Share this page
dan tasan haka, amma ta ya zaayi na fara soyayya da mutumin da ko sunana bai ta ɓa tambaya."  Haka na yini sukuku, har washe gari ma hakan, sai da aka sake ɗaukan sati ina cikin wannan yanayin kafin na ji na dawo daidai, sai dai a cikin wannan satin fa duk ƙawaye na sun yarda da maganar Malaika kan na faɗa soyayya. Ni kam tsakanina dasu sai da ido, daga baya ne ma na fara biye musu har wata rana suka ce wai sai na zayyane musu kammanin mutumin, da na rufe idona kawai sai na ganshi ya harɗe hannu yana kallona.  Duk yadda na kai ga gaya musu cewar yadda na fasalta musu shi, haka yake a gaske sun ƙi yarda, dan daga masu cewa jaruman indiya nake fasaltawa, sai mai cewa larabawan Dubai ne, ni kam daga ranar ban sake biye musu ba.  A lissafina ranar da na cika kwana goma da haɗuwa da Fahad Ta'ambo na sake ganinsa, sai dai abun da ya yi matuƙar bani mamaki shine inda na gansa, daga can gaban gate ɗin makarantarmu, da sauri na juya baya sai dai naga idanun ƙawaye na akansa. Fauziya ta yi saurin matsowa kusa dani sannan ta ce.  "Ke Rawasiya! Wannan ai shine sak mutumin da kika fasalta mana, ko shine?"  Na gyaɗa mata kai, gaba ɗaya na rasa nutsuwa ta, kamar ko da yaushe. Da zarar ya ɗor ƙawayar idonsa a kaina, shikenan na rasa nutsuwata.  "Gaskiyya ƙarya kike Rawasiya."  Mailaka ta faɗa a saitin kunnena.  "Kina ganin yadda yake kollonta, zaki ce ƙarya ne."  Amina Aminu ta faɗa..  "Wannan ai yafi ƙarfinki Rawasiya, bama haɗi wallahi." Na ji muryar Malika ta faɗa, a take Amina Aminu ta cafe da cewa.  "Ni ban ma yarda ba, gashi dai gani nake da idona, amma na kasa gasgatawa."  "Kinsan kuwa wane ne Fahad Ta'ambo?"  Malaika ta faɗa, daidai kuma lokacin ya fara takawo kusa da mu, ni kam gaba ɗaya sai na ji maganganunsu sun tsayan a raina, ni kaina nasan tabbas wannan saurayin yafi ƙarfina, bazan taɓa samun wannan saurayin ba domin kuwa duk wani abu da ake nema ya haɗa. Kyau, kuɗi, Nasaba, gayu, ilimi da duk wani abu da 'ya mace ke nema wajen datattacen Namiji.  Gaba ɗaya daskarewa na yi na kasa motsi, kar na yaudari kaina Fahad ba tsarar aure na ba ne.  "Yau ba magana ne, kin wane tsari ni da ido kamar yau kika fara kallona?"  Ya faɗa daidai lokacin da ya iso, gaba ɗaya yau sai na rasa wannan yanayin da nake ji idan yana gabana, jikina sanyi ƙalau na ce da shi.  "Ina wuni?"  Kallona ya yi sannan ya kalli ƙawayena ya ce.  "Baki da lafiya ne?"  "A'a, ina da lafiya."  Na faɗa ina kallonsa. "Uhm."  Ya faɗa yana taɓe baki irin bai damu ba. Ganin na yi shiru kusan minti biyar, kuma ban tafi ba ya sa shi cewa.  "Ina so mu yi magana ranki ya daɗe, naga yau a saurauniyar ki kike."  Bin shi kawai na yi a baya, ƙawaye na dai suna bina da na mujiya. Har mu ka ƙarasaa bakin motarsa ina jin idanunsu akaina.  "Me yake damunki?" Ya faɗa yana kallona, girgiza kai na na yi sannan na ce.  "Bakomai"  "ƙawayenki ne?" Na ɗaga sannan na ce.  "Wai sun ce idan kai saurayi na ne yaudarata zaka yi ba zaka taɓa aurena ba. Sabida kafi ƙarfina."  "To ke me kika gani?"  Ba tare da wani lissafi ba na ce.  "Da gaske suke."  Ya yi murmushi sannan ya ce.  "Rawasiya daman ni na ce saurayinki ne?"  Na gwalalo ido waje sannan na ce.  "Kasan suna na? Aina?"  "Taambayar da na yi miki kenan?" Na girgiza kai sannan na ce.  "A'a da a'a."  "Mene a'a da a'a?"  Ya tambayeni yana kallona.  "Da ka ce tambayar da ka yi min kenan shine a'a ta farko, a'a ta biyu da ka ce daman ka ce kai saurayi na ne?"  Murmushi ya yi sannan ya ce.  "You're very funny, I love it girl."  Na yi murmushi sannan ya ce.  "Baki tambayeni me nake yi anan ba?" A raina na ce.  "Duk inda nake ganinka da na taɓa tambayarka me kake yi a wajen?"  "Sabida yau wajenki na zo shi ya sa na tambayeki."  Na ji muryarshi ta katse min tunani na.  "Shekararka nawa?" Na tsince kaina da tambayarsa, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce.  "Ashirin da shida."  Wani daɗi na ji ya ratsani, irin mijin da nake so.  "Ke fa?"  Na ji ya tambaya.  "Goma sha bakwai da rabi."  "Ko ba rabi ba?."  Ya tambaya yana dariya. "Yau na ganka da sauƙin kai, daman haka kake?"  Na tambayeshi, sai dai ya yi dariya sannan ya ce.  "Au da da zafin kai nake zuwa kenan?"  "ƙawayena bari na tafi."  Na faɗa ina nuna masa su, nan take ya haɗe rai ya dawo asalin Ta'ambo da nasani.  "Je ki."  Ya faɗa cikin wani irin amon murya, ba shiri na tsaya na kasa tafiya.  "Je ki mana."  Ya faɗa yanzu muryarsa da alamun fusata.  "Ka yi haƙuri." "What do you do? Kin nuna sun fini amfani da muhimmanci to sai me?"  Gaba ɗaya jikina ya fara rawa, duk na rikice lokaci ɗaya, bakina har rawa yake na ƙara cewa.  "Ba haka ba ne fa." Legendspen 08*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na shida     (06) Bai ko kalleni ba ya shige mota ya tafi, na kusa minti biyu a tsaye sannan na juya ga su Malaika.  “Ku zo mu tafi.”  “Wallahi Nana ban yarda saurayinki ba ne sai yanzu.”  Fauziyya ta faɗa bayan sun ƙaraso inda nake.  “Ni har yanzu ma mamaki nake, kinsan su waye familyn Ta Ambo kuwa? Kaf jihar jigawa suna cikin manyan masu kuɗi guda biyar,  ‘yan kasuwa ne na gaske masu arziƙi, duk a turai suke rayuwarsu baki ɗaya, wannan ma kina ganinshi kinsan ba rayuwar nan ba ne, gashi duk ‘ya’yan attajirai suke aure.” Tin da Malaika ta fara magana har ta dire idanuna na kanta, domin nasan gaskiyya take faɗa zalla ma kuwa.  “Idan kuwa hakane tabbas wannan yafi ƙarfinki Nana, ina baki shawarar karki ɗaurawa kanki abinda bazai ɗaure ba, kizo ki sha wahala a banza.”  Fauziyya ta faɗa tana dafa ka faɗa ta, ni basu san abinda ke damuna ba wannan ba ne, fushin da ya yi ya tafi ya barni yafi komai ɗaga min hankali.  ‘Yanzu yaushe zan sake ganinsa?’  Na tambayi kaina sai dai ba mai bani amsa, tsoro na ɗaya kar ya yi dogon fushi, fata na dai Allah Ya kawo shi da wuri, sai dai fatan ba ai amso ba dan haka aka yi sati ɗaya babu shi babu alamunsa, duk na damu gashi ni irin mutanen na ce da ba su iya faɗar damuwarsu wa wani ba, sai dai na bar abu a zuciyata ya yi ta cina, ni kam sai dai aga ina ta rama duk na zagwanye. Haka kuwa aka yi na yi ta faman rashin lafiya a tsaye babu zazzaɓi sai ciwon kai sama sama, tari da kuma ɗacin maƙwogwaro, haka na yi ta fama sati ɗaya sati biyu har sati uku, hankali Hajiya da Alhaji duka ya tashi, kowa yasan akwai abinda ke damuna amma nakasa faɗa.  Haka su Malaika ko da yaushe sai sun tambayeni saurayina, kuma a ko yaushe sai sun nusar dani cewar yafi ƙarfina, tun ban fiya sa abun a rai ba har na yardarwa kaina Fahad yafi ƙarfina, har na fara jin cewa ya gane yafi ƙarfina ne shi ya sa ya tafi bai sake zuwa ba. Abu kamar wasa Fahad ya yi wata ɗaya, ya yi wata biyu, ya yi wata uku. Ta dole na haƙura da Fahad na fara tunanin cireshi a raina, sai dai hakan ya gagara duk ranar da na fita da sa ran ganinsa nake fita, haka zan ta ganin masu kama da shi a hanya.  Wata ranar juma’a cikin wata na huɗu da rabuwarmu da shi, ranar ma daƙyar na iya fita makaranta sai da Hajiya ta yi min jan ido sannan ma na fita, ko a cikin aji ma haka Malaika ta isheni da surutu.  “Daman na faɗa miki Fahad ba tsarar aurenki ba ne, bikin Cousin brother ɗinsa ake yi yanzu haka komai a Abuja aka yi sai jiya su ka dawo Jigawa ɗaurin aure zaayi yau ɗinnan sai kuma wani event ɗin anan dutse da zaayi gobe Asabar, ‘yar gidan ministan man fetur yake aure.”  “To yanzu ni mene alaƙa da hakan?.”  Na faɗa ina kallonta, wayarta ta zaro ta shiga dubawa, tana faɗin bari ki ga. Duk cikinmu daman ita kaɗaice mai waya, duk tafi mu waye sabida gidansu tsantsar ‘yan boko ne gaske.  “Kinganshi.”  Ta faɗa tana miƙomini wayar, idanuna suka saukan akan kyakyawar fuskarsa. Yana sanye da wani baƙin men lace da aka yi masa babbar rigar, yasa baƙar hula da baƙin takalmi haka baƙin agogo, wayanda suka ƙara haska farar fatarsa.  Ji nai zuciyata ta yi wani irin bugu da ƙarfi, na yi saurin runtse idona sai ga ƙwalla zir zir. ‘Ashe haka na yi kewarsa? Ashe haka nake son sa?.’ Na shiga tambayar kaina.  “Ke mene haka? Lallai iska na wahalal da mai kayan kara, chaɓ.”  Na ji muryar Malaika na faɗa, ban ko kulata ba na miƙa mata wayarta, na kifa kaina da benci na shiga kuka a hankali marar sauti.  Ina wannan yanayin har aka tashi, na ɗakko jakata na fito banko tsaya su ba, sai dai ina fitowa bakin gate na ji ƙirjina ya fara wani irin bugu, na shiga waige waige.  “Me kuma kike dubawa ne?”  Fauziyya ta faɗa, ban ko kula ta ba nasake waigawa. Yau daga can nesa ya tsaya, dan bana iya hango fuskarsa sosai sai dai na tabbatar da shi ne, baƙaƙen kaya ne a jikinsa sai dai na yau yadi ne, kuma motar ta sa yau ma baƙa ce. Basan lokacin da na fara ɗaga ƙafafuna ba ina bin hanya zuwa inda yake sai da na daina jiyo hayaniyar ‘yan makaranta sannan na waiga baya, ashe na yi nisa ma.  Haka na ci gaba da takawa har inda yake, bansan na yi kewarsa ba sai da na ƙaraso inda yake, na yi ƙasa da kaina na fara zubar da hawaye.  “Nana! Nana ɗago mana.”  Ya faɗa cikin sassanyar muryarsa, kasa ɗagowa na yi sai da yaji shasheƙar kuka ne, sannan ya ce. “Subhanallahi! Nana kuka kuma?”  Ɗagowa na yi na kalleshi, idanuna ne suka sanar dashi halin da zuciya da gangar jikina suke ciki. A hankali ya ce.  “I’m sorry Nana, kwana biyu da haɗuwar na tafi chaina, and daman zuwan da na yi nazo ma faɗa miki tafiyar ne, last week na dawo kuma Abuja na sauka sabida bikin brother na Aliyu, jiya muka dawo nan kuma jirgin dare ne, yau ko breakfast banyi ba na tawo nan, tun 9 nake wajen nan gashi har 12:30.”  Gaba ɗaya sai na ji wa’yannan ƙwayoyin kalmomin da ya faɗa sun goge duka wani ɗaci da ɓacin raina na wattanni, kalmar da ya faɗa ta. ‘Ko breakfast banyi ba na tawo nan, tun 9 nake wajen nan gashi har 12:30.’ Ta haifar min da wani zazzafan tausayinsa a cikin zuciyata, sai na ji dama nima banyi breakfast ba na tawo.  “Nana! Ki yi haƙuri dan Allah, baran sake irin haka ba.”  Sai da na ja numfashi sannan na ce.  “Na yi ta rashin lafiya sosai, har da low Bp.”  Ya gwalalo ido waje cike fa mamaki ya ce.  “Low Bp Nana? Akan me?”  “Ka tafi kana ta fushi da ni, gash bansake ganinka ba wajen kwana ɗari da uku.”  “Nana duk akaina haka? Ki yi haƙuri bansan zaki damu ba kwata kwata wallahi.”  “Uhm.” Na faɗa tare da niyar waigawa baya, sai dai da sauri na dakatar da hakan sabida bana son ma ganin ko sunan ko ba sa nan dan duk halin da na shiga sune suka ja min.  “Kawayenki?”  Ya tambaya, da sauri na girgiza kai sannan na ce.  “A’a basu ba?.”  Ya yi murmushi sannan ya ce.  “Suna nan tsaye.”  “Uhm su yi ta tsayawar, kasan me suke cewa?”  “A’a sai kin faɗa.” “Wai daman kaima kasan ba tsarana ba ne, shi ya sa ka daina zuwa.”  “Nana bana son sake jin wannan maganar abarta dan Allah.”  “Tom.” Na faɗa tare da fara wasa da yatsuna.  “Kizo na kaiki gida.”  “Yanzu ka dawo daga can ɗin gaba ɗaya kenan?” “A’a, zanyi one week anan sannan na je na yi 3weeks acan, shikenan.”  Tun daga wannan ranar kullum sai Fahad Ta’ambo ya zo wajena, soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanina da shi ba tare da kowa ya sani a gida ba, har ya yi satinsa ya koma.  Bayan tafiyarshi ma, munyi waya sau ɗaya a wayar Hajiya da na ɗauka na kirashi, sai kuma wata rana da na je gidan Yaya Radiya.  Ranar da ya cika sati uku cif ranar ya dawo kuwa, da na kirashi a wayar Hajiya ya ce dani ya dawo kuma zai zo har ƙofar gidanmu. Tun da ya sanar da na shiga tashin hankali, dan ko a hirar mu ta ƙarshe da Alhaji sai da ya tunasar dani akan course ɗin da yake so na karanta da kuma amfaninsa.  Afujajan na fice gidansu Amina Aminu, dan a cikin ƙwayenmu ta ɗan fi sirri, Fauziyya ma bata da matsala sai da yawan surutu marar amfani. Tana zaune a tsakar gida tana daka na shigo. Kallo ɗaya ta yi min ta gane ba lafiya ba.  “Nana me ya faru?”  “Muje soro dan Allah.”  Na faɗa ina fitowa, ta tashi ta biyo bayana.  “Amin wai Fahad ne zai zo kuma wai gidanmu.”  Na faɗa kamar zanyi kuka.  “To ke mene a ciki, ba son shi kike ba kuma duk wanda ya ce zai zo gidanku ai aure ne zai kawo shi, ji dai Abdul ɗin Fauziyya yanzu har magana ta tsaya.” “Ba haka ba Amina, kinsan ko ranan Alhaji ya ce da ni so yake na karanci ko Mass communication ko Law.”  “Kai Nana, Fahad ai me ilimi ne kuma da wayewa, kina tunanin zai iya hanaki karatun boko? Gaskiyya ba alama.”  “Nufinki zai ce zai jira nagama karatu? Mussamam Law wajen shekara goma.”  “Alhaji ba zai iya bari ki yi karatun a gidan mijinki ba, yanzu fa ke damuwarki kawai Alhaji ne, kuma idan kika matsa tsaf zai barki ki yi a gidan mijinki.”  Daga haka tai ta bani shawarwari kala kala, daga nan na koma gida na fara shiri. Ina zaune cikin ɗaki Hajiya ta shigo.  “Hajiya ina zaki?”  Na faɗa ganin irin shirin da ta yi.  “Ki shirya ki taso muje, Hajjace zata tsallaka titi mashin ya bugeta ta yi tsagewar ƙashi.”  “Allah Ya bata lafiya, amma ba inda zani.”  Na faɗa ina kwanciya.  “Bazaki tashi ba?”  “Uhm”  Na faɗa tare da rufe idona, haka ta ƙaraci faɗan ta ta fita, tana fita na miƙe tsaye tare da daka uban tsalle ina faɗin.  “Alhamdu Lillah.”  Ban ɓata lokaci ba na hau shiryawa, ƙarfe 05:30 daidai na ji yaro ya shigo wai ana kiran Nana a waje. A raina na ce. ‘Yanzu da Hajiya tana nan haka zaiyi mini chaɓ?.’  Ina shirin fita na ga Yaya Ridwan ya fito, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai ya fice. Nasan dai bazai taɓa yi masa magana ba dan ba halinsa ba ne, amma kallon da ya yi min tabbas ya bani tsoro.  Da yake gidan namu yana da girman compound kafin ka kai ga shiga cikin gidan ya sa na sauke anan, wajen yana da faɗi dan har mota biyu zasu iya tsayawa.  Tun da mike tsaye yake ƙare min kallo sai can ya ce.  “Na ga ma fa ke yarinya ce, anya za a aurar dake yanzu?.”  Na yo dariya sannan na ce.  “To ka jira na girma kawai, kafin nan na ƙarasa karatu na.”  “Ina bazai yu ba, ki girma kuma? Ai ba amfani.”  “Mene ba amfani?”  “Girman mana, bakisan mace tana ƙarama tafi daɗin zama ba, shi kanshi miji yafi son ya aureki kina ƙarama.”  Na yi dariya sannan na ce.  “Alhaji dai ya ce Karatu zanyi.”  “Dagaske ko wasa?”  Ya faɗa da alamar damuwa, ni kuma kai tsaye na faɗa masa gaskiyya.  “Kuma ba zai taɓa bari ki yi aure ba, sai kinyi karatun?”  “A’a zai iya bari na na yi mana idan mijin zai barni.”  “Nana!”  Ya kira sunana cikin wani irin yanayi.  “Na’am!”  “Nana, ina sonki dagaske, kuma aurenki nake son yi, bazan iya rayuwa ina kallonki a haka ba a matsayin matata ba, Nana ina da mugun kishi akanki sosai wallahi.”  Gaba ɗaya na ji tsigar jikina ta tashi, daidai lokacin kuma Yaya Ridwan ya shigo, kallo ɗaya ya yi mana ya ɗauke kai ya shige ciki.  “Nana wannam yayanki ne?”  “Eyh shi nake bi.”  “Okay, amma baya ganin mutane ne?”  Sai da na yi dariya sannan na ce.  “Ai haka yake, shi ko Abban mu ya gani a hanya ko Hajiya zai iya ɗauke kai.”  “Uhm.”  Ya faɗa yana zaro wayarsa, sannan ya ce.  “To yanzu mene mafita?”  “Game da me?”  “Kin manta?”  “A’a ban manta ba, amma maganganun da muka yi da yawa bansan akan wacce kake magana ba.”  “Zancen aure, Nana kina sona?”  Wani irin abu na ji a zuciyata, “wai ina sonsa?”  “Eyh Nana?”  Sai da na ɗago na kalleshi sannan na ce.  “Mugun so ma?”  Ya yi dariya sannan ya ce.  “Wane iri ne mugun son?”  Ƙasa na yi da kaina na fara wasa da yatsuna.  “Nana akwai wata matsala a gida, bansan ta yadda zan samu iyayena da maganar ina sonki ba, sabida mu family ɗin mu gaba ɗaya Rich Family suke aure.”  Gabana ne ya faɗi, maganarsu Malaika ta fito da suke cewa yafi ƙarfina, a Royal family suke aure ko ‘ya’yan manya.  “Nana wannan ba matsala ba ne, ni zanyi ƙoƙari da gida kema ina so ki yi koƙari anaku gidan ki tabbatar Abbanku ya ce zai miki aure.”  Shiru na yi gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, ta ina zan fara tunkarar Abba da zancen ya yi min aure?  “Kinyi shiru, wannam fa aiki ne babba muka ɗauka Nana, kina sona ina sonki, kuma kowa akwai matsala a ɓangarensa, naki ɓangaren ba yanzu za su yi miki aure ba, nawa ɓangaren ‘ya’yan masu kuɗi suke su.”  “Yanzu ni ta ina zan fara, wannan aikin babbane.” Na faɗa kamar zanyi kuka.  “Ta ina da zan fara, look Nana idan bakya sona ne ki fito ki faɗan.”  “Ina sonka mana.”  “Banga alama ba.”  Ya faɗa tare da kaɗa kai zai fice.  “Ka yi haƙuri dan Allah, zan yi musu magana Allah.” Banza ya yi ya sa kai ya fice.  “Shikenan na sake ɓata masa rai.”  Na faɗa tare da juyowa idanuna suka faɗa cikin na Yaya Ridwan, yana tsaye yana kallona.  Legendspen 08129553971 129*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na bakwai     (07) A hankali na shiga takawa zuwa cikin gidan, yana tsaye yana kallona har na shige, kamar daga sama na ji muryarsa.  “Wane wannan?”  Shiru na yi bance ko ƙala ba, a fusace ya sake magana.  “Ba dake nake ba?”  Bakina na rawa na ce.  “Saurayina ne?”  Ya yi dariya sannan ya ce.  “Ba shine Sardauna ba? Fahad Ta ambo.”  “Fahad Ta ambo.”  Na faɗa kaina a ƙasa.  “Nana.”  Ya kira sunana amma yanzu muryarshi a hankali, na ɗago kai na kalleshi.  “Zo nan?”  Ya faɗa yana nuna kusa dashi, kamar mai ciwon jiki haka na taka na je.  “Kinsan waye shi? Su ɗin masu kuɗi ne sosai kuma kinsan duk irin waɗan nan masu kuɗin ba wani kirki ba ne dasu, kaɗan ne masu mutunci.”  “Nasani.”  Na faɗa a hankali, ya kalleni sannan ya ce.  “Nana ki sani kefa macece, rayuwarki tana da daraja ga iyayenki da ‘yan uwanki, ba wai dan baku da kuɗi yana nufin ku ɗin baku da daraja ba, nasani muna cikin wani zamani wanda duk mai wani abu shine mutum, amma duk da haka kada ka ta ɓa bari darajarka ta ragu ko ki nuna baki da ita, karki ta ɓa sa wa ranki alfarma zai yi miki ko yake yi miki, ke macece kuma mai daraja. Dan haka ka da nasake ganin abinda ya faru yanzu ya faru.” Yana faɗin haka ya shige ɗaki, ya barni ina faman tunani, me ya gani? Me yake magana akai?.  Abu kamar wasa Fahad shiru, sati ɗaya sati biyu, idan na kirashi a wayar Hajiya ba ya ɗagawa, ta Malaika kam daman ya ja min kunne ya ce a wayar Hajiya kawai ya lamunce na kirashi.  Sai da aka yi sati uku baya ɗaga wayata kuma ba ya kirana, duk na bi na damu kuma na yi alƙwarin zanyi masa biyayya akan komai ya sani, tun da harshi ya ɗauki jahadin yi wa iyayensa magana akan yana son auren wacca ba ta kai ba, ni to me ya sa bazanyi ba.  Wata ranar laraba da yamma ina zaune a ɗaki na ɗauki wayar Hajiya na sake gwada lambarsa, ina kira ya katse ya kirani. Na ji wani mugun daɗi a raina, ina ɗagawa ya ce da ni.  “Ina bayan gidanku.”  Ba shiri na miƙi na zura hijabi na yi waje, Hajiya na tsakar gida tana kaɗa miya na ce da ita.  “Zani gidansu Amina.”  “Da yamman nan?”  “Eyh.” Ina faɗin haka na fice zuwa bayan layi, yana jingine jikin farar motarsa, yana sanye da light blue ɗin shadda, ina ganin fuskarsa na ji wani sanyi ya mamaye zuciyata, wata irin nutsuwa ta shigeni, duk wata fargabar da nake ji ta tafi.  “Yanzu ma kin daina damuwa idan ban nemeki ba.” Ya faɗa yana ƙare min kallo.  “Waya faɗa ma, wallahi na damu sosai da sosai.” “Ban yarda ba, gashinan har wata ƙiba kika yi.” “Ƙiba kuma?”  “Eyh, ya maganar mu? Me kika yanke?”  “Zanyi magana da Alhaji ta yadda zai fahimta.”  “Good girl.”  Ya faɗa yana buɗe motarsa, ya ɗauko leda ya miƙamin. Hannu nasa na amsa sannan na ce.  “Na mene?”  “Naki ne, na yi magana da Daddy ya amince amma Mom ce abun sai addu’a.”  Wani irin tausayinsa na ji ya ratsani, nasan irin wannan abun tabbas da wahala.  “Allah Ya sa ta amince itama.”  “Nana na sha wahala akan lamarinki, sai na ji kamar zan haƙura sai na ji bazan iya ba, amma ke  babu ruwanki ɓata min rai kawai kike, maimakon ki nuna sakayyar soyayya amma naga babu abinda kike so sai ɓacin raina.”  A tsorace na ce.  “Ya zaayi naso ɓacin ranka?”  “Gashi ina gani.”  Da irin waɗannan abubuwan Fahad ya dinga amfani yana cusa min tausayinsa da wata iriyar soyayyarsa mai girma, wanda a kullum gani nake yana shan wahala a kaina, sai da fa na kasa tarar Alhaji ko Hajiya da maganar, duk son da nakewa Fahad bana jin ya kai tausayin da nake yi wa Alhaji ba.  Shi kuma a kullum faɗa min irin tashin hankali da suke yi da mahaifiyarsa da ‘yan uwansa a kaina, har cewa ya yi dani ya daina shiga sabgar sister ɗinshi, a ranar na yanke shawarar tunkarar Alhaji akan maganar.  09:15pm.  Alhaji na zaune a ɗakinsa ya bayan ya yi wanka yana sauraren radio na shigo cikin ɗakin.  “Barka da hutawa Alhaji.”  “Nana barka dai, akwai abinda kike buƙata ne? Ko kin shirya sanar dani damuwar da na ce tana damunki kike ɓoyewa.” Gyaɗa kai na yi sannan na fara magana cikin rawar baki.  “Alhaji daman.. daman wani ne..”  Alhaji irin mutanen nan ne masu sauraron mutane, zai iya kwashe awa guda yana saurarenka ba zai katse ka ba, sannan kuma ba zai yanke ma hukuncin ba har sai ka kammala.  “Wani ne.. tun da daɗewa ya ce wai yana so ya turo iyayensa wajenka.”  Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce.  “Su yi mini me?”  “Wai yana sona zai aureni, kuma na faɗa masa kai bazaka aurar dani ba sai na yi karatu me zurfi na zama maaikaciya, ya ce wai ya ji ya gani zai barni na yi karatu duk wani waje da nake so.”  “Shi ɗin waye?”  “Sunansa Fahad Ta ambo.”  Wani murmushi Alhaji ya ƙarayi sannan ya ce.  “To ke me kika yanke, auren ko karatu Nana?”  Na yi shiru na rasa me zance. Allah Ya sani ina son Fahad ina tausayin halin da yake ciki a kaina, kuma bana son rasa shi, sannan kuma ina son cika burin mahaifina, amma kuma abu guda ɗaya da nake gani shine auren tun da Fahad zai barni na ci gaba da karatuna, domin a maganar mu ta ƙarshe da shi ya ce da ni.  ‘Idan kika ga zaiƙi sai ki faɗa masa ni zan barki ki ci gaba da karatun naki.’  “Nana”  Alhaji ya kira suna na.  “Na baki kwana biyu kije ki yi shawara, duk hukuncin da kika yanke zan amsa tare da nawa sharaɗin akai.”  “Na gode Alhaji.”  Na faɗa tare da tashi na fice, ko da na shiga ɗaki na kwanta abubuwa suka yi ta faɗomin a rai, na saƙa wancan na kwance wancan.  “Kalli su Yaya Radiya, da Rumaisa sunyi aure kuma suna cikin rufin asiri, ga Rumaisa nan ma ta koma makaranta tana karantar harkar lafiya, ke me kike jira zaki zauna wani zama idan kika gama karatun girma ya kama ki tsaf sai ki rasa mijin auren.”  Zancen zucin da na wayi gari da shi kenan, haka na yi ta abubuwa komai sukuku, dan ma yanzu ba makaranta muke zuwa ba WAEC zamu fara nan da sati biyu, shi ya sa bamu cika wani zuwa ba. Bayan Alhaji ya fita na shirya na lallaɓa Hajiya akan ina son zuwa gidan Yaya Rumaisa da Yaya Radiya duka a rana ɗaya.  “Wai me zakije ki yi musu duka su biyun a rana ɗaya?” Hajiya ta tambaya cike da mamaki, ganin tana neman hanane ya sa na ce.  “Alhaji ne fa ya ce na je dukkansu mu yi magana dasu.”  Kuɗi ta ɗauka

Chapter 4 of 16