Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Mansura take bukata ya fadi ma Auwal ya ba mahaifiyarsa kafin ya kashe wayarsa. Abba bayan ya koma bangaransa wanka ya yi ya sa jallabiyarsa kafin ya Kira wajan aiki ya kawo uzirinsa. Mahaifiyar Abba bayan ta dawo gidan Kiran Abba ta yi ta sanar mai ta dawo, Abba ma cikin karyar da ya koyo yau dinnan ya ce "Mama gani nima yanzu zan shigo gidan." Abba bayan ya gama kimtsawa ya nufo falon mahaifiyarsa inda ya isketa zaune da ledar magungunan. Abba zama ya yi ya gaida mahaifiyarsa tare da cewa "Yau Asibiti aka kirani da wuri na yi fitar safe shi ya sa ban samu shigowa ba." Haba, ni dama yau na jika shiru baka shigoba ina jimamin ko lafiya, sai na tuna Mansura ma ban ji duriyarta ba duk yau, shi ne fa na je dakinta ashe kwance take ba lafiya ban sani ba." Kai Abba ya sosai ya ce "Ayyah, meke damunta?." Muje ka gani." Cewar mahaifiyar Abba tana tashi suka nufi bedroom din Mansurar tare da Abba. Har yanzu Mansura tana kwance ta rufe baki daya jikinta. Abba dake tsaye kan Mansurar hannu yasa zai yaye bargon Mansurar, mahaifiyarsa ta rike hannunsa ta ce "Ni fa dadina daku likitoci kamar ba kusan addini ba wasinku, sai ku bage da ai lallurace, yanzu da kake ƙoƙarin yaye mata bargo in fa ba komai jikinta." Abba Kai ya sosa baice komai ba, kafin ya ce "Tom mama ya zan dubata?." Mahaifiyar Abba da wayau ta fara duba Mansura ganin akwai kaya complete a jikinta ya sa ta ja bargon Mansurar ta ce "Tom Bismillah." Abba hannu ya Kai ya taba jikin Mansura, jin babu zafi sosai ya sa ya ce yana kallan Mansura da idanta yake a rufe ya ce "Har yanzu kan na yi miki ciwo?." Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi tana murmushi ta ce "Ka ce Kasan ma bata da lafiya?." Abba lura da subutar bakin da ya yi kai ya girgiza ya ce "A'a yanayin temperature din ajikinta ne ya nuna ta yi ciwan Kai." Owo, ai fa dadina daku kamar mayu kuke." Cewar mahaifiyar Abba. Abba dai baice komai ba. Allura ya ciro ya hada yana kallan Mansura ya ce "Ki juyo zan miki allura." Abin mamaki duk rakin Mansura a allura juyowa ta yi bata yi musu ba Abba ya yi mata allurar. Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Allurar ma kyau ace ta karya aka yi, Mama ko tea a kawo mata tasha sai tasha maganin." Mahaifiyar Abba juyawa ta yi ta fita ta je hado ma Mansura tea din. Bayan ta fita ne Abba ya ce "Am sorry Mansura, ya jikin naki, da fatan dai bayan kan babu abin da yake miki ciwo?." Mansura kai ta daga ma Abba bata ce komai ba. Abba kuma cikin marairecewa ya ce "Idan Mama ta shigo ki ce Mata ta yi tafiyarta islamiyarya kin ji sauki, sai in yi jinyarki da kaina." Kai Mansura ta daga ma Abba. Mahaifiyar Abba babu jimawa ta hado ma Mansura tea tare da soyayyar doya ta kawo Mata, tea dinma da kyar Abba ya samu tasha ya bata magungunan duk ta sha babu musu. Abba jin Mansura ba ta yi ma mahaifiyarsa maganar tafiya Islamiya ba da ya ce ta yi ya sa shi ya ce "Mama karfa ki ce ba zaki je Islamiya ba saboda ciwan, inda anyi mata allura Kuma ta sha magani yanzu zaki ga ta ji sauki." Kai mahaifiyar Abba ta girgiza ta ce "A'a gaskiya koma na tafi hankalina ba zai kwanta ba, gara dai in naga tabbacin saukin nata zuwa gobe sai in je." Abba baice komai ba ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Allah ya bata lafiya na tafi aiki." Yana fadin haka ya tafi baiso ba yaso ace shi ya yi jinyar Mansurar. Abba yana gaf dawowa gida ya Kira Mansura ya ji ya jikinta da yake lokacin suna tare da mahaifiyar Abba ya sa bata daga Kiran ba. Abba 6:00PM ya shigo gidan rike da ledoji biyu a hannunta, zaune ya iske mahaifiyarsa tana yanka alayyahu. Abba zama ya yi yana mata sannu da aiki, kafin ya ce "Ya mai jikin mama?." Ta ji sauki, amma dai duk yau bata shigo falon nan ba." Abba ledar hannunsa ya mika ma mahaifiyarsa daya ya ce yana tashi "Bari in duba jikin nata mu gani ko tana da bukatar wani maganin." Abba na fadin haka bai saurari cewar mahaifiyarsa ba ya shige bedroom din Mansurar. Kwance Abba ya dadda Mansura ta rufe duka jikinta da bargo. Abba zama gefan bed din ya yi yana kai hannunsa akan Mansurar ya ji jikin nata. "Alhamdulillah, na ji jikin naki babu zafi, ko sanyin damuna ne?." Mansura dai bata ce komai ba. Abba ya Kuma cewa "Ya jikin naki ? Meke miki ciwo yanzu?." Kai Mansura ta girgiza ma Abba ta ce "Babu komai, sanyi nake ji na rufe jikina." Ajiyar zuciya Abba ya sauke, ya kama hannun Mansurar ya ce "Ki tashi ki zauna to." Mansura tashi ta yi ta zauna. Abba Kuma ledar ya shigo da ita ya dakko ya ciro yoghurt dinda ya siyo ma Mansura ya zuba Mata a cup ya mika Mata, da yake Mansura yunwa take ji duk ta kasa cin shinkafar da mahaifiyar Abba ta kawo mata da rana, hakan ya sa ta shanye yoghurt din. Abba ganin ta shanye wanda ya zuba Mata Kuma cika Mata cup din ya yi shima ta shanye, Kara Mata Abba zai yi ta girgiza kai ta ce "Ya isan." Abba ledar ya nuna mata ya ce "Akwai farfesu ciki sai ki ci anjima." Ya fadi maganar yana dakko biscuit ya fasa ya kai daya bakin Mansurar, Kai Mansura ta girgiza ta ce "Na fa koshi." A'a, ki ci biscuit din ki ji yana da dadi." Mansura bude bakinta ta yi tana cin biscuit din. Daidai Abba ya Kai biscuit din bakin Mansura yana Bata gashi sun zauna gaf-da gaf rabin jikin Mansurar kusan duk a jikin Abba take, dan duk ya manmatseta. Abba ganin mahaifiyarsa da ya yi ya sa ya rika Matsawa a hankali da wayau. Ita kanta Mansura batasan lokacin da ta amshi biscuit din daga hannun Abba, gashi dukansu sai su ka yi kamar marasa gaskiya. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Ta sha maganin ko?." Kai Abba ya sosa ya ce "Eh da yake maganin na da karfi yana dakyau ta ci abinci kafin shine ya sa namatsa mata ta ci abincin." Mahaifiyar Abba bata ce komai ba, hannu ta mika ma Abba ta ce "Ban maganin in Bata?." Abba kai ya sosa dan babu magani ma tare da shi, take da bara ta fado mai ya ce "Mama baki ji ba, na ce da yake maganin na da karfi shi ne natsaya ina bata abinci in ba haka ba zai wahalar da ita maganin." Abba ya fadi maganar yana tashi ya ce "Akwai alllurar da zan mata anjima." Abba na fadin haka ya fita. Mahaifiyar Abba bin Abba ta yi yana ta sauri zai fita, mahaifiyar Abba Kiran Abba ta yi, karasawa cikin falon ya yi ya zauna yana cewa "Mama gani." Mahaifiyar Abba daure fuska ta yi ta ce "Abba anya ko kana aiki da ilimin islamiyarka?." Abba dago kai ya yi ya ce "Mama me ya faru?." Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Kai kanka ai kasan abinda ka yi baikamata ba inda kana ganina ka fara Matsawa, da da iliminka Abba zaka zauna kana nanike ma mace wadda ba murramarka ba, to daga yau ban amince ba ban yadda ba karka Kara shiga dakin Mansurar Kai kadai dan Wallahi ka fara bani tsoro." Abba dai baice komai ba kansa kasa, mahaifiyarsa ta gama fadanta ta tafi ta barsa a wajan. Abba tashi ya yi ya fita yana dariyar fadan mahaifiyar tasa dake cemai "Duk inda kake Wallahi ka tuna Allah na kallanka." Abba wanka ya yi da sauri kafin ya nufi masallaci, bai dawo gidan ba sai da ya yi sallar issha'i. Abba ya san ko ya yi ma mahaifiyarsa karyar zai yi ma Mansura allura tare za su shiga bedroom din Mansurar hakan ya sa ya share maganar. Koda ya zo ya ci tuwa ya zauna suka yi fira da ya tashi zai tafi Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Hala ka manta da allurar da ka ce za ka yi ma Mansura?." Ban manta ba na bari sai da safe ne, ganin bata dade da shan maganin ba." Shi kenan sai da safen." Mahaifiyar Abba ta ce, fita suka yi tare da Abba yana fita ita Kuma ta sama kofar falon key ta rufe ta koma bedroomta ta kwanta. Misalin karfe goma Abba ya tabbatar yanzu mahaifiyarsa ta yi barci ya Kira Mansura a waya akan ta zo ta bude masa kofar falon, Amma Mansura Bata daga ba, Abba sai da ya yi ma Mansura Kira 5 bata daga ba dole ya rabu da ita. Ya koma bangaransa yana jin zafin kin daga wayarsa da Mansura ta yi . Mansura ko tana ganin Kiran Abba haka nan taki dagawa. Washagari da safe Abba da ya shigo gaida mahaifiyarsa, bayan sun gaisa ya ce "Mama bari in duba jikin Mnasura in ga jikin nata zan tafi aiki Kar sai na je a kirani irin na jiya." Mahaifiyar Abba tashi ta yi ta rufe alQur'anin hannunta ta ce "Muje nima inga jikin nata." Mahaifiyar Abba ta sa Abba ta yi har bedroom din Mansura, zaune suka iske Mansura daga ita sai towel ta fito wanka. Mansura hijab dinta ta dakko tasa tana rufe jikinta, cikin ladabi ta gaida mahaifiyar Abba da Abba. Mahaifiyar Abba ta amsa Amma Abba da kallo ya bita yana tsaye, mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi da yaja ya tsaya baice komai ba ta ce "Abba ka duba jikin nata Mana." Abba Matsawa ya yi inda Mansurar take ya juyo yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama tasa hijab ta rufe jiki taya zan ji yanayin dumin jikin nata, inda dai ba zan gane da ido ba." Mahaifiyar Abba wajan Mansurar ta matsu itama ta ce "Bari inji jikin nata?." Mahaifiyar Abba hannu sata cikin hijab din Mansura ta taba gefan wuyan Mansura, sanyi ta ji babu wata alamar zazzabi, hakan ya sa ta kalli Abba ta ce "Jikinta babu wata alamar zazzabi." Ya yanayin sanyi yake?." Abba ya tambaya Yana kallan mahaifiyarsa, mahaifiyar Abba daure fuska ta yi ta ce '"Kamar ya Kuma ya yanayin sanyi yake? Shi sanyin har wani yanayi garai, jikinta dai babu zafi sanyi ne a jikin." Abba dafe kai ya yi ya ce "Mama ke ba likita bace ba zaki fahimci abin da nake nufi ba, akwai sanyin da idan ya yi yawa yake saukar da zazzabi." Mahaifiyar Abba rigar da Mansura ta ciro zata sa ta dauka ta bata ta ce "Je kisa kayanki ki fito ya ji yanayin jikin naki." Mansura dauka ta yi ta Koma bathroom din ta sa kayan kafin ta fito. Abba zuwa ya yi ya sa hannu a wuyan Mansurar. Waigowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa ya ga idanta gaba daya akansa yake, Abba wayan cewa ya yi ya ce."Alhamdulillah, ta ji sauki babu zazzabin." Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Ba nace maka ba zaka nuna min iyawa." Abba dai baice komai ba ya juya ya tafi. Bayan ya je aiki ya Kira Mansura a waya, Kira daya ko ta daga. Bayan sun gaisa Abba ya ce "Man's me ya sa jiya baki daga wayata ba?." Yaya Abba na yi barci da wuri ne fa." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Shi kenan, yau karki yi barci daga mama ta rufe ta tafi ki zo ki bude min." Tom." Mansura ta ce. Bayan Abba ya dawo aiki ya zo sun gama fira da mahaifiyarsa kamar yadda ta saba bayan ya fita tasa ma kofar key. Mahaifiyar Abba na rufe kofa Abba ya Kira wayar Mansura ta je ta bude masa, Abba ya lallaba ya shigo yana shiga ya rufe bedroom din Mansura da sauri. Mansura kallan Abba ta yi tana dariya ta ce "Yaya Abba ka cika tsoro." Abba ido ya zaro ya ce "Hmmm." Abba zama ya yi yana ringumo Mansura suka karasa cikin dakin tare, Yana Zama Aisha na Kiran wayarsa, Abba bai daga ba jin tanace da Kira dama jiya ma ta Kira bai daga ba yau ma ya ga miss call dinta ya manta baibi ba, hakan ya sa Abba ya daga Kiran. Abba na dagawa Aisha ta fashe da kuka. Abba cikin sassauta murya yana satar kallan Mansura ya ce "Ya sallam, Momnyna meye na kuka tun da kika Kira wayata kika ji ban daga ba kinsan dai haka nan ba zanki daga kiranki ba, hankalina gaba daya yana akanki, yanzu yi hakuri ki fada min damuwarki ina jinki amaryata ya akai?." Mansura a hankali ta kwace jikinta daga rikon da Abba ya yi Mata ta matsa can gefe tana fashewa da kuka." Abba cikin sauri ya ce ma Aisha "Mommyna ina zuwa zan kiraki yanzu." Abba ya kashe wayar yana dawowa wajan Mansura. Abba na taba Mansura ta bige mai hannu ta ce "Karka Kara tabani ka tafi wajan Amaryarka wadda hankalinka gabadaya yake akanta ni ka rabu dani." Mansura ta fadi maganar tana Matsawa can karshen bed din tana fashewa da kuka, dan tasan bata ga komai bama sai Abba ya auro Aisha, inda ita ba wanda yasan da auranta. Abba jin yadda Mansura ke kuka da karfi rufe Mata baki ya yi ya ce "Mansura dan Allah ki rufamin asiri cikin darannan Kar mama ta jiyo kukanki, kinsan zata ce zata shigo, Aisha Kuma da kike magana akanta sanin kanki ne idan Kuma baki Sani ba ki tambayi Amina bisa umarnin mama zan auri Aisha, kwanakin baya ta yi yunkurin fasa aurena saboda rashin kulawata akanta, idan haka ta Kara faruwa zata fasa Wanda haka daidai yake da tsinuwar mama akaina, ki yi hakuri kin ji." Kai Mansura ta dagama Abb. Can bangaran Aisha Kuma ji ta yi kamar kukan Mace kusa da Abba, hakan ya sa ta Kara Kiran wayar. Har wayar ta katse Abba bai daga ba, hakan ya sa Aisha ta tabbatar yana kusa da Mansura sukai waya. Aisha tura ma Abba text ta yi kamar haka "Yaya Abba dole zaka ki daga wayata inda kana tare da Mansura." Abba ganin text din Aisha rudewa ya yi yasan in dai bai Kira Aisha ba zata dauka hakan ne Kuma yasan yadda take kishi da Mansura inda akanta ma ta ce zata fasa auransa, hakan ya sa Abba ya kalli Mansura ya ce "Man's kin amince in kira mommy, wayar minti goma za mu yi dan Allah?." Mansura kai ta dagama Abba. Abba Kiran Aisha ya yi yana kanga wayar a kunnansa.✍🏻 Kamar yadda kuka Sani bana update weekend, sai Monday in sha Allah za ku jini. Littafin ABBANA na kudi ne week din za zamu shiga zan kammala free pages idan kin shirya my number 08063830828 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 41-42 Abba Kiran Aisha ya yi yana kanga wayar a kunnansa. Daga bankaran Aisha cikin raunanniyar murya wadda ke nuna almar saura kadan ta fashe da kuka ta ce "Yaya Abba ka ce min ka fasa auran Mansura amma bisa ga alama har yanzu kuna tare da ita, nifa Yaya Abba ka fahimceni zuciyata na da rauni bana jure abu ko yaya yake musamman akan abinda nake so, shi ya sa na ce maka na hakura dakai saboda bana son damuwa." Abba kallan Mansura ya yi wadda itama shi take kallo duk da bata ji abin da Aisha ke cewa. Abba ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Mommyna tuntuni na fada maki na fasa Kuma saboda ke na fasa, ki bar dawo min da magana baya dan Allah, yanzu fada min meye damuwarki?." Mansura itace damuwata idan har kana tare da ita ba zan iya auranka ba, Kuma ko yanzu da na Kira na ji kukanta shi ne ka kashe wayarka." Abba da ransa ya fara bacewa cikin daga murya ya ce "Idan kina ganin sai kin fi samun kwanciyar anhali in kika fasa auran nawa shi kenan ni ba zan miki dole ba." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Abba tashi ya yi zai nufi inda Mansura take, Mansura ta yi sauri ta kwanta tana juya ma Abba baya. Abba hannu ya sa ya dago Mansura dake kwance ya ce "Afuwa meye Kuma na fushi bacin da amincewarki na yi waya da ita." Mansura dai bata ce komai ba. Abba jin ta yi shiru ya ce "Tom ya aka yi?." Ba komai." Mansura ta ce, amma a cikin ranta so take ta tambayi Abba akan Aisha amma ta kasa hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru ƙarshe ma juyawa ta yi ta kwanta ta bar Abba nan zaune yana cike da fargabar maganar da ya fada ma Aisha, tsoran Kar Aisha ta aikata abinda ta ce ya sa ya tashi ya shiga bathroom din Mansura ya Kira Aisha. Kira daya ta daga, Abba tashin kukan Aisha ya ji. Shiru Abba ya yi yana sauraran kukan nata gaba daya ransa abace yake da ita, amma tsoran abinda zata aikata ya sa ya ce "Mommyna, tun yaushe nace miki na fasa auran Mansura, tun da kika fadamin ra'ayinki na sanar dake na fasa auran me ya sa Kuma yanzu zaki dawo da maganar baya, indai akan Mansura ne ki bar bata ranki kin ji?." Kai Aisha ta daga ta ce "Shi kenan na fahimta." Yauw Mommyna, Kinga dare ya yi ki kwanta ki yi barci sai da safe." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Abbana na gama wayar ya Kuma badroom din inda ya bar Mansura kwance ya sameta tana kuka. Abba da mamaki ya matsa wajan Mansurar da bai san Abin da take ma kuka ba. Abbba hannu ya sa zai kamo Mansura Mansura ta daga ma Abba hannu ta ce cikin kuka "Ka fada Mata ka fasa aurena me ya sa ka aureni? Yaya Abba ka fada min me ya sa ka auran bacin ka yi ma wadda kake so alƙawarin ba zaka auran ba?." Abba ido ya fara zarewa yana mamakin ya akai Mansura ta ji wayarsa, sai dai yana daga kai ya ga akwai window a wajan Kuma window bude yake zata iya jin duk abin da yake cewa. Abba rasa abin da zaicema Mansura ya yi. Mansura Kuma cikin kuka ta ce "Sai yanzu na gane abinda kake nufi da ka ce mu yi auran sirri, dan Kar Aisha ta san ka aurene saboda ka yi mata alƙawarin ba zaka auran ba." Abba magana zai yi Mansura ta nuna mai hanyar waje ta ce "Yaya Abba ka fita kawai nagama fahimtar abinda kake nufi dani." Abba da mamaki ya kalli Mansura yadda take nunamai hanya ya fira alamun ba zama ta saurareshi ba, bacin aganinsa sanin kanta ne ita yake so ba Aisha ba, hakan ya sa Abba cikin bacin rai ya ce "Haba Mansura ki saurareni Mana nifa ba Aisha bace zabina ke ce zabina." Mansura kunne ta toshe, ta ce "Yaya Abba ka fita dan Allah." Mansura ta fadi maganar tana kuka. Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ba zan fita ba sai kin saurareni." Mansura da ranta ya gama baci, cikin fushi ta ce "Ki fita Wallahi ko in Kira Mama." Abba da zama ya yi bakin bed din Yana ma Mansura kallan mamaki. Mansura ganin haka daga murya ta yi tana Kiran mahaifiyar Abba tana cewa "Mama! Mama!! Maa.." Abba cikin tsoro ya tashi ya rufe ma Mansura baki yana zare ido cike da tsoro. Mahaifiyar Abba da barci bai dade daukarta ba ta jiyo Kiran Mansura, mahaifiyar Abba bakin kofar Mansura ta zo tana Kiran sunan Mansura ta ce "Mansura, lafiya ya aka yi?." Mansura to take ta yi magana amma Abba ya rufe mata baki yadda babu yadda za a yi ta iya magana. Mahaifiyar Abba Kiran sunan Mansura ta Kuma yi, jin shiru bata amsa ba ya sa ta dauka ko mafarki ta yi ta Koma ta kwanta. Abba da tsoran yin magana yake ji gudin Kar mahaifiyarsa ta ji hakan ya sa baiba Mansura damar Kara yin magana ba hannunsa na rufe da bakin Mansura ya kwantar da ita ya kwanta bayanta yana Mata magana a hankali a cikin kunne dan duk ya firgita da Kiran mahaifiyarsa da ta yi. Abba cikin sanyi da lallashi ya ce "Haba Mansura so kike ki tona min asiri kome? Meye na Kiran Mama cikin darannan? Yanzu dai inda duk bayanin da zan Miki kinki saurarata Kuma kin ki yadda da abinda nace zan Kira maki Amina ki ji, Wallahi har yanzu bana jin soyayyar mommy cikin raina zan aureta ne kawai dan in faranta ma Mama rai, maganar da kika ji ina yi awaya mommy ta fahimci ke nake so Kuma na fada Mata zan aureki shine ta ce ta hakura idan har zan aureki ba zata iya kishi dake ba saboda nafi sonki, tom idan har mommy ta furta ma Mama haka zan fuskanci fushin mama, Kuma kinsan fushin iyaye akan yayansu bashi da kyau, kin ji dalilin da ya sa na amsa ma Aisha na fasa auranki dan a wuce maganar." Abba har ya kari maganarsa ya gama Mansura batace mai komai, ranar dai haka suka yi barci kowa zuciyarsa ba dadi. Kiran sallar farko Abba ya tada Mansura ya bude kofar falon ya fita ita Kuma ta rufe ta koma ta kwanta. Mahaifiyar Abba bayan ta idar da sallar Asuba tana zaune Mansura ta shigo gaidata, suna cikin gaisawa Abba ya shigo. Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura hala jiya mafarki kika yi, kina ta Kiran sunana da karfi abin har ya naimi ya ban tsoro, na je Kuma inata bugun kofarki na ji shiru." Abba katse maganar ya yi ya ce "Ina kwana mama, kin tashi lafiya, hala mafarki ta yi." Lafiya lau Abba, ina jin Kam mafarkin ta yi baka ji ba Wallahi yadda take kwalamin Kira da na yi Mata magana Kuma shiru." Mansura tashi ta yi kanta kasa ta gaida Abba, ta tashi ta fita da sauri ta nufi kitchen tana so ta sha tea ta tashi da yunwa. Bayan Mansura ta fita ta jimawa Abba ya tashi ya fita, ya nufi kitchen din inda ya ga Mansura ta yi. Abba na zuwa ya yi hugging din Mansura ta baya ya ce "Da fatan kin tashi lafiya, ya fushi dani." Lafiya Lau, inanan Ina yi." Murmushi Abba ya yi ya ce "Shi kenan, yanzu za ki bar yinsa." Abba na fadin haka ya Kira Amina a waya. Amina da mamaki ta bi wayarta da kallo ganin kamar Kiran ya yi wuri. Dagawa Amina ta yi tana gaida Abba. Bayan sun gaisa da yake wayar a speaker ya sa Mansura na ji Abba ya ce "Amina Ina naiman taimakonki kisa baki Mana ko Mama zata janye aurena da Mommy." Daga bangaran Amina ido ta zaro ta ce "Yaya Abba har yanzu dai ka kasa hakura da Mommy, ko jiya Wallahi ta kirani tana kuka ta kawo min kararka ta ce baka kiranta sai in ita ta kiraka Kuma in ta kiraka dinma ba lallai ka daga ba. Haba Yaya Abba yau fa saura kwana 28 bikinku kake wannan maganar, Kuma kasan zaka fuskanci fushin mommy indai ka ce zaka fasa auran nan,Koda yake Yaya Ahmad ya ce wai Mansura kake so, tom Yaya Abba in ma Mansurarce zabinka ka hadasu su duka ka aura Mana." Shiru Abba ya yi yana kallan Mansura alamun kinji ko. Har yanzu hannunsa daya Yana rike Mansura. Daidai lokacin mahaifiyar Abba ta shigo kitchen din. Abba da sauri ya saki Mansura ya ce ma Amina "Shi kenan zan kirakk." Abba na fadin haka ya kashe wayar yana kallan Mahaifiyarsa ya ce "Ruwan zafi na zo samu yau a gida nake son yin breakfast." Mahaifiyar Abba bata tanka ma Abba, Abba Kuma ruwan zafin hannun Mansura ya amsa ya fita da sauri.

Chapter 14 of 15