Share this page
mini mutuwa yo mutuwa mana wannan da aljannu suka zama danginta jinin jikinta za a kawo min ita, baku san ni ɗin ma ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama ba, babu wani malam kawai MALAMIN BOGI ne' Cike da murnar kalamansa Mai Gari ya ce "Ai sai mu je ko? Dama mutane sun kewaye ta in ji mahaifiyar amma kowa cewa yake ai matar babban malamin larabawa ce daga ya zo komai ya ƙare" Baki Mai Gari ya washe ya ce "Shi ya sa nake alfahri da shi a garin nan Allah ya tarfawa garinmu nono" Sheik a ransa ya ce Ai dama ba wahalalle sai kwaɗayayye, haka kawai garin neman gira in je in rasa ido, ni ban amfani kuɗin da na tara ba in rasa abin da kuɗi ba zai saya ba, amma ya na iya haka zan ringa tarar aradu da ka, in ta yi ruwa rijiya in bata yi ba masai' A fili ya ce "Ai kar ka damu mai gari, mu ko a ƙasashen larabawa bamu san tsoro ba, zan yi ta ba mutanen garin nan magani mata na basu na gyaran aure kai kowa sai ya samu abin da yake nema" Sirikar da Mai Gari suka yi kabbarar jin furucin ta, tana murna ƴarta ta samu mijin nunawa sa'a. Ɗaki ya shiga ya ɗauko magani ya ɗakko dogon carbinsa ya fito, Sirikar Sheik ta ce "Ai Allah ya kawo mana ƙarshe wahala, yo wahala mana da asubar fari idan aljannunta suka tashi kowa na gidan nan sai jikinsa ya faɗa masa, haka za ka ji saukar doka da dorina" Gabaɗaya sai ya ƙara kiɗimewa zuwa yanzu ya gama tabbatarwa cewa matsala ya aura wato har tana duka. Tsabar ba ya hayyacin sa sai ya bi bayan su a haka. Mai Gari da ya waiwayo ya ce "Subhanallahi Ya Sheik kana lafiya kuwa, baka saka takalmi ba" Cike da wayincewa ya ce "Ashsha duk saurin zuwa nemowa amarya lafiya ne" A ransa ya ce 'Lallai akwai lauje cikin naɗi, yau dai na yarda cewa dalili ne kaɗai yake sa a leƙa gaban sirika' Takalmin ya ɗakko, lokacin da suka doshi gidan, sai haɗuwa da jama'a suke a hanya ana girmama Sheik basu san cewa ba ya gane abin da suke faɗa ma, shi hankalinsa ba ya jikin sa musamman da suka kusa shiga gidan suka ringa jin wani kururuwa da iface-iface. A zaure suka tsaya, Sheik zuwa yanzu ko magana ba ya iya yi ta fito sosai sai jan carbi da yake ta faman yi yana addu'a a ransa cewa, Allah ya ɗora shi a kan aljannun nan, shi yanzu so yake ya cigaba da bayar da magunguna amma batun aljannun nan ba so yake yi ba. Sai tashin hanyaniya da suke ji ta mata a cikin gidan, jim kaɗan sai ga sirikar Sheik ɗin ta dawo tana cewa "Bismillanku ai gata can ma jikin ya matsa, amma abin mamaki sunan Sheik take ta faman faɗa" Sheik da ya ji faɗuwar gaba an ce ana kiran sunansa sai ya yi zaton ko dai sunan sa na asali ta faɗa wato Ibra tun da ya san su aljannu babu abin da basu sani ba. Da ɗan diriricewa ya ce "Ya subhanallahi wane sunan daga ciki?" Ta ce "Sheik kawai take cewa, amma idanunta a rufe" Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ta shiga gaba suna biye da ita, duk mata ne da alama ƴan taron bikin ne da kuma kai amarya. Ɗakin da take karaɗin ihun ne wanda sai da aka rufe daga window ake leƙen ta. Mai Gari ne ya ja ya tsaya yana mai cewa "To Ya Sheik a fito lafiya" Ɗiff Sheik ya yi yana jin faɗuwar gaba tana ratsa dukkanin gaɓoɓin jikinsa da zuciyarsa, amma haja ya daure ya gyaɗa masa kai yana mai faɗin "In sha Allah" Haka sirikar tasa ta buɗe masa ƙofa ya shige, har da rufo ƙofar. Tana kwance reran sai wani gurnani take tana surutai da ihu. Gabansa yana tsananta bugu ya haɗiye wani yawu ya ce "A'uzubillahi minsh shaiɗanir rajim" Ya faɗa da ƙarfi saurin yana karaɗe ɗakin, kamar aljannu jira suke ya yi magana sai ta ɗifff kamar an ɗauke wuta, murmushi ya yi a ransa yana faɗin 'Ashe dai ku ɗin ma matsorata ne kamar ni, yanzu kuwa za ku faɗawa ƴan garinku don wallahi sai na mori faɗuwar gaban da kuka sakani sai na baku wuju-wuju, mu zuba mu gani' Ya faɗa a zuciyarsa yana ajiye maganin da ya taho da shi, carbinsa, da kuma hiraminsa ya naɗe hannun jallabiyarsa. A can tsakar gida kuwa jin ta yi shiru sai aka shiga ƙusƙus kowa yana murna, ana yabawa lamami daga ƙasar larabawa. Mahaifiyar ta ta ce "Kai jama'a aiki ga mai ƙare ka, ashe dai duk ihu suke bayan hari ka ji dai ya fara maganin su" . Mai Gari ya ce "Yo dama mai zai gagara ai da kike ji da gani ƴarki ta yi babar sa,a saboda yanzun nan za ki ji ya fitar da su, ke hatta nonuwanta dole su dawo mata da su" Wannan maganar da suka yi a kunnen Sheik da yake suna a ƙofar ɗakin ne. Sheik jin haka sai ya ƙara ƙaimi, ya leƙi da window yana cewa "A samu murɗuga-murɗugan bulali, guda biyar wannan dole sai sun ci ubansu" Ya faɗa da muryar hausar larabcin sa. Da sauri Mai Gari ya saka samari suka ciro a dalbejiyar ƙofar gidan, aka miƙawa Sheik, nan da nan sai ya hau karatun suratul fatiha ita kaɗai ya karanta har lokacin dai bata ƙara ko motsi ba ta yi ɗif kowa bata cewa komai sai dai yanzu ta buɗe idanunta sun yi faral kamar na gawa. Ganin hakan ya hau zagarta da bulala, yana faɗin "Za ku fita ko sai na koya muku hankali, sai na nuna muku kudu ba arewa ba ce matar malamin ƙasar yemen za ku ɗaukewa mashaya, baƙin ciki kuke min, kar in angwance" Ya faɗa yana tafka mata bulala. Sai da bulala uku ta karye duk ya burɗa mata jiki. Ya ɗaga ta uku zai zabga mata sai gani ya yi ta miƙe a fusace, yanayin yadda ta iyo kansa sai da hanjin ciknsa sa ya kaɗa, bulalar ta riƙe bai ankara ba ya ji ta warce, ja ɗaya ta yi wa bulala sai ga Sheik ya saka yana zare ido cike da tsoro, gabansa yana bugawa, ɗagawa ta yi ta tsula masa, tsabar yadda zafin ya shige tsalle ɗaya ya yi sai gashi a gefen gado, taku ɗaya ta yi sai gata a tsakiyar gadon, ta ɗaga bulalar tana rama dukan da ya mata, amma saboda gudun kar a gano lagwansa bai yi ihu ba, ko wani furuci da zai sa a gane halin sa yake ciki. Mai Gari ne cikin laga murya ya ce. "Aikin ka yana kyau Sheik kar ka bar su sai sun dawo mata da abubuwan nan masu muhimmanci a jikin mace(Breast)" Sheik dakyar ya mayar da kukan da yake ƙoƙarin ƙwace masa ya ce "Ai sai sun maido... Bai ƙarasa faɗa ba ta buge masa baki tana zare ido yana kallon ta ya san ba a hayyacin ta take ba. Shammatar ta ya yi ta ya fito daga lungun gadon sai ga shi a tsakiyar ɗakin, farɗo ta ya yi yana ɗaukan ɗaya bulalar ya zabga mata sai ta zube a kan gadon idanunsa ƙurrr a ƙirjin ta ya ga wayam babu breast kamar ƙirjin yara. Baki ya buɗe yana karanta qulhuwallahu ahad, yana zabga mata bulalar yana cewa "Ku maido da nonon da kuka ɗauke, ku maido da shi aka ce... Bai rufe bakinsa ba mai zai ji? Wani abu ya ji kamar an hura masa iska a ƙirjinsa, kafin ka ce kwabo sai ya ga tudu nan da nan sai ga breast ɗin duka biyu a ƙirjin Shaikul yemen. Idanu ya zaro cike da fargaba a zuciyarsa ya hau cewa 'Ƙirjin ta nake nufi fa aljannu, ƙirjinta nake nufi ku mayar ba ƙirjina ba na shiga uku ni Ibra jikan Inna' Ya faɗa yana kai hannu cike da tashin hankali ya shafo ƙirjin, breast ne ya ji tamkar ƙirjin mace.... *BOOK 1 free BOOK 2 500 shiga grp cmplt docment 800 za a biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay. Saura page 2 a gama book 1* *MAMAN AFRAH* 09025576222 💃 TALLAH TALLAH💃 *Kamfanimu na MEERAH B HERBS muna da kayan mata masu kyau da inganci, akwai maganin sanyi maganin gyaran breast, maganin hips, na rage ƙiba, na ƙara ƙiba, maganin rage tunbi, da kuma maganun MAN POWER ga matan da mazajen su ba sa uin kataɓus a wajen aikata sunna da sauransu.* *Mai so ya tuntuɓeni a layina 09025576222* [7/16, 6:52 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 14 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture *MUMMY* Shigewa ɗakin Daddy ta yi, kasancewar fitilar a kashe sai kawai ta durfafi kan gadon, cike da shauƙin soyayya ta ɗare gadon, sai dai wani abu da ya ratsa ƙwaƙwalwar ta shi ne, jin gadon kamar ma wayam yake babu kowa a ka, ma'ana kamar dai ita kaɗai ce da ta hau gadon yanzu a ka, mamaki da al'ajabi suka haɗe lokaci guda a kwanyarta tambayoyi da tunani barkatai suna safa da marwa a ƙwaƙwakwar tata. Da yake tun tana dab da zuwa ƙofar ɗakin ta kashe fitilar wayarta, saboda ta fi so sai ta hau gadon zai san da zuwanta, hannu ta kai ta gama zagaye kan gadon amma babu alamar mutum, fitilar wayar ta kunna sai yanzu idanunta suka ƙara tabbatar mata cewa ba ya kan gadon a zuciyarta ta ce 'To ko dai yana banɗaki?' Wata zuciyar ta ce 'Kuma banɗakin ne ba zai kunna fitilar ɗakin ba, sannan kuma ita ma ta banɗaki ba zai kunna ta ba?' Ƙafafunta ta zaro daga kan gadon, banɗakin ta nufa, bata kunna fitilar banɗakin ba sai ta yi amfani da fitilar wayar, amma sai ta ga babu shi babu alamar sa. Haka ta rufo ƙofar banɗakin ta dawo ta zauna, nazari take amma kwanyarta ta ƙi bata haɗin kan gano inda mai gidan nata yake, fitilar wayar ta kashe, tana jira ta ga ta inda zai fito. Daddy kuwa ransa fari tas ya fara haurowa sama, fitilar wayarsa a kashe saboda kar a samu akasin lissafi, saɗaf-saɗaf ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Hajiya, ganin fitilar a kashe a zuciyarsa ya ce 'Ka ga sarakan bacci ana can ana fama, ni ai da kike da nauyin baccin nan gaba ta kai ni gobarar titi' Ya faɗa a zuciyarsa yana kama hannun ƙofar ɗakin nasa ya buɗe ƙofar, Mummy da take zaune har sai da ta ji gabanta ya daɗi saboda bata tsammace shi ba, sannan bata kawo cewa zai shigo a duhu bai kunna fitila ko da ta wayarsa ba ce. Ɗif ta yi tamkar bata cikin ɗakin, Daddy kuwa yana shigowa ya yi wata miƙa yana salati, tare da sakin doguwar hammar biyan bashin baccin da bai yi ba a daren na jiya. Kan gadon ya nufa kasancewar ba ta wajen da Mummy take zaune ba ne, har ya hau gadon bai san tana zaune ba, sai da ya ja filo ya tada kansa yana sakin wata hammar a karo na biyu, hannu ta ɗan miƙa ta sauke a jikinsa, gabansa ne ya buga da mugun ƙarfi kasancewar bai ma taɓa kawo cewar Mummy ba ce, gabaɗaya sai ya razana, fitilar wayarta ta kunna a takw haske ya gauraye ɗakin, sai a lokacin idanunsa suka yi tozali da ita, duk da ya tsorata da kama shi ɗin da ta yi, kuma ya ga fuskarta ma babu yabo babu fallasa amma kuma sai ya maje ya ɗan saita kansa. Mummy ita dai haushin inda ya fita da tunanin amsar da zai bata take, amma kuma bata taɓa kawo cewar wai aure ya yi kai bata ma yi tunanin har zai iya fita daga gidan ba. Cike da tuhuma ta ce "Alhaji daga ina haka?" Ta tambaya tana kafe shi da idanu don gani ta harbo jirginsa musamman da ta ji wani ƙamshin turare da ba nashi ba, yanayin ƙamshin mai sanyin ya sa ta ji tamkar ma turaren na mata ne, sai dai ba za ta yanke hukunci ba, kai zuciyarta ma ba za ta bari ta zargi Alhajin ta ba, saboda ta bashi yarda, ba ma wannan ne abin yin ba, sai alƙawarin da ta sanya ya ɗauka na dole, a kan cewa ba zai mata kishiya ba. Cike da iya sarrafa harshe ya ce "Ni ke ce ma kika bani tsoro kawai sai ki zo cikin duhu ki zauna? " Sai ta ji gabaɗaya ma ranta ya ɓaci kasancewar tana tambayarsa yana tambayar ta. Rai ta haɗe ta ce "Kai ɗin ma ai a cikin duhun ka fita, da ka dawo ma a duhun ka dawo" Gabansa ne ya bada rass jin furucin ta, tunaninsa ko dai shuka ya yi a idon makwarwa wato Mummyn ya ga tafiyarsa ko kuma dai Rahma dama ta gan shi ƙyale shi ta yi ita ce ta faɗa mata, wani gumi ne ya karyo masa, ya san in her Rahma ta ganshi amma ta nuna bata ganshi ba sai da ya fita ta bi sawunsa to tabbas babu abin da za ta ɓoye wa Hajiya. Jarumta ya ara ya ce "Haba Hajiyata ai ni na fita a duhu ne saboda kar in kunna haske ki hango daga ɗakin ki, ki ce na bar miki idanuna basu runtsa ba wato ban yi bacci ba, kuma da na dawo ma wannan dalikin ne ya sa ban kunna hasken ba" Ya faɗa zuciyarsa cike da zulumin Allah tarkonsa ya kama tsuntsu. Wani daɗi ne ya baibaye Hajiya don yanzu kam na gane komai ma saboda soyayyarta ya yi, wani farrrr ta yi da idanunta ta ce "To yanzu dai ina ka je?" Hannu ya kai ya shafo gashin kanta da babu hula ya ce "Kawai fa ina kwance na falka nake jin motsi a ƙasa shi ne na sauka na duba, ashe ma dai kunena ne don ban ga komai ba" Murmushi ta yi tana cewa "Kai kam baka son abin da zai taɓa iyalinka" Murmushin jin daɗin samun nasara a kanta ya yi, don ya san tabbas matuƙar ta gano shi to akwai gagarumar matsala ko da kuwa ganin budurwarsa ne bare kuma a ce matar aure, auren ma kuma a ɓoye ba tare da sanin ta ba duk da cewa ya san ita ce ta ja koma mene ne, a ce mace ta ce ita ba za a mata kishiya ba, wannan son zuciya ne da dannewa namijin haƙƙinsa tun da Allah ya halatta masa. Washe gari tun da sanyin safiya Hajiya take famar a je a sallami Ma'aruf da kuɗin kota ya kama hanyar ƙauye, Daddy kuwa da ya gama shirin fita ya ɗauki Ma'aruf ɗin suka fita tare, bai zame da shi ko ina ba sai gidan Zee a nan ne yake gabatar da Zee a wajen Ma'aruf tun da ita dama ta san shi a bakin Daddy. Daddy ya ce ya zauna a ɗakin baƙi kafin ya gama sama masa admission a wata ƙasar inda yake ganin zai dace da cigaba da karatun sa. Ma'aruf ya yi mamakin jin cewa Daddy yana da wata matar bayan ya san babu wanda ya sani kuma ya san akwai matsala ko dai ya ce tashin hankali duk ranar da ƙwan ya fashe za a yi ɗan jijjiɓin yaƙi. Ya ji daɗin cewa Daddy za fitar da shi ƙasar waje karatu, wannan ya nuna cewa Daddy har yanzu yana riƙe da zumunci kuma, zugar Hajiya da Rahma bata yi tasiri ba kuma dama bashushe ya ce hassada ga mai rabo taki ce. Zee ta karɓe shi hannu biyu shi kuma yana girmama ta duk da cewa ya girme ta amma kuma, tun da dai matar Daddy ce babu wani batun girmansa tun da idan ana dara fitar da uwa ake. Daddy ya kammala masa komai na tafiya, inda zai tafi China nan da kwana uku, murna kamar zai yi mai, ashe da rabon ya shiga jirgi. Ana jibi zai tafi ya je Ƙundu ya musu sallama, duk da a tsaitsaye ya yi saboda bai gama shiri ba, har ya je ya dawo basu haɗu da Sheik ba. Ranar laraba misalin ƙarfe biyu jirgin su ya tashi, Zee da Daddy ne suka raka shi airport yana ta farinciki saboda shi yana son karatu. *(A page 15 buk 1 zai ƙare mai buƙatar book 2 zai biya ɗari biyar* Haka rayuwa ta cigana da tafiya, Rahma tana fantamawar ta, sai samari take yi kala-kala ƴaƴan masu faɗa a ji, don ita ta ƙi jinin masu ƙaramin ƙarfi ƴaƴan malam shehu. A ɓangaren Daddy kuwa har yanzu yana ta cin karensa babu babbakaa, domin babu ranar da za ta zo ta faɗa bai kwana a gidan amarya ba, ita kuma Mummy da yake hotiho ce bata taɓa lura ba, saboda idan ta je ta hangame baki sai bacci bata taɓa sanin abin yake wakana ba. Sannan basu da masaniya a kan tafiyar Ma'aruf karatu su duk tunanin su yana can ƙauye, don Mummy takan ce Ma'aruf ana can ƙauye an kama sana'ar sayar da rake. Ranar wata juma'a ne Mummy tana kwance bayan ta dawo daga fitsari, bacci bai ɗauke ta ba, sai ta ji kamar alamar hayowa saman benen, shiru ta yi tana son gano cewa ko dai kunnen ta ne amma sai sai bata kawo komai ba tana dai kasa kunne tana jiran ta bambance, kamar daga sama haka ta ji, ƙaran buɗewar ƙofar ɗakin Daddy mamaki ne ya yi masauki a kwanyarta, zaune ta tashi, amma yau kawai sai ta ji tana son sanin mai ya saukar da shi ƙasa, don zuciyarta ma ta fara wasi-wasi wato shaiɗan ya fara mata biyar ko dai ɓangaren masu aiki yake zuwa, ba komai ya sa wanann zargin ya ɗarsu a zuciyarta ba sai furucin wata ƙawarta da ta ce mata ba a gane gaban namiji bare bayansa, haka ta faɗa mata bayan ta bata labarin cewa ba zai msta kishiya ba kuma shi mata ma basu ishe sa kallo ba. Da sanɗa ta sakko duk da tana masa zato mai kyau amma kuma dai tana son idan ta yi abin da za ta yi ɗin ta tarar da shi a kan gaskiya. Abin da ma ya sa ta fara wannan tunanin sai tunawa da ta yi da wannan ranar ma da kamar wannan lokacin ne ya dawo inda ya ce mata ƙasa ya sauka ya ji motsi, a nata ganin ai ba kunnen maciji ne da shi ba da za a ce wani ƙaramin motsi ya je kunnensa. Jinginuwa ta yi a window tana ɗan ɗaga labule a zuciyarta tana cewa. 'Idan ka ji ana cewa raka no in yi kashi to tabbas kashin ba gudawa ba ne' A daidai lokacin da ta ɗaga labule Daddy yana dab da shiga ɗakinsa, abin da ya ɗaure mata kai kuma shi ne yadda yake wani sanɗa yana waige-waige, alamomin rashin gaskiya dai sun bayyana ƙarara a yanayinsa. Gabanta ne yake faɗuwa, amma haka ta daure tana kallonsa har ya shige ɗakin, kuma a duhu bai kunna fitilar waya ba ko kuma fitilar ɗakin. To in har ba babu gaskiya a tare da shi ba mai ya sa zai yi hakan. Sai da ta bari ya ɗan jima da shiga sai ta buɗe tata ƙofar ta fito, Daddy da ya shagala da yin waya da Zee bai ma san Hajiya ta buɗe ƙofa ba don ba ya cikin nutsuwar da zai ji ƙaran ƙofar. Sai da ta zo za ta buɗe ƙofar ta ji dirin maganarsa sai dai bata ji mai yake cewa ba, mamaki take da wa za su yi waya a doshin asubar nan. Ƙofar ta murɗa, Daddy da yake waya ya danne wayar da sauri ta ɗauke, idanu ya rufe kamar mai baccin ƙarya. Fitilar ta kunna abin mamaki har da munshari yake saki, wanann ne dalilin da ya sa ya fara jefa masa ayar tambaya a ranta, tana tunanin wane irin sake ne wannan ta yi a cikin gidanta, sai yanzu ne ma take mamakin yadda Alhajin ba ya ƙulafucin ta zo ɗakin nasa wanda a da can baya ba sa ɗaukan wannan tsawon lokacin ba tare da sun kusanci juna ba, amma sai yanzu ta lura da ita da babu ma duk ɗaya, bata san cewa sabuwar fulawa ya samu yake ban ruwa ba. Yadda ya mata bariki ita ma barikin ta masa, gaban gadon ta ƙarasa ta ɗan buga ƙafarsa tana kiran sunansa, idanu ya buɗe dakyar yana wani ƙanƙance su irin na mai bacci, sai ta ji wani haushin sa ma tun da ta ga zai munafurce ta. Ɗan washe fuska ta yi tana masa murmushi take cewa ya tashi lokacin sallah ya yi, ko kunya haka ya tashi yana wani murtsuka idanu, duk da ta san ba a ma fara kiran sallar ba, amma dai dama ta zo ne don ta tababtar da baccin makaho, da a ce yana da gaskiya Daddy da ba zai yi baccin ƙarya ba, sai dai ta ci alwashin sai ta gano abin da yake sauka yi a ƙasa. Ɗakin ta ta juya ta koma shi kuma ya shiga banɗaki, yana suuke ajiyar zuciyar kuɓuta don shi a nashi tunanin ko ta ji yana waya ne, don bai taɓa kawo cewa ta ga shigowarsa ba, bare har ya yi tunanin ta ji yana waya ya san ma ba zai yiwu ta yi shiru ba. Bata sauya masa ba ko a fuska bata nuna masa ba, sai dai a ɗauki alƙawarin sai ta ƙurewa motarsa gudu. Sai da dare ya yi ta hau ƙawar ya kwana a ɗakinta amma firrr ya ƙi yana cewa shi katifar ɗakin ce ba ya so, da ta nuna cewa ko ɗakinsa za su je, sai ta ga ya ɗan basa da zancen, ita kuwa bata wani nuna masa ta damu ba ko kuma ta damu, sai kawai ta kwanta a nata ɗakin ya mata sallama ya fita ya rufo ƙofar. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, tana jiran ta ga abin da zai faru. Har ta fara ganin lafin kanta da kanta cewa ta zargi mijinta kamar daga sama ta ji an buɗe ƙofar ɗakinsa, bizigir ta miƙw zaune daga kwanciyar da take ba tare da ta shiryawa hakan ba. A hankali ta lallaɓo ta zo window sai gashi ya fita, tana nan tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falon ƙasa, shi ma don idanun ta biyu shi ya sa ta ji kuma saboda ta kasa kunne. Gabanta ne ya tsananta bugu tana jin faɗuwar gaba don zuwa yanzu ta tabbatar da cewa wajen ƴan aiki yake zuwa, tun da dai babu abin da zai fitar da shi da dare, windown da ake hango harabar gidan ta zo ta leƙo sai kawai ta hangi Daddy ta cikin hasken farin wata yana ta sauri, kallonsa take hawaye cike a fuskarta don a halin da take yanzu gani take ko rantsuwa za ta yi cewa biyan buƙatarsa ce ta wajen ƴan aiki ta fita da shi. Sai dai akalar tunaninta ya sauya ne a lokacin da ta ga ya nufi ƙofar fita daga gidan ta baya, a sannan ne ƙirjint a ya shiga bugu da mugun ƙarfi,, ji ta yi hankalinta ya tashi, da sauri ta bar jikin labulen bayan ta ga fitarsa, a kiɗime ta juyo ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ko ina, ƙaramar lokar jikin madubi ta janyo inda take ajiye mukullai, dakyar ta samu mukullin ƙofar fita daga bayan gidan, jikinta yana ta ƙyarma, saboda jikinta ya bata akwai wani gagarumin abin da yake faruwa. Ko ƙofar ɗakin bata rufe ba, haka ta fito fitilar wayarta a kunne, da matakala bibiyu take sauka daga saman benen, ƙofar falon ma a buɗe ta bari ko takalmi babu a ƙafarta, ita fatan ta ɗaya shi ne Allah sa dai ba wai fira yake da wata macen ba, shi ne ba ya zuwa sai dare ya tsala saboda gudun ɓacin ranta, amma wace mace ce za a ce tana fitowa daga gidansu a wannan daren, sai dai in mutuniyar banza ce, haka take ta saƙawa har ta zo wajen ƙofar, ganin ƙofar a kulle , zargin ta ya zama gaskiya, mukullin ta saka ta buɗe ƙofar sai dai bata da nutsuwar rufe ƙofar, amma sai ta laɓe ta leƙo, daga can ta hange shi tsaye da alama wani yake jira, tana hango shi tana jin tsanarsa a ranta, wato su iyalansa suna nan suna bacci shi kuma lokacin ne safiyarsa ta waye. Wani machine ne ya tsayar ya hau, suna fara tafiya sai ga wata mata a mota, nan Hajiya ta tsayar da ita ko tsoro ma bata ji, matar kasancewar ta likita kuma sama da gidan su Mummy take, ta fito ne za ta je karɓar haihuwar wata mata, haka ta ɗauki Mummy ganin kamar ba a hayyacinta take ba machine ɗin ta nuna mata a kan cewa ta bi bayansu, ganin sai kuka take tana mata bayanin abin da ya sa ta biyo bayan mijin nata. Ta tausayawa Mummyn, sun ɗan tsaya daga ɗan nesa ganin machine ɗin ya tsaya a ƙofar wani gida, Mummy ta mata godiya bayan an buɗewa

Chapter 12 of 14