Share this page
shi number exam card ɗina zai duba min, Jamb kuma na yi wa mijina magana ya yi min Regostration.  Da dadare bayan ya dawo na faɗa masa amma dai ya yi banza da ni kamar bai ji ba, haka aka kwana ɗaya aka kwana biyu shiru bai sake min maganar ba, a kwana na uku na yanke shawarar ƙara tun kararsa da maganar, sai dai a lokacin ma banza ya yi da ni.  Washe gari Ra'is ya zo mun da sakamakona na WAEC da NECO na yi ta murna ganin result ɗin, ya ce da ni wai Abba ya fara tambaya akan wai na yi rijistar JAMB ko banyi ba, kar su rufe.  Lokaci na farko da na fara yi wa wani na gidanmu ƙarya akan al'amuran gidan aure.  "Ra'is ban masa maganar ba, kwana biyu suna aiki a kamfaninsu ne, bai ma cika dawowa da wuri ba, amma in sha Allah zan faɗa masa."  "Tom yakamata dai gaskiyya, kinsan su Jamb ba wani dogon lokaci suke badawa ba fa."  "Nasani sosai, ina Yaya Ridwan?"  "Yana nan."  "Baice ka gaisheni ba? Shi fa bai taɓa zuwa ba. Kuma ya je duk  gidansu Yaya Radiya."  "To ai su yayunsa ne, ke kuma ƙanwarsa ce. Yaya Radiya ma tana gida."  "Zuwa ta yi?" "Eyh, ta kwana biyu ma."  "Tafiya mijin na ta ya yi?"  "A'a saɓani suka samu da shi, wai yana da wata matar a waje."  "Mata a waje? Yau she ya yi auren ba mu sani ba?"  "Bawai matar aure ba, abokiyar iskanci."  Kama baki na yi sannan na ce. "Lallai chaɓ." "Jiya kuma Hajja ta zo ta sauke kwandon rashin mutuncinta tsaf a gidan."  "Da aka yi mata me? Ita kuma." "Wai ai Yaya ce ba tasan mene darajar miji ba shi ya sa ya fita ya nemi wata."  Na yi matuƙar mamakin jin wannan abun, ko da yake a son zuciya irin na Hajja inda za a bata kuɗi ta bataƙi ko kisa aka yi ba ta ce, wanda ya mutum shi ya taso ya kashe wanda ya yi kisan. "Ita ta sani, yanzu mai Alhaji ya ce?"  "Ita Yaya ta ce ba zata koma ba, haka kawai ya kwaso wata cutar ya goga mata."  "Wallahi Allah da gaskiyyarta, kuma ko ya ce zai daina ba lallai ya daina ba tun da daman ba mutunci ne da shi ba."  Na faɗa daman ni tun da ba gaisawa ma muke da shi ba.  "Haka Yaya Ridwan ya faɗa, ya ce ko kotu ne sai anje an raba auren."  "Uhm, ni kaɗai ce Yaya Ridwan ba ya so."  Kallona Ra'is ya yi sannan ya ce.  "Waya faɗa miki haka?"  "Ra'is alamunsa na gani, kana ganin ko Allah Ya sanya alheri bai yi min ba, kai ko gidana bai taɓa zuwa ba, farkon aure na da na kirashi da ya ɗaga ya ji ni ce sai ya katse."  "Kinsan halinsa dai."  Ra'is ya faɗa yana miƙewa. "Ni zan tafi."  "Tsaya na baka abu ka kaiwa Hajiya." Na faɗa ina shigewa ɗaki, na ɗauko wata leda da daman na ajiyeya na ba shi ya tafi sannan shima na bashi dubu bakwai, wanda shine kuɗina gaba ɗaya.  Ko da Sardauna ya dawo sai da ya tambayeni waye ya zo? Na yi mamaki sosai na yadda akayi ya sani, shi ba camera ce da shi ba amma ya sani, ko da na ce masa Ra'is ne bai wani saki fuska ba. Bayan ya ci abinci na ɗauko masa takardar da Ra'is ɗin ya ciro ya kawo min, buɗar bakinsa sai cewa ya yi.  "Kun dage dai sai kin yi karatun ko?"  "Alhaji yana so kasani kaima."  "Uhm."  Ya faɗa ya ci gaba da danna wayarsa, ni kuma na zauna ina wasa da ƙafarsa. Sai da aka kwana biyar da maganar sannan Sardauna ya kai ni wajen Rijsitar jamb, shima sai da na sake masa magana sannan ya kai ni.  Masu kuɗi basu da al'adar zuwa gidan mutane, amma kuma suna da kirki idan anje musu, duk ranar da mukaje gidan Hajiyarsu kamar zata cinye ni sabida kulawa ita da ƙannensa, haka idan na kiranta a waya shima kamar zata goyani, duk mutan gidansu suna sona sosai idan na je musu, sau ɗaya ƙanwarsa Lubna ta zo shima daga lectures ta dawo shine ta biyo.  Haka lokacin zana jarabarwar Jamb ya zo Sardauna ya kai ni na yi, idan na sami maki 189 na ji daɗi sosai domin zan sami Addmission a FUD, haka a gida kowa ya ji daɗi ya yi murna.  A lamarin Yaya Radiya kam, ta dage ba zata koma ba, haka Yaya Ridwan ma domin sun binciko asali ba iya wannan abun ba ne ya baro ta gidan, bayan neman mata harda shaye shaye yake yi, shima dalilin da ya sa su ka gano wata rana ne yazo gidan namu a buge ya yi wa musu tijara da hau na ƙarshe, ya ci musu mutunci sai da Ra'is da Yaya Ridwan suka fita dashi. Amma da Hajja ta zo yin ta ta tijirar sai cewa ta yi an dake shi an ji masa rauni. A yanzu Alhaji ya daina damuwa da abubuwan Hajja tsakanin shi da ita sai dai tom, amma ya faɗa mata a wannan maganar ba yadda ya iya tun da yarinya da 'yan uwanta sun dage akan ba zata koma ba. Sardauna ya ɗan san maganar tsilli tsilli ban saki jiki na faɗa mai komai ba, tun da naga kamar bai son maganar. Da kan sa ya kaini gidan Anty Adiza har sau biyu a cewarsa duk ranar da na je ina samu sabon ilimin sarrafa fulawa.  Kwance ta shi ba wuya a wajen Allah har aka zo lokacin da jami'a ta fara raba Addmission, kuma ina cikin mutanen da suka samu a lokacin farko. Alhaji bai taɓa zuwa gidana ba sai a lokacin ya zo ya yi wa Sardauna godiya akai, daga nan na fara shirye shiryen makaranta sai dai har zuwa wannan lokacin babu ciki a jikina, tun ina ɓoyewa har abim ya fara damuna, har na fara sanar da Sardauna amma sai ya ce shi haka yake so, da ya ga dai na fara damuwa da al'amarin bisa ga auren Malaika da akayi bayan namu, ta tafi jihar kano kuma a yanzu ta sanar da ni cikinta ya shiga watan haihuwa. Hakan ya sa na sake damuwa, sai shima ya fara nuna damuwarsa, yake kuma kwantar min da hankali. Da dai ya ga abun namu ba ƙarami ba ne sai ya ce na shirya zai kai ni naga likita. Rasheed shekoni special hospital ya kaini, asibiti da na yi ma sa gani na biyu a rayuwata, lokacin da mai mashin ya tsaya gyara. Kai tsahe wajem likitan muka je wanda daga yanayinsu kasan abokinsa sa ne, bayan ya yi masa bayani likitan ya sa na kwanta akan wani gado anan ya yi dube duben da zai yi sannan ya ce na koma na zauna.  Kusan mintina goma sha biyar, sannan ya fara bayani. "Madam mahaifar ta yi ƙanƙanta ne da ɗaukan ciki, amma kuma yau da gobe ya sa ta fara girma, idan kika yi haƙuri kuma kin zuwa ganin likita in sha Allah za ta buɗe."  "To wane magani za'a ba ni."  "A'a babu magani fa."  "A'a a bata wannan pils din mana."  Sardauna ya faɗa, wani kallo na ga Dr ya yi masa sannan ya ce.  "Ai zai yi mata ƙarfi, sai dai a dinga ba ta sha sau daya ko biyu a wata."  "Eyh hakan ma ya yi."  Sardauna ya faɗa, sannan ya dafa ni yana faɗin.  "Nana ki daina damuwa kin ji ko, rashim haihuwar ba matsala ba ne."  Na gyaɗa masa kai, sannan ya ce.  "Ki jirani a mota."  Na miƙe na fice na barsu a cikin ofis ɗin, ina fitowa waya ta ta hau ruri, ina dubawa na ga sunan Ra'is na ɗaga da faɗin.  "Ra'is ya aka yi?"  "An raba auren Yaya Radiya fa."  Gaba ɗaya sai na ji wani iri, Allah ya gani ina matuƙar tsoron mutuwar aure a rayuwata.  "Yaushe?"  "Shekaran jiya Hajiyarsa ta zo ta yi wa Hajiya rashin arziƙi. Yaya Ridwan ya sa 'yan sanda suka kamata, amma a ranar aka sake ta shine ɗazu ya aiko da takardar."  "Ka ce tashin hankali aka yi kenan? Allah Ya tsare gaba zan shigo in sha Allah."  "Amin amin, ya shirin makaranta?"  "Ranar monday zamu fara lectures."  "Allah Ya sa albarka."  "Amin amin."  Daga haka na katse wayar na shiga mota na jira Sardauna, sai da ya ɗau wajen mintina ashirin sannan ya fito, a hanya nake sanar da shi mutuwar auren Yaya Radiya, ya tausaya har muka koma gida.  Ranar Monday ranar da zan fara lectures Sardauna ya tashi baya jindaɗi kwata kwata, ta dole na haƙura da makarantar ban je, sabida bai samu kansa ba sai wajen sha biyu na rana. Haka washe gari ma ya tashi da irin ciwon, gaba ɗaya na ruɗe kamar shafar aljanu, duk asuba idan ya fara juye juye bai nutsuwa sai rana ta fito, kusan sati biyu a haka, ta dole na haƙura da makarantar sabida lafiyar mijina tafi min komai a duniya, har da ni kaina.  Legendspen 08129553971. *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha biyu.     (12) Abu kamar wasa ciwon Sardauna yana ta tsananta har lectures ɗin mu ta yi nisa, tun da ina bibiyar al’amarin makarantar ta waya har wasu malaman suna shirn fara yin test.  Tun ban damu da lamarin makarantar ba har na fara damuwa, mussaman da Baba ya kan kirani ya ce min ya karatu, gashi har Ra’is ya aiko ya kawo min dubu ashirin wai na ƙara kuɗin makaranata kar a bar mijina da wahala, ranar har da ƙwallata, da Sardauna ya dawo na yi masa maganar sai ya ce da ni, lafiyarsa zan sa a gaba sama da komai, daga ba ya na ce masa ai har lectures ɗin 12 muna yi har 2 wata ma 4 ce dan haka idan ya fita zan iya zuwa, ya daɗe yana kallona kafin ya ce ya amince.  Daga nan na fara zuwa, amma duk wata lectures ta ƙarfe takwas ko goma babu ni a ciki, cikin ikon Allah kuma ciwon na shi ya fara baya daga nan na samo damar hallartar ta ƙarfe goma amma dai banda ta takwas. Tabbas yanayin makarantar ta burgeni, kuma ina jindaɗin zuwa makarantar sannan na mayar da hankali akan karatun sosai, dan dana ta shi cikin masu ƙoƙarin ajin na shiga ana damawa da ni.  Kwance ta shi babu wuya a wajen Allah, mu ka cinye zangon karatu na farko, bayan munyi jarrabawa muka sami hutu na sati biyu, a lokacin ne naje gida Alhaji yana ta farin ciki da alfahari da ni da karatun, Sardauna kam ya sha albarka kamar Alhaji zai ari baki, ita ma Yaya Radiya Addmission za a sama ta a makarantar lafiya, washe gari na je gidansu, Hajiyarsa da Lubna gwanin sha’awa sai kuma na tarar da babbar yayarsa ta England ta zo jiya Sister Noor suke ce da ita, dake su lamarinsu kamar ‘yan chochi kowa Sister ce, kamar baki!  Sardauna na fita TURAKI ya shigo, wanda rabona da shi tun ranar Family meeting ɗin da suka yi wanda ba asake wani ba sai bayan wata shida kuma da dukkan alamu wata shidan ya kusa dan na ji Sister Noor tana cewa tana nan za ayi.  Yana ganina ya washe min baki tare da faɗin.  “Matar ƙani.”  Kaina a ƙasa na ce.  “Ina kwana?”  “Lafiya ƙalau ya kike ya gida?”  “Alhamdulillah.”  Daga nan ya shige wajen Hajiya, ita ma bai daɗe ba ya fito ya yi wajen Sister Noor, ita ce suka daɗe suna hira kusan awa ɗaya, har ya tafi Sardauna bai dawo ba. Bayan Sardauna ya ɗaukeni da yamma daga nam ya kai ni gidan Anty Adiza sai wajen tara ya dawo ya ɗauke ni.  A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah har muka cinye hutunmu muka koma makaranta, abubuwa suka ci gaba da gudana ba mu daɗe da komawa ba sakamakon jarabawar mu ya fito idan na sami 3.67cgp, na yi murna sosai kowa ma ya yi murna banda Sardauna, kuma na yi alƙwarin ƙara dagewa na sami sama da haka a wannan zagon, inda zan sami CGPA mai kyau.  Zancen ciki dai har yanzu shiru kamar an shuka dusa, magani dai ina sha sau biyu a wata wani lokacin ma Sardauna ya kan ce min na sha sau uku a wata ko zan samu cikin ya zo da wuri.  Wannan karon bansami zuwa Family meeting ɗinsu Sardauna ba sabida ina da test har biyu a ranar, dan mun kusa fara jarrabawar zango na biyu, daman haka karatun yake da zarar zangon ya fara zaka ga yazo ƙarshe. Lokacin jarrabawa da ya zo Sardauna ya tsiromin da wani abu, baya bari na na yi karatu kwata kwata, ya ta takuramin ayi ta abu ɗaya ba gajiya, gashi kuma ya ce dani yana so a rage amfani da kayan wuta sabida jan kuɗi, ya ce a daina amfani da dutsen guga da abin girki, na ce to daga baya ya ce adaina kumna ac sai dai fanka, duk da yanayin zafi na amince sabida tausayin da na ke yi masa. Wata rana bayan ya dawo ya ce wai na daina amfani da firinji kuma iya nawa, anan ne na so na ce wani abu sabida yanayin zafin da ake yi na gari amma ya ce da ni. "Nana! A gidanku babu firinji, baki sa ba shan sanyi ba, sabida yanayin unguwar ku ma zafi ake yi, dan haka anan ma ba zai zama wani abu ba dan na ce ba zaki dinga kunna firinji ba, sabida yanayin jan wutarsa." Tun daga wannan lokaci bansake gigin kunna firji ba da duk wani abu mai jan wuta, haka na yi ta fam da karatu ga wasu ƙarin wahalhalu da Sardauna ya fito da su, duk da ni ban taɓa ganin su da idon wahala ba, sai na bautar aure.  Cikin ikon Allah muka kammala jarrabawarmu, mu ka sami hoto na wata biyu, a wannna lokacin komai ya dawo daidai tsaƙani da Sardauna duk da bai janye wasu dokokin na sa ba, amma yanzu mun kan zauna mu yi hira, mu kan yi ‘yan wasannin mu da muka saba yi a baya.  Kwancw ta shi ba wuya a wajen Allah muka cinye wata biyu na hutu a kafara shirye shiryen komawa makaranta sai dai Sardauna ya fito min ƙarara ya ce da ni bazan koma makaranta ba, na yi tunanin a wannan lokacin ne ba zan koma ba shi ya sa ban damu da hakan ba. Amma ganin har an kusa cin tsakiyar zango na sake yi masa magana sai ya ce da ni gaba ɗaya karatun ne ba zan ci gaba, wata ƙara na ƙwalla tare da zubewa a ƙasa, abun mamaki sai ga jini yana zuba bayan faɗuwar da na yi, ko da muka je asibiti sai aka ce ɓari na yi. Na yi danasanin faɗuwar amma kuma na ji ɗaɗin cewar yanzu mahaifata ta yi ƙwari zata iya ɗaukan ciki.  Bayan na dawo gida na yi ƙaramar jinya na warke, mu ka ci gaba da Sardauna inda ya ce shi fa a’a Boko Haram, ba zam ci gaba. Na yi kuka sosai na nuna masa damuwata amma Sardauna ya ce a’a, ranar da abun ya yi ƙamari sardauna ya zaunar dani ya yi ta yi min bayani amma na nuna masa ni a’a Abbana yana son karatun nan gashi na fara har na cinye shekarar farko ga shi course mai kyau ma aka bani. Amma sardauna ya fara yi mini magiya yana haɗani da Allah.  “Dan Allah ka barni, tun da na fara kamar yau ne zan kammala.”  Na faɗa ina goge ƙwallar da ta fito daga idona, ya kama hannun tare da faɗin.  “Sakko nan.”  Na sakko na zauna, hannunsa yana cikin nawa ya fara magana.  "Nana, ina da arziƙin da zan riƙe ki bake kaɗai ba har da gidanku, muna da arziƙin da bazamu taɓa talauci ba, Nana a cikin gidan nan zaki zama kamar sarauniya ne, Nana bana son karatun boko nan, Nana bana son cuɗanya da maza, ina miki so mai tsanani, ina miki kishi mai zafi Nana dan Allah dan Annabi ki haƙura da karatun." Gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, maganganunsa gaskiyya ne dole akwai kishi a hakan, kuma ni ina son sa bana son abinda zai dameshi amma Alhaji fa?.  “Sardauna Alhaji fa? Na yi Yaya da shi?”  Wani murmushi ya sakar min, ganin ya fara nasara a kaina tin da har na fara tunanin yadda zaayi da Alhaji.  “Honey! Idan kin amince Alhaji ma zai amince ba zai zama mai wahala ba.”  Shiru na yi, ta ɓari ɗaya ina jin son mijina yana rura zuciyata, ta ɓari ɗaya kuma ina tausayin Abbana na yadda yake jindaɗin karatun nan da nake yi.  “Kin ji dan Allah My love.”  “Shikenan zan sake tunani.”  “No wane tunani, kawai ki amince idan ba haka ba shikenan zan barki ki yi karatun, nima sai na tafi can America na ƙaro karatuna bayan shekara bakwai sai na dawo.”  Kamar saukar aradu haka na ji maganar tasa, ya tafi ya yo shekara bakwai ya barni, ina zan sa raina?  “A’a shikenan na haƙura.”  Na faɗa amma har cikin raina ban so ba kuma banji daɗin haka ba. Allah Ya gani ina son karatuna, kuma ina tausayina Alhaji, ban ma san yanayin da zai shiga ba idan na sanar da shi hakan.  “Amma ya na ga kamar kin damu.”  Kallonsa na yi sannan na ce.  “Bansan ya Alhaji zai yi ba idan ya ji hakan.”  “Ba zai ji komai ba, ai yasan nine mijinki a yanzu nike da iko akanki, shi sai dai mu yi masa biyayya, kuma ai mun yi masa tunda kin fara karatun.”  “Uhm.”  Kawai na faɗa, dan bansan wani abu da zan iya ƙara cewa ba, ni gaba ɗaya ma kaina ciwo yake min, hutu nake buƙata.  “Je ki kwanta.”  Kamar mai jira na miƙe na nufi ɗaki na kwanta, sai dai gaba ɗaya bacci ya ƙaura ce min, na rasa abin yi kwata kwata, waya ta na ɗauka na shiga rubutawa Ra’is message ta whatsapp, na yi sa’a koma yan kai.  “Salam, Ra’is ina cikin damuwa Sardauna ya hanani komawa makaranta.”  Na tura masa, cikin ƙasa da mintuna biyu ya dawo min da amsa.  “Ki yi min ƙarin bayani, bangane abinda kike mufi ba.”  “Na ce ma Sardauna ya ce bazan ci gaba da zuwa FUD ba.” Na tura masa, can ya dawo min da amsa.  “Shi ya isa? Sai da kika yi wannan nisan?”  “Ra’is gaba ɗaya na rasa abinda yake min daɗi gashi result ɗin mu ya fita ɗazu har na duba.”  “Me kika samu?” “CGPA ɗina 3.84.” “Shine zai hanaki, kina da second class offer? Dole a san abun yi.” “Mene shawararka?”  “Zan yi magana da Yaya Ridwan.”  “Kasan ba zai shiga al’amura na ba.” “Me ya sa zai shiga mana, zaki ji duk yadda muka yi.”  “To karka kirani kamun magana kawai ta nan.”  “Me kike kalla haka a wayar, da dukkan nutsuwarki?”  Sardauna ya faɗa yana zama kan gadon, yaƙe na yi masa da baki sannan na ce.  “Da Ra’is muka yi magana.”  “Me kuka ce? Ko shawara kika nema wajensa?”  Na gyaɗa kai ba tare da na ce komai ba.  “Okay kin kyauta, ba ni wayar ki kwanta.”  Ba musu na miƙa masa wayar, na kwanta kamar yadda ya ce.  Washe gari da na ta shi na ga wayar a gefen drower na ɗauka na kunna data, ina shirin duba saƙon Ra’is sai dai babu lambarsa a wajen an goge ta, alamun Sardauna ya ga chat ɗin mu kenan ya goge?  Ajiye wayar na yi na fita zuwa kicin, bayan na haɗa komai na breakfast na ajiye masa, sannan na shiga toilet zan yi wanka, ina banɗakin na ji rurin wayata alamun ana kira, sai da na fito sannan na ga lambar Hajiya ce ke kiran, na yi tunanin zata iya kasamcewa Ra’is shi ya sa ban bi kiran ba na jira ya gama ya fita.  Sai bayan ya fice na dawo na bi wayar, Hajiya ta ɗauka bayan mun gaisa ta ce daman Ra’is ne kuma ya fita, na ce to idan ya dawo ya kirani. Daidai lokacin aka fara knocking ƙofa.  “Hajiya ina zuwa, an bugo.”  “To Nana sai anjima, Allah Ya yi miki albarka.”  “Amin amin.”  Na faɗa ina nufar ƙofar, Ra’is na gani na matsa masa ya shigo.  “Ina wayarki?” “Ga ta na miƙa masa.”  Dubawa ya yi ya ga babu lambarsa, sannan ya miƙa min ta sa.  “Karanta.”  Karɓa na yi na duba message ɗin da aka tura masa da lambata.  “Ka fita sabgar gidana, zan yi komai da kaina.”  “Ra’is na duba da safe na ga ko ka tura min saƙo na ga babu lambarka gaba ɗaya.”  “Na kira da safe naga ta na sa failed, mijinki ya duba wayarki kenan?”  “Da alama kam.”  “Lallai mutumin nan, Nana mun yi magana da Yaya Ridwan, ya ce tun farko abin da ya guda kenan, amma dai tabbas mijinki ba isa ya hanaki karatun nan ba.”  Zama na yi akan kujera, sannan na ce.  “Ra’is ni wallahi duk tsorona Alhaji, da halin da zai shiga.”  “Nana ko ba dan Alhaji ba, ko dan gobenki maza ba kowa ke da tabbas ba, yanzu ji dai Yaya Radiya, yanzu da ta yi karatun ta tun farko da yanzu an nema mata aiki.”  “Wallahi hakane Ra’is, duk jikina ya yi sanyi amma zan sake lallaɓashi nima.”  “Tom shikenan, mu dinga waya a wayar Hajiya.”  Ya faɗa tare da tashi ya tafi, da Sardauna ya dawo sai ya hau banbami, faɗa na ba gaira ba dalili ya ma ƙi bari mu yi wata magana da shi, na rasa aina ya sami labarin zuwan Ra’is ko CCTV ce da shi da bansan yana da ita ba? Wani ɓari na zuciyata ya ce mai gadi, da sauri na dakatar da wannan tunanin, sabida zato zunubi ne.  Kwata kwata Sardauna ya daina fahimta ta, ya daina zama da ni, ya daina magana da ni, faɗa ta ko ina? Na sanar da Ra’is halin da ake ciki ya ce da ni wai tsoratarwa ce amma idan ya ga na dage akan matsayata dole zai sakko tun da yana sona.  Abu dai sai gaba yake, har ta kai Yaya Radiya da Yaya Rumaisa sun san da maganar kuma babu wacca taban shawara akan na amincewa Sardauna akan ajiye karatuna, kuma na tabbatar dukkansu akan gaskiyya ne. Sardauna ya zuba min ido ni da ‘yan uwana akan harkar karatun da suka na ce sai na yi.  Ra’is ya ce da ni yau Yaya Ridwan zai sami Sardauna su yi magana, amma abinda ya ban mamaki yanda Sardauna ya shigo gidan yana wuci kamar zaki.  “Nana! Dole yau ki zaɓa ko ni, ko ‘yan uwanki da suke son ki yi karatun boko?”  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha uku.     (13) (Not edit) "Bangane ba Sardauna! Bangane ba?"  Na faɗa ina miƙewa.  "Na ce ki zaɓa 'yan uwanki ko ni?"  Wani abu na ji ya daki zuciyata, bansan haka nake ba sai yanzu, nasan dai ina son 'yan uwana amma bansan zan iya zaɓarsu akan Sardauna ba sai yanzu.  " 'Yan uwana mana."  Ya kalle ni sosai sannan ya ce.  "Nana 'yan uwanki?"  "Ina son su, suna sona Sardauna."  "Ni bana sonki Nana? Bana sonki? Wannan shine sakayar soyayyar da zaki yi min?"  "Sardauna ina sonka! Ina sonka, matsayin miji kake da shi a wajena mutum mai daraja a rayuwata sama da kowa, amma tabbas 'yan uwana abun so ne, kaima kana da su kana son su, kuma na zaka juri na yi wani abu mara kyau akam su ba."  Zama ya yi akan kujera, sannan ya ce.  "Nana ni mijinki ne, dole na yi kishinki sun san dalilin da ya sa bana son ki yi karatun? Sabida ina da kishi mussaman na ki, ban taɓa kishin wata mace a duniya ba sama da ke, Nana wallahi har cikin zuciyata nake kishinki bazan iya jurar gani kina fita kullum ba, bazan iya ba. Amma idan sun dage shikenan Nana zan sauwaƙe miki kije ki yi karatun acan, dan dama na fuskanci so suke su raba mu, zan bar musu." Ban taɓa tunanin jin wannam kalmar daga bakin Sardauna ba ko a mafarki, sai da na ji gabana ya yi wani irim faɗuwa. Na ɗaga kai na kalleshi amma na kasa magana, kawai na tsinci kaina da shigewa ɗaki na barshi s wajen.  "Rabuwa da ni Sardauna akan karatu? Tabbaa Sardauna baya son karatun nan, kuma hujjarsa ɗaya ita ce kishi, amma ai abinda kake so shi kake kishi, tabbas yana sona, nasake tunani."  Haka na yi ta ƙulle ƙulle da kwance kwance a cikin raina har wayewar gari, bayan na kammala masa abun karyawa ya ci na koma ɗaki, kasanxewar yau weekend ne bai fita sai rana kuma na ji yana cewa wai yau Big Daddy zai dawo, ko waye hakan oho masa.  Ina zaune cikin ɗaki bayan na sanar da Yaya Radiya yadda muka yi da shi, tana ta

Chapter 7 of 16