fa uwa da uba Allah Yake ɗauke musu rana guda lokaci ɗaya, su ce me? Allah Ya ce ku kasance masi godiya ni kuma zan ƙara muku, ko gode masa da ni'imar da ya yi muku Nana, zai ƙara muku wata."
Jawoshi na yi jikina na rungumeshi, sannan na ce.
"Hakane, Allah Alhamdulillah, ko kai da Allah Ya bani wata ni'imace da zan gode masa akai, ina sonka, ina ƙaunarka."
"Nima haka Nana, ina sonki! Ina ƙaunarki."
"Allah Yabar mu tare Mijina."
"Amin matata."
Tun daga wannan lokaci na fara rage damuwa akan rashin haihuwa, na yarda da Sardauna na kuma amince da shi, na kuma yi alƙwarin ninka tausayi da soyayyar da nake yi masa.
Washe gari, tun asuba da na tashi na shiga haɗa ma Sardauna lafiyayen abinci, wanda rabona da na yi masa ƙayataccen abincin tun kafin rasuwar Alhaji. Ina tsaka da aikin a cikin dabarar yi masa cupcake ta faɗomin, ba tare da wani dogon tunani ba na haɗa cake, ina wancan aikin ina wancan, wajen ƙarfe bakwai na fito na shiga ɗakinsa, yana kwance kan gado na shigo toilet na haɗa masa ruwan wanka sannan na fito, a hankali na zauna a gefen gadon sabida kar ma tashe shi, na kai hannuna kan sumar kansa na fara shafawa, da sauri ya buɗe idonsa ya sauke su akaina, ya sakar min murmushi sannan ya ce.
"Nanaty."
"Na'am, aje ayi wanka breakfast ya zama ready."
"Tom ɗago ni."
Ya faɗa yana miƙamin hannunsa, na kama tare da ja amma kamar banja ba.
"Ƙara dagewa."
Ya faɗa, na kuwa sa duka ƙarfina na ƙara ja sai da na ji hannuna ya yi ƙas amma kamar bashi na ja ba.
"Raguwa."
Ya faɗa yana jawoni kansa, ai kuwa kamar takarda na faɗo, ya zame ya barni kwance ya shige toilet ɗin, sif na buɗe na ɗauko masa kaya na koma kicin na ci gaba da aikina, kusan mintuna ashirin na ji maganarsa a gab da kicin ɗin.
"Baki gama breakfast ɗin ba ne?"
"A'a na gama gashi can a dinning bara na zo na baka."
"To me kike yi anan?"
Fitowa na yi sannan na ce.
"Girki nake ma."
"Me kike dafawa, kuma me zna yi da shi?"
"Cake ne na tafiya ofis."
"Awwww, thank you daman rabona da cake tun kina sona, gashi na ga alamar kin dawo da sona."
"Wai na daina sonka."
Na faɗa ina ƙarasawa wajen dinning ɗin, shima yazo ya zauna na fara zuba mai.
"Wow, ni Sardauna mijin Nana, dama haka kike min kullum."
Na yi dariya sannan na ce.
"To me nake ma ai haka nake ma, kai dai kawai ka ci."
Haka kuwa ya ci sosai da sosai, daidai lokacin na juye masa cake ɗin da na gama decorating ɗinsa a cikin ƙaramin box."
Sai da na rakashi har parking space, namu yana gefe na Turaki yana gefe, lallai fa ta dole sai sunyi zumunci domin kusancin gidan ya yi yawa, ko ƙara aka yi sai anji.
"Wannan yaron yana nan kenan?"
Ya faɗa yana shiga mota, sai na ga ya shiga sannan na juya na koma ciki na fara ayyukan, na gyara inda nake son gyarawa na goge ko ina sannan na dawo na zauna. Waya ta na ɗauka na fara dannawa, ga wayar dai amma babu layi babu wani abu da zanyi da ita, haka na gama juyata na ajiye, ga Tv babu damar yin kallo, daman gidan babu zafi amma gaba ɗaya na ji ya isheni, kamar na yi kuka haka nake ji duk gidan ya yi min zafi.
Ganin zaman ba zai kai min ba na tashi na fara zagaye ko ina, na leƙa can na leƙa can daga baya na dawo bakin taga ina kallon gidan tanan. Turaki na ga ya fito daga ɓangarensa cikin shirinsa na ofis bai ma kalli ina ɓangaren mu yake ba ya shiga mota shima ya fice.
"Shikenan yanzu ni kaɗai ce a gidan, na shigo ni Nana."
Ɗakina na koma na zauna, amma zaman ba daɗi, na dawo falo ba daɗi, haka na yi ta zagaye zagaye har yamma. Ina xaune a falo na ji magana da motsin abubuwa, na buɗe taga na leƙa kayan gado da kujeru ne ake shiga dasu ɓangaren Turaki a raina na ce.
"Gwanda ka yi auren, ko na sami abokiyar zama da ta ya hira."
Ina tsaye ta taga suka gama shi dasu, shi kuma yana basu umarnin inda zasu jera, har suka kammala suka tafi shima ya bisu, dambun cous-cous da miyar kaza na yi wa Sardauna, sannan na yi masa lemon abarba, tun biyar da rabi nake sa ran ganinsa amma ba shi ya shigo ba sai bayan magariba, yanayin dana ganshi kaɗai ya sani farin ciki, sabida na ganshi fuskarsa a washe.
"Ssnnu da zuwa."
Na faɗa ina amsar jakar hannunsa.
"Yawwa, sannu da gida matata."
Tsugunnawa na yi na shiga cire mai takalmin ƙafarsa sannan na kwasa na shiga ciki, bayan na fito ne na ce.
"Wanka ko abinci?"
"Abincin dai sabida ina so na sake fita yanzu."
"Tom muje na baka."
Na faɗa ina nufar dinning ɗin shi kuma ya biyo ni a baya, ya yi farin ciki ganin abincin amma kuma farin cikin dake cikin wayarss yafi yawa, ina jin kamar na tambayeshi me yake gani a wayar sai kuma na ƙyaleshi, nasan ko mene alheri ne dai.
Ina son yi masa magana akan zaman da na yi yau ba daɗi amma bai bani damar hakan ba, har ya kammala cin abincin sannan ya ce.
"Haɗamin ruwan wankan."
Na tashi na shige ɗakin na haɗa masa, bayan ya fito ya shirya sosai ya yi kyau kamar ko yaushe.
"Nana, zancen dinner ɗin abokina ne, na ga kamar kin damu."
Na yi murmushi sannan na ce.
"Allah Ya tsare zaka yi dare ne?"
"Bazan wuce goma ba ina ga."
"Tom adawo lafiya, amma dan Allah ko Tv ne zan iya kunnawa zaman ni kaɗai ba daɗi wallahi."
Kallona ya yi baice komai ba ya fice, sai na ji kamar ban kyauta ba, na dawo na zauna kan kujera tare da haɗa uban tagumi, bayan na yi sallar isha na dawo na sake zama, tun ina sa tan ganin Sardauna ƙarfe goma har sha ɗaya shiru, ta dole na bawa baccin da yake fisgata damar ɗaukana.
Cikin bacci na na ji ana cewa.
"Anan kika kwanta? Tashi Nana tun da ba zaki iya jirana na dawo mu yi magana ba."
A hankali na buɗe idona na kalleshi, cikin muryar bacci na ce.
"Ka dawo?"
"Eyh, tashi kije ki kwanta."
Miƙewa na yi na nufi ɗaki na kwanata, ba tare da nasan asalin daidai lokacin da Sardauna ya dawo ba.
Washe gari ma kamar jiya haka na tashi na shiga kicin, wani abu daban nasake haɗawa Sardauna, sanna na ɗauko wasu cikin cake ɗin jiya nasake docorating ɗinsu da icing suger, yau ko da naje ɗakinsa ma ya shirya da kansa, sai da wayarsa na kare a kunnesa yana magana.
"Breakfast ya zama ready."
Gyaɗamin kai kawai ya yi alamun ya ji, ni kuma na shiga nawa ɗakin na shirya, bayan na fito na sameshi akan dinning yana danna waya.
"Ina kwana?"
"lafiya ƙalau Nana."
Zama na yi na fara zuba masa abin breakfast ɗin, bayan na zuba mai nima na zuba, sai a lokacin ya kashe wayar ya fara ci.
"Nana!"
Ya kira sunana a hankali, na ɗago kai tare da cewa.
"Na'am."
"Kince bakya jin daɗin zama ke kaɗai ko?"
"Ba banajin daɗi ba ne, kawai bansaba da gidan ba ne."
"Hakuri ake yi Nana, yau da gobe zaki saba, amma tun da kina so na baki damar amfani da TV ɗin shikenan?"
"Eyh shikenan, sai kuma zancen sabon sim ɗin da ka ce zaka bani, ina son na dinga jin lafiyar Hajiya, kuma nasan itama zata nemeni, ya kamata na sanar dasu mun canja gida."
"Eyh, to da wannan kam."
Ya faɗa yana cire bayan cover wayarsa, ya ciro min sabon sim card sannan ya ce.
"Gashi, amma Nana bana son na ga lambar kowa sai ta Hajiya ita kaɗai, sai kuma tawa."
"Tom in sha Allah, na gode."
Daga nan ya ƙarasa abinda zai yi ya fita, bayan ya fita na sim ɗin na kira Hajiya muka gaisa nake sanar da ita muncan gida, umarni ne daga familynsu kan rashin zaman daɗi da suke da Turaki gidan ma guda ɗaya ne mu da shi.
Daga nan muka gaisa da su Yaya Radiya da su Ra'is, daga nan muka yi sallama na kashe wayar, haka kawai na ji zuciyata na ingizani akan na je na haɗa kayan Sardauna na wanke su, ba tare da na yi wani ja'in ja da zuciyata ba na ɗauka na shiga toilet na hau wanki, tun wajen sha biyu har uku na rana ina wanki, sannan na shan ya su na dawo na ɗaura girki, gaba ɗaya har na dare na yi. Bayan na ci na yi wanka na zo na kwanta na huta gajiya. Cikin barci na ji kamar ana bugu ƙofar tawa, buɗe da idona na yi tare da faɗin.
"Waye?"
"Ni ce."
Na ji muryar wata mata, tashi na yi zan nufi ƙofar sai dai idona ya kai kan waya ta na ga agogon wayar ya nuna ƙarfe 06:16, gaba na ne ya faɗi afili na ce.
"Ya ubangiji kasa ba baƙuwa na yi ba, a daidai wannan lokacin da Sardauna zai dawo ba."
Ƙara bugu ƙofar a ka yi na fita ina faɗin.
"ina zuwa."
Na faɗa ina ƙarasawa wajen ƙofar, a hankali na buɗe gabana yana faɗuwa, aikuwa baƙuwar ce sai sai bansanta ba, murmushu ta yi min sannan ta ce.
"Sannu!"
"Yawwa sannu, shigo mana."
Na faɗa ina matsa mata ƙofar, ta shigo cikin falon.
"Ina wuni."
Na faɗa ganin ta girmeni sosai ma.
"Yawwa Sunana Bilkisu, anan baya nake, na ga an kawo amarya kuma ina yawan cewa zan shigo Allah Bai nufa ba sai yau da na zagayo gidan kisto."
Ta faɗa tana nuna hannunta baya alamun kwatancen inda take, na yi mata wani murmushi mai wuyar fassara, domin ni kaɗai nasan irin bugun da zuciyata take, lokacin dawowar Sardauna ne yanzu, kowanne lokaci zai iya shigowa, gashi baya ƙaunar ya ga wata ƙawa ta kusa ko ta nesa ta zo wajena.
"Zauna mana to."
Na faɗa ina nuna mata kujera, ta yi min wani irin murmushi sannan ta ce.
"Ai sauri ma nake, amma zan dawo."
Ban kai ga buɗe baki ba na ji horm ɗin Sardauna, wanda yake yi daidai lokacin da zai kashe motarsa, wanda yake yinsa domin sanar dani ya dawo.
"Mai gidan ne ya dawo?"
Ta tambaya ne, na yi murmushi sannan na ce.
"Eyh shine."
"Ayyah to kinga kuwa ba sai na zauna ba, amma in sha Allahu zan dawo."
Ta faɗa tana juyawa zata fita, daidai lokacin kuma shi ya shigo. Kamar ana buga ganga haka na ji zuciyata na bugawa, da sauri na runtse idona sannan na buɗe.
"Sannu da zuwa."
Na faɗa ina ƙarasowa inda yake, ga mamakina ya sa hannu ya komo ni tare da faɗin.
"Nanaty baƙi ne damu?"
Ya faɗa yana shigewa ciki, na bi bayanshi ina faɗin.
"Ina zuwa."
"Uhmm."
Ta faɗa tare da zama, ni kuma na bishi ciki.
"Sannu da zuwa."
Nasake faɗa ina ajiye jakarsa a ma'ajiyinta.
"Yawwa"
Ya amsa yana zama kan gado, tsugunnawa na yi tare da fara cire mai takalmi ina faɗin.
"Wallahi bansanta ba, yanzu ta shigo wai anan baya take."
Kallona ya yi tare da kamo hannuna
"To mene a ciki? Ai hakan yana da kyau sosai da sosai, ke fa kika ce min zaman ke ɗai ba ya yi miki daɗi kuma daman ka yi ta zama a waje bakasan kowa ba? Ta shi kije ku gaisa."
Da wani irin yanayin mamaki nake kallon Sardauna. 'Sardauna dai? yau shi ke barin wata tazo gidan nan, har da cewa ayi ta zama a waje ba asan kowa ba, Sardauna da ya tsani ganin baƙo a gidan?'
"Ki tashi mana."
Muryarsa ta katse min tunanin da nake, na miƙe na nufi falon.
"Ki yi haƙuri na bar ki."
"A'a babu komai fa, ai mai gidan ne ya dawo, bari na zo na wuce amma zan dawo."
"Tom shi kenan na gode sosai da sosai, nima idan na samu fita zan shigo gidan naku in sha Allah."
Na faɗa ina rakata waje, a gurguje na dawo haɗa masa ruwan wanka sai na tarar yana toilet ɗin ma.
Na fito na dawo na jera masa abinci akan dinning, bayan na fito masa da jallabiyar da zai sanya na ajiye mai kan gado, nima na tafi ɗakina na gabatar da magariba na dawo falon.
*****
"Ko ka kirani na yi serving ɗinka."
Na faɗa ina zama kan dinning ɗin.
"Ah bakomai, har baƙuwar ta tafi?"
Ya tambaya, na gyaɗa masa kai sannan na ce.
"Ta tafi wai amma zata dawo, ni ba ma so nake ta dawo ba, nasan kai baka fiya son mutane suna zuwar mana ba. Zan ma taka mata burki."
"Nina faɗa miki? kawai dai akwai waɗanda ban yarda dasu ba ne."
Legendspen
08129553971
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na sha takwas.
(18)
"Su waye baka yarda da su ba?"
"Nana kenan? Ni wannan ma duk da ba wani kallo na yi mata ba amma tabbas tafi ƙawayenki da yayyunki da yawa kalal nutsuwa."
Haka kawai na ji ta kwantamin a raina sakamakon abinda Sardauna ya faɗa, daman kuma tabbas zaman ni kaɗai ɗin ya isheni na gaji da zaman.
"To yanzu ba matsala kenan?"
"Eyh! Ba matsala kam amma dai ba ko yaushe anyhow ba gaskiyya kinsan tsarina."
"Tom shikenan na gode."
Na faɗa ina ci gaba da cin abincin, shima ya ci gaba da ci bayan mun kammala ya kalleni sannan ya ce.
"Na yi wasu abokai anan baya, suna da majalisa ina tunanin zan fara zama ina rage dare kafin mu saba da yanayin unguwar."
"Eyh hakan yana da kyau kam gaskiyya, Allah Ya taimaka."
Na faɗa shi kuma ya tashi ya shiga ɗaki, can ya fito bayan ya ƙara gyarawa ya fice.
Daga wannan rana kullum Sardauna sai ya fita majalisar nan, baya dawo sai goma ta gota tun bana jindaɗin zaman har nasaba, Bilkisu kam ba ta sake zuwa ba tun ranar ba gaba ɗaya na damu, har na fara tuanin ko sardauna ne ya dakatar da ita sai kuma na tuna kwata kwata basu haɗu ba tin da ya shiga ɗaki bai fito ba sai da ta tafi. Sai da aka yi sati biyu sannan ta sake zuwa, ranar na yi murna kamar na cinye ta, haka itama ta dinga biya min mun hira sosai kuma na ji daɗin zama da ita sosai da sosai, tun daga wannan lokacin ta fara zuwa duk da ba ko yaushe ba, babban abin daɗin Sardauna bai taɓa yi min ƙorafi akan zuwa na ta ba, duk da wani lokacin su kan haɗu.
Na yi mata maganar rashin haihuwata, ta ƙara ƙarfafamim gwiwa tare da ba nj hakuri akan hakan, da cewa na dage da addu'a, babban abinda ya burgeni da Bilkisu shine karatunta ta ti degree a yanzu ma ta ɗaura masters sannan tana yin aiki, mace mai ilimi daban ce, komai na ta gwanin ban sha'awa akwai tsari, ban taɓa zuwa gidansu ba, amma ina yawan ce mata zanje idan na fita.
A ɓangaren Turaki har yanzu auren shiru, sai dai kawai na ji mostintsa idan ina falo amma bai taɓa shigowa ba kuma ko a waje bamu taɓa haɗuwa ba, da muka yi magana da Ra'is ta wayar Hajiya ya ce da ni wai Turakin nema yake nemansa a waya lokaci zuwa lokaci ya ji lafiyarsa da ta mutanen gidan.
A tsakanina da Sardauna abubuwa suna tafiya yadda suke, kawai dai kwana biyu ya ƙulla sabuwar abota da wayarsa da kuma zuwa majalisa, wanda a yanzu ya ɗan rage bai cika fita kullum ba.
Yau tum safe na kammala aikina, dan mu yi da Bilkisu zan koya ma ta yadda ake Samosa wrap, ta ce tana so kuma ta ga ina yi yawan yi tasan dole maza suna so.
Ina tsaka da aikin gida ta shigo, daman ta ce yau gudun wajen aiki za ta yi, murmushi na sake sannan na ce.
"Har kin ta so?"
"Na dai gudu, ai yau sai na koyi abin Samosar nan, har da wasu kayan fulawar tunda nima na kusa aure."
Murmushi na sakar mata sannan na ce.
"Ke ce muna da shan biki."
"Ke ba wanda nake kulawa, kawai ma faɗa ne."
"Wai damam ina ta so na tambayeki me ya sa bakya kula maza ne, ba ayi miki zancen aure a gida?"
"To Nana ai aurw lokacine, bazan iya biyewa namiji ba inda ba na aure ba, dan ba duka ba ne suke da kirki, yanzu zai yi miki SARTSE a rayuwarki indai namiji ne."
"Amma nikam Alhamdulillah wallahi, miji dai na yi da ce."
Na faɗa ina shiga cikin kicin, bayana ta biyo tana faɗin.
"Ga alamu nan dai, muma idan mun sami irin nakun sai mu aura, amma wa'yanan samarin shawon ba dani ba."
Na tuntsire da dariya sannan na ce.
"Lallai fa Samarin Shawo."
Haka muka shiga ina yi tana kallo tana 'yan tamnayoyinta har muka kammala. Daga nan muka dawo falo muka shiga hira tana nan har yamma sannan ta tafi.
Haka rayuwata ta yi ta tafiya, yau daɗi gobe akasin haka, abubuwa suna tafiya wasu yadda aka tsara wasu kuma ba yadda aka tsara ba, tsakanina da Sardauna kullum sabuwar soyayya, sabuwar biyayya, a kullum Sardauna yana farin ciki tare da yin alfahari da ni. Yana yawan ce min.
"Nana kin yi min komai a rayuwa, Allah Ya bani ikon faranta miki rai."
Ni kuma a kullum duk wata sabuwar na'uin biyayya yi wa Sardauna nake, wani abu ni a kaina na kan ji kamar ya zarci hankali, dan a yanzu takai idan Sardauna yana kan kujera ni a ƙasa nake zama, sai ya dage min nake zama akan kujerar ko na ga ya sauko ƙasa.
08:30pm.
Zauna nake a falo, hankalina yana kan wayata dan nasan Sardauna yanzu ba lokacin dawowarsa ba ne.
"Hon!"
Kamar daga sama na ji muryarsa.
"Kawo min abinci."
Ya faɗa yana nufar kan gadon, a tsorace na tashi gabana ya na faɗuwa, me ya sami Sardaunana haka?
A yanayinsa ma kamar cusa abincin yake dan kamar baya jindaɗi.
"Me ya faru dan Allah."
"Bakomai."
Ya faɗa yana ci gaba da abincin, yana cikin ci ya tashi ya shige ɗakinsa, ba shiri nima na bishi ciki amma kafin na je ya kulle ɗakinsa.
"Innullahi wa'inna illahir raji'un, me ya faru dan Allah, Ya Allah Ka kawo wa Sardauna na sauƙi."
Na faɗa ina komawa falon, sai dai gaba ɗaya na rasa abinda zan yi tunaninma na kasa, halin da Sardauna yake ciki ya dameni, Whatsapp na duba naga Bilkisu na online, na tura mata message
" 'yar uwa da matsala." Na haɗa mata da emoji na kuka, cikin ƙasa da minti ta dawo min sa amsa.
"Sisi me ya faru?"
"Sardauna ne ya dawo gida da damuwa."
"Me yake damunshi?"
"Bai faɗan ba wallahi."
"To me kike da baki tambayeshi ba, Nana kije ki tambayeshi mana, a shawarar da nake baki a kullum ina faɗa miki ki mayar da damuwar mijinki taki."
"Ya kulle ɗakin."
"Toopa, gaskiyya wannan babbar matsala ce, ko dai zuwan da na yi ɗazu ne?"
"Anya kuwa, Sardauna baya son mutane su zo amma ke bai taɓa min magana akanki ba."
"Ikon Allah."
Ta haɗo da emoji na mamaki.
"Yanzu mene abin yi?"
"Abin yi kije ki tambayeshi mene, ki yi amfani da duk wani ikon da ƙarfinki wajen ganin kin magana ce mai damuwar tasa."
"Na gode 'yar uwa."
Daga nan na kashe data ta na kwanta, ina ta faman saƙe saƙe har bacci ya ɗaukeni, washe gari da safe bayan na yi duk wani abu da nasaba, amma Sardauna har wajen ƙarfe tara bai fito ba, ina nan zaune akan a falo ya fito da shirinsa, da sauri na tashi tare da faɗin.
"Ina kwana?"
"Lafiya, ya kike?"
"Alhamdu Lillah, ga abin breakfast nan."
"Nana bazan iya cin abinci ba, ina cikin damuwa ki yi haƙuri."
"Me yake damunka dan Allah, ka faɗa min ka ji."
"Nana ina cikin damuwa kawai, ki yi haƙuri."
"Yanzu akwai damuwar da bazaka faɗan ba a matsayina na matarka dan Allah?"
"Ba haka ba ne Nana, ki yi haƙuri zuwa na dawo kinji."
Yana faɗin haka ya fice, ya barni tsaye kamar wacca aka dasa, na kusa minti goma sannan na sami waje na zauna, haka na shiga damuwa gaba ɗaya ko breakfast ɗin nima ban iya ba, sai wajen sha biyu na rana na iya sa abu a bakina, daga nan na dawo kan kujera na ci gaba da zaman damuwa, sai ƙarfe biyu Bilkisu tazo bayan ta dawo daga ofis, ta yi mamakin ganin yadda na rame ma fige duk a iya rana ɗaya.
"Nana haka kika damu da Sardauna? Duk akansa kin wani canja hala ji fa?"
"Bazaki gane ba Bilkisu, wallahi ina son mutumin nan sama da kowa, sama da komai a wannan rayuwar, bana so na ga wani abu guda ɗaya da zai dami Sardauna a duniya, bana son shi wallahi."
"Lallai Nana, to yanzu me ya ce miki yana damunsa?"
"Ya ce sai ya dawo."
"Allah Ya sa alheri ne, Allah Ya sauƙaƙa al'amuran."
"Amin amin."
Haka tai ta yi bani shwarwrin hamyoyin da zan bi na yi maganin damuwar tasa da yanda zan kwantar mai da hankali, na nuna komai zai zo da sauƙi, sai yamma ta tafi kamar ko yaushe.
Tana tafiya na yi wanka na gyara gidan, bayan na yi sauƙaƙƙen abinci na dawo na zauna, ina nan zaune na ji hayaniyar mutane. Labule na ɗaga na buɗe Turaki na gani yau ma kaya ake shigo masa da shi, da alama yau ya dawo dan dama na ji alamun baya gidan, komawa na yi na zauna akan kujera na ci gaba da tunanin yadda zanyi kwantarwa da Sardauna hankali yana dawowa.
Sai wajen tara sannan ya shigo gidan, babu damuwar a fuskarsa kamar jiya, amma bayan na shiga ɗaki na fito na ganshi ya haɗa lai da gwiwa, da sauri na ƙaraso inda yake tare da cewa.
"Sardaunana, jarumina, Honey me ya faru?"
"Nana! Bansan ta inda zan fara yi miki bayani ba, amma tabbas akwai matsala."
"Wace irin matsala ce haka dan Allah?"
"Nana su Big Daddy da Hajiya ta sun matsamin wai suna ganin jikokinsu na wajena, wai shirun ya yi yawa, Nana duk bayanin da yakamata na yi musu, amma su kasa fahimta, faɗi kawai suke duk inda matsalal take na nemo to na yi maganinta, Nana na shiga damuwa matuƙa na rasa abinda zan yi shi ya sa kika ga na damu kwana."
Shiru na yi nima kaina na rasa abinda zan faɗa, matsalal daga ina take, me ya kawo duka wannan zancen?
"Kinji abun wani kala ko?"
Na gyaɗa kai, sannan na ce.
"Yanzu mene abun da za ayi?"
"Ni kaina bansaniba, ina ta faman tunani."
"Allah Ya sauƙaƙa mana."
"Amin Honey nah."
Haka muka zauna jigun jigun gaba ɗaya na rasa abinda ke mun daɗi, me ya kai 'yan uwan Sardauna wannan zancen? Su da suke wayayyu, 'yan boko masu ilimi, amma zasu zo da wannan zancen?
"Kar ki sakawa ranki damuwa kinji Hon, komai zai zo da sauƙi."
"Nasani." Na faɗa tare da yi masa murmushin yaƙe, sai yanzu na ji ina ma ina da halin kiran su Hajiya na faɗa musu, gaba ɗaya rabona da su an kusa wata guda, Sardauna duk ya hanani.
Ko da muka je bacci ma haka kowa ya kwanta, ransa babu daɗi, ni barcin ma rabi da rabi na yi, Sardauna ne daman shi duk girman damuwa ba ta hanashi bacci, ni kuwa ko ya damuwa take mussamman ta al'amarin Sardauna to ba ni da wata nutsuwa akai.
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na sha tara.
(19)
Gaba ɗaya Sardauna ba walwala ya yi komai har ya fice, a yanzu ba ni da kowa na kusa sai Bilkisu ita kaɗai nake magana da ita, itama sabida mijina ya zaɓe ta, kiranta na yi a waya duk da nasan tana wajen aiki, har ta ƙaraci ringing ɗinta ba ta ɗauka ba, sai da na kira sau uku sannan ta ɗauka.
"Hello Nana, ya aka yi ina ofis ne."
"Bilkisu akwai matsala ne babba ba ƙarama ba."
"Ta mece? Me yake damun Sardaunan?"
"Matsalal daga gidansu take, akan zancen haihuwa ne."
"To ai Nana ba ke ce me matsalal ba ko? Kamar kince min kin taɓa ɓari ko?"
"Eyh na taɓa, nice me matsalal, wai mahaifata ƙarama ce, shi ya sa jariran basu fiya zama ba."
"Innullahi yanzu Nana mene abun yi?"
"Wallahi Bilkisu bansaniba, duk na shiga damuwa, mussamman ganin Sardauna da na yi a yanayin damuwa."
"Ai ba daɗi irin haka, ki lallaɓashi ki ji ko akwai wafa mafita da yake gani, yau bazan shigo ba sabida zani unguwa amma zan zo a satinan."
Daga haka ta kashe wayarta ta barni cike da damuwa. Ina nan zaune na rasa abinda ke min daɗi, kawai na kira Ra'is bayan mun gaisa na ce da shi.
"Ra'is akwai matsala a gidana."
"Ta mece ba dai mijinki ba."
"Shine Ra'is."
"Lallai Nana, ke kenan bamu da amfani sai matsala ta taso tsakaninki da mijinki shine mule da rana, ba kyajin kunya sai ki tunkare mu idan kuma kuna cikin soyayya babu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 16