin shirin kar kana zaune a zo a cika da yaƙi" Ta faɗa tana dosar zauren tana ɗan ɗar-ɗar. . Tunde yana tsaye ya ga Inna ta fito riƙe da gatari, a tsorace ya fara ja da baya yana faɗin "Ba tashin hankali bane ya kawo ni" Ganinsa sai Inna ta sauke gatarin da ta ɗaga saman, ta shiga kallonsa da mamaki ta ce "Bayerabe mai kuma ya kawo ka gidan nan?" Kallonta ya yi ya ce "Dama Ibra ne ya ci bashi a wajena... Tun bai ƙarasa ba Inna ta fara sababi tana faɗin "Allah sa uban bashi ya ci ba bashi ba, ni ina ruwana ko na san lokacin da kuka yi, ko ka taɓa gani ko siyen ashena na je shagonka, saboda ba na son arne ya ƙaru da ni, in sha fafutukar neman halal ɗina ta hanyar siyar da kayan miya amma in je in yi wa arne ciniki, on bar musulmi to na san ciwon kaina ehe" Ta faɗa tana muzurai Cike da jin haushin ta cw za ta yi wa musulmi ciniki ya ce "To in ma liman za ki yi wa ciniki ni babu ruwana, yanzu ki shiga ki fita ki biyani kuɗin da nake bin jikan ki tun da lika biya kuɗin saniya ma... Tana masifa ta ce "Wato ga Tasallar mahaukata, sai aka ce ni gabaɗaya rayuwata a biyan bashi za ta ƙare, ni ba zan yi abin kaina ba sai dai in yi ta biyawa Ibra rigimar da ya ɗakko, tun yana ƙarami nake faman asarar kuɗi a kansa, kuma wanda ya ce na biya kuɗin saniya ƙarya ya shirga maka, don ni wallahi Jummai ko kuɗin igiyar ɗaurin saniya ban bata ba bare kuma kuɗin wata saniya" Ransa a ɓace ya ce "Ko baki biyata ba ni dai dole ki bani, mayukan bilicin ɗin da ya karɓa kaɗai ma ba na ƙananan kuɗi ya karɓa ba idan baki bani ba sai na je birni na ɗakko ɗan sanda... Kamar za ta kai masa duka ta ce "Gwafar uban ɗan sandan, idan ka yi asarar kuɗin motar zuwa birnin ka ce ɗan sandan na ce ba sanda ba ko ƙota ce na bi ta kanta da gudu aikin banza da wofi, wani shegen ya ce ka bashi bashin man bilitin(Bilicin) Gabaɗaya ka sauyawa yaro kamanni da man turawa ka mayar da shi fata kamar ƙullin ƙosan da ya sha jan tattasai, fuska tana masa tabbare-tabbare, ni ba don na yi wa Ibra farin sani ba wallahi tsabar wannan shafe -shafen da yake ba zan gane shi ba, duk ya sauya halitta da jikinsa da baƙin bayan tukunya bambancin kaɗan ne wajen baƙi, amma yanzu gabaɗaya jikinsa babu baƙi, ban da ma Ibra ya girma yanzu na tabbata ko mazaunansa aka kwataye aka buɗe sai an samu sun yi fari ina dalili" Ta faɗa tana hararar Tunde da yake jin ba don kar a kore shi daga garin ba, ko kuma a yi shari'a da shi da tuni ya make Inna ta faɗi sumammiya saboda takaici. Ganin bashi da niyyar tafiya ta yi wurgi da gatarin tana faɗin "Yanzu zan yi maganin ka, ka bari in shiga in fito, kai ba kai kaɗai ba duk wanda ya ƙara zuwa neman bashi wajena, bayan ba ni na ci ba aradu sai ya gwammace kiɗa da karatu" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma ta shiga cikin gidan tana faɗin 'Anya Ibra zai ga annabi kuwa, a ce ka gudu da saniyar mutane, jiya ma da tsakar rana sai da me wainar rogo ta zo karɓar jaka biyu da rabi (500) Yo in ba fashi da makami nake yi ba ina zan samu wannan maƙudan kuɗi in biya ta in na biya kuɗin bashin Ibra sai na daina siyar da kalwa da kuka wallahi' Murfin wata ƙatuwar tukunya irin ta girkin gidan biki ta ɗakko, tana ɗauka ya fara rinjayarta kasancewar yana da nauyi, amma a haka ta nufi zauren da ɗan saurin ta, Tunde yana ganin Inna ya fita a guje don takardar ma a zauren ya barta, yana gudu yana masifa cikin yarbanci. Inna har ƙofar gida ta fito riƙe da murfin tana huci saboda nauyin da ya mata.... *A yi haƙuri da wannan yau ko malam bamu leƙo ba, in sha Allah sai a next page* MAMAN AFRAH 09025576222 [7/7, 7:36 PM] Mom mashkr & Afrah: 👳🏻 *MALAMIN BOGI*👳 NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 7 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha. Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE 👉join Here. Za ki sha mamaki!🤩 Muna da ✅Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅Kayan gyaran gida masu kyau 📞Tuntubi mu:+2347077532253 📩DM ;Whatsapp 📸IG/Tiktoc:@imzeed-venture *SHEIK* Gabaɗaya sai hankalinsa ya tashi ganin mutane da ya zo wajen don ya taimaka musu suna gudunsa, wato wasa tare amma ci bamban. Duk mutane an koma can nesa da kukar ana kalllon ikon Allah, Sheik kuwa gabaɗaya ya yi saranda ya san tabbas abin kunya yana dab da bayyanuwa, don bai san yadda zai kuɓuta daga wannan tarkon ba. Kan ƙwarangwal ɗin nan ya fara yawo a saman kukar da yake mutane babu wanda yake ganin kan sai Sheik abu ɗaya dai suka sani shi ne in ba aljannu ba babu wanda zai ɗaga Sheik ya kai shi saman kuka. Kan ne ya nufo kusa da fuskar Sheij, yana ji yana gani kan yake nema kaiwa bsminsa sumbata, Sheik ya shiga kawar da kai gefe, don ya san tabbas akwai gagarumar matsala a ce , amma kan kamar an ce dole ne ya sumbaci Sheik, duk ya ruɗe amma har lokacin saboda ƙarfin hali fantekar kuɗinsa tana ƙanƙame a hannunsa. Gashi yana son ya ɗakko robar ruwan maganin nan ta cikin fantekar ya watsawa kan amma kuma tsoro da fargaba ba zai bari ya yi hakan ba, ba ma a nan gizo yake saƙar ba so yake ya maje, ya jajirce kar ya bari rauninsa ya bayyana ga ƴan gari don idan ya bari suka gane yana tsoro to kuwa akwai babbar matsala, kuɗin da yake saka ran ci daga gare su ma zai zama ya masa wahala saboda za suke masa kallon kamar dai ba malamin bane. Lura da ya yi basa ganin kan wannan ya san hakan ba ƙaramar matsala ba ce amma da hakan yake ƙoƙarin saita kansa. Baki ya buɗe zai yi magana kan ya karkata ya saka masa kunne a baki, ma'ana ƙwarangwal ɗin ya saka kunnesa a bakin Sheik. Sheik a zuciyarsa ya ce 'Mai Gari a kawo taimako saboda aljannu sun fara mini ɗaurin goro' A fili kuma ya shiga ciccira idanu, amma saboda ƙarfin hali yana so ya ɓoye halin da yake ciki, duk da abin yana neman cin tura. Mai Gari a zuciyarsa ya ce 'Shikenan ma in suka ɗauke ka, uban kuɗin nan da ka tara ai sai na maye gurbinsa, kafin Allah ya sa ka kuɓuto' Ya faɗa idanunsa a kan fantekar kuɗin saboda gani yale matsayinsa na Mai Gari da a ce mutanen gari haka suk tara masa kuɗaɗe da yanzu ya yi ban kwana da talauci. Sheik da wani irin sauti ya ji wannn kan yana masa magana yana cewa "Ibra, ka baro garinku ka zo wannan gari baka san matsalolin da suke ciki ba, to ka kawo kanka cilin gagarumar matsala, ko dai ka haɗa kayanka ka koma inda ka fito ko kuma mu shiga fafatawa da kai" Tsuru Sheik ya yi yana jin maganar kamar tana amsa kuwwa amma ya lura shi kaɗai yake ji, idanu ya sauke a kan uban kuɗin da aka saka a cikin fantekar nan masu uban yawa, duk da yawanci ƙananun kuɗi ne amma ya lura akwai ƴan dubu-dubu. Ganin kuɗin nan sai ya ji babu gudu babu ja da baya tun da gani yake babu mai ja da cikar burinsa, wani yawu ya haɗiye yana muzurai, kai ya ƙara cewa "Ka amince za ka bar garin Ƙundu a yau?" Wannan tambaya ta sanya ya ji wani takaici saboda ga shi dai a kwana ɗaya ya haɗa wannan uban kuɗi babu aikin fari bare na baƙi, to ina ga ya yi watanni, duk da shi a ransa yana ganin in har ya samu dama a shekara goma ma ba zai bar garin Ƙundu ba, tun da ya ga wannan hanyar arziƙinsa. Shiru da ya yi sai kan ya ce "Shirunka ya nuna ba za ka tafi ba to mu zuba mu da kai" Ana gama faɗa masa haka sai ya ga kuɗaɗen cikin fantekar sun fara ɓacewa, idanu ya shiga zarewa yana son yin ihun kuka amma babu dama, ba ya so ya bayar da kansa a wajen Mai Gari da mutanen gari. Gabaɗaya cikin fantekar sai robar maganin kaɗai ta rage sai wata tsohuwar naira biyar. Takaici ne ya kama shi yana ji a ransa da a ce shi malamin gaske ne ba MALAMIN BOGI ba da sai ya yi addu'ar da zai ƙona aljannun garin gabaɗaya, tun da gashi yanzu ya ga samu ya ga rashi. Kafin ya gama wannan mamakin sai ya ji an fara tura shi daga baya kamar dai idan mutum ya hau lilo ake tura shi yana yin gaba yana dawowa baya, to haka ya ji, idanu ya runtse tun da shi banda fantekar wannan da ya riƙe babu wani reshe da ya riƙe, illa wuyan rigarsa ne kawai yanzu a maƙale da bishiyar kukar. Turashin da aka fara sai ya fara ganin kamar zai hantsila ƙasa, suratul nasi ce kaɗai ya samu nasarar wartowa a bakinsa ya shiga karantowa babu sautin yana fita a hankali sai shi kaɗai yake ji, su Malam Liman da suke ƙasa da mutanen gari suna kallon yadda ake shilla Sheik bakinsa kuma sai kaiwa da komowa yake alamar yana magana sai dai kasancewar a can sama yake basa iya jin furucin nasa. Ya daɗe a haka har ya fara fidda rai da rayuwa, hawaye suna safa da marwa a saman fuskarsa. Dakyar ya samu ya daina hangen ƙwarangwal ɗin kan wannan don ya ɓace ɓat, sannan an daina cilla shi yana lilo. Ganin haka sai ya fara tunanin mafitar da zai wanke kansa ba tare da mutanen gari sun gano ainihin abin da yake faruwa ba. Hannusa ɗaya ya cire daga jikin fantekar ya kaiwa jikin reshen kukar wani uban naushi, har sai da bayan hannun ya fashe alamar ƙumewar da ya yi, ya buɗe murya yana faɗin "Allahu akbar!" Sai da ya kaiwa reshen nan naushi sau biyar yana ambaton kabbara, duk da azabar da take ziyartar hannun nasa. Ji ya yi an finciko rigar tashi daga inda take a maƙale, idanu ya waro ganin ya nufi ƙasa gabaɗaya mutane aka dare daga wajen, Sheik fatansa da addu'arsa Allah ya sa ya faɗa a kan Liman ko Mai Gari, sai dai saboda ƙarfin hali yana dab da faɗowa ya buɗe murya yana faɗin "In sha Allahu balaraben malami ne da nasara a kan ku, garin Ƙundu ya fi ƙarfin ku aljannu" Da wanann kalaman ya faɗo sai gashi wancakar a tsakiyar wajen, ƙatuwar fantekar wannan ta kife kansa, gabaɗaya jama'a aka yi kansa, faɗuwar da ya yi ya ji hular gashin sa tana neman cirewa. Ga faɗowar da ya yi ƙugunsa kamar zai cire amma dai saboda wannan ce hanyar cutar jama'a da zai yi wajen samun kuɗinsa dole ya daure. Mai Gari ne ya miƙa hannu saman kan Sheik ya cire fantekar yana ta faman jera masa sannu. Duk da ya jigata kuma idanunsa a rufe amma a haka yake jero kabbara. Jin hular gashin kansa tana nema zamewa ya yi azama ya dafe kansa da hannu, mutane duk an kewaye shi ga hawayen nan da ya yi ga bayan hannunsa ɗaya a dauje, da kaɗan-kaɗan ya shiga buɗe idanun kowa ya zuba masa na mujiya ana jiran a ji ta bakinsa. Hannu biyu Mai Gari da Liman suka saka suna ƙoƙarin tada shi zaune, duk fa haka bai yi wasa dafewar da ya yi wa hular gashon kansa. Mai Gari ne ya buɗe baki ya ce "Sannu Ya Sheik, Allah ya maka alam nashra" Ya faɗa cike da tausayawa. Cike da ƙarfin hali Sheik ya ce "A haba kar ka damu Mai Gari ai mu Allah ya riga ya bamu, duk runtsi ba zan bari a cutar da garin nan ba sai inda ƙarfina ya ƙare" Liman ne ya ce "Kamar ya Sheik kai da ka sha wahala amma kake kiran sai ƙarfinka ya ƙare?" Sheik a zuciyarsa ya ce 'Ka ji masu hana ruwa gudu, waɗannan basa mutuwar tsakar ɗakinsu, wato zani zai kuncr mini a kasuwa' A fili kuma ya ce "Ai ni nan na hangi wani bala'in tashin hankali, gingimeman yaƙin duniya na uku ne aljannu suka shirya tsakanin su da mutanen garin Ƙundu, gabaɗaya so suka yi su tarwatsa ku, su yi muki bazata, cikin ƙoƙari don ba na so ku firgita hankalinku ya tashi, shi ya sa a zuciyata na ringa addu'a a kan iska ta kai ni saman kukar, domin daga can ne aka shiryo dakarun yaƙin, shi ne ma kuka ga na tashi a saman iska, to a can ma ku abin da idanunku yake gani da ban abin da yake faruwa da ban, kuna ganina a rataye amma bakwa ganin gwagwarmayar da take faruwa, yaƙi ne ake tafkawa suna kawo sara fa suka da wuƙaƙe da adda ta aljannu a ƙarshe duk na ƙwace makaman na ci su da yaƙi hatta wanann hannun nawa haɓar wani aljani na yi ta naushi da shi kun ga yadda na ji ciwo, ku za kuke gani ina naushin kuka amma ni ina ganin aljani ne mai ka bakwai, ganin dai zan musu lahani duk suka watse don duk na jinyata su, saboda baƙin talaucin da suke ciki ma, na raba musu kuɗin da kuka tara mini, domin na ji suna cewa za su bazo garin duk wasu kuɗaɗe su kwashe" Gabaɗaya maza da matan wajen suka yi wata kabbara tamkar a filin sallar idi. Suka ce "Allahu akbar" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin ƙaryar da ya zabga ta kuɓutar da shi, a take Mai Gari ya saka ƙasan babbar rigarsa yana sharewa Sheik ƙasa a bayan rigarsa ganin faɗuwar da ya yi duk ya kwashi ƙasa. Cike da tausayawa yana miƙa hannunsa kan hular Sheik daga ƙeya yana karkaɗe masa ƙasa, Sheik kuwa sai ƙara danne hular yake gudun afkuwar matsala, Mai Gari ya ce "Lallai garin Ƙundu ya yi dace mai shahada da sadaukar da kai ga mutanen garo domon ceton rayuka, in ba haka na ta yaya za ka amince da garin nan har haka?, Ni da ya kamata a ce ni zan yi wannan sadaukarwa" Sheik cike da lanƙwasa kuryarsa ya ce "Ina ai in har ina garin nan babu wata matsala da za ta tunkaro ku in ƙyale ta, saboda mu can a ƙasashen larabawa haka muke yi bare ni da na baro ƙasata don in zo in taimaka muku" Gabaɗaya sai aka shiga jinjinawa Sheik bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, haka ya ƙara girma a idanun jama'a kowa yana yaba masa. Haka aka yi yuya guda don raka Sheik gida ya huta saboda faɗa da aljannu. Amma a ransa baƙinciki ne fal na yadda aljannun suka ɗauke masa kuɗin da ya tara, yana murna ya samu kuɗi ashe dai da sauran rina a kaba. Har cikin gida aka rako shi ana girmama shi, da zai shiga ɗaki Liman ya ce "Sheik Allah gafarta malam ga robar ruwan maganinka, da naira biyar ɗin nan, ita da ka rage ta a cikin fantekar ko maganin aljannun za a yo da ita" Ya faɗa cike da girmamawa yana miƙa masa don an ba mai fantekar fantekar ta. Sheik kamar ya yi kuka ya ce "Eh ai ina sane na rage ta, ka san har hawayen tausayin garin nan na yi a saman kuka na ji tausayinku sosai" Ya faɗa yana danne takaicin da yake ji a ransa ga zafin da hannunsa yake yi. *DA YAMMA* Ƙofar gidan Sheik ya cika da jama'a maza da mata, masu karɓar magani, saboda ya ce ba za a ke bada magani a titi ba saboda kowa abin da zai nemi magani sirri ne a wajensa bai kamata ake faɗa ba, hakan ya sa aka yi dogayen layi biyu na maza da ban na mata da ban, aka ce idan mace ɗaya ta shiga sai namiji ɗaya ya shiga. Wata mata ce ta fara shiga gidan da sallama, Sheik ya amsa, yana mai mata umarnin ta shiga, shiga ta yi ta samu waje daga can nesa wajen ƙofar ɗaki ta zauna, shi kuma yana daga kan sallay ya lanƙwashe ƙafa sai wani ƙaton baho a ajiye daga can bayansa. Gyaran murya ya yi ya ce "Mai yake tafe da ke?" Matar wani daɗi ne ya cika mata rai jin muryarsa, sai yanzu take tabbatar da maganar mutanen gari da ake cewa maganarsa hausar ma bata fita, ba ma wannan ba farar fatarsa kaɗai ji take kamar wanda ta je garin makka. Cike da ɗan diriricewa irin tana magana da balarabe ta ce "Malam dama mijina ne ko kaɗan ba ya kiran sunana, sai ya kira kishiyata sa sunanta amma ni sai yake kirana madam, kamar wata inyamura mai bashi hayar gida" Ta faɗa cike da takaici don dama ta daɗe tana son ta magance wannan matsalar amma du wajen malaman da ta je sai a ce mata wai soyayya ce da girmamawa, waɗanda kuma take ganin sun cinye mata kuɗi ko an bata maganin ma ba ya yi, amma dai yanzu tun da ta samu balaraben nan wanda aka ce aljannu ma yana maganinsu, to tabbas ta san ta zo ƙare kukan ka. Sheik a zuciyarsa ya ce 'Mata masu duniya, mata iyayen kishi wato ita ba wata babbar matsala ba ce da ita ma"' Amma a fili sai ya ce "Allah sarki haƙiƙa na jimanta miki, wannan ba ƙaramin abu bane a ce mijinki yana kiranki da suna madam, kamar dai wata tunkiya, ko kuma bayerabiya mai gasa masara a bakin titi" Ya faɗa yana ɗan mayar da fuskarsa abin tausayi. Kai ta kaɗa irin ka ji dai ji, a zuciyarta tana jin daɗi don ta tabbatar da cewa wannan ba sunan soyayya bane ko na girmamawa. Yana ɗakko wani ƙullin magani ya dube ta da kyau ya ce "Wannan maganin ki samu ƙatuwar zabuwa ko kaza ki dafa da wannan maganin, ki juye masa ita duka amma sai ranar bakin girkin ki, kar ki ci ko ƙafar kazar, ki ce masa takanas kika dafa saboda kina son sa don ki faranta masa, sai ya kusa cinyewa ki ce masa kina da wata buƙata in ya tambaya sai ki ce daga yau ya daina ce miki madam, zai buƙaci sunan da zai kira ki da shi sai ki zaɓa ki faɗa masa, daga ranar zai daina kiran ki Madam!" Wani daɗi ne ya baibaye ta, ashe ma aikin ƙarami ne take ta ƙunsar baƙin ciki, kullum in ta ji ya kira kishiyarta da sunanta ita ranta ɓaci yake, ta lura idan ya ce mata madam kishiyarta har wata ɓoyayyar dariya ta cusa haunshi take mata. Maganin ta karɓa ta ce "Malam nawa ne abin sadaka" Sai da ya ƙare mata kallo yana son gane tana da halin kuɗaɗe masu yawa ko kuma kuɗi kaɗan take da shi, sai ya daure ya ce "Ai abin sadaka ba ya kaɗan ba ya yawa" Ita kuma jin haka sai ta buɗe jakarta ƙarama, ta fito da wasu uban kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar da ƴan dubu-dubu kuɗin gyaɗar yin ƙuli-ƙulinta ne wanda za a sayo mata buhu guda, mai da ƙarago take na siyarwa, malam sai washe baki yake a ɓoye yana ganin yana zaune a ɗaki zai ci bati. Amma sai ya ga ta ajiye kuɗin a gefenta tana ta duba cikin jakar, a tunaninsa wani za ta ƙaro sai ya ga ta fito da naira hamsin, sai kuma ta ɗauke kuɗin mai yawan da ta ajiye a gefe ta mayar cikin jakar ta zige zip ɗin, ta ɗakko hansin ɗin da hannu biyu ta zo gabansa tana cewa "Gashi Malam, Allah ya biya buƙatu, muna godiya babban balarabe na ƙasar larabawa" Tamkar Sheik ya saki ihu haka ya ji, kamar shi Sheik amma ta bashi hamsin. Tsaye ta miƙe bayan ta ajiye tana gyara mayafinta, ta juya tana masa sallama, ko amsawa bai yi ba, duk takaici ya ishe shi, yana jin da na sani dama bai ce mata abin sadaka ba ya yawa ba ya kaɗan ba. A

Chapter 6 of 14