fili ya ce
"Haka kawai shi fa za a dafawa zabuwa ma ai ya fini morewa, ni da na masa silar cin zabuwar
haka kawai na ƙare a kuɗin siyan goro, yo siyan goro mana hamsin in ba goro ba mai za a saya
da ita" Duk maganar nan da yake cikin hausa sak yake yinta, jin tahowar mutum ya ja bakinsa
ya yi shiru, yana mai yin sauri ya jefa hamsin ɗin cikin bahon gudun ma kar a ganta a gabansa
a zaci kuɗi kaɗan yake karɓa.
Wani saurayi ne gajere baƙi ya shigo da sallama, malam ya amsa saurayin bayan ya zauna ya
ce
"Malam ina da buƙata mai girma"
Sheik ya ce
"Ina jinka" Suarayi ya ce
"Matsalata guda ɗaya duk wajen budurwar da na je bata so na, sai ake cewa ba a son gajarta
ta, kuma wai na yi baƙi da yawa shi ne na ce ko za a bani maganin da zan kore baƙin jinin nan
daga jikina wato a bani maganin farin jini?" Shiru Sheik ya yi yana nazarin maganar, ya ƙara
kallonsa sai ya ga har wani sheƙi baƙin nasa yake, ga wani muni kamar me, hakan ya sa a
ransa ya ce
'Ni ɗin ma da kake gani duk bula ce, a toh ni ma ba farin bane mai ne ba don kar a yi saurin
gano ni ba da man bilicin ɗina zan ke tsiyayewa ina ɗaurawa a leda ina ba masu buƙata irin
taka, to kar a ce ni ɗin ma hakan take gwara in tsaya matsayina' A fili kuma ya ce
"Subhanalla, lahaula wala ƙuwwata illa billa, hasbunallahu wa ni,imal wakil, iyyaka na'abudu wa
iyyaka nasta'in" Saurayin gabaɗaya sai gabansa ya shiga faɗuwa jin abin da Sheik yake faɗa,
don har ya fara tunanin kar a ce aljana ce ta aure shi, ko kuma a ce ba zai taɓa auruwa ba a
haka zai rayu, gashi yana buƙatar aure.
Tun kafin Sheik ya ƙara magana ya ce
"Malam ba dai babu maganin jinyata ba?" Ya ƙarasa kamar zai yi kuka.
Sheik ya ce
",A haba ɗan saurayi ai kowace jinya Allah ya saukar da maganinta, mutuwa ce kawai bata da
magani" Wani gauron numfashi ya sauke ya ce
"Alhamdulillah"
Sheik ya ce
"Matsalarka tana da magani amma da sharaɗi" Ya ce
"Zan bi kowane sharaɗi ne in dai mace za ta amince in na ce ina sonta har ta yarda ta aureni"
Sheik ya ce
"Zan baka wani ruwa da za kake shafawa a fuskarka tsawon kwana bakwai, amma fa ka
tabbatar a kwanaki bakwai ɗin nan ka samu wata ƙwaƙƙwarar sana'a da za take kawo maka
kuɗi, sannan a ranar da ka cika kwana bakwai, ka nufi wajen budurwa da kake so kana zuwa
kafin ka gabatar da kanka ka bata dubu goma" Idanu saurayin ya zaro saboda shi ko kyautar
naira ɗari bai taɓa ba wata mace ba.
Yana kallon Sheik ya ce
"Malam dubu goma? Ni ai bana ba mace kuɗi" Sheik a zuciyarsa ya ce
'Ashe shi ya sa ake gudunka, yo ga muni ga cin zanzana, ma'ana ga talauci ka muni wace
mace ce za ta yarda, da aka bayar da kuɗi ai babu wanda zai ga muninka" A fili kuma sai ya ce
"Wannan shi ne sharaɗin maganinmu" Shiru ya yi sai kuma ya ce in dai da biyan buƙata to zai
yi.
Sheik ya san muddin saurayin nan yake bada kuɗi budurwa ba za ta ƙi son sa ba duk da ba
duka aka taru aka zama ɗaya ba wasu ƴan matan basu da son kuɗi.
Ruwan da Sheik ya tsiyaya masa a ƴar kwalba ya karɓa, ya ce masa na farin jinin ne da kuma
wanke shi da munin mata su daina ganin muninsa, godiya yake kamar zai ari baki, bai san
cewa ruwan ma a randa Sheik ya ɗuro shi ya ajiye, don ya lura in ya ce maganin da ya saya
wajen malam zai ke bayarwa ba lallai ya haɗa kuɗin ya ƙara komawa ya karɓo wasu ba, wanda
ya san zai iya warware matsalarsu ba tare sa magani ba sai ya basu maganin BOGI.
Yana karɓa ya tashi zai fita ba tare da ya bada kuɗin sadaka ba, ran Sheik ne ya ɓaci ganin
zai fita ya ce
"Ɗan samari babu abin sadaka ne ?" Juyowa ya yi cike da girmamawa ya ce
"Ai a gari aka yi sanarwa cewa a zo nan a karɓi magani an samu baƙo daga ƙasar larabawa na
ɗauka ba a biyan abin sadaka" Cike da jin haushi Sheik ya ce
"Hankali za ka taka aljani burubutu a gabanka dama su ne masu karɓar kuɗin sadakar" Da sauri
sairayin ya ja baya yana mai ɗakko dubu biyu hannunsa yana karkarwa ya ajiye a gaban Malam
ya juya cike da tsoro ya buɗe ƙofar ya fita.
Yana fita Sheik ya ɗauke dubu biyu.
Wani tsoho ne ya shigo yana dogara sanda, saboda tsufa har ya ranƙwafa, dakyar ya zauna,
yana sauke numfashin gajiya hannunsa yana karkarwar tsufa jikinsa duk ya yi yaba sannan
kansa da gemunsa duk furfura. Sheik kawai kallonsa yake ya rasa ma mai zai kawo tsohon nan
shi da ya dace ya zauna a gida yakenta sallah yana neman gafara ya jira zuwan mutuwarsa.
"Bakinsa yana karkarwa ya ce
"Ɗana balarabe, na sha wahala a waje wajen bin layin shigowa, yanzu ma ganin an bige ni a
turarreniya shi ne wata mata ta bar min layinta na shigo, ka san ai namiji ɗaya sai a mace ɗaya
aka ake shigowa, shi ya sa ka ga na shigo" Har lokacin Sheik yana mamakin abin da zai kawo
tsohon.
Daurewa ya yi ya ce
"Baba maganin basir kake so ko maganin ciwon baya?" Tsohon ya ce
"Haba ɗan nan balarabe, ni nan maganin maida tsoho yaro za ka bani, wato maganin ƙarfi ka
gane?Ƴan mata ne guda biyu zan ɗauka a rana ɗaya dukansu kowacce budurwa" Mamaki ne
ya mamaye Sheik dakyar ya danne harshen sa ganin bai yi magana da yaren hausa sak ba ya
ce
"Budurwa fa Baba?"
Tsoho ya ce
"Rass kuwa ba ma budurwa ɗaya ba ƴan mata biyu ake saka mini su a lalle gobe za su tare ka
ga kuwa aiki ya ganni dole in nuna musu basu auri tsoho ba"
Shiru Sheik ya yi ya rasa ma abin da zai faɗa masa, kawai ya ɗakko wani garin magani ya ce
ya saka a ruwan wanka ranar da amaren za su tare. Godiya kamar wanda aka bashi maganin
da tsofa zai barshi.
Dubu goma ya ba Sheik amma sai da Sheik ya kama shi ya iya dogara sandar ya tafi.
Wata mace ce mai ƙiba ta shigo, tana wani wurwurga idanu, ganin yadda take zazzare ido
tana wani soshe-soshen jiki sai Sheik ya ji duk ya tsargu, juyawa ta yi ta rufe ƙofar bai lura ta
saka mukulli ba, kuma sai ta cire mukullin, cike da ƙaguwa ya ce
"Mai yake tafe da ke?" Ta ce
"Ina so ka bani maganin da kullum mijina sai ni, sannan ka bani maganin da zan zubawa
kishiyata ta mutu, da wanda idan na shafa a hannuna duk inda kuɗi yake zai zo wajena" Ganin
kamar yadda take magana yanayin ya nuna kamar umarni take bashi ya ce
"Ayya ai ba a kisan kai a wajen nan, kuma kuɗin mutane ai kamar sata ce, zan baki dai wanda
mijink... Bai ƙarasa ba kawai sai ya ga ta tashi tsaye idanunta sun juye ta fara dalalar da yawu,
gabansa ne ya bada rasss ya shiga faɗuwa tamkar zuciyarsa za ta huda ƙirjin ta fito,
gadan-gadan ya ga ta biyo shi, ya ja baya ta matso ya yi wani tsalle sai ya ji ta riƙe masa
hiramin da yake rataye a wuyansa, jin za ta sheƙe masa wuya suka shiga kunce.
Idanunsa cikin nata ya gane aljannunta ne suka tashi ba ita ba ce, salati ya hau janyowa yana
ji a ransa anya ba zai haƙura da maluntar nan ta BOGI kuwa ba? Da gudu suka yi wajen ƙofa
sai lokacin ya lura ƙofar a kulle, idanu ya zaro gabansa yana faɗuwa ganin daga shi sai ita
kuma bashi da nutsuwar mata ruƙiyya, kafin ya yi wani yunƙuri sai ji ya yi ta fisge hular gashin
kansa, salati ya ɗauka a zuciyarsa kafin ya ƙarasa wani ya kamo wani , yana juyowa ya ga ta
tuƙunƙuna hular ta ɗaga rigarta ta totsa hular da gemo da sajen boginsa a bireziya. Kafin ya
gama tunanin asirinsa zai tono ta yi wani kukan kura ta shaƙo shi, rasa abin yi ya yi ya buɗe
baki ya ce
"Gabaɗaya na ƙofar gida ku shigo a guje ana ruwan kuɗi a ɗakin malam" Ya faɗi hakan ne don
a yi saurin kawo masa ɗauki, ya manta da cewa kansa babu hula, haɓarsa babu gemo, gefen
fuskarsa babu sajen larabawa...
MAMAN AFRAH
09025576222
💃💃TALLAH TALLAH💃💃
*INA MANYAN MATAN SUKE?*
*Masoyana ina ƙara talalta muku kayan sana,ata kamr su*
*Less, atamfa, laffaya, kamfala, mayafai zannuwan gado, kayan yara, takalma na yara da
manya, abayas, huluna na maza, mata, yara frames, sarƙa ɗan kunne zubuna banguls.*
*Akwai kayan maganin mu na kamfanin meera b herbs, maganin sanyi, maganin ƙiba,
maganin rage ƙiba maganin rage tumbi, maganin cire tabo ga wanda suk shafa mai ya ɓata
musu jiki ko fuska, sannan uwa uba maganin mata.*
*A ƙarshe ina tallata muku FURA dakan mai, wacce muke yi mai garɗi da ƙamshin man
shanu, muna yi don biki, ko suna, ko taron naɗin sarauta da dai sauransu muna aikawa ko ina,
akwai nono galan galan da bokitai ga masu buƙata, ku nuna min ƙauna ta hanyar siyar abin da
nake siyarwa* .
*Mai so ya min magana a number ta 09025576222 idan ba saya za ki yi ba kar ki min mgn.*
https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c
👳🏻♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻♂️
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.📝
Daga marubuciyar:
Ƙazamin miji
Bonono Rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal Da sauransu
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK1️⃣
PAGE 8
Sanye take da doguwar rigar less wacce ta kama jikinta, ta yi ɗaurin ɗankwali wanda ya zauna
daram a kanta sai mayafinta wanda yake kala ɗaya da leshin da ta saka, ƙarami ne mayafin
yana rataye a gefen kafaɗarta ɗaya. Ƙaran takalmin ta mai tsine wanda take sakkowa da
saman benen shi ne ya janyo hankalin Hajiya da take zaune a kan kujera tana waya.
Tana riƙe da wayarta ta ƙaraso tsakiyar rangameman falon, lokacin ya yi daidai da gama
wayar Hajiya. Ɗagowa ta yi ta kalle ta, ta ce
"Inyeee ka ga ƴan matan Daddyn ta, kyakkyawar mace kuma matar manya ƴan boko masu
faɗa ji, sanann matar masu kumbar susa" Wani daɗi ne ya mamaye zuciyar Rahma tana jin daɗi
jin furucin da Hajiya ta mata, tabbas a duniya ta tsani talaka, ta tsani talauci kuma, tana son
saurayi ɗan manya wato ɗan gidan masu kuɗi sannan ɗan gayu ko ma dai yaya yake in har za
a iya nunawa sa,a shi to tana son shi sosai. Kai ta langaɓae gefe cikin shagwaɓaɓɓiyar fuskarta
ta ce
"Ai ni sai na zaɓa sai wanda ya isa ne zai aure ni Mummy bana son duk wani namiji in har bashi
da masu gidan rana" Murmushi Hajiya ta yi ta ce
"Da gaskiyar ki ko ni talauci ya yi gabas na yi yamma, kuma ke da kika tashi a gidan naira ai
dole sai ɗan naira" Murmushi ta yi ta ce
"Bari na je baby nah yana jirana" Hajiya ta ce
"Ya zo kenan" Rahma ta ce
"Eh ya zo" Tana faɗa ta kiya cikin takunta na maau aji irin na mata masu ji da kansu.
Yana zaune a wajen da aka tanada don zama a sha iska zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun
wajen, hango ta ya yi ta taho tana tafiya tamkar tarwaɗa, tana tafiya tana yanga da wani jan a ji
da mata masu aji ne kawai suke yin irin taku. Sulaiman tun da ya hango ta kwacakwam ya
mayar da hankalinsa a kanta, dama yana chartin ne da wata budurwarsa, amma ganin Rahma
ta taho sai ya yi saurin kashe data ya sauka ma daga kan whatspp ɗin gabaɗaya.
Ma'aruf yana daga can ɗaki ya zo buɗe labulen window saboda ya ji ɗakin ya ɗauki zafi, dama
dawowarsa daga makaranta kenan, ya shiga ya yi wanka shi ne zai shirya. Ganin Rahma sai ya
ji gabans ya faɗi, musamman da ya hango irin kallon da Sulaiman yake mata mai cike da
soyayya. Kishi ne ya tsaya masa a rai. Idanu ya runtse yana jin irin yadda zuciyarsa take
bugawa.
Da son samu ne yana so ya samu ko da kwatar matsayin da Sulaiman ne ya samu a wajen
Rahma, shi in ba ma jarabawa ba da kuma zuciya da baka tursasa ta, ina shi ina kamauwa da
son Rahma bayan ya san ko suma yake yana falkowa ba zai same ta ba.
Cike da jin haushi ya rufe labulen dan sai ya ji gwara ya dawwama a cikin zafin ɗakin, a kan ya
bar windown a buɗe yake kallon takaici.
Rahma kuwa ƙarasawa ta yi tana ɗan murmusawa, ta samu kujerar da take kallon ta
Sulaiman ta zauna, idanun da ya kafe ta da su, hakan ya sanya ta sakar masa da wani
shu'umin murmushi mai bayyana haƙora, yadda hakoranta suke a jere reras kamar masara sai
ya ji ya ƙara mutuwa a kanta, ya san za a saka Rahama a sahun farko na kyawawa.
Cike da murya irin ta mayaudarin namiji, irin muryar da dama ta saba da yi digiri a yaudara ya
ce
"Sannu da zuwa sarauniyar matan duniya, alkairin Allah yana lulluɓe da ke, ina so ki sani
mutuwa ce kawai za ta raba mu, don na san na gama dacen mace ta kece raini ta nunawa sa'"
Ya faɗa yana kafe ta da idanunsa wanda har aai da ya sa ta ɗan sunkuyar da kai tanaƴar dariya
kaɗan.
Hannunsa ya miƙaya ajiye wayarsa a kan teburin da yake a tsakiyarsu ya ce
"Da a ce zan mallake ki da kuwa na gama dace a duniya, ke ni bana jin zan sake bacci a
duniya, don an sallame ni, a baya in jin tamkar wanda na rako maza duniya, in na ga suna da
budurwa mai aji kuma ana nuna musu kulawa da soyayya ashe dai ni ɗin ma zan samu rabona"
Sai da ta ɗago fuskarta ta sauke idanunta a cikin nasa sannan ta ce
"Ba kai kaɗai ne ka yi sa'a ba ni ɗin ma har kullum ina alfahri da kai, yanzu daga zuwana ko
gaishe da kai ban yi ba amma kana ta zuba mini yabo" Ta faɗa don kaf ta rasa inda za ta saka
ranta, tana son ta ji ana yabonta ko ana koɗa kyawunta sai take ji kamar duk duniya babu
kyakkyawa kamar ta.
Idanu ya lumshe ya buɗe su tarrr a kan nata idanun yana jifanta da wani kallo na mayaudara
wanda duk macen da akw mata sai an sace zuciyarta ya ce
"Ke ɗin ce kin cancanci haka, ke ɗin ce duk kin rikita mini lissafi, bana iya kallon kowace mace
sai ke, bana son kowacce mace sai ke, har abada na gama zamar mace sauran duk kallon
maza nake musu" Wani mugun daɗi take ji
Tana kallonsa yana kallonta, hannunta da ta ɗora a kan teburin ya miƙa hannunsa ya ɗora a
kan hannunta, Ma'aruf da fitowarsa daga ɓangarensa kenan sanye yake da farin yadi ɗinki
tazarce yadin marar nauyi, ya yi matukar karɓar jikinsa, Sulaiman ganin Ma'aruf ya fito ya yi
saurin janye hannunsa, ita kuma da yake ta ba Ma'aruf baya bata san ya fito ba, kuma ita bata
ma ɗauki cewa taɓa hannun nata wani laifi ne da har za ta janye hannunta, tun da tana ganin
yanzu dan ma saurayi ya taɓa hannun mace ma wani abun ƙarama bane, tun da yanzu har
wajen hoto saurayi da budurwa suke zuwa, kuma a kama hannun juna, har ma da abin da ya fi
hakan, kuma a ɗora a status mutane su gani babu mai cewa an aikata haramun sai dai ake
cewa sun yi kyau, idan aka samu wanda ya ce hakan bai dace ba, sai a ce ai saurayin da za ta
aura ne, ko a wane hadisi ko ayar aka bayyana haka? Kawai dai ƙarshen duniya ne duk da ba
duka aka taru aka zama ɗaya ba.
Ma'aruf zuciyarsa ce ta fara tafasa shi fa dama ya lura cewa duk mazan nan da suke son
Rahma ba wai son aure suke mata ba duk mayaudara ne. Wani mugun kallo yale jefaw
Sulaiman daga nesa, Rahma ce ta lura da Sulaiman hankalinsa ba ya kanta baya ta waiwaya ta
ga Ma'aruf ta yatsina fuska ta ce
"Baby mene ne" Ta faɗa lokacin da ta mayar da kallonta kan Sulaiman ɗin.
Haushi ne ya kama zuciyar Ma'aruf jin Rahma ta kira Sulaiman da wanann sunan, sunan da ko
a mafarki zai ji daɗi ta kira shi da shi, shi ya rasa ma yaushe ya kamu da son Rahma abin nan
yana ci masa tuwo a ƙwarya ya san dai ko a tsarinsa babu mace irin Rahma, wacce bata san
darajar ɗan adam ba amma gashi so yana neman ya kai shi ya baro.
Idanu Sulaiman ya ɗauke jin Ma'aruf yana masa kwarjini, shi dama ya tsani ya zo gidan su
Rahma ya ga wannan baƙauyen da bashi da komai sai gidadanci da rashinw wuyewa. Ma'aruf
kuwa ji ya yi da a ce yana da dama da ya je ya kora Rahma cikin gida, sai dai bashi da iko da
wannan damar.
Sulaiman ne ya yi ƙasa da murya ya ce
"Baby ki sa wannan baƙauyen yayan naki ya kawo min ruwa" Ta kalli Sulaiman cike da jimanta
abin da ya ce ta ce
"Ruwa kake so sha bari na kira Mummy ta sanya ƴar aiki ta kawo" Yana ɗan haɗe rai ya ce
"Ni ba na son wata ƴar aiki wannan nake son ya kawo mini" Murmushi ta saki cike da kulawa ta
ce
"Kar ka damu ai yanzu kuwa" Ma'aruf da ya nufi get zai fita so yake ya je masallaci ya karanta
qur'ani ko ya samu sauƙi da salama a zuciyarsa, jin ƙaran wayarsa da take aljihu ya fito da ita,
ganin sunan Rahma abin ya bashi mamaki har sai da ya tsaya ya juyo don ya tabbatar da cewa
ita ɗin ce take kiransa, don ya san saboda wulakanci irin nata kwanaki cewa ta yi ta goge
numbersa saboda bata son take jin maganar baƙauye a kunnenta.
Juyawar da ya yi sai ya ga ita ɗin na wajen take kallo, kamar wasa sai ya ga tana ɗaga masa
hannu alamar ya zo, bao je ɗin ba kuma bai cigaba da tafiya ba don ya san wannan kiran akwai
wani abu a ƙasa kuma shi bashi da wata daraja da zai rama ko ma mai suka masa, saboda
tana faɗawa Daddy shikenan ko kuma Mummy wacce a dole son babu yadda za ta yi ne yake
zaune a gidan.
Yana mayar da idanunsa kan wayar hakan ya yi daidai da tsinkewar kiran, yana katsewa ya
ga wani kira ya shigo, juyawa ya yi yana tafiya ya ɗaga wayar ya kara a kunne yana lumshe ido,
a hakan yake tafiya kasancewar gidan babban gida ne, akwai tazara daga harabar gidan zuwa
get ɗin.
Yana karawa a kunne sai ji ya yi ta ce
"Na ce ba" Ta daɗa cike da iko da raini.
Cikin nutsuwa ya ce
"Ina jinki"
Ta ce
"Ka dawo ka ɗakkowa Sulaiman ruwa zai sha" Ransa ne kawai ya yi mugun ɓaci kasanceqar ya
san al'adar Rahma ce ta tsani a kashe mata waya sai kawai ya kashe domin ita ma ya ƙunsa
mata ɓacin ran da ta sa ya shaƙa.
Yana kashewa ya cigaba da tafiya har ya buɗe get ɗin ya fita waje.
Rahma ranta ne ya ɓaci kamar yadda ya yi zato, cike da jin kunya ta ce
"Ya ce sauri yake zai je wajen suturar abokinsa da ya mutu" Ta tsinci kanta da sheƙa ƙarya.
Sulaiman banza ta mata ko da ta ce za ta ɗakko masa da kanta sai ya ce ta bari ma ya daina
jin ƙishin. Haka dai ranar hirar tasu ta wakana babu wani armashi. Da zai tafi ya shiga mota ya
ɗakko rafar ƴan ɗari biyar guda biyu ya bata wai ta sha ice cream. Motar ya shiga direbansa da
yake ciki zaune yana jiransa ya tada motar, tana tsaye tana ɗaga masa hannu, har mai gadi ya
wangale musu get suka fita tare da haurawa titi.
Tana komawa ciki ta kwashe abin da Ma'aruf ya mata ta faɗawz Mummy inda ta ringa faɗa ta
inda take ahiga ba ta nan take fita ba, tana faɗin zai dawo ya same ta, tun da ba ubansa Mai
Gari bane ya gina gidan, da har yana zaune ba za a amfane shi ba.
Daddy sai bayan magriba ya dawo gidan, ko da aka zo cin abinci Mummy ta kwashe komai
ta faɗa masa na tsinka Rahma da Ma'aruf ɗin ya yi a gaban saurayinta, duk da Daddy ya san
abin da Rahmar ta yi bata kyauta ba sai dai ba zai iya tsawatar mata ba saboda soyayya da
kuma Hajiya ya san ba za ta bari a ga laifin ƴarta ba kasancewar ƴar tata ƴar ido ce. Ma'aruf
dama sai dai ya ci abincinsa da ban saboda Hajiya da Rahma wai basa iya cin abincin idan
yana waje zuciyarsu tana tashi, wai suna jin yana warin ƙauye, kuma kawai tsabar rainin wayo
ne.
Sai da aka yi ishasha'i ya dawo don karatu suke tsakanin magriba da isha'i a masallaci,
Daddy ne ya kira shi yana masa faɗan rashin gaskiya, Ma'aruf ya ce
"Haba Daddy ni ne fa gaba da Rahma amma sai ta aike ni kuma a gaban saurayinta, kuma ma
saurayin fa zan ɗakkowa ruwa, duk ƴan aikin gidan nan, yanzu fa ko Yayan da ka ce take faɗa
min ta daina Ma'aruf take kir...
Daddy ne ya katse shi da cewa
"Haba kai kuwa ana ga yaƙi kana ga ƙura, ana maganar baka je aike ba kai kana maganar bata
ce maka Yaya.
Hajiya ce ta katse da cewa
"An ƙi a ce maka Yayan ubanta ne kai da sai ta girmamaka" Kai ya sunkuyar don ya san Daddy
kawai yana tsoron Hajiya ne amma ai ya san shi ne da gaskia, haka ya masa faɗan ya tashi ya
fita ya koma ɓangarensa.
*BAYAN SATI UKU*
Zaune take a lambu ta ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tana zaune ne bisa kujerar roba sai ta ɗora
ƙafafunta a kan wata kujerar, jarida take dubawa sai kayan maƙulashe a kan plate a gabanta
tana ci.
Tun da fa shigo lambun yake kallonta da yake idanunta a kan jaridar bata san da tahowarsa
ba ma, sanye yake da riga blue mai ƙaramin hannu sai jeans baƙi sai ƙamshin turare yake mai
daɗi.
Rahma da ta jiyo ƙamshin iska ta kawo mata ta lumshe idanu, don ƙamshin turaren ya mata,
kasancewae sabo ne ya saya ƙamshinsa ya sha bamban da wanda yake shafawa. Sai da ya zo
dab da ita ta ji ƙamshin ya ƙaru alamar ma ƙamshin ba iska ce take kawowa ba mai ƙamshin
yana dab da ita. Murmushi ta saki, saboda ta san sun yj waya da Sulaiman ya ce zai zo su fita
su shaƙata kuma ta faɗa masa tana zaune a lambu, a tunaninta shi ne ya zo zai tsokane ta take
son ya rufe mata ido ko dai wani abu makamanci haka.
Cike da shauƙi ta ce
"Barka da zuwa Babynah" Gaban Ma'aruf ne ya faɗi yana tunanin ko dai addu'ar da ya kwana
yana yi a kan Allah ɗora shi a kanta ta amince da shi, ita ce ta karɓu.
Ta cigaba da cewa
"Ƙamshin turarenka ne ya sanar da ni ƙarasowarka, zuciyata tana maka marhabin, tana maka
tuni cewa da kai kaɗai za ta rayu!" Kaɗan ne numfashin sa bai bar gangar jikinsa ba, tsabar irin
yadda maganar ta dake shi, a hankali ya fara taku a dawo gabanta, sai lokacin ta ɗago fuskarta
daga kallon jaridar tana murmushi mai ƙara mata kyau da kwarjini.
A kan kyakkyawar ƙafarsa da take cikin baƙin takalmu ta fara yi wa idanunta masauki, ko a
mafarki bata taɓa zaton Ma'aruf bane, cikin murya mai taushi, wacce take damfare da nutsuwa
ya hau faɗin
"A nawa ɓangaren ma haka ne, da ke kaɗai za ta rayu, kuma zuciyarta ta janyo linzamina ne
zuwa wannan wajen, don ta bayyana miki asirin da yake cikinta, tana fata da addu'ar mu rayu a
tare har mutuwa...
Waɗannan kalaman sun sauka a kan dodon kunnen Sulaiman da ya nufo wajen, wanda kuma
ya ƙara shiga kunnuwan Mummy da ta zo za ta sanar da Rahma cewa za ta fita, saboda ta kira
wayar ta ta ji bata shiga ba, shi ne ta tasho don ta faɗa mata sai kuma kunnuwanta suka yi arba
da wannan babbar maganar...
*INNA TASALLAH*
Zaune take a tsakar gida da yammacin ranar asabar, tana zaune hannunta riƙe da mangwaro
irin mai ƙamshin gawasa, nunanne ne jawur da shi, tana sha tana lunshe ido har wani karkaɗa
kai take saboda zaƙin da take ji har tsakar kanta.
Tana a wannan halin Lami ta shigo da sallama, idanu Inna ta buɗe ganin Lami afujajan ta
dakata da shan mangwaron ta ce
"Lami lafiya kamar an hakaɗo ki?" Lami cike da jin haushin Inna tana wani ɓata rai ta ce
"Wato ke Inna har kin samu damar sha mangwaro har kina lumshe ido" Galala Inna take
kallonta cike da takaici ta ce
"Haba Lami wai ni ku mutane mai ya sa bakwa son ku ga wasu sun ci gaba? Da raina da
lafiyata ma ba zan sakata in wala na sai ana sanya min ido, yanzu kayan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14