Share this page
mamakin yadda aka yi baya son karatu har haka, kuma gasu gidan 'yan boko? Ni kaina abun ya ɗaure min kai sosai da sosai. 'yanzu Sardauna ya sake ni ina na kama ni Nana, zan iya rayuwa ba na jin numfashim Sardauna a kusa da ni kuwa?.'  Irin tambayoyin da nai ta jefawa kaina kenan har zuwa yamma, ko ayyukan gidan bansami damar yi ba sai da yamman, ina cikin aikin su Yaya Radiya da Yaya Ridwan da Ra'is suka zo, nasan akan maganar ne sabida ba sa so Alhaji ya san da maganar, ni kam Allah Ya gani karatun ya sauka daga kaina, amma an sauke min shi haka na ji, kalmar saki ta girgizani.  "Wai dagaske kike sakinki ya ce zai yi?"  Yaya Radiya ta faɗa cike da ruɗewa, bayan na gama gaya mata abinda ya ce da ni.  "Wallahi Yaya, sai na ji gaba ɗayan na tsorata."  "Kuma kina ganin dagaske yake?"  Ra'is ya tambaya.  "To nima bana ce ba, amma fa yau ko magana ba mu yi da shi ba, kawai ya ce duk abinda na yanke ya yi daidai."  "Amma mijin nan naki ɗan iska ne, bai da mutunci." Ra'is ya faɗa, na watsa mai harara, sannan na ce.  "Bana ciki da iskanci."  "Ridwan mene abun yi yanzu?"  Yaya Radiya ta tambayeshi.  "Ya bata zaɓi biyu, ko ta yarda da karatun ta rabu da shi, ko ta zaɓeshi ta rabu da karatun farin cikin iyayenta, tun a farkon mu'amalal su Nana ita ce ta bada kanta, na faɗa karta ta sawa ranta wai alfarma zai yi mata kowani abu. A gani na farko da na yi musu tare na gane soyayyarshi ta yi wa Nana mugun kamu, sannan ta bada kanta, ta zubar da darajarta, ina mugun jin kishin wannan abun? Ƙin kulashi ko shiga al'amuran da naƙi yi ba wai son shi ne bana yi ba, a'a zallan kishi ne bazan iya jurar gani tana ƙasƙantar da kanta ba, a matsayina na ɗan uwanta, jininta Nana kina tunanin wai idan muna yi wa samarinku wani abun haushi ne ko tsana? Tun a lokacin abinda na guda mata kenan, amma bata gane ba, a yanzu idan ta takura wallahi tsaf zai iya sakinta, ya mayar da ita ƙaramar bazawara ya cuceta."  Wani irim tsoro ne ya ratsani, ace Sardauna zai iya sakina, bana fatan wannan ranar wallahi na haƙura da karatun, ba zan ba chaɓ.  "To yanzu mene abun yi? Shikenan duk wani burin Alhaji ya tashi a banza, shikenan?"  Yaya Radiya ta faɗa, ni kam a raina ma ce. "Alhaji zai fahimta, zuciyar Alhaji tana da ƙwari zata iya ɗaukan hakan, ni kam bazan iya ɗaukan ƙaddarar rashin Sardauna ba."  "Nana me kika yanke?"  Yaya Radiya ta tambayeni.  "Na haƙura wallahi, na fasa karatun bazan iya ba." Na faɗa ina zubar da zafafan hawaye, ni kaina nasan ba abinda ke cikin zuciyata ba ne, amma bani da wani abun yi da ya wuce wannan.  "Kin haƙura da karatun fa Nana?" Ra'is ya faɗa, na gyaɗa kai sannan na ce.  "Ra'is ya zanyi, tunda ba ya so kuma ya riga da ya aureni ba yadda zan iya." "To sai me dan ya rabu da ke? Sai me?"  "Ra'is ba zan iya ɗaukan ƙaddarar rabuwa da Sardauna ba, zuciyata tana da rauni."  "Amma ai zaki iya ɗaukan ƙaddarar rashin mahaifinki ko?"  Yaya Radiya ta faɗa tana miƙewa, Yaya Ridwan ya ce.  "Abinda na faɗa muku kenan, tana yi masa mugun son da mu kammu ba ta ganin a matsayinta mutane, idan aka haɗa mu da shi."  "Nana namiji kina tare da iyayenki ma ya kuka ƙare, bare kuma kin ce kin zaɓeshi akan kowa da komai, ban ce ki kashe aurenki ba, kuma bazan baki shawara akam hakan ba, amma ko ya ne ki nuna masa iyayenki na da daraja a wajensa."  Yaya Radiya ta faɗa tana miƙewa, duka suka miƙe Yaya Ridwan ya kalle ni sannan ya ce. "Nana, Allah Ya shiga al'amirinki ya kawo miki mafita, da haske amma tabbas kina cikin duhun soyayya, ina guje miki lokacin da Sardauna zai fama miki SARTSEN da ya yi miki, dan tabbas Sardauna ya yi miki SARTSE a zuciya, ba zan miki baki ba, amma tabbas bazaku kwashe ƙalau da shi ba."  "Shikuma Allah Ya isa tsakaninmu da shi, dan tabbas ya cutar dake, wallahi Allah sai ya saka mana."  Ra'is ya faɗa, daidai lokacin Sardauna ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, sai da ya ƙaraso inda suke sannan ya ce.  "Kunji kunya, dam girmanku kunzo kuna son kashe mata aure, mussamman ke."  Ya faɗa yana nuna Yaya Radiya, sannan ya ce.  "Kin kashe naki auren shine zaki kashe mata nata, ki zauna ke ba aure ita ba aure kuna yawo a unguwa daga nan ku ɓige da bin maz..."  Bai ƙarasa ba Yaya Ridwan ya sa hannu ya bige masa baki, har sai da jini ya fito, sannnan ya kama kwalarsa ya fara magana ya na wuci.  "Malam ka kama kanka, ka iya bakinka kafin na zubar ma da haƙwara wallahi Allah, ita dai da ka juyarwa da tunani ka je can, amma wallahi baka isa ka ce zaka gayawa wani magana ba a wajen nan."  Sardauna ya yi murmushi sannan ya ce.  "Na ji na juyar mata da ƙwaƙwalwar, ku yi abinda zaku yi idan zaku iya karatu ne wallahi ba za ta yi ba, dan na fusknci kai dayyus ne bakasan kishin kanka ba, bare kasan na wani, kuma ku fice mim daga gida, kar nasake ganin ƙafar wani cikinku, dabbobi."  Hawayene suka fara zubowa daga cikin idanuna masu ɗumi, gaba ɗaya na rasa abinda ke mim daɗi, me ma ya sa suka zo, me ya sa Yaya Ridwan zai dake shi?.  "Ba zamu sake zuwar ma gida ba, duk da cewa 'yar uwarmu na cikin gidan."  Yaya Radiya ta faɗa tana ficewa, Ra'is da Yaya Ridwan suka bi bayanta, nima na bisu da gudu ina faɗin. "Yaya ku tsaya dan girman Allah."  Amma babu wanda ya jiyo cikinsu, haka suka kaɗa kai suka tafi su ka barni ina faman zubar da hawaye. Ko da na dawo falon Sardauna baya nan , ban kuma nemeshi ba na shige ɗaki na hau kiran layinsu amma babu wanda ya ɗauka, har wajen ƙarfe goma babu Sardauna babu alamunshi, haka na kwanta bacci. Washe gari da safe ban iya ta shi da wuri ba, sabida ban samu bacci da wuri ba, karar bugun ƙofar da ake yi min ce ta tashe ni.  "Hon! Buɗe ƙofa."  Ƙafafuna na sauke daga kan gadon sannan na nufi ƙofar na buɗe, ban ko kalleshi ba na yi hanyar ban ɗaki.  "Ina zaki?"  "Wanke fuska zan yi."  "Okay ki yi sauri."  Bayan na wanke fuskar na ɗaura alwala na fito, kasancewar lokacin bana sallah ya ƙara ba ni damar mimiƙewa ina baccin.  "Zo.. ina da wani abu na baza ta."  Ya faɗa yana kama hannuna muka fito falo.  "Muje mu fara breakfast to."  Ya faɗa yana nuna min wajen dinning, da mamaki na kalli wajen sannan na ce.  "Waye ya yi girkin?" "Hon ai na iya girki sosai, muje ki ji."  Na nufi dinning ɗin, ya ja min kujera na zauna ya shiga zuba min, gasashen biride da ƙwai sai kuma shayin Na'a na'a. Komai ya yi daɗi sosai haka na ci ina mamakin yadda aka yi duk zaman nan Sardauna bai taɓa ce min ya iya girki ba.  Ina cikin ci ya tashi. "Hon ina zuwa." Ya faɗa tare da barin wajen, kusan minti uku sannan ya dawo hannun sa riƙe da wani ƙaramin kwali mai kyau.  "Hon, canki mene anan?"  Na yi murmushi sannan na ce.  "Mene?"  "Kin bani gari?" "Uhm na baka."  Aikuwa ya buɗe kwalin, kyakyawar sarƙa ta bayyana wacca aka yi ta da zinare sai sheƙi take.  "Hon naki ne."  "Wow, na gode."  Na faɗa bakina ya kasa rufuwa, ɗauka ya yi ya gwada min a wuyan, aikuwa ta yi kyau ta hau ɗas da ita kamat a wuyan nawa aka ƙera ta.  "Na gode."  Na sake faɗa.  "Akwai wani ta so." Ya faɗa yana kama hannuna.  "Hau na goyaki."  Ya faɗa yana sunkuyawa, aikuwa na hau ya ɗaukeni zuwa waje, bai sauke ni na  sai a harabar gidan.  "Kinga."  Ya faɗa yana nuna min wata ash ɗin mota. "Wow ta yi kyau wata ka sake siya."  "Eyh, amma wa ke, ta kice Hon."  "Ni.. tawa?"  Na faɗa cike da ruɗewa, ban taɓa hango kaina da mota ba a rayuwata, amma sai ga shi yau Sardauna ya bani, kai ina son Sardauna.  "Ko ba kya so?"  Na yi murmushi, sannan na ce.  "Na gode mijina, na gode Allah Ya biya ka da aljanna, Allah Ya ƙara maka arziƙi duniya da lahira."  "Amin Honey, na gode da soyayyarki a gareni, na gode sosai da sosai, muje ciki mu yi magana."  "Tom."  Na faɗa tare da binshi ciki, ya zauna akan kujera ya jawo ni kusa da shi, ya kura min idanu cike da wani irin tausayi na mussaman, ya fara magana cikin sanyin muryar tamkar mai shirin yin kuka.  "Nana, kin san me ya sa nake yin dukkan waɗannan abubuwan? Kin san dalilin da ya sa nake ƙoƙarin killace ki? Saboda Kishi ne, Nana. Kishinki nake yi fiye da yadda kike tunani. Duk lokacin da kika fita kika tafi wannan karatun na wahala, zuciyata ba ta samun natsuwa. Ina ganin kamar kowane namiji da kika bi ta gabansa, kallon sha'awa yake miki. Ba zan iya jure ganin wani namiji ya kalli kyakkyawar fuskarki ba, ko ya ji muryarki." Ya sauke numfashi, ya ɗago ya kalleni tare da matse hannuna dake cikin nasa.  "Wannan karatun na nan... Nana, wahala kike sha a banza. Kalle ki, yadda kika rame, yadda kika fita a hayyacinki saboda shiriritar malaman nan da ba sa ma san abin da suke koyarwa. Nana nasan ba kya gane komai, lokacinki kawainkike ɓatarwa, ni kuma bana son naga kina shan wahala. Shin darajar matar Sardauna Ta Ambo ita ce ta riƙa bin layin motar haya ko ta riƙa shiga aji ana cakuɗawa da ita? A'a, Nana. Matsayinki ya fi haka." Ya kamo hannuna ya ɗaura a kan saitin zuciyarsa, sannan ya cigaba "Nana, kalle ni cikin idanuwa na. Kin ga wannan motar? kin ga wannan zinaren? Duk ba komai ba ne a wurina idan aka kwatanta da darajarki. Ina son ki zama sarauniyar da ba ta taka ƙasa, sarauniyar da duniya za ta kalla ta san tana ƙarƙashin inuwar Sardauna Ta ambo. Nana a yanzu ina so na baki umarni, umarnin da nake son ki bi, ki je ki sami Alhaji. Ki gaya masa cikin lallashi cewa kin fasa wannan karatun na wahala. Ba wai kin daina ba ne, a'a ki gaya masa cewa ni Sardauna zan tafi ƙarin karatu a Turai, kuma na yanke shawarar tafiya da ke can. A can za ki yi karatu a manyan makarantun duniya, inda ba za ki sha rana ba, ba za ki fuskanci cin mutuncin malamai ba. Ba zaki yi karatu a wahala ba, can ne ya dace da matsayin matar Sardauna. Amma yanzu, kin daina ɓata lokaci a nan. Ki gaya masa kin gaji da wannan, kin fi son ki huta kafin mu tsallaka can ƙasar waje." "Nana, kina tunanin zan yaudare ki ne? Ni ne fa masoyinki. Idan ba ki bi maganata ba, za mu rasa wannan damar ta tafiya can tare, Nana ki amince da ni, sama da kowa, dan babu mai ƙaunarki kamar ni." Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha huɗu.     (14)  Na yi shiru har ya kammala, tabbas komai Sardauna yake faɗan gaskiyya ne, bai taɓa yi min ƙarya ba, kuma nasan bazai yaudareni ba, tun da da zai yaudareni ai da bai aure ni ba. Na buɗe baki yi zan yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga yana faɗin.  “Sister Memah, ya sauka?”  Da ke wayar tana handsfree na ji ta ce da shi.  “Yeah! Kuma yana zama maganarku kai da Turaki ya fara, an sanar da shi faɗan da kuka yi last time a company, ya ce duka yana nemanku.” “My god! Big Daddy akwai faɗa yanzu shikenan zan kira anjima thanks you.”  Ya faɗa tare da kashe wayar, sannan ya juyo ya kalleni.  “Ina saurarenki.” A hankali na fara magana, cike kulawa da soyayya.  “Na yarda da kai Sardauna, na yarda baza ka taɓar cutar da ni ba, na baka ragamar rayuwata gaba ɗaya, zan yi amfani da ƙarfina da lokacina wajen sama maka farin ciki, zanje na sami Alhajin.”  Ban ƙarasa ba na ji ya rungumo ni jikinsa, tare da faɗin.  “Good girl, tare zamuje umara this year in sha Allah, i love you Nana.”  “Love you More Hon.”  Daga nan muka shiga lamarin soyayya, yinin ranar Sardauna kamar zai mayar da ni ciki, haka yake kula da ni, ko girki ba mu yi ba fita muka yi muka ci daga nan muka biya shopping duka a sabuwar motata, har ya fara nuna yadda ake tuƙi.  Gaba ɗaya na manta da wani abu ya faru jiya tsakanin Sardauna da ‘yan gidanmu, hankalina yana kan mijina ban nemesu ba, suma basu nemeni ba. Haka kusan sati guda sannan Sardauna ya ce da ni gobe zan je gidan.  ****** Shi ya sauke ni, amma bai shiga gidan ba ya tafi ya ce da ni idan ya dawo zai shigo,  shiga ta gidan na tarar da Yaya Ridwan zai fito.  “Ina yini?” “Lafiya.” Ya amsa bai ko kalleni ba, haka na shiga gidan jikina ba ƙwari, Hajiya ce a tsakar gidan tana ganina ta washe baki da faɗin.  “Zuwa ba sanarwa.”  Na durƙusa kasa na ce.  “Hajiya ina yini?”  “Lafiya ƙalau Nana, ya gida da me gidan” “Lafiya ƙalau Hajiya.”  Na amsa tare da shigewa cikin falonta, sai bayan na zauna ne na ce.  “Hajiya ina Yaya Radiya, da Ra’is?” “Radiya ta je makaranta wai za ta yi screening, Ra’is kuma yanzu na aiki shi siyo salat, baki ga Ridwan ba ne?”  “Mun gaisa Hajiya, kinsan halinsa.”  Murmushi ta yi tare da faɗin.  “Bari na sauke miyar nan.”  Ina nan zaune Ra’is ya shigo daga siyo salat, bai nuna mamakin ganina ba kuma bai nuna ɓacin rai ba, bayan mun gaisa Hajiya ta zuba mana abinci muka ci abinci, bayan Hajiya ta tashi ne Ra’is ya ce.  “Ya zancen makarantar?”  “Bawani labari Ra’is a yanzu har an fara jarrabawar zango na farko ma, na zo ne kawai na faɗawa Alhaji na ji abinda zai ce.”  “Allah Ya kyauta.”  “Me ya faru?”  Hajiya da ta shigo ta faɗa.  “Mijinta je ya hanata komawa makaranta, gashi har an fara jarrabawa.”  “Innullahi wa’inna illahir raji’un, garin ya? Me ya faru?”  “Wallahi Hajiya haka kawai, har Yaya Ridwan ya masa magana da Yaya Radiya ƙarshe ya yi mana rashin arziƙi.” “Hajiya Yaya Ridwan fa fasa masa baki ya yi.”  Na faɗa kamar zanyi kuka, da mamaki ta kalleni.  “A yaushe a ka yi haka?”  “An kwana biyu.”  “Amma babu labari.”  “Ai ni na yi tunanin ma sun faɗa muku, ni kuma gudun ɓacin ran Alhaji yasa mana na ja baya da zuwa.”  “Amma bai kyauta ba, to yana da wani dalili ne?”  “Eyh Hajiya, yana da dalilinsa mai ƙarfi ma, kuma ya ce da ni ƙarshen shekara zamu tafi turai, zai sama mini wata makarantar acan.”  “Tom Allah yasa, yawwa Nana ina fatan dai ba haɗa baki kukayi da mijinki ba, kika sha wani abu da zai hanaki ɗaukan ciki ba ko? Abun shiru ya yi yawa.”  “Eyh Hajiya ba abinda nake sha, nama je asibiti an bani magani ina sha.”  “To Allah Ya duba lamarin.”  Na amsa da Amin, sai yamma Yaya Radiya ta dawo, ko da na faɗa mata sai ta ce ita babu ruwanta da al’amurana. Yaya Ridwan kam bai ma sake kulani ba, sai yamma Alhaji ya dawo wanda daman ya saba dawowa a wannan lokacin sai ya koma gab da magriba.  Ya yi murnar  ganina sosai da sosai, mun gaisa dashi bayan ya shiga ɗaki na bi bayanshi, na iske shi yana duba wasu takardu. Na zauna a ƙasa, jikina duk babu daɗi haka nake ji na, bayan na zauna na fara wasa da yatsun hannuna yayin da zuciyata ke bugawa da sauri. Alhaji ya kalleni cike da kulawa, sannan ya ce.  “Nana, lafiya na gan kin biyo ni? Ko Akwai wata damuwa ne?" Cikin rawar murya na fara magana.   "Alhaji... dama... maganar karatuna ce. Na zo ne na roke ka alfarma." Alhaji ya gyara zama, fuskarsa cike da mamaki.  "Ina jinki Nana. Mene ne ya faru?" “Hon, idan kika je har kuka zaki yi masa, sannan karki kuskura ki nuna masa ni na tursasaki.”  Kalaman Sardauna suka dawo raɗau a kunnena, a hankali na fara fitar da ƙwalla daga idona, muryata ta fara rawa.   "Alhaji, don Allah ka yafe min, amma gaskiya na gaji. Karatun nan na nan... naga kamar wahala kawai nake sha, kuma gaskiya ba na gane komai. Kullum ina cikin fargaba, gashi kuma kishin Sardauna ya sanya ba na samun natsuwa. Yana yawan nuna min yadda yake damuwa idan na fita cikin maza a makaranta."  "Nana, me kike fada haka? Karatun da kika dage a kai shi ne yanzu kike cewa kin gaji? Ko Sardaunan ne ya hana ki?" Na tuna da  kashedin Sardauna, aikuwa na yi saurin kare shi.  “A'a Alhaji, ba shi ya sanya ni ba. Tausayina ne yake ji, sannan kuma yana da kishi sosai. Shi kansa yana so na yi karatu, amma ya ce ba zai bari na sake yin wannan wahalar ta nan gida nigeriya ba. Alhaji, Sardauna ya riga ya kammala shirinsa na tafiya Turai domin ƙarin karatu, kuma ya ce da ni zai tafi. Ya ce a can ne zan yi karatu mai kyau, a cikin nutsuwa da daraja, inda babu wanda zai rika kallo na ko ya shiga rayuwata." Na ƙara narkar da murya.  "Don Allah Alhaji, ka bar ni na ajiye wannan na nan. Na yi maka alkawari zan yi a can idan mun tafi. Shi Sardauna ya fi son na huta yanzu, na shirya wa tafiyar mu ta can gaba. Gani nake idan na nace akan wannan, zan ɓata masa rai, kuma ba na so na saɓa masa tunda kishinsa ne ya sanya shi yake son ya kiyaye ni." Shiru Alhaji ya yi na kusan minti biyar, har sai da na ɗago na kalleshi sannan ya ce.  “Kina ganin baki takura ba?”  “Ta takura Alhaji.”  Ra’is ya faɗa yana shigowa, sannan ya sake maimaita abinda ya faɗa.  “Alhaji wallahi duk abinda ta faɗa karanta ma ta ya yi, baya son ta yi karatun kwata kwata, tun kafin yanzu ta faɗa mana kuma har can muka je muka same shi dukan mu, dan ya fahimce mu amma ya yi mana barazanar sakinta idan muka takura.”  Alhaji ya ɗago y kalleni, yadda nake kuka ya bashi tausayi.  “Barazanar saki ya yi miki?”  Da sauri na girgiza kai na ce.  “A’a ƙarya yake Alhaji.”  “Ke dai kike ƙarya, amma dai ba ni ba.”  “Ra’is, ka tabbatar da abinda ka faɗa?” “Na tabbatar Alhaji.”  “Nana yanzu kin zaɓi miji akan kowa naki?”  “A’a Alhaji, bana so ya sake ni wallahi, Alhaji bana son ya rabu dani, ina son sa bazan iya jure rashin sa ba.”  Shiru ɗakin ya yi kusan minti goma, sannam Alhaji ya ce.  “Shikenan Nana je ki, Allah Ya yi miki albarka.”  Na miƙe tare da amsawa da Amin, haka na dawo falo na ci gaba da kukana, Hajiya dai ba ta ce dani komai ba haka Yaya Radiya, sai gab da magriba Sardauna ya kirani a waya ya ce da ni ya dawo.  “Ba zaka shigo ba?” Na faɗa masa muryata ba ƙwari, ya kashe wayar ya shigo, da Hajiya kawai suka gaisa tun da Alhaji ya koma, Ra’is yabi shi shago, Yaya Ridwan kam ko kallo bai ishe shi ba bare Yaya Radiya ta bata ma fito ba.  Ko da muka koma Sardauna bai tambayeni yadda muka yi da Alhaji ba, nima bansanr da shi ba. Sai washe gari yake sanar da ni, Wai Big Daddy ya basu gida shi da Turaki kuma gidan guda ɗaya ne amma part biyu ne kuma ya ce dole mu koma can, shima Turakin dole ya zauna acan idan ya yi aure. Ni bai dameni ba ko a jikina hankalina na bai kan komawa gidan, tunanin Alhaji kawai nake yi, bayan kwana biyu da na kira Hajiya take sanar da ni baya jindaɗi, gaba ɗaya na shiga damuwa ta dole na sa Sardauna ya kaini gida, na yi ta yiwa Alhaji kuka.  Sai da na yi zuwa uku a jinyar ta shi, har Allah Yasa ya warke, tun zuwan da ‘yan uwana suka yi gidana babu wanda ya sake zuwa har yau sai da Ra’is ya zo sanar da ni rashin lafiyar Alhaji.  Mun ci gaba da zuwa wajen Dr Ɗan Adala, yana ɗorani akan magani amma har yanzu haihuwa shiru, Sardauna yana ta shirye shiryen komawarmu sabon gida, ya hana duk wasu ƙawayena zuwa, ‘yan uwana kam dama ba wanda zai zo ko baice ba, gashi bana fita ko ina daga gida sai gida.  Bani da wani abu da nake yi sai kula da mijina, a kullum burina na yi abinda zaj faranta masa, son shi nake kamar raina, bana son duk wani abu da zai ɓata masa rai. Uwa uba ma tausayinsa da kullum ke cika min zuciya, wata rana bayan anyi refeiling ɗin gas yake sanar da ni kusan dubu saba’in aka yi ya gaji ga kuma yana son ƙara abubuwa na sabon gida, kamar wasa na ce da shi ko zai siyo min gawayi da abun girki na gawayi, ba arufa sati ba sai gashi da buhun gawayi biyu da kurfoti.  Rana ɗaya Hajja ta zo gidana tun daga ranar ba ta sake zuwa ba, sabida ya yi mata nisa gidan. Ranar da ta zo na ga tashin hankali wajen Hajja, har sao da ta fasa min plast ɗin ruwan zafi guda ɗaya, sabida fitina ta dinga yi kin kamar ƙaramar yarinya, kifin gwangwani ta ci ta ci har sai da ta yi amai, ƙarshe ta ci wai mai ƙarni na ba ta kamar ba ita ta zaɓa ba, kwana uku ta yi amma ji na yi kamar shekara uku ta yi. Sai da Sardauna ya zo da police dog gidan ta tafi, wai ita zaman jego za ta yi min tun da naƙi haihuwa. Amma tun da ta ga karen ta kwashe tsunmokaranta tafi Tunda ta tafi ba ta sake zuwa ba har yau. Ina zaune a gida na alfarma da ya ji kayan more  rayuwa amma dani da wadda ke zaune a gidan ƙasa na ƙauye marabar mu kaɗan ce.  Wannan shine asalin labarin.  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha biyar.     (15) Ci gaba. Babu abinda na iya yi har Sardauna ya dawo, ina zaune jigum kamar wacca aka yi wa mutuwa.  “Honey! Me ya faru na ganki so sad?”  Tashi na yi na faɗa jikinsa na fara hawaye, gaba ɗaya ya rikice yana faman tambayata.  “Honey ki faɗa min mana.” Cikin muryar kuka na ce.  “Alhaji ne ba shi da lafiya sosai.” “Ya salam Honey, me yake damunshi haka?”  “Nima bansaniba wallahi.”  “Wa ya faɗa miki?”  “Ra’is, kuma Yaya Radiya ta kirani ban ɗauka ba, ashe faɗamin zata yi, sai yanzu da Ra’is yazo.”  “Ki kwantar da hankali kin ji, gobe zan kai ki.”  Ya faɗa yana zaunar da ni akan kujera. “Ki yi haƙuri kin ji, nima yanzu akwai wani abu da ya taso min.”  “Mene?”  “Big Daddy, bai kyauta min ba, ta dole sai ya haɗani da wancan yaron, ya sami duka labarin abubuwan da suke faruwa, a yanzu ya bamu gida ni da wancan yaron Turaki, ya ce dole mu koma can da iyalan mu mu zauna, gidan part biyu ne wai sabida faɗan da muke yi.”  “To ai nasani, wani abun ya sake faruwa?” “Eyh ya ce a cikin satinan zamu koma.” “Yanzu barin gidan nan zamu yi?”  “Eyh. Haka ya ke so kuma nan da next week.” “To shi Turakin yana da aure ne?”  “Ina yake da aure, yana can sai lalata da ‘ya’yan mutane.”  “Lalata kuma?”  Na faɗa a tsorace. “Eyh mn! Hon ace mutum ya yi wannan girman babu iyali ai kuwa sai dai idan lalata yake da yaran mutane, shekara talatin da ɗaya fa.”  “Talatin da ɗaya!”  Na faɗa cike da mamaki, ya gyaɗa sannan ya ce.  “To kinga kuwa.”  Ni ba zancen turakin yaban mamaki da tsoro ba, illah Sardauna, rufe idona na yi a take na tuna lokacin da na tambaye Sardauna shekarunsa, lokacin da ya zo makarantarmu. Ya ce da ni ashirin da biyar, har na ce irin mijin da nake so kenan, kuma ance shida Turaki ko kwana biyu ne a tsakaninsu ‘shin Sardauna ƙarya ya yi min a wancan lokacin? Sardauna zai iya yi min ƙarya kenan? Ko dai wasa yake min? Gaba ɗaya na ji jikina ya yi sanyi, ina so na tambayeshi amma bana buƙatar ɓacin ransa, ko ya ga kamar ban yarda da shi ba.  “Yau bazaki kwanta ba ne?”  “Uhm uhm zan kwanta mana.”  “Na yi tunanin dan Alhaji bai da lafiya ba zaki yi bacci ba, zaki zauna ki yi ta yi masa addu’a.”  Wani iri na ji a raina, gaba ɗaya a al’amurana ban iya tashi cikin dare na yi addu’a ba, idan ka ga na yi addu’a to bayan kowacce sallar farilla ce, tabbas mahaifina yana buƙatar hakan daga gareni.  “Eyh zan jira ƙarfe ɗaya

Chapter 8 of 16