Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zauna gidan, tom ta ya Kuma za ta cigaba da zama babu Amina. "Wayyoo Allah na, ya zan yi? Ina zan koma da zama. Ya Allah ka kawo min daukin wannan tsillatsillar rayuwar da nake shirin fadawa. Allah ka iyakamce min haka nan, ba dan halina ba ko abin da na aikata, Allah ka dubeni da idon rahama." Mansura kuka take sosai na rayuwarta. Mansura tun da ta zo gidan ba ta yi kukan da ta yi yau ba, uwa uba ga damuwar da ta sa ma ranta na auran Amina. Hakan sai ya taru ya yi Mata yawa, Wanda take ya saukar mata da zazzabi. Kwance take duk ilahirin jikinta rawa yake tsabar zazzabin da take ji, ga gidan babu kowa sai ita kadai. Amina ma da ke banmata wayarta ta bar banmata, saboda ko ta bar Mata ba amfani take da ita ba, hakan ya sa ta bar barmata. Inda dama tana banmata ne dan ta debe mata kewa. Mahaifiyar Amina Koda ta dawo daga Islamiyar da take zuwa ba ta yi tunanin zuwa duba Mansura ba, in da dama ita ba ma'abociyar zaman falon bace. Hakan ya sa zazzabin ya ci gaba da rukurkusar Mansura, ga amai da take ta famar yi, Wanda hakan ya hadu ya Kara galabartar da ita. Amina ba ita ta dawo gidan ba sai 1:30PM kamar yadda ta saba dawowa kusan kullum. Amina Koda ta dawo da yake hankalinta na kan ta watsa ruwa ta yi Sallah, shi ya sa hankalinta bai kai kan Mansura ba dake kwance tana rawar sanyi. Amina ba ita ta lura da halin da Mansura take ciki ba har sai da taga Mansurar ta tashi ta ruga bathroom dinsu tana kwara amai. Amina da idar da sallar ta kenan, tashi ta yi tana kallan Mansura, Wanda Amina sosai ta rude ganin yadda Mansura ta fita hayyacinta. Amina cikin tsoro da yadda ta ga Mansura ta koma ta matsa da sauri tana kamo hannunta ta ce "Mansura, baki da lafiya ne dama ban Sani ba? Kin ga ko yadda kika rame lokaci daya haka." Mansura dai zame hannunta ta yi daga na Amina ta kwanta ta lillibe saboda sanyi da take ji. Sosai Mansura ke rawar sanyi. Amina mahaifiyarta ta je ta samu dake zaune tana tulawar karatun da suka yi, ba yan idar da sallar azahar da ta yi. Amina cikin damuwa da halin da ta ga Mansura ta ce Kamar za ta fasa kuka, "Mama, Mansura ba ta da lafiya sosai, bi ki ga yadda ta koma ba." Mahaifiyar Amina rufe littafin hannunta ta yi tana kallan Amina ta ce "Subahallah, da yake na saba ba fitowa take ba shi ya sa Koda ban ganta ba ban yi tunanin komai ba. Mu je in ganta." Amina da mahaifiyarta tsaye suka yi kan Mansura da ke tsananin rawar sanyi. Mahaifiyar Amina Koda ta taba jikin Mansura zafi ta ji sosai, hakan ya sa ta Kalli Amina ta ce "Amina, Kira yayanki a waya ki sanar da shi ya zo ya duba jikin nata." Amina Kiran Abba ta yi, Amma har ta katse bai dauka ba. Amina sai da ta yi ma Abba Kira uku bai dauka ba. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama bai dauka b..." Amina bata rufe baki ba Abba ya Kira, yana tambayar Amina lafiya. Amina cikin damuwa da halin da ta ga Mansura ciki ta ce "Yaya Abba, Mansura ce bata da lafiya tun safe take amai yanzu haka cikin zazzabi take sosai." Shiru Abba ya yi sannan ya ce "Me ya sa baki fada min ba kafin in fita." Yaya Abba kasan ita Bata magana, tom nima sai yanzu da na dawo na gani, mama, ta ce ka zo ka dubata yanzu." "Okay." Abba ya ce ya kashe wayarsa. Mahaifiyar Amina jin shiru-shiru Abba bai zo ba ya sa ta sa Amina ta Kuma Kira Mata Abba. Mahaifiyar Amina da kanta ta yi ma Abba magana akan jikin Mansurar. Shiru Abba ya yi, kafin ya ce "Mama Wallahi Ina cikin busy, Amma na kusa kammalawa yanzun." Atakaice Abba, bashi ya zo gidan ba sai 4:00.PM lokacin daga ka ga Mansura kasan ta gama galabaita. Abba ganin mahaifiyarshi ta daure fuska,alamun ta yi fushi, ya ce "Afuwa Mama, Wallahi ba laifina bane, Ina yarinyar take?" Amina ita ta yi ma Abba jagora har zuwa bedroom dinsu, dama Abba ya dakko duk abin da ya kamata, ya hado alluransa da drip din da zai sa Mata. Abba kallan Amina ya yi Wanda duk da bai yi magana ba ta fahimci abin da yake nufi. Hakan ya sa Amina ta hau kan bed din tana bubbuga Mansura ta ce "Dear, ki daure ki tashi ga Yaya Abba nan zai duba ki." Amina ta yi maganar tana yaye rufar da Mansura ta yi. Jikin Mansura rawa yake tsabar zazzabin dake cinta. Abba zama ya yi bakin gadon yana kallanta ya ce"Bayan zazzabin da kike ji sai me ke miki ciwo?." "Kaina da cikina." Mansura ta ce a hankali cikin rawar sanyin zazzabi. "Kina da ulcer ne?." Abba ya tambayeta har yanzu idanshi na a kanta. Kai Mansura ta daga mai. alamun Eh. Ruwan Allura Abba ya hada ya mika ma Mansura hannu almaun ta miko mai hannunta, Mansura Kai ta girgiza kamar za ta yi kuka tana kallan Amina, kamar ita ce za ta yi mata allurar, ta ce "Ni dai a ban magani, bana son Allura." Mansura ta idasa maganar kamar zata fasa kuka. Dan Babu abin da ke daga Mata hankali a ciwo kamar allura, duk da shima maganin ba shanshi take ba. Amma gara Mata magani tana daurewa ta sha. Amina kallan Abba ta yi cikin sanyi kamar za ta taya kawarta kuka ta ce "Yaya Abba, dan Allah ka bata magani mana ba sai ka yi Mata allurar ba." Da yake Amina itama bata son Allura shi ya sa ta fahimci halin da kawarta take ciki. Abba hanyar fita ya nuna ma Amina da hannunshi alamun ta fita. Hakan ya sa Amina ba tare da ta Kuma cewa uffan ba ta fita. Abba kuma , mika ma Mansura hannu ya yi alamun ta miko mai hannunta babu alamar wasa. Mansura yarfe hannunta ta fara kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai dan Allah ka ban magani n..." Abba jawo hannun Mansura ya yi batare da ya Kara magana ba, da kansa ya nannade hannun rigarta zuwa gwiwar hannunta yana naiman jijiya. Mansura hannunta gaba daya rawa ya kama gashi tana tsoran musa mai ganin yadda ya daure fuska. Mansura tsabar tsoro hannun rawa ya kama yi sosai, yadda babu yadda za a yi a yi allurar. Abba kallanta ya yi ya ce, "ki natsu ki bar rawa da hannunki, idan ba haka ba aka samu matsala babu ruwana." Mansura rufe ido ta yi jikinta gaba daya yana rawa, dan wannance ranar farko da wayanta da aka taba yi mata allura, ko za a yi Mata kuka take, mahaifinta Kuma da ya ga haka sai ya ce a rabu da ita a bata magani. Hakan ya sa gaba daya tunanin Mahaifin Mansura sai ya dirar Mata a rai, da ace shi ne da ba zai bari a yi Mata allurar nan ba. Mansura rufe ido ta yi lokacin da ta ji shigar allurar a jijiyarta. Abba Kuma ganin yadda take rawa da hannunta ya ce "Wallahi idan kika bari ta kauce sai na sake miki wata garama ki tsaya ruwan ya gama shiga jikinki." Kusan dai yadda allurar jiji take ruwan na fara shiga zaka ji wani zafi sosai. Mansura na jin zafin nan ta fuske hannunta tana mai fashewa da kuka. Dan gaba daya tunanin mahaifinta sai ya dawo mata a rai ga Kuma zafin allura. Abba da mamaki yake kallanta, ga ruwan allurar ko rabi bai shiga ba. Tashi ya yi ya barta zaune ya iske mahaifiyarshi da Amina. Amina ya watsa ma magungunan ya ce "Gashi nan ki bata yanzu ta sha dan ba tsayawa ta yi akayi allurar ba. Abba na fadin haka ya juya ya koma wajan aikinsa. Amina Kuma wajan Mansura ta koma, inda ta iske Mansura ta koma ta kwanta ta Kuma lillibe duka jikinta saboda sanyin da take ji. Amina zama ta yi bakin gadon ta ce "Mansura, ki tashi ki sha magani dan Allah, kin ga Yaya Abba ya ce baki tsaya ya yi miki allurar ba." Mansura cikin rawar sanyi ta ce "A'a ni dai ba zan sha ba." Babu yadda Amina ba ta yi da Mansura ba Amma taki shan maganin, daga ƙarshe ma da ta dameta kuka tasa mata. Amina wajan mahaifiyarta ta je ta sanar da ita abin da ke faruwa. Mahaifiyar Amina cikin takaici ta ce, "Ka ji min shirman banza, ki ce itama shashasha ce kamarki, ba ta son Allura Kuma ba ta son magani.mu je in sameta." Mahaifiyar Amina na zuwa da kanta ta tada Mansura, ta bare magunguna ta mika Mata tare da ruwa ta ce "Maza ki amsa ki shanyesu." Mansura amsa ta yi tana raurau da ido. Rufe idonta ta yi ta watsasu duka a bakinta. Amma Ina ko ciki basu kai ba ta dawo dasu. Mansura sai da ta amaye kaf abinda ke cikinta. Mahaifiyar Amina da takaici take kallan Mansura na amaye magungunan da ta yi. Cikin takaici ta ce "Mansura, yanzu kin fi son a barki da ciwan kenan? Haba Mansura ana ciwo ba a shan magani ne?." Mahaifiyar Amina haka tai ta yi ma Mansura fada-fada nasiha akan kin shan maganinta. Amina yaye bargon ta yi ta Kai bathroom dinsu ta wanke tas. Sannan ta je ta hado Mata ruwan tea. Amma Babu yadda Amina ba ta yi ba Mansura taki tashi bale ta sha tea din dole ta rabu da ita. Mansura na nan kwance har dare gashi har yanzu zazzabin bai sauka ba, hakan ya sa jikin nata ya yi taushi sosai. Abba kamar yadda ya sa ba dawowa aiki, haka yauma ya dawo. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Abbana, ya aikin. "Alhamdulillah mama, aiki babu dadi Kuma ba a fatar a bari." Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce"Gaskiya ne Abbana. Dan Allah ka je ka duba jikin yarinyar nan, magungunan dakabada a bata tana sha ta amayar dasu, yanzu haka ba ka ji jikin nata ba kamar wuta, na ce ko ruwa zaka sa Mata ne, inda na ga dazu ka zo da shi." "Mama, ku shirya ku kaita asibiti kawai, ni ba zan iya dubata Yarinyar nan ba. Mutum ace baya son Allura Kuma baya shan magani to ya take so a yi Mata. "Abba ya fadi maganar yana tashi. Mahaifiyar Abba Kai ta girgiza ta ce "Abba idan Amina ce ya za mu yi haka nan za mu lallabata ta sha, dan haka wannan dinma daurewa za ka yi ka sake dubata." Abba juyawa ya yi zai fita ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Mama bari in watsa ruwa sai in zo in dubata." "A'a Abbana, dazu da na taba jikinta ya yi taushi sosai, ka dubata kafin" Abba ba tare da ya musa ma mahaifiyarshi ba ya juya ya nifi bangaran su Mansura. Amina na zaune ta yi ta gumi ta tasa Mansura gaba tana kallo. Abba gefan bed din ya zauna, hannu ya sa ya yaye bargon da Mansura ta rufa, wanda har yanzu jikinta zafi rau. Abba tashi ya yi ya fita. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ganin zai fita ta ce "Abbana, ba dai har ka dubata?." "A'a mama, sai an sa Mata ruwa Ina zuwa bari in je chamist layin nan in siyo. Abba bai dade da fita ba ya dawo. Kwance ya samu Mansura kamar yadda ya barta. Allurai ya hadama drip din, kafin ya kamo hannun Mansura yana naiman jijiyar da zai jona mata ruwan. Mansura naiman janye hannunta take ganin allurar da Abba yake ƙoƙarin sa Mata ta Karin ruwan da zai Mata. Abba bai Sanda ya buga Mata wata uwar tsawa ba ya ce "Wallahi kika kauce jijiyan nan da na samo, ta kubuce za ki ga abin da zan miki." Mansura tsabar tsoro ga tsawar da Abba ya yi mata kasa tsayar da hannunta ta yi ya yi ta rawa. Abba hannu ya daga zai wanke ta da mari, Amina ta yi saurin rike hannun Abba ba tare da ta san ta yi ba. Da wani mugun kallo Abba ya bi Amina, kafin ya nuna Mata hanyar fita da hannunsa. Amina har tana tuntube garin sauri ta fita. Kallan Mansura ya yi ya ce "Kina son in tsira miki ita a cikin ido?." Mansura Kai ta girgiza kamar za ta yi kuka." "Yauwa tom, idan har baki so tom ki natsu ki bar rawa da hannunki, idan ba haka ba zan mareki Wallahi, Kuma akwai Allurar ta jijiya da zan miki idan na sa miki ruwan, gara ma ki natsu. Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom ai ba da gangan nake rawa da hannun ba, shi ne yake rawa." "Ki rufe idonki, har sai na ce ki bude ki bar gani." Mansura rufe idonta ta yi kamar yadda Abba ya umarceta ta mika mai hannun. Abba cikin lallabawa ya kama hannunta ya tsira mata allurar drip din." Mansura tsabar tsoro ko zafin allurar ba ta ji ba. Abba da sauri ya hada ta jijiyar zai tsira Mata ta bude ido jin shiru-shiru har yanzu ba a yi ba, ba ta san har ya sa mata ta Karin ruwan ba, wata zai Kuma yi mata. Mansura da sauri ta janye hannunta, Abba na gaf tsira Mata ta jijiyar. Abba kallanta ya yi ya ce "Me ye haka kuma ba na ce sai na ce ki bude idonki ba za ki bude ba?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom har yanzu ba ka yi min ba." Abba nuna Mata hannunta ya yi Wanda ya jona mata Karin ruwan ya yi. Mansura da mamaki ta zaro ido, jin ba ta ji shigar allurar ba. Abba umartar ta ya yi da ta sake rufe idanta. Mansura kamar dazu cikin tsoro ta sake rufe idon. Kasan cewar allurar jiji na da zafi, Kuma ita kadan-kadan ake sa ruwanta har ya gama shiga jiji, hakan ya sa ruwan na fara shiga jikin Mansura da sauri ta bude idanta tana naiman fuske hannunta. Abba da karfi ya rike hannun Mansurar ya ce "Wallahi idan baki tsaya ba allurar ta goce sai na sake miki wata." Hakan ya sa Mansura tsawa ba ta shirya ba. Abba na gama mata ya fita ba tare da ya Kuma tanka Mata ba, dan duk ta bashi haushi yadda ta ci mai alokaci abin da ya kamata ace tuni an angama ✍🏻 Fadila Sani Bakori ce Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK ⭐ABBANA⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* P 11-12 Zaune ya iske mahaifiyarshi da Amina da a falon. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce"Ta tsaya ka yi mata alluran ko?." Eh, na sa Mata wasu a drip din, daya ce aka yi mata ta jijiya, yanzu sai wadda za a rika mata kullum sau biyu kwana uku." Ma Sha Allah, tom Allah ya sawake."Ameen." Abba ya ce ya fita zuwa bangaransa. Amina Kuma bangaransu ta koma in da ta iske Mansura na ƙoƙarin yaye bargon da ta rufe da shi. Amina da sauri ta yaye mata bargon tana cewa "Alhamdulillah, da alama zazzabin ya sauka." Amina zama ta yi tana jiran ruwan da aka sama Mansura ya kare ta cire mata, barci ya dauketa. Mansura ko dama tana nan ta tasa ta tsare tana jiran ruwan ya kare ta zare abinta, yana karewa ta zare tana mai ciccije baki. Mansura kasa kwanciya ta yi saboda wata uwar yunwa da take ji. Tashi ta yi ta shiga kitchen din ta sa ruwan tea, ta hada tea ta sha kafin ta kwanta. Washegari, Abba kasan cewar 8:00AM yake fita aiki, hakan ya sa yana tashi, bayan ya zo sun gaisa da mahaifiyarsa ya ce "Mama, allurar yarinyar nan guda biyu ce a rana, idan ta tashi zan yi mata kafin in wuce" Abba suna cikin maganar Amina ta fito da shirinta na fita aiki itama. Amina da fara'arta ta gaida Abba, dan ta ji dadin haduwarsu dan ko ba komai zai rage mata hanya. Bayan Abba ya amsa gaisuwar Amina ya ce "Yarinyar nan ta tashi in yi mata allurarta" ."Kai, Aiko ba ta tashi ba, bari in tadata. "A'a, ki rabu da ita kawai" Abba ya fadi maganar yana tashi. Mahaifiyar Abba Kai ta girgiza ta ce "A'a Abbana, bari in tadata, ai tsallaken bashi da amfani, Kuma ka ga zazzabin ya bugeta sosai karya dawo mata gara a yi." Mahaifiyarsu Amina na fadin haka ta tashi ta nufi bangaransu Amina. Tana zuwa ta ji motsin ruwa a toilet. Zama ta yi tana jiran Mansura ta fito, dan ta San in ta koma ta sanar da Abba ta shiga wanka tafiyarshi zai yi. Mahaifiyar Amina na nan zaune Mansura ta fito. Mansura cikin fara sakin jiki a gidan ta gaida mahaifiyar Amina. Mahaifiyar Amina Kuma tashi ta yi ta ce "Ki yi sauri ki shirya Abba na falo yana jiranki zai miki allurarki ta safe." Mansura da ba ta son allura bata fuska ta yi ta ce"Mama, na fa warke." Mahaifiyar Amina ko kanta ba ta koma ba ta ce "Bana son sakarci shi baisan kin warke bane, ki sa ko hijab ne gashi nan zuwa." Mahaifiyar Amina na kaiwa haka ta fita. Mansura Kuma kamar za ta yi kuka ta dakko hijab din sallarta ta zura, tana zama Abba na shigowa. Mansura Kara bata fuskarta ta yi, zabar razanar allura ko gaida Abba ba ta yi ba. Abba Kuma kallanta ya yi ya ce"Ina ledar magungunan take Alluran na ciki?." Mansura Kauda da fuska ta yi tana turo baki ta nuna ma Abba ledar da hannu. Abba kallanta ya yi da mamaki, amma sai baice mata komai ba ya je ya dakko ledar magungunan. Zama ya yi ya hada allurar, kafin ya umarceta da ta miko hannunta. Mansura goge hawayan ta yi da ya zibo Mata ta na tunawa da Abbanta da ta yi, duk ciwan da za ta yi baya bari ayi mata allura saboda ya san bata son Allura. Abba da mamaki ya kalli Mansura yana zaro ido ganin tana kuka akan Allura. Da katawa ya yi da kamo hannunta ya ce "Lafiya? Me akai miki?." "Ni dai bana son allurar." Mansura ta fada tana goge hawayanta. Abba kallanta ya yi ya ce "Idan kina da kudin da za ki biya na alluran shi kenan, sai in fasa miki kin ga ban yi asarar kudina ba." Tom, ka bari Amina idan ta dawo zan amsa in baka." Abba hannun Mansura ya jawo ya ce "Ki bari idan ta dawo kika amshi kudin kika ban na zubar da sauran." Mansura kuka ta fasa ilahirin jikinta na rawa. Abba tsayawa ya yi yana kallanta, dan ya ci karo da masu tsoran Allura da dama Amma nata azimin ne. Abba ganin za ta bata mai lokaci ya ce "Kin San Allah ko ki bar rawa da hannun ko Kuma in yi miki ita a cikin ido." Mansura jin Abin da ya ce yarfe hannu ta yi tana cewa "Wayyo Allah na ba fa nike rawa da hannun ba shike rawa da kansa." Abba hannun ya Kara kamowa, Mansura ta Kuma fusgewa tana cewa "Tom ka tsaya in shirya." Ta fadi maganar tana mai kara gyara zamanta, Wanda daga gani dai duk cikin razanar allura ne. Abba shi dariya ma taso ta bashi, ganin sai ciku-ciku take wai tana shiryawa. Abba ganin ciku-cikun yaki karewa kallanta ya yi ya ce "Kin gama shiryawa?." Kai Mansura ta girgiza kamar za ta yi kuka ta ce "Bari in daura dankwalina." Abba da mamaki ya kalleta ita dake sanye da hijab. Amma sai ya tsaya ya ga ikon Allah. Mansura tashi ta yi ta je ta dakko wata doguwar riga ta d'aga hijab dinta ta zira, sannan ta kama naiman hular da za ta sa. Abba ganin abin bana kare bane ya ce "Madam ke fa nake jira." Mansura kallan Abba ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Hulata nake nema in sa." Abba wurga mata wata hula ya yi da ya gani a kan bed din nasu, ya ce"Ga wata ki sa." Wannan fa ta yi datti." Abba ganin in dai ya biye ma Mansura bata da ranar shiryawa, inda ya fahimci allurar take so ta zukemawa , hakan ya sa ya tashi ya karasa inda take din ya kamo hannunta ya ce "Malama na makara zo in miki kin ga sai ki ji dadin naiman hularma a natse." Mansura kamar za ta fada ihu ta ce "Wallahi Allah yunwa nake ji." Abba Kai ya girgiza ya ce "Minti goma ya yi yawa ai, yanzu zan Miki, idan kuma kika aata min lokaci kin ji na ce Allah biyu zan Miki, Amma idan kika tsaya yanzu zan miki shi kenan." Mansura jin Abin da Abba ya ce mika mai hannun ta yi tana rufe idonta dake zubar da hawaye. Abba cikin dabara ya tsira mata allurar, Wanda tsananin tashin hankalin ya sa ko zafin allurar ba ta ji ba, sai ji ta yi ya saki hannunta yana cewa "Ki liliya wajan." Abba na fadin haka ya fita. Mansura Kuma dagewa ta yi tana liliya hannun. Abba Koda ya zo falon ba kowa, Amina ta yi tafiyarta, mahaifiyar Amina Kuma tana kitchen. Abba har kitchen din ya bita ya yi Mata sallamar ya tafi aiki. Amina kamar yadda ta saba dawowa aiki yauma haka ta dawo. Tana zuwa ta iske Amina zaune a falon tana cin Abinci. Amina ido ta zaro ta ce "Da alama dai Yaya Abba har da maganin cin Abinci ya hada miki." Mansura turo baki ta yi tana kallan Amina ta ce "Wallhi dear nima na fara tunanin haka, tom Amma Kuma ban sha maganin ba ko daya ba, kodai allurar da ya yi min tana sa cin Abinci ne?." Amina ido ta zaro ta ce "Wai kina nufin ba kisha maganin ba?." Ni Wallahi bana shan magani ni fa ko allura ba a taba yi min ba sai a nan, Abbana ma ko ban da lafiya idan akasa da Allura cirewa yake." Amina da yake itama ba gwanar shan maganin ba ce hakan ya sa ta ce "Ke kinsan Allah ban ga laifinki ba, nima fa haka nake, akwai ranar da ban da lafiya Mama ba ta nan ta je Kaduna biki, daga ni sai Yaya Abba, naki shan magani ya yi min duka ya Kuma ban maganin na sha, tun daga ranar idan ya ban magani na bar yi mai musu." Mansura ido ta zaro ta ce "Ki ce Allah ya taimakan, dazu da kila ma nima duka zai min?." Kai Amina ta girgiza ta ce "Ai Mama na nan, ba zai bigeki ba." Amina tashi ya yi ta ce "Bari in watsa ruwa." Amina gaf la'asar ta shiga kitchen ta dora masu tuwan dare, sai dai ta yi mamaki ko da ta fito kitchen din ba Mansura. Amina na cikin aikin ne mahaifiyarta ta yi sallama ta shigo. "Sannu da dawowa mama, ya jikin Aunty Zainab din?." Mahaifiyar Amina da murmushinta ta ce "Ta haihu, ta tafi da namiji." Ma Sha Allah, Wallahi mama bacin yamma ta yi da yau na je naga jariri." A'a, ki bari nasan kila gobe Abba zai je sai kuje tare." Amina ido ta zaro ta ce"A'a, gaskiya ba zan bi Yaya Abba ba, daga anje ya ce a tafi." Shi kenan, kin tafi ke kadai ai." Amina na nan falon suna hira da mahaifiyarta, ta na yi tana duba girkinta, a haka har ta gama. Amina ba ita ta koma bangaransu ba sai da za ta Sallah Magriba. Koda ta shiga kwance ta iske Mansura ta lillibe da bargo. Amina ganin yadda Mansura ke rawar sanyi cikin damuwa ta ce "Mansura, zazzabin ne ya dawo?." Mansura kai ta daga ma Amina. Amina shiru ta yi, kafin ta ce "Ki tashi ki daure ki sha maganin Mana." Mansura Kai ta kuma girgiza ma Amina ba tare da ta yi magana ba." Amina alwalla ta yi ta ta gabatar da sallar Magriba, kafin ta nufi site din mahaifiyarta, in da ta isketa zaune kan Sallaya ta idara da

Chapter 4 of 15