Share this page
nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar da zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.” Wani irim tausayinsa neya ratsamin zuciyata, sai na ji dama ni ce nake shiga wannan matsin ba Sardauna ba, dama nice nake wannan kukan ba Sardauna ba, bazan iya jure ganin hawayen Sardauna ba, suma azabatar da rayuwata.  “Ka yi haƙuri, haihuwa ba dole ba ce, amma tabbas a idon iyayenmu gani suke dole ne, Sardauna a yanzu ma da ka zo maganar muke da Bilkisu amma taƙi fahimta ta duk da nasan zata fahimta in sha Allah. Ina tunanin idan ka yarda zanje gidansu gobe mu sake magana da ita.  “Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana watangarirya. Na yarda ki je da kanki, kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka, ko menene zan iya yi mata wallahi indai zata aureni.”  “Ya zaayi kaje ka durƙusa mata? Haba dai. Ka barni da kaina zanje gobe, zan yi magana da ita ta yadda dole zata amince, ka sa haƙuri a ranka dan Allah.” “Nana idan ba ta amince ba ina cikin tashin hankali, ni dake Nana bamu da wata mafita.”  Ji na yi kamar na tashi a cikin daren na je gidansu Bilkisu amma ba hali, daƙyar na lallaɓa Sardauna ya nutsu amma bai iya cin abinci ba, haka muka kwanta duk ranmu ba daɗi. Washe gari lokaci ɗaya muka fita dashi, ya yi ofis ni kuma na yi gidansu Bilkisu ta hanyar kwantancen da ta yi min tun kwanaki. A bakin gate ɗin na tarar da wata mata mai kama da Bilkisu na shirin fita, ƙasa na tsugunna tare da faɗin.  “Ina kwana?”  “Lafiya.”  Ta amsamin a daƙile, sannan ta ce.  “Wa kike nema.” “Bilkisu.” “Tana ciki.” Ta faɗa tare da hucewa, na kusa minti biyar a tsaye ina faman tunanin ta yadda zan fara da Bilkisu, bana son ta tirjemin kamar yadda ta yi jiya. A hankali na tura ƙofar falon na shiga, zaune na tarar da su 'yan mata ne sun kai su biyar da alamu ma wasu ƙawayenta dan ba 'yan gidansu ba ne, duk da nima wannan ne zuwa na na farko gidansu. cikin wani irin yanayi kamar na isgili haka ta tarbeni.  "A'a Nana kina ƙaraso."  Na yi mata murmushi sannan na ce.  "Eyh wlhi, ya gida?"  "Muna lafiya."  Zama na yi sannan na kalli sauran matan dake ɗakin, sannan na ce.  "Sannunku."  Bansaniba ko sun amsa ko basu amsa ba, nidai abinda ke gabana shine kaɗai ke damuna.  Gaba ɗaya tunanin maganganun da muka yi da  Sardauna ya cika min ƙwakwalwa, bana iya tuna komai sai muryarsa.  'Nana nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar sa zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.' "Allah Sarki Mijina."  Na faɗa a zuciyata, a fili sai kuma na kalli Bilkisu na ce.  "Dan Allah magana nake so mu yi dake, ina son mu shiga daga ciki."  Dariya ta yi ita da mutanen nan nata sannan ta ce.  "Haba Nana kamar ba wise ba."  Ɗaya cikin ƙawayen ta ce.  "Baiwar Allah kizo ki ganmu tare sannan ki ce wai ta tashi ku shiga ciki a wane dalili?"  Baki sake nake kallon ikon Allah.  "Nana waɗannan ƙawayena ne duk wani sirri zan iya yi dasu, dan haka ki faɗi abinda zaki faɗa."  Ji nai na yi wani irin muzanta, kamar bata san maganar da zamuyi ba, to ma wai 'ƙawayenta ƙawayena ne?, ko da ƙawaye na ne kowacce magana yakamata na yi a gabansu?. "Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana tangarirya Hon, na yarda amma ki je da kanki kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka."  Kalaman Sardauna suka dawo kunnuwa kamar yanzu yake faɗinsu.  "Bazan taɓa bari ka hulaƙanta ba in sha Allah Mijina."  Na faɗa, sannan na kalleta tare da tasowa zuwa inda take, na sanya gwiwoyina a ƙasa sannan na ce.  "Maganar mu ta jiya, ki taimaka ki auri mijina."  Wata shegiyar dariya na ji ƙawayen na ta sun kice da ita, kamar daman jira suke na yi magana. “Bilkisu wannan mahaukaciya ce?” Ɗaya cikin ƙawayenta ta faɗa, tana wata irin dariya.  “Bana ce ba, ni yadda nasanta lafiya ƙalau take, amma daga jiya zuwa yau gaba ɗaya ta canja.”  “Bilkisu kinsan komai, wannan abun mafita ce gani da ke.”  “Nana ki saurareni, na gama magana fa wai ma idan aure ne macece zata nema masa aure? Ke awa da zaki nema masa aure, ba zai zo da kansa ba? Kinga kenan kece kika aureni bashi ba.”  “Ba haka ba ne Bilkisu, kusancin dake tsakanina dake ne yaja haka, amma da kin bashi dama zai zo da kansa Bilkisu.” “Ke amma kin rako mata wallahi, bantaɓa ganin ballagaza marar kishin kai ba irinki, mijin naki kike yawo da shi a haka? Kina neman a aure shi? Sannu Saratu ba ki yi wa kanki tanadi ba wallahi, bama alfahari dake.”  Wani irin ɗaci na ji ya tsayamin a maƙogwaro zuciyata ta fara wani irin raɗaɗi. ‘Ko Bilkisu ta kawo waɗannan ƙawayen na ta suci mutunci na ne?.’ Na tambayi kaina, ban kai ga samun amsa ba na ji wata ta ce.  “Ni yau na fara ganin asara irin wannan ba, amma dai duk da yadda aka yi mijinne baya sonta, shine ya bata dama ta kawo mai wata ko ya rabu da ita.”  Suka tuntsire da dariya, Bilkisu ta ce.  “Ba fa haka ba ne, ni bansan mene asalin matsalal ba kamar haihuwa ne ba ta yi.” Wani zafi na ji a zuciyata, wai Bilkisu ke hulaƙantani, tana shela da ni haka, kamar ba ta san komai ba.  “Ai kuwa babbar matsala ce, dole ta fito ta nema masa aure kafin ya kaɗata, dan ba kowa zai iya jurar mace daga ci sai kashi ba.”  Ƙwalla na ji tana zirara daga idona, a fili na furta.  “Ya Allah Ka na ji ka na gani.”  “Nana idan zaki tashi ki tashi, babu abinda zai sa na auri mijinki, gwanda ma ke nemi wata mafitar.”  “Ji ta ballagaza.” Wannan ita ce maganar da tafi ƙonamin rai, ba shiri na miƙe a raina na ƙudiri cewar zan nemawa Sardauna wata ba dole sai Bilkisu ba, tun da daman ba sonta yake ba.  “Na gode Bilkisu.”  “To Nanan Sardauna, ki gaida gida sannan ki canja shawara.” Bilkisu ta faɗa, wata cikin ƙawayen ta ce.  “Ki canja tunani kam, kuma a dage a rage ci tun da ba haihuwa za ayi ba.”  Ban kai ga ƙarasa fita ba, na ji sun kece da wata irin dariya, haka na tawo ina haɗa hanya sakamakon matsanancin jirin da nake ji, fuskata ta jiƙe shargab da hawaye, wannan cin mutuncin har ina? Lallai Bilkisu.  A haka na shigo cikin gidan, daidai lokacin da Turaki ya fito daga ɓangarensa, da sauri na yi ƙasa da kaina sabida kar ya ga fuskata. Ba ni da damar yin sauri sabida jirin da nake ji, hakan yasa na tafi a hankali.  “Nana!”  Ya kira sunana, ta dole na tsaya ba tare da na juyo ba.  “Kuna waya da Hajiyarki?”  Na gyaɗa kai, ba tare da na yi magana ba.  “Good.” Ya faɗa tare da fara tafiya, jan hanci na yi tare da wata shasheƙa da ta ƙwacemin ba tare da na shirya ma ta ba ya sa shi dawowa.  “Nana! Meke damunki? Kuka kike?” “A’a.”  “Ƙarya zaki yi min, Sardauna ne ba lafiya?”  “A’a.”  “To me ya sa ki Kuka?”  Ya faɗa yana matsowa inda nake, girgiza kai na yi bance komai ba.  “Me ya saki Kuka!”  Ya faɗa a tsawace. “Ba komai, ka yi haƙuri, zan faɗa ma.”  “Haƙurin me Nana? Me ya ta ɓa ki haka?”  “Ka yi haƙuri, zan faɗa ma.”  Na sake maimaitawa gaba ɗaya na ruɗe. “Nana kina da damuwa ne? Duk kin ruɗe kin fita hayyacinki, are you okay?”  “Yes! I’m okay.”  “Hhhm.”  Kawai ya faɗa tare da sa kai ya fice, ni kuwa har da harɗe ƙafa sabida sauri na shige ciki, ina shiga na faɗa kan kujera na fashe da kuka, mai tsuma zuciya. Kuka nake yi mai ƙarfi har sai da na fara jin ɗaci a maƙwogarona. Kukan da ya haifarmin da wani ciwon kan wanda ya haɗe da jirin da nake ji gaba ɗaya na ji duniyar ta fara yi min zafi, abubuwan sun har gitsemin sama ta juye ƙasa.  Daƙyar wani wahalallen bacci ya ɗaukeni marar daɗi, ina yi ina firgita, ina zabura kamar wacca za a taɓa, cikin barci na fara jin hayaniya sama sama. A hankali na buɗe idanuna sa suke jawur, wani irin sarawa na ji kaina ya yi, amma a haka na dafe kan na miƙe sabida jin kamar cacar baki. A hankali na leƙa ta window Sardauna da Turaki ne.  “Turaki ina so ka sani, ni Sardauna na yi maka nisan da har abada ba zaka taɓa kamoni ba, Turaki duk abinda zaka yi tsakaninka da ni sai da ido. Kasani abinda Sardauna ya taɓa har abada ya yi maka nisa.”  Turaki ya saki wani murmushi, sannan ya dafa kafaɗar Sardauna ya ce.  “Alfahari da fariya na ƙarya kake yaro, ni lokacin da zan zauna na yi wannan maganar marar amfani ma ban da shi, sannan ina tunasar da kai cewar Ajuri zuwa rafi, wata rana tulu zai fashi. Shashasha.”  Yana faɗin haka ya wuce yabar Sardaunar a wajen, da sauri na koma kan kujera na kwanta, na rasa mene asalin wannam faɗan dake tsakanin Sardauna da Turaki. Da ƙarfi ya saki ƙofar bayan ya shigo, na runtse idona sabida wani irin bugu da na ji zuciyata ta yi.  “Nana! Nana! Nana!”  Na buɗe idanuna na kalleshi.  “Me kike yi a kwance.” “Bakomai.”  Na faɗa ina miƙewa zaune.  “Me ya shigo da wannan ɗan iskan bangarena?” “Waye?”  “Karki rainan hankali mana, waye banda Turaki.”  “Bai shigo ba.”  “To aina ya ganki?”  “A parking space ne, bayan na dawo daga gidansu Bilkisu.”  “Hhm, har ni zai cewa wai na dinga yin adalci, me kika ce masa?”  “Babu abinda na ce masa, to me kake yi min da zan faɗa masa?”  “Nasan mike, nasani ko kin yi min wani sharri.”  “Uhm.”  Kawai na faɗa tare da sake komawa na kwanta, kallona ya yi sai kuma ya sha jinin jikinsa.  “To kawai yana ganina ya wani hau yi min magana, ni da ba shiga sha’aninsa nake ba, tun muna yara Turaki yake son shiga rayuwata, yana baƙin ciki da ni a rayuwarsa, ni kuma ko magana ma bana son naga ta haɗani da shi, ina kishin naga nasan abu Turaki ya san shi, shi ya sa ma duk family na bar masa, na ja rayuwa ta na yi gefe, ranar da na ga ya yi miki magana a family meeting wallahi Nana ji na yi kamar an watsamin tafasheshen ruwan zafi a zuciyata, na ji zafi fiye da yadda kike tsamanni.” “Hhhm, to yanzu ni me zai haɗani da shi da har zan hau yi masa magana akanka.”  “Ki yi haƙuri to.”  Ya faɗa yana kama hannuna.  “Bakomai.”  “Ya kuka yi?”  Tashi na yi zaune duk da jirin da nake ji yana ɗibana, na kalleshi sannan na ce.  “Akwai matsala fa.”  “Wace irin matsala?”  “Babu wani nau’in rashin mutunci da kasani da Bilkisu ba ta yi min ba, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, abun babu daɗin ji.”  “Ita Bilkisun?”  “Ita fa, ni kaina har mamaki na yi, kamar ba ta sanni ba.”  “Innullahi wa’inna illahir raji’un, to yanzu Hon ya zaayi?”  “Ina ganin kamar a ƙyaleta a nemi wata kawai.”  “A nemi wata kuma Hon?”  “Eyh a nemi wata, tun da ita ba yarda za ta yi ba.”  “Nana haka zamuyi ta zagaye mutane muna faɗa musu matsalalmu, suna ƙin amincewa shikenan mun tonawa kanmu asiri?”  “To ya kake gani zaayi? Mene mafita a ganinka?”  Shiru ya yi na tsahon mintina sannan ya ce.  “Ni fa da har ta kwantamin a rai, Nana ki sake komawa.”  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da huɗu.     (24) “A sake komawa? Wajenta kenan?”  “Eyh Nana, aganina a sake komawa mai nema ai yana tare da samu, kuma muke nema bai kamata mu yi zuciya ba Nana.” Shiru na yi ina faman tunani, tabbas zancen Sardauna gaskiyya ne, wanda yake nema ba ya taɓa fushi amma tabbas abinda Bilkisu ta yi min abu ne da yake nuna zallan rashin mutunci, amma ya zanyi tun da Sardauna yana so.  “Shikenan gobe zan sake zuwa ko?”  “Yawwa Nana, ki bi duk wata hanya da zaki bi kinji ‘yar Aljanata.”  “Ina son gobe zanje asibiti, ina yawan jin jiri da ciwon kai sosai.”  Na faɗa ina lumshe idona.  “Okay tom daga gidan nasu sai ki je asibitin, da mota zaki fita?”  Na girgiza masa kai tare da cewa.  “A’a.”  “Tom, me aka dafa mana?” Na girgiza kai.  “Banyi komai ba, amma muna da gurasa.” “To aban na sha da tea.”  “Tam.” Na faɗa tare da miƙewa, anan falon na kawo masa ya ci bai ji dinning ɗin ba. Bayan ya gama ci na kwanatar da kaina akan cinyarsa.  “Yaushe zanje na gaida Hajiya.”  “Wace Hajiyar? Taki ko tawa?”  “Duka biyun.”  “A’a Hajiya ta dai ba yanzu ba, yadda take wannan fushin, sai da Hajiyarki, ita ma ba yanzu ba.”  “Sai yaushe?” “Mu gama da abinda yake gabanmu Nana.”  “Eyh hakan kam gaskiyya.”’ “Yawwa ko ke fa.”  “Ya zancen tafiyarmu Turai? Gashi kuma Maulidi ya tawo ka ce Umarar Maulidi zamu.”  “Nana, turai ba yanzu ba dan Big Daddy ma ya hana, sai dai Umarar.”  “Shikenan yanzu an fasa?” “Ko za a je ba kusa ba.”  “Shikenan yanzu karatuna fa, gashi ‘yan anjimu on 11 this month zasu yi resuming level 300 zasu shiga.”  “To Nana ya zaayi? Haka Allah Ya ƙaddara amma ki kwnatar da hankalinki kin ji Nana.” “Alhaji ya mutu da burin na yi karatu, akwai alƙwarinshi akaina fa.”  “Nana mene haka wai? Da matsalal da take gabanmu zamuji ko kuma da wacca kike shirin kunno mana?”  “Ni ba matsala nake son kunnowa ba.” Na faɗa ina goge ƙwallar dake idona, ban ƙara ko minti biyar ba na tashi na shige ɗaki na kwanta, ina jinsa har ya shigo ya gama gyaran muryarsa ban ce ko ƙala ba, ya jawoni jikinsa.  “Nana nah, me na yi?”  “Babu komai.” “Bangane ba komai ba, gashinan kina wani yi min banza.” “Ni ba banza nake ma ba, kaina ke ciwo ne.”  “Tom, na ƙyaleki kike so ki ce ko?”  “Jiri nake ji.”  “Uhm, shikenan.”  Yana faɗin haka ya cikana ya juya ya kwanta, haka kawai yau na ji ni bana wani marmarinsa ko magana ma ban son yi da shi.  “Bazaki kulani ba ko?”  Matsowa na yi kusa da shi sannan na ce.  “Ka yi haƙuri.”  “Nana kullum baki da aiki sai ayi haƙuri, amma kuma ko an haƙura ba kya fasawa.”  “In sha Allah za a gyara.”  Daga haka ya muka kwanta.  ****** Yau ma kamar jiya tare muka fita da Sardauna, na yi gidansu Bilkisu ya yi ofis, yau ma na ɗan jima a ƙofar gidan kafin na shiga, ko dame zata zo yau oho? Sai da na ƙarewa gidan kallon, su Bilkisu sun fi mu kuɗi sosai da sosai ko unguwar da suke ma kaɗai ya isa tabbatar min, ga gidan masu ya tsaru da tsaruwarshi. A hankali na tura ƙofar falon na shiga sai dai babu kowa a ciki, haka na tura kai na shiga tare da yin sallama, sai da na yi sau biyar sannan aka amsa min.  “Nana! Me ya dawo dake kuma? Kar dai ki ce baki haƙura da wannan zancen ba.”  “Bilkisu kenan, ai kya tsaya mu gaisa.”  “Tom zauna mana.”  Na sami waje na zauna ita ma ta zauna.  “Ina ina saurarenki.”  “Bilkisu dagaske kike akan maganar da kika faɗan?”  “Wace magana?” “Ta wajen mahaifinki.”  “Nana zan miki ƙarya ne?”  “To amma me ya sa baki amshi mafitar da nazo da ita ba.”  “Nana! Wai ta ya zan auri wanda baya sona? Da auren mijinki da auren wanda Abbana zai ban duk ɗaya ne tun da duk ba sona suke ba.”  “Bilkisu baki bawa Sardauna dama ba ne, amma yana sonki kuma zai nuna miki soyayya, Bilkisu dan Allah ki gwada ba shi dama.”  “Wace kalal dama?” “Ya zo ku yi magana, ko tattauna ko fahimci juna.” Shiru ta yi sai kuma can ta ce.  “Shikenan ya zo yau.”  Har cikim zuciyata na ji daɗi, kuma na kasa ɓoye jindaɗina.  “Na gode miki sosai Bilkisu.” “Karki gode min Nana, dan ba cewa na yi na amince zan aure shi ba.”  “Nasan ma zaki amice, daga hakan in sha Allah.”  Na ɗan zauna a gidan nasu har wajen ƙarfe goma sannan na ta shi na nufi asibiti, dan har zanje wajen Dr Ɗan Adala, kawai na yanke shawarar zuwa asibiti mafi kusa.  Duk da kasancewarsa asibitin gwamnati amma ma’aikatan ciki sun kasance masu matuƙar kirki, tun daga zamana har layi yazo kaina ban ji sun hantari wani ko wata ba.  “Wacece Nana.” “Ni ce.”  Na faɗa ina miƙewa.  “Ki shiga ciki.” Godiya na yi mata sannan na ta shi na shiga Likitar babbar Macece mai mutunci, Dr Na’ima Daƙayyawa. Shine sunan da naga an rubuta a jikin tag ɗin ta, kallo ɗaya ta yi min ta ce da ni.  “Mrs Ta ambo, gaba ɗaya shekarunki nawa? Me yake damunki da zai haifar miki da Low Bp a wannan ƙarancin shekarunki?”  “Low Bp Dr.”  Na faɗa a hankali, ta gyaɗa min kai sannan ta ce.  “Yeah! Low Bp ma’ana jininki ya yi ƙasa fiye da tsammani, ya kamata ki cire duk wata damuwa a ranki, ke yarinya ce ƙarama. Baki kai matsayin da abu zai dameki ba.”  “Yanzu mene abun yi?” “Ki cire duk wata damuwa a ranki, ki miƙa al’amuranki ga Allah, komai ya yi farko yana da ƙarshe.”  “Tom.” “Matsalal gidan aure ce ko? Ki yi haƙuri muma dukkanmu haƙuri muke, rayuwar gaba ɗaya haƙuri ake da ita, kin ji?”  “Tam na gode, amma dan Allah likita na tambayeki.”  “Allah Ya sa Nasani.”  “Zuwa shekara nawa ne mahaifar mace take yin ƙwarin da zata ɗauke ciki?”  “Bangane ba.” “Ina nufin zuwa shekara nawa mace take iya fara ɗaukan ciki?”  “Shekarun da ta girma mana.”  “To wasu da mahaifarsu ba ta da ƙwari fa?”  “Mrs Ta Ambo am sorry bangane abinda kike son faɗa ba, can you please open your mind and talk?”  “Shikenan zan dawo wata rana.”  Na faɗa tare da tashi.  “Okay Allah ya ƙara lafiya.”  Har na fita na dawo, “Dan Allah zan iya samin numberki?” Kati ta ɗauko mai ɗauke da sunanta address ɗinta da lambar wayarta ta ba ne, na amsa tare da yi mata godiya na fice.  Kai tsaye gida na dawo, bayan na sha magunguna da aka bani na kwanta bacci ya ɗauke ni wanda ban tashi na sai gab da la’asar, a gurguje na yi ayyukana na gama, yau Sardauna zai je gidansu Bilkisu Allah Ya sa su fahimci juna, ayi ayi auren nan kowa ya huta da ko zan sami nutsuwa jina na ya dawo daidai.  Lokacin da ya saba dawowa ya dawo, da farin ciki na tarbeshi kamar yadda nasaba yi masa a farko, da mamaki yake kallona, har ya kasa ɓoye mamakinsa ya ce da ni.  “Nana me ya faru?”  “Ka fara wanka ka shirya sai mu yi magana.”  “A’a kinsan ni bana son irin wannan kawai ki faɗa min.”  “Bilkisu ta ce dai ta yarda ka je ku yi magana ku fahimci juna.” “Ma sha Allah, na gode miki matata abar alfaharina, Allah Ya biyaki.”  “Amin amin, yanzu je ka yi wanka ka shirya sai ka tafi.”  “Tom, yadda kika ce haka za ayi Hajajju, ko tare zamu je.” Ya faɗa yana shigewa ɗaki, na yi dariya sannam na ce.  “Ni wa? A’a dai.”  Ina zaune a falon ya fara kirani, na tashi na shiga.  “Ya baka gama shirin ba?”  “Ke zaki shirya ni.”  Dariya na yi tare da buɗe sip ɗin ta sa na ɗauko masa wani men lace milk clour. A yanzu Sardauna ba shi da kayan da suka fi men lace, tsaf ya shirya ya yi kyau, sannan na bashi lambarta ya tafi, bayan na yi masa addu’a. Ina jin ya tayar da motarsa wani abu sa soki zuciyata mai zafi da raɗaɗi, zuciyata ta fara bugu da ƙarfi numfashina ya kasa daidaituwa. Kowane bugu na zuciyata kamar guduma yake dukan ƙirjina.  08:00pm Na dubi agogon falon, ƙarfe takwas na dare. A yanzu nasan Sardauna ya ƙarasa gidansu Bilkisu, tun da ba wani nisa ba ne damu, wataƙila suna zaune a kan kujera ɗaya, ko kuma yana kallon fuskarta da wannan idanunsa masu sa mutum ya mance kansa. Na tashi na fara kai da komowa a tsakar falon da ya yi mini faɗi da yawa kamar yau na fara zama ni kaɗai, na ji gidan ya yi mini tsit. Na kalli kaina a madubi, idanuna sun kumbura, fuskata ta yi jawur saboda kukan da na sha tun ɗazu bayan fitar Sardauna wanda bansan ma na mene ba? ‘Yanzu haka ko me yake gaya mata?’ Zuciyata ta tambaye ni. Wani abu mai zafi ya taso mini daga can ƙasan makogwaro. Na runtse idona, sai na ga hoton Sardauna ya bayyana a raina yana yi mata wannan murmushin nasa mai bayyana kyawawan haƙoransa. Wannan murmushin da na ɗauka nawa ne ni kaɗai. Wataƙila ma yanzu ya manta da kukan da ya rinka yi mini a baya a kafaɗata. Wataƙila ya mance da ni da rayuwata ma, ya mance da duk fafutuka ta akan auren nan. Na matse hannayena da ƙarfi har sai da ƙasusuwan yatsuna suka yi ƙara ‘Ƙas’. Wani irin zafi mai cin zuciya ba tare da hayaki ya fito ba, na ji ya ratsamin zuciya. Na ji tamkar an matse mini maƙoshi, iskar ɗakin gadon ta daina isata. Na nufi taga na janye labulen, ina kallon waje ko zan ga hasken motarsa, amma duhu kawai nake gani. Shin ta fi ni kyau ne? Na sake tambayar kaina cikin damuwa. Shin ita ma zai koya mata yadda yake son abincinsa? Ko kuwa ita ma zai rinka cewa kishinta yake yi shi ya sa yake son killace ta? Kowane tunani yana soka mini wani sabon mashi a rai. Na tsinci kaina da fara zargin kaina. Wataƙila da na dage akan karatuna, da hankalina ba zai rinka karkata ga wannan kishin da yake neman haukatani ba. Na tuna yadda Sardauna ya rinka yaudara ta da kalamansa , yadda ya rinka nuna mini cewa ni ce tauraruwarsa ta har abada. Amma yanzu, tauraruwar wata tana shirin fitowa a sararin samaniyar rayuwarsa. Na koma na zube a kan dadduma, na takure waje ɗaya, ina jin yadda ɗakin yake juya mini. Duk dukiyar da Sardauna ya zuba mini a wannan gidan, duk motar da ya saya mini da zinaren da ya ba ni, a wannan daren na ji ba su da wani amfani. Domin dukiyar ba za ta iya siyan natsuwar zuciyata ba. Wani sabon kukan ya sake kufce mini. Kukan da ba na rarrashi ba ne, kukan da yake nuna cewa yanzu na shiga tarkon da ba ni da tabbas idan zan fito lafiya. Ni da kaina na ba shi izinin tafiya zance, ni da kaina na ce ya bi maganar iyayensa, amma a yanzu, na gane cewa sadaukarwar mace ga namiji babban kuskure ne. Agogon wayata ya buga ƙarfe goma. Shuru har yanzu bai dawo ba. Kowane minti ɗaya jin sa nake tamkar shekara guda. Zuciyata ta ci gaba da saƙa mini abubuwa daban-daban. Shin yanzu sun daidaita? Ko har an tsayar da ranar auren? Na dafe kaina, ina jin tamkar zai rabe gida biyu.  Kishin Sardauna ya riga ya zama wani baƙin lillibi da ya rufe mini dukkan farin cikina, ya bar ni a cikin duhun fargaba da rashin tabbas na abin da gobe za ta zo da shi. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da biyar.     (25) “Sardauna ba zai dawo ba ne?”  Na tambayi kaina ganin har ƙarfe sha ɗaya da kwata, tabbas nasan a yanzu sun sasanta kansu, ƙila ma sun tsayar da ranar aurensu, yanzu burin Hajiyar zai cika.  Sai sha ɗaya da arba’in Sardauna ya shigo ɗakin da nake, daga yanayin yadda yake magana zaka san fuskarsa fal take da fara’a kamar wanda aka yi wa bishara da gidan al’janna.  “Nana! Kina ina?”  Ya faɗa yana kunna hasken ɗakin, da sauri na runtse idona da.  “Oh My, wai kinyi bacci?”  Daidai lokacin wayarsa ta fara ƙara alamun kira na shigowa. “Salamu alaikum.” Ya faɗa cikin amon muryarsa.  “Alhamdulillah yanzu nake shiga gidan, ya na barki.”  Wani irin abu na ji ya doki

Chapter 13 of 16