Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Amina a matsayin gudummuwarta. Mansura sosai take cikin damuwar rabuwa da Amina Amma ta daure dan karta rusa farincikin da Amina take ciki. Koda mai lalle ta zo yi masu Mansura kamar ta ce bata so amma tana tsoran maganar mutane hakan ya sa ta zauna aka ranga da Mata kunshinta. Ana yin kunshin Amina ta ce ma maikunshin "Ki yi Mata mai kyau fa kamar nawa itace babbar kawar Amarya." Hakan ya sa mai kunshin da zana ma Mansura filawa mai kyau. Da yake duk sun sha dilka hakan ya sa kyan kunshin ya Kara fita sosai. Washagari aka kafa manyan rumfuna a harabar gidansu Amina. Mahaifiyar Amina da Amina duk sunyi gayyatar walimar, haka mahaifiyar Aisha ma ta gayyaci duk dalibanta walimar, hakan ya sa walimar ta samu halartar mutane da yawa. Amarya Amina wanka ta yi ta cakare cikin wata farar lifaya, sosai ta yi kyau daga kaganta babu tambaya ka ga Amarya, duk wanda ya zo gidan sai ya yaba kyan da Amina ta yi. Mansura bayan ta tafito wanka ta dauki daya daga cikin kayan Amina za ta sa inda dama kayan Aminar take sawa. Amina dake zaune kusa da Mansura hararta ta yi kafin ta wurga Mata wata farar lifaya wadda adonsu ne kawai ya banbanta da tata, ta ce "Ga wadda za ki sa nan." Mansura da mamaki ta kalli Amina tana son yin magana Amina ta yi Mata nunu da mutane cikin dakin, hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Wadda ta yi ma Amina kwalliya ita ta yi ma Mansura ta nada Mata lifayar. Wayyo mutane rasa Wanda ya fi kyau suka yi tsakanin Mansura da Amina, idan ka gansu zaka dauka su duka amaran ne. Amina ko da bata taba ganin Mansura da kwalliya ba sosai ta rude ganin yadda Mansura ta yi Mata kyau kamar ka saceta ka gudu. Wasu da dama kance Mansura ta fi masu kyau, wasu Kuma suce Ina ma za a hada Amarya ai dabance. Nan fa aka yi ta yi masu hotuna. Aisha ta tasha adonta cikin wani green hijab, duk sai ta sha jinin jikinta ganin yadda Mansura ta sha kyau kamar ita ce amaryar. Hutuna akaita daukarsu Amina, Wanda duk abin da ake Mansura na yake ne kawai, amma bi ainihi jitake kamar ta fasa ihu, amma ta daure ta cije dan karta sama kawarta damuwa. Hassana da itama tasha adonta da Hajiya babba sosai ta yi kyau, jawo hannun Aisha ta yi suka bar falon Abba da yake acan suke shirin nasu. Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha in fada miki gaskiya kin yi kyau, amma shegiyar yarinyar nan ta fiki, ke bakya kishin Yaya Abba ya ganta haka, wai ke ko kunshin ma kinkasa yi." Aisha kallan hannuwanta ta yi ta ce "Ki bari kinsan Mommy ta dauki nauyin walimar nan tom aiki ya yi yawa, saidai gobe zan je a yi min da wuri, inda na ji ance sai lahadi za a kai Amarya ba ranar da aka daura aure ba." Hassana shiru ta yi ta ce "Shi kenan, Amma dai ki kula kema gobe ki yi wankan kece raini." In sha Allah ." Aisha ta ce tana kama hannun Hassana ta ce zo muje mu yi hoto da Amarya." Hassana da yake duk kawayansu daya da Amina kusan, hakan ya sa duk sai da ta bisu ta rada masu su yi hankali da Mansura maciyiya Amanace tana naiman kwace ma kawarta Aisha saurayin da zata aura, hakan ya sa duk sai suka rika yi ma Mansura kallan munafuka, sukaita sakar mata habaici. Amina tana so ta yi masu magana amma Kuma bata son Mansura ta ji tana musu magana inda ta ga kamar bata barga da ita suke ba. Mansura ko tasan ta ita suke saidai damuwar da take ciki ya sa bata maida hankali akan habaicin nasu ba, dan bisa ga alama ma ba ta su take ba. Aunty Zainab ta shigo bangaran Yaya Abba inda kawayan Amarya da Amarya suke. Aunty Zainab kallan Mansura ta yi cikin fada-fada ta ce "Mansura me kuke yi ne tun dazu gashi can har an fara gabatar da Malamai bakwanan." Mansura cikin sanyi ta ce "Afuwa Aunty Zainab, bamu san amfara ba." Mansura kama hannun Amina ta yi kawayan duk suka rufa masu baya suka fita. Suna zuwa aka gwada masu inda zasu zauna. Take Malama Safiya ta fara wa'azi akan falalar dake tattare da aure, menene aure, waya ce ai yi shi, da Kuma darajar da yake tattare da ita. Bayan ta gama dogan bayani, ta kuma koma magana akan hakin dake rataye akan mace akan mijinta. Take jikin mutane ya yi sanyi. Bayan ta gama taba Malama Farisatu wadda ta fara bada kisa akan yadda Nana Khadija ta zauna da ma'aiki S.A.W. jikin Amina sanyi ya yi da yake babu wuyar kuka take ta fara kuka wadda ita kanta bata san me ya sa ta kukan ba. Mansura da dama kiris take jira, take itama ta ji kukan na niyyar kwace Mata, hakan ya sa da wayau Mansura ta bar gun kamar tana sosa ido kamar wani abu ya fada mata a ido. Mansura can bayan window Abba ta je inda tasan babu wanda zai ganta ta duka a wajan ta fashewa da kuka. Mansura kuka take sosai har tana jan ajiyar zuciya irin na wanda ya gaji kuka ya yi yinsa. Mansura sai ji ta yi an dago kanta. Dago fuskarta ta yi wadda ta dame gaba daya saboda kuka. Abba bai cema Mansura komai ba handkerchief dinsa ya ciro yana goggo ma Mansura hawayanta. Sai dai ya gama kafin ya kama hannunta ta tashi daga duken da take. Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Kalli yadda kika bata kwalliyarki, Haba Mansura ba za ki iya hakuri ki adana duk damuwarki ba har Amina ta bar gidan nan ba kamar yadda na ce maki ko? Kuma ahaka ne kike cewa ke bakya son komai kin fi so a barki ki ci gaba da zama gida, ai dole ma in sama maki abin yi idan aka gama hidimar bikin nan." Abba shiru ya yi yana kallan Mansura dake sauke ajiyar zuciya akai-akai, kafin zuwa can ya ce "Kin ga kin bata kwalliyarki, zo muje ki wanke fuskarki ki koma wajan walimar Kinga Amina yanzu zata kasa natsuwa idan ta fahimci baka wajan. Abba shigowarsa kenan ya shiga bangaransa ya dakko kayansa da zaisa gobe ya ci karo da kukan Mansura bayan window shi. Can bangaran Hassana ko ganin Abba ya shigo Mansura Kuma ta tashi ta yi bangaran nasa, Wanda basu san ita bata san shigowarsa ba, inda ita a saninta kamar yadda mama ta ce sai taro ya watse zai dawo da kwana gidan, hakan ya sa ita ba ta yi tunanin yana gidan bama. Hassana ganin haka radama Aisha ta yi, yarinyar can ina jin wajan Yaya Abba zata, Kinga ta yi bangaran da muka shiga dazu, ba ance nan ne sight dinsa ba, zo muje mugani idan ya tabbata hakane Wallahi mu taru mu taka Mata burki." Hassana dakyar ta samu Aisha ta yadda ta bita, dan ita Aisha bata son ganin abinda zai bata mata rai, Amma kamar yadda Hassana ta ce mata wai zata kafa hujja ne. Lokacin da Aisha suka iso wajan su Abba sun shiga falonsa kenan shida Mansura yana rike da hannun Mansurar. Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Kinga abinda nake fada miki ko? Yanzu Kinga ya kama hannunta sun shiga dakinsa, lallai Allah ya sa wannan ma ba wani mugun abin suke aikatawa ba." Aisha tsabar kishi kasa magana tayi sai hawaye dake zuba daga idanta. Suna nan tsaye sai ji suka yi an daba su. Hassana da sauri ta waigo tana kallan Khadija ta ce "Khadija lafiya?." Nazo wucewa ne na hangoku da fatan dai lafiya na ga Aisha na kuka?." Hmmm Ina fa lafiya ana shirin kwace mata Wanda zata aura." Nan Hassana ta kwashe komai ta fada ma Khadija. Khadija wani uban ashar ta yi ta ce "Yanzu kunsan yadda za yi ke Aisha ki tsaya acan yadda ba zai ganki ba, Hassana mu Kuma zo muje da sunan mun zo daukar Abu inda dai yasan nan muka zauna muka shirya, mu shiga mu gani." Aisha inda suka ce Mata ta tsaya tana jira, inda Hassana da Khadija suka tusa kansu cikin falon Abba ba tare da sun yi sallama ba. Abba Kuma daidai ya kama ✍🏻 Fadila Sani Bakori ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 25-26 Abba daidai yana taimaka ma Mansura wajan gaya nadin Lifayarta su Hassana suka shiga. Ganin Abba da Hassana sai suka yi kamar marasa gaskiya, Abba Kuma kota kansu bai bi ba haka Mansura ma ci gaba da tayata ta gyara nadin Lifayarta ya yi. Kallan Hassana da Khadija ya yi da suka ja suka tsaya sukai kai kuri ya ce "Lafiya?." Khadija cikin wayancewa ta ce "Mansura dan Allah ba ki ga handbag dita ba kamar anan na barta." Ku shigo ku duba Mana. Abba ya ce yana kamo hannun Mansura suka fita. Khadija da Hassana rike baki sukai suna kallan juna. Khadija ta ce "Lallai maganarki gaskiya, wannan ma ai ya wuce soyayya sai dai abarshi layin iskanci, in ba iskanci ba lifaya fa yake tayata nadawa." Hassana dai tsabar al'ajabi ta kasa magana sai zuwa can ta ce "Tab dijam, inko hake ne akwai aiki a gaban Aisha babba ." Khadija Kai ta jinjina ta ce "Wani Anya ko Yana ma wani son Aishar kuwa?." Ke bisa ga alama fa Yana sonta, munafukar yarinyar nan ce ke son yi mai kutse cikin rayuwa, ni yanzu tunani na daya yadda za mu yi mu taimaka ma kawarmu dan idan har muka ce ta bar mata shi ai ta shadamu gara mu nuna Mata ita karamar Yar iska ce." Hassana koma hannun Khadija ta yi ta ce "Muje Aisha na can tana jiranmu." Har suka koma Aisha na kuka dan taga fitowar Abba rike da hannun Mansura yana mata magana mai kama da lallashi. Hassana dafa Aisha ta yi ta ce "Tabbas abin da zafi Wanda kake so ka bashi Amana ka ganshi yana cin amanarka, amma ki yi hakuri sai yarinyar nan ta yi fiye da kukan da kika yi. Yanzu muje ki wanke fuskarki Kar a ganema kin yi kuka." Aisha zuwa ta yi ta wanke fuskarta kafin suka koma wajan walimar inda suka iske Mansurama zaune kusa da Amarya. Kasan cewar an gayyato malamai mata da yawa hakan ya sa anjima ana walimar kafin aka rarraba abun rabon da mahaifiyar Aisha ta yi kafin aka watse daga walimar. Amina kalllan Aisha ta yi ta ce "Mommyna ya dai na ganki so silent." Aisha fashe ma Amina da kuka ta yi cikin kukan Aisha ke fada ma Amina ita ta hakura da Abba inda ta ga gaba daya hankalinsa ba akanta yake ba." Amina gudin Kar hankalin mutane ya dawo kansu ya sa ta jawo hannun Aisha da sauri suka nufi bangaran Abba, ganin sauran kawayansu a falon Abba ya sa Amina ta bude bedroom din Abba suka suka shiga. Amina zaunar da Aisha ta yi gefan katifar Abba, sannan ta zauna kusa da ita. Amina cikin damuwa da lamarin ta ce "Mommyna duk abin da zan fada maki ba lalle ki yadda ba, amma a iya sanina fara hidimar bikin nan nawa ne Yaya Abba suke magana da Mansura." Aisha Kai ta girgiza ma Amina ta ce "Amina Allah na hakura da Yaya Abba saboda dama nike sonshi shi baya Sona, sannan maganar ace wai yaya Abba baya soyayya da yarinyar nan ba haka bane, kila dai ke ce baki Sani ba." Amina shiru ta yi dan ta rasa yadda zata fahimtar da Aisha ta gane, Amina ta ce "Aisha Koda ma ace Yaya Abba na son Mansura kamar yadda kika ce kinsan dai sai ya aureki Koda zai aureta." Aisha Kai ta girgiza ta ce "Amina ba zan iya zama da wanda hankalinsa baya kaina ba Yana kan watane, da ace daga ni sai shi ne ina da tabbacin babu wata a ransa da zan iya hakura in auresa, amma yanzu Kam na hakura ina mai tabbatar miki yanzu haka daga na je gida zan sanar da Malama." Amina hankalinta tashe ta kamo hannuwan Aisha ta ce "Mommyna Wallahi Allah kin ji na rantse miki Yaya Abba baya sa soyayya da Mansura idan baki yadda ba Bari in Kira Mansurar ki ji daga bakinta." Amina na fadin haka ba ta saurari ta fita. Babu jimawa Amina ta dawo tare da Mansura. Bayan Mansura ta zauna Amina cikin sanyi ta ce "Mansura Aisha wai ta fasa auran Yaya Abba saboda ita a zarginta Kuna soyayya da Yaya Abba ne, na yi ƙoƙarin in fahimtar da ita taki ganewa shi ne na kiraki ki fada mata da kanki ko zata fi yadda." Mansura tabe baki ta yi kafin ta ce "Ni bansan meye ma wata soyayya da take magana akai ba, Yaya Abba ma ni sanadiyar bikin nan muka fara magana dashi, idan kin ce za ki fasa auranki da Yaya Abba ni babu ruwa." Amina kallan Aisha ta yi ta ce "Kin ji ko mommy, Idan da tana soyayya da Yaya Abba ai da nafi kowa Sani, abinda kike tunanin Wallahi ba haka bane." Aisha sai yanzu ta ji ta gamsu. Cikin sanyin muryarta ta ce "Shi kenan na fahimta." Amina ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wai lallai sannu hajiyar kishi, ki gode ma Allah ma Yaya Abba bamai kula-kulan yan Mata bane, ki ce da munsha kallo." Aisha murmushi ta yi Bata ce komai ba. Da daddare kawayan Amina duk sun watse ya rage daga Amina sai Mansura, Wayar Amina ringing ta yi, bayan ta dauka, ta ce "Okay gani nan zuwa." Aisha kallan Mansura ta yi ta ce "Ina zuwa Yaya Abba ke kirana, Allah dai ya sa ni ba aiki zai Sani ba." Amina zaune ta samu Abba cikin motarsa, Abba umartar Amina ya yi da ta shiga, Amina bayan ta zauna ta kallli Abba ta ce "Yaya Abba ka kirani Kuma ka yi shiru. Murmushi Abba ya yi ma Amina ya ce "Ba wani abu bane Amina tambayarki zanyi, tun da yarinyar nan ta zo gidan nan bata taba baki labarin wani na gidansu ba ko labarin mamanta ko babanta ba?." Amina shiru ta yi tana kallan Abba, azuciyarta ta ce "Me Yaya Abba zai yi da bincikar labarin Mansura, ko dai da gaske ne suna soyayyar kamar yadda Aisha ta ce ." Abba ganin Amina ta fada duniyar tunani muntsilarta ya yi ya ce "Idan kin gama tunanin ina jinki." Amina murmushi ta yi tana kallan Abba ta ce "Yaya Abba kasan Mansura bata magana ko labari ka kawo Mata daga eh, sai uhm, idan abun dariya ne ta yi murmushi shi kenan, kwanannan ne ma idan ina magana har take samun baki, Amma bata wata doguwar magana bare har ka ji sirrinta. Abba shiru ya yi kafin ya ce "Amma ke me kika fahimta game da yarinyar?." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Wallahi Yaya Abba na kasa fahimtar komai akanta, amma dai koma meye iyayanta da alama attajirai ne." Kai Abba ya jinjina ya ce "Nima naga alamar haka. Amina gobe za a daura miki aure ina so yau din nan, ki zungureta da maganar ahalinta da kin ji me zata ce, Ina so ki min recording hirar taku, abin da nake so ki ce Mata, Mansura niko inata so in tambayeki wai wacece Fatima da kike yawan Kira a mafarkinki." Daga nan Kar ki ce mata komai." Amina Kai ta jinjina ma Abba alamun za ta yi, kafin Amina ta ce tana wasa a hannunta alamun maganar kamar ta yi mata nauyin fada ta ce "Yaya Abba kana son Mansura ne?." Abba hararar Amina ya yi ya ce "Dan na yi miki wannan maganar akanta shi kenan ina sonta, Kinga ke aure zaki yi mama Kuma kullum tana Islamiya, shine nake so mu ji wacece ita in ta kama mu maidata gidan iyayanta sai mu maidata kamar zaifi." Amina turo baki ta yi ta ce "Allah sarki Yaya Abba tashin hankalin Mansura kenan akan auran nan nawa zaku ce ba za ku iya zama da ita ba, gashi nan tun kafin in yi auran Kun bayyana min hakan, inda gashi kana maganar maidata gidansu." Abba da mamaki ya kalli Amina dake goge hawaye ya ce "A'a Amina ya zamu koreta bayan kin riga kin maidata Yar gida, kawai dai Yana da kyau mu San wacece ita din." Shi kenan Yaya Abba zan tambayeta yanzu daga na shiga ciki, duk yadda muka yi da ita zan tura maka ta WhatsApp." Amina fita ta yi daga motar ta koma bangaran Abban da yake can zasu kwana. Amina kwance ta samu Mansura kamar yadda ta barta. Zama ta yi gefan Mansura tana kallanta ta ce "Na zaci zan dawo in iske Kun yi barci, in fara jin labarin Fatima, kinsan har so nake ki rigani yin barci dan in ji labarin Fatima, wai wacece Fatimar nan ne da kika dameni da kiranta a barcinki?." Tun da Amina ta fara magana Mansura ke aikin zazzare ido tashi Mansura ta yi daga kwancan da take ta ce "Dan Allah me nake cewa?." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Ina tambayarki wacece Fatimar da kike Kira a barcinki kina tambayata me kike cewa." Mansura tari ta kama ta dafe karjinta da take jin kamar zai fito, take idanunta suka kada suka yi jajir, har yanzu Kuma ba ta fasa tarin da take ba, take hankalin Amina ya tashi ganin yadda Mansura ke tari gata rike da kirji. Amina dafa Mansura ta yi tana mata aikin sannu. Mansura dago idanunta ta yi da duk haskansu sai da suka kada suka yi ja ta ce "Amina dan Allah ki yi shiru koda ace kin ji bakina ya furta wata kalma akan Fatima dan Allah karki tambayan akanta, zuciyata ta yi raunin da bana iya bayani akan komai." Amina Kai ta daga ma Mansura tana danasanin tambayar da ta yi mata ganin yadda take ta birkice Mata. Amina ruwa mai sanyi ta kawo ma Mansura ta ce "Dear ki sha ruwan sanyi." Kai Mansura ta girgiza ma Amina hakan ya sa ta aje ruwan cikin sanyi. Amina tsabar yadda jikinta ya yi sanyi da halin da taga Mansura ya sa ko takan Abba ba ta biba da yake jiran ta tura mai recording din da ta yi mai na firarta da Mansurar. Abba da ya ji shiru text ya tura ma Amina na ya ji shiru, Amina sending recording din ta yi ma Abba ta WhatsApp. Abba koda ya gama sauraran daukar bai fahimci komai ba game da Mansura, sai rudin da ya fahimci tambayar ta je fa Mansura, dan ko yananin yadda Amina ke magana ya nuna hankalinta atashe take ma Mansura magana. Abba bai gama jin ƙarshen daukar ba ya kashe ya Kira wayar Amina. Amina na dagawa Abba ya ce "Ba Mansura Wayar." Amina tashi ta yi ta kanga ma Mansura wayar a kunnanta. "Hello, Mansura kina jina." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Eh Yaya Abba ina ji." Abba shiru ya yi kafin ya ce "Ya na ji muryarki kamar kina kuka?." Mansura sanin ta yi ma Abba alƙawarin ba zata Kara kuka ba ya sa ta ce "A'a ba kuka nake ba." Kin tabbata." Eh Allah Yaya Abba ba kuka nake yi ba." Okay gani a wajan get fito in gani." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Mansura tashi ta yi tana Kuma goge hawayanta ta kalli Amina ranta alamun bace ta ce "Ke kika ce ma Yaya Abba ina kuka?." Amina kallan Mansura ta yi ta ce "kin ji na yi waya dashi ne?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom ni ya zanyi hawayena ya tsaya?." Amina tashi ta yi ta zauna tana kallan Mansura ta ce "Bari in Kuna miki kira'a ki saurara ranki zai yi sanyi." Mansura turo ma Amina baki ta yi ta ce "Yaya Abba fa ya ce inje in ya gani in ba kuka nake ba, Kuma na yi mai alƙawarin ba zan Kara kuka ba." Okay, ki dauraye fuskarki ki shafa powder ba zai gane ba." Mansura fuskarta ta dauraye ta zo Amina ta shafa Mata powder kafin ta fita. Abba na zaune ckin motarsa ya hango Mansura hakan ya sa ya fito daga cikin motar ya jingina da motar. Mansura na wasa da hannuwanta ta karaso inda Abba yake. Abba hararar Mansura ya yi ya ce "Baki iya sallama ba ko ?." Mansura shiru ta yi batace komai ba, Abba ya ce "Shi kenan inda ba zaki yi min sallama ba wace ki tafi." Mansura turo baki ta yi kafin ta ce "Assalamu alaikum." Ameen Wa'alaikumussalam. Yauwa ko kefa, bari inga da gaske ne baki yi kukan ba." Abba na fadin haka ya kunna flashlight din wayarsa ya haske Mansura. Mansura hannu ta sa tana kare fuskarta saboda haskan na kashe mata ido. Abba kashe hasken ya yi ya ce "Da gaske dai baki yi kuka ba, tom daga yau har a tashi taron baki idan har baki sake yin kuka ba ki fadi duk abin da kike so ni Kuma zan miki shi." Mansura dai murmushi ta yi ma Abba ba batace komai ba. Abba Kuma kallanta ya yi ya ce "Muje in rakaki." Abba sai da ya ga shigar Mansura kafin ya juya ya tafi. lokacin da Mansura ta koma Amina ta gama waya da Ahmad kenan. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Ina mamaki waiku salon soyayyartaku ta sirrce ce, yanzu na gama waya da Yaya Ahmad na tambayeshi dan nasan Yaya Abba na fada masa komai nasa, amma ya ce min bai sanar da shi soyayyarku ba. Mansura me ya sa kike boyemin soyayyarku da Yaya Abba? Ko shi ya ce ku boye ne?." Mansura hararar Amina ta yi ta ce "Wai ku anan Katsina haka ake yi ne babu damar a ga mace da Namiji suna magana sai ace soyayya suke, har yaya Ahmad dinma kenan baki yadda da abin da ya ce ba, Allah raina sosai yake baci idan Kuna irin wannan maganar sai inga kamar Kuna banbanta tsakanina dake ne dan da kin daukeni kamar yadda kike fada ba zaki rika hadani da Yaya Abba ba dan kinganmu kawai Muna magana." Amina shiru ta yi dan abinda Mansura ta fada hakane, ya za ai daga sun yi magana ace soyayya suke. Amina ganin ran Mansura ya bace hannunta ta kama ta ce "Yi hakuri Mansura, na yadda Allah tunda Yaya Ahmad ya fada min, nasan da ace Yaya Abba na sonki da ke kanki kafin ya fada miki zai fadama Yaya Ahmad ne, na gamsu Allah." Mansura da Amina sun yi fira kadan kafin duk barci ya kwacesu. Washagari da wuri mai dilkar Amarya ta zo ta yi ma Amarya da kawar Amarya, wadda ta ragu kawayan Amarya da dama suka shafa a fuskokinsu. Bayan Amarya da kawar Amarya sun wanke jikinsu daga nan suka dunguma suka tafi gidan Aunty Zainab da yake acan zasu yi sitin. Suna zuwa wasu daga cikin kawayan suka fara daura girki. Kawayan Amina kusan kaf sun hade ma Mansura Kai duk inda ta yi habaci kusan suke sakar mata. Mansura bata wani fahimci da ita suke ba, hakan ya sa hidimarta take ba ruwanta da kowa sai wata kawar Amina da ta nuna tana sonta. Hakan ya sa Mansura itama ita kadai take kulawa. Ana cikin hakane Amina ta shira cikin wani blue din lass, inda me makeup din ta yi Mata simple makeup. Amina sosai ta yi kyau, haka Yan matan Amaryar suka fara shiryawa daya bayan daya mai makeup na aikinta na gyara duk wadda ta shirya. A haka duk suka shirya, inda Mansura ma ta shirya cikin wata green atamfar anko da suka yi, sosai ta haskata ta yi kyau. Haka

Chapter 9 of 15