Share this page
Daddy ya shige ta fita daga motar ta ƙarasa a ƙafa. Ganin katangar bata da wani tsayi a ranta ta ce 'In ka ji kana ba za ka iya ba to bai same ka ba ne, ai ni yau sai na ga ƙwal uwar daka' Ta faɗa a zuciyarta tana komawa daga can bayan gidan ta kama katanga ta ɗare, haka ta ti dabara ta dira amma fargabar abin da za da tarar sai ya sanya bata ji buguwar da mazaunanta suka yi ba. Tashi ta yi ta yi saurin laɓewa ganin ana hasko fitila, sai da ta dakata mai gadin ne ya zo ya yi ɗan haske haske ya juya bai ganta ba, da alama bai fuskanci cewa gidan aka diro ba. Ƙofar falon ta lallaɓa ta tura a hankali jin ba a saka mukulli ba zuciyarta tana ta ayyana mata cewa "Namiji ba ɗan goyo ba ne, tun da ta yarda da mijinta ashe dai saka reshe kama ganye ta yi, sai dai ta ɗaukarwa kanta alƙawarin za a yi kan mai uwa da wabi, domin ta lura tsugunne bata ƙare ba amma sai ta nuna musu tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, tun shi Alhaji ganin hadarin nesa zai sa shi yin wanka da kashi, don ta lura wadatar biki ne tsarki da romo, tun da har ya iya zuwa wajen wata mace za ta nunawa matar cewa abincin wani gubar wani ne, don abin nasu aikin banza ne shafa lalle a ɗuwawu' Ɗan hasken da ka bari a falon wanda yake kawowa yana ɗaukewa hasken mai kalar blue, ganin falon shiru hakan ya bata tabbacin suna sama, saman ta hau tana jin cewa yau duk sai sun baƙunci lahira, a ɗaki na farko ta fara jin magana ƙasa -ƙasa muryar Zee ta ji tana cewa "Haba kai kuwa gaskiya yau ka makara baka fito da wuri ba, ka san dai ai bana iya bacci sai da kai, sai ka je ka tare a gidanka ni ka barni da kewa" Mummy ji ta yi kamar ta fasa ihu, Daddy ta ji ya ce "Haba ƴar lele ai komai nake hankalina yana kanki, kin sha gaban duk matan duniya ke kaɗai idanuna yake iya gani da kuma hange, haba amarya mai capacity, amarya kin fi quality, mu kwanta... Banko ƙofar da Mummy ta yi shi ya ankarar da su juyo, zumɓur Zee ta miƙe daga cinyar Daddy, a take idanun Mummy suka sauka a kan cikin wata huɗu na Zee wanda ya yi kufkuf a jikinta kamar ƙaramar ƙwarya... *BOOK 1 free shiga grp na BOOK 2 500, cmplt doc 800* *Acc no faiza abubakar 9030283375 opya shaidar biya 09025576222 gobe za mu gama book 1* *Yau ba samu leƙo inna amarya ba da kuma ango Sheik mai breast* 😂😂😂😂😂😂 *Sai gobe in muna raye* MAMAN AFRAH 09025576222 [7/17, 7:31 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 15 *END OF BOOK 1 LAST FREE PAGE* *BOOK 2 500 naira pay in to faiza abubakar 9030283375 opay* IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_ventureƊ *INNA TASALLAH* Cike da tsoro take kallon sabuwar addar hannun Jummai gabanta yana faɗuwa, ta ɗauka Sule jarumin maza ne zai yi iya yainsa don ganin ya dakatar da Jummai daga wannan barazana ta mummunan aikin da take so ta yi amma sai ta ga har lokacin yana dafe da mararsa yana ciccira idanu tamkar kwarton da aka kama a ɗakin amarya. Jummai kuwa babu alamar wasa ko kuma yin barazana a kalamanta ko yanayinta kana ganinta ka san iya gaskiyarta take faɗa iya abin da yake cikin ranta ne kuwa alwashin da take ci babu gudu babu ja da baya. Inna a zuciyarta ta ce 'Tabbas ƴan magana sun ce kifin fadama ba ya gasa da kifin kogi, amma wannan mata tana son kawo min cikas a ɗan amarcin da na ɗora rai zan dangwala, tana son shuka min salalan tsiya' ,A fili kuma sai ta ce "Haba Sule ka yi wani abu mana, kana dai jin abin da take faɗa tana neman kawo tsaiko a lamarin kasancewarmu tare, kuma sanin kanka ne Mai Gari ya kashe wannan maganar, kuma maganar ta mutu murus" ,Wani yawu Sule ya haɗiye ya lura Inna bata san abubuwan da sukw faruwa a duniya ba, shi da yake ma'abocin sauraren rediyo ne babu abin da bai sani ba saboda yana jin labaran yadda wasu matan suke yankewa maza mafitsara musamman a kan lamarin kishi, bare Jummai da haka nan ma tarar aradu da ka ne da ita bata barin ta kwana. Yana ɗan sakin murmushin yaƙe ya ce "Haba Tasleey ai kin san Jummai a kan gaskiyarta take, haƙiƙa saniya ba tawa ba ce ke ma kuma kin sani" Wani takaici ne ya rufe Jummai jin wai Sule yana kiran Inna da Tasleey wato ta lura maza basu da gaba basu da baya wato sawun keke ne su, amma in ba haka ba ita yake kiranta Jummai amma Inna daga tarewa har ya sauya mata Tasallah zuwa Tasleey. Inna kuma wani haushin Sule ne ya kamata tana ji kamar ta hau shi da duka, yana ji za a mata sagegeduwar amarcin amma babu wani kataɓus da ya yi, ita ba ma wannan ne tunanin ta ba yadda maƙociyar yarinyar nan ta bata ƙwaƙwalwar raƙumi ta yi amfani da shi gashi yanzu ana neman sakawa ta shiga uku. Inna ta ce "Ban gane a kan gaskiyarta ba?" Ido ya shiga ƙiftawa Inna yana mata alama da addar hannun Jummai, ita ma Inna hannunta riƙe da mazaunai ta ce "To shikenan saboda ta ɗauki adda sai a ƙi faɗar gaskiya, kana ji fa ta ce wai ni za ka bata in koma ɗakinta, ka taɓa jin wannan ɗanyen aiki ni fa tun da an ɗaura mana aure ni ɗin fa na zama mallakinka ita kuma tana a matsayin kishiyata ne, yanzu kawai sai in koma ɗakin kishiya?" Jummai ce jin har suna shawara, kenan suna ja da maganarta hakan ya sanya ta fara taku ta zo gaban gadon ta zauna ta miƙe ƙafa ranta a ɓace ita kuma adda sai walwali take, wannan ƙallin da addar take shi yake ruɗawa Sule ciki. Sule ganin haka ya ce "Tasleey maganin kar a yi kar a soma... A hargitse Jummai ta katse shi da faɗin "Wane suna ne wannan ɗin?" Da sauri ya gyara da faɗin "Tasallah a bar maganar nan Jummai iya gaskiyarta take faɗi" Inna saroro ta yi tana kallonsa ganin da gaske dai Jummai yake tsoro, duk da ita ma tana tsoron amma tana so ne ta yi yaƙi ta karɓi ƴancin ta. Inna ta ce "Jummai kin san dai na yi jika da ke, ni ba na son tashin tashina, tun da Allah ya yi na auri mijinki ki ɗau dangana, duk ranar da Ibra ya dawo da kuɗinki zan sa Sule ya warware igiyar" Kai Jummai ya ɗaga tana wani yatsina ta ce "Sule ya muke ciki ne? Ka ga yadda na kulle ɗaki daga ni sai ku, sannan ga sabuwar adda" Sule cike da zuga da kambamawa ya ce "Jummai ikon Allah, Jummai masallacin kura kike ba a ba kare limanci, ƙarfe duka ƙarfe ne amma a cikin ƙarfe akwai zinare da azurfa" Ya faɗa cike da kirari don ganin ya faranta mata ta janye batun ta, don shi yana tsoron mutuwa saboda bai shirya tafiya ba, kar a je ta guntule shi tsakiyar dare ya shiga uku. Inna jin ta yi sake reshe kama ganye, wato dai amarcin nan ba ciyuwa zai yi ba, sai kawai ta fashe da kukan takaici" Sule bai lallashe ta ba ko bata baki gudun kar ya yi laifi. Jummai ta sheƙe da dariya ta ce "Wato an ga samu an ga rashi, to ai sai ki tashi ki koma ɗakin mijinki, wato ni kenan ɗakin mijin ki Jummai" Cewar Jummai tana ƙara bushewa da dariya Kai Sule ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, alamar eh, Inna ta kalli Jummai ta kalli sule wanda zuwa yanzu ya fara motsu-motsu da harhaɗa ƙafafu wanda ba komai ba ne ya haifar da hakan sai maganin da ya sha ne yake tambayarsa. Cike da sanyin murya ya ce "Tasleey au... Ya dakatar da maganar tunowa da ya yi Jummai ta yi magana ɗazu. Yana sauya akalar maganar ya ce "Tasallah ki tashi ku je ku kwanta" Wani haushinsa ne ya kama Inna tana ganin saboda tsabar shi saunan namiji ne kana da amarya amma ka ba mace saboda namijin hotiho ne shi. Jummai ta miƙe tsaye tana wata hamma, ta je saitin ƙofar ɗakin ta tsaya, ganin Inna bata taso ba, sai ta saka addae a jikin bango ta karta alamar wasawa ta yi, tsabar ruɗewa a kuɗime Sule ya miƙe bai san ya aka yi ba sai ganinsa ya yi a gaban Jummai, sai da ya ganshi a gabanta ya tuna cewa ashe ba shi ne za a tafi da shi ba. Inna kuma karta addar a bango sai ya sa ta miƙe tsaye har zani yana neman kwancewa ta gyara, Jummai ce ta ce "Sule ko har kai za a tafi ne?" Yana wayincewa ya ce "A haba da girman kujerarki ai da Tasallah ne za ku tafi" Ya faɗa ransa yana ƙuna gabansa kuma yana faɗuwa a lokaci guda, don shi duk abin da za a ce an haɗa da rai to tabbas ba ya son maganar mutuwa. Inna tana yin yaƙe ta ce "Eh da ni ce" Dariyar cin nasara Jummai ta saki a ranta tana saka hannu ta buɗe sakatar ta saka Inna a gaba suka nufi ɗakinta suna fita Sule ya yi zaman ƴan bori yana ambatob Lahaula wala quwwata. Kai ya dafe da hannu biyu a fili yana faɗin "Kin cuce ni Jummai, sai da na gama ɗora rai zan kwashi garaɓasa kika mini shigar sauri, yanzu a ce sai da na gama bankar magani abokaina suka gama zuzuta maini amarcin zan kwashi ganima amma ki zo ki min haka" Ya faɗa idanunsa suna masa jawur. Inna kuwa ɗakin Jumman suka shiga, warin fitsarin yaran ne ya ankarar da Inna cewa an shigo ɗakin ƙazama Jummai, don yaran sun isa su daina fitsarin kwance ma. Cike da umarni ta nunawa Inna gado, haka Inna ta hau gadon tana jin tsinkon da marar ta take mata. Amma babu yadda ta iya haka ta hau ta kwanta, tana tuno tsiren amarcin ta da kuma ruwan ledar da aka kawo mata na amarci. Jummai wuri ta samu ta ajiye addar ta hau gefen Inna ta kwanta, sai yanzu Jummai ta ji sauƙin zafin ranta da yake mata raɗaɗi tun lokacin da aka ɗaurawa Inna auren, ga kishi ga rashin saniya, yanzu kuma tun da Inna ta dawo ƙarƙashin ta sai take ji daidai yake da saniyarta ce a kusa. Sule a nan tsakar ɗakin ya yada zango, don ko gadon ƙarfen Inna bai samu hawa ba, haka nan tsire ma bai samu shiga ba saboda yanzu amaryarsa kawai yake buƙata amma babu hali, don da alama Jummai da gaske take ba za ta bar Inna a ɗakinsa ta kwana ba, tun daɗewa yake jiran dawowar Inna ya ɗauka Jumman za ta barta ta zo amma dai har har yanzu shiru, kamar maye ya ci shirwa ba amo ba labari, tun da dai babu niyya ango ya kwana da wando. Har dare ya tsala yana nan tsakar ɗakin yana murƙususu, ganin dai abin ba zai masa ba, tashi ya yi ya lalaɓo ya fito yana sanɗa ya nufi ɗakin Jummai, tun kafin ya ƙaraso yake jin tashin munsharin Jummai, da na yaran da suke kwance a tsakar ɗakin. Da yake akwai fitilar ƙwai irin ta mutanen da, an barta a kunne amma kuma an rage hasken. Inna wacce ita ma baccin ta kasa tana ta juye-juye, a kan idanunta Sule ya shigo ɗakin, ai kuwa ta ɗan ɗago kai yake mata zancen kurma da hannu yana tambayarta ina adda, da hannu ta nuna masa inda ta ga Jummai ta ajiye, lallaɓawa ya yi ya ɗakko ya tura ƙasan gadon, gaban gadon ya ƙarasa ya juya bayansa Inna da sauri ta tashi ta ɗare bayan Sule ya goya ta, cike da zumuɗi suka baro ɗakin Jummai ransu fari ƙal. Ashe tun shigowar Sule Jummai ta falka tana kallonsa munsharin ƙarya take, kawai ta bari ta ga gudun ruwansa, suna fita ta sakko daga gadon ta ɗauki addarta, ta fito ta bi bayansu Sule yana shiga ɗakin ya garƙama sakata, sai kuwa ga Jummai ta sake dawowa, amma kasancewar a rufe sai ta kasa shiga, ta window take musu magana tare da cin alwashin muddin Sule ya kusanci Inna sai ta ɓalla ƙofar ta zo ta musu aika -aika. Tsabar tsoro sai Sule ya kasa komai, tun da tana tsaye ma Jumman tana kallon su, haka ya zauna a ƙasa yana kifa wani uban tagumi, don shi ya ga mace a ɓagas yana ganin ya tsinci dami a kale, babu sadaki babu kuɗin aure ko biyar bai kashe ba. Inna tana zaune ta miƙe ƙafa tana jin kamar ta shaƙe jummai, a haka suka kwana babu wanda ya runtsa a cikin su. Da asuba haka Inna ta yi alwala sai da ta ɓata buta guda a wajen tsarki saboda ni'imar da ƙwaƙwalwar raƙumin nan ta sanya mata a zuciyarta ta ce 'Wannan yarinya Jummai an yi ƴar kan uwa, da bata kasa ta tsare ba jiya Allah kaɗai ya san ganimar da za mu kwasa, amma don asara kalli yadda nake wanke ni'imar a banza tana bin makwararar banɗaki' Haka ta yi sallah ranta duk ba daɗi shi dama tun da ya tafi masallacin ma bata ganshi ba, ita kuma Jummai sai da ya fita sannan ta bar ƙofar ɗakin, amma Inna a ranta ta ci alwashin yau sai ta kai ƙara wajen alwalin ta wato Mai Gari. Haka kowa ya kama sabgar gabansa, Duduwa kishiyar Jummai ce ta yi ɗumame ta kaiwa Inna,, haka yaran Jummai suka tare a ɗakin Inna suna ta murna Inna mai kayan miya ta zama amaryar babansu, haka ta ɗauki tsiran nan ta raba musu. Jummai kuwa wata kaza ta kama aka yanka ta gyara ta dafa, ta juye a kwano ta bayar aka kaiwa Mai Gari ba tare sa kowa ya san wanda aka kaiwa ba. Dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya ta san dole ta amsa kiran Mai Gari yau, shi ya sa ta yi riga malam masallaci, ta dafa kaza ta aika masa saboda toshiyar baki da kuma cikar burinta. Wajen ƙarfe goma aka aiko kiran Jummai daga fadar Mai Gari, haka ta tarar da Inna da Sule a can, bayan ta zauna Mai Gari ya kalli Inna ya ce "Tasallah wai lafiya kike ta tagumi kina cika kina batsewa?" A ƙufule ta ce "Haba Mai Gari ya kake so in yi to? Ko baka ji a akan abin da muke ƙaran Jummai ba" Mai Gari ya ce "Na sani mana" Inna ta ɗora da faɗin "To wannan ne dai ai ka ji kan maganar, amarcu dai daren jiya bai ciyu ba" Ta faɗa tana gallawa Jummai harara. Amma buɗar bakin Mai Gari sai ya ce "To ai Jummai ta fiku gaskiya" Sule da Inna suka kalli juna suka kalli Mai Gari, Jummai ta saki wani murmushi, don ta san tabbas Mai Gari ya ji daɗin dahuwar kalwar da ta yi masa wacce ta sha farin maggi. Nan ya shiga faɗin dole a bi abin da Jummai ta ce har zuwa dawowar Ibra wannan shi ne adalci. Kowa ya ji ba a kyauta amma amma mai gari in ya tuna dabgen kazar da ya ci da sanyin safiyar nan sai ya ji ba zai iya musawa Jummai ba An yanke hukunci a kan Inna ta zauna a ɗakin Jummai takaici kamar ya kashe Sule, Inna kuwa ba a magana, haka aka tashi daga fada kowa yana jimami ban da Jummai da ta san amasar tambayar. Tsawon kwana biyar Inna tana kwana a ɗakin Jummai, saboda yanzu an kasa kwana ma tsakanin Duduwa da Jummai amma ban da Inna Tasallah. Yau da ya kama alhamis tun da yamma Jummai take gyare gyare sannan kuma Inna tana lura da magungunan mata da take sha, sai dai kuma ta san yau bakin Duduwa ne ba na Jummai ba. Abin da ya ba Inna mamaki yau yaran ba a ɗakin za su kwana ba, tun da wurin ta musu shimfiɗa a wani ɗaki da ake ajiye tarkace ta gyara musu tas. Tsakanin Inna da Sule sai gani daga nesa Jummai ta kasa ta tsare duk da Inna ta ci wani alwashi da zai rusa duk wani shirin Jummai, saboda tana ta ayyana yadda za ta zamewa Jummai ƙadangaren bakin tulu. Haka ta ga an gyara ɗakin, gadon ta hau ta kwanta, ita ma Jummai ta hau. Tsakiyar dare Inna tana bacci sai ta ji an dafa mata kafaɗa ranta fari ƙal ta buɗe idanu tunanin ta ko Sule ne, amma abin mamaki sai ta ji Jummai ce, Jummai ta ce "Inna tashi matata" Idanu Inna ta zaro tana tunanin ko ta yi makuwa ne amma saj ta ji da gaske take, cike da mamaki ta ce "Mai kike cewa Jummai?" Jummai ta ce "Tashi za ki yi ki biya ni sadakina" Inna ta ce "Na ce miki sai Ibra ya za a biya ki" " Jummai ta ce "Ai kin san a birni an ce akwai abin da ake yi mace tana auran mace to nima yanzu kin zama matata, don haka dole ki bani haƙƙina" Ta faɗa tana farwar zanin Inna, sai ga zanin Inna an warɓar gefe sai ɗan tofin ta(Skirt ɗin ciki) A take Inna ta tuna da ana cewa ana lalata mace da mace in bata manta ba an ce hakan yana faruwa a gaske to yaushe Jummai ta zama a haka ba a sami ba, a take Inna ta hau ihu tana cewa ",Ihu kwartuwa, Sule taho ka ga marar imanin nan za ta mini fyaɗe... *MUMMY* Babu wanda zai gane ko ya iya fasalta yadda tanji wani abu ya caki ƙahon zuciyarta, jikinta ne ya hau karkarwa a lokacin da ta yi wa idanunta masauki a kan fuskar yarinya, ko daga bacci ta tashi tabbas ba za ta kasa shaida Zainab Zee ba ƙawar ƴarta. Hannu ta saka ta dafe bango ɗaya hannun tana nuna su da yatsa. Duk rikicewar Hajiya Daddy ya fi ta rikicewa saboda shi ji ya yi wani irin tsoro da fargaba a masa dirar mikiya, bai taɓa zato ko mafarkin wannan rana ba, kenan duk wannan sirrin da yake binnewa ya aka yi Hajiya ta sani. Mummy kanta ne ya shiga juyawa, a take ta yanke jiki yaraf ta zube a ƙasa, Alhaji ne ya yi kanta yana kiran sunanta, ita kuma Zee ganin yadda duk ya birkice sai take ganin kamar ya fi son matarsa a kanta ita a nata ganin tun da ba zaman dadiro ne suke yi ba, ai ba komai ba ne don Mummyn ta sani, ita a ranta ma daɗi ta ji doin za ta saki jiki ta yi rayuwarta son ranta, duk da ta san dai yanzu tun da Hajiya ta sani da wuya ta ci gaba da samun Daddy a ɓagas kamar a baya da kullum ma yake mallakin ta, babu ranar bakin ta babu na Hajiya. Haka ya kira mai gadi ya fito da mota shi kuma ya kinkimo Hajiya ya saka a motar Zee kuma ganin yana rawar ƙafa kawai sai ta ce ita banu inda za ta je. Asibiti ya kai Hajiyar inda aka shiga bata taimakon gaggawa. Bata farfaɗo ba sai wajen asuba, ta falko da kiran sunan Rahma, Daddy yana riƙe da hannun ta ko da ta kalle shi sai abin da ya wakana jiya ya dawo mata a take ta warce hannunta tana fashewa da kuka. Misalin ƙarfe bakwai aka sallame su, amma Hajiya ta ƙi shiga motar ta hau napep duk da cewa Daddyn yana tabbayar mata cewa ba fasiƙanci yake yi ba matarsa ce ta sunna. A ganinta ya ci amanar ta tun da ya yi aure matar har da ciki. Daddy yana bin bayan napep ɗin da take ciki har suka je gida, ko parking bai gama ba ya kashe motar ya fito shi ya sallami mai napep ɗin ma ta hanyar masa transper tun da bai fita da kuɗi ba. Yana shiga falon ya haura sama kasancewar bai ganta a ƙasa ba, zaune ya tarar da ita a ɗakinta a bakin gado tana ta faman rasgar kuka Rahma tana bata haƙuri, duk da Mummy ta mata bayani amma ta ji haushin Daddy da kuma Zee da ta auri ubanta. Daddy yana shigowa Rahma wani takaici ya cika mata zuciyarta, a take ta yi ƙunci, fita ta yi daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado ta fashe da kuka, tunanin ta ɗaya yadda mahaifinta ya auri ƙawarta yanzu abin da ya tsaye mata a rai wai har Zee tana ɗauke da cikin mahaifin nata kenan Zee ta ga Daddyn ta babu kaya a jikin sa har wani abu yana shiga tsakani. Mummy kuwa ko sauraren sa bata yi ba ta ce ya fita mata a ɗaki, haka ya fita yana tunanin gwara ya bari idan ta huce ya yi aikin lallashin. Rahma ta kasa jurewa, wajen sha biyun rana da ya fita ta je ta cewa Mummy za ta tafi Ƙundu ta je ta faɗawa Mai Gari halin da ake ciki, don ita abin ya mata ciwo tamkar dai wanda aka ce Daddy babu aure ya yi wa Zee ɗin cikin. Tana fita Mummy ma ta rufe ƙofar ta kwanta ranta yana ƙuna tana tunanin mafita da kuma yanda za ta yanke shawara. Rahma mota ta ɗauka ta saka jakarta a ciki, direba ta sa ya tuƙa ta suka doshi garin na Ƙundi wanda rabon ta da ƙauyen har ta manta kuma ta san dai Mai Gari yayan Daddy ne kaɗai yake iya sanya Daddy ya yi ko ya hana shi. *SHEIK* Cike da tashin hankali Sheik ya yi cilli da bulalar hannun sa, yana kai hannu biyu ya taɓa ƙirjin yana faɗin "Innalillahi, na shiga uku ya zan yi?" Ya faɗa a hankali yana kallon amaryar tasa da ta zube a ƙasa kamar wacce ta suma. Mai Gari da ya ji Sheik yana cewa su maido da nonon da suka ɗauka, kuma dai sai ya ji Sheik ɗin ya yi shiru wannan dalilin ne ya sa murna ta cika Mai Gari don a tunaninsa Sheik ya sa aljannu sun maido da nonon amaryar, baki ya buɗe yana cewa mahaifiyar yarinyar "Kin ga abin da nake faɗa miki ko? Ai balaraben malami mashayar ɗa ba ko mutum sukutum aka ɗauka sai Sheik ya dawo da shi bare wani nono ai abu mai sauƙi ne fitar da wando ta ka" Ya faɗa yana dariya mai sauti, duk matan tsakar gidan a kunnen su aka yi wannan magana, a take aka fara ƙusƙus kowacce tana cin alwashin ta samu wajen zuwa neman maganin damuwarta. Mahaifiyar amarya ta washe baki tana jin daɗin sa'ar sirikin da zai zama silar warakar ƴar tata. Duk maganar nan da ake a kunnen Sheik da ya jiƙe jagaf sa gumi ƙirji da tudun breast. Maganar Mai Gari ce ta katse shi da faɗin "Ya Sheik sun maido ko?" Sheik yana kallon ƙirjin sa ya buɗe baki dakyar ya ce "Ina ta fafatawa dai da su suna gab da maidowa" Ya faɗa yana hawaye da jin da na sanin wannan maluntar BOGIN Ya cigaba da karanta qulhuwallahu wacce ita kaɗai yake iya tunawa zuwa yanzu, yana tofawa amaryar don yanzu bashi da ƙarfin dukanta ma. Yana yi sai ya ga ƙirinta ya fara tasowa kamar almara sai ga tudun ƙirjinta ya dawo, a rikice ya kalli nasa ƙirjin ganin bai ɓace ba kuma dai natan ya dawo das dashi. Da sauri ya tsugunna yana yin ƙasa da murya ya ce "Haba aljannu kar mu yi haka da ku, ni na yafe nonuwan nan domin Allah ku raba ni da shi" Amma atishawar amaryar tasa ce ta tabbatar masa da cewa aljannun sun sake ta. Ƙuri ta masa da idon ta ɗaya tana washe baki, fuska ya tamke yana ganin duk ita ce silar shigarsa matsalar da yake ciki. A wayince ya shiga kare ƙirjinsa gudun kar ta gani, ya janyo hiraminsa ya yafa a kafaɗa yana dibara wajen kare ƙirjinsa. Magana take masa yana amsawa a daƙile, ya buɗe ƙofar ya fito ta biyu bayansa tana tafiya dakyar alamar ƙarfin jikinta bai dawo ba, mahaifiyarta ta rungume ta cike da murna, kowa na wajen ya zo ana kallon yadda Sheik ya sa aljannun suma maido mata da nonon ta, sai dai babu wanda ya lura da ƙirjin Sheik bare a ha ajiyar da aljannun suka masa. Mahaifiyarta tana ta masa godiya, tana cewa yanzu ai za a kawo masa ita gidan, amma buɗar bakinsa sai ya ce aljannun sun ce ba yau za ta tare ba idan ta tare yau za su haifar da gagarumar matsala a garin. Jin haka sai Mai Gari ya ce a dakata da tarewar yau, shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda rufuwar asirin sa, don ya san matsawar aka kai amarya to tabbas ita ce za ta fara tona masa asirin ajiyar da aljannu suka masa a ƙirji, bare kuma shi da rayuwarsa gabaɗaya sirri

Chapter 13 of 14