Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 FUTURE WRITERS ASSOCITION (FUWA) Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Gaisuwar SARTSE zuwa gareku Iyalan Fam. Alherin Allah Ya kai muku a duk inda kuke.  Shafi na ɗaya     (01) Labarin Sartse ƙirƙirarren Labari ne, ban a rubuta shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan akwai wanda ya yi shige sa yanayin labarinsa muna neman yafiyarsa akan hakan. Haƙƙin Mallaka nawane ni kaɗai.  Kamar ko yaushe Book one zai kasance Free, Two da Three kuma zasu a paid, akan ƙaramin farashi.  Shimfiɗa *Jihar Jigawa , Nageriya.* Jihar Jigawa tana daya daga cikin jihohin da aka kirkira a karkashin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 27 ga watan Agusta, 1991. An ciro jihar ne daga tsohuwar Jihar Kano, inda aka ba ta sunan "Jigawa" wanda ke nufin kasa mai tudu ko yashi, yanayin kasar da ya shahara a yankin. Jihar ta kunshi hadakar manyan masarautu guda biyar (5) masu tsohon tarihi, wadanda suka hada da: Hadejia, Kazaure, Gumel, Ringim, da kuma Dutse. Wannan ya sa jihar ta zama matattarar al'adu daban-daban na Hausawa da Fulani da kuma Mangawa. Ana yi wa jihar lakabi da Sabuwar Duniya saboda burin da aka sa a gaba na gina ta a matsayin jiha mai dogaro da kanta ta fuskar noma da kasuwanci. *ƙaramar Hukumar Dutse*  Dutse birni ne mai dadadden tarihi a kasar Hausa. Asalin sunan garin ya fito ne daga manyan duwatsu da suka mamaye yankin. Kafin kafuwar jihar Jigawa a shekarar 1991, Dutse tana karkashin jihar Kano ne kuma tana daya daga cikin tsofaffin gundumomi masu daraja. Birnin na da sarauta mai karfi wato Masarautar Dutse, inda sarkin garin ake kiransa da "Sarkin Dutse." Tarihi ya nuna cewa mutanen farko sun zauna ne a kusa da wadannan duwatsun domin samun kariya daga makiya a lokacin yake-yake. Yanayin Girman Garin a Taswirar Nigeria Dutse tana nan a Arewa maso Gabashin Najeriya. Haka A taswirar jihar Jigawa, Dutse tana tsakiya zuwa kudancin jihar. Ba birni ne mai matukar fadi kamar Kano ko Kaduna ba, amma yana bunkasa cikin sauri sakamakon zama babban birnin jiha. Yanayin garin akwai zafi sosai a lokacin rani, sannan akwai hunturu mai ratsa jiki saboda duwatsu da kuma kusa da hamada. Haka a bangaren Sana'ar Mutanen Garin Mutanen Dutse galibi Hausawa ne da Fulani, don haka sana'o'insu sun hada da • Noma: Shi ne babban jigo, musamman noman gero, dawa, wake, da kuma shinkafa a wuraren da akwai ruwa. • Kiwon Dabbobi: Ganin cewa akwai Fulani sosai a yankin, kiwon shanu da awaki sana'a ce mai matukar muhimmanci. • Kasuwanci: Akwai manyan kasuwanni inda ake hada-hadar amfanin gona. • Aikin Gwamnati: Kasancewar sa babban birnin jiha, akwai ma'aikata da dalibai da dama (musamman saboda Jami'ar Tarayya ta Dutse - FUD). Takur Site unguwa ce da ke zaman kanta a cikin birnin Dutse, wacce ta yi fice wajen tsari da kyawun gine-gine. Unguwar tana cike da manyan gidaje na zamani wadanda aka gina su da faffadan fili. Galibi gidajen suna dauke da fulawa da korayen bishiyoyi da ke kara wa unguwar kyan gani. Sannan Mafiya yawan mutanen da ke zaune a nan ma'aikata ne, manyan jami'an gwamnati, da kuma malaman jami'a. Wannan ya sa za ka iske mutanen cikinta masu ilimi ne da sanin ya kamata. Babban abin da ya bambanta Takur da sauran anguwanni shi ne shiru. Babu hayaniyar yara a titi, babu kade-kade, kuma babu cinkoson mashina. Daga karar fankar sai kukan tsuntsaye; hakan ya sa ta zama gurin da mutum zai iya hutuwa cikin natsuwa. Sannan Tana da tituna masu kyau da hasken wutar lantarki wanda ya fi na sauran sassan garin tabbas saboda kasancewarta unguwar manya. Da misalin karfe 05:40 na yamma.  Wani irin azababben zafi nake ji yana shiga jikina, kamar ana tafasa ni a cikin tandar gurasa. Kicin ɗin gaba ɗaya ya ɗumame yana fitar da wani irin wuci, sakamakon girkin da nake a kurfoti guda biyu.  "Wayyo Allah!."  Na faɗa a fili bayan na juya ga miyar da take tafasa akan ɗayan kurfotin, tsumma na ɗauka na sauke ta ƙasa na fara juyata.  "Maggi bai ji ba! A'a ya ji Sardauna baya son maggi ya yi yawa." Na faɗa a dabarbarce, ina mai sa hannu na taɓa wayata, allon wayar ya kawo haske na yi tozali da kyakyawan hotona ni da mijina a ranar ɗaurin aurenmu, a fili na furta.  "Ina sonka mijina, ina ƙaunarka, Allah Ya kula mini da kai."  Ina faɗin haka na maida kallona ga agogon, shida da rabi daidai. Nasan kowanne lokaci zai iya shigowa, ƙaurin gurasar da nake gasawa ne ya daki hancina, ba shiri na miƙe tsaye na sa hannu a kan kaskon da nake gasawa da niyar juyawa, sai dai cikin rashin sa'a na kama dandarrayar kasakon maimakon gusar, wani irin zafi ya ratsani har tsakar kaina, na yi baya da sauri ina faɗin.  "Wayyo Allahna."  Ƙwalla ta cika min ido sakamakon raɗaɗin zafin da nake ji a 'yan yatsuna, ga kuma zafi da turirin da yake tashi daga cikin kicin ɗin.  Sake komawa na yi  na kama gurasar a hankali na juya. Bayan na juya na ƙara ɗaukan wani curi ɗaya na ɗorashin akan abinda nake murzawa da shi na fara murzawa ina faɗaɗashi, har sai da ya yi falai falai, sannan na cire takan kaskon na ɗora wannan, daga nan na koma kan miyar na ɗauko plast mai kyau na juye ta a ciki gaba ɗaya, da niyar idan ya ci ya rage ni sai na ci. Domin azababben ƙamshinta da ya cika mini hanci ya cire mini sha'awarta na lokacin, bayan na juye na ɗauki plast ɗin na fito daga kicin ɗin zuwa makaken falona na alfarma da ya ƙawato da kayan ado masu kyau da tsari.  Ɓangaren dinning na nufa, shi kansa abin tsayawa ka kalla ne, domin ni kaina lokaci zuwa lokaci na kan tsaya na kalli gidana da irin ƙoƙarin da iyayena suka yi wajen cika shi da kayan alfarma, bayan ƙoƙarin da Mijina Sardauna ya yi na gina makeken gida a anguwar Takur. Ina ajiyewa na koma kicin ɗin na juya gurasar dake kan wuta, sannan na fara ƙoƙarin juye wutar dake cikin kurfotin da na sauke miya a cikin wani bukitin ƙarfe, sabida bana son kashe wutar a cikin kicin ɗin toka ta ɓata minin aikin da na yi, bayan na juye na ɗauki Bukitin na fita bayan gidan ta ƙaramar ƙofar kicin, ƙaramin famfon na nufa na tara bokitin da wutar garwashin a ciki, bayan ruwan ya taru na zubar da iya ruwan da ya yi sanyi a bakin rariya, da sauri na koma kicin na sauke gurasar da ke kai na ɗauki ta ƙarshen na fara murzawa, bayan ta yi faɗi na ɗora ta akan kaskon, daga nan na koma na shanya gawayen da na kashe ɗazu a ƙasa, sannan na dawo kicin ɗin.  Daidai lokacin da motarsa ta fara horn, da sauri na dawo falo na buɗe taga na fara kallonsa, tun daga parking ɗin har fitowarsa, yanayin yadda yake tafiya ma kaɗai abin a tsaya a kallani.  "Wayyo Mijina, Allah Ya ƙara maka arziƙi, lafiya da nisan kwana."  Na faɗa a raina, ina ja da baya.  Ƙamshin turarensa ne ya fara dukkan hancina kafin sassanyar muryarsa ta daki dodon kunne na.  "Sannu da zuwa."  Na faɗa kamar zan durƙusa ma sa, tsabagen biyayya da ƙauna.  "Yawwa! Sannu da gida."  Ya faɗa yana miƙo mini jakar hannunsa, na russuna na amsa, ya ƙara ciro hulal kansa ya miƙa mini kana ya sami kujera ya zauna, ɗakinsa na nufa zan ajiye cikin kakausar muryarsa ya ce.  "Ranki ya daɗe takalmin fa."  Murmushi na saki sannan na ce.  "Ina shirin fara shiga da waɗannan ne."  "Ko dai kin barni na cire?."  Na dawo kusa dashi, na tsugunna na cire masa takalmin, bayan na cire na kwaɓe mai safar sannan na ɗauka na shiga dasu cikin ɗakinsa, komai a mazauninsa na ajiye su na ƙara gyara inda na ga kamar bai gyaru ba a ɗakin sannan na shiga toilet na haɗa masa ruwan zafi daidai yadda nasan yana so.  A inda na barshi na sameshi yana danna wayarsa. Sai da na gyara muryata yadda zata fito da zaƙi sannan na ce.  "Ruwan wanka ya zama ready."  Ajiye wayar ya yi ya miƙi zuwa ɗakin.  "Ki jera mini abinci kafin na fito."  Ya faɗa cikin kakkausar muryarsa sannan ya shige ciki. Ina nan tsaye sai da naga ya yi kusan minti biyar a ciki sannan na sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, jin shi shiru ya bani ya bani tabbacin ruwan ya yi masa daidai.  Kitchen na koma na shiga haɗo kayan abinci, a hankali a hankali na jera komai akan dinning ɗin bayan na gama na shiga nawa toilet ɗin nima na watsa ruwa a gaggauce na fito daga bayin na hau shiryawa.  "Nana! Nana! Nana!!."  Na ji muryarshi, ba shiri na zura Hijabi na fito. "Na'am! Gani."  "Kina jina ina ta faman kiranki."  Ya faɗa yana zama akan dinning.  "Yanzu na fito daga wanka ne."  Na bashi amsa.  "Okay i see, zuba mini."  Ya faɗa hankalinsa yana kan wayarsa. Plate na ɗauko na saka masa Gurasar guda uku, sannan na ɗauki bowl na zuba masa miyar, sannan na ƙara ɗaukan wani bowl ɗin na saka masa farfesun tsokar rago, sai kuma kofi na zuba masa lemon citta da ya sa na yi masa. Sai da nagama gaba ɗaya sannan na ce.  "Gashinnan."  Wayarsa ya ajiye ya fara cin abinci, ganin ya fara cin abincin yasa na koma ɗaki na ci gaba da shiri na, sai da na taje dogon gashina sannan na fara shiri, sauƙaƙƙiyar kwalliya na yi, sannan na ɗauko doguwar rigar abaya na saka, bayan na feshi jikina da haɗin turarruka.  Ko da na fito falon  ban ganshi akan dinning ɗin ba, sai da na ƙarasa shigowa falon na hango sa acan kan kujera yana yana faman danna waya, kan dinning ɗin na nufa na zauna, buɗe plast na yi zansa gurasar sai sai guda ɗaya na gani, murmushi na yi a raina na ce.  "Yau yallaɓai anji daɗin girkin kenan."  Na ɗauki ɗayar nasa a plate ɗin da ya gama ci, na buɗe plast ɗin miyar zan zuba sai dai fa sam babu miyar a ciki ya shanye, karo na farko cikin abubuwan da Sardauna yake yi mini na ji babu daɗi, buɗe plast ɗin da farfesun naman ragon yake ciki na yi shima dai babu.  "Me ya faru haka?."  Na tambayi kaina, dan nasan dai Sardauna bazai taɓa cinye duka wa'yannan ba, dole wani wajen ya kai ko ya kai kitchen.  "Ka kai ragowar kicin ne?."  Na tambaye shi, muryata na rawa kamar wacca ta yi tsaren gudu, ko dayake ba shakka tsare na yi, domin na yi tsere da zuciyata kafin bakina ya iya fito da wanann tambayar.  "Ban ɗauke komai ba, ai aikin ne ko?."  Zama na yi akan dinning ɗin, gaba ɗaya raina babu daɗi na rasa abinda ke mini daɗi. Muryar shi na juyo ya na cewa.  "Me kike yi anan ne?."  Na goge ƙwallar da ta fito daga ido na ce.  "Babu komai?."  "To tawo nan mana."  "Abincin zan ci."  Na faɗa ba tare da na taso ɗin ba.  "Tom."  Kawai ya faɗa ya ci gaba da abinda yake, na tashi na shiga cikin kicin ɗin, ban masan me zan iya dafawa ba wanda zansa a cikina, ga yatsu na sai wani irin zugi suke yi mini kamar wacca na taɓa attaruhu.  Haka nagama zagaye na a cikin kicin ɗin na fito zuwa falo, na bude firij na ɗakko biredi na dawo kan dining na haɗa da ragowar romon farfesun naman na ci.  Bayan na kammala na ɗauke komai na kai kicin, na gyara wajen tsaf sannan na nufo shi zan zauna na huce gajiyar da take cin jikina. Sai dai ban kai ga ƙarasowa ba idanuna suka sauka kan abinda yake yi, ya zuge zif ɗin ɗaya daga cikin fulallukan kujera yana fito da katifar ciki yana gutsirawa a hankali, kamar ƙaramin yaro yana wasa, sai da na haɗiye wani abu a raina sannan na ce. "Sardauna! Kujerar kake yagawa fa?"  Na fada ina kallon katifar da yake gutsirawa, gabana yana faɗuwa ganin yadda yake ɓarnatar da kayan gidan namu. Kallona ya yi sannan ya kalli abinda ya watsar.   "To kin barni nan ni kaɗai, ba dole na yi duk abinda zanyi ba dan ma banyi miki kuka ba."  Murmushi na yi sannan na zauna kusa dashi da faɗin. "Abinci fa na ci." Cuno baki ya yi kamar ƙaramin yaro zaiyi kuka sannan ya ce.  "To kuma sai ki bar mijin ki da yake sonki fiye da komai shi ka ɗai, babu abokin ta ya shi zama."  "To ai gani nan nazo."  Na faɗa ina shafa masa kai, ai kuwa ya kwanto akan cinyata.  "Daman kaina ƙaiƙayi yake, ki gyara mini."  Ya faɗa bayan ya kwanto, tare da  janyo wayarsa ya fara dannawa, wani irin nauyi na ji kamar an ɗoramin dutse, kamar da gangan ya sakar mini nauyinsa, na fara shafa masa kansa, ina jin dumin gashinsa a tafukan hannuna. "'Nana." Ya kira sunana a hankali, idonsa har yanzu yana kan wayarsa.  "'Na ga yadda kika yi shiru ɗazu da kika ga na cinye Gurasa, Ko dai kin fara gajiya ne da yi mini girki ne, ko gajiya da zama dani a cikin gidan? Rayuwar aure fa bauta da soyayya ne! Na ɗauka kin fi kowa sanin cewa duk abin da yake nawa, naki ne... har da yunwar ki.'" Na haɗiye miyau me ɗaci da ya tsaya mini a maƙwogaro, na yi ƙoƙarin yin murmushi duk da raɗaɗin da yatsuna suke mini na ƙunar da na yi ɗazu na ce.  "'Haba Sardauna! Kai fa mijina ne, ni kuma matarka ce mai ƙaunarka, ai na ji daɗi ma da ka cinye abincin, hakan na nufin girkin ya yi daɗi kuma hakane burina." Ya ɗaga idonsa ya kalle ni, wani kallo mai wuyar fassara sannan ya ce.  "Yauwa. Domin idan kika fara ƙorafi a kan abinci, zan fara tunanin ko ni ɗin ne ba kya so... ko kuwa kin fara manta yadda iyayenki su ka gaya miki yadda mace ta gari take zama da mijinta?"  Ƙarar wayata ne ya katse mini maganar da na yi niyar yi, na kai hannu zan ɗauka amma Sardauna ya riga ni.  "Wake kiranki a daren nan?" Murmushi na yi sannan na ce.  "Bansaniba wallahi, amma bani na ɗaga."  Sardauna bai ba ni wayar ba, sai ma juyawa da ya yi ya fuskanci allon wayar, hasken ya haska kwayar idonsa da ta canza launi lokaci guda. Ya dade yana kallon sunan dake kan allon wayar kafin ya dago ya kalle ni, wani irin kallo nasa da yake mini wanda ni kaina bana gane me yake nufi dashi, sai kuma ya saki wani irin murmushi kana ya ce.  "Daga gida ne..."  Ya fada muryarsa na rawa kaɗan.   "Radiya ce."  Ya kama sunan babbar Yayarmu kai tsaye, sannan ya ce. "Me take nema gunki a wannan lokacin?" Ban kai ga ba shi amsa ba, ya danna maɓallin kin amsa kiran (Reject). Ya ajiye wayar a kan kirjinsa, ya kara gyara kwanciyarsa a cinyata yana kallon silin din dakin. "Ita taƙi zaman aure, tana so ta hanaki kula da miji ko bawa mijinki lokacinki. Nana, kin san ina son ki ko? Kuma kin san ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Wannan gidan namu ne mu biyu, duk wanda zai kawo mana rarrabuwa, ko da kuwa danginki ne, to ba ya son mu." Wani irin nauyi na ji ya ƙara danne ni, ba nauyin Sardauna ba, nauyin kalaman da ya jefo mini ne. Ya kama hannuna da ya kone dazu, ya matse shi a hankali sannan ya ce.  "Gobe me zamu karya dashi? Ni bana son cin biredi abinci nake son ci very special, ba irin wanda muka saba ci ba."  Na yi murmushi muryata na rawa sannan na ce.  "Tom Mijina na me kake so?."  "Zaɓi yana wajenki, amma dai abu na daban, ko zan sami Vento cake wanda zan fita dashi ofis?."  Na gyaɗa kai sannan na ce.  "Zaka samu mana." Bansan ashe ƙwalla ta fito daga idona ba, sai ji na yi ya kai hannu gefen idona ya goge hawayen da yatsansa, sannan ya kai yatsan bakinsa ya ɗanɗana.  "Hawayenki suna da ɗanɗanon gishiri, Nana. Kada ki sake kuka... domin kukan mace a gidan miji, alama ce ta rashin godiya ga Allah ko kuma raina kulawar da miji yake ba ta." Washe gari. Gaba ɗaya jikina babu daɗi haka na tashi, bayan na yi sallar asuba na shiga kicin, ba tare da sanin ainahin abu na daban da Sardauna yake maganarsa ba. Sai da na ƙarewa kicin ɗin kallon sannan basira ta faɗo mini, na tsugunna gaban kurfoti bayan na zuba gawaye na fara ƙoƙarin kunna wuta, sai dai da na kunna hutar iska take kaɗe ta, abu kamar wasa na kusa minti sha biyar a gaban huta amma taƙi kunnuwa.  Miƙewa na yi na nufi kan gas ɗina yau kawai zanyi girki akansa, ina kunnawa na ɗora tea kafin na ɗakko fulawa na shiga kwaɓa Fanke, amma wannan mai attaruhu da albasa da maggi ne a ciki, banda tabbaci amma nasan Sardauna bai taɓa cin wannan ba, nima na ko yi sarrafa fulawane a wajen Anty Hadiza matar Isah Nadabo dake ita 'yar kano ce kuma a kanon ma ƙwararriya ce a harkar sarrafa fulawa. Bayan kwaɓa na rufe shi na shiga juye tea din a flask sannan na ɗakko kasko na ɗora akan gas ɗin na zuba mai.  Ina ƙoƙarin fara saka fanke a cikin mai ya shigo kicin ɗin, har ƙasa na tsugunna ina gaida shi kamar zan yi masa sujjada. "Ina kwana, an tashi lafiya?."  Kallona ya yi sai kawai na ji ya ce. "Me yasa baki da tausayi ne Nana, me yasa imaninki yake raguwa a ko da yaushe?."  Gabana yashiga faɗuwa, ƙirjina ya fara dukan uku uku, bansan tausayin da ya kaini kunna gas ba, duk da ba wani amfani nake dashi ba, sai na yi sati biyu banyi girki akai ba, hasali ma shi ke amfanin da shi wajen dafa ruwan wanka, ko tea idan yana sauri.  "Ka yi hakuri dan Allah, gawayin ne yaƙi kamawa gaba ɗaya, na kusa minti goma ina kunnawa amma yaƙi kamawa."  "Mitchewww."  Ya ja wani uban tsaki, sannam ya ce.  "Minti goma kacal? Ba zaki iya minti goma wajen kunnawa hutar da zaki yi wa mijinki girki ba? Nana bansan yaushe rashin imaninki ya kai haka ba, tabbas 'yan uwnaki zawara suna fara ɗoraki a turbar da suka bi suka kashe aurensu."  Hawaye na ji ya fara gangaro mini daga ido, cikin sanyi murya na ce.  "Ka yi hakuri dan Allah, nasan kana son fita da wuri kar na ɓata maka lokaci, amma in sha Allahu bazan sake amfani dashi ba har Abada."  Na faɗa muryata na rawa, alamun kuka ya fara cin ƙarfi na.  "Kuka kuma? Nana me yasa kike son azabtar da zuciyata da hawayenki ne? Nifa mijinki ne mai sonki fiye da komai a duniya, Nana kawai ina guje miki bin hanyar da 'yan uwnaki suka bi." Shiru na yi bance komai ba, sai shashaƙar kuka da nake yi.  "Nana! Goge hawayen nan ki ci gaba da abinda kike amma bana son almubazaranci, kinsan yadda rayuwa ta yi tsada, ko da yake ba sai na faɗa miki ba, gidanku ka ɗai ya isheki ishara."  Legendspen 08129553981 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na biyu     (02) Goge hawayen na shiga yi, na rasa me yake mini daɗi, Allah Ya gani ina mugun so da ƙaunar mijina, kamae yadda shima na tabbatar yana sona, to me zai sa na tsaya akan gas ina ɓata masa rai. Tashi na yi na je na kashe Gas ɗin sannan na ce.  "Ka yi hakuri dan Allah, idan ban tausaya maka ba wazan tausayawa a duniya? Wa nake dashi da zan zo bayan kai?"  "Nana ai naga alamun kamar ana son shiga tsakanin mu a hure miki kunne."  Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushin da nake kallo a matsayin soyayya mai girma, sannan ya ƙara cewa.  "Nana ina son na nemi alfarma a wajenki guda ɗaya."  Na gyaɗa masa kai sannan na ce.  "Ina sauraronka."  "Nana duk runtsi duk wuya ka da ki bari wani ya shiga tsakanin ki da mijinki, ina faɗa miki hakane a matsayina na mijinki, mai ƙaunarki."  Cike da farin ciki da gamsuwa da soyayyarsa na ce.  "Tom in sha Allah, yanzu kaje ka yi wanka zan kunna wutar gawayin na soya na kawo ma."  "Tom ki yi sauri kinsan dai fita nake son yi."  Ya faɗa yana juyawa ya fice, ni kuma na kulle ko ina na kicin din na fara ƙoƙarin kunna wutar.  Gaba ɗaya kicin ɗin ya turniƙe da hayaƙi wanda ya tsaya mini a maƙwogarona na fara tari babu ƙaƙƙautawa, ba shiri na tsugguna a ƙasa na fara kakari, ina jin kamar hanjin cikina zai fito waje, da ƙyar na iya tashi na fara buɗe kokafin bayan na ga wutar ta kama. Idona fal da ƙwallar da ta taru sabida hayaƙi na tashi na ɗakko farantin silba na shiga firfita wutar har takama.  Na sakko da kaskon daga kan gas din na ɗora akan kurfotin, ina yi ina firfitawa har man ya yi zafi na fara sanya fanken ina soyawa. Kusan minti talatin sannan komai ya kammala na juye a filas na fito falo, yana zaune kan kujera ɗaure da tawul ɗin wanka.  Kan Dining na nufa na ajiye plast ɗin, sannan na koma Kicin na ɗakko kufuna da faranti na dawo na jera akan dining sannan na dawo cikin falon.  "Komai ya kammala."  Na faɗa ina ƙoƙarin zama sabida sandarewa da na ji bayana ya yi, sakamakon durƙushen da na yi na soyawa fanken, kallona ya yi sanan ya ce. "Ni ai ban kammala ba! Ko ni zan shirya kaina ne?."  Murmushin yaƙe na yi sannan na ce.  "Aha ba dai! Ya zaayi ka shirya kanka ni ina nan, mene amfanina?." "Babu kam, idan har ba zaki yi mini biyayya ki faranta rai ba, babu."  "Mene haka?."  Na faɗa arazane sakamakon abinda nagani, sosa ƙeya ya fara yi sannan ya ce.  "To na buɗe zan shirya tun da naga kina kicin, kuma ni banga kayan da suka yi mini ba shine sai na fito dasu duka."  Yanayin yadda ya yi magana ya yi matuƙar burgeni, ya kuma goge

Chapter 1 of 16