Share this page
ta bani tare da cewa.  “Kuma karki yi yamma.”  Ta gidan Yaya Rumaisa na fara, tun da shi yafi nisa, akan gidan Yaya Radiya. Shi ya sa na fara zuwa gidan Yaya Rumaisa, yanayin da na sameta ya yi matuƙar burgeni, ta yi ƙiba abunta duk da karatun da take yi ga yaranta kyawawa guda biyu Afra da Affan. Bayan mun gaisa ne na kalleta sannan na ce.  “Yaya shawara nazo nema wajenki.”  “Ina saurarenki.”  Sai da na ɗan yi jim sannan na ce.  “Nasami Miji kuma dagaske aure na yake so ya yi, sannan ya yi min alƙwarin bari na na ci gaba da karatu da nuna masa Alhaji yana son karatun.”  “Rawasiya, kinyi magana da Alhaji.”  “Na yi, shi ya ce na yi shawara.”  Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta kalli ni cikin idanu tare da kamo hannuna, sannan ta numfasa ta fara magana cike da nutsuwa.  “Nana zan gaya miki abubuwan da suke cikin aure na daɗi da rashin daɗi, idan na faɗa miki sai ki yi tunani da kanki, ki ga wanne kika zaɓa.”  “Tom Yaya.”  “Nana, aure ba kawai canza gida ba ne ko samun wanda zai riƙa lura da ke. Aure ibada ne, kuma makaranta ce da ba a yaye ɗalibi har sai mutuwa ta raba. Idan kika ga mace a cikin jin daɗin gidam aure, to dole akwai matakan da ta bi waɗanda suka kai ta ga wannan matsayin jindaɗin. Nana abinda zaki fara sani a farkom farko shine, mene ne Aure kuma yaya Rayuwarsa take? Aure haɗaka ce ta rayuka biyu. Manzon Allah (SAW) ya ce a cikin Hadisin Al-Baihaqi Idan bawa ya yi aure, to tabbas ya cika rabin addininsa.... Don haka, rayuwar aure tana buƙatar haƙuri da juriya. Za ki ga daɗi, za ki ga wuya. Amma mabuɗin shi ne Biyayya da Fahimta. Sannan kisani akwai Abubuwan da ake so Mace mai aure ta yi, duk da suna da yawa amma bari na baki wasu daga ciki. Nana na farko akwai Biyayya. Ki sani Nana, biyayyar miji tana kai mace Aljanna. Amma fa muddin bai sanya ki saɓon Allah ba. Na biyu akwai Kwalliya da Tsafta, Nana ki zama kullum idon mijinki yana ganin abin da zai faru da shi, hancinsa ya riƙa shaƙar ƙamshi mai daɗi. Sannan kuma akwai riƙe sirri. Kada ki yarda sirrin gidanki ya fita waje, koda ga mu ‘yan uwanki ne, muddin ba neman shawara ta lalura ba ne. Bayan wayannan akwai abubuwan da ba a so Mace ta yi. Misali Gasar Iko, Kada ki riƙa nuna wa mijinki ke ma kina da iko kamar sa. Shi ne shugaban gida, don haka ki ba shi matsayinsa. Sannan Yawan ƙorafi Kada ki zama mace mai yawan gunaguni a kan kowane ƙaramin abu. Sai kuma wani abu da muke yawan yi shine ƙaryata Alkhairi. Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa yawancin mata suna shiga wuta saboda rashin godiya ga mazajensu. Don haka, ko kaɗan ne ya yi miki, ki ce 'Na gode'." Ta ɗago ta kalleni yadda jikina ya yi sanyi, sannan ta ce.  “Nana aure kala biyu ne, ko na ce zaman aure kala biyu ne, na farko akwai farin cikin aure idan aka yi dace. Nana, idan kika samu miji na gari, miji mai tsoron Allah kamar nawa, to za ki ji kamar kina Aljanna a duniya. Za ki samu abokin shawara, wanda zai kiyaye miki mutuncinki, ya kare miki rayuwarki, kuma ya zama silar ƙarin kusancinki da Allah. Za ki ji wani sanyi a zuciyarki wanda ba shi da misali. Na biyun kuma shine akasin haka Idan ba a yi dace ba, Idan kuma aka samu rashin da ce wanda Allah Ya kare mu, to aure yakan koma kurkuku. Idan miji ya zama mara tsoron Allah, mai son kansa kawai, to zai riƙa amfani da ikon da Allah ya ba shi yana zaluntar mace. Zai iya raba ta da mutuncinta, ya raba ta da danginta, ya kuma mayar da ita tamkar baiwa a gidansa. Shi ya sa nake ba ki shawara Nana; Kada ki yi gaggawar aure don kawai kina son yin sa, ki yi shi don kin samu wanda ya dace, kuma ki tabbatar ba za ki daina karatun ki ba domin ilimi shi ne gatanki." Jikina ya yi sanyi, ya mutu baki ɗaya. Tabbas duk wata shawara da nake nema nasame ta wajen Yaya Rumaisa, kuma dole na zauna na yi zurfun tunani akai sosai da sosai.  “Nana karki yanke hukunci cikin gaggawa, ki sami lokaco ki nutsu, ki duba halayen saurayin naki Nana ki ga nagartacce ne ko akasin haka.”  “Shikenan Yaya Na gode sosai.”  Daga nan na yi mata sallama na wuce gida, ban ma je gidan Yaya Radiya ba, ko da Hajiya ta tambayi ya na dawo da wuri sai na ce da ita.  “Iya gidan Yaya Rumaisa na je.”  Da ta cika ni da tambayar ya take ya gidan, kawai na tashi ma shige ɗaki. Kwata kwata ma bana son magana, so nake na nutsu na saurari zuciyata me take ce min, me ta hanga a tare da Fahad, sai dai fa ko mene ina matuƙar ƙaunar Fahad, rabuwa da shi da wuya.  Legendpen 08129553971 553*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na takwas     (08) Har dare ban iya ce da kowa komai ba, shiru kamar wacca ba ta da lafiya. Haka na kwana ina faman tunani har washe gari, gaba ɗaya ba mu haɗu da Alhaji ba shima kuma bai neme ni ba, har zuwa yamma lokacim da nasan Sardauna zai zo, Hijabi kawai na sanya na fita dan bana jin zan iya wata kwalliya a yanayin da nake, sai dai tambayar da nake yi wa kaina. ‘Wai shin me ya dame ni?.’  Kallo ɗaya Sardauna ya yi min ya gane yanayin da nake ciki, tambayar farko da ya yi min.  “Abban bai amince ba ne?.”  “A’a ya ce na je na yi tunani akan aure ko karatu?”  “To Nana me kike jira? Kinsan abinda na yi fama da shi yanzu kafin na fito?”  A hankali na buɗe baki na ce.  “Jiya da daddare muka yi maganar da shi, jira nake ya dawo na ce mai na amince.”  Ya yi wani murmushi sannan ya ce.  “Ko ke fa Hon.”  Nima na yi murmushi.  “Kinsan sunana?”  Na ɗago kai na kalleshi, ya gyaɗa mun kai.  “Wane suna?”  “Ban taɓa ji kin kira ba, shi ya sa na tambaya ko kin sani?”  Sai da na yi murmushi sannan na ce.  “Ya zaayi na kira sunan ka, ai babu ladabi.”  “To ai akwai sunan da nake so ki dinga faɗan.”  “Wannene?”  “SARDAUNA!” Har cikin raina na ji daɗin sunan, sai da na maimaita a raina sannan na ce.  “Sunan ya yi daɗi.”  “Ina som sunan &akata ce ta samin shi, shi ya sa na ce shine sunan da mata zata dinga kira na, kuma a yanzu naga komai ya kusa kammala, shi ya sa na faɗa miki dan nima Mom ta fara amincewa.”  “Kai Alhamdulillah.”  Na faɗa a fili, shi kuma ya ce.  “Yanzu saura ke da Abba.”  Daga nan muka ɗan taɓa hira sannan ya tafi, abu ɗaya da na kasa sabawa da shi, shine duk sansa Sardauna ya zo wajena zai tafi sai na ji ba daɗi, nifa ko ba zamuyi magana ba ya dinga kallona da ido kaɗai ina kallonsa abun farin ciki ne. Daga nan gidansu Amina na shiga, abun mamaki na tarar da Fauziyya da Malaika duka a gidan.  “Da banzo ba da ba zama a nemeni ba kenan?” Na faɗa ina kallonsu.  “To banza mun zo gidan naku aka ce kin fita, sai da muka zo Amina ta ce wai Fahad ne ya zo.”  “Eyh daga can nake.”  Na faɗa ina zama.  “Dagaske dai auren naki zai yi?”  Fauziyya ta tambaya, na kalleta sannan na ce.  “Eyh wallahi, a yanzu ma ‘yan gidansu so suke su zo, Alhaji ne har yanzu bai gama amincewa ba.”  “Kai ma sha Allah, muna da shagali a gabanmu, amma ya zancen karatunki?”  Amina ta tambaya, kafin na bata amsa Malaika ta bata amsa da cewa.  “Ke wai kin san gidan da zata shiga, to ƙila ma a ƙasar waje zata ƙarashe karatun na ta.”  “Kai Mailaka! Wai masu kuɗin gaske ne?”  Amina ta tambayeta.  “Wanne masu kuɗi kika sani kaf Jigawa?”  “Gidan gwamna.” Amina ta bata amsa.  “Ai gwamna kuɗin jama’a ne, wannan magana ake kan masu kuɗin kan su, yarinya kin yi da ce za ki shiga cikin manyan mata masu aji.”  Ni dai jinsu nake har suka kammala hirar, na dawo gida. A bakin ƙofa na ga Yaya Ridwan yana kallona, ban kai ga shiga gidan ba na ji muryarsa na faɗin.  “Na ƙara ganin kin tsaya da wani ɗan iskan sai na ci uwarki.”  Daga haka ya shige nima na shige ciki, sai dare sannan Alhaji ya dawo, sai da na jira ya kammala komai ya shiga ciki sannan na shiga ɗakin na sa.  “Alhaji Barka da dare.”  “Barka dai Nana.”  Ya amsa yana saurarena, sai dai na yu shiru na kasa magana.  “Nana ya aka yi? Kin yi shwarar ne?”  Na gyaɗa kai a hankali, ba tare da na yi maganar ba.  “Faɗi mana, ki yi magana ina sauraren kinji.”  “Al Haji.. da ma.. Daman Alhaji na gama ne.”  Na faɗa a rarrabe, ya ɗago kai ya kalleni sannan ya mayar da kansa ga abinda yake.  “Kinga me?”  A hankali na ce.  “Shwarar.”  Muryar na ba ta fito sasai ba.  “Tom me kika yanke, ina saurare.”  “Auren.”  Ya ɗago kai ya kalleni kusan minti biyar sannan ya mai da kai ƙasa.  “Wannan ita ce shawarar taki?”  “Eyh Abba.”  Abba ya sauke numfashi bayan ya gama sauraro na, ya kalle ni da idanuwan da suka nuna damuwa amma kuma cike da soyayya, sannan ya fara magana "Nana, na ji abin da kika zaɓa. Kuma a matsayina na mahaifinki, ba zan taɓa tilasta miki abin da zuciyarki ba ta so ba, domin aure ya fi ƙarfin dole. To amma, kafin mu kai ga mataki na gaba, akwai wasu abubuwa da nake so ki sani, kuma akwai sharuɗɗan da zan gina aurenki a kansu nasan kinsan Aure, Nana, ba wasa ba ne. Mutuncinki shi ne mabuɗin darajarki a gidan miji. Ina so ki sani cewa kowace mace ita ce take gina mutuncinta ko ta ruguza shi. Ki zama mai hakuri, mai biyayya, kuma mai kiyaye sirrin mijinki. Amma kuma, ki sani cewa Allah ya ba ki daraja a matsayinki na mace, kada ki bari wani ya take miki mutunci. Kamar yadda kika sani, burina ne ki karanta ilimin likitanci ko wani fanni da zai amfani al'umma. Tunda kin zaɓi aure yanzu, to zan bar ki ki yi auren, amma a kan sharɗi guda Lallai sai kin ci gaba da karatunki a gidan mijinki. Ba zan yarda ilimin ki ya tsaya a nan ba. Ilimi shi ne gatanki, shi ne haskenki, kuma shi ne zai ba ki ‘yanci koda bayan raina. Sannan, ina so in ga wanda ya sace zuciyar ‘yata har ta zaɓi barin karatu a yanzu. Dole ne in ganshi, in tattauna da shi, kuma in fahimci wane ne shi, daga wane gida yake, kuma wane irin hali yake da shi. Ba zan ba da ke ga mutumin da ban yarda da asalin sa da addininsa ba." Gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, soyayyar da mahaifina yake yi min babba ce ba ƙarama ba, kuma in sha Allahi sai na cika masa wannan burin nasa, nasan Sardauna yana sona kuma zai so abinda nake so.  “Abba na yi maka alkwarin zan tsaya kai da fata akan karatuna, zan zama ‘yar da zaka yi alfahari da ita.”  Na faɗa muryata tana fitar da wani irin sauti, kamar mai kuka. Alhaji ya yi murmushi sannan ya ce.  “A kullum ina alfahari dake da dukkan ‘yan uwanki Nana, Allah Ya yi miki albarka.” “Amin Abba.”  Na faɗa tare da ta shi na fice, ko da naje ɗaki ban wani iya bacci sosai ba, bawai ina cikin yanayin farin ciki ba ne da amincewar Abba ba, ba wai kuma ina cikin damuwa ba ne, kawai wata iriyar soyayyar Alhaji ce ke ratsa zuciyata, ina son Abbana so mai girma. Washe gari.  A wayar Hajiya na kira Sardauna na faɗa masa yadda muka yi da Alhaji, maimakon naji farin ciki a muryar Sardauna sai tsoro.  “Hon ina jin tsora gaskiyya, ba zan iya tunkararsa ba sai dai kawai na turu.”  “Alhaji fa ba shi da matsala, kuma ba wani abu zai ce da kai ba kawai tattaunawa zakuyi ku yi hira da shi.”  “A’a Honey pls.”  Nasan dole aiki ne babba akaina, na lallaɓa Sardauna ya zo wajen Alhaji, cikin sanyin murya na ce dashi.  “Ko zaka zo yau mu haɗu.”  “So kike na zo ki haɗani da shi?”  “A’a magana zamu yi da kai.”  “Tam zan zo.”  Ya faɗa tare da kashe wayar, haka na mayarwa da Hajiya a barta, ni dai gaba ɗaya wani sukuku haka nake, tunanin yadda zan fara fahimtar da Sardauna muhimmamcin zuwa wajen Alhaji kawai nake.  Ra’is ne ya buɗe labulen ɗakin.  “Wai daman baki mutu ba?”   Na watsa mai harara sannan na ce.  “Sakar mini labule ka fita.”  “Naƙiya, wai me kike yi a ɗaki kwana biyu?”  “Ra’is ka sakar min labule ka fita kafin na yi ma rashin mutunci.”  “Karki fasa.”  Ya faɗa yana shigowa ya zauna gefen gadon ɗakin.  “Wai na ji aure zaki yi?”  A razane na juyo na kalleshi sannan na ce.  “Waya faɗa maka?” “Duk abinda ake ɓoyewa ai mun sani, mun yi waya da Yaya Rumaisa ta faɗan, sannan ta ce na zo na baki shawara.”  Shiru na yi ban ce komai ba, shi kuma ya ɗora da cewa.  “Wallahi indai saurayinki yana sonki, kin yarda da soyayyar da yake miki, to ki yi aurenki me zaki zauna ki yi a gidan? Ke mace fa, ba ‘yar zama ba ce, akwai lokacin da mace take samin samari cike har da na aure, da ta yi wasa ta ƙara girma shikenan zasu tsiyaye kamar hawaye su tafi.”  Kallon Ra’is na yi a raina na ce.  “Shi kuma kalal tashi shawarar kenan.” A fili kuma na ce.  “Alhaji yana so na yi karatu”  “To ai a gidan mijin ma zaki iya ci gaba da abinki, wannan fa a ganina ba matsala ba ce.”  Haka Ra’is ya yi ta bani nasa shawarwarin, bayan ya tafi na zauna na haɗe komai na cakuɗa a kwalwalwata, na yi ta faman kwashewa da ɗebewa har zuwa yamma.  Wajen ƙarfe biyar na tashi na fito tsakar gida lokacin Hajiya na shara, kallona ta yi sannan ta ce.  “Kwana biyu iskancin zaman ɗaki kika ɗaukarwa kanki ko Nana?”  “A’a Hajiya, bani da lafiya ne fa.” “Baki da lafiya shine bazaki sanar ba.”  Yaya Ridwan ne ya leƙo daga ɗakinsa sannan ya ce.  “Hajiya ƙyaleta kawai.”  Ni a raina na rasa me yasa Yaya Ridwan baya sona da Sardauna, ina tuna lokacin bikin su Yaya Radiya duk da bai yi magana ba amma yanayinsa ya nuna yana farin ciki da hakan, amma ni ya fito ya nuna baya farin ciki da hakan, dan ko jiya da daddare sai da ya sake min magana akan Sardauna.  Wayar Hajiya na ɗauka na shiga ɗaki, ina shiga na kira wayar Sardauna, ya katse bai ɗaga ba can kuma ya yi min text.  “Ki fito.” Abinda ya rubuta kenan, na rasa me yasa duk lokacin da Sardauna ya shigo unguwarmu sai na ji a jikina.  “Ina zaki ke da ba lafiya?” Hajiya ta faɗa ganin ina shirin fita. “Abu zan amso a waje.”  “Wajen wa a waje?” “Ɗan ajinmu ne.”  Sai da ta kalleni sossi sannan ta ce.  “Idan kinga dama ki zauna a wajen.” Sannan ta ci gaba da abunda take, ni kuma na fice.  Yau a barandarmu na sameshi, ya tsaya ya harɗe hannunsa a ka faɗa. Kamar ko yaushe dai cikin kyakyawar shiga yake.  “Ke baki damu bama da kiran da Alhajin yake min ko?”  Abinda ya fara faɗa kenan, bayan na ƙaraso inda yake. Na rasa me ya sa Sardauna yake ce min ni bandamu ba, ko so yake ya ga damuwar ƙarara a fuskata?  “Ba fa wani abu ba ne Allah.”  Na faɗa bayan na ƙaraso inda yake.  “Nana ajikina nake jin Abba bazai ban aurenki ba, ni dai idan kina da wata hanyar kawai ki faɗan.” “Wace irim hanya?”  “Wacca zamu bi a fasa zuwa wajensa.”  “Maganar makaranta kawai zai yi ma fa, Alhaji ba zai janye maganar karatu ba fa, kuma Alhaji idan yana ce akan magana babu mai sauye sai Hajjansa ita kaɗai.”  “Wace Hajja?”  “Kakarmu fa.”  “Aina take?”  “Dutse Gadawur.”  “Kina ganin ba zanje na gaishe ta ba yau, sai na ce mata nine saurayinki?”  Taɓe baki na yi tare da cewa.  “Ni ban wani cika shiga al’amuranta ba, hasali ma ba ta son mu.”  Murmushi ya yi sannan ya ce.  “Zata so ku, bani address kawai.”  Ba shi cikakken address na yi na gidan, bai wani jima ba ya tafi, na shiga gida. Ina kallon wani irin kallo da Yaya Ridwan yake min, ni narasa na mene haka?.  Ko da dare da Alhaji ya dawo bai yi min maganar ba, sai ma sanar damu da ya yi ansa bikin Isah Nadabo sati biyu, ya sami mata a jihar kano.  Na ji daɗi sosai a raina tare da yi masa fatan alheri, nasan dai bikine zamu sha dan a gidanmu zaayi komai daga farko har ƙarshe, dan iyayensa  ba anan suke ba ‘yan Gumel ne.  Kwata kwata ba muyi magana da Sardauna ba har washe gari, sai da safe ya kirani muka sha soyayya kuma a yanayinssa babu wannan fargabar, nima kuma ban tambayeshi ba.  Wajen ƙarfe tara da rabi, ina zaune bakin rariya ina wanke wanke, Hajiya na ɗakin Alhaji yana shiryawa, Ra’is kuma na sharar tsakar gida muka jiyo baloƙoƙon Hajja.  Gabana ya yanke ya faɗi. ‘Me ya kawo matar nan gidan nan kuma?.’ Na faɗa a raina, sabida daman a tsarin Hajja sai ta gama baloƙoƙo kafin take shigowa gidan. Hajiya da Alhaji duk sun fito tsakar gida suna jiran ta shigo, ita kuma tana can ta tagar ɗakinsu Yaya Ridwan ta baranda tana faman yi masa sababi.  “Ni dai kaf zuri’a ta a kanku a gama tabbatattu, ga dai farin jini Allah Ya yi muku amma sai baƙar zuciya, wacca nasan wajen uwarku kuka gado, yo daman fulanin jeji ina zuciyar arziƙi a tare da su, Allah Ya kyauta dai.”  Abinda ta shigo da shi cikin tsakar gidan kenan a bakinta, Alhaji ne ya fara tarar da faɗin.  “Hajja Barka da safiya, sannu da zuwa.”  “Yawwa sannu.”  Ta faɗa tana kauda ido, Hajiya ma ta ce.  “Hajja sannu da zuwa, ina kwana.”  “Lafiya.”  Ta amsa a daƙile, Ra’is ma ya ce.  “Sannu da zuwa.”  Banza ta yi da shi, nima na ce.  “Sannu da zuwa.”  Aikuwa ta washe haƙora tare da faɗin.  “ ‘yar arziƙi ke nake ta baza idanun ganin, kinsan idanun ba kowanne ke da kyau ba, gashi ke ba zuwa kike ba uwar mai mugun nufi ta hanaki.” “Ikon Allah sai kallo, yau rikicin tsufan nan ya kawo ta kenan.”  Ra’is ya faɗa yana daga inda yake, ni kaina nasan rikicin tsufa ne, dan ina ga ma Yaya Radiya take magana akai, tin da ita ce ta auri jikan da take so.  “Kina ina ne, matso na shafiki, na shafi arziƙi.”  Ta sake faɗa, kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki haka na taka na je idan take.  “Sannu mai ƙashin arziƙi! Sannu ‘yar nan.”  Ta faɗa tana riƙe hannu, sannan ta juya ga Alhaji.  “Sannu tabbatacce, kai yanzu ace yarinyar nan tana da wanda yake sonta daga gidan arziƙi irin haka kamar gidan Ta ambo, amma ka ɓoye min, sai yaron da kansa ya nemeni ya kawo min kayan arziƙi, ka ji tsoron Allah.” Legendspen 08129553971 971*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na tara     (09) Da ido kowa yake kallonta, dan babu wanda yasan ma suna saurayin nawa bare familinsa a tsakanin Alhaji da Ra’is da suka san maganar, bare Hajiya da batasan komai a kai ba.  “Hajja wane yaro kike magana a kai?”  Alhaji ya tambaya, dan shi tunaninsa ko Isah Nadabo zata ce, shine ta ce Ta ambo, dan dai dukkansu sunsan Familin Ta ambo ba ƙaramin ahali ba ne. “Ka ce haka mana, wallahi zama da wannan matar ta shafa maka mugun abu, shi ya sa na gwammaci na ƙyale mata kai ka je ka ƙarata daman ba wata tsiyar kake ban ba, to yanzu gashi ɗan gidan arziƙi yana son yarinyar Gawasiya take kowa, mai dai sunan Mutanen can, jiya da daddare yazo gidana ya cika shi da abun arziƙi sannan ya cika mini ƙugu da sulalla. Dan haka abinda nazo na faɗa ma shine, idan kana nan da wannan mummunan ra ayin naka na sai yara sunyi karatun yawudu da nasara ta ka sauke shi akan yarinyar nan, dan na yi mata miji na ce ya tura maka iyayensa ko sati yake so ka fito da kuɗi, kema ki fito da kuɗin shanu, aje a aurar da ita.”  Ta ƙarashe maganar tana kallon Hajiya, ƙasa Hajiya ta yi da kai ba tare da ta ce ko ƙala ba.  “Magana nake da kai fa.”  Cike da ladabi da girmamawa Alhaji ya ce.  “Hajja bangane kan zancen ba.”  “Baka gane ba, mene baka gane ba, ke yi masa bayani.”  Da sauri na kalle ta na ce.  “Wane bayani kuma?”  “Yaron da yake son ki.”  Gaba ɗaya idanuna sun cika da ruwa na rasa me zance.  “Ko kema bakya son sa? ‘yai mai baƙin hali.” Gaba ɗaya Hajja ta rikita gidan, kowa ya kasa gane inda ta nufa, kuma taƙi ta yi bayani yadda za’a gane sai faman cewa take.  “Ni dai na faɗa ma zai tura iyayensa.”  Da ta gama banbamin ta tafi, Hajiya ta kalleni bayan Alhaji ya fita rakata ta ce.  “Wane yake zuwa wajenki?”  Ra’is ya yi saurin cewa. “Akwai saurayinta da yake zuwa wajenta wanda har Alhaji yasan maganar ya ce yana son ganinsa.”  “To shine ɗan gidan da Hajja take faɗa?”  Girgiza kai ya yi sannan ya ce.  “Wannan ne kuma bansaniba.”  “Dake nake.”  Hajiya ta faɗa tana kallona, na gyaɗa kai kamar ƙadangariya sannan na ce.  “Eyh… eyh, a gidan Ta Ambo yake.”  “Aina ya san Hajja? Har yasan gidanta?”  “Ya tambayeni yana son ya je ya gaida ‘yan uwanmu ne na ce masa na Hajiya ba anan suke ba, na Alhaji ne anan.”  “Shi baki faɗa masa halinta ba.”  “Bansan ma zai gane gidanta ba, kuma na ce mai ma bata son mu.”  Daidai lokacin Alhaji ya shigo, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce.  “Yaron da yake zuwa wajenki ɗan gidan Ta  Ambo ne?”  “Eyh Alhaji.”  “Shine kika ce masa ya je ya sami mahaifiyata, ya bata abun duniya?” Da sauri na girgiza kai sannan na ce.  “Wallahi A’a.”  “To Lallai kisa shi yazo.”  Daga haka ya juya ga fice, ni kuma na yi cikin ɗaki.  A ranar na sake sanar da Sardauna saƙon Alhaji, cikin wayo da dabara ya dinga tambayata abubuwam da Alhaji yake so akaina, nan na sanar dashi zance karatu, kuma yana son nasami miji mai ilimi da tarbiya.  Bayan Magariba Alhaji ya dawo, sabida zuwan Sardauna, wanda bai zo ba sai ƙarfe takwas. A tsakar gida suka zauna mu kuma duka muna cikin ɗakin gaba ɗayanmu, amma hankalina gaba ɗaya yana kan su Sardauna da Alhaji. Yadda Sardauna yake magana da Alhaji cikin ladabi da nuna tsantsar tarbiya ya burge mu duka da muke cikin ɗakin, Hajiya, Ra’is da Ni.  Yadda yake nunawa Alhaji zallar soyayyarsa ga karatu da burin na zama wani ya haifar da soyayyarsa mai girma a zuciyar Alhaji, haka kuma yadda yake magana da Alhaji kamar yana karɓar Umarni wajen mahaifinsa ya nuna tsantsar tarbiyarsa.   “Ma sha Allah, ubangiji Allah Ya sanya albarka a taraiyyarku, ya albarkace ku da zuri’a ta gari.”  Alhaji ya faɗa, daga cikin ɗakin na ji wani daɗi ya ratsani har cikin zuciyata.  “Ka sanar da magabatan naka, sai su zo Allah Yasanya alheri.”  Maganar Alhaji ta ƙarshe kenan, bayan Sardauna ya tafi Alhaji ya haɗa mu gaba ɗaya har da Yaya Ridwan.  “A gaskiyya na yaba da irin nutsuwa da tarbiyar yaron nan da Nana ta kawo, dan haka na bashi damar ya turu magabatan nasa.”  “Gaskiyya ne Alhaji, ni kaina daga cikin ɗaki na tsinci nitsuwa a cikin muryarsa, Allah Ubangiji yasanya alheri.”  “Amin Amin.”  Farin ciki ya cika rayuwata gaba ɗaya, bacci rabi da rabi na yi shi. Gari na wayewa ko takwas ban bari ta cika ba na je gidansu Amina na sanar da ita, ƙawayena sai murna suke.  Kwana biyu a tsakani ‘yan uwa Sardauna suka zo gidanmu aka tsayar da rana wata uku, lokacin na kammala jarabarwata.  Lisaafi ya canja, abubuwa sun ɗau harama, ni da ƙawayena babu zama. Kowa ya ganni yasan wanda nake so zan aura, Su Yaya Rumaisa da Yaya Radiya da Ra’is kowa farin ciki yake ta ya ni, idan ka cire Ridwan da na kasa gane kansa, ko sakarwa Sardauna fuska ba ya yi, idan muna tare zai zo ya wuce sau ɗari bai isa ya kalleshi ba, Hajiya ta ce mu dinga taɗi a cikin ɗakinsu amma Yaya Ridwan ya ce ban isa ba, gaba ɗaya gani nake ya tsani Sardauna.  A cikin wannan lokacin ne auren Isah Nadabo yazo da matarsa Adizatu ‘yar jihar kano, biki ne aka yi shi na alfarma daidai zamani, kuma mun halarci komai na bikin tun daga farko har ƙarshe, kano ne kawai

Chapter 5 of 16