Share this page
na yi sallah.” Dawowa ya yi ya zauna daga miƙewar da ya yi sannan ya ce.  “Dagaske?”  “Eyh dagaske.”  “To ai yanzi akwai tazara sosai zuwa ƙarfe ɗaya, ki tashi mu shiga ciki idan kin yi bacci ni sai na tashi ki ƙarfe ɗayan.”  Ta shi na yi nabi bayanshi zuwa ɗakin, ko a ɗakin ma na daɗe a zaune har sai da ya ƙara cewa na kwanta zai tashe ni sannan na kwanta.  Ƙarar alam ce ta tashi ni, wanda na saita ƙarfe biyar daidai na asuba. ‘Sardauna ya manta.’ Na faɗa a raina ina saukowa, a gurguje na shiga banɗaki na ɗaura alwala na fara yin nafila kafin na gabatar da asuba, cikin hanzari na haɗa masa abin kari sabida ina son na fita da wuri, duk hankalina yana wajen Alhaji gaba ɗaya, ji nake a jikina kamar ni ce sillar kwanciyarshi wannan rashin lafiyar.  Haka Sardauna ya yi ta jan lokaci, ba shi ya fito ba sai sha biyu da kwata, kuma a hakan ma bai yi breakfast, har ƙwalla sai da na yi.  “Am sorry Hon, na ɗan duba wani abu ne shi ya sa na makara, yanzu ma ban ƙarasa ba amma ki zubamin breakfast ɗin na yi ke sai kije ki ƙarasa mayar da takardun kafin na kammala.”  Jikina duk babu daɗi, haka na je kan dinning na zuba masa farfesun naman rago da na yi sai kuma doya da miyar kaza da na dafa, sabida ina son tafarwa da Alhaji kuma nasan zaifi son dafaffiyar doya maimakon soyayyiya. Ina zuba masa ma nufi ɗakin, takardune duk ya zubar dasu a ƙasa, haka na shiga haɗasu ina zuba su a jakar da suke, ina yi ina ɗan duba wasu. Kwatsam idona ya faɗa kan wata takardar CV ɗinsa, date of birth na fara cikin karo da shi 11/08/1994.  ‘Ya tabbata dai Sardauna ba shekarunsa 25 ba?.’ Abinda na fara tambayar kaina kenan. ‘Amma me ya sa ya ɓoyemin, tabbas ƙarancin shekarunsa suna daga cikin abubuwan da suka sa na far son Sardauna.’ Na sake faɗa a raina, ƙwalla na ji ta fara zurara daga idona. ‘Ashe Sardauna zai iya yi min ƙarya? Kai ba zai yi min ba sai dai idan a lokacin ni ce na ji ba daidai ba, kunnuwana sun yaudareni.’  Haka na kwashe takardun ina ta saƙe saƙe a raina, ba mune mu ka bar gidan ba sai ƙarfe ɗaya da kwata, ni da na shirya tun tara. Kallon plast ɗin hannuna Sardauna ya yi sannan ya ce.  “Na mene wannan?”  “Ragowar doyar da na dafa ce, ban iya ci ba duk bakina ba daɗi, shi nake son tafiya ko Alhaji zai iya ci.”  “Shine kika bani kaɗan ni ko?”  “A’a ba haka ba ne?.”  “Ke kika sani.”  Ya faɗa yana shigewa motar, nima na shiga har mukaje gida baice dani ko ƙala ba, haka bai ce dani na gaida me jiki ba, amma na yi masa uziri ko ya yi mantuwa ko idan yazo ɗaukana zai shigo. Da sallama na shiga cikin gidan, mutanen gidanmu suna falon Hajiya duk sun yi zugum zugum, hankali a tashe na shiga ɗakin. Yanayin da naga Alhaji ya yi matuƙar tsorata ni,  yana kwance kamar marar numfashi, baya ko motsi.  Jikin Hajiya na faɗa ina faɗin.  “Yana ganshi a haka Hajiya?” Hajiya kuka take dannewa, ba ta iya ba ni amsa ba sai Yaya Radiya ce ta ce da ni.  “Haka kawai muka ga jikin nasa ya yi?”  Kusa da shi na matsa ina faɗin.  “Alhaji.. alhaji.” Yana kallona da ido amma bazai iya magana ba, Ra’is ya ce da ni.  “Ba zai iya magana ba fa.”  “Ina Yaya Ridwan baku tafi asibiti ba?.”  “Nana ki nutsu dan Allah.” Yaya Rumaisa ta faɗa, kowa fuska cike da hawaye.  Tashi na yi na janyo plast ɗin da na zo da shi.  “Alhaji dan Allah ka ci doyar nan.”  “Zo ki ba shi.” Ra’is ya faɗa, na matso kusa da shi na buɗe plast ɗin na ɗauki doyar na mammatse ta nasa masa a baki, a hankali ya cinye ta na ƙara samasa wata, sannan na ɗauki farfesun zan ba shi Yaya Rumaisa ta ce.  “Kar ki ba shi akwai maggi, ki ba shi iya doyar.”  Daidai lokacin Yaya Ridwan ya shigo ɗakin.  “Ga motar an samo.”  A raina na ce. ‘Yanzu mota ce ta hana akai mahaifina asibiti a lokacin da yakamata? Mene amfanin motocin da suke gidana? Ina ranar motar da Sarduna ya bani wacca ba na ko amfani da ita.” “Rid..wan.”  Alhaji ya faɗa a hankali, da sauri duka muka kalleshi, ya yi masa alamu yazo da hannu, sannan ya yi yawa Yaya Radiya da Yaya Rumaisa, ni da Ra’is daman muna kusa da shi, ɗai ɗai yake kallonmu sai da ya gama kallonmu duka sannan ya ce.  “Kaine Babba, kaine babansu Ridwan… ba ni na baka wannan nauyin ba Allah ne ya baka, ina mai rashim jindaɗin cewar zan tafi na barka da nauyi a kanka, Ridwan ka yafe min.”   Gaba ɗaya jikin mu ya yi sanyi kowa ƙwalla yake matsewa.  “Ku yi haƙuri kar ku yi kuka, ku haɗe kan ku ka zama tsintsiya ɗaya, ga mahaifiyarku nan, a tsahon rayuwata da ita babu komai sai alheri da kyautatawa, ku ci gaba da yi mata biyayya har ƙarshen numfashinku.”  Sannan ya nuna ni, ni da Ra’is.  “Sune ƙanana, ku yi musu afuwa, ku dinga haƙuri da su, mussaman Nana.”  Ya nuna ni, sannan ya ce.  “Tana sonku, ku yi mata afuwa kar ku taɓa fushi da ita, karku watsar da al’amuranta ƙaramar ku ce, ba ta da wani gata sai na Allah sai na ku.”  “Alhaji ka taso a kai ka asibitin dan Allah.” Hajiya ta faɗa tana kuka, ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. “Na gode, na gode miki. Allah Na gode maka da rayuwa da ka bani, Allah ga Amanar ‘ya’yana da matata, Allah ga Amanarsu nan, Allah ka kula su, ka zame musu gata a duk inda suke ka kare su Ya Allah.”  Gaba ɗaya ɗakin ya yi shiru baka jin komai sai shasheƙar kuka, ya sa hannu ya nuna Yaya Radiya ta matso kusa da shi.  “Ki yi haƙuri, ki miƙa al’amuranki ga Allah Yana gani, kuma zai kawo miki mafita, ke ce babba Allah ne gatanku, ki haɗe kanku dan Allah, karki bari wani abu ya tarwatsa ku.”  “Alhaji ka yi ƙoƙari akanmu tun haihuwar mu har zuwa yau, ka cika mahaifini na gari, ka tsaya akanmu ka kula da mu, mun gode maka alhaji mun gode maka, ko a yanzu rayuwa ta tsaya Alhaji ka cika gwarzon uba, Alhaji mun gode maka.”  Yaya Radiya ta faɗa tana fitar da wani irin kuka mai taɓa zuciya, ya yi murmushi sannan ya nuna Yaya Rumaisa, itama ta matso kusa.  “Ki dinga dannar zuciyarki, ki dinga haƙuri da ‘yan uwanki dan Allah, ki yi wa mijinki biyayya, Allah Ya yi miki albarka ya haɗa kawunanku, ku ya fe min dan Allah.”  Cikin kuka itama ta fara magana.  “Alhaji muna sonka, mun kuma gode maka da dukkan abinda ka yi mana, Alherin Allah Ya tabbata a gareka Alhaji, Mun gode mun gode.”  Ya matse hannun Yaya Ridwan dake cikin nasa, sannan ya ce.  “Haƙuri! Haƙuri! Haƙuri dan Allah, Ridwan ban so na barka maka nauyin akanka ba, amma nasani Allah Ya na gani, kuma zai shiga al’amuranka zai buɗa maka yabaka ikon kula da ‘yan uwanka, a ko da yaushe albarka ta tana tare da ku.”  Yaya Ridwan kuka kawai yake bai iya cewa komai ba, Alhaji ya kalleni ya ce.  “Nana! Ki kasance mai karɓar ƙaddara kowace iri, Nana rayuwarki tana cike da ƙalubale da yawa, Nana karki yi wa Allah butulci, karki koka, ki yi haƙuri ki sa a ranki komai zai wuce Nana, komai da komai zai zama labari.”  Rungume shi na yi na ci gaba da rera kukan da nake yi.  “Ka kasance mai biyayya, mai kyautatawa ‘yan uwa, kasa a ranka Allah ne gatanKa sune gatanka, Ra’is ka yi haƙuri a duk irin rayuwar da ka tsinci kanka, Allah yana gani ka ji.”  Shima Ra’is ɗin kuka ya fashe da shi,  kowa kuka.  “Na gode miki, Na gode miki Allah Ya yi miki albarka, ya baki haƙurin rashi.”  Hajiya dai ba ta iya cewa komai ba sai faman ƙwalla da take.  “Allah ko a yanzu Alhamdulillah, Allah na gode maka, na ƙara gode maka, zan kasance mai gode maka Ya Allah, Tammat bi hamdillah Allah.”  Daidai lokacin Isah Nadabi ya shigo ɗakin, ganin dukkanmu muna kuka ya sa shi cewa.  “Me ya faru dan Allah, Ridwan ya baku tafi asibitin ba?”  Cikin Kuka Yaya Ridwan ya ce.  “Ya ce kar aje asibitin.”  Matsowa ya yi ya kama hannun Alhaji sannan ya ce.  “Alhaji akai ka asibiti dan Allah.”  “A’ah Isah, tsaya ka ji.” Alhaji ya faɗa murya a wahalce, ya riƙe hannunsa sannan ya ce.  “Allah Yasa ka maka da mafificin alheri, ubangiji ya raya maka zuri’arka, Allah Ya dauwamarma da suttura, ɗawainiyar da ka yi akaina ubangiji ya mayar maKa, na gode.”  “Alhaji ka bari dan Allah, Ridwan kama shi dan Allah.”  “A’ah! A’ah! Dan Allah ku barni.” “Me ya sa, Alhaji?”  “Ka barni, na ƙarasa rayuwata a cikin iyalina.”  Bai kai ga yi masa magana ba tari ta sarƙeshi, yanayi yana haɗawa da kalmar shahada. Gaba ɗaya muka zagaye shi muna kuka, a hankali har muka ji ya daina kakarin.  Gaba ɗaya duniyar ta tsaya mana cak, Isah Nadabo ne ya fara ɗaga hannuna yana faɗin.  “Alhaji Alhaji, innullahi wa’inna illahir raji’un.”  Ina daga zaune na ji wani irin jiri ya ɗebeni, aikuwa na kifi ƙasa kif.  Legendspen 08129553971. https://chat.whatsapp.com/DPr8Zlw33HeAkt3hhxIPYv?mode=gi_t *Munyi nisa a Arewapen, ta wannan link ɗin ko username Legendspen* https://www.arewapen.com/book?id=69d7e87dfc259651b7635bff *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu) Shafi na sha shida. (16) Sama sama nake jin hayaniyar mutane, a hankali na fara buɗe idona, dishi dishi nake gani kafin idon ya buɗe tarwar. A take komai da ya faru ya shiga dawomin kamar an haskan majigi. "Alhaji!" Na faɗa ina koƙarin ta shi, hannuna na ji an riƙe tare da faɗin. "Nana! Nustu ki nutsu." Muryar Sardauna ce, na ɗaga ido na kalleshi tare da faɗin. "Alhaji!" Ya riƙe ni tare da girgizamin kai, sannan ya ce. "Alhaji is no more Nana, Alhaji ya tafi ki yi haƙuri." Wani irin kuka na saki me raɗaɗi da taɓa zuciya tare da faɗin. "Innullahi wainna illahir raji'un, na rasa Alhaji na rasa gata na rasa komai, dan Allah ka mayar dani gida ka mayar da ni." "A'a Nana ba zaki koma yanzu ba, sai kin warke." Miƙewa na fara ƙoƙarin yi tare da faɗin. "Na warke Sardauna ka barni na tafi, na je na ga mahaifina, dan Allah." Kallon agogon hannunsa ya yi sannan ya ce. "Ƙarfe uku da rabi za ayi jana izarsa, kuma a yanzu uku da arba'in Nana, an kaishi gidansa na gaskiyya, ki yi haƙuri ki ɗauki rashi, ki karɓi ƙaddara Nana, ni zan zame miki gatan da kika rasa Nana, dan Allah." Kuka na ci gaba da yi, ni kaɗai nasan irin  yanayin da nake ji, ina jin kamar na fitar da zuciyata daga cikin jikina, ina jin zafi kamar an watsamin gishiri a jikin ciwo, raɗaɗi kawai nake ji da wani irin zafi yana ratsani, na gaji na rasa me zanyi, ba kuka ba, ba ihu ba, na gaji da rayuwar ma, na gaji. "Nana ki yi haƙuri dan Allah, ki yi haƙuri kinji." Ya faɗa yana jawoni jikinsa, na kwanta ina kuka mai tsuma zuciya, shi kuma yana shafa bayana. A hankali na fara sauke ajiyar zuciya. "Nana! Kina jina, Allah Yana jarabtar bayinsa ta kowanne fanni, Allah Ya jarabce ki da rasa mahaifi a yanzu, amma kuma ya yi miki sakayya da ni Nana, Nana ina son ki ɗauke ni a matsayin duk wani abu da kika rasa Nana, zan zame ki bango, zan zame miki inuwa Nana." Haka Sardauna ya yi ta lallaɓani da zafafan kalamai masu saukar da nutsuwa, amma gaba ɗaya a hankalina baya tare da ni, burina na ga 'yan uwana, ko zan tabbatar cewa Alhaji bai mutu ba, dan tabbas na hana zuciyata yarda da ko kalma ɗaya kan faɗin rasuwar Alhaji. Ba mu muka bar aaibiti ba sai bayan biyar, hannu maƙale da kanula sabida ba a gamin allura ba, har da ƙarin ruwa. Jama'ar da na gani a kwanar layinmu suka dawo min da kuka na sabo, so ake a tabbatar min na rasa mahaifina, na rasa Alhaji ina zan sa rayuwata. Yanayin fakin ɗin motar shi na fito, ban ko tsaya ba duk kiran sunana da yake yi. Da gudu na shiga cikin gida idon kowa ya yo kaina. "Wayyo! Wayyo!." Na ji muryar Hajja, wani takaici ya cikani na fara tafiya zuwa ɗakin Hajiya sai dai kawai na ji wani jirin na ɗibana, kan ka ce me na sake zuɓewa a ƙasa sumammiya. Sanyi da na ji a fuskata ne ya sa na buɗe idona, Maman walid wata maƙwafciyar mu na gani a kaina tana shafan ruwan, can na jiyo muryar Sardauna yana faɗin. "Ba yadda likitan baiyi ba, amma ta dage sai na kawo ta." "Da ba kawo ta ba, yanzu gashi ta sake zubewa." Banma tantance me muryar ba na ce da Maman Walid. "ina Hajiya? "Tana ciki Nana." "Kamani dan Allah." Na faɗa ina ƙoƙarin tashi, ta kamani ta shiga dani ciki, anan na tarar da har da mutane da yawa a  cikin ɗakin, har da Mamansu Amina Aminu da Fauziya. "Nan da zafi, a fita da ita wancan ɗakin ta sha iska mana." Wata maƙwafciyarmu ta faɗa, Maman Walid ta sake riƙeni zuwa ɗakin da yake seat room, ɗakin yana da faɗi kuma ba komai a ciki carpet shi ya sa yake da iska.  A cikin ɗakin na ga mutane da yawa har da ƙwayena da su Yaya Radiya kowa ya yi zungwi zungwi, haka nima na zauna a raina ina ta nanata kalmar. 'Alhaji is no more.' Da Sardauna ya faɗa min, haka na zauna har dare ban nemi Sardauna ba, sai wajen tara sannan ya sa aka kirani, ko da na je ban wani saki baki na yi mai magana ba, shima kuma bai daɗe ba ya ce da ni zai tafi sai gobe zai zo. Haka na koma ciki, jigun jigun ba magana ba ci ba sha, sai washe gari ne ma nasami damar shan shayi da safe, Sardauna da sassafe ya zo har da wasu daga 'yan uwansa wayanda daman jiya sun zo su Big Daddy ma duk ance da su aka yi sallar Alhaji shine dai babu shi, sabida zuwansa kenan ya gani a kwance ya ɗaukeni zuwa asibiti, da yamma su Hajiyarsa da su lubna suka zo har da su Sister Seemah. Ranar kwana uku ya ƙara tabbatar mana da cewa Alhaji ya tafi babu dawowa, haka muka yi haƙuri muka amshi rashin Alhaji. Washe gari ranar kwana na huɗu kowa ya watse gida daga mu sai mu sai 'yan uwan Hajiya da suka zo, sai Anty Adiza matar Isa Nadabo da bata koma ba tun da ta zo, a ranar muka ƙara tabbatar da rashi musamman da muka kasance muka ɗai, ranar kwana na shida Turaki ya zo ya yi min gaisuwa, baya ƙasar sai jiya da daddare ya dawo, ya yi min gaisuwa sosai da sosai, da zai tafi ya ce na haɗashi  da 'yan uwana maza, sanin halin Yaya Ridwan yasa ban ma haɗasu ba sai Ra'is na nema, bayan sun gaisa ya yi masa gaisuwa ya karɓi lambar Ra'is sannan ya bawa Ra'is ta shi, ya kuma sanar da shi akan cewa bayan anyi kwana bakwa ya tuntuɓeshi. Ranar bakwai aka sake zaman addu'a, da dare kowa ya watse aka sake barin mu daga mu sai mu sai Anty Adiza da take kamar 'yar gida, 'yan uwan Hajiya ma sun tafi, su Hajja kam tun ranar da aka yi rasuwa suka tafi gida akan cewa suma zasuyi nasu zaman makokin acan, bayan sun jidi kayan abinci a shago tun da ga nan Isa Nadabo ya karɓe mukkullin shagon. Ranar bakwai Sardauna ya tambayeni yaushe zan dawo na ce da shi sai na tambayi Hajiya, bai tankan ba ya tafi na koma cikin gidan, a zuwa yanzu mun karɓi rashin Alhaji, mun ci gaba da wasu abubuwan har magana da cin abinci, mu kan ɗan zauna mu tattauna wasu abubuwan. "Yaya, ɗazu mutumin nan ya kirani da kansa." Ra'is ya faɗa, na kalleshi na ce. "Wane mutumi?" "Wanda kika haɗani da shi ranar nan." "Aouho, me ya ce da kai?" "Waye ne?" Hajiya ta tambaya. "Wani ɗan uwan Sardauna ne." "Me ya ce ma?" Yaya Radiya ta tambayeshi, sai sa ya gyara zama sannan ya ce. “Da farko ya ce dani a wane aji nake, na ce da shi yanzu na shiga level 1 a FUD Sai ya tambayeni sauran fa, na ce masa Yaya Radiya tana shekara ra biyu a Health, sai Yaya Rumaisa da za ta gama, har ya tambayeni wace babba na ce Yaya Radiya, na ce ai ita ba ta fara karatun ba sai bayan aurenta ya mutu, sannan na ce da shi Yaya Ridwan ya shiga 400 level a FUD sai ya tambayeni Reg ɗina nawa nw na faɗa masa da na Yaya Radiya da na Yaya Ridwan to yanzu duk ya yi budget kuɗin har kowa ya kammala wai zai kama miliyan ɗaya da duby ɗari biyu, sai ya ce ba tura mai acc zamana anan na tura mai na Yaya Radiya, yanzu ya tura min recipt ya sa miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar, sannan ya ce duk wani abu na karatu ko nawa ko na Yaya Radiya ko Yaya Ridwan a sanar da shi in sha Allah.” Ba ƙaramin mamakin jin abinda Turaki ya yi na yi ba, cike da mamaki na ce. “Shi Turakin?” “Shi dai wanda kika haɗani da shi.” “Mene alaƙarsu da mijinki?” Hajiya ta tambaya. “Kamar ɗan wa da ƙani suke, amma dai gaskiyya Hajiya a iya sani na basa mutunci da Sardauna, hasali ma abokan faɗan ne basa ga maciji kuma nasan Sardauna bai san maganar ba.” “Kuma kika faɗa masa wallahi Nana sai ranki ya ɓaci.” Yaya Radiya ta faɗa, sannan ta ce. “Wannan mijin naki bai da hali, shi kaɗaine bai sallaci Alhaji ba.” “To ba suna asibiti ba ke kuma.” Hajiya ta faɗa. “Haba Hajiya, ƙarfe biyar fa aka yi sallar Alhaji kuma ya sani, ina ganin ko da yana kaita zai iya dawowa.” “Ƙarfe biyar kuma?” Na faɗa a fili, a raina kuma ina tuna lokacin da Sardauna ya ce da ni ƙarfe huɗu da rabi za ayi, kuma yanzu huɗu da arba’in. “Eyh mn biyar aka yi wa Alhaji Sallah, kowa ya sani wani abun ne?” Yaya Radiya ta tambayeni, na girgiza kai sannan na ce. “A’a ba komai, kawai gani nake babu rabom ganawarmu, amma da na fito lokacin da na farka ai da zan same shi.” “Zaki samu mana, ina Dutse clinic ina gidan nan ko minti biyar ba zaku yi ba.” A raina na ce me ya sa Sardauna yake son fara yi min ƙarya? Mutuwar mahaifina ce ta goge damuwar ƙaryar shekarun da ya yi mini, ga shi kuma yanzu ya sake min wata, ya san mene ganawa da mahaifi kuwa, anya ya sani? “Yanzu ya za ayi da wannan kuɗin?” Muryar Yaya Radiya ta katseni, sai na ji Hajiya na cewa. “Idan makarantar zasu yarda kowa aje a biya nasa gaba ɗaya kar ya kammala, idan kuma basu amince ba za a iya kaisu banki a ajiye idan lokacin biyan ya yi sai a dinga ɗauka ana yi.” Daga haka aka yanke shawara, ni dai an barni da tunani kala biyu a raina, yaushe Sardauna ya fara yi min ƙarya ko me ya sa ya fara? Washe gari na shirya komawa gida ni da Yaya Rumaisa, bayan Hajiya da Yaya Radiya sun yi mana faɗa sosai, kuma an gargaɗe ni akan kar na sake na sanar da Sardauna abinda Turaki ya yi tin da na ce ba sa shiri, da suna shiri ne ma za a sa shi ya yi masa godiya. Ko da na kira Sardauna na ce da shi yazo ya ɗaukeni sai ya ce da ni yana aiki na tawo kawai, haka na sami mashin na hau har gida. Gidan gaba ɗaya ya yi ƙura ya yi datti, ba wani zauna na ba na hau gyaran gida, ina cikin yi Sardauna ya dawo. Bai nuna wani farin ciki da dawowa ta ba ko kuma irin alamun ya yi kewata ba, sai ma sanar da ni da ya yi a cikin satin nan zamu koma sabon gidanmu dake Takur Site C wanda yanzu muke a A, ganin haka ya sa na dakatar da wasu ayyukan sabida wasu abubuwan duk kwashe su zamuyi, Sardauna bai duba halin rashi da nake ciki ba, haka ya yi ta fama, sannan kuma ya ƙara matsamin akan shan magunguna wai akwai abu da yake shirin faruwa. Ranar juma’a da yamma muka ta shi daga gidanmu na Takur Site A muka koma Takur site C, babban gidane mai ɓangare biyu, kowanne ɓangare ɗaya yafi gidanmu na site A, namu ne a hannun hagu na Turaki a hannun dama, muna shiga na ce da Sardauna. “Wai to shi Turaki shi da wa zai zauna? “Yaran mutane zai ci gaba kawowa yana abinda ya saba da su.” Ada ina yarda haka Turaki yake, amma yanzu kam bana yarda kwata kwata. Gidan ya yi kyau ya tsaru sosai da sosai, komai sabo ne a cikin gidan, kowanne ɓangare sai ya ɗauki mata uku a wadace. Abubuwan da muka tawo dasu basu da yawa, daga abin gawayi sai kayana da wasu kayan kicin ɗin. Ranar da muka koma da wani irin ciwon ciki na kwana, gaba ɗaya cikina ya wani irin murɗawa ta wajen marata, na sha matuƙar azaba har sai da jini ya fita daga jikina, Sardauna ya kaini asibiti wajen Dr Ɗan Adala, tambayar farko da ya yi min sau nawa nake amafani da magunguna, na ce da shi har sau biyar a wata na yi. A take ya ce na dakatar da shan maganin ba lallai ya yi wa mahaifata aiki ba, za a duban wani maganin nan gaba ko daga Turai ne sai akawo min, daga nan muka dawo gida. “Nana, ki daina damuwa da rashin haihuwar nan, gaba ɗaya ba mu shekara biyu da aure ba, wasu su kan shekara goma da aure ba haihuwa, dan haka ki daina damun kanki kin ji dan Allah, ke na ki so Nana, ba wai Baby daga jikinki ba, dudu nawa kike, Nana ko kinsan bana so tsufa. Nana girma bazai taɓa yi miki kyau ba.” Ga masu tambaya, Littafin Sartse Book one ne kaɗai Free wanda kuma mun kusa kammalashi, Book Two & Three. Kuma na kuɗi ne, domin sabuwar tafiya ce; sabuwar rayuwa ce da za ta girgiza ku. Komai zai sauya,Book one gaba ɗaya shimfiɗa ce, dan bamu fara tafiyar ba, Book 2 da 3 shine ainahin labarin. Kuna iya fara biyan kudin littafinku tun daga yau, kafin mu kammala Book One. • Account Details: • Account No: 8165383931 • Bank: Opay • Name: Sani Muhammad Lawan • Farashi: • Naira Dari Bakwai (700) kacal. Akwai giveaway na lokaci-zuwa-lokaci wanda muke yin ragin zuwa N500 ga mutane 20 na farko da suka fara biyan kuɗinsu. Garaɓasa ce ta iya mutane 20 ɗin farko, kar ku bari ku rasa. Masu VIP kuma babu tsarin VIP sai dai arewapen, da ake saka page 5 zuwa 6 kullum. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha bakwai.     (17) Na ɗaga kai na kalleshi, ban gane inda kalamsa suka nufa ba kwata kwata. 'Tsufa bazai min kyau ba? To ai dole na nutsu fa ko? In da rai ko ba lafiya ai sai na tsufa, kuma ni Allah Ya gani ina son ganin 'ya'yana, amma ya zanyi da shi tun da ba ya so? Me zan so bayan abinda yake so?.'  "Shikenan, Allah Ya nuna mana lokacin."  "Amin Nanaty, me kike shiryamana na a sabon gidan nan?"  Na yi dariya sannan na ce.  "Me zan shirya mana kuwa?" "Sabuwar rayuwa mana Nana, sabuwar soyayya, sabuwar kulawa, ina ganin kamar kina rage tausayina, ada Nana kina tausayina sosai kin damu da ni da damuwata, amma yanzu sai nake ganin kamar ba haka ba ne Nana, ada abinci har abaki kike ban, amma yanzu kin barni na ci da kaina, me ya sa Nana?"  "Bakomai wallahi, kawai kutuwar Alhaji ce har yanzu ba ta gama sakina ba, ina jin rashin sa a cikin zuciyata sosai."  "Nana, Allan da yafi bamu Alhaji yafi mu son shi kuma ya amshi abunsa, ba yadda zamu iya, Nana wasu

Chapter 9 of 16