kamani sai ya ɓallani.
"Nana buɗe min ƙofa."
"Ka yi haƙuri dan Allah."
"Na ce ki buɗen ƙofa zaki zauna kina cewa na yi haƙuri?"
"Karka dake ni dan Allah."
"Bazaki buɗe min ba Nana, na buɗe da kaina sai na ɓaɓɓallaki."
Ba shiri na taso na buɗe ƙofar, na maƙale a jikin bango. Da iya ƙarfin shi ya kamo hannuna ya matse shi sosai, idanunsa har wani hayaƙi ne yake fitowa daga cikinsu.
"Nana! Nana! Nana! Me ya sa kika shiga motar ɗan iskan can? Me ya sa ?"
"Bakomai ka yi haƙuri dan Allah."
"Har wani murmushi kika yi masa? Har ƙamshin turaranki ya ji, ya kama miki hannu ko?"
Da sauri na girgiza kai.
"A'a wallahi, ko kallona bai yi ba."
"Ni zaki yi wa ƙarya, sai na make ki."
Da sauri na runtse idona tare da maƙalewa a wajen ɗaya.
"Ka yi haƙuri dan Allah."
"Me ya yi miki?"
"Bakomai wallahi."
"Bazaki faɗan ba sai na sumar dake?"
"Zan faɗa ma, zan faɗa ma wallahi."
"To faɗamin."
"Babu abinda ya yi min kawai ce min ya yi wai ni da kai mun fara hankali tun da har ina zuwa gida, sai kuma ya ce yanzu saura na makaranta na ce mai tom."
"Uban mene haɗinshi da ke da har zai ce miki saura makaranta, shi uban me ya kaishi unguwar Talakawan nan? Nana daga yau har Abada kar na sake ganin magana guda ɗaya ta haɗaki da Turaki, kin jini?"
"Eyh! Na ji ka."
"Shi kuma sai na ɗau mummunan mataki akansa."
Yana faɗin haka ya fice zuwa ɗakinsa ya barni anan, sai da na yi kuka na na gode Allah sannan na yi wanka na kwanta, dan yanzu Sardauna ba ko yaushe muke kwana tare ba.
Washe gari na tashi da ciwon kai sabida kukan da na yi daren jiya, adaddafena haɗa masa shayi da soyayayyen biredi ya ci, har ya fita ya dawo ya kalleni.
"Nana Har abada bake ba Turaki."
"Tom."
Ya sa kai ya fice, nasan dai asibitin su Bilkisu zai tafi, wai ashe ma ƙanin babanta ne ba shi da lafiya shine duk ya ruɗe, bai fi awa ɗaya sa fita ba ya kirani a waya wai 'yan uwan Bilkisu zasu su yi mata jere acan part ɗin, ban ce masa komai ba bayan tom, ni a yanzu kalaman Yaya Rumaisa nake son zama na baje su a faranti na yi musu filla filla. Amma bansami damar hakan ba sabida kiran da Sardauna ya sake yi min akan lallai na yi wa 'yan uwan Bilkisu abun taɓawa. Ta dole na tashi na shiga kwaɓa musu cup cake, bayan na yi na haɗa musu sa cincin, sabida bana son abun da zai wahalal da ni.
Wajen ƙarfe biyu na ji motoci suna shigowa nasan sune, hakan ya sa na ƙara gyara jikina na fito. Manyan matane masu kyau, gayu da ilimi, kowacce tafiya take cike da izza, sai na ji ma na raina kaina abun da na yi musu. Kowacce ta shigo zata ɗibi iska daga gabas ta watsa yamma, sai na zama kamar wata 'yar aiki, dan ba wadda tabi ta kaina, hakam yasa na tattare jikina na koma ɗaki, sai da suka kammala na ji wata na cewa.
"Ba mutane a gidan ne?"
Fitowa na yi, tare da faɗin.
"Gani."
"Ke kamar ba kya ganin mutane ne?"
Murmushi na yi sannan na ce.
"Na gaisheku tun zuwanku, ganin kamar ba ku kula dani ba ya sa na shige nawa part ɗin."
"Ke 'yar talakawa 'yar mitsiyatan Yelwawa, ki iya bakinki nan baki ga mai kama da wacca zaki gayawa magana ba."
Wani irin ɓacin rai na ji ya ziyarce ni, wannan da ta yi maganar ba manta ta ba, ita ce ta ce danj ballagaza a lokacin da na je wajen Bilkisu, cike da ɓacin rai na ce.
"Ko da na ke 'yar mitsiyatan Yelwawan na sami ilimi da tarbiyar da nasan na girmama baƙo a duk inda ya same ni, kuma a 'yar mitsiyatan Yelwawan nake da ƙimae da 'yar masu kuɗin Takur zata nemeni da kanta."
"Ya isa."
Wata mata ta daka tsawa, sannan ta nuna yarinyar da ta yi maganar.
"Subisha baku kyauta ba, Nana ki yi haƙuri."
Na yi mata murmushi, sannan na ce.
"Bakomai Anty, har zaku wuce ne?"
"Eyh, zamu wuce sai kuma mun dawo kawo amarya."
"Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, ga Snacks da ya ce ayi muku."
Na faɗa ina shigewa kicin, box uku na yi na snacks ɗin na ɗauko na kawo musu, tare da faɗin.
"Gashi an gode, Allah Ya sanya alheri."
"Amin amin, ku ɗauka mu tafi."
Suna fita na koma ɗaki na kwanta, dan ni yanzu gidan ma gaba ɗaya ya daina min daɗi, na ƙagu ayi auren nan a gama hankalin Sardauna ya dawo jikinsa.
Washe gari ta kama rana littinin, ranar suka yi football match, tsakanin familyn Ta Ambo da na su Bilkisu, ba Sardauna ya shigo gida ba sai wajen ɗaya saura na dare, lokacin har na yi bacci na farka.
"Honey! Duk na yi busy al'amuran aure da wahala."
Iaa daga kwancen na yi mishi murmushi, sannan na ce.
"Sannu ko na yi ma tausa?"
"Mene tausa Nan?"
"Massage."
"Uhm, ai kema kin gaji Nana."
"Idan kana so ai sai na yi ma."
"Ki huta kawai Sarauniyar mata Nana, uwar gidan Sardauna Ta ambo."
Wani daɗi na ji kamar na jawo shi ma haɗiyeshi, washe gari Talata suka yi wani party, tsakanin 'yan gidan Ta ambo da 'yan gidasu Bilkisu, ina daga gida amma nasan su kansu 'yan uwa Sardauna sun fi farin da auren Bilkisu akan nawa, ranar kam sai bacci na yi na ƙyale Sardauna, dan ban san lokacin da ya dawo ba.
Ranar Laraba suka tafi Abuja, zasu dawo ranar juma'a bayan anyi ɗaurin aure, duk irin hidimar da Sardauna ke ciki ba cikakken awa sai ya kirani.
"Nana karki kula Turaki, karki kula wani namijn, ko su Ra'is."
Shine kaɗai abinda yake faɗa da zarar ya kirani, na kira Hajiya awaya na ce mata dan Allah Yaya Radiya ta zo ta yani zama, a yanayin ina buƙatar wani a kusa da ni, Hajiya ta ce sai dai ta dinga zuwa tana yini idan dare ya yi sai ta tafi, ta dole na amince da hakan.
A zuwan da Yaya Radiya take yi, ta kan ɗan bani 'yan shawarwari akan yadda zan rayu da kishiyata, ba kowanne al'amuranta zan shiga ba har Sardaunan ma, na dinga kama kaina akansa a gabanta, na ja mutuncina. Haka dai ta dinga ba ni shawarwari.
Ranar juma'a ƙarfe ɗaya aka ɗaura auren SARDAUNA DA BILKISU, a babban masallacin birnin tarayya na Abuja. Duk da Yaya Radiya da Yaya Rumaisa suna nan hakan bai hanani zubar da hawaye ba, Sardauna dai ya zama ba nawa ba ni kaɗai, ya zama namu mu biyu da wata, ɗakin Sardauna ya zama ba sirrina ni kaɗai ba, ya zama sirrinmu mu biyu, na yi kuka kamar raina zai fita daga baya kuma na haƙura na fawawwala komai.
A daren juma'ar su ka dawo, amma Sardauna bai shigo, arzƙina ɗaya ina jin motsin Turaki dan baije Abuja ba kwata kwata, sai washe gari asabar Sarduana ya shigo, shima a gurguje ya zo yana shirye shiyen tafiya dinner ta yau. Bai ko tsaya ya ji yana ke ba, ya na rayu bayan tafiyarshi, ta dole na haƙura na sallama Sardauna, Allah Ya kaimu a gama bikin.
Anyi gagarumar dinner ta gani ta faɗa, wacca gaba ɗaya jihar jigawa ta ɗauka, ko ina kaduba sune suke yawo, Malaika daga kano ta kira layina, ina ɗagaqa ta fara magana kamar zata hau ni da faɗa.
"Nana ashe tun can da Sardauna ba sonki yake ba kika aureshi? Yanzu gashi duniya ta shaida a yanzu yake auren matar so."
Wani ƙululun abu ne ua tsayamin a raina, na fashe da wani irin kuka sannan na kashe wayar gaba ɗaya, mutane daman har jira suke wani abu ya faru su hau turama salan su ɗaga ma hankali, haka na yini ina kuka babu me rarrashina, ni dai har na yi bacci banga Sardauna ba, banji ɗuriyarsa ba. Haka na tashi da wani irin ciwon kai mai azaba, ko breakfast ban iya ba na watsa ruwa da ƙyar na kira Sardauna a waya akan banda lafiya, amma bai ɗauka ba sai na kira Yaya Rumaisa na sanar da ita, ba ta ce min komai ba rta kashe wayarta, can sai na ga ta turumin text da wata lamba DR NA'IMA DAƘAYYAWA. Tabbas a yanzu nake ƙoƙarin gano gaskiyyar cewa 'yan uwa 'yan uwa ne, duk daɗin da namiji yake baki bai ko rabi 'yan uwa ba, duk da irin fushin da suke da ni, bai hana su zuwa gidana ba lokacin da nake cikin matsala, haka bai hana su ba ni taimako ba a lokacin da na buƙata. Lambar na kira bugu ɗaya aka ɗauka.
"Salamu alaikum, ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah."
Ta amsa muryarta a sake, sai da na gyara murya sannan na ce.
"Ni ce wata da na taɓa zuwa wajenki, har kika yi min faɗa akan Low Bp, sannan na fara yi miki maganar haihuwa."
"Oh! Mr's Ta Ambo Right?"
"Eyh ni ce."
"Okay, me ya sake faruwa?"
"Daman yau ne na tashi da ciwon kai da jiri sosai. Ko zama na yi jiri nake ji, shine na kira sister ɗina kuma sai taban numberki."
"Ayyah! To mene matsalal Kina cikin damuwa ne ko?."
Sai kuma ta fara magana cikin sanyin murya.
"Tun a wancan lokacin na faɗa miki sakamakon gwajin jinin da muka yi miki ya nuna cewa hawan jinin ki ya yi ƙasa sosai, wato Low BP. Kuma shi ne yake kawo miki wannan yawan jiri da matsanancin ciwon kai da kike ji."
Ji na yi idanuna sun sake yin nauyi, na sauke wayar daga kunnena na kalle ta, ban ce uffan ba na sake mayar da wayar kunnena a cikin raina nake jin kamkar wani sabon nauyi ya sake danna mini ƙirji.
"Nana, ke fa yarinya ce ƙarama, mai ƙarancin shekaru." Likitar ta ci gaba da magana, muryarta cike da gargaɗi.
"A wannan ƙanƙanun shekarun naki, bai kamata kina yawo da Low BP irin wannan ba. Illar da zai yi miki yana da yawa; zai iya sanya ki yawan suma, ya raunana miki jiki, kuma yana iya shafar yadda jini yake kwarara zuwa ga ƙwakwalwarki da zuciyarki. Me yake damunki ne?"
Tambayarta ta na ji kamar ta soka mini mashi a zuciya. Me yake damuna? Sardauna ne... auren da zai ƙara ne... kishin da yake shirin cinye mini rayuwa ne. Watsar da ni da ya yi. Amma sai na tsinci kaina da girgiza kai kamar ta na gani na, hawaye guda ɗaya ya subuce mini a kumatu.
"Dole ne ki rage saka damuwa a ranki, Nana," ta faɗa cikin muryar lallashi. "Mata da yawa ba su sani ba, amma damuwa ita ce babbar makashiyar mace. Ki janye kanki daga duk abin da zai ɗaga miki hankali, ki huta, kuma ki rinka cin abinci mai gina jiki. Idan ba ki kula da kanki ba, babu wanda zai kula da ke ba, kin ji ni?"
"Eyh na ji."
"Yawwa."
Sai kuma ta sauya salon maganar zuwa wani batu da ya fi komai fasa mini zuciya.
"Sannan akwai zancen rashin haihuwar da ku
Ika zo da shi a wancan zuwan. Ina so idan za ta yiwu, yau ko kuma gobe da safe ki daure ki zo asibiti mu ƙarasa dukkan gwaje-gwajen da suka kamata. Dole ne mu gano tushen matsalar da wurin da take, domin mu san matakin da za mu ɗauka, nasan yana ɗaya daga abunuwan da suke saki damuwa."
Kalmar 'Rashin haihuw_ar' ta daki kunnena tamkar tsawa. Na ji wani irin jiri ya sake kwasata a kan kujerar. Rashin haihuwa shi ne dalilin da Sardauna ya dogara da shi zai kawo mini kishiya. Shi ne silar da iyayensa suka matsa masa. A take na ji dukkan gidan yana juya mini, maganganun Yaya Rumaisa na cewa na ajiye soyayyar Sardauna gefe na kula da kaina suka dawo mini daki-daki.
"Zan zo Likita... zan zo gobe Insha Allah," na faɗa cikin dasasshiyar murya, ina ƙoƙarin haɗiye kukan da yake shirin kufce mini.
Legendspen
08129553971
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na ashirin da takwas.
(28)
Tun bayan gama wayarmu da Dr Na’ima na rasa me yake min daɗi, ta shi na yi na shiga ɗaki na ɗauko drugs ɗina na kwanaki na dawo falo, fridge na buɗe na samu ragowar cake na zo na zauna na tura shi da tea kamar ina cin ganyen darbejiya haka na tura shi, ina gamawa na ɗauki drugs ɗin na sha, ciki har da nasa bacci.
Banyi ƙwaƙwaran minti sha biyar da shan maganin ba bacci ya ɗauke ni, sai dai kuma banyi nisa da baccin ba na ji muryar Sardauna akaina, a hankali na buɗe ido.
Dishi dishi na fara ganinsa, sai kuma can naganshi tar.
“Wayyo Allah.”
Na faɗa yayin da nake ƙoƙarin miƙewa zaune.
“Nanaty mene yake damunki?”
Girgiza masa kai na yi kawai, ba tare da na ce mai komai ba.
“Ki yi haƙuri Nana dan Allah.”
Na sake girgiza kai, hawaye suka shiga zarya a a fuskata.
“Ya salam! Nana mene dan Allah.”
“Yanzu shikenan sabida zaka ƙara aure ka manta da ni? Ka watsar da ni ka manta akwai wata mata Nana a duniya?”
Ya kamo hannu ya matse su, sannan ya ce.
“Nana har abada. Babu abinda zan samu na manta da ke, na manta da hallacinki, ki yi haƙuri dan Allah.”
Ya sa hannu ya fara gogen hawayen, na kauda kai gefe na ci gaba da zubar da abuna.
“Nana dan Allah ki yi haƙuri, ki tuna yau fa wannan babin zai ƙare, zamu shiga sabon babi, sabuwar rayuwa, sabon zama Nana, ki bari mu mori wannan lokacin a matsayin na ƙarshe tsakanina da ke.”
Na ɗago na kalleshi, alamun bangane na ƙarshen da ya ce ba.
“Nana! Daga yau mun gama zama matsayin ni dake mu biyu kawai, mun zama uku, mun ƙara yawa Nana. Zanyi kewar hakan sosai da sosai.”
Na ji wani irin tausayin Sardauna, son sa ya sakw mamaye guntun ɓacin ran da nake ji, na kama hannunshi cike da soyayya.
“Sardauna ko mu ɗari ne a gidannan, ni taka ce kai nawa ne har abada.”
Ya yi murmushi, ya sa hannu ya ɗaukeni muka yi cikin ɗaki, muna shiga ya mai da hasken zuwa Dum light.
Ɗakin ya yi duhu, ƙanshin turaren wuta na ɗan kullum ya cika kowane lungu da saƙon ɗakin, yana tashi a hankali. Sardauna yana zaune a gefen gadon, yayin da ni kuma ya kwantar da ni akan gadon, amma na ɗora kaina a kan cinyarsa, yana wasa da gashin kaina cikin wani irin salo mai cire wa mace kowace irin damuwa.
Ya sauko da fuskarsa daidai tawa, idanunsa cike da wani irin kallo mai narka zuciya, ya kawo bakinsa dai dai kunnena ya raɗa mini cikin sanyayya muryarsa.
“Nana... kin san wani abu? Duk duniya babu macen da nake gani na ji numfashina ya tsaya sai ke. Wannan auren da za a yi, kaddara ce kawai ta iyaye, amma babu wata mace da za ta taɓa samun ko da rabin matsayin da kika taka a zuciyata ne. Son da nake miki, ya wuce tunanin kowa.”
Na ɗago idona na kalle shi, ina jin yadda duminsa jikinsa yake ratsa ni. Murmushi ya yi, ya sumbaci goshina sannan ya hawo kan gadon, ya kishingiɗe a jikin manyan matashin gadonmu, yayin da ya jawo ni jikinsa na kwanta luf, na ɗora kaina a kan ƙirjinsa, jikinsa ɗumi, ina jin yadda bugun zuciyarsa yake harbawa a hankali. Hannunsa ɗaya yana yawo a cikin gashin kaina, yana rarraba su a hankali, yayin da ɗayan hannunsa kuma yake shafa lallausan kumatuna da bayan yatsunsa.
“Kishinki nake yi, Nana. Kishinki nake yi ko da da iskar daren nan ne da take taɓa fatarki. Wani lokacin idan na rufe idona na tuna cewa nan gaba kaɗan zan rinka raba kwananki, har hakan yana sanya ni tsoro da fargaba. Na san ranar da ba zan kwana tare dake ba, ba zan iya baccin kirki ba, domin jikina ya riga ya saba da numfashinki da zazzafan duminki, Nana.”
Hannuna na hagu na ɗora a kan fuskarsa, ina shafa sajen sa da ya sha gyara, ina jin yadda dukkan jikina yake ɓari saboda kalamansa. Ya kama hannun nawa, ya zura yatsunsa a cikin nawa ya matse su da ƙarfi, sannan ya ce.
“Har yanzu ba zan taɓa mance ranar farko da na ganki ba. Nana kinsan ba ranar da na zo umguwarku na fara ganinki ba?”
Ya ƙarashe maganar yana kallon cikin idona, wanda zallan mamaki ya bayyana.
“Kin tuna wata rana da kuka je Manpower ke da Alhaji da wannan yayan naki a wajen taron nan? Kina sanye da fararen kaya, a lokacin kallo ɗaya na yi miki na ɗauke kai, amma Nana wata magana da kika yi ta ja hankalina gareki, haka kawai na ji ƙuruciyarki ta burgeni, kin iya tsokana, kin iya dariya, kin iya fari sa ido, sannan kin iya shiru. Fuskarki kamar ta jirirai da basu san komai ba sai rigima Nana, tafiyarki ta kamun kai da yadda kike kallon ƙasa, shi ne abun da ya fara sace mini zuciya. Na so na ƙyaleki amma sai na ji bazan iya ba, tun daga nan na fara bibiyarki, yadda kike rayuwa da komai Nana, a hankali kika fara shiga raina, har ta kai ko ina gida na kan iya tuna wasu ɗabi’unki na yarinta.“
Ya ƙara matso da ni jikinsa, yana shafa fuskata cikin soyayya, “Nana bansan ina son ki ko kishinki ba, sai ranar da kika nuna kin zaɓi ƙawayenki a kaina, Nana ranar duniya ta tsayamin zafi, na ji wani irin zafi a raina, a ranar na ji a raina ina so ki zama mallaki na nine kaɗai Nana.”
Ya rage tsayin muryarsa ta koma kamar raɗa, ya sumbaci gefen wuyana wanda ya sanya wani irin sanyi mai daɗi ya ratsa mini dukkan jikina, sai kuma ya ce.
“Ranar da na ji zai kin zama mallaki na ni kaɗai, ranar da nazo da hotonki family meeting, kowa yana gani ana bawa wancan mitsiyacin yaron Sardauna kallon da ya yi wa hoton, kallo ne mai nuna sha’awa, na ji wani zafi a zuciyata, kuma na ƙudirci cewar sai na kareki daga dukkan sharrinsa, sai na haramta masa ke har Abada Nana,ke tawa ce ni kaɗai, daga yau har abada Nana.”
Na ɗago idona waɗanda suka riga suka yi ja saboda shauƙin ƙauma, na kalli cikin kwayar idanunsa. Ya ƙara matse ni a jikinsa, yana shaƙat ƙanshin jikina tamkar wanda ke tsoron za a ƙwace masa ni. Murmushi ya yi, ya sumbaci lips ɗina a hankali.
“Nana sai bayan na aureki na ji ina da burin mallakarki har abada, sai dai ƙuruciyarki da take burgeni kin dage sai kin kawar da ita Nana.”
A hankali na ɗan zame jikina, sannan na ce.
“Ƙuruciyata kake so ba ni ba?”
“Nana ko bake nake so ba, ke tawa ce har Abada Nana, mallakar da na yi miki ta har abada ce, me yake kawo kishi Nana?”
“Sone.”
“To ina yi miki kishin da babu wata hallita da nake yi wa irin shi, abu mafi girma a zuciyata shine tsanar Turaki, to Nana kishin da nake yi miki ya zarci tsanar Turaki sau ba adadi a zuciyata.”
Na ji wani sabon shauƙi ya lilluɓe ni, kalaman sa kamar zuma suke malala a cikin jyjiyoyin jikina. Duk wata fargabar kishiya da nake ji ta gushe a wannan daren, na ji tamkar ni kaɗai ce mace a duniya.
“Don haka nake so ki kwantar da hankalinki, uwar gidana. Kewarki da zan rinka yi, ita ce zata riƙa addabar rayuwata a kowane minti. Babu wata mace da ta isa ta maye gurbinki.”
A cikin tsantsar daɗin baki da zafafan kalaman Sardauna, na mika masa dukkan ragamar rayuwata, har ina jin cewa ko da duniya zata tashi, wannan mutumin Sardauna nawa ne ni kaɗai.
***********
06:30pm
Zaune yake gefen gadon, ni kuma ina tsaye na gama sanya masa babbar rigarsa, haka hulal ma da kaina na yi masa karinta, ya fito fes kamar ango a daren aurenshi na farko. Duk wani jiri da ciwon kai da nake ji ɗazu, yanzu babu shi.
Muna nan zaune masu kawo amarya suka shigo, kallon kaina na yi a mudubi, na yi kyau na gaji da haɗuwa, lace ɗina dark blue ne da touch ɗin golden, ya yi matuƙar amsar jikina. Ɗikin doguwar rigar ya kwanta a jikina ɗas, na yi ɗaurina mai kyau na ɗora ƙaramin blue mayafi akaina ma zagayoshi ta ka faɗa, kunnena da hannu ɗankun zinare da Sardauna ya siya min ne. Sallama da na ji ana yi a ɓangarena, ya sa na fita zuwa falon, iyayen amarya ne da ita amaryar. Cike da ladabi na tare su tare da basu mazauni.
“To Uwar gida ga amarya mun kawo miki, muna fatan zaku zauna lafiya da juna.”
Na yi murmushina na ko yaushe, sannan na ce.
“Ni da Bilkisu kamar ‘yan uwa muke, in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai ɗimbin alheri, ‘yar uwa barka da shigowa.”
“Ma sha Allah, gaskiyya Nana munji daɗi sosai na yadda kika karramamu, Allah Ya yi albarka.@
“Amin na gode sosai.”
Daga haka suka miƙe nima na miƙe suka fice zuwa part ɗinta, na dawo na sameshi zaune gefen gadon.
“Amarya ta zo.”
“Ina sonki Nana.”
Kallonshi na yi, a raina ina jin daɗi. ‘Me yafi wannan daɗi? Mijinki yana ƙara aure amma babu abinda yake ce miki sai yana sonki. Shin a matan duniya akwai wacca tafi ni sa’a kuwa? Ni Nanan Sardauna.’
“Ina sonka Sardauna, ina tare da kai komai runtsi komai wuya Sardauna, Allah Ya baka ikon yin adalci mijina.”
“Nana!”
“Na’am.”
“Bilkisu ta ce min ba za ta iya girki a gawayi ba, amma na amince mata tunda daman kece kika zaɓi yin amfani da shi, sannan ta ce ba zata rayu ba Ac, ba Iron, ba fridge ba, shima na amince mata, duba da adalaci ke baki saba da su ba, ita kuma ta saba, tun da a addini ma ance idan ka auri mace ka ba ta abinda take ciki a gida, ko wanda ya fishi, idan ba zaka iya ba kar ka aureta, shi ya sa Nana, ke kuma ko da na hanaki wannan Nana nasan na baki fin abinda yafi na gidanku ko?.”
“Sardauna! Ni ba duk wani ƙyale ƙyalen duniya nake buƙata ba a zama na da kai, Sardauna kai kawai nake so, kai nake buƙata, kai ne zan rayu da shi Sardauna.”
Rungumo ni ya yi jikinsa, sannan ya ce.
“Nana girmanki da kimarki a idona abune da bazasu taɓa taɓuwa ba, Nana zan iya yaƙi da kowa akanki, Nana ina so a yadda kike yi min uziri a yanzu ki ci gaba da yimin har ƙarshe Nana, ina sonki ina sonki ina sonki.”
“Ina sonka nima sosai da sosai, yawwa gobe zanje asibiti akan ciwon kaina.”
“Tom Nana, Allah Ya kaimu.”
“Amin amin.”
“Ƙarfe tara ta yi Nana bara na je wajen amarya, ki shiryawa zuwana, da akwai magana Nana.”
“Tom Allah Ya tsare, amma ina kazar?”
“Nana tana mota, yanzu zan shigo da ita, akwai taki akwai ta ta Nana.”
“Tom Ango.”
Ya sa kai ya fice, ni kuma na zauna a gefen gado. ‘Idan ace haka Sardauna zai nuna min soyayya, ya auri mata dubu mana, ni dai Allah Ya sallameni wallahi, na yi da ce da Sardauna, na yi da ce da miji na arziƙi, Allah Ya barmin Sardauna na. Dan na yi imani Sardauna ya cika jarumin maza, ya cika miji, wai ni shin idan ban bautawa mijina na me zan masa, ni na daina zuwa wajen su Yaya Rumaisa, tun da na fuskanci kamar basu san me suke faɗa ba, ina dalili ace wai biyayy zan masa ba bauta ba, Mitcheww.”
Na ja tsaki tare da tashi na fito falo, ina nan zaune har wajen goma Sardauna bai dawo ba, a raina na ce ko Sardauna ya je siyo kaza ya yi dare ne bai dawo ba? Ganin goma da kwata ya sa na ɗaga labule sai dai ga motarsa Nana.
“A’a ina ya yi ne? Ko yana can wajen Bilkisun?”
Na faɗa cike da mamaki, daidai lokacin kuma na ji sautin takunsa, komawa na yi na zauna akam kujera daidai lokacin kuma ya shigo.
“Nana!”
“Na’am.”
“Ta so muje ko?”
“Zuwa ina?”
“Ɗakin Bilkisu mana? Ko kin manta.”
“Na yi tunanin nan za ta zo.”
Na faɗa ina miƙewa.
“Ki kijiki ta zo ta yi miki me?”
“Bakomai.”
Yana gaba ina binsa a baya muka shiga ɓangaren nata, ya ji kaya na alfarma, kina gani kinsan ‘yar masu hali ce a gidan. Da sallama a bakina na shiga, tana zaune kamar ba amarya ba, ta mimmiƙe tana danna waya, ɗaki ga Ac ga fanka abunta.
“Hajiya Bilkisu amarya.”
Na faɗa ina washe baki da niyar zama akan kujera.
“Ke dakata! Kar ki kuskura ki zauna min akan kujera.”
Kallon ta na yi baki a sake, na kalli Sardauna
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 16