ba mu je ba, Amma Alhaji, Yaya Ridwan, da Ra’is duk sun je. Tun da Sardauna ya ji na ce masa matar Isah Nadabo ‘yar kano ce Sardauna ya dame ni akan naje ta koyan girkin kano, yadda ake sarrafa fulawa ayi gurasa da su cincin.
Ni ban fiya shigewa mutane ba, amma akan sardauna sai da na shigewa Anty Aadiza, daman ba ta da wata matsala tana son mu ta ɗauke mu ƙannen miji, ta ɗauki Hajiya Uwar miji, dan ko da aka kawo ta daga kano hannun Hajiya aka miƙa ta. A hankali ta fara koyan sarrafa fulawa mussamman da na faɗa mata wanda zan aura ne ya ce yana so.
Hajja ba ta cika zuwa gidanmu ba, tun da Sardauna ya kan je ya kai mata kuɗaɗe da kayyaki har gida lokaci zuwa lokaci. Shi ya sa ta ƙyalemu mu ci tsiyarmu.
Kwance tashi ba wuya a wajen Allah, har muka kammala jarabarwamu, inda bayan sati biyu aka ɗaura mana aure da Sardauna, biki ne aka yi shi na garari, masu kuɗine ke hada hada ta ko ina a wajen events ɗin da familin su Sardauna suka shirya. A cikin raina babu abinda nake ƙauna da tsumaye irin a gama wannan kiɗe kiɗen akaini gidan Sarduna, inda zan samu soyayya mai daɗi.
Daga wajen taron aka wuce da ni gidana na Takur, tun ina cikin mota nake mamakin irin girman gidan, da aka fito da ni kuma sai na fara mamakin irin tsaruwar gidan.
Haka aka shiga dani cikin gidan, kowanne ɗaki a tsare yake kuma sannan a cike yake da kaya.
“Allah Sarki Alhaji da Hajiya, Allah Ya ƙara muku arziƙi, lafiya da nisan kwana.”
Na faɗa a raina lokacin da aka shiga dani ɗakin gadona, nan masu kawo ni suka zauna suna ta faman yi min nasiha, nikam gani nake kawai ƙari suke domin Abinda Alhaji da Hajiya suka faɗa min, bana jin zan sake samun nasihar da ta wuce wannan, haka ma ‘yan uwana. Yaya Ridwan ma ganin dai dagaske za a kaini ɗakin aure ya zo ya same ni da yau da safe, ya yi min nasiha mai ratsa jiki. Akwai kalma da ya faɗan guda ɗaya wacca har yanzu tana nan daram a kunnuwana.
“Nana ba tsanar saurayinki na yi ba, da ki kaga ina miki haka, Nana ina matuƙar kishin ‘yan uwana mata, bana son naga wani abu zai wahalal da su.”
Wannan kalmar kishin ta tsaya min sosai a zuciyata, nasa hannu na goge ƙwallar da ta fito daga idona.
Haka aka tafi aka barni da ƙawayena, suma ba su wani daɗe ba Sardauna da abokansa suka zo suka tafi da su, aka barni daga ni sai Sardauna.
“Nana!”
Ya kira sunana a hankali, nima na amsa masa a hankali.
“A yau sai mu gode Allah da ya cika mana burinmu, ya nuna mana wannan ranar ga ni ga ki a matsayin miji da mata, tabbas ina cikin farin ciki da hakan Nana, ina farin ciki marar misaltuwa.”
Ya ƙarasa maganar tare da tasowa zuwa inda nake, yasa hannu ya yaye lulluɓin fuskata, ya kalli fuskta da take sheƙi, ya sa hannu ya jawo ni jikinsa.
“Nana kina jin sauti bugun zuciyata.”
Na ɗaga kai tare da cewa.
“Ina ji.”
“Nana ki saurare abinda zan faɗa daga zuciyata bawai bakina ba, ina matuƙar ƙaunarki Nana, ƙaunar da nima bansan irin ta ba, ina jinki cikin jini da tsokar jikina, ina son ganin walwalrki Nana, ina jin wani irin shauƙi idan na ganni ga ki.”
Kalaman Sardauna suka kashen jiki, suka haifar min da wani irin yanayi mai daɗi, tabbas Nana na yi sa’ar miji, na yi da ce da miji na gari.
“Nana.”
Ya faɗa yana matseni a jikinsa.
“Kina jin yadda nake ji?”
“Uhm.”
“Kina jin kamar ki cinye ni, na koma jikinki gaba ɗaya?”
“Uhm.”
Haka Sardauna ya yi ta yi min kalamai masu nuna zallar soyayya da shauƙin ƙauna, mun kusa awa ɗaya a wannan yanayin sannan ya ce da ni.
“Nana ta shi ki yi alwala mu yi sallah, mu miƙa godiyarmu ga Allah.”
A hankali na tashi daga jikinsa na nufi toilet na ɗaura alwala, bayan na idar na fito shima ya shiga ya ɗaura tashi alwala daga nan ya ja mu mu ka yi sallah, tare da addu’o’i na neman albarkar aure.
Daga nan muka ci nama da lemo sannan ya kalli ni.
“Kin gaji ko?”
“A’a.”
“Ta shi ki canja kaya ki zo mu kwanta.”
Daga nan ya tashi ya fice, nima na tashi na sauya kaya zuwa na barci, bayan na sauya na zauna ina jiranshi. ‘Yan mintina kaɗan shima ya shigo cikin shirinsa na bacci.
“Wai baki kwanta ba? Sannu Nana.”
Ya faɗa yana hawa kan gadon.
“Matso kusa.”
Ya faɗa tare da jawo ni, ya rugume ni jikinsa a hankali bacci mai daɗi ya ɗauke mu. A raina ina faɗin haka ake aure? Haka rayuwar take da daɗi?
Kiran sallar asuba ne ya tashe ni na buɗe idona, idan da sabo na saba dan dama shine daidai lokacin tashinmu. Ina matsawa daga jikinsa ya buɗe ido.
“Come on Nana.”
Ya faɗa cikin magagin bacci.
“Kiran sallah ake.”
Na faɗa a hankali.
“I know, matso!”
Ya faɗa yana kamo ni, ba shiri na koma na kwanta ya sake rungume ni bacci ya sake ɗibansa, ni kam idona biyu ina ta faman saƙe saƙe. Ba shi ya farka ba sai 6:30.
“Honey! Baki san irin gajiyar dake jikina ba.”
Ya faɗa yana kamo hannuna, na yi murmushi sannan na ce.
“Ina kwana.”
“Mu fara sallah mana.”
Toilet na shiga, sai kawai na ga shima ya biyo ni.
“Mu fara yin wanka, sai mu yi sallah.”
Abu kamar wasa Sardauna ya ce tare zamuyi wanka, haka kuwa akayin, daga nan mu ka yi alwala mu ka gabatar da sallah.
Bayan mun gaisa ne ya ce.
“Ya kwanan sabon gida?”
Na yi murmushi sannan na ce.
“Da godiya.”
“Nana i really love you, i love you smile please keep it.”
Muna zaune muna hira ya hanani tashi naga shiga kicin, sai da aka yi masa waya sannan ya tashi, can ya shigo yana cewa.
“Je ki haɗa mana breakfast.”
Na tashi na fita, wani babban kwando nagani ya ajiye akan centre table na ɗauka na kai kan dinning sannam na shiga kicin. Ba ƙaramin mamakin irin girman kicin ɗin na yi ba, dan zai iya fin girman wani ɗakin a gidanmu, amma duk da haka an zuba kaya masu yawa a ciki.
Da kansa ya zagaya dani ko ina na gidan, ya nuna ko ina har da ɗayan part ɗin, da kuma ɗakinsa na nan.
Sai can yamma sannan ‘yan uwana suka yi min zuwan nan da suke yi, da daddare ma cikin irin yanayin jiya muka sake kwana da Sardauna.
Har tsawon kwana goma da aurenmu muna zaman jin daɗi da soyayya da Sardauna ina samun soyayya da kulawa a wajen Sardauna, yana riritani kamar jaririya, ko ƙwai da ake tsoron fashewarsa.
Ranar juma’a su Malaika, Amina da Fauziyya suka shirya zuwa, tun safe nake rawar jiki da zuwansu, na faɗawa Sardauna ya kai sau goma, tun yana kulani har yafara min banza, haka har ya tafi ofis, girki wajen kala uku na yi musu sabida murnar zuwansu.
Wajen ƙarfe ɗaya suka zo, har wani tsalle na yi da na gansu, suma cike da farin ciki suka tarbeni suna murnar ganina cikin farin ciki, bayan sun zauna na shiga yi musu safarar abun sha, lemo kala kala na gora da na kwalli, sannan kuma wa’yanda na yi da kaina.
“Oh my, Nana kinga yanda kike glowing.”
Malaika ta faɗa tana kashen ido.
“Nana duk waɗannan abun shan namu ne mu kaɗai, duniya sabuwa.”
Amina aminu ta faɗa, na yi dariya sannan na ce.
“Ku yara ashe haka aure yake da daɗi? Haka ake rayuwar auren, ai wallahi aure yafi komai daɗi idan kuka sami irin mijina. A shawarce karku ce zaku zauna, wallahi kuna komawa gida ku ce sai anyi muku aure.”
Legendspen
08129553961
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na goma
(10)
Dariya suka kece da ita sannan Malaika ta ce.
"Yarinya ta ji daɗin aure."
Ni kuwa na ce.
"Ba dole ba? Mene wanda nake so mijina ba ya yi min, a zaman nan namu sau uku yana fita dane manyan wajen cin abinci, gaskiyya duk wacca ta yi dacen miji ta yi riba."
Haka muka yi ta shan hirar mu muna dariya, wajen ƙarfe biyar Sardauna ya kirani a waya, a gabansu na ɗauka ya ce dani yana son na yi masa cous-cous da miyar kaza. Ina gama wayar na kallesu sannan na ce.
"Bara na shiga kicin."
"Kaga matar aure." Suka faɗa suna dariya, suna nan zaune na shiga kicin na fara haɗa masa girki, sai dai sanda na duba friza ɗaukar kaza babu kaza, sai a lokacin na tuna gaba ɗaya na yi amfani da ita, waya na ɗauka na kirashi sai dai bai ɗauka ba. Sai kawai na ɗora cous-cous ɗin. Ina cikin Kicin ɗin Fauziya ta sanar da ni cewar zasu tafi, haka na fito falon mu ka sake taɓa hira kafin su ka tafi, Naira dubu biyar na basu na ce su hau mota, ni kuma na dawo kan girki na. Ashe Sardauna ya kira ni ban kula ba ina kicin wayar na falo, ganin lokaci zai ƙure sai kawai na ɗora miyar na yi masa ta nama, amadadin kaza tun da duk nama sunansa nama.
Bandaɗe da gama abincin ba ya shigo, da murna ta kamar ko yaushe na je na tare shi, na yi tsalle na faɗa jikinsa ya rungumoni yana faɗin.
"Hon yau bana jindaɗi."
"Meke damunka?"
Na tambaya ina amsar jakarsa hannunsa, zama ya yi kan kujera tare da miƙamin ƙafarsa na fara cire masa takalmi.
"Wane mistiyacin yaro ne a family, ya dawo ƙasar shine yake neman yi min rashin kunya."
Ya faɗa yana taɓe baki, sai duk na ji ba daɗi.
"Ka yi haƙuri ka ƙyaleshi kawai."
"No! Turaki bai isa na ƙyaleshi ba, dole na ɗau mataki zan nuna masa ni ba sa'ansa ba ne."
"Kai Sardauna shi Turaki?"
Tambayar da na fara yi kenan, kallona ya yi sannan ya ce.
"Granny ce ta sama na sunan dukkanmu, sa'a na ne, kusan lokaci ɗaya aka haife mu da shi, amma na girmeshi. But seriously Nana tun ina ƙarami bana son yaron nan, abokin dabi na ne, komai na yi sai ya ce zaiyi, natsani na ganshi da abuna ma gaba ɗaya."
"Ka daina faɗin haka Hon, ba a cewa antsani musulmi, mussaman shi da yake ɗan uwanka."
"Ƙyale wannan maganar Hon! Yunwa nake ji."
Ya faɗa yana tashi zuwa wajen dinning, nima na ta shi na shiga da takalmi da jakarsa ɗaki.
"Me ya sa ma bazan yi biyyar aure ba, bayan Yaya Rumaisa da kanta ta ce Biyayya na ƙara soyayya kuma gashi ina gani, ni ina mamakin matan da basa yi wa mazajensu biyayya. Me suke nema a duniyar?."
Na faɗa bayan na ajiye kayan, sannan na fito falon yana zaune kan kujerar dinning yana jirana. Plate na fara ajiye mai sannan na buɗe cous-cous ɗin na fara zuba mai, sai bayan na gama na buɗe miyar na fara zubawa.
"What is this?"
Ya katseni.
"Abincin."
Na faɗa muryata na rawa, leƙa miyar ya yi sannan ya kalleni.
"Bance miki chicken nake so ba, me ya sa naga beef?"
"Ahm. Daman kazan ne babu, da na duba sai naga saura nama shi ya sa na yi na nama"
"Me ya sa baki sanar dani ba?"
"Na kiraka baka ɗauki wayar ba."
"Ban kiraki ba bayan nan? Me ya sa baki ɗauka ba, sabida kina can ƙawayenki sun zo ko? Ni ban isa na sa ki abu ba? Ban isa na ce ga abinda nake so ba ni da gidana?"
Ya yi maganar cike da tsawa kamar zai dake ni.
"A'a ba haka ba ne, ka yi haƙuri wallai gobe zanyi."
"Dalla malama rufemin baki, shashasha marar hankali, abinda zaki fara yi min kenan? To wallahi Nana baki isa ba."
Yana gama faɗin haka ya yi fatali da abincin ya yi waje, wani irin zafi na ji ya mamayeni, kamar ba wacca take cikin Ac ba, jikina gaba ɗaya ya fara rawa ba shiri na tsugguna ƙasa na fara raira kuka, sai da na yi kusan minti talatin ina kuka na babu mai rarrashina sannan na tashi daga baya na shiga kwashe kayan, sannan na gyara wajen na koma kan kujera na zauna.
Ba Sardauna ya shigo ba sai wajen ƙarfe tara, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai, da sauri na tashi ina faɗin.
"Dan Allah ka yi haƙuri."
Ɗauke kai ya yi ya shige ɗakinsa, ya tura ƙofar ya murɗa mukulli, haka na yi ta faman bugu amma bai buɗe ba, sai wajen ƙarfe 12:30 na je na kwanta ganin Sardauna bazai buɗe ba.
Wannam shine karo na farko da muka sami saɓani da Sardauna tun zuwana, wannan ta kasance baƙar Rana a wajena domin naga abubuwa kala kala, ko baccin kirki ban iya ba.
Washe gari da safe tun da na yi sallar asuba ban koma ba, na shiga kicin haɗa masa abincin kari mai kyau da lafiya, sabida ina son na burgesa kuma ya yafe ni. Gurasar da na koya wajen Anty Adiza na yi masa da miyar farfesun naman rago, na juye a plast na kawo kan dinnig ɗin. Na shirya na dawo falon na zauna jiranshi, bai fito ba sai ƙarfe tara kasancewar yau Asabar ne kuma babu aiki.
"Ina kwana?"
Kallona ya yi sannan ya kalli dinning ɗin, ya nufi wajen ba tare da ya ce da ni komai ba. Na bi bayanshi ina kuka ina faɗin.
"Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi bazan sake ba dan Allah."
"Uhm." Ya faɗa yana zama kan kujerar, ya fara zuba abincinsa, in tsaye akansa ina faman zubar hawaye amma ya yi banza dani kamar bai san ina wajen ba, har ya kammala sannan ya kalleni.
"Ki biyo ni."
Ba shiri na bi bayanshi zuwa falo, ya zauna akan kujera ni kuma na zauna a ƙasa, sai da aka kusa minti biyar sannan ya ce.
"Nana!"
"Naam."
Na amsa masa. "Nana wanene ni a wajenki?"
"Mijina."
Ya kalle ni sannan ya ce.
"Shine matsayina a wajenki?"
"Eyh."
"Nana"
Ya sake kiran sunana, na sake amsa masa.
"Nana, ina so ki canja min matsayi daga na mijin da kika ba ni. Ina so ki bani matsayin da yafi kowanne matsayi a wajenki, ki bani matsayin Uwa, Uba, dangi, Nana ina so ki ɗauke hankalinki daga komai daga kowa ki mayar dashi kaina, Nana ni kaɗai. Nana irin son da nake yi miki bana so naga kina mu'amala da kowa a duniya, Nana ina jin kishin akan kowa ciki har da 'yan uwanki, Nana ko da mace naga kina magana ina jin zafi a cikin raina, ina jin duniya ta yi min zafi. Nana zaki iya yi min wata alfarma?"
"Eyh zan iya."
"Nana ina so ki cire kowa a rayuwarki, ki cire komai sai ni Nana, ni kaɗai zaki gani, ni ka ɗai zaki ji."
"Na yi maka alƙwarin."
"Ta shi ki zauna anan."
Ya faɗa yana nuna min kusa da shi, na miƙi na zauna ya kama hannuna.
"Nana ni mijinki ne, mai sonki! Da ya sadaukar da dubban farin ciki dan ya rayu dake, Nana ina son sakayya mai girma dan Allah."
Da irin waɗannan kalaman Sardauna, ya dinga dasa zazzafan tausayinsa a zuciyata, har na ji babu wani a rayuwata sai Sardauna.
Daga nan komai ya dawo daidai tsakanina da Sardauna, muka ci gaba da rayuwa cikin soyayya da farin ciki. Sardauna yana yawan magana akan ayyukan gida sun yi min yawa, hakan yasa ya kawo 'yar aiki me ta ya ni aiki, a farko mun fara zama tare da ita tana ta ya ni aiki, amma daga baya na fara fuskantar abubuwa sun fara yi wa Sardauna yawa, mussaman yadda wata rana ya fara magana akan yawan kuɗin wuta da aka kawo masa bill. Hakan ya sa na sallami 'yar aikin, da ya yi magana na ce masa bana son yana yawan kashe kuɗi, amma bayan kwanaki ya sake dawo da ita na sake sallamarta, a haka ya kawo har guda uku ina sallamarsu, daga baya ya daina kawo wa.
Haka mu ka ci gaba da rayuwa cikin so da ƙaunar juna, Sardauna yana riritani tamkar ƙwai akan cokali wanda ake tsoron faɗuwarsa. Ina rayuwa ta cikin farin ciki kowa yana ta ya ni murna, na je gida sau biyu sannan na je gidan yayuna sau ɗai ɗai, suma sun zo baki ɗaya har da Ra'is amma banda Yaya Ridwan.
Ranar wata juma'a bayan ya dawo, yake sanar dani wai ƙarshen wannan satin ranar Lahadi suna da baban family meeting, kuma ana buƙatar kowa yaje har da iyalansa.
Tun da Sardauna ya faɗan na fara tunani, danni ban taɓa haɗuwa da 'yan uwansa ba tun lokacin biki, sai dai 'yan gidansu da ya kaini sau ɗaya. Hajiyarsa mutuniyar arziƙi da ƙannensa duk ba su da matsala, amma fa wannan ya ce wai babban famili meeting, duka 'yan uwansa zasu je.
Washe gari na kira Yaya Rumaisa a waya na faɗa mata bayan ya fita, nan ta bani shawarar irin yadda zan shirya, yadda zan kama kaina a cikinsu, da sauran abubuwa.
Ranar Sunday tun safe, na fara shirina amma ina yin komai cikin nutsuwa sabida kar ya ga rawar kaima, kamar yadda Yaya Rumaisa ta faɗa. Bayan munyi breakfast ya ce dani.
"Ki shirya muje da wuri, zan ajiye ki sai na fita zuwa 12:00 ake farawa, zan dawo kafin lokacin."
Tashi na yi na shiga ɗaki, na ƙarasa shirina daga nan na dawo falo lokacin shima ya gama shiryawa.
FADA AREA
09:30am.
Babban gidane na gaske da ya ji kayan more rayuwa, mutane ne tsilli tsilli cikin gidan sabida basu gama hallara ba, yana gaba ina binsa a baya ya yiwa wayanda ya ga dama magana, ya yi banza da wayanda ya ga dama, har ya kaini inda Hajiyarsu take tare da 'yan uwansu. Dukkansu na gaishesu kamar yadda na ga ya yi, suna ta samin albarka kowacce fuskarta washe da fara'a.
Bayan mun gaisa ne na koma gefe na zauna a babban falon inda naga Lubna ƙanwarsa ta zauna, shi kuma ya tashi ya fice. Kowa sabgar gabansa yake masu danna waya na dannawa masu hira na taɓawa cikin harshen turanci, ba ruwan kowa da ni, hakan ya sa nima na ja waya ta na fara dannawa, nan ga message ɗin Amina Aminu cewar an fara cire WAEC, sun cire tasu a cafe kuma sun sami 8 credit, sannan an fara registration ɗin Jamb. Na yi mata reply da cewar Okay idan ya shigo zan faɗa masa sai ya ciro min.
"Salamu alaikum."
Da sauri na ɗaga kai sabida yadda na ji muryar kamar ta Sardauna sai da ba shi ba ne, wannan wani matashin ne daban shima ɗan gayu amma Sardauna yafi shi kyau nesa ba kusa ba.
"Uncle Turaki Welcome."
Na ji muryar wata yarinya ta faɗa tana nufo sa.
"Dotti, how are you."
Ya faɗa cikin wani irim ƙwarewar turanci, kamar ma bai iya hausa ba, a raina na ce.
"Wannan shine TURAKIN? Duk rashin girman SARDAUNA da nake gani, sai naga wannan yafi ƙanƙantar jiki."
Na faɗa a cikin raina, ƙarasowa ya yi inda iyayensu suke ya fara gaishesu cike da girmamawa, ya ɗan fi Sardauna sakin fuska amma Sardauna yafi shi komai na duniya, haka kawai sai na ji bai yi min ba sabida yadda suke da mijina. Daga nan ya juyo inda sauran yayunsu suke suka ya fara gaishesu, yadda yake ɗan wasa da su Sardauna duk ba ya haka, dan ko da yazo daga Ina wuninku, Ya iyalai shikenan ya tashi ya fice. Amma shi gashinan sai hira suke har da wasa da yaransu, suma sai jan shi suke da hira mafi akasarin hiran na su ma cikin harshen turanci suke.
A raina na ce. "Su waɗannan sun maida turanci yaren uwarsu da ubansu, ba ga yaran ba ga iyayensu ba." Daga nan kuma ya juyo inda muke nan kowa ya fara gaisheshi, nima na gaisheshi ya amsa ba tare da ya kula da ni baƙuwa ba ce a cikinsu. Wata da na ji suna cewa Sister Seemah ta ce. "Blood meet your Amarya." Ta faɗ tana nuno ni, gaba na ne na ji yana faɗawa sabida irin kallo daya ke min, sai da ya kalleni tas sannam ya dawo inda nake.
"Daga ina?"
Ya tambayeta, Sister Seemah ce ta matso sannan ta ce.
"Sardauna's Wife."
Kallona ya sake yi tare da jijjiga kai, sannan ya ce.
"Matar ƙanina kenan? Me sunanta?"
"Nana." Lubna ta faɗa.
"Sannu Amaryarmu, sunana Turaki yayan mijinki Sardauna, kuma babban abokinsa."
Na yi murmushi sannan na sake cewa.
"Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ina ɗan uwan nawa?"
"Yanzu ya fita zai dawo."
Na faɗa a raina na fara mamakin me ya sa to basa mutunci da Sardauna, amma shi ga shi anan yana sakar min fuska har da cewa matar ƙaninsa.
"Okay zan jirashi a main falo, ya gidan?"
"Lafiya lau."
"To Allah Ya sanya alheri, Allah Ya bada zaman lafiya."
Na buɗe baki da niyar cewa Amin, muryar Sardauna ta cika ɗakin.
"Malam matsa daga kusa da matata."
Legendspen
08129553971.
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na sha ɗaya.
(11)
"Kai yaro gyara bakin ka."
Turaki ya faɗa yana kallon Sardauna.
"Ni kake cewa yaro?"
Sardauna ya faɗa yana ƙarasowa wajen.
"Relax boy."
Turaki ya sake faɗa, hannu Sardauna ya sa ya fisgo ni na faɗi ƙasa, da sauri Matar da na ji suna cewa Hajiya Maama ta shi tana faɗin.
"Sardauna bita a hankali, ba ita a lamarinku."
"Maama me ya sa zai zo kusa da iyalina, mene haɗin shi da ita."
"Shut up malam, bansan har yarintarka ta kai haka ba, na yi tunanin duk wani abu da yake tsakaninmu zai ƙare a tsakaninmu ba sai ya shafi iyalanmu ba, amma na fuskanci har yanzu da yarinta a kanka."
Cike da wani irin fushi Sardauna ya yo kansa, Hajiya Maama ta ce.
"Dakata Sardauna, anan kaine baka da gaskiyya. Duk wani abu da yake between you guy's ku tsayar da shi iya ku biyu, karku sanya familinku."
"But she is not our family she is mine, my family, so ya yi baya da ita."
"Sardauna karɓi wannan, ka ce she is not our family she is yours?"
Wata dattijuwar mata ta faɗa, ni mamakina ma yadda aka yi ta iya turanci har haka.
"Dada wasa yake."
Turaki ya faɗa, sai a lokacin na fuskancin yafi Sardauna wayo ne.
"No let him, allow him to say his mind."
"Dada wasa nake."
Sardauna ya faɗa.
"Are you kidding your parents?"
"Wannam tsohuwa da mita take."
Na faɗa a raina.
"Kar nasake jin irin wannan."
Ta faɗa tare da komawa ciki, ni kuma na tashi zaune, Sardauna ya fice sauran kowa ya koma ya zauna. Haka su ka yi ta fira har zuwa 12 iyayensu maza su ka shigo suka tattauna abinda zasu tattauna daga nan aka ci gaba da hirarrakin su, banda Sardauna da ya fice. Duk lokacin da na ɗaga kai sai na ga munyi ido huɗu da Turaki, wani lokacin ya yi min murmushi wani lokacin kuma ya yi kamar bai ganni ba.
Haka aka gama zama kowa ya watse ya tafi, Sardauna ko a mota baice dani ƙala ba, bare kuma da aka koma gida. Nima dai ban ce masa ci kanka ba haka shima bai ce min ba, sai zuwa dare bayan ya sake dawowa na yi masa sannu da zuwa, sai da ya kallani sannan ya ce.
"Aini yanzu dole na kama kaina, nasan matsayina tun da kin raina ni bakya so na."
Bakina har rawa yake na fara magana.
"Wallahi ba haka ba ne, shi da kan shi ya yi min magana kuma ni bansan shi ba."
"Waye? Kar dai ki ce min yaron can, bana so! karki sake maganarsa a gidana, ni ba akan shi nake magana ba, akan ƙyale ni da kika yi."
"Ba ƙyaleka na yi ba wallahi Allah.."
"To me kika yi?"
"Bakomai, kawai bana so ma cika takura ma a yadda kake ranka babu daɗi."
Jawoni ya yi kusa da shi, sannan ya ce.
"Ni na taɓa ce miki kina takura min?"
"A'a ba ka ce ba."
"To me ya sa kika yi wannan tunanin?"
Na yi shiru na rasa amsar da zan bashi. "Uhm? Magana nake."
"Kawai."
Kawai me?"
Ya faɗa yana miƙewa tare da ni zuwa ɗaki, ya ajiye ni kan gado ya hawo.
"Ina tambayarki?"
"Ba kowa."
"Tom."
Ya faɗa yana matseni a jikinsa, tun zamana a gidansa kusan wata huɗu yau ce rana ta farko da wani abu na aure ya shiga tsakanina da shi. sardauna ya zauna da nine kaiwa yana kallona kuma yana ba ni kula, sai a wannan ranar nagane aure da wata wahalal shi da ake faɗa.
Tun daga wannan lokacin zamanmu da Sardauna ya canja taku, da ba ya nuna sha'awarsa a kaina, amm yanzu kullum ne, ɗaiɗaikon rana kune yake fashi. Tun ina jin wahala da azaba har komai ya wuce. Irin azabar da na sha a ranar ta mantar da ni zance jarabawa ta sai da aka kwana biyu sannan na tuna, shima sakamakon wayar da muka yi da Ra'is yake ce min na ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 16