Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kawan Amarya ma duk suka gama shiryawa cikin wannan a tamfa ta anko. 2:30PM dubban jama'a suka shida daurin auran Amina da Ahmad....✍🏻 Littafin ABBANA na kudi ne, free pages ya kusa karewa idan kin shirya 400 ne daga zarar na gama zai koma 500 my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 27-28 Amina na zaune kawayanta sun sata tsakiya sai guda suke mata tare da shaigantaka irin ta kwayan Amarya, Allah ya kaimu shekara mai zuwa kamar haka mu sha suna. Amina dai ta yi banza dasu bata tanka ba, sai Aisha ce ke tare Mata. Mansura Mika ma Amina wayarta ta yi da aka Kira ta ce "Gashi, Yaya Ahmad ke Kira." Khadija rangada guda ta yi jin Wanda akace yana Kiran wayan, Amina Koda ta daga hayaniyarsu hanawa ta yi ta ji, hakan ya sa ya Ahmad tura Mata text kamar haka "Assalamu akaimu, zuwa ga zabin zuciyata a maryata, Ina fatan tana cikin farin ciki irin Wanda nima nake ci, na gode ma Allah da ya kaini wannan lokaci ya nuna min auran gimbiyata Amina, Ina rokan Allah ya bani tsawan randa zan rayu tare da ita, ya Kuma bani zuciyar kautata Mata Koda ace ta yi min badai ba, in sha Allah babu ranar da zanga abinda gimbiyata Amina ta yi min a matsayin laifi. Na kirane in jin muryar Mata, in kuma sanar da ita ta sanar da kawayanta 5:00PM zamu zo mu daukeku keda kawayanki zuwa wajan party da Abba ya hada Mana." Amina dora wayar ta yi a kirjinta bayan ta gama karanta sakon Ahmad tana rintse ido, da alama sakon Ahmad sun yi tasiri sosai a cikin zuciyarta. Khadija dafa Amina ta yi ta ce "Amarya an shiga sauki ne." Tana dariya ta idasa maganar. Amina bude ido ta yi tana hararar Khadija ta ce "Yar sa ido, yaya Ahmad ya ce ku shirya 5 za a zo daukarmu za a yi party wai." Khadija kallan Amina ta yi ta ce "Wato ma wai baki san da maganar bane?." Kai Amina ta jinjina ta ce "Allah ban Sani ba sai yanzu da yake fada min da alama shima bai Sani ba." Amarya da kawayanta haka suka ci gaba da hidimarsu, inda sukaita daukar hotuna, da videos tare da Amarya. Mansura ko kamar yadda ta yi ma Abba alƙawarin haka ta kasance ta aje duk wata damuwatata gefe hidimarta kawai take sha, daga ka ganta ka ga kirjin biki. Bangaran su Hassana ko tun suna habaicinsu har sun gaji sun yi shiru, dan sunga alamar Mansura batatasu take ba. Ana cikin hakane aka sanar dasu ga abokan ango nan zuwa, masu gyara daurin dankwaki na yi masu fesa turare da masu kara powder a fuska duka. Ahmad tare da abokansa a harabar gidan Aunty Zainab suka tsaya, sukasa aka Kira masu Amarya da kawayan Amarya a yi hoto. Wasu daga cikin kawayan amaryar ne suka fara fitowa da Amarya. Abba babban abokin ango ansha babbar riga wadda ta Kara fito da baiwar kyawunsa da Allah ya yi masa, sun yi shiga iri daya da ango ko mai nasu hatta agogonsu iri daya. A hankali-ahankali kawayan amaryar duk suka fito, Abba da wayau ya gama kallace kawayan amaryar kaf bai ga Mansura ba. Yana cikin naimanta da idanusansa Aisha ta zo da iyayinta ta ce "Assalamu alaikum, abokin ango mai kama da ango." Abba juyowa ya yi yana kallan Aisha, kafin ta kakaro, murmushi Abba ya yi mata ya ce "Mommyna, ya kuke ya hidima." Aisha cikin jin dadin yadda Abba ya amsheta ta ce "Alhamdullah, Yaya Abba ya taku." Alhamdullah." Abba da wayau ya Kara dubawa ganin bai ga Mansura ba ya ce "Kice mu kama karamin hole naga kamar baku da yawa." Aisha murmushi ta yi ta ce "Kuma ka ganmu Ina jin mutum uku ne basu anan suke je su dawo." Abba cikin son sanin su waye saboda yana saran ko akwai Mansura a ciki ya ce "Dawa-dawa ye basa nan?." Aisha da dadin soyayyar Abba ya kasa ankarar da ita Abba Mansura yake nema ta ce "Da Khadija da Rukayya da Jamila." Kai Abba ya jinjina. Zai yi magana Ahmad ango ya yafatoshi da hannu alamun ya zo su yi hoto." Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Kin ga Ango na kirana ina zuwa." Aisha bin Abba ta yi ta ce "Yaya Abba muje a yi hoton dani." Abba zuwa ya yi kafin a dauki hoton ya matsa kusa da Amina saitin kunnanta yadda babu wanda zai ji ya ce "Amina, Wai Ina yarinyar nan ne?." Amina sai yanzu ta farga ba Mansura, waige-waige ta fara yi, ganin ba ta ganta ba ta ce ma Abba "Yaya Abba, tana cikin gidan ka Kira wayata tana hannunta." Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Minti daya ina zuwa zan yi waya." Abba Matsawa ya yi ya Kira Mansura a waya. Mansura dake kwance tana danna wayar Amina tashi ta yi ganin Yaya Abba is calling. Amina picking call din ta yi tana sa wayar a kunnanta. "Kina nan kina aikin kukan naki ko?." Abba ya ce ma Mansura. Mansura turo baki ta yi kamar Abba Yana kallanta ta ce "Kai Yaya Abba, Allah duk yau ban yi kuka ba." Okay ki fito waje yanzu Ina jiranki." Mansura jimbur ta tashi ta fita, ita kanta Mansurar tana fita ta fara naiman Abba da idanunta. Can ta hangesa shi gefan ango da Amaya ga Aisha kusa da Abba ta nanike Mai ana hoto, ita ala dole bata son wata macan ta tsaya kusa da Abba. Mansura karasawa ta yi tana murmushi ta gaida Ahmad, Ahmad da fara'arsa ya amsa ya ce "Babbar kawar Amarya ya hidima." Mansura murmushi ta yi ta ce "Alhamdullah." Ahmad nuna ma Mansura ya yi kusa da Amina ya ce "Zo mu yi hoto." Mansura tsayawa ta yi kusa da Amina akadaukesu hoto su duka, da ita da Mansura da ango da Kuma abokin ango da Aisha. Abba ya yi mamaki yadda Mansura ta dauke kanta daga shi da ta fito. Da yake Amina ta rada ma Ahmad cewar ga wadda Abba zai aura wato Aisha ta nuna mai ita, dayake Ahmad ya san komai game da Aisha ita dince kawai baisani ba. Ahmad kallan Aisha ya yi Yana murmushi ya ce "Aisha zo mu yi hoto." Haka suka yi hoton su hudu da Aisha da ango da Amina da Kuma Abba." Bayan sun gama Ahmad ya ce ma Mansura itama ta zo su yi. Babbar kawar Amarya da baban abokin ango da ango da Kuma Amarya su hudu kenan." Mansura tsayawa ta yi gefan Abba, kamar yadda Amina take can gefan Ahmad. Abba take ma Mansura kafa ya yi da dan karfi, Mansura Kai ta dago ta kalli Abba tana turo baki. Daidai nan maihoton ya dauka. Abba Kuma kanne ma Mansura ido ya yi. Mansura ganin Abba da gangan ya takata hakan ya sa ta fara buga kafa tana Kara turo baki Wanda daga mai daukar hoton da Amina da angon da Aisha duk suna kule dasu ba kamar Aisha ba. Abba cikin kunnan Mansura ya rada Mata ya ce "Maganin wanda bai iya gaisuwa ba kenan." Ahmad tabo Abba ya yi, Abba waigowa ya yi yana kallan Ahmad, Ahmad Kuma a hankali Aminace kadai ta ji abinda ya ce ya ce "Amaryarka na kallanka dan haka ka kula malam." Abba harar Ahmad ya yi baitanka masa ba. Haka aka ci gaba da hotunan Wanda Abba shi dai gaba daya hankalinsa na kan Mansura, ya kasa iya rike kansa akan Mansurar, ta yi mai kyau sosai gashi ta saki ranta. Abba ya yi masu hotuna masu yawa shi da Mansura. Mutane da dama sun dauka budurwarsa ce, wa inda suka ji labarin saranarsa Kuma sun dauka ita zai aura. Aisha daga ka kalleta Kamar ta fasa kuka Amma ta daure tana yake ne kawai. Amina lura da hakan da ta yi ta sanar da Ahmad ta ce "Yaya Ahmad dan Allah ka yi ma Yaya Abba magana mana Allah haka cin fuska ne fa, ya za ai ya yi ta hotuna da Mansura a gaban Aisha haka ai ba zata ji dadi ba." Abba zuwa ya yi ya jawo Abba gefa ya ce "Abba meye haka ne za fa ka hada yaran nan fada ne abin da kake yi, Taya za ka zo kana hotuna da wata macan a gaban matar da zaka aura, gaskiya haka bai kamata ba cin fuska ne Wallahi." Abba bata fuska ya yi ya ce "Duk Mai gulma ya je ya yi ni kallan da nake ma Amina shi nake ma Mansura. Hoto Kuma kafin in yi da Mansura ai da ita na fara yi." Ahmad duk yadda ya so Abba ya fahince shi yaki hakan ya sa dole ya rabu da shi. Bayan an gama hotuna Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ku shirya nan da 1hour zamu zo mu dauke ku." Kai Mansura ta jinjina ma Abba, Abba har ya juya zai tafi ya kalli Mansura ya ce "Ki rike wayar Amina a hannunki zan kiraki." Mansura Kai ta daga ma Abba ya ja motarsa suka tafi. Hassana ce ta sanar da sauran kawayansu akan kowa ya sa lass din ankosa 5 za a zo daukarsu zuwa party. Bangaran Aisha waje ta samu ta zauna ta yi tagumi. Khadija da dawowarsu kenan kallan Aisha ta yi dake zaune ita kadai ta yi tagumi. Khadija karasawa inda Aisha take ta yi ta cire mata hannun da ta yi tagumi dashi ta ce "Aisha, lafiya kika zo nan kika yi tagumi kekadai?." Aisha dago manyan idanunta ta yi tana kallan Khadija kafin ta ce "Baba komai." Shi kenan." Khadija tace suka tafi. Khadija bayan ta shiga falon Aunty Zainab, Hassana ta naima dan ta fita kusa da Aisha tana tunanin in itace kila za ta iya fada mata damuwarta. Kasancewar wajan da mutane ya sa Khadija hannun Hassana ta kamo har zuwa inda Aisha take. Zama suka yi gefan Aisha, kafin Khadija ta ce "Hassana kawarki na gani cikin damuwa na tambayeta ta ce min ba komai shine na kiraki kila ke ta fada miki." Hassana dafa Aisha ta yi ta ce "Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, Aisha akan Ina komai ya faru gaskiya harda laifinki, lokacin da kika je kina ma Yaya Abba magana baikwalasheki ba, hasali ma har hoto naga kunyi tare amma yarinyar nan na zuwa Ina lura da ke kika janye jikinki kika koma gefa, ma'ana kin bar mata shi kenan. Aisha idan har kina son Yaya Abba da gaske kamata ya yi ki tsaya ki yi yaki ki kauci soyayyarki." Hassana ta dade tana ba Aisha shawarwari kafin suka tashi suka shiga ciki domin canza kayansu zuwa lass Wanda za suje wajan partyn dashi. 5:00PM motocinsu Abba suka cika kofar gidan Aunty Zainab zuwa daukar kawayan Amarya zuwa wajan party. Kawayan Amarya kowace ta cakare fatar kowacce ace babu kamarta. Ga lass din peach color da dige-digen fari-fari, sai kalar ta haska kowa, hakan ya sa duk sai suka yi kyau. Mansura da Aisha suka rike Amina har zuwa wajan motar da Ahmad yake ciki. Wanda babban abokin anko wato Abba shi zai ja motar. Abba kallan Aisha da Mansura ya yi ya ce "Babbar kawar Amarya ta shiga gaba mu tafi." Abba Kiran wani abokinsa ya yi ya ce "Habibu, ga Mommyna nafi yadda da tukinka ka taho min da ita." Haka din da Abba ya yi sai ya rage ma Aisha zafin da take ji, inda ko mahaifiyar Amarya tana jin tana Kiran Mansura da babbar kawar Amarya har dilka ma tare aka yi masu. A cikin motar Amarya ko Abba ya kure volume din motar da wakar Hanta da jini. Tafiya suke Abba na karkada kafa da Kai. Mansura dai mamaki ya isheta ganin yadda Abba kebin wakar. Green g hotel anan Abba ya kama wajan gudar da partyn bikin kanwarsa da babban abokinsa. Mutane duk sun gama halartar a hall din, har iyayan Amarya duk an kawosu ya zamana Amarya da anko kawai ake jira. Bayan Amarya da anko sun iso MC ya fara announcing na isowar Amarya da anko. Kawayan Amarya da abokan ango suka je suka taro a Amarya da anko inda aka sasu tsakiya. Wasu daga cikin abokan manni kawai suke ma Amarya da angon a haka har suka karasa wajan zaman da aka tanada domin amarya da ango. MC ya dade yana bayanansa kafin aka tada daya daga cikin akoban anko ya bude wajan da addu'a. Bayan haka MC ya Kira Mansura babbar kawar Amarya yana son ganinta. Mansura kin tashi ta yi sai da wasu daga cikin kawayan Amarya suka kama hannunta suka rakata har wajan MC din kafin suka juyo. MC ya dade yana wasa Mansura, kafin ya Kira babban abokin Ango Abba. MC inda Mansura take tsaye ya nuna ma Abba ya tsaya kusa da Mansura, kafin ya ce "Jama'a dan Allah ku kallesu, ya kuka gansu dan Allah, a tafa ma babbar kawar amarya da babban abokin angonnan ." Rap-rap, haka hall din ya dauka. MC kallan DJ ya yi ya ce "DJ sa masu wakar da tadace tasu su bude Mana filinnan." Eye-eye eh-eh, a'a. Nasan so dashakuwa, jininmu ne yake ta haduwa, matso ki zo nasamu natsuwa, dannn kinhanaminni damuwa.oo'ooo oo'oo, laaaaaa oo-oo ." Take hall din ya dau ihu ganin yadda Abba ya fara bin wakar. "Wadda na damka amanata akanta na jaddada kalmanata, na fada zan nanata azuci nasata na riritata .... kamar wasa" wata kallar rawa Abba ya fara irinta Mayan guy , breaking dance, daidai lokacin da aka fara " kullum inata fada miki sai ke." Abba ya fada yana nuna Mansura, ya ci gaba da cewa yana nunata "Kaunarkice ke yimin tsinke, tattarani ta sani a shinke, sai da ta sani a tsinke, Bata barni da yunwa ba, ba ta ki bani ruwan sha ba, baza nace Mata uffan ba domin agaran haka ribace." Wani taku Abba ya yi yana dansewa har ya karaso wajan Mansura yana cewa "Mitazamanamu ba wa'adi, komai mukayo so ne sanadi, sa'in da ba kiciran wa'adi, rabo dake sai dai in na ji naga kaza ta yi kaho, mai kishina Ina sonki me zan baki na aureki, sonki yana ta ginan layi, mizamanmu atare acan ciki, acikin ciki can ciki." Hall din gaba daya ya dau ihu anata taba masu Abba dan sosai abin ya kayatar ya tada ma wasu tsimin soyayyarsu. Mansura dai tsaye take tana kallan Abba tana murmushi, wani wajan Kuma ta rufe ido. Abokan Abba ko ku zo kuga yadda suke yi ma Abba liki. Mansura ma wasu daga cikin iyayan Amarya sunyi Mata liki Amma kawaye ko daya babu wadda ta yi Mata liki. Mc yabama abokan ango ya yi sosai ya ce "Ya haka ne? abokanka Abba sun yi Kara munsan kana da Abokai Amma kawar Amarya har yanzu bamu shaida tana da kawaye ba, dan duk su mamane suka yi Mata liki, Dj sa masu wata wakar da alama waccan Bata burge kawayan Amarya ba ne." Dj waka nake so wadda ba zamu bar nan wajan ba sai abokin angonnan ya yi wuf da zuciyar kyakkyawar kawar amaryar nan." Hall din gaba daya ihu ya dauka jin wakar da dj ya sa. Abba take ya fara bin wakar tare da rawa irin wadda ta dace da wakar. " Dubaaa akanki ana kallona majanuni." Abba ya nuna Mansura ya ci gaba da bin wakar" Babban burina ki kasance daf dani, in zaaki irga masoya naki kisanyo dani, duba akanki ana kallona majanuni, ni Kuma nacee indai kainaki ne ban fadi ba, Sako ya bayyanane tun daga zuciya, sannan kaunarki tana kaman zuciya, kin kaaamani kurwata tun jiya, har yaake matsayin bana samun lafiya." Abba gab Mansura ya matsa ya kureta da ido kamar irin wajan bakowa sai su kadai haka yake ji ya manta da kowa, kallan Mansura yake Yana cewa "Kin shiga Raina kin zauna dan kinsamu guri inata kiranki na amsa kuma nazo da wuri, ki ce farko Kuma ki ce karshe bishiyar nan maigirma wadda kikai minni dashe, bana ji bana gani bana son mai kushe burina in rayu dake har numfashin ƙarshe." Abba nuna ma Mansura ya yi Yana cewa " kinkirkita dukka tunanina." Abba Hannu ya hada alamun roka lokacin da aka zo baitin "Taimakaki bani gurin kwana, sanki ya hanamini barcina, Ina ganki har a mafarkina, sonkiii yanaiii min dadi ban son mu rabu, kijaddada jaarumta taki karmu rabu, bani da kowa sai ke inatafe ba wani..." Abba dakatawa ya yi da bin wakar ganin Mansura ta yi kasa da kanta tana kuka, gaba daya sai ya ji rauni shima, hakan ya sa ya kama hannun Mansura yana rungumota suka bar cikin hall din da sauri...✍🏻 Littafin Abbana na kudi ne, wa inda suka biya kafin ingama free pages 400, daga na gama 500 zai koma, my number 08063830828. Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 29-30 Abba dakatawa ya yi da abin da wakar ganin Mansura ta yi kasa da kanta tana kuka, gabadaya sai Abba ya ji rauni shima, hakan ya sa yakama hannun Mansura yana rungumarta suka bar cikin hall din da sauri. Abba inda ya yi parking din motarsa ya nufa da Mansura, cikin motarsa suka shiga, Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu hawaye ke zuba a idanunta. Handkerchief dinsa ya ciro ya dago kan Mansura dake kafadarsa ya fara goge ma Mansura hawayanta, ya ce "Kinmanta alkawarin da kika yi min kenan." Abba ya ce yana kallan Mansura da har yanzu hawayanta bai tsayaba. Mansura hannu tasa tana goge hawayanta. Shiru Abba ya yi yana kallan Mansura da ta sadda kanta kasa. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura, har yanzu baki shirya fadamin damuwari ba,. Meye sa ko cikin farin ciki kike kuka?." Mansura shiru kanta kasa batace ma Abba komai ba. Hannun Mansura ya kamo ya ce "Fada min yanzu me kike so?." Gida zani." Abba kallan Mansura ya yi kafin ya ce "Kinga yanzu idan kika tafi gida jama'a zasu dauka ko wani abune, ki yi hauri ki zo mu koma har a tashi." Abba ya fadi maganar yana fita daga motar, Mansura ma fita ta yi tana jingina da motar. Abba ruwa ya ba ma Mansura ta wanke fuskarta kafin suka jera suka koma hall din. Cancikin hall din ko lokacin da Mutane suka Ankara Mansura kuka take, bayan Abba ya fita da ita ihu aka kama, wasu nacewa shaukin so ne ya dibeta take kuka. Aisha ko daurewa kawai take, gudin karta fasa kuka cikin Jama'a, hakan ya sa ta lallaba mutane na can suna ma Amarya da ango liki bayan an fitar dasu fili Aisha ta fita daga hall din, daidai zata fito su Mansura kuma zasu shiga ita da Abba. Abba kallan Aisha ya yi da hanzari ganin yadda ta fito hall din, Abba juyawa ya yi yana kiran sunan Aisha ya ce "Mommyna ina zaki?." Aisha bata tanka ma Abba ba ta tafi da sauri. Abba juyawa ya yi ya bi Aisha, shan gaban Aisha ya yi ya ce "Mommyna lafiya ina zaki." Aisha da dama kiris kawai take jira ta fashe da kuka. Abba da mamaki ya bi Aisha da kallo ganin yadda take kuka, Abba cikin sanyi ya ce "Mommyna me ya faru?." Aisha banza ta yi da Abba, ta Kuma juyawa zata tafi, Abba hannun Aisha ya kamo ya ce "idan gida zaki ki tsaya in samu wani ya kaiki a mota." Abba ya fadi maganar yana Kira a wayarsa, sunanan tsaye saiga Wanda ya Kira ya karaso, Abba nuna mai Aisha ya yi ya ce "Bilya ka Kai Mommyna gida." Yana fadin haka ya juya ya tafi. Mansura Kuma tana nan inda Abba ya barta tsaye, Abba na karasowa inda take ya kalleta ya ce "Muje." Da yake hankalin mutane duk suna kan Amarya da ango dake tsakiyar hall din hakan ya sa mutane basu lura da shigowar Mansura da Abba ba, Abba bindir din dari biyu ya diba ya ba ma Mansura ya ce "Kima Amarya da ango liki." Yana fadin haka ya saki hannun Mansura ya yi wajan Amarya da ango Yana masu liki. Mansura ma tashi ta yi ta je ta lika masu kudin da Abba ya bata. An dade ana gudanar da hidimar bikin sai 11 kafin aka tashi suka dibi kawayan Amarya da sauran iyaye da basu tafi ba aka maida kowa gidansu Amarya. Aisha ko misalin karfe 8 ta koma gida tana zuwa ta nufi dakinta tana kuka. Mahaifiyar Aisha tsaye ta yi kan Aisha tana kallanta, Wanda ita Aishar ma bata lura da mahaifiyarta dake tsaye kanta ba. Mahaifiyar Aisha cikin daga murya ta ce "Ke Aisha lafiya meke damunki kike kuka haka?." Aisha dago kanta ta yi tana kallan mahaifiyarta ta ce "Malama, dan Allah ku janye maganar aurena da Yaya Abba." Aisha ta idasa maganar tana goge hawayanta. Malama zama ta yi gefan katifar kusa da Aisha, ta dade tana kallan Aisha kafin ta ce "Saboda me za a janye maganar auranku? Laifin me ya yi Miki?." Aisha gyara zamanta ta yi ta ce "Malama Yaya Abba zai aureni ne bisa umarnin mahaifiyarsa bawai dan Yana Sona ba, yana da wadda yake so, ki yi hakuri Malama rannan karya na yi Miki da nace miki Yana kirana muna chart na fadi haka ne kawai tunanin ko zai canza, Amma yanzu na gama tantance baya sona ba tani ma yake ba, ko na auresa bakin ciki kawai zan kwasa." Shiru Malama ta yi dan tuni ta fahimci haka, sannan tunda Aisha ta fito ta furta haka tasan tana da babban dalilinta. Malama kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha, kin riga kin makaro da kika boyemin gaskiya tun farko, kina ganin yanzu zan iya tunkarar mahaifinki da maganar nan ne in ce mai bakya son Abba, ba zaima sauraran ba, dan haka ki yi hakuri kawai kita addu'a." Malama na gama fadin haka ta tashi ta fita ta ba Aisha waje. Ita ko Aisha abin da ya Kuma ta fasata ta tabbatar Abba baya sonta ganin ta tafi tana kuka Kuma baidamu yasan damuwarta ba, sannan ko ya kirata, abin da ya kamata yadda ya barta tana kuka ace ya kirata. Amina ko taron mutane da yawa hayaniya ta yi yawa shi ya sa bata lura Aisha ta tafi gida ba. Bayan su Aisha sun dawo gida daga wajan partyn, Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura kinsan Allah dazu a wajan partyn nan da aka ce keda Yaya Abba za ku bude fili har kosawa na yi inga Dj ya sa maku waka, inga yadda za ku yi, abin mamaki wai sai ga yaya Abba yana rawa, abin nikam na rasa yadda za ai ya bar ban mamaki." Mansura tashi ta yi ta zauna ta ce "Ni Wallahi kunya ma na ji da farko, ke kece fa baki lura ba tun a cikin mota lokacin da za mu tafi wajan fatin yake rawa baya sa wata waka ba, tun a nan ya fara rawarsa." Amina rike baki ta yi ta ce "Shi ya sa Yaya Abba akwai zuwa biki ai, Amma nikam na sha mamaki, Kuma Allah baki ga abin ba Kun bada kala fa, sai kuka yi kamar wasu Masoya." Mansura hararar Amina ta yi bata ce komai ba. Amina dai gudin karsu yi fada da Mansura cikin daran nan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru ba ta Fadi abin da ke ranta ba. A haka barshi ya kwashesu. Washagari da wuri aka fara Shirin tafiya da amarya, dan abokan angon dama duk suna nan basu tafi ba. Da wuri mai yima Amarya makeup ta zo ta ta yi mata, aka nada Mata jar lifiya da ta ji adon stone daga wajan kan, sosai Amarya ta fito ta yi kyau. Mansura ko tun dazu jikinta ya yi sanyin rabuwa da Aminiyarta, hakan ya sa ko wankan ta kasa yi. Aunty Zainab da shigowarta kenan, kallan Mansura ta yi ta ce "Haba Mansura

Chapter 10 of 15