Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
komai ba, kafin ya ce "Man's kinsan ansamin ranar aure da mommy? To ta tura ma mama text cewa ta fasa aurena, amma mahaifiyarta taki yadda tana so mama ta je ta sa Mata baki mahaifiyarta ta amince tasan maganarta kadai zata ji, tom shine mama take ganin laifinane ya sa tace ta fasa auran, taban nan da kwana biyu in daidaita tsakanina da ita, na rasa yadda zan yi man's" Mansura shiru ta yi dan bata san me za ta ce ma Abba ba. Abba jin ta yi shiru ya ce "Man's ke fa nake saurare." Mansura cikin rashin sanin abinda zata ce ta ce "Yaya Abba ka yi abinda mama tace Mana." Tom ni ai bana sonta, akwai wadda nake so." Daga can bangaran Mansura ta ce "Yaya Abba, ita wadda kake son tana sonka?." Abba shiru ya yi, kafin ya ce "Ban Sani ba, amma dai na yi ma kaina alƙawarin dolanta ma ta soni." Ido Mansura tazaro ta ce "Yaya Abba ana soyayya dole ne? Idan takika fa?." Sai in makata kudi kawai." Mansura dariya ta yi bata ce komai ba. Abba jin Mansura ta yi shiru ya ce "Ya wakar nan da na tura Miki kin jita kuwa?." Mansura tana so ta cema ma Abba a'a amma Kuma ba ta iya garya ba, hakan ya sa ta ce "Na ji." Ido Abba ya lumshe kafin ya ce "Ina so ki Kara jinta, anjima idan na dawo za mu yi magana akan wakar." Kai Mansura ta daga kamar Abba na kusa da ita. Abba bayan ya gama waya da Mansura ji ya yi kamar anwanke mai duk wata damuwa dake damunsa, hakan sai ya bashi kwarin gwiwar Kiran Aisha. Aisha ba ta daga ba sai da ya sake Kira, kafin ta daga tare da sallama cikin sanyinta. Abba cikin salon yaudara dan Aisha ta janye kudirinta kamar yadda mahaifiyarsa ta umarcesa da ya sasanta tsakaninta da ita nan da kwana biyu ya sa Abba ya ce "Mommyna, laifin me na yi kika fasa aurena?." Aisha shiru ta yi kafin ta ce "Yaya Abba naga kamar baka sona ne shi ya sa." Kamar bana sonki, Mommyna da bana sonki da ba zan aminta da auranki ba, wayace miki anayima Namiji auran dole Mommyna haba, Yama za ai in ki son mommyna sai ka ce danbanza." Aisha dariya ta yi da yake zuciyar da ta kamu da so bata da wuyar yafiya ga masoyinta hakan ya sa Aisha gaba daya ta manta da furucinta da ta yi ta fara ganin gangancinta da wautarta ta ce "Shi kenan Yaya Abba, Ina tuba na janye kalamaina masu cike da tarin wauta." Abba cikin jin dadin furucin Aisha batare da yasha wuya ba ya ce "Yauwa Mommyna, yanzu yaushe za ki zo yi ma mama bangajiyar biki danni da ita mu shaida da kin janye maganarki?." Aisha murmushi ta yi ta ce "Umarninka kawai nake jira, ko yanzu ka ce min in je ashirye nake." Abba tabe baki ya yi ya ce "Ki bari sai weekend Kinga Ina gida lokacin." Abba sun jima suna waya da Aisha kafin ya yi Mata sallama da karyar in ya tashi aiki da wuri zai zo ya ganta. Abba bayan ya koma gida, falon mahaifiyarsa ya yi direct, sai dai yana magana tana dauke Kai, sallamarsa ma ciki-ciki ta amsa mai. Abba murmushi ya yi ya ce "Mama akan wata kike fushi da Abbanki, mai sunan mahaifinki." Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Akan Aisha ai Wallahi har falon nan ka kusa bar shigowa, nifa bawai na ce dole ka auri Aisha bane, alokacin da na yi maka maganarta sai ce min ka yi koma baka ganta ba inda ta yi min shikenan, Amma duk da haka ban yadda na yanke hukunci ba sai da ka je ka ganta ka amsa ta yi maka sannan na tura iyayanka, sai yanzu Kuma ka zo ka sani a kunya, tom Wallahi baka isa ba." Abba dariya ya yi ya ce "Mama inda mommy ce tuni muka shirya, dan ta sanar dani ma zata zo yi miki bangajiyar biki." Mahaifiyar Abba shiru ta yi tana kallan Abba, kafin ta ce "Abba dan Allah Annabi ka taimakeni ka fiddani a kunyar uwar yarinyar nan, kana ganin hidimar da ta yi abikin Amina, kasan ba dan itaba ba zamu ga malamai da damaba a wajan walimar nan." Abba kansa ya shafa yana sauke ajiyar zuciya ya ce "In Sha Allah mama zan auri mommy." Abba, bawai ka aureta kadai bane damuwar, ka sota, ka bata kulawa wadda duk wata 'ya mace take bukata, idan ka yi min haka ka gama min komai Wallahi." Abba hannun mahaifiyarsa ya kama ya ce "In sha Allah zan yi ƙoƙarin haka mama." Abba wayarsa ya dauka ya tura ma Mansura text kamar haka "Gani a falon Mama ki fito." Mansura bayan ta gama karanta sakon murmushi ta yi ta maida mai kamar haka. "Yaya Abba yanzu na bar falon, Kuma na yi ma mama saida safe." Abba bayan ya gama karanta sakon Mansura wani ya tura Mata kamar haka "Bana son musu idan kika dawo yanzu korarki za ta yi ki ce kin je kin kasa barci." Mansura bayan ta gama karantawa tashi ta yi ta fito. Abba kamar ba yanzu suka gama chart da Mansura ba dauke Kai ya yi. Mansura zama ta yi tana gaida Abba. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama kullum idan na shigo bana samun Mansura a falon nan, na ce tana tayaki girki ma kuwa?." Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "A'a ai har yanzu kewar kawarta bata saketa ba." A'a, Mama daga yau ta rika fitowa tana tayaki aiki itama ta huta zaman shirun da takeyi , Ina so ma in Samar Mata teaching a school din da Amina ta yi ta huta zama shirun." Mansura turo baki ta yi jin abinda Abba ya ce ta ce "Yaya Abba ni dai banaso." Abba da mamaki ya kalli Mansura ya ce "Shi kenan, akwai computer training in kina so?." A'a, Ni dai bana son komai." Mahaifiyar Abba dariya ta yi ta ce "Shi kenan Abba inda bata so karka takura mata." Abba daga nan baikuma cewa komai ba ya tashi ya fita. Bangaran Aisha da safe tana zaune ta turama Abba Sako na barka da safiya. Abba na wajan aiki ya ci karo da sakon Aisha kamar haka "Barka da Safiya Habibina da'ima. Na farka cikin wallawa, saboda kasancewarka a rayuwata. Ina addu'a Allah ya sa ka soni Koda rabin Wanda nake yi maka ne. Daga Masiyarka mai kaunarka har abadan abidina." Abba copy din text din Aisha ya yi bayan ya gama karantawa ya gyara ya tura ma Mansura. Abba replying a yi ma Aisha kamar haka "Na gode da kulawarki amaryata." Bangaran Mansura ko Koda ta ga sakon Abba maida wayarta ta yi ta aje. Bangaran Abba Kuma jira yake ya ga replying dinta ga ji shiru, hakan ya sa ya Kira Mansura, Kira daya ko ta daga. Abba cikin sanyi ya ce "Baki ga sakona bane?." Yaya Abba naka sakonka Amma.." shiru Abba ya yi kafin ya ce "Amma me?." Mansura cikin sanyi ta ce "Yaya Abba mommy." Shiru Abba ya yi, sannan ya ce "Mansura nasan da mommy ai nace Ina sonki, mommy zabin mahaifiyatace, ke Kuma zabina ce, dan haka daga yau Kar in Kara jin kin min maganar mommy." Mansura shiru ta yi batace komai ba, Abba jin haka ya ce "Mansura, ina sonki, na so ace mu yi maganar gani gaki, Amma naga kamar kina tsoran mama tasan muna soyayya, bana jin mama zata kiki Mansura, idan har mama kike gudu dan Allah ki saki jikinki dani, yau idan na dawo akwai maganar da nake so mu yi." Mansura shiru ta yi kafin ta ce "Yaya Abba mu yi ta a waya Mana." A'a zaki fi saurin amincewa idan muka yita a fili." Abba na fadar haka ya kashe wayarsa. Mansura bin wayarta ta yi da kallo. Abba bayan ya dawo aiki falon mahaifiyarsa yayo kasan cewar bata falon ya sa Abba ya shiga bedroom din Mansura. Mansura na kwance kamar yadda ta Saba, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Tashi ki zauna mu yi magana." Abba ya fadi maganar yana zama bakin gadon Mansura. Mansura tashi ta yi ta zauna tana kallan Abba batace komai ba ta maida kanta kasa. "Man's, ya zaman gida." Abba ya ce yana kallan Mansura. "Alhamdulillah." Mansura ta ce. Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Mansura Ina so ki amince min a yi auranmu tare dana mommy." Mansura dago manyamanyan idonta ta yi cikin razana da jin Abin da Abba ya ce. Kai Mansura ta girgiza ta ce "A'a, Yaya Abba ba zai yuwu ba." Mansura ta idasa maganar tana kuka. Abba kallan Mansura ya yi dake kuka sosai kamar wadda aka yi mata wani abun ya ce "Shi kenan, ya Isa ki bar kukan, ki yi tunani tukun." Abba na fadin haka ya fita da sauri, dai-dai mahaifiyar Abba ta fito itama suka haɗe da Abba da yake fitowa daga bangaran Mansura. Mahaifiyar Abba da mamaki tabi Abba da kallo, dan asaninta ko lokacin da Amina na gidan baya shiga bedroom din Amina in ba ciwo take ba ya shiga ya yi mata allura. Abba kallon da mahaifiyarsa takemai sai ya naimi ya maidashi mara gaskiya, Abba kai ya sosa ya ce "Mama, shigowata kenan na duba Mansura inga lafiyarta na Kira wayarta bata daga ba." Mahaifiyar Abba bata tanka ma Abba ba, cikin falon ta karasa ta zauna kan 2seater kafin,ta kalli Abba da shima ya zauna har yanzu idanshi akan mahaifiyarshi ganin kallan tuhuwar da take mai. Mahaifiyar Abba cikin damuwa ta ce "Abba me ya kaika bedroom din Mansura?." Abba ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Babu komai mama, na Kira wayarta ne bata daga ba shine na shiga in dubata." Kai mahaifiyar Abba ta jinjina alamun mamaki ta ce "Abba meye tsakaninka da Mansura? Kar dai kace maganar da Aisha ta taba fada min ina ganinta kamar a shirme ne gaskiya ce?." Abba shiru ya yi kansa kasa baice komai. Mahaifiyar Abba Kuma ta ci gaba da cewa "Ko shi ya sa kake wulakanta Aisha har ta ce ta fasa auranka?." Nan ma dai Abba shiru ya yi ya kasa magana. Mahaifiyar Abba cikin daga murya yadda Abba bai saba jin tana magana ba ta ce "Abba ba da Kai nake magana ba, me ye tsakaninka da yarinyar can nace." Abba dago idanunsa ya yi yana kallan mahaifiyarsa kafin ya ce "Mama dama ina son zan hada mommy da Mansura in aura rana daya idan kin amince." Mahaifiyar Abba tashi ta yi tsaye tana yi ma Abba kallan banza kafin ta ce " Baka isa ba Wallhi, ban amince ba bazan taba amince waba." Abba shiru ya yi kansa kasa, kafin ya dago yana kallan mahaifiyarsa da yake ma kallan mai saukin Kai ya ce "Mama, auran Mansura ne baki yadda in yi ba, koka in aureta da mommy rana dayane baki yadda ba?." Duka Abba ban yadda ba, ban aminta ka auri yarinyar da har yanzu taki fada Mana ainihin asalinta ba, idan har Mansura ta sanar da Kai ko ita wacece na yadda ka aureta amma idan har zata ci gaba da boyemana asalinta to ni Kuma ban yadda ba ka aureta." Abba shiru ya yi, ya dade bai Kara cewa komai ba kafin ya tashi ya fita. Abba ranar babu dadi a ransa ya yi barci. Washagari ya kama weekend Abba ba za shi aiki ba, Kuma ranar sukayi Aisha zata zo. Aisha da safe ta tura ma Abba sakon text message kamar haka " Assalamu alaikum, na kasa boye farin cikin dake cikin Raina, yau zan ga kyakkyawar fuskar yaya Abbana da nake muradin son gani kullum." Abba sai da ya ga text din Amina ya tuna da yau suka yi zata zo. Aisha da yake gandoki muje biki ce, gashi ta kosa dama taga masoyin nata hakan ya sa karfe goma ta yi shirin zuwa gidan su Abba. Abba ko dama yasan mahaifiyarsa na Islamiya, tana fita shi Kuma ya shiga bangaran nasu, Kiran Mansura ya yi. Mansura gaida Abba ta yi, Abba ko gaisuwar Mansura bai tsaya amsawa ba, da yake a matsaye yake da abin da yake son tambayar Mansurar, hakan ya sa Abba cikin sanyi ya ce "Mansura dan Allah ki fada min labarinki Mana ko kadanne, narantse miki babu wani abu da zaisa in gujeki, Mansura so kawai nake maki ba kaunace, kauna Mai zurfin gaske wadda babu abin da zaki aikata Koda duniya duka zata kiki ne ni ba zan iya kinki ba Mansura, karki ma furucina kallan kalaman baki kawai ko na fada don Ina son sanin wacece ke, da gaske nake har ckin raina nake fada miki haka. Ina jinki me ye ainihin abin da ya sa kika bar gidan iyayanki..✍🏻 Littafin ABBANA na kudi ne, 400 wa inda suka biya kafin in gama free pages daga zarar na kammala zai koma 500 ainihin kudinsa my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Masu tambayar Abbana daga farko ga Link nan 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 35-36 Mansura dagowa ta yi tana kallan Abba da jajan idanunta, baki ta bude zata yi magana ta fashe da kuka. Abba shiru ya yi baice komai ba, yana kallan Mansura da ke aikin kuka, ganin bata da alamar yin shiru ya sa Abba ya ce "Shi kenan, baki son maganar?." Kai Mansura ta dagama Abba tana mai ci gaba da kukanta. Abba cikin damuwa ya ce "Mansura mama ba zata bari in aureki ba idan har baki fada min ainihin wacece ke ba." Mansura tashi ta yi da sauri zata bar falon tana kuka. Abba ma da sauri ya tashi ya rike mayafin Mansura. Mansura jan mayafinta ta yi zata fizge tana cewa "Yaya Abba ka sakan." Abba na rike da mayafin Mansura yana kallanta ya ce "Mansura, akaran kaina Wallahi bana bukatar sanin komai akanki, amma Ina da iyaye su ba za su yadda in aureki a haka ba. Mansura idan har kina sona ki yadda dan Allah ko ahalinki in sani." Mansura kuka take sosai wanda ya sa dole Abba ya yi shiru. Abba na rike da hannun Mansura suka zauna, bayan sun zauna Abba handkerchief dinsa ya ciro yana share ma Mansura hawayanta ya ce "Inda dai baka son maganar bazan sake yi maki itaba." Abba ya dade yanata lallashin Mansura kafin ya samu ta yi shiru, duk da taki cemai komai,shashshekar kuka kawai take. Suna a haka ne Aisha ta yi sallama ta shigo falon, Aisha daskarewa ta yi a tsaye a inda take ganin Abba da Mansura zaune gaf da juna. Abba kallan Aisha ya yi yana kakaro murmushi ya ce "Mommyna, ki shigo Mana." Aisha shigowa ta yi tana yake, duk annurin dake tare da ita take ya gushe ganin Abba da Mansura da ta yi tare. Abba wajan zanma ya nuna ma Aisha. Aisha cikin sanyi ta gaida Abba, dan gaba daya farin cikinta ya gushe. Abba cikin sakin fuska ya amsa gaisuwar Aisha ya ce "Mommyna, ya mutanan gidan, shi ne baki kirani ba kika sanar dani zuwanki ba ko?." Aisha murmushi ta yi ta ce "Ka manta Yaya Abba, yau na sanar da Kai Mana a text din da na tura maka." Abba sosa Kai ya yi ya ce "Ni Kiran waya nake magana ba text ba." Aisha kallan Abba ta yi tana murmushi ganin alamun canji da yayi, ada idan yana tare da Mansura ko kallo bata isheshi ba, hakan ya sa Aisha cikin sakin fuska ta ce "Afuwa Yaya Abba, hakan ba zai sake faruwa." Abba kallan Mansura ya yi da kanta yake a kasa ya ce "Mansura kawo Mata ruwa." Aisha kamar tace a'a, Amma saboda wadda ya sa ta kawo mata ruwan ya sa bata ce ba. Mansura tashi ta yi ta je ta dakko ma Aisha ruwa mai sanyi ta kawo mata. Aisha bude baki ta yi ta ce "Sister ana wannan sanyin damunar, idan akwai mara sanyi kiban in Sha." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Babu duk sun yi sanyi." Ta fadi maganar ahankali kamar an yi mata dole. Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ki je falona akwai ruwa ki kawo Mata babu sanyi." Mansura juyawa ta yi ta fita ta nufi bangaran Abba. Aisha kallan Abba ta yi bayan Mansura ta fita ta ce "Yaya Abba, dan Allah meye tsakaninka da Mansura?." Shiru Abba ya yi, sai kuma ya ga ya yakamata ya fadamata gaskiya kamar yadda tanaima inda yana fadan auransu duk a hada a yi tare dana Mansura, hakan ya sa Abba ya ce "Mommyna, Mansura matar da zan aurece, rana daya nake so ayi tare da naki." Aisha dago idanta ta yi tana kallan Abba cikin gigita da jin Abinda ya ce, Aisha da hawaye har ya fara taruwar mata Kai ta girgiza ta ce "Yaya Abba indai hakane na hakura da kai Wallahi, na hakura ba zan iya kishi da Mansura ba, na hakura na bar Mata kai." Aisha ta idasa maganar tana tashi zata fita tana kuka. Abba hannun Aisha ya kamo cikin tashin hankali, dan yasan idandai ta furta ta hakura dashi ya bani wajan mahaifiyarsa. Hakan ya sa Abba cikin damuwa ya ce "Mommyna, dan Allah karki yi min haka Mana, ki zauna mu yi magana." Abba ya fada Yana nuna ma Aisha caution ta zauna. Aisha Kai ta girgiza ma Abba ta ce "Yaya Abba Ina sonka Amma Wallahi idan har da yarinyar nan zaka hada ka auremu na hakura dakai, ka sakar min hannuna tafiya zan yi." Abba goge zufarsa ya yi ya ce "Aisha na ji tom ki zauna mu yi magana." Daidai lokacin Mansura ta shigo rike da faro a hannunta, tsayawa ta yi tana mamakin abinda ya sa Aisha kuka. Abba kallan Mansura ya yi dake kallansu, Abba hannun Aisha ya kama ya ce "Muje in kaiki gida." Abba ya fadi maganar yana tafiya. Kallan Mansura ya yi da itama shi take kallo ya ce "Bari in Kai mommy gida." Mansura Kai ta daga ma Abba bata ce komai ba. Abba tare da Aisha suka jera suka bar falon, Aisha har yanzu tana goge hawaye. Abba bayan sun fita motarsa ya bude ma Aisha front seat ya ce "Shiga muje babu musu Aisha ta shiga. Bayan Aisha ta shiga Abba kallanta ya yi ya ce "Mommyna meye damuwarki da auran Mansura da zanyi? Idan ma baki so ku zauna gida daya sai ki zabi inda kikeso in ajeki ko nan gidan ko Kuma gidan da na gina." Aisha kallan Abba ta yi da idanunta dake zubba da hawaye ta ce "Yaya Abba dan Allah ka fahimceni ba zan iya kishi da Mansura bane, saboda nasan kana sonta fiye Dani, impart ita kake so bani ba, taya zan hada kishi da ita, bannaima ma kaina kwanciyar hankali bama idanna yi haka. Tursasani Kuma da kake so ka yi in amince maka kana yi ne Yaya Abba kawai dan ka guje ma fadan mama bawai dan kana Sona ba, Yaya Abba dan Allah mu fahimci juna Wallahi da gaske nake na kura dakai zan yi ma Mama bayani nice bana sonka Ina da Wanda nake so." Abba ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan indai haka ta faru baya tunanin zai Kara ganin hakorin mahaifiyarsa, hakan ya sa Abba ya kalli Aisha ya ce "Idan na fasa auran Mansura shi kenan kin hakura zaki auran?." Aisha da mamaki ta kalli Abba jin abinda ya ce. Abba Kai ya daga ma Aisha ya ce "Da gaske nake zan fasa auran Mansura idan har zaki janye kudirinki." Aisha runtse ido ta yi jin abinda Abba ya ce, ko a mafarki Aisha bata taba tunanin Abba zai iya haka ba akanta, tunani ta fara anya ko ba gudin bacin ran mahaifiyarsa ya sa shi in yi haka ba, wata zuciyar ta ce Mata in ma yakasance haka ne zai kula dake kenan ko bayan aure saboda gudin bacin ran mahaifiyar tasa kenan. Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba nasan baka sona karka yaudari zuciyata dan Allah, ka fadamin me ya sa ka zabeni akan Mansura? Bacin nasan Mansurace zabinka?." Abba shiru ya yi yana kallan Aisha, azuciyarsa ya ce tabbasa Mansura ce zabina. Afili Kuma ya ce "Mommyna, auran Mansura ni kadai nake maganarsa Amma mama taki aminta in aureta, Kinga idan na bari kika sukubuce min na yi biyu babukenan." Aisha sosai ta gamsu da hujjar Abba, hakan ya sa ta ce "Shi kenan Yaya Abba na fasa dama zan tursasa zuciyatane rabuwa da Kai ba wai danna daina sonka ba." Abba murmushin jin dadin nasara ya yi ya ce "Yauwa my love har hankalina ya kwanta." Abba na fadin haka ya tada motar suka tafi, suna tafiya suna hira har suka kai gidansu Aisha. Abba hira suka yi yau sosai da Aisha wadda basu taba irinta ba, Aisha bata taba jin ta gamsu da auran Abba ba sai yau, ji take kamar an cire mata wani nauyi a kanta. Abba bayan sun zo kofar gidansu Aisha kallan Aisha ya yi ya ce "Gamu a kofar gidanku, shi kenan in wuce?." Aisha kai ta girgiza ma Abba ta ce "Ka shiga ka gaida Malama kafin." Aisha ta fadi maganar dan ta ji abinda Abba zaice inda tasan Malama bata gida tana makaranta. Abba kayan jikansa ya duba ya ce "Kalli fa kayan dake jikina, gaskiya ba zan iya zuwa da k'ananan kaya ba." Aisha bata rai ta yi ta ce shi ya sa Wallahi na ce zan fasa auran baka sona gashi nan ko mamana baka taba gaidawa ba." Abba da a halin yanzu babu abinda ke tata mai hankali kamar Aisha ta ce zata fasa auransu, dan yasan mahaifiyarsa ko bata tsinenemai ba tom kadanne, inda ta ce ko bayan ranta in bai auri Aisha ba bata yafe ba. Abba cikin sanyi da son nuna ma Aisha ba haka bane ya ce "Mommyna so nawa Ina fada maki bani da lokaci in ba rana irinta yau ba, yanzu ki bari da daddre Zan zo sai in gaidata ya yi Miki?" Aisha damamaki ta ce "Da gaske zaka zo da daddre ka gaidata?." In sha Allah, ki kirani ki tuna min." Aisha yau cikin farin ciki suka rabu da Abba, soyayar Abba ko ta Kara nunkuwa a zuciyarta. Abba lokacin da ya shiga gida ya iske mahaifiyarsa harta dawo, saidai ita kadaice a falon babu Mansura. Abba fita ya yi ya Kira wayar Mansura, har ta katse bata daga ba saida ya sake Kira. Mansura daga wayar ta yi tana kangata a kunnanta. Abba cikin sanyi ya ce "Man's, gani na dawo ki fito falon Mama plz." Mansura kamar zata fasa kuka ta ce "Yaya Abba dan Allah ka rabu dani ka kyaleni." Abba shiru ya yi jin Abinda Mansura ta ce, Abba cikin damuwa ya ce "Man's ki yi hakuri nasan akan Aisha ne, idan ban yi haka ba Mama zata yi fushi dani kito fito dan Allah yanzu kin ji." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa ya koma falon mahaifiyarsa, amma har ya gama zamansa Mansura bata fito ba, dole ya hakura ya fita gidan baki daya. Gaf magariba Aisha ta Kira Abba ta tuna mai zuwa gidansu, Abba kamar ya ce ba za shi ba, amma Kuma Yana tsoran ya yi ma Aisha laifi hakan ya sa bayan ya dawo sallar magariba ya shirya cikin wata brown din shadda ya yi kyau sosai ya shigo falon mahaifiyarsa. Zaune Abba ya iske mahaifiyarsa da Mansura suna hirar Amina da suka gama waya da ita yanzu. Abba cikin sanyi dan yanzu gaba daya mahaifiyar tasa ta canza mai ya ce "Mama zani gidansu mommy zan gaida iyayanta." Tom ka dawo lafiya." Mahaifiyar Abba ta ce. Abba fita ya yi yana kallan mansura da ta sadda kanta kasa. Abba fita ya yi ya Kai Koda ya juyo suka yi ido hudu da Mansura, murmushi Abba ya sakar mata ya tafi. Abba na gaf kaiwa gidansu Aisha ya kirata a waya ya sanar da ita zuwansa. Aisha daketa rawar Kan Abba na ji da ita yanzu, mahaifiyarta ta

Chapter 12 of 15