kina jin ance 10 za a tafi da Amarya Amma kallarki ko wanka ba ki yi ba." Mansura kanta kasa bata dago ba, Aunty Zainab hannun Mansura ta kamo ta rakata har bakin bathroom din kafin ta juyo.
Mansura bayan ta fito babu yadda mai makeup din ba ta yi da ita ba ta yi Mata amma Mansura taki, dole ta rabu da ita ta.
Amina 9:30 aka shiga da ita bangaran da iyayanta maza suke, wato kannan babanta su yi Mata nasiha. Sun dade suna Mata nasiha akan zaman aure da ankarar da ita akan mahimmanci dake tattare da hakuri, tun a nan Amina ta fara kuka. Aunty Zainab hannunta ta kama ta shiga da ita bangaran mahaifiyarsu, mahaifiyar Amina ma kukan take, Amina ganin haka sai ta kara azzaza kukanta. Sun dade kowa ya kasa cewa komai iyayan Amina Mata, su Abba ko suna waje kawayan Amarya da wasu daga cikin iyayan Amarya duk sun shiga mota Amarya kawai ake jira a tafi. Abba cikin jin haushi ya shigo gidan har falon mahaifiyar Rashi ya karasa inda sun tasa Amina sun taru kusan sai kuka suke, masu yin maganar kadan ne. Abba kallan Aunty Zainab ya yi yayar Amina wadda Amina ke bimawa ya ce " Zainab wai meye haka ne." Agogon hannunsa ya kalla ya ce "Kalli dan Allah 11:15AM, muda muka so tafiya tun 10. Aunty Zainab iyayanta ta yi ma magana akan su tashi su tafi ana jiransu.
Amina suka dakko wadda ke aikin kuka tana rirrike mahaifiyarta, shi kanshi Abba sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, Amina Kuma ganin Abba da sauri ta rungumesa tana kuka. Abba hannun Amina ya kama tare da sauran iyayanta da zasu tafi suka fita, da yake a motarsa zai dauki Amarya.
Kasan cewar ya bar gidan gaba ne da a matsayin wajan da Mansura zata zauna, gashi Bata, Kuma Yana lure babu ita gaba daya motocin. Abba shiru ya yi dan baisan wa ma zai tambaya ba Ina take. Wayar Amina ya Kira ya ji ringing dinta a jakarta. Abba kallan Aunty Zainab ya yi dake kusa da Amarya ya ce "Zainab Ina Mansura ne, ta fito mu tafi Mana gashi har an fara tafiya."
Sai yanzu Aunty Zainab tatuna da Mansura tashi ta yi ta ce "Laa ka ka ga namanta da antafi an barta."
Zainab bangaran Abba ta nufa, kwance ta iske Mansura sai kuka take. Auny Zainab tsaye ta yi kan Mansura tama rasa abin da zata ce Mata. Hannun Mansurar ta kama ta ce "Shi kenan ki yi hakuri ya isa haka, tashi mu tafi ke ake jira." Mansura tashi ta yi ta rufe kanta da mayafinta kamar wata Amarya a haka suka karasa wajan motar da Aunty Zainab, Aunty Zainab da kanta ta bude ma Mansura motar ta shiga, kafin itama ta zagaya ta shiga. Suna shiga Abba ya ja motar suka tafi.
Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu ba ta yi shiru ba, ya ce "Ki yi shiru Mana, kanki fa zai iya ciwo."
Aunty Zainab kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura ba za ki yi shirun ba sai kanki ya yi ciwo kenan."
Mansura da kyar ta lallaba kanta ta yi shiru daga nan barci ya dauketa.
3:00PM Abba suka shiga cikin gidan Ahmad dake cikin garin Kaduna.
Yan'uwan Ahmad tarba mai kyau suka yi ma kawayan Amarya da yan'uwanta.
Bayan an ci ansha sun huta, dangin Amarya suka shirya lafiyayyar walima a gidan Amarya. Sosai Walimar ta kayatar saboda ta hada da Amarya da ango kamar yadda ta zo a musulinci, an fadi hakin Mata akan miji, an Fadi hakin miji akan Mata, sai gaf magariba aka tashi daga walimar.
Amina ba ta tashi lura Aisha bata zo ba sai dare, duk suna zaune suna hira ta lura Aisha ba ta zo ba. Amina sosai fargaba ta kamata dan tasan Aisha ta yi fushi ne.
Amina suna zaune suna hira Abba ya Kira wayarta lokacin 8:30PM, banji mai Abba ya ce ba sai ji na yi ta ce "Bari in fada Mata."
Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Saurayinki na Kira." Mansura da yake tasan Abba Amina ke nufi hakan ya sa ta ce "Wallahi ban fita tun da kikace haka."
Amina ido ta zaro ta ce "Ki rufa min asiri karyace ban fadamiki ba, dan Allah ki je." Da kyar Amina ta samu Mansura ta fita.
Mansura can harabar gidan ta hango Abba tsaye a jikin motarsa yana danna wayarsa.
Mansura da sallama ta karasa inda Abba yake.
Abba dagowa ya yi Yana kallan Mansura yana murmushi ya ce .... ✍🏻
Karku manta bana update weekend, sai mun hadu Monday in sha Allah.
Littafin ABBANA na kudi ne 400 kafin a gama free pages my number 08063830828
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 31-32
Abba dagowa ya yi yana kallan Mansura Yana murmushi ya ce "Ke ce farko, Kuma ki ce karshe, bishirnan mai girma wadda da kikai minni dashe, bana ji bana gani bana son mai kushe, burina in rayu da ke har numfashin ƙarshe...."
Mansura rufe ido ta yi tana murmushi ta ce "Yaya Abba da alama kana son wakar nan?." Kai Abba ya girgiza ma Mansura ya ce "Ni ba waka na yi ba, sirrin dake cikin zuciyata na fada."
Mansura da bata gane abin da Abba yake nufi ba ta ce "Yaya Abba wakace sirrin zuciyarka." Kai Abba ya girgiza ma Mansura.
Mansura shiru ta yi dan bata gane abin da yake nufi ba, hakan ya sa ta wuce maganar ta ce "Yaya Abba Amina ta ce kana kirana gani."
Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Gaki, irin in baki abin da zan baki ki wuce ko?." Mansura Kai ta daga ta ce "Dare fa ya yi Kuma na gaji, sannan barci nake ji." Shiru Abba ya yi baice komai ba ya zuba ma Mansura idanu. Ya jima Yana kallanta kamar hoto, Mansura baki ta turo ta ce "Ni dai Yaya Abba Allah zan tafi." Ki tafi ai na baki sakon." Abba ya fada yana kallan Mansura.
Mansura ido ta zaro ta ce "Kaban sakon Kuma? Yaya Abba Wana sako?."
Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Da farkon zuwanki wajan nan me na ce?." Shiru Mansura ta yi da alama tana son ta tuna Abin da Abba ya ce, sai zuwa can ta ce "Yaya Abba baka ce komai ba, waka ka yi fa." A wakar me na ce?."
Mansura bata fuska ta yi alamun ta gaji da tambayoyin kafin ta ce "Tom ai ni ban iya wakar ba." Shi kenan zan tura ma Amina wakar ta WhatsApp ki ce mata ta baki ki ji sakona ne zuwa gareki."
Mansura murmushi ta yi ta ce "Yaya Abba sakon waka?." Eh, ki je ki ji gobe ma yi magana akai, sai da safe."
Abba yana tsaye sai da ya ga shigewar Mansura kafin ya koma part din Ahmad inda zasu kwana tare da Ahmad.
Mansura lokacin da ta shiga Amina na waya da ango, ta shiga ba jimawa suka yi sallama inda shima bangaran angon abokin hirarshi wato Abba ya shigo.
Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Aunty Mansura kin dawo." Eh, na dawo Aunty Amina ya aka yi?." Cewar Mansura.
Amina baki ta rike ta ce "Wallahi Aunty Mansura bakinki ya fara budewa fa."
Mansura hararar Amina ta yi. Kiran da akai ma Amina a waya ya sa ta fasa fadar abin da zata fada, Amina daga Kiran ta yi tana saurar abin da yayan nata ke cewa, da "Okay bari in duba."
Amina WhatsApp ta hau tana bude data sakon Abba yana shigowa. Amina kallan Mansura ta yi tana murmushi ta ce "Aunty Mansura Yaya Abba ya turo miki sako ya ce abaki."
Amina playing wakar ta yi, tare da Mansura suka saurari wakar har ta kare. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Wani abun sai Masoya, Allah sarki sai na tuna soyayata da Yaya Ahmad, ranar da zai fara furta min kalmar so wata waka ya tura min ta Auta MG boy, labari a zuciya ke ce soyayyace taki ta yi tasiri 'yan mata. Kinsan Allah lokacin sai da ya zamana babu wakar da nake so kamarta, da ita Yaya Ahmad ya bayyana min kalmar so ba da bakinsa ba."
Mansura shiru ta yi jin kalaman Amina, hakan ya sa ta dago idanunta ta suka fara tara kwalla ta ce "Amina idan na fahimci abin da kike nufi kina nufin nima Yaya Abba ya sanar min da sakon soyayyarsa ne dawakar nan?."
Shiru Amina ta yi, kafin ta ce "Mansura bahaushe ya ce wai ido ba mudu ba amma yasan kima, yanzu ki a shekarunki ba za ki iya fahintar in Namiji na sonki ba? Tom zan sanar miki da abin da yaya Abba ke ƙoƙarin fada Miki ta waka ni zan fassara miki abin da yake nufi. Mansura Yaya Abba ya kamu da soyayyarki mai tsanani Wanda Ina jin shi kanshi bai san yaushe ya fara ba, amma Yana miki so mai girma wanda ya kasa boyuwa a cikin kwayar idanunsa..."
Shashshekar kukan Mansura ya sa Amina ta dakata, ta tsaya tana kalan Mansura, Amina kallan Mansura ta yi damamaki ta ce "Me ye abin kuka aciki."
Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Nima ban Sani ba, ji na yi kawai Ina kukan."
Kai Amina ta girgiza ta ce "Ki rika addu'a kin ji Mansura, Allah zai miki maganin koma meye, yanzu idan Yaya Abba ya tambayeki kin amshi ta yin soyayyarsa wata amsa zaki bashi?."
Mansura cikin sanyi ta ce "Ni ba zan yi aure ba." Kai Amina ta girgiza ta ce "Ba wannan na tambayeki ba, shima ba maganar aure ya yi ba maganar soyayya wadda take kaiwa matakin aure ya yi, me za ki ce mai?." Amina ta fada tana kafe Mansura da idanunta.
Mansura kasa ta yi da Kai kafin ta ce "Bansan me zancemai ba Amina." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Mansura kina son Yaya Abba?."
Mansura Kai ta dago tana kallan Amina wadda itama ita take kallo, Mansura cikin sanyi ta ce "Ban Sani ba."
Murmushi Amina ta yi ta ce "Mansura ni macece matashiya kamarki, zan iya yadda da furucinki wata soyayyar takan dade a zuciyarka kafin ka fahimci irinta, kai Karan kanka bare Kuma Wanda yake sonka, shi ya sa wata soyayyar sai ki ji cikin masoyan wani na cewa nakasa gane kan wance, alhalin ita kanta ma har yanzu ta kasa gane kan ainihin zuciyarta, idan na Fadi haka a wani wajan ana karyatani ace wai kana sanin sirrin zuciyarka, ni Kuma nasan zuciya ba ko yaushe take ba mai ita damar sanin sirrinta ba, dan haka na fahimceki na taba riskar zuciyata a matakin nan. Yanzu idan Yaya Abba ya ce ki fadi Mai amsar tambayarshi ki yi amfani da kalar salonsa ki bashi amsa, Ina da wata waka zan baki ki bashi amsa da ita kema."
Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Da wata wayar?." Amina murmushi ta yi ma Mansura ta ce "Kin manta Yaya Ahmad ya sa min waya a lefe, da ita zan fara amfani zan baki wayata ki tafi da ita ta rika tayaki hira inda kin zabi zaman gida."Na gode."
Mansura ta ce.
Amina sun jima suna fira da Mansura kafin suka kwanta.
Washagari Abba ya Kira wayar Aunty Zainab ya sanar da ita su shirya da wuri, hakan ya sa Aunty Zainab da wuri suka tashi suka Kara gyagygyara dakin Amarya, suna cikin gyaran ne Abba ya da sauran abokan Ahmad da zasu maidasu gida suka zo, Abba fada ya yi ganin duk basu gama shiryawa ba, haka dai suka shirya da sauri-da sauri suka tafi. Lokacin da suka gama shiryawa za su rafi Amina rungume Mansura ta yi tana kuka taki sakinta, haka suka rungume juna suna kuka, Aunty Zainab da Hassana kawar Amarya babu yadda ba su yi ba amma sunki sakin juna. Abba jin shiru bayan sunce gasu nan fitowa number Aunty Zainab ya Kira Yana fada, Aunty Zainab cikin sanyi ta ce "Yaya Abba ya zanyi dasu gasu sun rungume juna mun yi munyi sunki sakin juna." Abba tsaki ya yi ya kashe wayar ya shigo har falon Aminar, Abba da kyar ya samu ya banbare Mansura jikin Amina, Mansura kuka take har da Majinarta tana "Wayyo Yaya Abba niba zan tafi ba ku barni."
Sosai Mansura da Amina suka ba mutane tausayi, dan da yawansu sun san babu dadi irin rabuwar nan.
Abba cikin lallashin Mansura ya ce "Ki yi hakuri ba za a jima ba zan kawo ki wajanta.". Abba na rike da Mansura dake rusa kuka a haka har suka karasa wajan motasa ya bude Mata ta shiga kafin ya zagaya ya shiga suka tafi. Sun yi nisa da tafiya har lokacin Mansura bata bar kuka ba.
Su Aunty Zainab ne sukaita bata baki a haka suka samu ta hakura ta yi shiru.
Da yake Basu fito garin da wuri ba hakan ya sa gaf La'asar suka shiga garin Katsina.
Suna zuwa Mansura da tun a hanya kantake Mata ciwo na kukan da ta yi suna shiga ta ruga bangaransu da sauri tana kuka, mahaifiyar Mansura Kai ta girgiza ta ce "Dama ni nasan ai za a yi haka." Uhmm, mama danma baki ga yadda aka rabasu da Amina ba, Kinga yadda suka rike juna da kyar aka rabasu, Aminar ma can muka barota tana aikin kukan." Cewar Aunty Zainab.
Kai Mahaifiyar Amina ta jinjina ta ce "Ni dama nasan za a yi haka." Haka dai Aunty Zainab taita ba mahaifiyar Amina labarin tarbar arziki da dangin Ahmad din suka yi masu, Aunty Zainab ta ce "Gaskiya mama Amina ta yi sa'ar dangi miji idan har zasu dore da abinda muka gani, sai dai mu yi mata fatan zaman lafiya Kuma."
Mahaifiyar Amina sosai ta ji dadin maganar da Aunty Zainab ta yi hakan ya sa ta ce "Tom Allah ya daurar da kauna a tsakaninta da su da Kuma Ahmad din baki daya. Allah dai ya sa kun Kara jamata kunne da zaku taho duk da Amina bata da matsala." Ai mama Amina ko fada suka yi da Ahmad ni zan iya cewa laifinsa ne, yarinyar da batasan fushi ba, ba ta dauki rayuwar duniya komai ba ai Kar ki ji komai mama indai akan Amina ne."
Lumshe ido Mahaifiyar Amina ta yi, tsabar jin dadin yabar Aminarta da Aunty Zainab ta yi ta ce "Tom Zainab ina rokan Allah Allah ya sa Amina ta ci gaba da tafiya kamar yadda muka Santa karta canza". Ameen mama."
Aunty Zainab sun dade suna hira da mahaifiyarta.
Bangaran Mansura ko Aunty Zainab ganin har an yi magariba Mansura bata fito ba hakan ya sa Aunty Zainab ta shiga wajan Mansurar da tea a hannunta,. Zaune ta iske Mansurar kan abin Sallah da alama bata jima da idar da Sallah ba, ta yi shiru ta yi ta gumi daga ganinta ta yi nisa a duniyar tunani. Aunty Zainab zama ta yi tasa hannunta daya ta cire tagumin da Mansura ta yi. Sai yanzu Mansura ta dago tana kallan Aunty Zainab. Aunty Zainab kallan Mansura ta yi ta ce "Dauki tea din kisha ga biscuits naga alama kema Amina ta koya miki shan tea da biscuit."
Mansura yake ta yi ma Aunty Zainab kafin ta dauki tea din tana sha kadan-kadan a haka ta shanye.
Aunty Zainab kallanta ta yi ta ce "In kawo miki tuwo Kinga tun safe rabonki da abinci." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Na koshi."
Jinjina Kai Aunty Zainab ta yi ta yi shiru tana kallan Mansura kafin ta ce "Mansura dan Allah karki sama ranki damuwar rashin Amina, haka dama ita rayuwar 'yamace ta gada, kema watarana haka zamu kaiki mu baroki Kuma dole zamu yi hakuri, daga kin yi hakuri a hankali za ki Saba, zan yima Yaya Abba magana kema ya Samar maki ko teaching dinne ya rage miki zaman kadaici."
Aunty Zainab ta dade tana ma Mansura nasiha kafin ta fita ta barta.
Aunty Zainab na fita Kiran Amina Amarya ya shigo wayar da tabar ma Mansura. Mansura bin wayar ta yi da kallo ganin sunan dake jikin layin my bea, Mansura daga Kiran ta yi ta ce "Lafiya Lau muka iso, ya muka barki?." Shiru Mansura ta yi da alamar Amina take saurare kafin ta ce "Tom ma Sha Allah ki gaida min Yaya Ahmad din."
Bayan Amina ta kashe wayar Mansura tashi ta yi ta tada sallar issha'i, tana idarwa ta kwanta, tana kwantawa ko barci ya kwasheta.
Bangaran Abba kasan cewar yasan wayar Amina na hannun Mansura ta bar Mata, hakan ya sa bayan ya yi shirin kwanciya ya Kira layin Amina dan yasan in ba sa'a ba Mansura nacan na kuka, saidai ya yi Kira harta katse ba a daga ba, sake Kira ya yi nanma haka, sai da ya yi ma Mansura Kira 5 Bata daga ba, kafin ya hakura ya kwanta yana tunanin kila ta yi barci ne.
Washagari da wuri yan biki aka fara watsewa, zuwa a zahar ya zamana gidan babu kowa duk sungama tafiya sai Aunty Zainab kadai, itama mijinta anayin magariba ya zo ya dauketa suka tafi ya zamana sai Mama da Mansura kadai a gidan.
Mansura ko washagari kota kan wayarta bata biba dan ta farka da ciwan Kai dan har sai da Aunty Zainab ta sa aka siyo Mata Panadol. Hakan ya sa kusan kwance ta wuni.
Abba Kuma da yake yana wajan aiki hakan ya sa ya shiga busy sai dare ya dawo gidan, kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama taro ya tashi kenan." Bari Abbana, taro ya tashi lafiya ma sha Allah." Abba sun jima suna hira da mahaifiyarsa har ya ci abinci Amma baiga fitowar Mansura ba, hakan ya sa ya ce "Mama na ganki ke ka dai Ina yarinyar nan fa?." Mansura, tana can kila kwance, ni banta ba ganin Wanda baya gajiya da kwanciya ba kamar yarinyar nan." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Wai mama kina nufin duk yau kwance ta wuni ko falon nan bata fito ba?." A'a, ta fito lokacin da Zainab zata tafi."
Abba shiru ya yi baice komai ba, kafin ya tashi ya fita, yana fita ya Kira number Mansura, harta katse bata daga ba, sake Kira ya yi nan ma shiru ba a ta yi picking ba. Abba tafiya ya yi yana tunanin dalilin kin daga Kiransa da Mansura ta yi. Abin da ko baisani ba Mansura bata kusa ta shiga wanka.
Bangaran Aisha sosai take cikin damuwar rashin ganin Kiran Abba a wayarta, hakan ya Kara tabbatar mata Abba ba ta ita yake ba, dan a ganinta ko yadda ta bar wajan party ya kamata ace ya kirata ya tambayi lafiyarta, haka Kuma Bata je Kai Amarya ba nanma a ganinta ya kamata ya Kira ya ji dalilin rashin zuwan nata, Amma shiru, hakan ya sa ta yanke ma kanta shawarar hakura da Abba, Amma Kuma ta sanar da mahaifiyarta ta ce bata isa ba, hakan ya sa Aisha ta kudiri aniyar sanar da mahaifiyar Abba, dan bata jin zata iya auran Wanda baya sonta. Aisha text ta tura ma mahaifiyar Abba kamar haka. "Assalamu alaikum, mama Ina wuni, ta fatan an tashi taro lafiya. Mama dan Allah kisa baki nasan Malama zata ji maganarki, na fasa auran Yaya Abba, na fada ma Malama taki yadda."
Mahaifiyar Amina ba ita taga sakon Aisha ba sai da ta idata idar da sallar asuba. Sosai sakon furucin Aisha ya data Mata hankali, hakan ya sa ta kira Aisha a waya, mahaifiyar Amina cikin sanyi ta ce "Aisha yanzu naga sakonki, ko zaki fadamin dalilinki?."
Aisha cikin sanyi ta ce "Mama Wallahi Yaya Abba baya Sona zai aureni ne kawai bisa umarninki."
Shiru mahaifiyar Amina ta yi dan tarasa abin da zatace, hakan ya sa ta yi shiru ta ce "Shi kenan Aisha zan kiraki."
Bangaran Abba ko duk ya kasa sukuni na rashin samun Mansura a waya da ya yi. Kamar yadda ya saba idan ya yi shirin tafiya aiki yana zuwa su gaisa da mahaifiyarsa.
Yau Abba Koda ya shigo ya gaida mahaifiyarsa bata kallesa ba bare ta amsa mai. Abba shiru ya yi yana kallan mahaifiyarsa. Mahaifiyar Abba wayarta dake kusa da ita ta mikama Abba.
Abba amsa ya yi ya karanta sakon Aisha, bayan ya gama karanta text din dagowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa ...✍🏻
Littafin ABBANA na kudi ne, 400 kafin in gama free pages daga na gammala zai koma 500 my number 08063830828
Fadila Sani Bakori ce.
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 33-34
Abba amsa ya yi ya karanta sakon Aisha, bayan ya gama karanta text din dagowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa.
Mahaifiyar Abba cikin damuwa ta ce "Abba abinda zaka sakamin dashi kenan? Dawana ido kakeso in kalli Malama? Na baka nan da kwana biyu ka yi gaggawar daidaita tsakaninka da Aisha ta yanje kudirinta.
Abba shiru ya yi kafin ya ce "In Sha Allah mama." Yana fadin haka ya tashi ya fita, Yana fita ya Kira number Mansura nanma bata daga ba, abin tsoro ya ba Abba gashi ya kasa tambayar mahaifiyarsa Mansura ganin yadda suke. Abba kallan bedroom din da Mansura da take ciki ya yi, tafiya ya yi ya tura kofar dakin Mansurar, Allah ya taimakesa kofar babu key a jiki ya tura ya shiga. Abba kallan Mansura ya yi da ta lillibe ilahirin jikinta da bargo, Abba tsaye ya yi yana kallanta, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya matsa wajan gadon, bubbuga kafar Mansura ya yi, Mansura cikin barci ta ji ana taba mata kafa, Mansura bude ido ta yi tana kallan Abba dake tsaye akanta.
Mansura tashi ta yi tana mutsika ido, tana kallan Abba.
Abba cikin sanyi ya ce "Kin yi sallah?." Kai Mansura ta girgiza alamun A'a.
"Tashi ki je ki yi Sallah."
Mansura sauka ta yi kan gadon ta shige bathroom da sauri, babu jimawa ta yi alwal ta fito ta zo ta tada Sallah.
Abba zama ya yi bakin bed din yana jiran ta idar da sallar.
Mansura bayan ta idar da sallar, juyowa ta yi tana kallan Abba, kafin cikin sanyi kanta kasa tana wasa da hannunta ta ce "Ina kwana yaya Abba."
Abba kallan Mansura ya yi ba tare da ya amsa gaisuwarta ba ya ce "Me ya sa kika ki daga kirana?."
Mansura waige-waige ta fara nanaiman wayarta ta ce "Namanta da wayarne ban gants bama." Tashi ki duba wayar." Abba ya fadi maganar babu annuri a fuskarsa.
Mansura tashi ta yi tanaimi wayar, Mika ma Abba wayar ta yi, Kai Abba ya girgiza ya ce "Duba ki gani Kira nawa na yi miki."
Mansura dubawa ta yi kafin ta juyo da kallanta ga Abba ta ce "Yi hakuri Yaya Abba Banga Kiran bane."
Abba tashi ya yi ya ce "Okay, ki ajeta kusa." Yana fadin haka ya tashi ya fita. Mansura da kallo ta bi Abba har ya fita, ganin yau yadawo mata ainihin Abban da ta sani.
Abba ko yau Koda ya je aiki ya kasa komai saboda damuwar nauyin da mahaifiyarsa ta daura mai.
Abba zaune yake a office dinsa ya kasa komai, so yake ya Kira Number Aisha amma ya kasa, dan gaba daya sai ya ji ta Kara fita ransa, Abba number Mansura ya Kira Kira daya ta daga. Abba cikin muryarsa mai bayyana yanayin damuwa ya ce "Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata ga zuciyar da ta hana zuciyar Abba sukuni." Ya fadi maganar cikin rashin walwala.
Mansura shiru ta yi, kafin ta ce "Tare da Kai Yaya Abba." Abba kuma ya ci gaba da cewa "Man's Ina cikin damuwa." Abba ya fada cikin damuwa.
Mansura cikin alamun tausaya masa ta ce "Ayyah Yaya Abba me ya saka a damuwa?." Mama ce ta sani a damuwa Mansura." Mansura da alamun mamaki ta ce "Mama Kuma? Yaya Abba yadda mama ke ji dakai nasan ba za ta sa ka a damuwa ba, saidai in baka fahimci mama bane."
Shiru Abba ya yi jin Abin da Mansura ta ce, ya ji ma baice
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 15