ka canza."
Abba ba tare ya kara cewa komai ba ya tafi ya canza kayan daga can ya wuce gidansu Aisha, da yake yasan gidan yana kai mahaifiyarsa in abin Allah ya sa alkairi ya samu ko alakyauta.
Kasan cewar ansan da zuwan Abban ya sa duk wani abu na tarbar bako an tanadar masa shi. Yana zuwa gidan ya Kira Aisha a waya. Aisha na zaune cikin jillimin bakon da mahaifiyarta ta sanar da ita zai zo wajanta yanzu, ta ji ringing din wayarta. Aisha cikin siririyar muryarta ta daga wayar tare da yin sallama.
"Gani a kofar gidanku." Abba ya ce yana mai kashe wayarsa.
Aisha tashi ta yi tana sanye da hijab dinkin bare kyada.
Abba na nan tsaye hankalinsa gaba daya ya tafi a wayar hannunsa, Aisha ta yi masa sallama ta yi.
Abba dago kansa ya yi yana mai zuba mata idanunsa. Aisha kanta kasa ta gaida Abba.
Abba amsa mata ya yi babu yabo babu fallasa. Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Mu shiga falon Daddyna kamar zai fi safe."
Kai Abba ya girgiza ya ce "A'a nanma ya isa." Shiru ya yi kafin ya dora da cewa "Nasan gida an gabatar miki da koni waye tun kafin in zo."
Aisha Kai ta jinjina ma Abba, ta ce "Eh, haka ne,Malama ta fada min komai."
Abba shiru ya yi, kafin ya ce "Ma Sha Allah na ganki mai sunan mommyna, kamar yadda mahaifiyata ta umarce ni. Ya kiba ganni na yi Miki?." Abba ya tambayi Aisha.
Aisha jin tambayar ta yi wani iri, kasa cewa komai ta yi kanta kasa.
Abba, Kiran sunanta ya yi ya ce "Malama baki ban amsa ba kin sidda Kai kasa, dalilin da ya sa na yi miki tambayarne bansan ko kina da Wanda zaki aura ba ake son hadaki dani, kamar ni Kinga ban shirya aure ba, zan ne bisa umarnin mahaifiyata ba bisa son raina ba."
Aisha shiru ta yi tana jin maganganun nasa wasu iri, hakan ya sa ta ce "Ayyah, yayana nima hakane a bangarena, zan yi biyayya da umarnin mahaifiyata ne."
Murmushi Abba ya yi ya ce " Ni a ganina bai kamata mu yi abin da zamu cutar da kanmu ba ki yi tunani, na barki lafiya."
Abba na fadin haka ya ja motarsa ya tafi ya abar Aisha da tunani, dan idan zata fada makanta gaskiya Abba ya yi Mata, dan haka ba ta jin zata iya mujirema bukatar zuciyarta, sanan uwa uba mahaifiyarsa na sonta.
Abba ba shi ya koma gidan ba sai bayan sallar issha'i. Mahaifiyar Abba da fara'arta ta tarbi Abba tana cewa "Babana fira ta yi dadi, da alama dai tare da na Amina za a hada nan da wata uku musha biki."
Abba zama ya yi yana murmushi.
Amina ko da ta kaku ta ji sauran labarin ido ta zaro ta ce "Laa, Yaya Abba aure zai yi mama?." Amina ta ida maganar cikin jin dadi sosai. tana taba Mansura da yake duk suna falon.
Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "Aiko ki fara shirye-shiryan tarbar Auntynki. Oh namanta she bakya gidan kema lokacin za mu mika ki gidan Ahmad." Amina turo baki ta yi.
Mahaifiyar Abba maida kallanta ga Abba ta yi ta ce "Abbana, ya Aishar?."
Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ganin yadda take ta doki da lamarin, cikin danne abin da ke damunsa ya ce "Na ganta Mama, ita ba kyakkyawa ba ita ba mummuna ba."
Mahaifiyar Abba bata fuska ta yi ta ce "Abbana, babu mummuni a musulmi, Kuma kyawun zuciya ya fi na fuska, ni dai yanzu fadamin ya kuka yi da ita?."
Abba ji ya yi bakinsa ya kasa furta kalmar a'a, hakan ya sa ya ce "Mama itama fa yarinyar ta sanar dani tana da Wanda take so."
Mahaifiyar Abba bata fuska ta yi ta ce "Idan tana da Wanda take so kenan shi kenan Kai ma kana da wadda kake so baka sonta, Yes or no?."
Abba kallan mahaifiyarshi ya yi wanda daga gani kiris take jira ta ji ya furta abin da ke ransa ta ci ubansa. Abba cikin jarumta ya ce "Mama, dan Allah ki canza min wata, yarinyar ta cika shiru-shiru, tana magana tana tsugunnar da Kai kamar munafuka."
Mahaifiyar Abba ta dade tana kallan Abba kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce " Kamanta abin da ka ce min jiya ko, ka ce ko baka ganta ba in dai ta yi min to zaka aureta, kenan dadin baki ka yi min, dan haka in dai ka ga baka auri Aisha ba to ban da raine, amma Wallahi tun da bakinka ya furta sai ka aureta, inda har sai da na ji ta bakinka kafin in sanar da mahaifiyarta, dan haka baka isa ba kasa in yi karamar magana ba Wallahi, idan kana da shirin da za ka yima ka shirya dan in sha Allah tare za a hada auran da na Aisha, zan samu baban yara mu yi magana gobe."
Mahaifiyar Abba na kaiwa haka ta tashi tabar ma Abba falon, dan bai taba bata mata rai irin yau ba, tun da ta fara ganin Aisha yarinyar ke burgeta, dan da dama itake masu karin karatu idan mahaifiyarta ba zata zo ba. Sai da Allah zai amsa mata rokanta da ta yi ya naimi kawo Mata matsala.
Abba shiru ya yi ganin mahaifiyarsa ta tafi, dafe kai ya yi yama rasa abin cewa. Mansura da gaba daya itama ba cikin hayyacinta take ba tun da ta ji maganar auran Amina. Tashi ta yi da sauri ta bar falon jin kuka zai kubuce Mata.
Amina Kuma zuwa ta yi ta zauna kusa da yayanta ta ce "Yaya Abba Wai meka faruwa ne tsakaninka da mama?."
Abba kallan Amina ya yi cikin damuwa ya ce "Wata yarinya Mama ta lakaba min in aura, Wallahi Amina kafin in ga yarinyar sai na ji na aminta da zabin mama, Amma Kuma da na ganta sai na ji gaba daya bata yi min ba, shine nake sanar da mama akan ta canza min wata, kin ji dalilin fadan."
Amina cikin damuwa itama ta ce "Amma Yaya Abba meye aibunta, gata da ilimin addini sosai, da dama ma fa ita ke koyar da su Mama."Amina Wallahi na rasa dalili, Amma actual abin da na sani bana so in ga mace ta cika sanyi irin nata haka."
Amina kallan Abba ta yi ta ce "Tom Yaya Abba kana da wadda kake so ne?." A yanzu babu."
Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Yaya Abba indai haka ne ka yi hakuri da zabin mama, idan ba haka ba da alama zaku iya samun saba ni."
Ajiyar zuciya Abba ya soke ya ce "Zan yi ƙoƙarin ganin na koya ma kaina sonta." Yauwa yayana shi ya sa nake yinka da yawa kana da saurin fahimta."
Abba dungure Amina ya yi Yana murmushi ya tashi ya nufi bangaransa.
Amina kwance ta iske Mansura tana kuka, ta tusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka. Amina cikin damuwa ta ce "Mansura wai ke yaushe zaki daina kuka ne? Baki gajiya da kuka ? Shi kenan ba damar ki kasance ke kadai sai kuka. Yanzu yi hakuri dan Allah ki fada min meye?." Mansura dagowa ta yi tana kallan Amina, ta ce "Idan kika yi aure dawa zan zauna, Kuma bansan Ina zani ba, nan da wata uku za ki yi aure ki barni. Wallahi ba zan iya jure abin da ke raina ba babu ke, kashe kaina zan yi in huta, da azabar kuncin da furgicin da nake sha a raye."
Amina da idonta da ya cika da kwalla take kallan Mansura jin kalamanta. Amina ta dade tana kallan Mansura kafin ta ce "Mansura ki huta da kuncin da furgicin da kike sha a raye kika ce, kuma kika furta kalmar za ki kashe kanki, duk da na yi alƙawarin ba zan sake tambayarki akan abin da baki son asani ba, hakan ba zai sa in janye daga gareki ba, dan Allah Mansura ki bar irin kalaman nan, kin manta na yi miki alkawari zan yi ma Yaya Abba magana a d'aga har sai sanda kika samu muji kafin a hada a yi gabadaya?."
Kai Mansura ta girgiza ta ce "A'a ni dai karki fada ma kowa Kar a hada auran, ni Babu wani miji da Allah zai fito min da shi, ni bazan taba yin aure ba.."
Amina rasa abin da zata ce ma Mansura ta yi hakan ya sa ta yi shiru tana lallashin Mansurar, a haka dai har barci ya kwace Amina.
Bangaran gidan su Aisha, mahaifiyar Aisha Koda ta tambayi Aisha yadda suka yi da bakonta, Aisha ba ta gayama mata gaskiyar yadda suka yi da Abba ba, ce ma mahaifiyarta ta yi sun aminta da junansu.
Aisha duk da ba taga alamar Abba zai kirata a waya ba, amma tuk da haka daga wayarta ta yi ringing sai ta dauka ko shine, sai ta duba taka daga akasin hakan. Aisha wayata ta dakko ta tura ma Abba da sako kamar haka. "Ina fatan ka kaje gida lafiya."
Bangaran Abba ko Koda ya ga sakon tsaki ya yi.
Aisha irin matannan ce masu shishshige, hakan ya sa tana jin mahaifiyarta ta ce mahaifiyar Abba ta sanar ba za ta zo Islamiya ba kwana biyu saboda kanwar Abba ta haihu. Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama ni ko Ina son zuwa sunan." Aisha ta fada tana kallan mahaifiyarta ta ji abin da za ta ce.
Mahaifiyar Aisha shiru ta yi, kafin ta ce "Shi kenan bari in sanar da Aishar." Da yake Aisha sunan mahaifiyar Abba gareta.
Mahaifiyar Aisha Kiran mahaifiyar Abba ta yi ta sanar da ita ta Aisha za ta je masu suna.
Mahaifiyar Abba ko da murnarta ta ce "Shi kenan, Zan ba Amina number Aishar sai su tafi tare."
Mahaifiyar Abba bangaransu Amina ta shiga bayan ta gama wayar, zama ta yi tana cewa" Amina, gobe da yaushe ne za ku gidan sunan? Aisha wadda yayanku zai aura tana so za ta je na ce sai ku je tare." Amina ta shi ta yi da murnarta ta ce "Wayyo Mama ban numberta." Amina ta idasa maganar tana dakko wayarta.
Mahaifiyar Amina number Aisha ta sama Amina ta mika mata ta fita. Amina da yake mai son mutane ce take ta doka ma Aisha Kira, sun jima suna waya kafin Amina ta yi mata sallama da sunan sai sun hadu gobe.
Bangaran Aisha Kuma duk wata fargaba dake damunta game da Abba duk sai ta ji babu ita, dan kiran Amina sai ya Kuma tabbatar mata da auranta da Abba kamar yadda take fata. Hakan ya sa take ta dakko wayarta ta fara rubuta ma Abba text message kamar haka. "Assalamu alaikum mosoyin zuciyata, Ina fatan kana cikin koshin lafiya da nishadi."
Abba Koda ya ga sakon Aishar tsaki ya yi ya maida wayarsa ya aje.
Washegari, Amina da wuri ta tashi suka yi shirin tafiya gidan suna. Jin Aisha shiru kiranta ta yi ta sanar Mata sun shirya ita suke jira. Aisha ta ki Kiran Amina ne dama dan ta ga ko sun damu da ita, ana haka ko kiran Amina ya shigo wayarta ta sanar Mata ita suke jira.
Aisha simple makeup ta yi, ta zura hijb dinta doge har kasa tare da nikabi ta rufe fuskarta. Sallama ta yi ma mahaifiyarta dan ta bata address din gidan surukan nata.
Amina suna nan zaune Aisha ta yi sallama ta shigo gidan. Amina da kallo ta bita dan bata gane itace Aishar ba, mahaifiyar Amina da yake tana falon kallan Aisha ta yi tana murmushi ta ce "Amina ga Aishar nan ta karaso.
Amina da gudu ta ruga ta rungume Aisha, a haka suka karaso har falon. Aisha cikin girmamawa ta gaida surukarta.
Amina kallan Mansura ta yi tana mamakin halinta ganin ko inda Aisha take bata kalla ba, Amina dafa Mansura ta ce "Dear mu je ko?." Mansura tashi ta yi suka tafi. Bayan sun fita gidan Aisha ta kalli Mansura ta ce "Ina kwana sister." Lafiya." Mansura ta ce mata ta dauke kai. Amina da mamaki ta kalli Mansura amma Kuma sai ba ta ce mata komai ba.
Napep suka hau har gidan sunan, Aisha da Amina sai firarsu suke Mansura dai ba ta sa masu baki ba. Amina cikin hirarne ta ce "Aunty amaryar yayanmu Abba, ni fa na gaji da kawaici ki bude mana fuska mu ganki."
Murmushi Aisha ta yi ta ce "Ki bari sai mun je gidan sunanko ba a nan a titi ba." Amina bude baki ta yi ta ce "Tom mu da muka sa gyale sai Yaya kenan?." Dariya Aisha ta yi ta ce "Ku kunsaba fita haka, nima na saba fita a haka." Haka dai suka ci gaba da hirarsu har suka Kai gidansunan, ban da Mansura da bata tanka masu ba, dama Kuma ita ba ma'abociyar magana ba ce.
Ko a gidan sunan Mansura fita waje ta yi dan duk sai taji ta takura kasan cewar yawan jama'a da hayaniya, hakan ya sa ta fita waje ta zauna.
A cikin gidan kuma Amina sai naiman Mansura ta ke, Aisha ce ta kalleta ta ce "Anya kuwa ba fita ta yi ba." Wajan suka duba inda suka iske Mansura zaune ta yi tagumi, daga ganinta ta yi nisa sosai a duniyar tunani. Amina dafa Mansura ta yi ta ce "Mansura lafiya kika fito waje kika zauna anata hutuna?."
Mansura dako jajayan idanunta ta yi ta ce "Ni gida Zan tafi."
Amina da mamaki ta ce "Gida Kuma Mansura, baki ga na zo Mana da kayan canzawa ba ? A nan fa zamu kwana." Ni dai gida zan tafi." Mansura ta sake maimaitawa Kamar za ta yi kuka.
Aisha tsugunnawa ta yi ta dafa Mansura ta ce "Sister, dan Allah idan wani abun akai miki ki yi hakuri ya za ayi kun zo suna daniyar kwana Kuma ku tafi gida, ko mama ma in taga Kun koma gida suna baiwatse ba ai ba zata ji dadi ba."
Mansura ture hannun Aisha ta yi dake kan kafadarta ta ce "Da allacan malama ki sakan za ki zo ki kama dafa ni da katsamin hannunki."
Amina da Mansura ta gama kaita bango cikin fushi ta ce "Haba Mansura wai meye kike yi haka ne? Matar da Yaya Abba zai aura kike in gijewa dan ta fada miki gaskiya."
Mansura da babu abin da tasani ban da ririta, yana daya daga cikin abin da ya sa ta saki jiki da Amina har itama take mata kallan masoyiyartace, amma ganin yanzu ta dake tana mata faɗa akan Aisha sai ta ji ranta ya bace har ta fara daukar ko Amina ta gaji da ita ne. Mansura cikin goge hawayan da ya fara zubar Mata ta ce "Na ingijeta din." Amina kama hannun Aisha ta yi suka tafi suka bar Mansura nan tsaye. Mansura fashewa ta yi da kuka. Mansura ta dade tana kuka kafin ta samu napep ta tafi gidansu Amina. Mansura kallan mai napep din ta yi bayan ya sauketa ta ce "Dan Allah ka yi hakuri ban da kudi."
Wani mugun ashar ya mulmulo ya danna ma Mansura ya ce "Wallahi ko ubawan waye ya tsaya miki sai kin ban kudina zaki bar wajan nan."
Mansura da kwatakwata ba ta da wuyar kuka fashewa da kuka ta yi ganin wai yau itace za a rike akan k'ananan kudi. Gashi lokacin duhu ya fara yi ana ta sallar magariba, ana cikin haka sai ga Abba ya dawo Sallah zai shiga gidan. Abba damamaki ya tsaya jin kuka mace shi Kuma Mai napep din ya dage sai cewa yake "Wallahi ko kukan jini za ki yi sai kin biyani kudina, ubanwa ya ce ki hau min keke baki da kudi."
Abba karasawa ya yi wajan ba dan ya san dawa ake fadan ba.
Da mamaki Abba ya bi Mansura da kallo, ta dage sai uban kuka take ci. Abba tsawa ya yi ma mai napep din ya ce "Ba kada da ankali ne da zaka riketa akan k'ananan kudi, sakarta."
Da yake mai napep din irin yan tashar nan ne ya ce " Yo rankashidade aban kudina mana aga in ban saketa ba." Sakarta. "Nawa ne kudin naka?." Dubu biyu ce."
Abba kudin ya ba ma mai napep din, sannan ya kalli Mansura ya ce "Ina Aminar fa?." Tana can." Mansura ta ce tana goge hawayanta. Abba juyawa ya yi ya yi cikin gidan Mansura ta bi shi a baya.
A falon Mahaifiyar Abba Abba ya zauna, kafin ya ce ma Mansura "Me ya sa ke kika dawo?."
Mansura zata yi magana sai kuka, babu irin tambayar da Abba bai yima Mansura ba amma taki Magana sai kuka take. Abba Kiran Amina ya yi a waya tana dagawa ya ce "Amina me aka yi ma yarinyar nan?." Amina na jin haka ta san Mansura yake nufi, cikin jin haushin Mansurar ta ce "Yaya Abba babu fa abinda aka yi mata, ita kawai komai kuka take Mai, matar da za ka aurace fa daga ta yi...." Tsawar da Abba ya yi ma Amina ce ya sa ta yi shiru. Dan yasan wa take nufi an fada mishi tare da Aisha suka tafi.
Abba cikin bacin rai ya ce "Wallahi Koda wasa kika kara hadani da yarinyar nan zaki ga abin da zan mik.." ai ko hadaka da ita yanzu ma ta fara, dan gobe iyayanka za su je naimamaka auranta✍🏻
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
Litafin Abbana na kudi 400 my number 08063830828
P 17-18
Abba cikin bacin rai ya ce "Wallahi Koda wasa kika kara hadani da yarinyar nan zaki ga abinda zan Miki.." ai ko hadaka da ita yanzu ma ta fara, dan gobe iyayanka za suje naimamaka auranta."
Abba shiru ya yi bai tanka, ba daga ƙarshe ya tashi ya koma sight dinsa.
Washegari kamar yadda mahaifiyar Abba ta ce iyayan Abba suka je naiman auran Aisha. Kasan cewar iyayan Aisha manya mutane ne, mahaifinta babban malami ne kusan ansa shi kaf cikin garin Katsina, hakan ya sa aka yi komai kamar yadda addinin musulunci ya tsara.Inda aka sa ranar auran daidai dana Amina sati 11 kenan.
Bayan an kammala komai baba karami ya taho da cingam da biscuit da sweet ya nufi gidansu Abba.
Kasan cewar weekend ne ya sa Abba yana gida, yana falon mahaifiyarsa zaune baba karami ya yi sallama ya shigo rike da kwalayan biscuits a hannunsa, diresu ya yi kafin ya dora da cewa "Aisha ga abin sa ranar nan, munje anyi komai an gama an tsaida lokacin aure daya da na Amina. Amma gaskiya duk mun yi murna ganin inda Abba yaje ya naimi aure, dan gidan shaikh Sani babban gudane, juri'ar gidan duk malamai ne, fatan dai Allah ya nuna Mana ranar lafiya."
Mahaifiyar Abba sun dade suna tataunawa da Baba karami akan auran kafin ya yi mata sallama, ya kalli Abba da bacin gaisawa da suka yi uffan baice ba. Baba karami ya ce "Abba muje sauran kayan na motata ka dakko."
Abba tashi ya yi ya bi Baba karami, suna fita Abba ya kalli baba karami cikin alamun damuwa ya ce "Baba karami, Wallahi ko kadan bana son yarinyar nan da mama ke shirin hadani da ita, tom amma inda aikin gama ya riga ya gama ya zanyi, inda har kun riga kunje, Amma baba dan Allah Ina naiman alfarmar a daga auran nan da wata 5 lokacin na kammala duk wani shiri da zanyi, ka ga shi kanshi wanda zai auri Amina bashi da amini sama dani, dukanmu ba za mu ji dadin hudimarmu ta kasance rana daya ba."
Shiru Baba karami ya yi kafin ya dafa Abba ya ce "Abba ka kwantar da hankalinki ka ji, hakika mahaifiyarka ta zabar maka aure gidan ya ya dace, gidan mutunci, in sha Allah za ka yi alfaharin zama da ita nan gaba, maganar aure Kuma da kake so adaga inda kaine me yi ba za a shiga hakinka ba za a d'aga kamar yadda kanaima, gobe zan je in samu iyayan yarinyar mu yi magana."
Godiya sosai Abba ya yi ma baba karami kafin ya dauki kwalayan ya shiga da su falon mahaifiyar tashi.
Aisha ko lokacin da mahaifiyarta tasanadarmata da sa ranarta da Abba tayi murnar amma fargaba tafi yawa atare da ita, dan tun ranar da Abba ya zo wajanta har yau bai sake dawowa ba, bare Kuma ya kirata. Amina wayarta ta dakko ta tura ma Abba da Sako kamar haka "Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata ga zabin zuciyata. jiya na zo gidanku cike da dokin ganin kyakkyawar fuskarka, sai dai kash lokaci ya rike min Kai baibani damar ganawa da Kai ba, amma banyi fushi ba inda na ga fuskar da ta yi sanadin zuwan taka fuskar duniya. cikim hikimar Allah Kuma a yanzun nan na ji wani daddadan albishir din rayuwa tare da kai na har abadan abidina in sha Allah.
Abba Koda ya gama karanta sakon Aisha tsaki ya yi ya goge text message din.
Mahaifiyar Abba ko sosai ta yi mamaki lokacin da sakon daga ranar auran Abba ya isa gareta, ta nan zaune Abba ya shigo da shirinsa na tafiya aiki.
Abba ganin yadda mahaifiyarsa ta daure fuska kamar ba ta taba dariya ba hakan ya sa ya sha jinin jikinsa, dan Koda ya gaidata ba ta amsa gaisuwarsa ba ta ce "Meye nufinka na daga auran nan da kasa aka yi?."
Abba cikin son mahaifiyar tasa ta fahimce shi ya ce "Mama nifa kadai ne maiyin hidimar nan, duk da baba karami ya ce zai yi ma Aisha kayan daki ba barmai zan yi ba inda hidima yanzu shima ta yi mai yawa, Ina ganin kamar in aka daga din zan fi jin dadin yin tawa hidimar cikin kwanciyar hankali idan ba a hada ba."
Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Hmmmm, Idan ma da wata manufar ka yi ya rage naka, dan ko bayan raina ka fasa auran Aisha ban yafe maka ba."
Abba da mamaki ya dago kansa ya kalli mahaifiyarsa jin murucinta, amma baice komai ba ya yi mata sallama ya tafi.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya babu ranar da Aisha ba za ta tura ma Abba sakon gaisuwa ba, daga ya ga itace ko karantawa ba ya yi yake gogewa.
Mahaifiyar Amina ganin biki sai gabatowa yake har yanzu ba ta ji sun yi maganar anko ba ya sa ta samisu Aminar ta ce "Mansura Wai ba za ku fidda anko bane? Wata daya biki ya rage amma har yanzu ban ji Kuna maganar anko ba? Ko ba za ku yi bane, ga kudin gyaran jiki har na biya mai gyan jikin zata fara zuwa duk abin da za ku yi ku yi kafin a fara gyaran jiki dan daga an fara babu fita."
Mansura duk da take ba ma'abociyar zuwa biki ba tasan ana anko, hakan ya sa ta kalli mahaifiyar Amina ta ce "Mama gobe sai mu je musiyo."
Amina dai ba ta ce komai ba,dan tuni take so ta yi ma Mansura maganar ankon amma Kuma tana tsoran Mansura ta shiga damuwa dan daga anyi maganar bikin take shiga damuwa tunanin zata fara rayuwa babu Amina.
Amina Kuma wayarta ta dakko ta Kira Aisha ta shaida Mata ta zo gobe za su je siyo anko."
Aisha sosai ta yi murnar hakan, dan tana jin dadi duk lokacin da ta ga sun nuna kalawarsu akanta, hakan na rage mata fargabar zama da Abba inda Allah ya bata soyayyar danginsa.
Washegari su Amina suka shirya suka je suka siyo ankon, inda suka zabi lass dinsu me kyau da atamfa. Suna hanyar dawowa ne Aisha ta kalli Amina ta ce "Amina za ku yi walima ne?." Tom Wallahi ban sani ba amma kila mama ta yi." Cewar Amina.
Haka suka ci gaba da hirarsu har aka zo kofar gidansu Aisha ta sauka aka wuce da su Mansura gida.
Tun daga wannan ranar walwalar Mansura ta rage ya zamana kullum cikin damuwa take. Haka nan take
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 15