tanayi mata alamar waye kafada madiha ta daga alamar ohhhu tashi yayi akan sofar kana ya juyo yana kallonsu tofa kallan kallo ake tsakanin Abdallah da Jannat da madiha..............
NA'EEMERH SULAIMAN🤕
[3/15, 2:24 PM] Naeema: *🤦♀KADDARAR MACE🤦♀*
~by~
~nimcy luv~
4⃣0⃣
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
@wattapad
Nimcyl
08119237616
*do the best and be the best✌*
✨✨✨✨✨✨✨
Cigaba yayi da kallonsu, yayinda zuciyyarsa taci gaba da bugawa, yasan cewa madiha na Singapore, amma baiyi tunanin zasuyi kusa da juna ita da bebynsa ba, nutsuwarsa ya saita kana yayi murmushi yace dasu.
" 'yan kauye kawai kunzu kun zubamun ido daka zuwana an rasa Wanda zaiyimin oyoyo a cikinku kamar baku sanni ba ya fada yana dallah masu harara"
Madiha ce tayi murmushi dan tunaninta wajan yazo, tunda baisan Jannat ba, da sauri ta karasu wajansa shima bai nuna wata alama ba,amma yasu Jannat ce ya farajin dumin jikinta, tana karasuwa ta fada jikinsa tasaki kuka hannunsa yasa yana bubbuga bayanta amma bai rungumeta ba, itama Jannat kukan ta farayi kasa-kasa dan hakan ya tuna mata da farin cikinta kuma jigwan rayuwarta ganin Abdallah na shirin kamata tana kuka yasa ta joya baya ta gyara fuskarta ta kakaro murmushi ta kalleso inda haryau madiha tana makale jikinsa taki sakinsa gyara murya tayi sannan tace "barka da zuwa bakwanmu, ya hanya ta tambayeshi inda take kallon wani wajan daban"
Basarwa yayi dan kar madiha ta gane komai ya kalli Jannat yace "lpa Allahamdulliah enmata"
Bata kara magana ta huce bedroom dinta ta barso anan dan tagaji sosai ga kuma yadda zuciyyarta keyi mata kunci da ciwo ga bata da magani tana shiga ta samu ruwa faro mai sanyi ta bude tasha kusan fin rabi sannan ta ajiyye, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet tayi wanka a gurgoje, sannan ta nemi riga mara nauyi ta saka iya gwiwwa ta gyara gashin kanta ta daure da ribbon ta feshe jikinta da turare da yake ta riga tayi sallarta yasa ta haye saman bed dinta taja baleket ta rufe jikinta sai bacci dan tana bukatar nutsuwa a zuciyyarta.
Janyeta yayi daka jikinsa ya samu waje saman sofa ya zauna yana lumshe idanu shikadai yasan abinda da yakeji gameda Jannat yasani a wannan lokacin tana bukatar tai makwansa dan yaga sanda take kuka ga kuma madiha wacce bama dan ita yazo Singapore ba ya salam what should i do now, let me make her busy kallon madiha yayi yace .
"Zonan sister"
Babu musu tazo ta zauna kusa dashi ta zuba masa idanu sannan tace.
"Gani nurul hayat"
Yauwa sister pls inajin yunwane inason kiyimin fatan duya da hadin fruits idan babu damuwa"
"La ai yazamemin dole koda duniyyar kace na daukoma zan iya daukoma bare kuma abinci ta mike tayi mai light kiss sannan tayi kichin dan sama mai abinda ya bukata murmushi kawai yayi ya kwanta saman sofa kafin ta fara aikin 5minutes yasan tashi ga busy sosai dan haka ya tashi a hankali yayi bedroom din Jannat yana zuwa ya murda kofar yajita alamar a rufe ansa mata key juyowa yayi dan karya buga madiha taji kwaciyayi sosai a kan carpet yana kallon sama yayi da yakeji babu dadi cikin zuciyyar sa Abdallah kenan.
A dayan bangaran waya take tayi amma anki picking gaba daya ta fita haiyyacinta dan masifar ta taso mata kara kira tayi harta kusa tsinkewa sai taji andaga ko gaisawa basuyi ba ta fara mgn.
" haba muhuseen tun dazo ina kira but you didn't pick my call why? "
Dry yayi kadan kamar bayaso sannan yace.
"Dunda kikajini shuru aikinsan ba lafia ba, wlh 2days banajin dadi zazzabi na damuna, amma ki bari zuwa jibi zamu hado".
Dan karamin tsaki taja dan ta fara gazawa tace.
" Malam banason dugwan bayani, kawai kana ina yanzo zanzo".
Uhm aa kiyi hkr zuwa jibin, ina mijinki? meye amfaninsa kije gunsa mana"
Niba dugwan zance nace kayimin ba kaga sai anjima da kashe wayar gaba daya tana juyi saman bed dinta tashi tayi ta nufi 6angaran anwar tana shiga ta ganshi ya fito cikin shiga ta alfarma tsayawa tayi tana kallonsa dan bakaramin kwarjini yayi mata ba bakin buyal ne ajikinsa yasaka hula fara mai zanan baki sai a gogu da takalmi duk farare zai zuba kamshi yake sumar kannan tasha gyara sai kyalli take kallonta tayi kamar zai mgna sai kuma ya basar dan anwar badai shariya ba matsuwa tayi ta fada jikinsa tana kuka bai cemata komai ba kawaidai ya zuba mata idanu saida tagaji sannan tace"
"Pls hubby ka taimakeni ina cikin wani hali, dan Allah karkasa rayuwata tayimin ba daidai ba, karka manta ni matarka ce ta sunna"
Janyeta yayi ajikinsa ya kalleta sosai still baice komai ba kuma bashi da alamun mgana, hannu yasa ya goge mata hawayen, sannan ya daga 'yan ya tsunsa guda biyar alamun ta jirashi zuwa 5minutes murmushi tayi sannan ta kara rungomeshi uhm hajiya maimuna kenan.
Ta gama jera komai akan carpet dan Abdallah bayacin abinci a darning saida anisha wanka tayi ta sauya kayan jikinta ta dawo parlour Jannat inda taga Abdallah shima ya sauya kaya jikinsa alamun yayi wanka kenan da murmushi a fuskarta ta karasu wajansa tace.
"Barka da zaman jira nurul hayat, bisimillah ga abinci?"
Uhm daman haka ake kin bar 'yar mutane tun dazo a daki a kulle har kina shirin cin abinci babu ita sauri tayi ta tashi tana cewa"
"Kai beby bakya rabu da damuwa wallahi, mutum yaje daki ya zauna shi daya na hanaki bakiji ba, gaban Abdallah ne ya fadi jin abinda madiha ta fada wato kullum cikin damuwa take gsky rayuwar Jannat abar dubawace gashi haryau family su babu Wanda yasan tana da ciwon zuciya gashi yana tsoran gaya masu ya salam ya fada yana runtsa idonsa motsi yaji a bayansa yana dubawa ya gansu sun fito tare haryau shirgar dazone ajikinta kanta ko dan kwali babu zame hannunta tayi taje da hado milk mai sanyi ta shanye tas duk gaban Abdallah kana ta dawo saman sofa ta kwanta tana maida numfashi dan wani irin ciwo takeji a zuciyarta nantake girjinta ya fara dagawa ahankali hannu tasa ta danne saitin zuciyarta madiha ce ta kalleta tace.
" beby taso muci abinci, tun dazo ke muke jira nida nurul hayat pls"
Still idonta a rufe yake,tayi murmushin karfin hali tace.
"No! Madiha kuci kawai banci ngd"
Girgiza kansa yayi kana ya dau spoon din zaikai bakinsa kenan sai yaga Jannat ta fara mikewa jikinta gaba daya ya dauki rawa nan take ta fara tari sosai saiga jini ya fara zuba ta cikin bakinta har lokacin tana rike da saitin zuciyarta da gudu Abdallah yayi kanta gaba daya yama manta da wata madiha a rikice yake cewa.
"Pls ruhina Karkiyimin haka Idan kika muto nima mutuwa xanyi kece rayuwata kece komai nawa ya fada yayin daya kankameta ajikinsa gaba daya duk karfin rokwan da yayi mata mai hana jikinta karkarwa ba tana wata irin fisga da gyar ta bude baki tace.
" Abdallah rayuwa bata da amfani a wajena tabbas mutuwa itace hutu a gareni farin ciki jin dadi abokin rayuwa duk sunyimi nisa Wanda nake tunanin zai bani farin cikin a yanzo wani dalili yasa bazan sameshi ba kaga dole na bukaci mutuwa wata irin shakuwa tayi hade da kankame Abdallah sai kuma bugun numfashinta ya tsaya ya salam Jannat kenan.
Da sassarfa ya shigo part din su abban Jannat a parlour ya samesu da Abba sai mama sai kanwarsa meera da yayan Jannat faisal mijin meera ne tun kafin ya karasu suka zubamai idanu yayin da shikuma ya tsaya cak yana kallon wani wajan kallon wajan sukayi Ashe picture din Jannat yake kallo Wanda yake manne a parlour tana dry dukkan dimples dinta sun luma wani jiri ya faraji yana dibansa ji sukayi ya ambaci sunan jannat da karfi sai kuma ya sulale a wajan a sume babu numfashi.........
💃💃💃💃💃ahhyeee wata tafi wata a hankali wata tafi wata a comments wata tafi wata💃💃💃💃
NA,EEMERH SULAIMAN🤕*🤦♀KADDARAR MACE🤦♀*
~by~
~nimcy luv~
4⃣1⃣
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
@wattpad
Nimcyl
08119237616
*Absence is the best presence, because,if people are absent then u miss them,and if u miss them that means they are present in ur heart💔*
✨✨✨✨✨✨
Abbah, Umma, Faisal, Meera gaba daya sukayu kan anwar dan ganin lafiyar sa , suna isa sukaga babu inda ke motsi a jikinsa wani ruwa na fita ta bakinsa, A gigice Faisal da Abba suka dauki anwar sukayi waje dashi su Meera na biye dasu, A mota suka sakashi dan zuwa asibiti a duba lafiyar sa, 30minutes dai-dai suka isa Aminu Kano teaching hospital,suna zuwa Dr kamis ya amshi shi yana tambayar meya sami Dr anwar haka, Abba basarwa yayi dan besan anwar a matsayin dr ba, kawai sai yayimai bayanin abinda ya faru, emajency aka shiga dashi, su Abba suna wajan sunyi jumgun-jumgun kowa yana tunanin abinda yasami anwar addu'a kowannen sukeyi akan Allah ya bashi lpa, sun dau awa guda cib kamin Dr kamis ya fito hakan yayi dai-dai da zuwan Daddy da mummy iyayen anwar kenan, tasuwa sukayi gaba ɗaya suna tambayar abinda yasami Anwar, Dr kamis ya kallesu kana ya numfasa yace.
"Munyi nasarar dai-dai ta numfashin shi, ba wani abune yasame shiba face razana da yayi da kuma firgici akan wani abu da ya daɗe bai gane niba, daka nan zuwa ko yaushe zai iya farkawa kana yayi masu sallama ya fice"
Gaba ɗayansu dakin da yake suka shiga,a kwance suka sameshi numfashinsa na sauka ahankali, hankalinsa kwance yake baccin ya kara haske da kyau da kwarjini gashin ƙanan nasa a kwance sai sheƙi yakeyi da kuma sajansa daya sha gyara gaba ɗaya ya sauya kamar Balarabe uhm Anwar Muhammad sai muce Allah ya baka lafiya.
Gajiya tayi da jiransa ranta yayi mugun ɓaci ta ƙuduri niyya ko yadawo bazata kulashi ba ta hakura wayar tace ta fara ringin dauka tayi ta kara a kunne ganin amrah ce mai kiran tace,
"Hello amrah, ykk"
Daka ɗaya ɓarin amra tace "sannu maimu yamai jiki naji ance muhuseen babu lafiya ko ta faɗa tana dariya"
Uhmm! An not sure but since munyi yawa dashi yace bayajin daɗi"
Ohhh! To Allah ya sauwake"
Ameen, something new?
Komai shurune and you?
"Wlh amra ina cikin matsi da takura pls ko akwai wani guy a ƙasa ne jinake kamar nayi hauka"
Hahaha kaji ƴar iska idan kinyi akwai dawanau a gari ai, nikam bana ma gari saidai hkr"
Haushine ya ishi maimu babu shiri ta katse wayar tana cije lips dinta na azaba uhm maimuna ambassador kenan.
*Singapore* A gigice Abdallah ya dauki Jannat yasata akan bed dinta, gaba ɗaya ya rikice ya fita hayyacin sa, ruwa mai sanyi ya dauko ya hauro kan gadun ya daguta yasata a jikinsa ruwa sanyi ya shiga shafa mata a fuskarta da wuyanta, ajiyyar zuciyya ta sauke numfashinta ya fara sauka a hankali ruwan ya kafa mata a baki nan kuwa tasha kusan rabin ruwan ajiyyar zuciyya taketa saukewa babu adadi, ƙanƙame Abdallah tayi sannan ta fashe da kuka maicin rai kana ta fara magana a hankali tace.
"Tabbas Abdallah koda inasonka dole ba hakura da kai sabida madiha, nida madiha Akwai kyakkyawar fahimta bazanso abinda ƴar uwata takeso ba, hannun madiha ta ɗauko ta haɗa dana Abdallah kana ta ɗura hannunta saman na madiha tace.
"Abdallah kayi hakuri ga madiha ƴar uwata ita tafi dacewa dakai bani ba, still tana jikinsa a kwance pls Dr karkace aa, nasani nice rayuwarka kai kuma kaine Rayuwar madiha ni kuma mutuwa itace abinda nake jira a yanzu, ko wacce mace akwai kaddararta, ni soyyayar ɗan uwana itace tawa kaddarar da kuma ita zan kuma lahira, nayarda da ita taci amanar yardar danayi mata, taci amanata ta ruguzamin farin cikina, ta tarwatsamin jin daɗi na da kuma mafarkina ta faɗa tana danne kirjinta"
Rungume ta ya ƙarayi yana bubbuga bayanta yana jin so da kuma kaunarta yana kara yawa a zuciyyarsa, why do this to beby, meyasa zaki zaɓi rabani da farin cikina tabbas rabuwa dake kamar rabuwa da numfashi nane uhm adaiyi hakuri Abdallah ibraham Makka kenan.
Part ɗinta ta koma ta murza key, kuka take sosai na fitar hayyaci idonta yayi ja sosai sabida kuka "meyasa zakaimin haka Abdallah tabbas kaine rayuwata kaine farin cikina kaine jin daɗina kaine walwalata kaine komai nawa Rayuwa babu kai cikin duniyyata tabkar rayuwa ce babu ruwan sha, beby kiyi hakuri da zan iya barmaki Abdallah wlh dana barmaki, nima shine farin cikina zan tayaki da addu'a Allah ya kawo maki mafita, banason ganin Abdallah da kuwacce irin mace faceni Abdallah nawane ni ɗaya babu wata ta faɗa tana hargitsa kayan ɗakinta, tab Allah mai iko su madiha kenan.
*Nigeria Kano* da misalin karfe 9:00 suna zaune bakin gadon anwar dukkansu sunyi shuru suna jiran sammani, mutsi ya farayi idonsa na fitar da hawaye na baƙin ciki da taiki da kuma ladama, ido ya buɗe a hankali yana kallon iyayansa da kuma ƴan uwansa saida ya gama duba ko ina sannan ya kalli ƙofa kana ya juyo da idonsa kanna Daddy Yace.
"Daddy an gama ɗaurin auranne?.........
*NA'IMA SULAIMAN🤕*
More comments pls and shere[3/18, 1:56 PM] Naeema: *🤦♀KADDARAR MACE🤦♀*
*NA'EEMERH SULAIMAN*
NIMCY LUV
4⃣2⃣
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*@wattpad*
Nimcyl
~ameena firstlady wannan page din nakine✋✊ mungode da amsa gayyatar mu zuwa program dinmu na musamman~
✨✨✨✨✨✨✨
Wani farin cikine ya saukarwa Daddy da Abba dama dukkan wanda yake wajan, fuska daddy ya haɗe yayi kamar baiji abinda anwar yace ba, ganin daddy bazai magana ba yasa anwar kallan abban jannat yace.
"Abba ina beby? An gama ɗaurin auranne? Meya kawoni asibiti kuma? Haka yayita jero tambaya, yana jiran Abba ya bashi amsa.
Murmushi Abba yayi kana ya jinjina kai yace.
"Son wanne aure kake magana ne, koka manta yanzo wajan 2years da auran ka"
Zabura anwar yayi daka kangadon da yake yana kokarin cire karin ruwan da aka samai bakinsa yana rawa yace.
"Abba ban gane makakeson cewa ba, nawa auran ko nasu yaya Faisal kake magana"
Numfasawa Abba yayi kana ya girgiza kai daman yasan dole akwai wannan ranar gashi yazo koya za'a ƙare dashi ohhho, kallonsa yayi kana yace "a'a kai idan akace shekararsu Faisal 2 da aure ka yarda, ina mgnar auran kane da matarka maimuna ina fatan yanzo ka gane"
Ai bai jira Abba ya karasa maganar da yakeson yiba ya ƙunduma wata ashar yana hantsiluwa akan gadon ya zare allurar hannunsa jikinsa na rawa ga rashin karfin jiki idonsa yayi ja hawayene ya fara zubuwa bakinsa na shaking yace wa .
"No! Abba how can i marriaed her, pls abba think about this, i don't like her at all, she can't be my wife ever Abba ya fada yana jijjiga kafaɗar Abba"
Wani wawan mari daddyn Anwar ya sakarwa anwar a fuska har sau biyu, kana ya nuna shi da ɗan yatsa yace.
"Kai banason shirman banza dana hofi, lokacin daka wulaƙanta beby agaban ƴan daurin auran kace baka sonta ka tsaneta kai maimu kakeso, ubanwa yayi maka magana uban ya takura maka, ina gargaɗinka da babu ruwan ka da jannat karka ƙara shiga rayuwarta bare ka ƙara War gatsa mata farin cikinta, kaje can ka ƙarata da mara ƙunyar matarka amma beby tafi karfinka kaji ko yana kaiwa nan ya fice ya bar ɗakin"
Jirine yake ɗibansa waishin yaya zaiyi da rayuwarsa, taya zai iya samu farin cikinsa a wannan lokacin, mafarkinsa ya wargatse, tunaninsa ya gushe shin ina zaisamu mafita, ji yake duniyya tayi mai zafi kallon key din hannun Abba yayi babu wanda ya kula ya fisgi key ɗin ya fice a guje.
*Singapore* da gyar ya samu ya shawo kan Jannat ta daina kuka, yayi mata dukkan tai makon da zai mata tarin da takeyi ya tsaya, yayi nasarar shawo kanta harya bata abinci taci ya bata magani tasha, yana shafa kanta yana bubbuga bayanta har bacci ya ɗauketa, tunanin mafita ya farayi amma ya gaza yin komai dukkan abinda ya saƙa sai yaji baya yimai dai-dai daka karshe ya yanke shawarar zai jira su gama exam idan yaso Saidu tafi Nigeria gaba ɗayansu dukkan abinda za'ai saidai ayi No matter how he can't life without her, madiha kowa dunda ta shiga ɗaki bata fito ba, tayi kaca-kaca da ɗakin nata tazama kamar mahaukaciyya, tayaya Abdallah saiso kawarta wacce take matukar jin kunyarta, kin yaudareni jannat kinso abinda nafi kauna aduniyya mai yasa baki gayamin dunda kuna tare ba, meyasa kinsan ina sonsa zakici amanata meyasa aminiyyata, what am did to you, tunda muka haɗo komai nawa ke nake tambaya hatta shawara idan inaso kenake tambaya why beby meyasa hakan ta faɗa tana cilli da Laptop ɗin gabatan ta.
*Bayan sati ɗaya a Singapore* sun gama exam lafiya sai jiran saka makon, shirye shiryen kumawa gida suke, idan kaga beby da madiha bazakace wani abu ya faru ba son koma dai-dai saidai ta ciki na ciki Abdallah yana basu kulawa sosai haka zai ce su shiga kichen gaba ɗaya amma madiha hakuri kawai take dan gaba ɗaya hankalin Abdallah na kan beby, abu kaɗan zai mata ta hau kuka harda dukansa, daman beby badai kukan kissa ba.
Tayiwa madiha da Abdallah sallama sbd dare yayi bacci takeji, ta gama shirinta na kwanciyya bacci, azkar take karantawa a wayarta ta gama kenan zata kwanta bacci message yana shigowa wayarta..........
*Gsky idan banga comments yadda nakeso va😡😎yasin yajin aiki zani ahhha✋🙅*
Comments and shere
[3/18, 1:56 PM] Naeema: *🤦♀ƘADDARAR MACE🤦♀*
*NA'EEMERH SULAIMAN*
*(NIMCY LUV)*
4⃣3⃣
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
@Wattpad
Nimcyl
NIMCY LUV FANS
*👉 LITTAFAI*
*ƘADDARAR MACE*
*ASHE ƳAR BABATA CE*
~i know am not best🤷♀but i luv who luv me, I Care about who about me am nimcy luv don't ever forget this~
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ saurin tashi zaune tayi ganin number da akayi message ɗin da ita maimai ta sunan tayi HONEY SWEET wani farin ciki kine ya cika mata zuciyya abinda ya fara zuwa kanta yayanta kuma jigon rayuwarta ya dawo hayyacinsa cikin zumuɗi tana addu'a Allah yasa tunaninta gsky message ta buɗe dan karantawa abinda ta gani yayi matuƙar furgi data bakinta na rawa ta fara karantawa.
_bani da lokacin yimaki sallama jannat ,sannan ina mai farin cikin gaya maki cewa kada kisake kidawo gida, dan zakiyi ladamar hakan,sannan ni anwar koda duniyya zata ƙare ni dake bazan taɓa auranki ba, na tsaneki tsana mai yawan gaske kada kitaɓa tunanin zanyi tunaninki koda na lokaci ɗaya ne, daka karshe nake cewa kiji daɗin zamanki a Singapore, ANWAR MUHAMMAD RANO_
Rontsa idonta jannat tayi tanajin wani ɗaci a zuciyyarka, ta kaici da bakin ciki ya hanata kuka jikinta sai tsoma yakeyi idonta yayi jajawur kamar gauta, ta karanta message ɗin yakai sau 5 taki kasgata yayanta kuma jigon rayuwarta, farin cikinta kuma wanda take fatan yazama wani ɓangare na rayuwarta, wani yawo ta haɗiye mai ɗaci kana ta kashe wayar gaba ɗaya kuma ta dauki niyyar baza koma gida ba, koda anyi masu hotu,tashi tayi alwa ta fara sallar lafila har wajan 3 bata runtsa ba daka karshe bacci barawo ya ɗauke ta akan lardumar da take Sallah sai muce asuba ta gari.
*Nigeria* anwar ba tsaya ko inaba sai gidansa taret bedroom ɗin maimu ya nufa, kofar ta daka da karfi yana huce ya shiga bedroom din, a kwance ya sameta saman bed tana bacci tsaki ya buga kana ya finci kota da karfin gske bata fito ko inaba sai gabansa, gabanta na faɗowa ta kalleshi tace.
"Habibie lpa, meya sameka da faɗa tana faɗawa jikinsa"
Wani gigitatten mari ya sakar mata tana shirin komawa jikinsa ya kara kifa mata wani marin kana ya hanka ɗata ta faɗi ƙasa, kara tashi tayi zatayo kansa dan ita burinta bai huce taji ɗomin jikin saba duk dokan da yayi mata bai dameta ba cikin karaji ya daka mata tsayawa har wayar hannunsa na faɗowa kallanta yayi yace.
"Kada kiyi tunanin anwar wawane baisai mekike aikatawa ba, kin rabani da farin cikina, cigon rayuwata, nasan halin da kika jefamu kadai ya isheki balle na zinar da kike aikatawa, ni yanzo baki isa nayi maki wani abuba kuma karkiyi tunanin dan nasan komai zan sakeki wlh kinyi karya dole zaki ɗanɗana kallar azaba ta dan baki da muhimmancin da zan yafe maki, kuma ki sani kinan harsai nadawo da Jannat rayuwata, yana faɗin hakan ya fice yana huce ko wayarsa beby ta kaiba"
Murmushi takaici tayi da kuma shirin aikata wani abu, baki taɗan ciza kana tace.
"Good anwar i like ur actin aibaka komai ba game ɗin yanzo aka fara tana faɗin hakan hade da ɗaukan wayarsa danne² naga ta farayi a wayar tasa na rasa abinda take rubutawa daka haka na cife na bar mata ɗakin.
Yana fita bai zarce ko'ina ba sai part ɗin abban jannat akan sofa ya sameshi yana duba jarida, ƙarasawa yayi yana zuwa ya faɗa jikin Abba yana kuka kamar ransa zai fita cikin kuka yake maganar yana faɗin.
"Pls Abba ka yafemin nasan na cutar da rayuwar beby bada sanina ba, hakika hakkinta bazai barni ba, dan Allah Abba ka taimakeni ka gayan inda bebyn take wlh zan iya mutuwa idan bangan taba, wlh beby ce rayuwata beby ce ni, beby ce farin cikina, beby ce jin daɗi na, amma nayi alƙawarin bazan ƙara abinda zai nisan tani da beby ba koda na 1minute da ya faɗa yana shassheƙar kuka"
Kallonsa Abba yayi kana ya numfasa yace.
"Shikenan son zan duba maganarka nasan abinda zan iya, maza jeka kwanta kafin gobe"
Shagwabe fuska anwar yayi yama manta Abba sirikin sane yace.
"Wallahi Abba babu inda zan iya zuwa harsai kun fitomin da matata ya faɗa ƙara rungome Abba"
Murmushi Abba yayi yana kokarin mgna sai yaji numfashin anwar yana sauka a hankali alamun yayi bacci.
*Singapore* a hankali Abdallah ke turo kofar dakin jannat yana gama shigowa ya isketa kwance a ƙasa ta riƙe saitin zuciyyarta wata kwallar tausayice ta zobumai kana ya karasu wajan ta yana zuwa ya ɗauketa cak ya maida ta kan bed yana shirin fita yaji ta riƙo hanunsa murmushi yayi ya shafi gefen fuskarta yace.
"You Are my everything, wlh ƙalbi i can't life without you ya faɗa rongumeta a jikinsa yana sauke numfashi a hankali ita ta shige cikinsa tana ƙara rikeshi still tana bacci turo kofar akai kafin yayi wani yunƙuri madiha ta shigo ɗakin.........
*COMMENTS AND SHERE*
AM SORRY FOR MY TYPING ERROR
NO EDITING
[3/18, 1:56 PM] Naeema: *🤦♀ƘADDARAR MACE🤦♀*
*NA'EEMERH SULAIMAN*
*(NIMCY LUV)*
4⃣4⃣
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
@wattpad
Nimcyl
NIMCY LUV FANS
*👉LITTAFAI*
*ƘADDARAR MACE*
*ASHE ƳAR BABATA CE*
_DEDICATED TO WATTPAD FANS👯👯👯👯_
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨da sallama abakinta ta shigo ɗakin, fuskarta ɗauke da murmushi, duk da wani irin zafi da zuciyyarta ke mata ta kawar dashi kefe tace.
"Good morning nurul hayat"
Murmushi Abdallah yayi yana shirin kwantar jannat akan bed yace.
"Mrng my madiha, ya kika tashi?"
Lpa lou Dr na, ya beby kuma da jiki,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 14