Share this page
'yan iska sama damu ko? To wallahi kisani babu wanda zai ƙara shiga al'amuranki tsakaninki da mijinki tun da kin zaɓi mutumin da ya haɗu dake ta haƙwaranki talatin da uku, kin bar wacca ta raini ki a cikinta har kika fito duniya, ta yi ɗawainiya dake, kin bar wayanda suka raine ki, su ka so ki, su ka bakk farin ciki, su ka tsoraci kukanki Nana, duk akan wani mutumi guda ɗaya, ki je rayuwar duniya ce."  Yana gama magana ya kashe wayarsa, kuka na fashe da shi, tabbas nasan maganarsa gaskiyya ce, kuma ya faɗa min abinea nake buƙatar a tinasar da ni, amma ya zanyi da Sardauna Allan da ya hallice ni shi ya sanya mini soyayyarsa.  Daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar bazan sake kiran kowa a gidanmu akan damuwa ba sai dak gaisuwa kawai.  Bayan sati biyu.  Tun lokacin da maganar nan ta fito gidanmu ya canja daga gidan farin ciki zuwa damuwa, daga gidan walwala zuwa na ƙunci, babu wani abu ɓai daɗi a gidan, kullum muna neman mafita amna taƙi samuwa, ta ɓangaren gida kullum Sardauna matsanta masa ake yi, an hana shi sakat. A yanzu Sardauna har baya son zuwa gidan Hajiyarsu ko Family House, kullum daga gida sai Majalisa yanzu ma da mota yake fita majalisar, ni kam bana iya komai banda tunanin mafita. A ko yaushe cikin saƙe saƙe nake, na yi baƙi na rame gaba ɗaya na fita hayyacina.  Gashi Bilkisu ba ta sake zuwa ba, tun ranar da na faɗa mata matsalal ta ce zata zo a cikin satin, idan ma na kira ta sai ta ce ba ta gari ma baki ɗaya.  Jiya da muka haɗu da Turaki sai da ya tsareni da tambayar me yake damuna, me ya faru tsakanina da Sardauna, amma na ce da shi komai lafiya. Daga ƙarshe ma ya fara yi min nasihohi masu ratsa zuciya akam haƙuri da rayuwar aure, sannan ya dinga jaddadamin na dinga yi wa mijina biyayya, har sai da na yi mamakin me ya sa ya yi haka. Da na dawo ɗaki ma na yi ta faman tunani maganganun Turaki me suke nufi, yanayin maganar kaman faɗa da nasiha yake min daga baya kuma ya dawo shawara.  "Allah Ya sa alheri ne."  Na faɗa, sai kuma can na yi tunanin ko akan maganar da ta ɓullo ne ta haihuwa shi ya sa.  "Innullahi wa'inna illahir raji'un, ya zan yi ni Nana?" Na tambaye kaina tare da fashewa da kuka, sai da na yi mai isata na ta shi na shiga ɗaki, zaman gidanma ya isheni tun da na zo gidan ban taɓa fita ba ko sau ɗaya, a yanzu an kai wata uku zuwa huɗu amma ban taɓa fita ba ko gida ban je ba.  Kwanciya na yi akan gadon na shiga tunanin rayuwa, da irin abubuwan da Sardauna ya saukar akaina, gashi kuma yana ƙara fuskantar wasu.  "Lallai Sardauna ya cika sadauki, Allah Ka ƙara mai lafiya da arziƙi, Allah Ka ƙarawa Sardaunana haƙuri da juriya akan abubuwanda suke tun karoshi, Allah Ka sani ina son bawan nan naka, Allah Ka so shi, ka yarda da shi, ka amince masa akan duk abinda ya sa gaba."  Cikin ikon Allah wani bacci ya ɗaukeni, wanda kiran sallar magariba ne ya tayar da ni, ina tashi na ɗaura alwala na yi sallah, dan yanzu Sarduna a waje yake magariba, idan aka yi isha kuma ya fita, tara da rabi zuwa goma yake dawowa.  Ina idar da sallah na shiga haɗa masa abinci akan dinning, ina cikin haɗawa ya shigo, fuskarsa kamar kullum amma yau ma tafi raunana, ajiye abinda nake na yi tare da tawowa inda yake.  "Sannu da zuwa Mijina."  "Yawwa Nana."  "Ya ofis?" "Nana rayuwa babu daɗi, abubuwa duk sun kacame."  "Innullahi wa inna illahir raji'un, me aka sake cewa kuma?"  "Mene ma ba a ce ba Nana, mene ba a ce ba? Kinsan yau kwanakin da Big Daddy yaban zasu ƙare gashi babu wata mafita da muka samu."  "Ya baka kwanaki ne?"  Na tambaya cike da mamaki, ya gyaɗa kai kusan minti biyar sannan ya ce.  "Big Daddy ya ban 10days akan na fitar da mafita, na ce ya ƙara min zuwa sati biyu to kinga yau anyi sati biyun."  Hawaye na ji suna gangaromin a fuskata, da sauri na gogesu sabida kar Sardauna ya gani, ni da zan ƙarfafa masa gwiwa bai kamata na raunana ba.  "Nana bansan abinda Big Daddy zai ce ba."  "Ni kaina kwana biyu na dage da addu'a sosai da sosai, abinda nake gudu kenan tun farko akan rashin haihuwar nan ka ce kai ba komai, yanzu ga shi komai ya juye."  "Nana ni kaina matsamin aka yi a gida, shi ya sa kuma wallahi nauyinki nake ji Nana, ina jin kunyar yi miki magana akan haihuwa Nana."  "Nasani, duk wannan matsi da takurar da muka shiga akan haihuwa ba ra ayinka ba ne, na kasance me yi maka uziri a ko yaushe Sardauna, ina sonka son da na yarda da kai fiye da kowa fiye da komai, na yi imanin har abada ba zaka taɓa cutar da zuciyata ba Sardauna."  Na kama hannunsa, ya ɗago ya kalle ni. Idanuwansa fal da damuwar da ta dame ni.  "A ko da yaushe ina miƙawa ubangiji Amanarka Sardauna, ina miƙawa Allah ragamar kula da kai, nasani Allah zai amss addu'a ta, ba zai taɓa ɗoramin abinda zaifi ƙarfinka ba, a ko da yaushe ina sonka zan kasance mai sonka Sardauna har numfashi na ƙarshe." Ji na yi ya jawo ni jikinsa ya rugumeni tare da faɗin.  "Nana, bani da wata kalma guda ɗaya da zan iya godewa kan alherin soyayyarki agareni, Nana nasami damarmaki masu yawa sanadiyar soyayyarki, na gode Nana, nima ina sonki." Haka mu ka yi ta lallaɓar juna, ina ƙara nunawa Sardauna girman soyayyarsa a zuciyata, har na samu ya ci abinci ya shirya ya fita Majalisa.  Sai goma ya dawo gida, ina nan inda ya barni ina ta faman saƙe saƙe dan yanzu babu abinda na ƙware da shi kamar damuwa, ina saƙa wancan na since wancan.  "Honey baki yi bacci ba?"  Ya faɗa yana zama.  "Ban yi ba tukunna, har ka dawo?" "Eyh na dawo Honey, kin ga." Ya faɗa yana buɗe ledar da ya shigo ita, kwalin wayar iphone, ya miƙomin.  "Nana take."  Na sa hannu na amsa ina mai jindaɗi.  "Buɗe mana."  Na fara kici kicin buɗewa, iphone 16normal ce pink kala mai kyau.  "Na gode sosai mijina, Allah Ya ƙara arziƙi lafiya da wadata."  "Amin My love."  Ya faɗa tare da ɗaukana zuwa ɗaki.  Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, muna gida gashi ba weekend ba, da na tambayeshi sai ya ce.  "Bana som fita ofis, zan haɗu da Big Daddy. Kuma kinga yau kwana goma sha huɗu ta cika."  Kamo hannunsa na yi, sannan na ce.  "Wane irim hukunci kake tunani kake tunanin zai yanke?"  "Nima bansani ba, amma bana son ya bani hukunci mai tsauri Nana."  "Duk tsaurinsa bai zai yanke ma hukuncin da zaka rasa rayuwarka ba, Sardauna nasan ba zai yanke ma hukuncin da zai cutar da lafiyarka ba, to ina ganin duk wani hukunci da ya biyo bayan wannan mao sauƙi ne a wajena da kai, ni zan ta ya ka karɓar kowanne irim hukunci ne Mijina."  "Na gode Nana, Na gode amma bana son wani hukunci da zai cutar da rayuwarmu, ko wani hukunci da zai sa mu yi abinda ba zamu ji daɗi ba, Nana ke nake so ke kaɗai a duniya, ban damu da 'ya'ya ko rashin su ba Nana, amma tabbas ina jin ba daɗi idan na ga Hajiya ta a cikin halin damuwa, na kan ji zafi idan na ga Alhajina a cikin damuwa, duk akan yara."  "A kullum kaine mai cemin haihuwa da rashinta duk na Allah ne, akan wannan na tashi, akan shi na ɗaura yarda ta, kuma nasan suma sun san da haka, dan haka nasan ba zasu yanke maka hukuncin da zaka kasa ɗauka ba."  "Nana ki yi haƙuri, na yi miki laifi mai girma."  A tsorace na ce.  "Wane irin laifi kuma?" "Nana, na sanar da Hajiya asalin matsalal rashin haihuwarmu, a tunani za ta fahimta ko ta yi mana uziri, kuma nasan ta sanar da Big Daddy."  Shiru na yi na rasa me zance, yanzu tun da sun san matsalal daga wajena ne zasu iya cewa ya sakeni? A fili na furta.  "Innullahi wa inna illahir raji'un."  "Nana calm down kin ji, ko mai zai zo da sauƙi, kece mai faɗin haka."  Gaba ɗaya na tsorata idan babu Sardauna ina zan sa rayuwata ni Nana, ina zan kalla na ji daɗi, ta ina zan iya numfashi bayan babi Sardauna a kusa da ni, na shiga uku ni Nana.  "Ki nutsu ba zasu yanke hukunci mai kamar wanda kike tunani ba in sha Allah."  Cikin muryar kuka na fara magana.  "Wallahi cewa zasu yi ka sake ni wallahi, me ya sa  ka faɗa musu haka?"  "Nana baza su ce haka ba kwata kwata, in sha Allahu." "Sardauna."  Na faɗa tare da tsugunnawa a ƙasa. "Na'am Nana."  "Dan Allah, dan Annabi da girman iyayenka Sardauna kar ka sake ni, ko mene zai faru, wallahi ina sonka, ina sonka ban da wanda nake so bayan kai, Sardauna idan ka rabu dani bani da wata rana a rayuwata, ka yi min alƙwari dan Allah."  "Tashi Nana, tashi ki zauna."  Ya faɗa yana kamoni na zauna.  "Nana, ina sonki fiye da yadda kike tunani, na yi yaƙi mai girma kafin na aureki, sabida haka zan yi wani yaƙin akan na rayu da ke."  "Tabbas Sardauna idan ba kai ni gawa ce."  "Nasani Nana."  "Sardauna kai ne dalilin da yasa nake numfashi, Sardauna kai ne dalilin da murmushi yakw fitowa a fuskata, ka tausayamin dan Allah."  Rumgume ni Sardauna ya yi sannan ya ce. "Nana, na yi miki alƙwarin duk tsanani dui wuya ba zan taɓa rabuwa dake ba, ko da ke ce kika buƙaci haka, Nana wallahi ina yi miki kishin da bazan iya numfashi ba muddin na ga wani namiji a tare dake, ko da ɗan gidanku ne, Nana a ƙarƙashin ikona zaki rayu, anan zaki mutu na yi miƙi alƙwarin hakan Nana."  Duk wasu kalamam Sardauna daɗi suke mim a rayuwa, babban buri na shine na rayu na kuma mutu a ƙarƙashin auren Sardauna. Yinin ranar bai fita ba sai dare, haka washe gari ma wai duk akan big Daddy, sai da ya kwana uki a gida sannan ya yanke shawarar zai fita, shima dai duk a tsorace yake. Ni kuma wani tausayinsa ne yake taɓa min zuciya, Allah Ya gani bana son wani abu da zai dami mijina ko kaɗan, bayan ya fita na yi ayyukana na kwanta bacci.  ***** 06:30pm Yamma ce mai cike da sanyi, ina zaune a falo ina jiran dawowar Sardauna. Tun safe bayan ya fita na ji zuciyata tana bugawa, wani irin nauyi nake ji wanda na kasa fassara shi.  Ko da na yi bacci wani irin mafarki na yi marar daɗi, amma abinda ya kwantar min da hankali shine ba Sardauna ba ne a mafarkin ni ce, ni kuma nasan ina zaune anan babu wani abu da zai sameni, duk da a mafarkin ganina na yi ina kuka a zaune a falon nan, amma yanayin kujeruj falon su sauya kuɓa duk hotona na da suke falon babu su, nasan dai wannan duk mafarki ne.  Ina zaune ina ta faman addu'a Allah Ya sa alherine, duk da al'amuran gidansu Sardaina sun dame ni sosai da sosai, gashi rabon Bilkisu da gidan nan an kwana biyu, sai dai ta waya da muke magana. Ina jin ƙarar motarsa, na tashi da sauri don na tarbe shi kamar yadda na saba. Ina buɗe ƙofar, na gan shi tsaye, amma yanayin da na ganshi ya sanya na sandare a wajen. Sardauna ne, amma ba wannan Sardaunan mai takama da izza ba. Idanunsa sun yi jajir, fuskarsa ta kumbura alamar ya sha kuka, har lokacin hawaye suna zirara a kumatunsa. Legendspen 08129553971 Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin.     (20) "Sardauna! Me ya faru? Me ya faru da kai?" Na faɗa muryata tana rawa, hankalina ya gama tashi. Bai ce mini komai ba, ya ƙaraso cikin falon ya zube a kan kujera, ya rufe fuskarsa a cikin tafin hannunsa, kuka yake yi mai taba zuciya, yana girgiza kai tamkar wanda aka yi wa rasuwa. Ban san lokacin da nima hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na durƙusa a gabansa na kamo hannunsa. "Don Allah Sardauna ka yi magana, ka tsoratar da ni. Ko wani ne ya rasu a gidan?" Ya ɗago idanunsa waɗanda suka rine suka yi ja, ya kalle ni da wani irin tausayi, sannan ya fara magana cikin muryarsa wadda ta dashe sabida da kuka. "Nana... gara ma mutuwa ta ɗauke ni na huta da wannan mummunar kaddarar. Nana, Big Daddy da Hajiya sun sanya ni a gaba sun ce lallai sai na ƙara aure. Wai saboda har yanzu shiru ba ki samu juna biyu ba. Kuma matsalal daga gareki take Nana, su kuma ba za su iya jure  hakan ba, tun da ba asan zuwa lokacin da mahaifar taki za ta yi ƙwari ba Nana, ina cikin damuwa gwanda mutuwa ta ɗaukeni da wannan abun." Wani irin jiri na ji ya kwashe ni, na ji numfashina yana shirin ɗaukewa. Aure? Sardauna zai ƙara aure? "Sun ce... sun ce idan ban yi ba, to za su cire ni daga cikin komai na gidan. Nana, na yi kuka, na roƙe su, na ce musu ke kaɗai kika isa ki zama uwar 'ya'yana, ke kaɗai nake so Nana ke  kaɗai nasani a cikin duka matan duniya amma sun ƙi saurare na. Wai ko dai na sake ki ko kuma na yarda na ƙara aure, idan lokacin da suka ba ni ya cika to za su aura mini wata ko wace." Ya sake fashewa da wani sabon kukan, ya jawo ni ya rungume ni yana kuka a kafaɗata, ni kuwa kamar mutun-Mutumi haka nake jina, ba na gane komai. "Nana, ba zan iya rabuwa da ke ba, amma kuma ba zan iya saɓa wa magabata na ba. Ina son ki Nana, amma kaddara tana shirin raba mana farin ciki." Nima kukan nake yi kamar raina zai fita. Ganin yadda Sardauna yake zubar da hawaye saboda ni, ganin yadda yake nuna mini yana cikin matsanancin hali, sai na ji duk duniya ba ni da masoyi kamarsa. Na ji tausayinsa ya mamaye mini zuciya, har na manta da zafin kishin da yake shirin shiga rayuwata. "Ka yi haƙuri Sardauna,"  na faɗa cikin dasasshiyar murya.  "Idan har hakan shi ne zai kawo maka kwanciyar hankali a gida, to ka bi maganar su. Ba na son ka shiga matsala da iyayenka saboda ni." A daidai wannan lokacin, na lura da wani ɗan gajeren murmushi da ya gifta a fuskarsa ba tare da na fuskanci ma'anarsa ba. Sai na ga ya ɗago ya kalleni, ya sake murmushin.  "Nana kina da hankali? Kinsan me kike cewa? Na je na yi auren haka kike cewa Nana wa zan aura, wa na sani? Kin taɓa ganina da wata mace? Kin taɓa kamani da wata mace? Nana ba kya kishina ne ko me?"  Da sauri na girgiza kai sannan na ce.  "A'a ba haka ba ne, amma ina ganin bamu da wata mafita a yanzu da ta kai hakan, babu ita dole ne mu yi biyayya, idan muna son kasancewa tare."  Kuka ya sake fashewa da shi, tare da tashi ya shige cikin ɗaki. Yana tashi na bi bayanshi har zuwa cikin ɗakin, nasan dole a yanzu ni zan tausashi Sardauna, tabbas yana cikin damuwa mai girma nina sani. Zama na yi akan gadon kamar yadda ya yi.  "Kai daina tagumin nan dan Allah."  "Hhhm! Nana idan banyi tagumi ba me zanyi? Ina da abun yi ne? Wai baki ji abinda na ce miki ba aure fa, aure suka ce na sake nan da two weeks ko zasu bani wacca suka ga dama kuma na sake ki."  "Nasan sun yi fushine, amma ka bi komai a hankali nasan Hajiya za ta sake fahimta dan Allah." "Nana kina nufin na je na yi musu wani bayani? Kina tunanin akwai abinda ban faɗa musu ba? Nana kin raina girman soyayyarki a zuciyata ne?"  "Ko kaɗan ba haka nake nufi ba wallahi, ina nufin mu nutsu mu sami mafita a hankali."  "Kina da mafita? Dan Allah Nana na faɗa min."  "A yanzu dai babu, amma dole na yi tunani na sami mafita domin matsalalka matsala ta ce."  "Allah Ya bamu mafita Nana, ki yi haƙuri kin ji ko?"  "Dame? Me ka yi min haka? Kai zan bawa haƙuri Sardauna."  ****** Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, yana gida gaba ɗaya babu abinda yake iya zuwa, ni ke ta ɗawainiya da shi kamar ƙaramin yaro, kuka kuwa ya yi yafi a ƙirga. Gaba ɗaya bai bani wata dama da zan yi wani tunani ba, gashi a yadda ƙwaƙwalwata ta toshe ina buƙatar isashen hutu kafin na yi tunani, nasan matsala ta babba ce amma har yanzu naƙi yardarwa kaina matsalar babba ce, gani nake akan Sardauna komai zan iya yi.  Sai wajen ƙarfe biyar sannan ya shirya ya fita, bai daɗe da fita ba na kira wayar Bilkisu, ina kira ta ɗauka, cikin muryata dake cike da damuwa na fara magana. "Sister kin daina zuwa kwata kwata, abubuwa duk sun caɓe mini."  "Ba haka ba ne Nana, nima ayyuka sunyi min yawa ga wata matsala da ta fara kunnomin kai a gida."  "Ya salam, ni kaina abubuwam sunyi yawa daga gidansu Sardauna."  "Nana tun da gidansu Sardauna ne ai da sauƙi, nifa akan kaina nake magana, Nana kinsan Abbanmu ya bani sati ɗaya na fito da mijin aure ko ya auramin wani abokinsa, Nana dattijo ne ya kai kusan shekara 70, gashi kinsan ni babu wanda nake kulawa, Nana ina cikin damuwa."  "Allah Sarki 'yar uwa, muma makamanciyar matsalalki muke fuskanta."  "Bangane ba?"  "Gidansu Sardauna sun matsa mishi akan ya ƙara aure."  "Saboda me to?"  "Rashin haihuwa mana."  "Nana kika ce kin yi ɓari har sau biyu, kuma kince mahaifarki ce ba ta yi ƙanƙanta ko?"  "Hakane."  "To ai zaki haihu Nana, ki yi musu bayani mana."  "Bilkisu ba zaki gane ba, a yanzu dole Sardauna sai ya ƙara aure ko kuma ya sake ni."  Na faɗa ina fashewa da wani irin Kuka, bana son kalmar sakinan ko kaɗan a rayuwata. "Idan har haka ne mafita Nana ki amince masa, tun da kina son sa, kina son farin cikinsa, farin cikin iyayensa ai shine nashi, Nana ke kika ce kina son Sardauna sama da kowa sama sa komai, to ki nuna masa a wannan lokacin, ki nuna masa soyayya ki dage ki danne ki barshi ya yi auren."  "To ai ba anan matsalal take ba."  "Nana ga Momy nan mu yi magana anjima."  Ta faɗa tana kashe wayarta, bayan wayar ta mutu ta barni cikim tunani. 'Idan da gaske nake son Sardauna yanzu ne lokacin da zan nuna masa soyayyar ta hanayar ƙarfafa masa gwiwa kenan? To amma Sardauna baya kula mata ba ruwansa.'  Wani ɓari daga zuciyata ya ce da ni. 'Ko a wajen aikinsa ba zai rasa ba, ko a 'yan uwansu.'  'A 'yan uwansu fa?' Na tambayi kaina.  'Kai a'a gaskiyya a gari kawai ya nema ya aura, zanyi haƙuri zanyi biyyaya in sha Allah.' Wannan ita ce shawarar da na yanke akan Sardauna, ita ce mafita guda ɗaya da nake ganin za ta fiye mana daga ni har shi. Sai wajen ƙarfe tara ya dawo, ina zaune a falo ya shigo.  "Sannu da gida Honey."  "Yawwa sannu da dawowa."  Na amsa masa, kasancewar ba shigar ofis ba ce yasa ban cire mai takalmi ko wani abu ba.  "Ga abinci."  "Honey ba ni da nutsuwar cin abinci, ni kaɗai nasan abinda nake tun kara Honey, ni kaɗai nasan abinda nake ji.Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana watangarirya."  "Ka yi haƙuri, komai ya yi tsanani sauƙi yana tafe, a yanzu na yi tunani kuma na fitar da wata shawara da nake ganin kamar ita ce mafita Hon."  "Mecece? faɗamin dan Allah."  "Hon, rayuwa tana bamu zaɓi da dama, wani abun da muka tsara da kanmu, wasu kuma sukan afku ba tare da muntsara su ba, kamar yadda bamu taɓa tsara zamu san juna ba kafin nan, haka bamu taɓa tsara zamanmu zai zo da wata tangarɗa ba bayan munsan juna, Honey ubangiji ne ya dasamin sonka a zuciyata, na yi imani da Allah na yi imani da soyayyar da kake min Hon, dan haka ni dai a ganina kawai ƙara auren ne mafita agaremu dukkanmu. Duk son da nake yi maka, duk ƙaunar da nake yi miki ba ta da wani amfani a ranar da narasa ka, a ranar da nazama ba mallakinka ba, duk wata iriyar soyayyarka da nake ji ba ta wata rana. Idan har ina son ka me zai sa ba zan so ma farin ciki ba? Me zai sa bazan so ma ladan biyayya ga iyaye ba? Menene wata riba a duniya da ta wuce ta biyayya ga iyaye Sardauna?"  "Nana wai kina nufin kema kin amince na ƙara aure?" Wani irin zafi nake ji a zuciyata a duk lokacin da Sardauna ya ambaci ƙara aure, amma ya zanyi ƙaddara ta riga fata, dole ne na goyi bayansa akan yiwa iyayensa biyayya.  "Na goyi bayan ka yi biyayya ne Sardauna, domin kasami rabauta da tsira a duniya."  "Nana bazan iya ba, bazan iya ba, bazan iya ba wallahi, na yi miki kishiya fa Nana, wa zan aura to? Wa nasani ma bayan ke?"  "Ka duba zaka samu in sha Allah."  "Cikani."  Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa.  "Ka fahimce ni dan Allah, idan fa baka yi auren ba rasani zaka yi, zasu ce ka sake ni."  "Nana su faɗa, ai ba lallai ba ne na yi musu biyayya."  "A'a Sardauna, idan ka neman albarka dole ka yi wa iyayenka biyayya, ni dai ka fahimce ni."  "Nana kenan, wace kalal fahimta zan miki? Zancen ki anan babu abinda yake nunawa sai zallar rashi Kishina, Nana kalamanki tsaf zasu yi wa zuciyata Sartse mai raɗaɗi."  Kuka ne ya ci ƙarfina, ni a yanzu ai angama yi wa zuciyata Sartse gaba ɗaya, domin duk lokacin da na ji a raina wai Sardauna zai ƙara aure sai na ji wani raɗaɗi daga cikin zuciyata mai haɗe da ya ji, amma yana iya? Dole na so farin cikin mijina sama da komai a wannan rayuwar.  "Ka yi haƙuri Sardauna."  Na faɗa ina jawo shi jikina, ya rungume ni iya ƙarfinsa kamar zai mayar da ni jikinsa, ina jin yadda yake shasheƙar kuka.  "Ka yi haƙuri ka ji." "Ya zanyi Nana?"  "Ka yi tunani ta ina ka haɗu da ni, har ka tun kare ni, nasan zaka samu zaka samu wacca zaka iya aura."  "Nana bana so su bani a dangi, bana so su ce na rabu dake Nana, bazan iya ba."  "A waje zaka samu."  "Hhhm, Nana kenan."  ******* Har dare Sardauna ya kasa fahimta ta, ya kasa fahimtar inda zance na yake son nufa, a haka muka haƙura mu ka kwanata, sai dai fa ni bacci yaƙi zuwa idona, tunani nake anya zan iya kasadar barin wata kusa da Sardauna, babban abinda yafi bani mamaki, ban ji mahaukacin zafi a cikin zuciyata ba akan zancen ƙarin auren, zafin da fi ji shine na rabuwa da ni, ko dan maganar sake ta shigo ita ce ta cire min raɗaɗin kishin? Amma kwata kwata ban ji ina mugun kishi ba, ko a baya ma bana iya tuna kishin da na yi akan Sardauna ba.  Ƙarfe uku na dare na tashi, bayan na yi nafila raka'a biyu na yi addu'o sosai, sannan na dawo na kwanta, sai a lokacin bacci ya ɗauke ni.  Washe gari ma haka muka tashi da Sardauna yanayin babj daɗi, na yi masa bayani yafi sau cikin carbi amma amsa ɗaya yake ba ni.  "Honey bazan iya ba, Honey ban da ita."  Ya koma kamar wani ƙaramin yaro ba abinda yake iya ganewa, abinda ya ƙaramin tausayin Sardauna kenan, gaba ɗaya ji nake duk ni ce na ja masa komai ma, ko kuma na ji dama akaina waɗannnan abubuwan suke faruwa ba akan Sardauna ba, domin duk damuwar sardauna guda ɗaya, sau dubu nake jinta a zuciyata.  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da ɗaya.     (21) Da ƙyar na iya lallaɓa Sardauna ya fita ofis, amma da ya ce wai bazai iya fita ba sabida kowa ya ganshi zai san yana cikin damuwa. Sai da na yi masa daɗin baki sosai na nuna masa babu wanda zai gane yana cikin damuwa, sannan ya fita.  Tun bayan tafiyar Sardauna na shiga aikina na kullum, amma sai dai na yau zuciyata tafi nuna min wa Sardauna zai aura, wani irin zama zamuyi shin zai so ta kamar yadda ya so ni, ko ma zaifi sonta, za ta yi masa biyayya irin yadda nake yi? Ko za tafi ni? Dole fa na dinga raba mata kwana da Sardauna, duk da hakan bai

Chapter 11 of 16