Share this page
lokacin da Alhaji yake Alhaji bare nasan yadda aka shiga lokacin da ya dawo Hajijiya, wannan ya sanya Alhaji yake matukar so da tausayina, kasancewar gatan da yayuna suka samu a lokacin da suke kamar ni bansame shi ba, Alhaji ya fara zuwa kasuwar Laraba da take ci Mako Mako yana siyar da kayan abinci, sauran ranakun kuma yake zama a shagon da ya bude shima na awon kayan abinci a gida. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na huɗu     (04) Shekarata uku a duniya, Hajiya ta sake samun ciki wanda shine cikin autanmu Ra’is a zuwa wannan lokacin Alhaji ya fara samun rufin asiri, duk wani ci da suttura na masu rufin asiri baya gagararmu, haka karatu babu wanda bamayi, na zamani da na addini, bayan haihuwar Ra’is sai Alhaji Yasa aka shigo da shagon waje zuwa cikin gida, bayan ya sami wani babban shago a bakin titi, tabbas ance haihuwar Ra’is ta zo da alheri sosai domin akwai wasu cikin yaran da Alhaji yake biyawa kudin karatu da ‘yan buƙatun rayuwa lokacin da yake amsa sunan Alhaji, wani cikinsu mai suna Isah Nadabo da ya zama babban mutum shine ya siyawa Alhaji Shagon a bakin titi, bayan ya cika masa shi da kayan siyarwa, sannan wani kuma ya cika mana gida da kayan abinci.  Tun daga lokacin haihuwar Ra’is bamu sake zama da rashi ba a gidan, muna zaune cikin rufin asirin ubangiji, haka kuma muna samun tsayayyiyar tarbiya daga wajen mahaifiyarmu Hajiya, domin Hajiya macece mai tsayawa kan tarbiyar yara. A bangaren kyau, dukkanmu irin kyawunta mu ka yi mussaman mu matan da mu ka yi har farinta, Yaya Ridwan da Ra’is da suka dan dakko duhun Alhaji, sai suka fi mu kyau ma, sabida ba suyi duhu dilik ba, sannan ba suyi haske fatau ba, sun yi black beauty ne, ko na ce Brown, ga sumarsu irin ta fulani, wacca duk muka ɗebo daga Hajiya, dan mu matan ma babu wacca gashinta bai kai gadon baya ba, kasancewar nafi su Yaya Rumaisa ƙanƙanta sai akafi ganin kyawuna akansu, kuma ni kaɗai ce na yo dara dara idanu irin na Alhaji, shi ya sa aka fi ganin kyawuna akansu. Sai da fa duk gidan kowa ya kwana da sanin cewa Yaya Ridwan yafi kowa kyau dan shi kama yake da larabawan Dubai. Yaya Radiya tana da matuƙar sauƙin kai, hakuri da kawar da kai akan abu, saɓanin Yaya Rumaisa Al-jarabatu, sunan da kowa ke kiranta dashi, bata neman sauki a rayuwatar ko kaɗan, rigima bata ta ba sai ta shiga ta yi kane kane, sai ka rantse ta tace. Yaya Ridwan kam, ɗan kurma dinfa kenan. Babu ruwanshi da abunda ba a sashi ba, wanda aka sa shi mai sai ya yi kamar bai ji ba, sai ya yini a gidan amma bai ce da kowa ƙala ba, ko abokai ba shi da su kullum yana cikin daki, sai ya yini a daki bai fito ba idan ba massallaci ba. Ni kuma ina cikin wasu nauyin mutane da ba agane kansu, idan naso zanyi surutu sai na addabi kowa, idan kuwa banso ba buɗe baki ma wahala yake mini, duk da cewa inda hakuri da kawar da kai, surutun nawa ma sai da ‘yan gidanmu nake yi idan na ga damar, abun da ba asani ba dai bazan shiga ba, sannan kwata kwata ba na cikin nau’in mutane marasa kunya, sannan duk abinda naga zai wahalal dani ina yi tattarashi gefe na watsar ko na tattara rayuwata na yi gaba. Haka ma Ra’is bai da hayaniya shima ko kaɗan duk cikinmu dai Yaya Rumaisa ce ta fita zakka, dan idan taso jarabarta kowa sai ya kula ta, Yaya Ridwan ne kawai ba ya kulata.  Kasancewar sunana Rawasiya yasa ‘yan makarantar daren mu suke tsokanta, yau su ce Rawasiya, gobe Gabashiya, jibi har shamiƙantun sai su ce min, gaba daya na zama abar tsokana a unguwar, shi ya sa na tattara sunan na watsar na koma Nana, indai aka ce dani Rawasiya to a gidane ko ‘yan uwa. Lokacin da na shiga FUD STAFF SCHOOL J S 1, idan ‘yan ajinmu suka ji suna yayuna sai su yi ta tambayata me ya sa sunana bai fara daga Ra ba, amma na yayuna duka Ra, kasancewar dukkanmu muka shiga makatantar, Yaya Radiya da Rumaisa suna J s 3, Ridwan J s 2, ni kuma J s 1, Ra’is ne kawai babu, sai na ce musu ni ba ‘yar gidan ba ce. Wata rana da Yaya Rumaisa ta zo ajinnu ta ce da ni Rawasiya nan ‘yan ajin suka ɗauka Rawasiya shamiƙatin, amma da yake ban bada fuska ba akan sunan sai Nana yafi zama a bakin nasu. Sanda muka shiga Aji na biyu lokacin su Yaya Radiya sun shiga Siniya, a lokacin Yaya Ridwan ne kawai, ‘yan matan makaranta tin daga ‘yan ajinmu har na ajinsu kowacce sai ta zo ta ce dani tana son Yayana, kaf makarantar yafi kowa yawan masoya, ga halinshi na rashin son magana ya kara ja masa farin jini a makarantar. Lokacin da zan shiga Siniya ne lokacin da muka yi saukar Al-kur’ani ni da Yaya Radiya, Yaya Rumaisa, Yaya Ridwan, ban da Ra’is sabida mun yi masa nisa sosai a karatu mussaman na addini.  Alhaji yana da burin mu yi karatu me zurfi, amma Allah bai nufi hakan ba, domin yaya Radiya tana shiga Aji 3 na babbar sakandire, Yaya Hadi dan gidan babbar yayarsu Alhaji ya ce yana son aurenta, babu yadda Alhaji ya iya haka ya sa ya aminta, sabida bai isa ya tunkari Hajjansa da maganar yana so ta yi karatu ba, ko da wani ne a waje ya ce yana sonta bare kuma Yaya Hadi jikan da tafi so a rayuwarta.  Tabbas Hajjansu Alhaji macece mai mugun son zuciya da sabon abun duniya, an ce sanda Alhaji yana da arziki babu wanda take so sama da shi, amma tun da ya sami karayar arziki ta watsar dashi da iyalansa, ta kama wanda yake da shi, gashi ba ta wani cika son Hajiyarmu ba, har wani suna take kiranta dashi wai Fulanin tashi ko Fulanin jeji ne, ni ban wani sani ba, tun da ba cika shiga sha’aninta na yi ba, domin nida Ra’is ta tsanemu har ce mana take masu farar ƙafa wai mune muka yi sanadiyar talaucewar ɗanta, wani lokacin ma ta ce ubanmu idan tana jin tsiyarta.  Shi ya sa ma mu a famili mu ka zama ware, muna gefe sai ayi abubuwa nawa ba muje ba, wani ma bamu sani ba, wani ko mun sani ba zama bu, da idan ba muje ba Hajiya na ta kura mana daga baya kuma ta kyalemu, tunda da zuwan da rashin zuwan ba tsira zamuyi da zagi ba, har gwanda bamu je ba ma zagin a bayan idanun mu ne.  Allah Ya haɗa jini Yaya Hadi Yaya Radiya tun da ita ma tana son abunta, ita ma Yaya Rumaisa ana haka saurayinta mai sunan Alhaji ya fito, ita ta turoshi ba ita ta turoshi ba Allah masani, dan da ya ce sai ta gama karatu amma rana tsaka ya sake maganar, hakan ya sa Alhaji ya amince zai aurar dasu tare da dora burinsa a kaina, ko ba komai ina da karancin shekaru a lokacin.  Ba mu dade da yin biki sauka ba aka sanya ranar aurensu duka su biyun, dan Hajja ta ce babu amfanin karatun da zasu yi. Haka ya sa aka sanya auren nasu, sai dai duk wannan baloƙoƙon da ta yi da aka tashi bikin babu kobo da ta bayar duk Alhaji ne da kudinsa ya yi, sai kuma yaransa da yake tare da shi Isah Nadabo har wannan lokacin, wanda ya siya maa shago a bakin titi ya cika masa shi da kaya, shine ya dauki nauyin yin kayan daki na duka su biyun.  Haka aka zo lokacin biki Alhaji da Hajiya sunyi hidima dai gwargwado, hidimar da babu wanda ya yi tunanin zasu iya irinta, dan bayan angama biki ma sai da Hajja ta kira Alhaji ta ce wai aina ya sami kudi, sai ya ce da ita ‘yan uwan Hajiya ne suka yi, maimakon ta gode musu ko ta yaba musu sai ta hau aibatasu, wai basu dauke ta da daraja ba da bazasu kawo gudumawa wajenta ba sai dai su ba wa ‘yarsu, abu kamar wasa sa ga Hajjan a gidanmu ta zo ta yi wa Hajiya tas, sannan kuma wai tafito da ragowar gudumawar sai dai Hajiya ta ce jiya ta haɗe komai anyiwa Yaya da Radiya da Rumaisa gara an kai musu, abu kamar shafar iska sai ga Hajja a gidan Yaya Rumaisa ba ta je gidan Yaya Radiya ba sabida tasan jikanta ne zai ci komai, sa ta je gidan Yaya Rumaisa, haka ta dinga jidar kayan garar abun haushi a gaban dangin mijin Yaya Rumaisa, har da kukanta sai sune suka rarrashe ta bayan Hajjan ta tafi.  A da Alhaji baya ɓoyewa Hajja komai amma yau da gobe tafi karfin wasa, a hankali ya gane Hajja ba ta yi dashi dan ba zai ce ba ta kaunarsa ba tun da babu uwar da zata haifi ɗa ta ce ba ta son shi, shi ya sa ya boye mata Isah Nadabo, mutumin da ya taimaka masa wanda ya rike amana ya dawo yana sakawa Alhaji da fin abinda ya yi masa, dan tsaf Hajja zata sa shi a gaba yakirashi ta kuma sa shi ya bata maƙudan kudaden da ba lallai gobe ya sake tun karar Alhaji, kuma ta dinga iƙirarin tsine masa idan yaƙi, a haka ma duk sati sai ta aika an amsar mata shinkafa da wake har dasu mai da maggi da kudi a shagon nasa, wani lokacin ma sai ta zo da kanta tai ta jidar indomi da madara, wani abun ma bata san shi ba kawai mugun hali ne, dan akwai lokacin da ta dauki Izel na wanke bandaki ta tafi dashi ta dauka abun sha ne ta sha, dakyar ta miƙe dan ta yi jinyar wajem wata biyu, maimakon ta yi hankali sai ta ce ita yanzu ta fara. Haka take rufe ido ta yi ta jidar kaya duk sanda tazo, akwai ma lokacin da ta fado daga kan kanta, dake shagon akewaye yake anyi gini tsakanin inda  kayan suke da inda mutane zasu tsaya, sai da fridge da kayan ruwa sune daga waje, shagon yana da girma da fadi, to garin haurowa ta tsallaka ciki ne ta dawo kasa ta fadi, nan ma sai da ta yi jinya, amma dake matar nan babu Allah a ranta sai ta ci gaba da zuwa. A kullum burina shine na yi karatu mai zurfi, na zama wata ko da a iya Dutse ne, na taimaki iyayena da ‘yan uwana, ina son ganin na yi wa Alhaji wani abu da zai ji dadinshi a rayuwa, mahaifina da mahaifiyata suna da buri akaina na ganin cewa na yi karatun boko mai zurfi, kuma ni kaina haka sabida na fahimci idan banyi karatu mai zurfi ba, babu inda zani.  Haka rayuwa take ta tafiya, yau fari gobe baƙi. Yayuna suna gidan aurensu kuma kowacce babu abinda zamu ce da Allah sai godiya, dan kowacce da ka ganta zaka san tana cikin rufin asiri, a hankali rayuwa tana gangarawa inan da burin na karatu mai zurfi, sai dai bansan me kaddara ta tsara mini ba. 09:30pm.  Zaune muke a tsakar gida ana dan taɓa hira, ni da Hajiya da Ra’is, ko na ce Hajiya da Ra’is da ni da ido kawai nake binsu, bansan me ke damauna ba amma gaba ɗaya tun yamma banajin daɗi, gaba ɗaya ji na nake wata sukuku. Yaya Ridwan kam yana can daki yana faman game, dan yanzu game ya siya da ake yi a tv da wani abu na rikewa a hannu wai shi Handle, in ji Ra’is.  Alhaji ya shigo bakinsa dauke da sallama, da sauri na miƙe ina faɗin.  “Sannu da zuwa, babanmu.”  Ya sakar mini murmushi sannan ya ce.  “Yawwa.”  Bayan ya zauna ne Ra’is da Hajiya suka yi masa sannu da zuwa, Hajiya ta miƙe ɗakko masa abinci, Ra’is da Hajiya Aminan juna ne, ko da yaushe tare zaki gansu, dan Ra’is ina ga ko a waje baida wasu abokan kirki, kullum suna zaune da Hajiyya hirar su ba ta ƙarewa, karasa me suke cewa, yanzun ma tare suka nufi kitchen din ɗauko ma Alhaji abinci.  Bayan Alhaji ya gama cin abincine ya ce.  “Rawasiya ga saƙonki.”  Ya faɗa yana miƙamin leda, nasan saƙon bai wuce maset da kalkuketa ba, dan su na ce masa ina so ɗazu da safe, sai kuma biskit na makarantar gobe, kafin na gama buɗewa Ra’is ya ce.  “Hajiya nima ina so littafi nawa sun cika, sannan rulata ta karye.”  Dariya na yi masa sannan na ce.  “Ai Hajiya ba ta da shago.”  “Barshi dai ya faɗa mata, ina ga kantin zata bini ta karɓa masa.”  Alhaji ya faɗa, Hajiya kuma ta ce.  “Ina ni ina binka kanti, kawai dai a kawo masa.”  “Wannan ya yi bacci ne?”  Alhaji ya faɗa yana nuna ɗakinsu Ya Ridwan.  “Yana ciki yana faman sana’ar.”  Hajiya ta faɗa, sannan ta ƙara da cewa.  “Wai ni kuwa Alhaji yaushe yaron nan zai fara zaman kantin nan ne? Ya kamata ya fara rage ma wasu abubuwan da wannan zaman asarar da yake.” Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce.  “Yaron da yake shirin shiga jami’a, ina yake da lokacin zaman kanti?” “Ni kuwa ansama masa Addmision din ne? Bai ma faɗan yadda suka yi da bawan Allah nan ba.”  Hajiya ta faɗa sai da Ahaji ya sha ruwa sannan ya ce.  “Ai Isah Nadabon ma ya zo waje na ɗazu, har yake yi mini maganar ita Rawasiya.”  Da sauri na katseshi da cewa. “Alhaji Nana dai.”  Banza ya yi dani ya ci gaba da cewa.  “Yana tambaya wai aure zata yi itama ko sai ta yi karatu, na ce dashi sai ta yi karatu, to wai da ya nuna sha’awar shi ne akan yana son aurenta, sabida ya na son ya yi tafiya ta shekara biyu kuma shi kanshi zaifi son ace ya tafi tare da iyali ne.” Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na biyar     (05) Tunda Alhaji ya fara magana gabana yake faduwa, aure kuma? Ni ba auren ba ma wallahi kwata kwata bana son mutum ya girmeni sosai, gaba daya shekara ta sha bakwai, Isah Nadabo a yanzu ya kai wajen talatin, ni nafi son yaro dan shawalwali, wanda baifi 26 ba haka, maganar Hajiya ce ta katse min tunanin da na shiga da na tana cewa.  "To Alhaji kamar Isah Nadabo ai yafi ƙarfin haka a wajenmu ko, da an bashi."  "Kai Hajiya!"  Na faɗa a raina, Alhaji ne ya ce da ita. "A'a dai, ai bama za ayi haka ba ita yarinyar ba ta da zaɓi ne?"  "Ai shikenan dai, Allah Ya bata na gari."  Alhaji ya ce. "Amin." Ni dai nan zaune bance ko ƙala ba, amma naji dadi gaskiyya, na auri Isah Nadabo na ce na auri wa, ƙanin babane ko me? Babba dashi da ace ya yi aure a shekara goma sha wani abun da yanzu yana da yarinya kamar ni, kowacce ta girmi ni ma. Gashi wani baki ma, ni Allah Ya gani ina son dan gayu dan zamani, shi kam kallo daya zaki yi ma Isah Nadabo kinsan mutum ne mara walwala, kansa a kulle yake.  Daga wannan rana ba a sake wata magana da ta shafi Isah Nadabo ba, kuma nima na ji daɗin haka, haka na ci gaba da rayuwa ina 'yan matancina a gida har zuwa ranar da ƙaddarar Yallaɓaina ta faɗa mini.  Ranar wata lahadi bayan sallar magariba na fito daga gida ina shirin tafiya makarantar dare da nake zuwa, wacca gaba daya banfi a sati biyu da fara zuwanta ba. Tafiya nake kamar ko yaushe cikin nutsuwa,kamar ance ɗaga idonki.  Kyakyawan matashin saurayi, mai kyakyawan yanayi da kyakyawar shiga, fuskarsa fara ce sosai yana da tarin kwantacciyar suma. Gaba ɗaya kammaninsa ba sa yanayi da na 'yan nigeria sabida yanayin idonsa har wani walƙiya suke mai daukan ido, hancinshi mai matsakaicin tsini haka bakinsa, wani kyakyawan gashin baki ya yi masa ƙawayan ya gangaro gefe da gefe ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa.  "Ya Hayyu Ya Qayyum!"  Abinda na faɗa a raina, sannan na ce. "Wasu kamar sune suka hallicci kansu, sabida tsabar tsagwaran kyau, ina ganin Yaya Ridwan yafi kowa kyau ashe mummunane a gaban wannan."  A hankali ya fara ta kawo yana tun karo ni, wani irin "Dif! Dif!" Na ji ƙirjina yana bugawa, ƙafafuna suka fara karkarwa, ƙwalla ta taro a idona sakamakon matsanancin bugun da zuciyata take mai ƙarfi. A lokacin da ya matso gab da ni, sai da na ji numfashina ya ɗauke na daƙiƙa. "Salamu alaikum."  Wata sassanyar murya mai yanayi da busar sarewa ta shiga kunnena, bayan sassanya ƙamshin turarensa ya cika min rayuwa gaba ɗaya.   "Ina wuni?."  Na tsinci kaina da faɗa har da durƙusawa, ya yi murmushi sannan ya ce.   "Gidan can zan aiki ki."  Ya faɗa yana nuna min gida dake kallon namu, na juya na kalli gidan sannaan na ce.  "Toh!"  "Nan ne gidan Alhaji Hadi ko?" Ya tambaya, ni kuwa jikina har ɓari yake amsa tare da gyaɗa kai.  "Eyh! Nan ne."  "Ki shiga ki ji yana nan? Idan yana nan ki ce masa Fahad Ta'ambo ne, wanda su ka zauna tare a jirgi daga Dubai zuwa Nigeriya, ya yi mantuwar ne a cikin jakata shine na zo kawo masa."  Tun da ya fara magana gabana yake faɗuwa har ya ƙarashe. Yana gamawa kamar wacca aka umarta na fara tafiya, ban tsaya ba sai da na shiga gidan, bayan na isar da saƙon Alhaji Hadi ya ce dani yana zuwa, na dawo na faɗa masa ya yi min godiya, amma maimakon na kama hanyar makarantar sai na dawo gida, gaba daya ji na nake wani sukuku, unguwar ta yi min faɗi, ƙamshi turarensa ne ka dai yake yawo a kwanyar kaina, sai kuma maganarsa tun daga farko hat karshe, ban manta ko kalma daya ba.  "Ki shiga ki ji yana nan? Idan yana nan ki ce masa Fahad Ta'ambo ne, wanda su ka zauna tare a jirgi daga Dubai zuwa Nigeriya, ya yi mantuwar ne a cikin jakata shine na zo kawo masa."  Abinda na fada kenan da safe bayan na buɗe idona, da sauri na daki kaina tare da faɗin.  "Rawasiya wake-up, me yake damunki ne haka?"  Miƙewa na yi tare da nufar banɗaki na wanke baki na na fito zuwa tsakar gida, sai da ƙamshin turarensa har yanzu yana yawo a hancin na,  yanayin da na ji jiya yana nan kamar yanzu yazo unguwar.  Haka kwana daya ya wuce ina jin wannan yanayin a tare da ni, kwana na biyu ya wuce, sai da na yi sati sannan na ji yanayin ya fara raguwa, sai da na ɗau tsawon wata guda ina fama, kafin manta amma kuma har lokacin kammaninsa da sunan sa suna nan a kwakwalwata, domin a kallo daya kwakwalwata ta dauƙi hoton sa, wanda ya tsaya a a zuciya. Ranar da Allah Ya nufa zan sake ganinsa ranar wata laraba da yamma, lokacin Hajiya ta aiki ni gidan wata ƙawarta a fagoji, banson zuwa fagoji kwata kwata, ni ba ma fagoji ba gaba daya ban fiya son zuwa wani waje nesa ko kusa ba. Daidai bakin titin Rasheed shekoni special hospital mashin din da nake kai  ya tsaya, me mashin ɗin ya tsaya yana duba mashin ɗin ni kuma na sauka ina jiranshi.   A jiki na naji ido na yawo a kaina baya ga matsananciyar faduwar gaba da naji. Ina kai idona bakin asibitin na ganshi tsaye ya harɗe hannusa a ka faɗa yana kallona. Da sauri na sunkuyar da kaina ƙasa ina faɗin.  "Wayyo Allah."  Dan wani irin ƙarfaffan bugu zuciyata ta yi lokacin da muka haɗa ido dashi.  "Sannunki."  Na ji muryarsa dab da ni sai dai na kasa ɗagowa, idanuna suka kai kan ƙafarsa, takalminsa ma kaɗai abun tsayawa a kalla ne.  "Kamar ke ce ta unguwarsu Alhaji Hadi ko?"  Da sauri na gyaɗa kai, tare da faɗin.  "Eyh! Ni ce."  "Lol, me kike yi anan?"  "Mashin ne ya sami matsala, amma gashinan ya gama dubawa."  Ya kalli mashin din sannan ya kalli ni.  "Kuma a wancan unguwar kike?"  Ya faɗa yana baya da hannu alamun can. Na gyaɗa kai tare da cewa.  "Eyh! Yalwawa."  "Uhm! I see."  Ya faɗa yana shafa gashin bakinsa daga tsakiya zuwa gefe sannan ya ja shi zuwa ƙasa.  "Mu tafi ko?"  Mai mashin ɗin ya faɗa, na juya zan hau mashin ɗin sai na ji ya ce.  "Na ce ki tafi?"  Ba shiri na tsaya kaina a ƙasa.  "You're eager to go, kin gaji ko?" Ya faɗa cikin wani irin yanayi na fushi, da sauri na girgiza kai sannan na ce.  "A'a, bangaji ba.... Me mashin ɗin."  Kallon me masahin ɗin ya yi sannan ya ce.  "Malam ka jira."  "Alhaji sana'a fa nake, idan na ajiyeta wasu zan ɗauka."  Hannu Ya sa a aljihu ya zari kuɗi 'yan dubu dubu da a ƙalla sun kai guda goma ko sha, ya miƙa masa. Ba shiri me mashin ɗin ya amsa tare da matsawa gefe ya zauna, a raina na ce.  'Yanzu mu dai babu yaren da muke ganewa sai na kuɗi."  "So ba zaki tambayi sunana ba?."  Ya faɗa yana kafe ni da idanun da nake jin su tamkar na zaki sabida kaifi.  "Ka yi hakuri ai naga ranan ka faɗa min."  "Ni... when?"  "Da ka ce na cewa Alhaji Hadi Fahad Ta'ambo ne."  Shiru ya yi yana kallona na kusan minti biyar sannan ya ce.  "So kin ma riƙe sunana, shine da kika ganni kika yi kamar baki sanni ba ko? Na gode."  "Ba haka ba ne, ban kula da kai ba."  Na faɗa murya ƙasa ƙasa.  "Amma ni na kula da ke?"  "Ka yi haƙuri."  "It's fine, you can go. Na gode."  Shiru kamar an shuka ni a wajen na kasa matsawa.  "You can go fa."  "Ka yi haƙuri."  "Kije kawai."  Ya faɗa yana barin wajen, sai da ya shiga cikin motarsa sannan na iya matsawa zuwa ga mai mashin ɗin, ya ɗauke ni muka ci gaba da tafiya.  Gaba ɗaya hankali na ba yaga hanya, na tafi tunanin wannan mutumin, komai na shi burgeni yake, ya iya magana. Amma abinda ya bani mamaki shine kwata kwata banji ya tambaye ni sunana ba, ko da yake mene alaƙarshi da sunana da zai tambaya, kamar daga sama na ji ana cewa.  "Mun kusa wuce jakshon ɗin fa."  Na kalli me mashin ɗin na kalli hanya, sannan na ce.  "Wannan layin zaka shiga."  ******** 08:30pm Kamar wancan lokacin na farko da na haɗu da Fahad Ta'ambo na kasa mantawa da komai na shi, to yau ma haka. Tun dawowa ta na ƙure a ɗaki ina zaune ni kaɗai ina maimaita duk wata kalma guda ɗaya da ya faɗa a cikin zuciyata.  Hajiya ce ta leƙo tare da faɗin.  "Rawasiya me kike yi a ɗaki ne, bazaki ci abinci ba ne?"  "A'a Hajiya na ci acan, duk gjiya ce wallahi ke ci na."  "Mene abin gajiya a zuwa Fagoji? Sai ka ce yau kika fara?"  "Bazaki gane ba Hajiya."  Na faɗa ina juya baya.  "Eyh, bazan gane wannan karatun sangartarba."  Ta faɗa tare da ficewa, ni dai daren nan haka na ƙarar dashi a ɗaki ina ta hango kammanin kyakyawan matashi Fahad Ta'ambo.  Washe gari ma dai da mafarkin kyakyawar fuskarsa na tashi, ni dai ban taɓa soyayya ba, amma nasan yanayin da nake ji game da Fahad na san yanayi ne na soyayya. A gurguje na yi shirin makaranta na fito tsakar gida na ɗauki abin kari na na yi, bayan na karya na amshi kuɗin makaranta wajen Alhaji na nufi makaranta.  FUD STAFF SCHOOL 11:30am.  Tun da aka fita break ban matsa ko ina ba daga kan bencina, duk ƙawayena su Fauziya Tasi'u su Malaika sun fita sun dawo amma sun tarar dani anan zaune. Malika safwan ce ta zauna kusa dani tana faɗin.  "Nana meke dumunki ne haka? Tun ɗazu kina zaune sai faman murmushi kike?"  "Murmushi?" Na faɗa da alamun tambaya.  "Au baki ma san kina murnushin ba, sai dake malamar soyayya."  Ta faɗa tana dariya, na kalleta na ga yanayin ta ko a jikinta, daman Malika irin wayayyun 'ya'yan nan ne, dan a yanzu haka ma tana da saurayi abunta, idan anyi magana sai ta ce 'idan basu yi min aure ba, jiƙani zasu yi su sha?.' A yanzu haka har cikin Malamai tana da saurayi, sabida wayewarta ma Malaika Arora ake ce ma ta.  "Ni Malaika ban faɗa wata soyayya ba."  Na faɗa bakina yana rawa, kallona ta yi sannan ta ce.  "Mai da karuwa 'yar iska."  Tana faɗin haka ta juya ta shiga sabgoginta ta barni da faman tunani.  "Ya zaayi ace na faɗa soyayya, faɗawar da har wani zai iya ganewa, ko da yake a wayewa da gogewa irinta Malika ba abun mamaki ba ne

Chapter 3 of 16