mini dukkanin ɓacin ran da sheɗan yake son san ya mini.
Na yi murmushi ina matsowa sannan na ce.
"Ai da ka jirani, amma bari na duba maka nina san wa'yanda zasu yi maka kyau."
Na tsugunna a ƙasa na fara kwashe kayan da ya zuzubar a ƙasa ina zuba su kan gadon, sai da nagama kwashe su tsaf sannan na ce.
"Bari naga wanda zaifi maka kyau."
"Hon!."
Na ji sassanyar muryarsa ta kira sunan ds na tabbatar sai soyayya ta yi daɗi yake kiranshi.
"Naam Hon!."
Na amsa masa nima cikin tawa sassanyar muryar da nasan ba ta yi ko rabin tasa a daɗi da sanyi ba, abu guda ɗaya da nake ƙara yararwa kaina shine. Sardauna Mijina ba tsarar aure na ba ne, Sardauna ba aji na ba ne, Sardauna yafi ni komai, ko naƙi ko na so Sardauna alfarma ya yi mini ya aureni, sabida yana sona.
"Kayan nan kamar ba'a taɓa gogesu ba ko?."
Ya faɗa yana taɓa kayan a yamutse kamar ba na sa ba. Da mamaki na kalleshi, sannan na kalli kayan, inda sardauna yake kai wanki da guga ba ƙaramin waje ba ne a Duste, idan suka yi maka wanki zaka rantse kayan ba a taɓa sa su ba, gasu nan suna sheƙi amma yake cewa kamar ba'a taɓa gogewe ba, 'ko ya fara ciwon ido ne?'
"Ko?"
Ya sake faɗa, sai da na yi murmushi sannan na ce .
"Wai Hon me ka gani ne?"
"Duk sunyi wani sikwizin, kamar an ƙwato su daga bakin kura."
Na yi dariya ganin yadda yake taɓe hanci, kamar yana riƙe da kashi.
"To ai duk kaine ka yi musu haka."
Na faɗa ina ci gaba da duba kayan.
"To ai bansan zasu yi haka ba, yanzu haka zan dinga fita kamar almajiri?."
Ya faɗa kamar zaiyi kuka, gaba ɗaya naji nustuwata tana shirin barin gangar jikina, a ruɗe na ce.
"A'a Hon! Ya zaayi ka fita a haka? Zan bawa Madu ya kai wajen guga a sake gogewa, tun da kaga mu nan bama amfani da abu mai jan huta, mussaman dutsen guga, Tv, hita, da kukin gas, wani lokacin ma cewa kake a kashe fanka sabida Mita kuɗin wuta da wahala."
"To ya zaayi idan abu yakama dole ayi, ki yi amfani da dutsen kawai ki gogesu, amma kafin na dawo fa dan Allah Hon."
Haka kawai sai naji jikina ya yi wani iri, Miji na da nake so, nake ƙauna sama da komai shine zai dinga haɗani da Allah akan na yi masa guga, guga dai abar banza.
"Haba Hon! Haba Haba! Kafin ka dawo angama in sha Allah."
Na faɗa ina miƙa masa wani light bulun yadin.
"Kaga wannan bai yi sikwizin sosai ba."
Karɓa ya yi yasa, ni kuma na ɗau mataji na hau taje masa gashi, sai da gashim ya yi kyau sannan na sa masa hularsa, na fesa masa turare muka fito.
"Nifa na makara gaskiyya, na yi birek fas a ofis kawai."
Ya faɗa yana niyar ficewa.
"Haba Hon, ka tsaya dan Allah."
"Hon it is almus 10:30, na makara sosai fa, ki ajiye min idan na dawo na ci."
Bai jira amsa ta ba ya fice, yunwar da nake ji tun ta daren jiya da kuma ƙarin ta yau da safe ya sa na nufin kan dinning ɗin na fara cin abincina, bayam na kammala na kwashe koma na kai kicin, sannan na shiga ayyukana.
Ban ni na kammala komai ba sai wajen ƙarfe tara da rabi, Sardauna ya kawo mun masu aiki har guda huɗu amma ina sallamarsu, Allah Ya gani ina tausayin mijina bana so na ga yana ta kashe kuɗi a aikin banza, shi ya sa da ya kawo nake sallamarta, amma sai ya sake kawo wa, wai ance yawan aiki yana sa mace ta tsufa shi kuma bai son ma tsufa, sai da na yi da gaske kafin na fahimtar dashi cewar na haka ba ne.
Ina zama kan kujera bacci ɓarawo ya yi gaba dani ba tare da sani na ba. 'Gur! Gur! Gur!' Cikin bacci nake jiyo kukan wayata, ba shiri na buɗe ido na kai hannu na ɗauka, sunan Fauziyya ya bayyana akan Skirin ɗin wayar, bude ido na na yi gaba daya na ƙarewa wayar kallo, ina son ɗauka ina jin tsoron Sardauna ya rabani da kula ƙawaye, haka wayar ta ƙaraci kukanta ta gama kiran ya katse, sai a lokacin na duba naga wannan shine kira na bakwai da ta yi mini.
"Ko mutuwa aka yi?."
Na tambayi kaina, ba shiri na fara kokarin buɗe wayar na kira ta, sai dai ban kai ga kiran ba na ta kiran ta sake shigowa, ɗagawa na yi da faɗin.
"Salamu alaikum, Fauziyya."
Na faɗa murya ta ƙasa ƙasa.
"Nana ina kika saka wayarki, ina ta kira?."
"Wallahi bacci nake Fauziyya, Ya kike?."
"Ina lafiya, matar nan gaskiyya kina hutawa abunki. Sardauna ya tsaya miki."
Na yi murmushi mai nuna jindaɗi, sannan na ce.
"Wallahi tun da ya fita kawai na kwanta."
"Ai haka ake so, kin ga nazo bayan ku ne gidan yayar mijina shine na ce ko kina gida na biyo, kuma gashi na samu tabbaci."
Dum! Dum! Na ji gabana ya shiga faɗuwa, Sardauna baya sona da kowacce ƙawa, bai taɓa ce mini kar da ƙawayena su zo, amma ya fito ya nuna baya son ina kula su, ba ma iya su ba kowa ba ya so, ni kuma duk wani abu dai zai ɓata ran Sardauna bana maraba dashi.
"Kinyi shiru?"
Muryar Fauziyya ta dawo dani daga tunanin da na fara.
"Dan zaki zo gidana sai kin tambayeni? Kawai ki tawo, amma da wuri dan Allah kafin huɗu zai zo mu fita."
"Ah to ko ba sai na zo ba."
"Kai! Ya zaayi kive haka, kizo mana dan Allah."
"Toh shikennan yanzu zaki ganni."
Daga haka ta katse kiran, na miƙe na shiga ɗakina na ɗaura alwala na gabatar da sallah azahar ganin karfe ɗaya ta yi, ina idarwa na shiga kicin na ɗora taliya jollop, sanin cewa zata iya zuwa a kowanne lokaci yasa na yi amfani da gas na ɗora girkin.
Ina fitowa daga Kicin ɗin, na koma ɗakin Sardauna na fara haɗe kayan ina ninke su, daniyar idan ta tafi sai na goge su tunda mu nan bama rasa wuta kwata kwata.
Ina cikin ninke kayan na ji sallama a falo, Allah Ya gani bana maraba da dukkan abinda zai ɓata ran mijina, na yarda da Allah, na yarda da cewar ina son Sardauna sama da komai. Hakan ya sa bana farin ciki da zuwan Fauziyya, ƙaramin tsaki naja sannan na miƙe na fito, sai na zo dab da falon sannan na janyo murmushin yaƙi na sanya shi a fuskata. Itama fuskarta ɗauke da murmushin ta tare ni da cewa.
"Ƙawatah, ƙawar yarinta, ƙawar girma."
Na yi dariya na zauna akan kujera ina faɗin.
"Tawo mana."
Zama ta yi tana ƙare mini kallo. "kin canja gaba ɗaya abinki, kinsami aljannar duniya."
Na yi dariya da faɗin.
"Alhamdulillah wallahi, bara na kawo miki ruwa kafin mu ci abinci."
"A'a yana ji ba sanyi a wannan zafin?."
Ta faɗa bayan na kawo mata ruwan, na yi murmushi sannan na ce.
"Kinga ni mura nake, shi kuma kwata kwata ba ya shan sanyi."
Sai bayan na faɗa na yi mamakin yadda na iya shirya ƙarya a lokaci guda, na tuna lokacin da muka yi magana da Sardauna akan firjin.
"Nana! A gidanku babu firinji, baki sa ba shan sanyi ba, sabida yanayin unguwar ku ma zafi ake yi, dan haka anan ma ba zai zama wani abu ba dan na ce ba zaki dinga kunna firinji ba, sabida yanayin jan wutarsa."
Allah Ya gani ina tausayin mijina, ko bai ce ba nasam yadda kuɗin wuta yake anguwar masu kuɗi, shi ya sa ma yana faɗin haka, na ce Babu matsala.
Kicin na shiga na zuba mana abinci, na kawo mana falo jallop ɗin taliya da ta ji naman kaji zaƙwa zaƙwa, haka mu ka zauna muka ci, muna ci muna hira ko ba komai na ji matuƙar daɗin zuwanta.
Bansan cewar ina zama kaɗaici ba sai da tazo, bansan cewa zaman da nake ni kaɗai ba, a ƙuntace nake ba sai da ta zo.
Muna tsaka da cin abincin aka yi sallar la'asar, hakam yasa muka gaggauta muka ci mu ka yi sallah, bayan mun idar ne Fauziyya ta ce.
"Gidanki ya yi kyau sosai, arziƙi da wadata faca-faca, sai dai ke din duk kina zaune babu wani kuzari kamar ba matar da take auren wanda take so ba?."
Murmushi na yi mata sanan na ce.
"Wanda nake so sama da komai ma a rayuwata, Fauziyya kinsan yanayin rayuwar auren, dole fa mace ta yi sanyi duk rawar jiki da kanta."
"Hakane kuma wallahi, to yanzu ya maganar wannan?"
Ta faɗa tana nunan cikinta da ya tasa, na yi dariya sannan na ce.
"Yana hanya."
"Kun fa kawo shekara biyu da aure ko?"
Na gyaɗa kai.
"Ikon Allah, kuma bai fara miki magana akai ba?"
"Bai fara ba gsky, ai yansan komai lokaci ne."
"Da gaskiyyarku shi ya sa fa auren mai ilimi wayayye yake da daɗi, yanzu da irin mazajenmu timawan ƙauye ne, ai da yanzu andame ki da magana, ko shi bai yi ba 'yan uwansa sai sunyi."
A raina na ce. "Gaskiyya dai kam." Dan ko da wasa Sardauna bai taɓa yi mini maganar ciko ko haihuwa ba, ko zancen yara ma.
"Kinga har hudu da kwara, bara nazo na huce."
Fauziyya ta faɗa tana miƙewa, nima na miƙi mu ka nufi waje na rakata, ina dawo wa hankali na ya yi kan gugar Sardauna, ba shiri na shiga ɗakin na dumbuzo kayan wajen Set goma na fito falo na jona dutsen gugar bayan na shimfiɗa darduma na zauna na fara gugar.
Kusan awa ɗaya da fara gugar ya shigo cikin gidan, haka kwai na ji gabana yana faɗuwa, duba da ko cikakken set bakwai bam goge masa ba, amma bayana ya ƙage, gashi ban ɗora masa girki ba. Jikina na rawa na kashe dutsen na miƙi na shiga kitchen.
Dame zanji kunna wuta? Ko tunanin abinda zan dafa masa? Ga kayansa da na bari a falo.
Ina jin ya shigo falon na fito da sauri tare da faɗin.
"Barka da dawowa."
Wani mugun kallo na ga ya watsamin, mai ɗauke da harara ya shige ɗakinsa. Dum! Daram! Haka na ji gabana ya buga. A fili na furta.
"Innullahi wainna illahir raji'un."
Na nufi ɗakim da ya shiga, yana zaune gefen gado ya haɗe rai, fuskar kamar bai taɓa murmushi ba.
"Sannu da zuwa dan Allah."
Na faɗa bakina yana karkarwa.
"Mitchew."
Ya ja tsaki yana ƙoƙarin cire takalminsa, da sauri na ƙaraso na tsugunna zan kama takalmin ina faɗin.
"Kawo na cire ma, wallahi kaina yake ciwo na kwanta, sai wajen huɗu na tashi."
Wani kallon ya ƙara watsamin, sannan ya fara cire takalminsa, na kai hannu zan cire masa ya janye ƙafarsa tare da taƙemim ɗan yatsa. Na ƙwalla uwar ƙara tare da riƙe hannun da yake mini wani irin zugi kamar na sakawa ciwo gishiri. Yatsun da basu gama warkewa daga ƙonuwar jiya ba, gashi sun sha taku.
Miƙewa na ga ya yi ya shige ban ɗaki abunsa, ya buga ƙofar hakan ya ƙara tabbatar mini da cewa yana cikim fushi mai tsanani.
"Wayyo Allahna."
Na faɗa idanuna na zubar da hawayen da bana raɗaɗin da hannuna yake ba, na raɗaɗin fushin da mijina yake yi dani.
"Me ya sa na kasance haka? Me ya sa na kasance sakarar da batasan abinda take ba? Me ya sa na kasance butulu mai manta alheri? Mutumin da yake sona, amma na zaɓi kullum na ɓata masa rai? Tir dani! Tirr da halayena."
Abinda nake faɗa a raina kenan, wani ɓari daga zuciyata da yake matuƙar ƙaunar Sardauna ya ce dani.
"Maza ki ƙara ɓata masa rai da baza kije ki yi masa girki ba."
Kamar mahaukaciya sabuwar kamu haka na miƙe na fice zuwa kicin, idanuna na zubar da hawaye na fara ƙoƙarin kunna wuta, hayaƙi ya turniƙe kicin ɗin, amma banaji bana gani.
Legendspen.
*SARTSE*
-Amanar-Janafty-
*Sayyid Legendspen*
MAH/2026/001
Sadaukarwa.
RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA
(Mai Dambu)
Shafi na uku
(03)
A gurguje cikin ƙasa da minti ashirin na haɗa cus-cus da mayar ganye, wacca sai da na kwashe tsawo minti na goma ina tunanin mai zan dafa, haka nake, a ko yaushe burina na ga na dafawa Sardauna abu na daban.
Albarkacin miyar ganyen da nagani a firiza ya gajarta mun tunanin da nake yi. Fuskarsa ka ɗai na kalla na ji gabana ya faɗi har na kusa yin tuntuɓe. Ajiye masa plast ɗin abincin na yi akan dinning sannan na shiga ɗakinsa na buɗe ƙaramin firinji dake ɗakin na ɗakko ruwan sanyi na fito dashi, daman anan kawai ake samun ruwan sanyi sai kuma firiza ya ce ita firiza sabida kar kaji kifi ko abinci ya lalace baya son asara, shi kuma na ɗakinsa ƙarami ne ba zai ja wuta ba.
Ko da na fito falon yana zaune kan dinning din ya fara zuba abincin, na ajiye masa ruwan da faɗin.
"Kawo na zuba..."
Ya kuwa gallamin uwar harara, ba shiri na cika mai cikolin na yi baya, da idonsa ya kalli kayan da nake gogewa sannam ya ɗauke kai.
Ba shiri na matsa daga wajen na dawo kan kayan na hau gogewa jikina yana ɓari haka nake gugar.
Ina nan zaune ya gama cin abincin ya tashi ya shige ɗaki, ba shi ya fito ba sai da aka yi sallar isha, yana tafiya massallaci na kashe dutsen na tashi na ɗaura alwala na yi magariba na yi isha. Sannan na kwashe kayan da na goge na shiga ɗakin na sanya su a sif, na sake ɗebu ragowar na dawo falon.
Sai da na yi nisa a gugar wajen ƙarfe goma na dare sannan ya shigo, bai kalleni bare na sa ran zai mini magana ya huce ɗaki, haka nai ta guga ta har wajen ƙarfe sha biyu da rabi na dare sannan na kamalla. Na ɗauki kayan zan kai su ɗakin sai jin ƙofa na yi a kulle, wani irin abu ya tsaya mini a raina, tabbas nasan na kai mijina bango har ya iya kullen ƙofa, tabbas ban kyauta ba, ban kyautawa kaina ba. Na daɗe a falon sai wajen ɗaya sannan na shiga ɗakina na kwanta, sai dai baccin da na yi ya kasance marar daɗi kwata kwata.
A tsakanin karfe ɗaya zuwa biyar da rabi na dare, na farka ya kai sau shida.
Yau kam tun asuba na shiga kicin, na hau haɗa masa abincim safe, cikin sa'a na kammala komai kafin ƙarfe bakwai. Ina tsaka da jera masa dinning ɗin ya fito cikin shirinsa, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai ya nufi ƙofa zai fita.
"Baka karya ba."
"Bazan karya ba, ai bakya sona Nana, kin gaji da yi mini biyayya, kin daina jin maganata."
Ya faɗa yana tsareni da kaifaffun idanunsa, jikina yana ɓari na fara cewa.
"Wallahi a'a ba haka ba ne."
"To ya ne? Har ƙarya fa kika yi mini jiya, wai bacci kikayi, bayan ƙawayen da na hanaki mu'amala dasu ne suka zo suka zuga ki. Nana dan ina sonki bazan juri abinda kike mini ba, kina ƙaskantar dani, kina nuna banda daraja banda mutunci. Nana a kaf faɗin duniyar nan ko iyayen da suka haifeki basu kaini sonki ba, Nana kinsani, ina sonki, ina kyautata miki, ina baki duk wani haƙƙinki, amma Nana me kike sakamini dashi? Mene abu ɗaya?"
Na yi shiru, gaba ɗaya jikina ya yi wani irin sanyi, wani sabon tausayin mijina ya lulluɓe ni, a hankali na fara magana, idona cike da hawaye.
"Ka yi hakuri dan girman Allah, wallahi bazan sake ba, sai da na ce mata kar ta zo amma taƙi."
Sai yanzu na fara mamakin kaina, yadda aka yi na zama maƙaryaciya lokaci ɗaya, duk dan na faranta masa.
"To bance duka kike goge lambobi su ba?."
"Na goge fa, ai kana ganin wayar babu lambar kowa sai taka da ta 'yan gida, to idan suka kirani ne nake ganesu."
"Bani wayar."
Ya faɗa yana takawo cikin falon, fuskarsa a haɗe kamar zai dake ni, hannuna har karkarwa suke yayin da nake kokarin mika masa wayar, ya sa hannu ya fusgeta da ƙarfinsa. Daidai lokacin saƙo ya shigo wayar ji kake. 'ɗilim.' ƙarar shigowarsa.
"Waya turu miki saƙo?."
Ya tambaye ni, cikin muryar kuka na ce.
"Nima bansani ba."
Wayar ya danna ya bude saƙon, ya ƙura ma wayar ido yana motsa baki, idanunsa na yawo akan sikirin ɗin wayar, wanda yake daidai da ƙaƙƙarfan bugun da zuciyata ke yi.
"Mitcheww."
ya ja tsaki, ya danna maddanin gogewa ya goge saƙon.
"Ina so ki ciro mini layin nan yanzun nan."
Ya faɗa yana miƙomini wayar, da rawar jiki na amsa na fara ƙoƙarin cire layin, yana kallona da idanunsa har na cire na miƙa masa, ya karɓa ya sa a aljihu, kana ya zauna akan kujera, ya runtse idanunsa kusan mintina biyu sannan ya buɗe su, ni dai ina tsugunne ina kallonsa, ƙaunarsa da tausayinsa suna cika mini zuciya, ina son mijina,ina tausayinsa.
"Hon! Matso ki zauna."
Sassanayar muryarsa da tafi ruwan ƙanƙara sanyi ta doki kunnunwana, ba shiri na miƙi na matso kusa da shi na zauna, ya sa hannuwansa ya kama nawa, a hankali ya fara matsa su.
"Nana, kin san me ya sa nake yin haka?"
Ya tambaya, muryarsa tana fitowa da wani irin sanyi mai ratsa zuciya. Ya kura mini ido, idanunsa da suke daidai da kwayar idona suka sanya na ji wani irin mugun tausayinsa.
"Domin ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Ke tawa ce ni kaɗai, Nana. Idan kika bari waɗancan kawayen naki da 'yan uwanki suka ci gaba da shigo miki da ra'ayoyinsu, za su lalata mana wannan kyakkyawar rayuwar da muke yi."
Na gyaɗa kai, hawaye na wanke fuskata na ce.
"Na gane Hon. Nagode da kake kare ni, nagode da kake nuna mini gaskiya."
"Yauwa Nana. Don haka, tunda yanzu babu layin a wayar, babu wani abu da zai dinga raba miki hankali. Ina so ki maida hankalinki gaba daya a kaina da kuma wannan gidan. Kuma ina so yau ki goge sauran kayan da suka rage."
Ya sumbaci tafin hannuna, wanda har yanzu yake zugi saboda kunar jiya da kuma takewar da ya yi mini ɗazo. Amma kalaman sa sun sanya na manta da raɗaɗin.
Na gyada masa kai cikin sauri na ce.
"Yanzu yanzu ma, kana fita zan ƙarasa."
"Tashi ki je ki soma, ni kuma zan karya da kaina."
Na miƙe ina jin kamar an dora mini wani sabon nauyi, amma nauyin da nake ganinsa a matsayin Ladan Bautar Aure, da kuma tukwici ga soyayyar da ake nuna mini. Kai tsaye na shige ɗakinsa na fito da ragowar kayan gaba ɗaya.
Ina tsaka da guguwar bayan fitar sardauna naji ana sallama, gabana har faɗuwa yake yayin da na tashi zuwa buɗe kofar. Ra'is!
"Ra'is lafiya?."
Na faɗa baki na yana rawa, ya kalleni cike da bacin rai, sannan ya ce.
"Alhaji bashi da lafiya, ya ce yana son ganinki, yana son magana dake amma kin ƙi, Yaya ta kira ki a waya kin ƙi ɗauka, anyi miki test message akan baba yana cikin halin jinya, amma kin gani baki ce komai ba, yanzu da safe an kiraki ma wayar akashe, sai kuma yanzu kika yi message a wayar mijinki kika wai ke ma baki da lafiya. Nana me yake damunki ne? Dan kinyi aure a gidan hali shine kika tsani 'yan uwanki?."
Tun da Ra'is yake magana ƙirjina yake bugawa, duk wata kalma da yake faɗa guda daya tamkar ana doramin dutse a kirjina ne, fuskata cike da hawaye na ce.
"Wallahi Ra'is ba haka ba ne, bansan Baba bashi da lafiya ba, kuma Sar...."
"Ta ina zaki san ba shi da lafiya, kin zaɓi miji mai abun duniya akan 'yan uwanki da iyayenki, wallahi Nana kin bawa kowa kunya ciki hardani, wahala da Alhaji da Hajiya suka sha akan aurenki basu sha ta akan kowa ba, Nana kinsan tunda kika ajiye karatun da Alhaji ya ci buri akanki bai ƙara lafiya ba. Wallahi Nana daba dan Baba ya takura ba babu abinda zai kawo ni gidanki babu shi, kuma idan kinga dama ki je ki ganshi idan baki ga dama ba kar ki zo, amma ki kwana da sanin duk wani abu da yasami mahaifinmu ba zamu taɓa yafe miki ba."
Yana faɗin haka ya juya zai tafi, cikin muryar kuka na ce.
"Ra'is! Dan Allah tsaya."
Tsayawa ya yi ba tare da ya juyo ba, na tako inda yake sannan na ce.
"Dan Allah kira mini Alhajin, na yi magana da shi dan Allah."
Kallona ya yi sannan ya ce.
"Ki yi magana dashi? Kina nufin bazaki zo ba?."
"A'a Ra'is zan zo, amma dan Allah na fara jin muryarsa kafin nazo."
Murmushin takaici Ra'is ya yi sannan ya sa hannu a aljihu ya zaro wayarsa, ya danna kiran sannan ya miƙo mini. Hannuna har rawa yake yayin da na amshi wayar, ana ɗagawa na fara magana.
"Ba..Baba!"
Na fada, daga can bangaren Yaya Radiya ta ce.
"Bara a miƙa masa."
"Yaya ki yi hakuri, wallahi bansan komai ba akai, wayar ta hannun Mijina."
"Mijinki kuma? Amma saƙon da kika turu dazu ai kece kika rubuta."
Yaya Radiya ta fada, ban kai ga bata amsa ba ta sake cewa.
"Ga Alhajin."
"Alhaji ina kwana, Ya jikin naka?."
Na faɗa cikin rawar murya.
"Rawasiya kina lafiya?."
Ya tambaya muryarshi cike da alamun rashin lafiya, wani abu ya tsaya min a rai, yana cikin halin rashin lafiya amma tambaya ta yake ina lafiya?
Ina son Sardauna sosai, amma tabbas bai kai ko rabin soyayyar da nake yi wa Alhaji ba.
"Alhaji lafiya kalau, ya jikin naka?"
"Nana yaushe zaki zo?"
"Baba anjima zan zo, yana dawowa zan faɗa masa ko da daddare ne sai nazo, ko gobe da safe."
"Toh shikenan! Ubangiji Ya yi miki albarka."
"Amin Baba, Allah Ya baka lafiya."
"Amin amin Nana."
Ya faɗa yana mikawa Yaya Radiya wayar.
"Nana ki samu ki shigo dan Allah."
Yaya Radiya ta fada, duk jikina ya yi sanyi na ce.
"In sha Allah Yaya." Daga nan na katse kiran na bawa Ra'is wayarsa, ya kaɗa kai zai tafi.
"Ra'is, baka shigo ba! Baka sha ko ruwa ba."
Murmushi ya yi sannan ya ce.
"A'a ba komai, zan wuce kawai sai kinzo."
Yana faɗin haka ya fice, ni kuma na koma ɗaki na zauna kan kujera, kamar wacca aka haskawa majigi haka rayuwata ta baya ta shiga tariyo wa a idanuna.
******
Asalin labarina.
Da farko sunana Rawasiya Alqasim Babuga wacca kowa ya sani da Nana, sunan da na zaɓawa kaina kenan, tun ta sowa ta ni macece marar son hananiya ko kaɗan, bana son abun da zai dame ni a rayuwa ko ya ne, abun da nasa a gabana shi nake yi, shi nake so.
Mahaifina Alhaji Alqasim sannanne a anguwarmu dama gari gaba daya, kasancewarsa dan siyasa mai aƙidar riƙau. Sannan ɗan kwangila ne da yake da kamfaninsa wanda yake karbar ayyukan daga 'yan siyasa da ma sauran mutanen gari.
Mahafiyyata Sailuba haifaffiyar jihar Adamawa yola ce, irin kyawawan fulanin nan ne na Yola, a lokacin da mahaifina yake tashin aikin kwangila da kuma siyasarsa Allah Ya haɗashi da ita, bayan shimfiɗa kyakyawar soyayya kuma suka yi aure, inda mahaifina ya dawo da ita unguwar Federal Low-cost dake dutsen jihar jigawa. Unguwa mai kyau da daɗin zama, unguwar da ta kasance ta masu matsakaicin hali, akwai manyan gidaje da kuma ƙananan, akwai hadaƙar masu kuɗi da talakawa.
Zaman tsarkakkiyar soyayya ya ginu tsakanin Mammanmu da Abbanmu da muke kira da Alhaji da Hajiya, tun haihuwarsu ta farko Alhaji ya zo da wani tsari, babbar Yayarmu sunanta Radiya, bayan yan shekaru aka sake haifi wata aka saka mata Rumaisa, bayan ita kuma sai namiji da aka sa masa Ridwan, a lokacin Alhajinmu yana tsaka da siyasa da samun kudi ya dauƙesu gaba ɗaya suka sauke farali, a lokacin ina ciki sai bayan sun dawo da aka haifeni inda aka samin Rawasiya, ban kai shekara ba dukkanmu Alhaji ya kwashe mu zuwa aikin Hajji, wanda bayan dawowarmu daga aikin Hajji karyar arziki ta sami mahaifina.
A lokacin ina da wata goma sha ɗaya a duniya, wannan lamarin ya afku, inda mahaifina da alhalina suka shiga matsanancin tashin hankali na rayuwa, duk arzikin mahaifina ya kare a yadda nasamu labari wani lokacin gidanmu suna iya kwana ba tare da suncu abinci ba, ana haka mahaifiyata ta shawaraci Alhaji da ya sayar da gidansa na Federal low-cost ya nemi wani karamin mu koma can ragowar kudin ya sa su a kasuwa, haka kuwa aka yi mahaifina ya siyar da gidansa na Federal Low-cost ya nemi matsakaicin gida a unguwar Yelwawa, inda suka dawo nan, gida mai dauke da dakuna uku, Na Alhaji (Baba) daban, na Hajiya (Umma) daban, Yaya Radiya da Yaya Rumaisa daya, shi kuma Yaya Ridwan tun da shine karami yana kwana dakin Hajiya, ni kuma ina karama. Daga Amana Academy makaranta mai zaman kanta aka dawo da yan gidanmu zuwa Government Day School Yelwawa, canji rayuwa ya yi wa gidanmu ƙawanya, ni kam basan duk dadin da aka sha ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 16