samu ta shaida Mata Abba na nan zuwa gaidata.
Mahaifiyar Aisha da alamun mamaki a fuskarta ta ce "Abban ne zaizo gaidani?." Kai Aisha ta daga ma mahaifiyarta tana murmushi. Mahaifiyar Aisha kallan Aisha ta yi ta ce "Kin janye maganarki kenan ta fasa auran." Aisha dariya ta yi ta ce "Malama ai yanzu mun fahimci juna." Aisha suna cikin magana da mahaifiyarta Abba ya kirata ya sanar da ita ya karaso. Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Malama, bari in je in taho da shi." Aisha na fadin haka ta fita.
Abba da ya shigo bayan ya gaida mahaifiyar Aisha har falon mahaifin Aisha aka kaisa ya gaidata kafin ya yi masu sallama ya tafi, bai biyema Aisha sun yi fira ba, Yana fitowa ya kalli agogon hannunsa ya ce "Mommyna dare ya yi bari in tafi." Tom Yaya Abba Allah ya tsaremin Kai cikin tsarewarsa."
Abba bayan ya koma gida da ya shigo mahaifiyarsa bata falo hakan ya sa ya nufi badroom dinta.
Abba sallama ya yi, yadda mahaifiyarsa ta amsa mai ya sanar dashi ta fara sakkowa. Abba zama ya yi Yana Bata labarin karamcin iyayan Aisha da tattakonsu. Mahaifiyar Abba cikin jin dadin hirar ta ce "Haba ai baka ga komai bama sai in Allah ya yi auranka da Aisha, zaka san ka yi aure gidan mutunci."
Abba dai murmushi ya yi. Kafin Abba ya ce "Mama dama akan Mansura ne, baki ganin indan mun yi aure da ita zata sanar da ni ahalinta, saboda mama idan zaki kalli Mansura bata da wata wani mugun hali ko rashin da'a ko dabi'a, daga ganinta duk inda ta fito ta samu tarbiya daidai ta addini musulinci, Kuma Wallahi mama inaji ajikina akwai alkairi sosai a aurena da ita."
Mahaifiyar Abba kallan banza ta yi ma Abba ta ce "Nima bance babu alkairi ba, Amma Abba indai ka ga ka auri Mansura ba tare da ahalinta ba saidai in bana raye, idan tana da gaskiya meye abin tsoro a sanin a halinta, tom Wallahi Koda wasa ka karamin maganar nan sai na bata maka rai, idan yau ka je ka ga a halinta na amince ko a ranar ka aureta."
Abba shiru ya yi baice komai ba ya ja bakinsa ya yi shiru, ƙarshe ya tashi ya fita.
Abba na fita bedroom din mahaifiyarsa ya yi wuf ya tura badroom din Mansura ya shiga.
Lokacin da ya shiga bata dakin, Abba na zama ita Kuma ta fito daga toilet. Mansura karasawo inda Abba yake ta yi ta zauna kan abin sallayar da ta yi Sallah. Abba bakin bed din Mansura ya nuna Mata ya ce "Zo ki zauna magana za mu yi."
Mansura tashi ta yi ta je ta zauna kusa da Abba, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Mansura, saura wata biyu bikina da Aisha, ina so in aureki kafin Aisha idan kin amince, amma Kuma auran sirri nake so mu yi bana son kowa ya sani har Amina bana so ta sani."
Mansura Kai take girgiza ma Abba ta kasa magana, da yake bata da wuyar kuka goge hawayan da ya fara zubar Mata ta yi ta ce "Aure Kuma Yaya Abba, auran ma na sirri? A'a gaskiya ni ba zan iya haka ba, ba zan taba amincewa ba Yaya Abba."
Abba shiru ya yi Yana kallan Mansura dake furta kalmar haka ba zai taba yuwu bama Ina.
Abba cikin sanyi ya ce "Mansura ke kanki zakifi samun natsuwa, na tabbata auran zai rage miki wannan damuwar da kike cikinta, ki yi tunanin magata akwai alkairi sosai a cikinta."
Mansura Kai ta girgiza ta ce "Yaya Abba dan Allah mu b.." Abba rufe ma Mansura baki ya yi jin Mahaifiyarsa na Kiran Mansurar tana cewa "Mansura badai kin yi barci ba zo ki bude min.. ... ✍🏻
Littafin Abba na kudine, 400 kacal kafin in gama free pages daga na kammala zai koma 500 my number 08063830828.
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 37-38
Mansura ido ta fara zarewa jin Kiran da mahaifiyar Abba take Mata. Abba cire hannunsa ya yi daga bakin Mansura ya je ya dauke takalminsa ya yi ma Mansura nuni da ta je ta bude ma mahaifiyarsa kofa da har yanzu take Kiran sunan Mansura tana buga kofar, shi kuma ya shiga bathroom din Mansura ya boye.
Mansura tashi ta yi ta je ta bude kofar tana mutsika idanu alamun daga barci ta tashi.
Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura me ya sa kike kwanciya baki ci abinci ba? Yanzu na shiga kitchen na ga jollop din da na yi biki ci ba, maza ki je ki dibo ki ci."
Mansura Kai ta girgiza ta ce "Mama na koshi ne fa."
Mahaifiyar Amina kofar ta ja ma Mansura ta ce "Shi kenan sai da safe."
Mansura ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma inda take ta zauna. Abba na jin tafiyar mahaifiyarsa ya fito. Mansura kallan Abba ta yi ta yi dariya ganin yadda yake zare ido kamar wanda ya yi karya asirinsa ya tonu.
Abba hararar Mansura ya yi bauce komai ba ya juya ya fita da sauri yana sauke ajiyar zuciya.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tsakanin Mansura da Abba, Abba bai sake mata maganar auran da ya naimi su yi ba, haka Kuma bai Kara tambayarta ba akan ahalinta kamar yadda ya yi mata alkawari.
Bangaran Aisha Abba ya yi ƙoƙarin shirya tsakaninsu gudin karta Kuma cewa ta hakura dashi.
Mansura ko kullum cikin waya suke, dan yanzu sai su raba dare suna waya ko chart.
Yanzu haka saura wata daya auran Aisha da Abba, inda soyayyarsa da Mansura yanzu ta yi karfi sosai, dan ita kanta Mansura duk yadda take shashshare Abba yanzu ta daina, idan bai kirata bama har rasa nazuwarta take, sannan abinda Abba ya lura dashi yanzu shigowarsa rayuwar Mansura kamar ya rage mata kunci, ya rabu da ganinta tana kuka kamar yadda take yi da, duk da har yanzu lokuta da dama tana yin kuka amma ba kamar da ba.
Yanzu Haka Abba zaune yake suna fira da Mansura a falon mahaifiyarsa da yake tana islamiya, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Man's kin yi shiru gashi lokaci sai gabatowa yake, na ce ki yi min list na abubuwan da kike bukata wanda zaki yi hidimar bikin Aisha dashi."
Mansura dagowa ta yi tana kallan Abba da idanunta da suka cika da hawaye. Abba kai ya girgiza ma Mansura ya ce "Bana so, me ye Kuma abin kuka anan."
Mansura goge hawayanta ta yi kafin ta ce "Yaya Abba narasa dalili bana son auranka da Aisha, baka ji ba yadda nake ji duk lokacin da ka yi min maganar."
Abba ya dade yana kallan Mansura kafin ya ce "Kina so in fasa auranta ne?." Kai Mansura ta daga ma Abba.
Abba murmushi ya yi ya ce "Shi kenan, gobe idan Mama ta tafi Islamiya zaki rakani wani waje kafin ta dawo."
Mansura dai batace komai, Abba gudin Kar mahaifiyarsa ta dawo ta iskesu tare da Mansura tashi ya yi ya koma wajan aiki. Da yake yanzu Haka yake yi su samu su yi hira da Mansura idan mahaifiyarsa ta tafi Islamiya shi Kuma sai ya zo susha hirarsu.
Washagari kamar yadda Abba yake yi bayan mahaifiyarsa ta tafi Islamiya Abba ya Kira Mansura a waya ya shaida mata ta samesa a waje. Bayan Mansura ta fito Abba fita ya yi ya daga cikin motasa ya rufe get din gidansu kafin ya ja motar suka tafi.
Mansura kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba Ina zamu." Abba bai tankama Mansura ba saida ya yi parking daidai kofar wani gidan almajirai, ya kalli Mansura ya ce "Mansura na yi iya bakin ƙoƙarina ganin na samomana hanyar da zamu cimma burinmu amma na kasa, hakan ya sa naga wannan hanyar ita kadaice mafitarmu."
Mansura kallan Abba ta yi cikin sanyi ta ce "Yaya Abba ban gane me kake cewa ba, wata hanyar ce mafitarmu?."
Abba fita ya yi daga motar yana kallan Mansura ya ce "Muje zaki fahimta yanzu."
Mansura na biye da Abba har wajan wannan almajiran, Abba tambayar daya daga cikin almajiran ya yi ya ce "Kai Malam na nan?." Eh yanzu ya shiga gida." Kai Abba ya jinjina ya ce "Yauwa yi min sallama dashi."
Abba nanan tsaye shida Mansura Malam ya fito. Da fara'arsa ya ce "Usman Kai ne, ku karaso ciki."
Malam har cikin falonsa ya kaisu Abba, bayan sun Kara gaisawa ne Malam ya kalli Mansura ya ce "Usman wannan ce Yarinyar?." Abba Kai ya jinjina ya ce "Eh itace Malam." Malam maida kallansa ga Mansura ya yi ya ce "Yarinya ya sunanki?." Mansura kanta kasa ta ce "Mansura."
Kai malamin ya jinjina ya ce "Ma sha Allah, Mansura ya sunan mahaifinki?." Take idanun Mansura ya juya jin tambayar da malam ya yi Mata, malam lura da halin da Mansura ta shiga ya ce "A'a yan Mata daure kinji sunan mahaifinki kawai zaki fadamin daganan shi kenan."
Mansura cikin rawar murya ta ce "Kabiru." Ta fadi sunan kamar an fusgoshi daga bakinta.
"Ma Sha Allah, Mansura da fatan kina son Usman Kuma kin aminta in miki jagoranci anjima za'a daura auranki dashi kamar yadda ya bukata."
Mansura da tsananin mamaki take kallan Abba Wanda shima ita yake kallo. Mansura kuka ta fashe dashi tana tashi da sauri zata fita. Abba da sauri ya kamo hijab din Mansura yana girgiza Mata Kai.
Malam kallan Mansura ya yi ya ce "Koma ki zauna kinji." Mansura komawa ta yi ta zauna.
Malam cikin hikima ya fara yima Mansura bayani kamar haka "Mansura, Usman ya sanar dani duk abin dake faruwa, abinda zaiyi miki gatane sosai a rayuwarki a matsayin da kike yanzu babu abinda yafi da cewa dake kamar aure, Mansura wannan wata ni'imace Allah ya yi miki karki bujire ma ni'imar Allah Mansura, ki dauki haka a matsayin zanan kaddararki, ko wana dan adama zaki ga da yadda aure yake zuwa masa, dan haka ki amshi ta yin Usman kin ji."
Mansura dai kanta kasa bata ce komai ba har yanzu kuka take, dan bata ganin aure ya dace da ita a rayuwarta.
Malam jin Mansura ba ta ce komai ba ya ce "Mansura, kin amince in zama waliyinki a daura auranki da Usman?."
Mansura kasa magana ta yi hakan ya sa ta daga ma Malam kai, ta tashi da sauri ta fita.
Malam kallan Abba ya yi ya ce "Usman, ka yi jahadi Allah ya saka maka da alkairi, amma da alama akwai wani boyayan al''amari game da yarinyar nan, ka yi hakuri watarana zaka San komai game da ita.
Abba godiya ya yi ma Malam sosai kafin ya ce "Malam yanzu maganar sadaki ita zanba?." Eh Mana Usman ita zaka ba." Abba godiya sosai ya yi ma Malam kafin ya tafi ya sanar da shi zai dawo anjima.
Abba a mota ya samu Mansura ta tusa kanta tsakankanin kafafunta tana kuka. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura bakya son auran ne ki sanar dani ba zan miki dole ba."
Mansura kai ta dago tana kallan Abba, kafin cikin kuka ta ce "Yaya Abba me ya sa ka zabi mu yi auran sirri?."
Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "Mansura, na yi ma mama maganar Ina so in aureki taki amince min, ta ce dole sai in naga ahalinki kafin idan ba haka ba bazata yadda da auranmu ba, kin ji dalilin da ya sa na naimi mu yi auran sirri."
Mansura kallan Abba ta yi ta ce "Ranar da mama ta sani fa?." Bama zata taba Sani ba, sannan idanma ta sani zata yi hakuri dole."
Mansura shiru ta yi bata Kara cewa komai ba, Abba ya tada motar suka tafi da sauri gudin Kar mama ta dawo.
Bayan sun shiga gida Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Nawa zan baki sadaki?." Mansura rufe idanunta ta yi bata yi magana ba.
Abba murmushi ya yi kafin ya ciro kudi ya Mika ma Mansura ya ce "Gashi two hundred thousands ne, amma tsadarki ta ninninka haka, dan ke kin wuce a biya sadakinki da naira saidai saifa, Ina fatan za ki min alfarma ki amshi nairata." Mansura dai kanta kasa batace komai ba. Abba agogon hannunsa ya kalla ganin mahaifiyarsa na gaf da dawowa ya sa ya kalli Mansura ya ce "Zan tafi mama ta kusa dawowa, nan da 1 hour zan zama angon man's." Abba ya fadi maganar yana tafiya dan mahaifiyarsa zata iya dawowa a kowana lokaci.
Mansura zama ta yi bayan tafiyar Abba tana tunanin rayuwarta, ta rasa halin da take ciki farin ciki ko akasin haka ta rasa, amma tana jinta kamar wadda bata da laka a jiki, gaba daya jikinta ya yi sanyi. Mansura na nan zaune cikin wannan yanayin mahaifiyar Abba ta yi sallama ta shigo gidan.
Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi damamaki ganin hijab a jikinta ga Kuma ta kalminta da ta gani kofar falon. Mahaifiyar Abba da mamaki ta ce "Mansura unguwa kika jene na ganki da hijab ga takalmi kofar falo da na gani?."
Mansura ido ta fara rabawa ta ce "A'a mama sanyi nake ji na sanya hijab na fita Ina zazzagayawa harabar gida dan kar in kwanta."
Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "Da'alama dai 'yata ta fara zama jaruma." Mahaifiyar Abba ta fadi maganar tana zama. Bayan ta zauna kallan Mansura ta yi tana dubawa wayarta ta ce "Mansura zo ki gani, ankon bikin Abba da yan iskamiyarmu suka fidda, ni sai na ga kamar wanna tafi kyau?."
Mansura da kallo tabi mahaifiyar Abba.
Mahaifiyar Abba damamaki ta kalli Mansura ganin bata taso ba, hankalinta ma gaba daya ba akanta yake ba ta ce "Mansura lafiyarki kuwa?." Firgigi Mansura ta juyo tana kallan mahaifiyar Abba.
Mahaifiyar Abba shiru ta yi tana kallan Mansura da mamaki ta ce "Mansura lafiyarki kuwa? Tunanin me kike haka?."
Mansura kasa ta yi da kanta batace komai ba.
Mahaifiyar Abba bata sake bin takan Mansura ba ta tafi ta barta nan zaune tana cewa "Allah yaye miki wannan tunane-tunanan Mansura, kina yarinyarki karama zaki maida kanki shohowa tsabar sama rai damuwa da kika yi."
Mahaifiyar Abba har ta shiga bedroom dinta tana mita akan halin mansura na tunane-tunane da tasa ma ranta.
Mansura tarasa dalilin rikicewarta akan maganar ankon bikin Abba da mahaifiyar Abba ta yi.
Gaba daya wunin yau haka Mansura ta yi sa wani iri, ga damuwar auran da Abba daya dora Mata ga Kuma maganar auransa dake gabatowa.
Abba bayan magariba ya dawo gidan ya nufi bangaran mahaifiyarsa, yau Abba ya dage sai ziba yake ma mahaifiyarsa, mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi tana murmushi ta ce "Abba wannan fara'a haka, fada min wana albishir din akai ma?." Abba dariya ya yi yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama Wallahi haka na tsinci kaina nima cikin farin ciki." Tom Allah ya daurar da shi, ya maganar lefan Aisha." Kai Abba ya sosa dan yama manta da maganar laife ya ce "Mama akwai wata Mata a asibitinmu sanarta kenan hada lefi, ita ta hadama Aminu abokina, zan mata magana gobe."Bana son shiririta kaga saura kwana 33 yau bikin, ya kamata ace ka gama hada komai."
Abba sun jima suna fira da mahaifiyarsa kafin ya fita ya nufi bangaransa, wanka Abba ya shiga, bayan ya fito ya shirya cikin wasu k'ananan kaya masu kyau ya dauki key din motarsa ya fita, baidade sosai ba ya dawo. Abba rufe motarsa ya yi ya fita rike da leda ahanunsa ya nufi bangaran mahaifiyarsa yana addu'ar Allah ya sa bata falon. Abba na zuwa ya tura kofar falon rufe ya jita alamun ansa Mata key, Abba Mansura ya Kira a waya da tundazu take tsimayinsa, ta ji an daura auran nasu ko a'a.
Hakan ya sa Mansura na ganin kiran Abba ta daga. Abba cikin kasa da murya ya ce "Zo ki bude min kofar falo, amma fa ki yi a hankali Kar mama ta ji." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa.
Mansura lallabawa ta yi a hankali ta bude kofar falon kamar yadda Abba ya naima. Tana budewa Abba ya maida kofar ya rufe, Mansura magana za ta yi ganin Abba ya rufe kofar amma sai ya yi Mata nuna da hannu akan su shiga ciki."
Mansura na biye da Abba har bedroom dinta. Abba zama ya yi gefan bed din Mansura. Mansura Kuma kanta a kasa daga gani dai tana jira ne daga Abban.
Abba gyaran murya ya yi kafin ya ce "Mansura Kinga yadda kaddarar auranmu mukuma ta kasance ko? Dazu bayan na dawo dake gida na koma malam ya yi jagoranci aka Daura Mana aure bayan fitowa daga massalaci bayan sallar azahar. Ga sadakinki." Abba ya ciro kudi masu yawa daga cikin ajjihunsa ya aje a cinyar Mansura ya ce "Dubu dari da biyu ne kamar yadda na biya na Aisha, ina fatan za ki ci gaba da rufa asirin auranmu har ranar da Allah zai da mama ta amince da auranmu?."
Mansura dago idanunta ta yi da suka cika da hawaye ta kalli Abba, amma bata ce komai ba, ta maida kanta kasa.
Abba cikin sanyi ya ce "Mansura kuka baya maganin komai, duk da soyayyarki ita ta fara zama silar kulla wannan auran namu, amma abu na biyu har da fatan waraka daga zubar hawayanki na kulla Mana wannan auran Mansura."
Mansura fashewa ta yi da kuka jin abinda Abba ya ce ta ce tana kuka "Yaya Abba, hawaye ba za su taba gushewa daga fuskataba har ranar da zan yi bankwana da rayuwa, na aikata kuskure mafi muni a rayuwata, na aikata kuskure Yaya Abba." Mansura ta yi maganar cikin tsantsar kuka.
Abba kallan Mansura ya yi da ya kasa hanata daina kukanta cikin sanyi da rauni ya ce "Wana kuskure ki aikata Mansura? Fada min me kika aikata?."
Mansura kuka take sosai wanda Abba bai taba ganin ta yi irinsa ba, Abba bai hanata ba sai da ya ji tana yi da karfi gudin Kar mahaifiyarsa ta jiyo ya sa Abba ya matso kusa da Mansura ya kwantar da kanta kan kafadarsa yana shafa bayanta, shi kansa ya kasa magana. Sun dauki shawan lokaci a haka. Sauke ajiyar zuciyar Mansura ya ji wanda ya tabbatar mai da ta yi barci, Abba dago kan Mansura ya yi da mamaki yaga barci take, hakan ya sa Abba ya matsar da Mansurar tsakiyar gadon ya kwantar da ita a hankali yana tsoran ta tashi.
Abba bin ledar da ya shigo da ita ya yi da kallo ta kaza da Yoghurt ya mamanta da ita gashi wadda ya siyo mawa din ta yi barci.
Abba tashi ya yi ya shiga toilet din Mansura kafin ya zo ya kwanta gefan Mansurar Yana tofe su da addu'a.
4:00AM Abba ya farka rike da kansa saboda wani mummunin mafarkin da ya yi, Abba sauka ya yi daga kan gadon ya je ya doro Alwallah ya yi nafila da naiman tsari akan mafarkin da ya yi, Abba nanan zaune kan abin sallah yana lazimi Mansura ma ta farka a firgice tana ihu tana Kiran "Abbana."
Abba da sauri ya je ya rirrike Mansura Yana tofa mata addu'a ganin yadda ta firgice har yanzu Kuma Bata bar Kiran "Abbana." ba din da take yi.
Abba rungume Mansura ya yi ajikinsa yana shafa kanta Yana Kuma tofa Mata addu'a.
Mansura jinta jikin mutum da ta yi ya sa ta dawo natsuwarta, dago Kai ta yi suka hada ido da Abba. Mansura zaro ido ta yi tana ƙoƙarin tashi daga jikin Abba .
Abba a hankali ya ce yana Kuma shafa kan Mnasura "Ki natsu Mana, Wana mafarki kikai wanda ya firgitaki haka?."
Mansura goge hawayan da ya fara zubar Mata ta yi ta ce. "Yaya Abba na yi mafarkin Ina sanye da kayan prisoner hannuna an samin min handcuff."
Abba shiru ya yi yana bin Mansura da kallo dan shima irin mafarkin ya yi.
Mansura ko ta dage sai kuka take, Abba hannun Mansura ya kama ya kaita har toilet kafin ya dawo ya ce "Ki yi Alwallah yanzu za a Kira Sallah ki samu raka'atanal fijir."
Bayan Mansura ta fito ta yi raka' a tanal fijiri, Abba ya jamusu limanci suka taka sallar subihi.... ✍🏻
Littafin ABBANA na kudi ne, 400 ne kafin in gama free pages daga zarar na kammala 500 my number 08063830828
Free pages ya kusa karewa.
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 39-40
Bayan sun idar da sallar Abba kallan Mansura ya yi da ta yi tagumi, Abba cire ma Mansura tagumin ya yi ya ce "Mansura dole za ki shiga Islamiyar da mama take zuwa, bazai yuwu a rika barinki ke kadai ba, yanzu bacin mun kwana tare da haka zaki Kari ihunki har ki farka, sannan ki rika salati ba ihu ba kar in kara jin kin farka barci kina ihu haka kamar ba musulma ba."
Mansura dai Kai kawai take tada ma Abba amma gabadaya damuwar mafarkin nan ba karamin tashin hankali ya sata ba.
Abba hannun Mansura ya kama ya ce "Mu je mu koma barci kafin 7."
Abba na rike da hannun Mansura suka hau kan bed din Mansurar, Wanda ita gabadaya tsantsar damuwa tasa bin Abba kawai take ta zama kamar butun butumi. Abba bayan sun kunta da Mansura da tashin hankalin da damuwar halin da take ciki ya sa gaba daya kusan a rabin jikin Abba take amma damuwa da furgicin da take ciki bai bata damar ankarar da ita ba. Wanda yana yin kwanciyar da Mansura ta yi ajikin Abba sai ya taka muhimmiyar rawa ga Abba, Wanda ya ja hankalin Abba zuwa ga Mansura. A cikin sanyayyar Safiyar nan Abba ya kusancin Mansura, bayan mai faruwa ta faru barci ya kwashesu baki dayansu Wanda bugun da mahaifiyar Abba take ma su ne ya tadasu daga barcin da suke yi. Abba furgigi ya tashi da alamar bayyanar tsoro a tare da shi, dan yasan mahaifiyarsa tana buga ma Mansura kofa ne jin shiru Bata tashi ba. Abba wayarsa ya jawo Koda ya duba 8:30 AM, Abba kallan Mansura ya yi da itama daga gani a tsorace take da yanayin.
Mahaifiyar Abba Kara bugawa ta yi tana cewa "Mansura, lafiyarki kuwa yau dinnan."
Abba nuni ya yi ma Mansura da ta je ta bude ma mahaifiyarsa kofa.
Mansura tashi ta yi tana ciccije baki, tana rike kanta dake ciwo sosai har bata gani ta nufi kofar.
Abba Kuma ledar da ya shigo da ita ya dauka da wayarsa da takalminsa da sauri ya yi bathroom din Mansura dasu.
Mansura na rike da kanta taje ta bude ma mahaifiyar Abba kofa. Mahaifiyar Abba bin Mansura ta yi da kallo ganin yadda Mansura ke rike da kanta. Mahaifiyar Abba dakin tashigo da sauri tana kamo Mansura ganin kamar tana layi zata fadi. Mahaifiyar Abba na rike da Mansura har suka karasa kan bed din Mansura. Kwantar da Mansura mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Haba ni dama tun da na ga har 8 baki fito ba nasan kullum kina shigowa da asuba nasan yau ba lafiya, ga Abba ma yau sammakon fita ya yi ko shigowa wajena baiyi ba, amma bari in dakko wayata in kirasa ya zo ya duba ki, yau zuwa Islamiya ma ai bai ganni ba bari in je in Kira wayarsa in fada mai."
Mansura dai bata ce komai ba mahaifiyar Abba ta juya ta fita, bedroom dinta ta je ta Kira wayar Abba, yana dagawa ta sanar da shi ya zo yanzu Mansura babu lafiya.
Abba da baisan yadda zai yi ya fita bedroom din Mansura ba, gashi yana ji tana cewa yau babu zuwa Islamiya ma'ana zata yi jinyar Mansura kenan, Abba dabara ta fado mai ya ce "Mama, gani kusa da gida babu mota ma na fita ki je chamist din Auwal ki bashi wayar zan fada masa abin da zai baki daga na zo sai an mita allura kawai."
Mahaifiyar Abba na kashe wayar ta zura hijab dinta ta ta fita daga gidan, Abba na jin fitarta ya fito da sauri ya nufi bangaransa.
Da yake chamist din babu nisa sosai bayan layinsu ne, tana zuwa ta Kira Abba ta ba Auwal wayar, Abba magungunan da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 15