Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin kamar ba za ta iya rayuwa a gidan babu Amina. Hakan sai ya Kara c maida Mansura shiru-shiru a gidan. Yau mahaifiyar Abba suna zaune kallan Abba ta yi ta ce "Wata daya kenan da kwanakai da sa ranar auranka da Aisha, tun da aka sa ranar ka je wajanta?." Abba Kai ya fara sosawa alamun rashin gaskiya. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi kafin ta ce "Ka shirya ka je yau, idan ka je ka tambayeta nawa ne kudin ankon Amina kabata, Kuma ka kirata ka sanar Mata zuwanka." Abba shiru ya yi baice komai ba ya tashi ya fita. Amina ya Kira ya ce ta zo ta rakashi gidansu Aisha. Amina da dokinta ta bishi suka tafi bayan ta sanar da Mansura zata raka Abba. Abba suna tafiya ya kalli Amina ya ce nawa ne lass din da kuka fidda da atamfa?." Duka 45 thousands." Kai Abba ya jinjina. Suna zuwa kofar gidansu Aisha Abba ya tura ma Amina text message kamar haka "ki fito ga ni a kofar gidanku." Kasan cewar wayar Aisha ba ta kusa da ita hakan ya sa bataga sakon Abba ba. Abba jin shiru-shiru Aisha bata fito ba key ya sa ma motarsa ya juya zai tafi. Amina rike hannun Abba ta yi tana marairaicewa ta ce "Yaya Abba baka kirata Mana." Abba daure fuska ya yi ya ce na tura Mata text tun dazu wayau zata raina ma mutane." Amina Kai ta girgiza tana tunin in ita ce Aisha gara ta fasa auran nan, dan kadan daga cikin rashin son namiji kenan ba zai yi maka uziri ba ko daya, gashi nan ita tun kafin a yi auran ya kasa jurewa akan abin da baikai ya kawo ba. Amina wayarta ta dakko ta Kira Aisha, ba ta daga ba sai da ta sake Kira kafin ta dauka. Amina cikin tausaya ma Aisha ta ce "Mommyna gamu a kofar ginku ni da Yaya Abba." Aisha sai yanzu ta lura da sakon da Abba ya tura Mata. Hijab dinta ta zura har kasa ta fito. Amina kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba dan Allah ka so Mommyna Mana kodan sunan mama da take da shi, Kuma Wallahi tana sonka sosai." Abba daure fuska ya yi, hakan ya sa Amina ta ja bakinta ta yi shiru. Suna a haka Aisha ta fito. Amina rungume Aisha ta yi tana cewa "Mommyna." Dan Amina sosai take jin son Aisha a ranta. Abba Kuma 30k ya ciro ya mika ma Aisha ya ce gashi ki yi manage na ankon Amina." A'a Yaya Abba hidima ta yi yawa dan Allah ka barshi Aisha ta fada cikin jin dadin Abba ya fara sonta. Abba Amina ya mikamawa ya ce "Amina amsa ki Bata." Aisha ganin haka ta dauka ya yi fushi ne dan taki amsa, hakan ya sa ta amsa daga hannun Abban. Abba kallan Amina ya yi ya ce "Shigo mu tafi." Amina shiga ta yi tana jin rashin jin dadin yadda Abba ya yi ma Aisha wanda ita Kuma jin dadi take ganin kamar ya fara sonta. Amina bayan sun taho tana so ta yi ma Abba magana akan abin da ya yi ma Aisha amma Kuma ba ta ga fuska ba, hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru dole, amma sai ya ban halin Aisha take, wanda har ta gama Abba bai tanka mata ba. Bangaran Aisha ko tana rungume da kudin ta je ta nuna ma mahaifiyarta. Mahaifiyar Abba Kai ta jinjina ta ce "Amma kamar yanzu na ga kin fita, Kuma Aisha ina lura yaron nan ko waya bakwayi anya ko mahaifiyarsa ba tursasa mai auranki ta yi ba?." Aisha Kai ta girgiza ta ce "A'a mama muna chat sosai a WhatsApp, yanayin aikinsa ne ya sa kika ga baizuwa." Mahaifiyar Aisha shiru ta yi kafin ta ce "Oh ai ban san kuna chat ba."Mahaifiyar Aisha na fadin haka ta juya ta tafi. Aisha Kuma wayarta ta dakko ta fara rubuta ma Abba sako kamar haka "Habibatina na gode sosai ta kulawarka agareni, zan dade ban manta ba." Abba Koda ya ga sakon tsaki ya yi ya goge text din. Yau mahaifiyar Amina ta dakko Mai gyaran jikin da zata fara yi ma Amina gyaran jiki da Mansura kawar Amarya. Mansura kallan Amina ta yi bayan mahaifiyar Amina ta tafi jin ance har da ita ta ce "Amina dan Allah bana so kima Mama magana." Mai gyaran jikin da keta kallan Mansura ta ce ma Amina "Ni ko kamar na San wannan?." Ta fada tana nuna Mansura. Mansura Kai ta dako a gigice tana kallan mai gyaran jiki, jikinta har ya fara rawa. Amina Kuma da fata lura da halin da Mansura ta shiga ba ta ce "Eh ai haka ne kila maikama da ita kika Sani." Mai gyaran jikin kallan Mansura ta yi ta ce "Ke ko za a yi biki gidanku ki ce ba kyason gyaran jiki, Koda yake kila dan Kinga kina da kyau ne, amma da za ki yi kyanki zai Kara fita sosai. Mansura dai mai gyaran jikin gaba daya ta rudata furta kalmar kamar ta Santa da ta yi, hakan ya sa ba tare da ta ce mata komai ba ta tashi ta fita. Can cikin gidan Mansura ta fi je tana ta kuka, kuka take kamar wadda aka aikoma sakon mutuwar iyayanta. Kuka take tana mai cewa "Allah ka takaita min wannan razanannan rayuwar da nake yi, Allah ka kawo min dauki acikinta, Allah idan har rayuwata ba ta da alkairi cikin jama'a Allah ka dauki rayuwata. Kuka Mansura take yi sosai tana bubbuga kafarta. Abba da cikin barci yake jiyo kukan mace, Wanda har ya yi nasarar tadashi daga dogon barcin da yake yi. Abba dafe Kai ya yi kafin ya tashi ya zauna yana mamakin wake kuka haka. Abba tashi ya yi ya saka jallabiyarsa ya ya zo wajan window sa, da mamaki ya bi Mansura da kallo ganin yadda take kuka, daga gani tana cikin tsananin damuwa da tashin hankali. ga uwar rama da ta yi dama tun da bikin Amina ya gabato kulum cikin damuwar yadda za ta ci gaba da zama gidan ita kadai take yi babu Amina. Abba ya dade yana kallan Mansura da babu alamun zata yi shiru daga kukan da take yi, fita ya yi ya je ya sameta. Abba tsaye ya yi kan Mansura da ko'alamar tsayuwarsa bata ji ba balle ta ji tafiyarsa. Abba tsugunnawa ya yi kusa Mansura yana dago kanta da ta tusa tsakankanin cinyoyinta✍🏻 Fadila Sani Bakori ce. ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Daga Marubuciyar *Fadeela *Meenalyn Daddy *Oga Habib *Abdurrahim *In da rai *Daga Allah ko d'ora ma Kai *So ne sila *Rayuwar Haidar *Bakin kishi Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r Page 19-20 Mansura dago jajayan idanunta ta yi ta saukesu kan Abba, Abba ya dade yana kallan Mansura kafin ya kamo hannunta, Mansura da kallo ta bi Abba, Abba na rike da hannun Mansura har zuwa madaidaicin falonsa ya yi ma Mansura masauki. Kallan Mansura ya yi da har yanzu ba ta fasa share hawayanta ba. Abba kan lover chair din falonta ya nuna ma Mansura da hannu ya ce "Zauna." Mansura zama ta yi tana mai goge hawayanta. Abba zama ya yi gefan Mansura kamo hannuwan Mansura ya yi guda biyu duka ya rike yana kallanta, Wanda Mansura ta sidda kanta kasa tana mai ci gaba da zubba hawayanta. Abba cikin sanyi ya ce "Idan har kina min kallan da Amina take min kin daukeni dan'uwanki tom ki fada min damuwarki?." Mansura kasa ta yi da kanta har yanzu hawayan dake zuba idanunta basu tsaya ba. Abba hannu ya sa ya dako kan Mansura ya ce "Ina jinki fada min me kike yi ma kuka?." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Ina kukan rabuwa da Amina ne, inatunanin yadda zan yi rayuwa ni kadai a gidannan babu ita." Kai Abba ya girgiza ya ce "Karki yi min karya, kukanki bashi da alaka da auran Amina, amma zan iya yadda idan kikace auran Amina ya fama miki raunin dake zuciyarki, dan kukanki ya fi kama da na wanda aka fama ma wani rauni, zuwa yanzu ya kamata ace kin bar mana boye-boye, kin fada Mana gaskiyar abin da ke damunki, ni Kuma na yi miki alkawarin taimakonki akan duk halin da kikeci." Mansura shuru ta yi bata ce komai ba, Kuma ta tsaya da kukan da take yi. Abba jin ta yi shiru tana kallansa, ya ce "Ina jinki, meye damuwarki? Meke yawan saki kukan nan da kike yi?." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Yaya Abba da Ina da wata damuwa da nasar da Amina tuni, saboda bacin Fatima kawata ban taba shaguwa da wani ba adduniya kamar Amina, Yaya Abba da ina da wata damuwa da na sanar da ita." Abba shiru ya yi yana nazarin kalaman Mansura da babu kamshi gaskiya kodaya a cikinsu, amma sai ya shareta ya ce "Ina ita Fatimar take?." Bakaramin tashin hankali Mansura ta shiga ba dalilin wannan tambaya da Abba ya yi Mata, hatta Abba ya fahimci halin da Mansura ta shiga sanadiyar wannan tambaya tashi. Abba ganin ta yi shiru sai hawaye dake ta gudana a fuskarta kamar an bude famfo. Abba cikin sanyi ya Kuma cewa "Ko itama Fatimar ta mutu n..." Abba bai karasa sanadiyar kukan da Mansura ta fashe dashi tana cewa "Wayyo Abbana Fatima, Wayyoo Fatima, ina kike Ina jin kunyarki bana iya hada ido dake wayyo Abbana me ya sa? Me ya sa..?." Abba dai ya zira mata ido yana kallanta yana Kuma jin furucin dake fita daga bakinta. Mansura Kuma zumbur ta yi ta tashi kamar wata zautatta har yanzu tana kiran sunan Fatima. Abba hannun Mansura ya kamo ganin kamar bama cikin hayyacinta take ba, ga uban kuka da take famar rushawa tana Kiran Fatima. Abba hannun Mansura ya rika murzawa yana cewa "Shi kenan ki yi hakuri ya isa haka." Handkerchief dinsa ya ciro ya mika ma Mansura, wadda ta ci kuka harda majina. Mansura kallan handkerchief din ta yi taki amsa. Abba cikin sanyi ya ce "Ki amsa ki goge hawayanki." Mansura amsa ta yi ta gode hawayanta tana jan ajiyar zuciya na irin wanda ya sha kuka sosai. Ana cikin haka ne wayar Abba ta hau ringing. Abba dagawa ya yi yana kanga wayar a kunnansa. Cancikin gidansu Amina, Amina hankalinta tashi ya yi sosai ganin ta duba ko Ina babu Mansura babu alamarta, hakan ya sa Amina ta fara kuka gashi ita kadaice a gidan sai mai yi mata gyaran jiki, Amina ganin kukan ba zai yi mata bane ya sa ta kira Abba ta fada mai bata ga Mansura ba cikin kuka. Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu bata bar share hawayanta ba ya ce "Gata a bangarena ki zo ku tafi tare." Abba na fadin haka ya kashe wayar. Amina Kuma sosai mamaki ya kamata me ya Kai Mansura bangaran Yaya Abba. Abba Kuma bayan ya kashe wayar kallan Mansura ya yi ya ce "Mansura." Mansura da mamaki ta dako tana kallan Abba, dan ganin ba shiga safgarta yake ba ta yi tunanin ma yasan sunanta ba. Mansura cikin sanyi irin muryar Wanda ya gaji da kuka ta ce "Na'am." Kina son Amina?." Abba ya tambayi Mansura yana kallanta. Mansura turo baki ta yi ba ta ba Abba amsa ba. Abba murmushi ya yi kafin ya ce "Yau saura sati daya auran Amina, me za ki bata gudunmuwa?." Mansura kuma turo bakinta ta yi, can ciki ta ce "Ni ai banda kudi." Kai Abba ya jinjina dama amsar da yake so kenan daga bakinta ya ce "Inda baki da kudi yanzu abin da ya kamata ki bata wanda ba zata manta dake ba shine farinciki, farincikin nan ko zaki ba Amina shine ta hanyar kauda duk wata damuwa da ta dameki ki ajeta gefa har ayi baki a gama, saboda Amina tana dariya ne da dariyarki, idan kikace zaki ci gaba da kunci ko kuka Amina ba zata yi hidimar auranta cikin walwala ba, amma idan ta ga kin saki ranki kina mu'amularki kamar yadda kowa yake yi, itama zata gudanar da hidimar auranta ranta sake. Ina fatan zaki min haka? Daga nan har a daura auran Amina ba zaki Kara kuka ba ko wani damuwa d...." Daidai nan Amina ta yi sallama ta shigo cike da mamakin yaushe Yaya Abba da Amina suka Saba haka. Mansura tashi ta yi kafin ta mai da kallanta ga Yaya Abba ta ce "Ba zan sake ba." Mansura na fadin haka ta kama hannun Amina suka tafi, Amina dai da mamaki take kallan Mansura. Cikin sanyi Amina ta ce "Mansura kamar kuka kika yi ko naga idanki da muryarki sun nuna?." Mansura baki ta murguda ma Amina ta ce "Ai na daina." "Allah ya sa da na fi kowa murna." Mansura dai ba ta kula Amina ba. Amina kalan Mansura ta yi ta ce "Wai yaushe kuka fara magana da Yaya Abba ban Sani ba?." Mansura kwashe abin da ya faru ta yi kaf ta fada ma Amina. Mansura zuwa ta yi itama aka shafa mata ragowar hadin dilkar Amarya da ya rage. Tun daga ranar ya zamana Mansura ta fara sakin ranta a gidan, sosai take ƙoƙarin ganin ta kauta duk wata damuwa dake damunta, dan tana so Amina ta yi hidimar bikinta cikin kwanciyar hankali. Hatta mahaifiyar Amina sai da ta lura da sauyin Mansura. Yanzu haka zaune suke an gama yi ma Amina dilka, Amina ta ce "Mansura, na yi shiru na zira miki ido Ina jira in ji kinyi maganar kudin sitin Amma Kuma na ji kin yi shiru." Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Me ye kudin sitin?." Amina da mamaki ta ce "Wai da gaske baki San meye kudin sitin ba?." Wallahi ban Sani ba." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Kila hausarce ta banbanta, ku ya kuke Kiran kudin da ake ba kawayan Amarya na girki ranar daurin aure?." Murmushi Mansura ta yi ta ce "Tun da nake sau daya na taba zuwa bikin aure, ke nifa duk wani abu da kika san za a yi kawai ki min magana ban San komai ba , ya kamata ki fahimta ma." Kai Amina ta jinjina ta ce "Gaskiya na ga alama ai, jiya na yi ma Yaya Ahmad maganar kudin sitin ya ce in yi ma Yaya Abba magana, wai duk abin da muke so mutambayi Yaya Abba, sai da na yi mai maganar ma na tuna ashe muna tare da babban abokin anko. Amma Mansura kinsan ni da kunya in ma Yaya Abba maganar kudin sitin, dan haka yau ko gobe ki yi mai, kin ga yau saura kwana hudu gobe uku ya kamata ce mun amsa musan abin da za mu yi." Mansura ido ta zaro ta ce "Wai ke bakya ganewa ne, Wallahi ban san yadda ake kowata hidima ba ni." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Haka fa kawai zakice mai Yaya Abba kudin sitin Kai muka sani abokin anko, idan kika amshi kadan Kuma kin cika sauran." Mansura ido ta zaro ta ce "Ni dai ki Kira wadda Yaya Abba zai aura mu yi mai magana tare gaskiya, ni Allah ban iya ba." Amina dungure Mansura ta yi ta ce "Kada Allah ya sa ki iyar babu wata mommy da zan yi ma magana wallahi, wai baki iya ba sai ka ce wani abu ake yi, cemaifa kawai za ki yi kudin sitin shi ai ya san maganar." Mansura ganin ran Amina kamar ya fara baci ya sa ta yi shiru, ta amsa za ta yi mai magana. Amina zaune suna hira da Mansura, duk da yawanci hirar Amina take yi, Mansura takan yi ƙoƙarin biye Mata suyi, amma bata taba kawo labari ba ko hira akaran kata, sai dai in an kawo ta yi t comment akai. Yanzu haka zaune suke suna fira Amina ta ce "Mansura kinsan Allah yanda hidimar nan ta gabato Yaya Abba a busy yake, bari in kirasa mu ji yana ina." Amina Kiran Abba ta yi a waya, ta ce "Yaya Abba muna ta tsimayinka shiru?." Amina shiru ta yi da alama dai Abba take saurare, kafin ta ce "A'a, Yaya Abba Mansura ke son magana da Kai." Mansura sai da ta dafe kirji jin Abin da Amina ta ce. Amina katse Kiran ta yi tana kallan Mansura ta ce "Kin ji ko gara da na kirasa, ya ce ki samai a bangaransa." Mansura dafe kirji ta yi ta ce "Ni dai Wallahi kin dora min aiki." Amina hararar Mansura ta yi kafin ta ce "Mansura dan Allah karki amsar Mana kudi kadan." Mansura turo baki ta yi ta ce ma Amina "Nawa to zance?." 200k zaki ce mai haka aka bamu a auran Maryam." Mansura shuru ta yi tana zaune sai aikin turo baki take ita kadai. Amina ganin Mansura ba ta da niyyar tashi ta ce "Mansura dan Allah ki je mana Kar ya fita, Kinga kyau gobe a je ayi cefanan komai." Mansura tashi ta yi tana yafa dankwakin doguwar rigar jikinta ta fita. Mansura bakinta dauke da sallama ta shiga falon Abba, wanda da ke waya da ango. Abba jin sallama katse Kiran ya yi bacin ya sanar dashi zai kirasa. Mansura zama ta yi tana mai gaida Abba, kafin ta dora da cewa "Yaya Abba kudin sitin na zo amsa." Nawa ?." Abba ya tambayeta. "Two hundred thousands." Abba aje wayarshi ya yi yana kallan Mansura ya ce "Dubu dari biyu ku yi me da su?." Mansura turi baki ta yi ta ce "Girkin abincin biki Mana." Kai Abba ya jinjina kafin ya ce "Ban account number zan muku transfer One hundred thousand." Yaya Abba Wallahi ya yi kadan, Amina ta ce bikin kawarta da aka yi ba a dade ba 200 aka basu." Shi kenan zan baku 150." Mansura turo baki ta yi ta ce"Tom Yaya Abba ka cike Mana, Wallahi Amina ta ce Idan bakabada da yawa ba ni zan cika." Abba Kallan Mansura ya yi ya ce "Idan basu isheku ba zan Kara muku, bani account numberki sai in miki transfer din kudin." Ka yi Mana a na Amina bani da account." Okay." Abba ya ce. Mansura Kuma tashi ta yi ta fita, cikin sanyin jiki ta koma wajan Amina saboda Abba bai cika masu kudin ba sunkai 200 kamar yadda Amina ta so. Amina shanjinin jikinta ta yi ganin yadda Mansura ta dawo. Amina kamo hannun Mansura ta yi cikin damuwa ta ce "Kadan ya bamu ko?." Kai Mansura ta daga ta ce "Wallahi na yi na yi ya cika ya Kai 200 ya ki, wai idan basu ishemu ba mu yi mai magana zai Kara Mana." Amina cikin kosawa ta ce "Wai nawa ya bamu." 150, ya ce zai tura a account dinki." Amina rungume Amina ta yi ta ce "Ni Wallahi na sadakar ma, ban sha zai bamu haka ba, yanzu gobe zan Kira Mommy da Hassana ku je ku yi cefanan tare." Mansura baki ta turo ta ce "Kinsan nifa bana son hayaniya, su je su kadai." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Kar ki so hayaniyar Mana Wallahi da ke za a. Kinga nama manta ince miki ki fada ma Yaya Abba gobe shi zai kaiku siyayar, inda mudai shi muka Sani amatsayin abokin anko shi Yaya Ahmad ya nada ya ce duk abinda muke so mu tambayeshi. Kobai nadashi bama dole ya kaimu inda Yaya Ahmad bashi da aboki sama da shi. Nasan halin Yaya Abba idan muka bari sai gobe zai iya cewa ba za shi ba baisan da maganar ba, dan haka bari in kirasa a waya ki fada Mai." Mansura turo baki ta yi ta ce "Ke ki fada mai Mana." Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Ai kawaye ke yin irin haka ba Amarya ba, Kuma ma ai da kunya kamar banda kawaye ace ni zan Kira, Wallahi ke zaki Kira, tsabar mama ma tasan ke ce gaba da komai ya sa ta hada gyaran jiki harda ke a matsayinki na babbar kawar Amarya, Kinga ko komai kawa za ta yi kece nan za ki yi sa." Mansura hararar Amina ta yi ta ce "Anji din." Amina Mika ma Mansura wayarta ta yi ta ce "Amsa na kira." Mansura amsa ta yi tana tura baki. Ringing daya Abba ya daga." Yana cewa dama yanzu zan kiraki in ce ki samin account detail naki." Mansura tura baki ta yi ta ce"Ba fa ita bace." Abba shiru ya yi dan ya gane mai maganar. Mansura ma shirun ta yi, Abba jin shiru-shiru ba ta yi magana ba ya kashe wayarsa. Mansura Mika ma Amina wayar ta ta yi ta ce "Ga shi ya kashe wayar." Amina cikin jin haushi ta ce "Haba Mansura ba dole ya kashe ba, kin yi shiru ki sake kira." Mansura sake Kira ta yi sai da ta kusa katswa Abba ya daga. Mansura kamar yadda Amina ta tsara Mata ta ce "Yaya Abba dama zaka kaimu siyayyane gobe." Abba shiru ya yi, dan sun yi maganar da Ahmad tuni akan shi zai yi jigila dasu akan duk abin da ya kama, sannan Abba ya ce "Ke da wa zaku?." Da mommy da Kuma wata friend din Amina." Ya sunanta?." Abba ya tambaya dan idan har da Aisha ba zai kaisu ba wani zaisa ya kaisu, da yake Abba bai San mommy suke cema Aisha ba. Mansura Kuma ta ba shi amsa da "Hassana." Ajiyar zuciya Abba ya sauke jin ba su ambaci Aisha ba. Ya ce "Da misalin karfe nawa zaku tafi." Da yake wayar a speaker take Amina duk tana jin abin da suke cewa, da hannu ta nunama Mansura. Mansura ta ce" 10:00 AM." Okay Allah ya kaimu bana son shiririta ku shirya da wuri." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa. Amina Kuma take ta tura ma Aisha da Hassana massage akan gobe su zo da wuri 10 za su tafi shiyayya, Yaya Abba ne zai kaisu baya son jira." lokacin Aisha da ta ci karo da sakon Amina sosai ta yi murna jin Abba zai kaisu, take Aisha ta fara shirya kalar kwalliyar da za ta yi tare da tanadan kalmomin masu hikima da basira da za ta yi amfani da su ko Allah zai sa ta ci zuciyar Abba da ya ki. Washegari Aisha da wuri ta tashi, ta samu kankana ta goge fuskarta dashi, sannan ta debo kurkur sokali daya da fulawa itama cokayi daya da Madarar gari itama cokali daya ta fasa danyan kwai tasa kwaiduwar ta hada ta motse kafin ta shafe fuskarta da hannuwanta da hadin. Bayan 30 minute Aisha ta wanke fuskarta da ruwan dimi, kafin ta shiga wanka. Da yake mahaifin Aisha komai yana koya masu hadin gargajiya ne saboda baya so su yi amfani da kwaya ko man bleaching, hakan ya sa yake koya masu hadin islami wajan gyaran jikinsu. Aisha bayan ta fito wanka man kwakwa ta shafe jikinta da fuskarta da shi. Kafin ta dakko wata bakar Abaya ta sa ta tanannane kanta da farin jesi. Wayyo Allah ku zo kuka Aisha yadda ta yi kyau, mahaifiyars Aisha kallan Yar tata taita yi ganin yadda take sheki. Aisha za ta fita mahaifiyarta ta kirata ta ce "Ki kula Wallahi idan mahaifinki ya ganki da gyale babu ruwana. Aisha turo baki ta yi ta ce "Mommy duk inda zamu a mota fa zamu ba a kafa ba." Shi kenan Allah ya tsare." 9:45AM Aisha ta shiga gidansu Abba.,...✍🏻 Abbana sai Monday za ku jini in sha Allah bana yin update ranar weekend, wancan week dinma na yi ne saboda a week din na fara littafin. Fadila Sani Bakori ce ⭐ ABBANA ⭐ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r P 21-22, Aisha koda ta yi sallama falonsu Amina babu kowa, hakan ya sa ta nufi bedroom dinsu Amina kai tsaye. Amina da tashi ta yi tana murmushin ta rungume Aisha ta ce "Oyoyoo Mommyna." Aisha zama ta yi tana kallan Hassana ta ce "Hassana yahaya dama wai kina garinnan." Wadda Aisha ta Kira da Hassana murmushi ta yi ta ce "Ke dai zan ce kina gari." Take hira ta barke tsakaninsu dan sun dau dogan lokaci basu

Chapter 7 of 15