Mahaifiyar Abba Mansura ta bi da kallo, kafin ta ce "Mansura kina so ki bata tarbiyar da nasanki da ita ko? Tom shi kenan babu ruwana idan kin biye ma Abba auransa zai yi kina gani, Kuma kisa a ranki duk yarinyar dake bari Namiji na taba bata wallahi ba auranki zai yi ba, inma Allah ya sa ya aureki ba zai ganki da daraja ba, idan ma tsoro kike dan karya rabu dake kike sake mai jikinki nanma daga ya samu abinda yake so rabuwar zai yi dake."
Mansura dai shiru ta yi kanta kasa bata ce komai ba, mahaifiyar Abba Kuma ta dage sai fada take mata.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, inda yanzu shakuwar Mansura da Abba ta wuce duk yadda kuke tunani, soyayyarsu suke sha sosai abinsu, kullum mahaifiyar Abba daga ta rufe kofa Mansura zata je ta bude ma Abba ya shigo sai asuba zata bude mai ya fita ita Kuma ta rufe kofar falon ta koma ta kwanta.
Sai dai yanzu Mansura cike take da fargaba da tunanin auran Abba da Aisha dan saura sati daya bikin.
Yau Mansura suna kwance da Abba suna babarci ta tashi cikin gigita tana dafe Kai, saboda mafarkin da ta yi.
Abba kallan Mansura ya yi yadda ta yi zufa kamar wadda ta yi gudu, Mansura Kuma fashewa da kuka ta yi tana cewa cikin kuka "Yaya Abba na sake maimai mafarkin rannan, na yi mafarkin ansa min handcuff a hannu gani a gidan yari Kuma Wai ga jariri a hannuna sai kuka yake." Mansura ta idasa maganar cikin kuka tana cewa "Na fara tsoran mafarkin nan na fara razana da abinda nake gani ina tsoro." Mansura ta idasa maganar cikin kuka sosai.
Abba bubbuga bayan Mansura ya yi ya ce "In sha Allah babu abinda zai sameki sai alkairi, ki yi ta addu'a, yaron da kika gani Kuma yaron za ki haifa Mana ne in sha Allah." Kai Mansura ta girgiza ta ce "Ina yawan faduwar gaba Yaya Abba yan kwanan nan a firgice nake, Ina ji kamar wani mugun abu zaisam.." Abba rufe ma Mansura baki ya yi ya ce "Babu abin da zai sameki in sha Allah."
Mansura bata Kuma cewa komai ba, kanta ta dukar tana kuka kadan-kadan.
Abba cikin damuwa ya kalli Mansura ya ce "Mafarki fa ba gaskiya bane."
Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Ko ba haka ba Yaya Abba mun kusa rabuwa za ka yi min nisa zaka koma gidan matarka da kwana, bacin kasa ba min barci tare da kai."
Abba kan Mansura ya shafa ya ce "Shi ya sa na tsaida aikin gidana, ba ayi komai ba, yau dinnan nake shirin sanar da Mama Mommy anan gidan Aisha zata zauna a bangarena kafin na gara gidana, kin ga sai in raba maku kwana, duk ranar kwananki zaki bude min kofar in shigo nan in kwanta haka ya yi miki ai?."
Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Ita Aishar ya za ka ce Mata duk ranar da ba zaka kwana dakinta ba?."
Murmushi Abba ya yi ya ce "Zan fada mata a Asibiti aka maidani haka idan na yi kwana biyu gida kwana biyu a Asibiti."
Mansura dai batace komai ba, Abba Kuma ganin an fara kiraye-kirayan Sallah ya kalli Mansura ya ce "Mu je ki bude min."
Mansura bude ma Abba kofar falon ta yi ya fita ita Kuma ta rufe ta koma ta kwanta.
Yau Abba bayan sun gaisa da mahaifiyarsa ya kalleta ya ce "Mama gobe zansa an yi fenti sabo a bangarena, saboda a nan Mommy zata fara zama, har yanzu aikin gidana ya kasa karasuwa, Wanda na ba kudin aikin gidan ya cinye kudin baiyi koma ba sai jiya da naje na gani."
Shiru mahaifiyar Abba ta yi kafin ta ce "Shi kenan, sai ka yi kokari ka gyara karta jima a nan din." Abba sun jima suna magana akan bikin da mahaifiyarsa kafin ya tafi wajan aiki.
Yau saura kwana uku bikin Abba da Aisha, yau Kuma Amina ta iso garin, zoka ga murna wajan Mansura da Amina kamar za su cinye juna tsabar murna. Mansura na rike da Amina ta saketa ta ruga da gudu zuwa bathroom tana amai.
Amina bin bayan Mansura ta yi tana mata sannu, Mansura daga ma Amina hannu ta yi ta ce "Karki karaso kusa Dani, bana son kamshin turaran da kika sa shi ya sa ni amai."
Amina da ido ta zaro ta ce "Ka ji wani ciwo mai kama da na masu ciki."
Mansura hararar Amina ta yi batace komai ta dauraye bakinta ta fita.
Abba ko bayan ya dawo aiki ya iske Amina ta zo bai yi wani dokin zuwan Amina ba saboda ta toshe duk hanyar zai samu su kebe da Mansurar, Abba akwatin da ya shigo da shi ya Mika ma Mansura ya ce "Gashi kayan da zaki sa na biki akwai angon da su mommy suka yi duka aciki."
Mansura magana take son yi ma Abba amma ganin Amina ya sa ta waske ta ce "Na goge Yaya Abba Allah ya Kara budi." Ameen Abba ya ce ya tashi ya fita.
Bayan Abba ya fita Amina ta bude akwatin amfofi ne da lass a ciki sai bra da panties. Amina ido ta zaro ta ce "Ki ce soyayyarku da Yaya Abba ta yi nisa haka ban Sani ba, Amma soyayar taku Kamar ta yan bariki har da bra da panties, kin San Allah ki dauke bra din nan da panties dinnan ki boye Kar mama ta gansu."
Mansura daukewa ta yi ta bar kayan sawar kawai da handbag da kayan makeup ciki. Koda mahaifiyar Abba ta zo ta gani dadi ta ji sosai ganin yadda Abba ya gwangwaje Mansurar bata kawo komai a ranta ba.
Haka aka ci gaba da shirye-shiryan bikin Aisha da Abba, gidan su Abba ko ya cika da baki, ana gobe bakin da baki Yan nesa duk sun iso.
Ana gobe biki gidansu Aisha suka shirya Walima inda babu yadda Amina bata yi da Mansura dan suje walimar ba Amma taki zuwa, Amina ma lura da kamar Mansurar bata jin dadi ya sa ta rabu da ita.
Washagari aka Daura auran Abba da Aisha, daga ka ga Abba zaka lura da rashin kuzarin da yake ciki.
Bangaran Mansura ko duk hidimar bikin nan da ake Mansura tana yake ne kawai saboda bata jin dadin jikinta kusan kullum da zazzabi take kwana.
Da magariba aka kawo Amarya gidan, inda gidan ya cika da mutane, Wanda duk budirin da ake yi Mansura na kwance ta lillibe kanta hidimar biki ya sa ba Wanda ya lura da halin da Mansura take ciki.
Abba Kuma ya Kira wayarta ya fi a kirga ba ta daga ba dole ya sa ya rabu da ita.
Washagarin kawo Amarya yan uwansu Abba duk suka watse ya zamana daga Amina sai Aunty Zainab, itama ana yin magariba mijinta ya zo ya dauketa ta tafi.
Tun da aka fira hidimar bikin Abba baisa Mansura ba a idansa, gashi ko ya Kira wayarta bata dagawa.
Abba shigowarsa gidan kenan ya iske mahaifiyarsa da Amina sun rako Aunty Zainab. Abba da sauri ya nufi bangaran mahaifiyar tasa har bedroom din Mansura, Kwance ya samu Mansura can karshen gadon bedroom dinta ta gudindine da bargo, Abba cikin damuwa da yadda ya ga Mansurar dan bisa ga alama bata da lafiya ya ce "Mansura." Ya Kira sunanta a hankali yana janye bargonta. Mansura cikin muryar irinta ciwo ta ce "Ni ka rabu dani ka tafi wajan Amaryarka, tun da aka fara bikin nan ka manta dani baka ma san halin da nake ciki ba."
Abba cikin damuwa da yadda ya ji jikin Mansura rau da zazzabi ya ce "Haba baby kulllum sai na kiraki a waya baki dagawa ga gidan cike yake da mutane na rasa yadda zan yi in shigo, dama baki da lafiya baki fada min ba."
Abba ya dago Mansura yana kallanta ta yi mai rama sosai kamar wadda ta dade tana ciwo. Abba cikin mamaki da ganin yadda Mansura ta rame mai ya ce "Subhannallahi, meke damunki kika rame haka?."
Mansura fashe ma Abba da kuka ta yi.
Abba kwantar kan Mansura ya yi kan kafadar yana bata hakuri ya ce "Ki yi hakuri bari in kawo miki magani ki sha." mahaifiyar Abba da Amina jin kukan Mansura suka shigo bedroom din.
Daga mahaifiyar Abba har Amina da kallo suka bi Mansura da Abba, ganin yadda Mansura kusan gaba daya take kwance ajikin Abba tana kuka.
Abba rudewar halin da ya ga Mansura tasa ya bai lura da yadda suke da Mansurar ba ya ce "Amina dama tun da aka fara hidimar bikin nan yarinyar nan bata da lafiya Amma dan iskan ciki baki fadamin ba kika ci gaba da hidimarki bacin ke ke tare da ita, kalli yadda ta rame kwana biyu kawai."
Mansura ko har yanzu tana jikin Abba tana kukanta.
Daga mahaifiyar Abba har Amina sun kasa cewa komai tsabar mamakin yadda suka ga Mansura jikin Abba kwance dukansu ko ajikinsu.....✍🏻
Littafin Abbbana na kudi ne na gama free pages daga yau na gama posting dinsa Mai bukata my number 08063830828
Littafin ABBANA cike yake da cakwakiya, karku manta Abba auran sirri ya yi da Mansura koya zamansu zai kaya.....?
Wacece Mansura.... ?
Shin bakwa ganin mafarkin Mansura zai iya zama gaskiya kuwa ?
Koya zaman Mansura da Aisha zai kaya acikin gidansu Abba a matsayin kishiya da Kishaya.....
Ko waye Wanda Mansura take yawan Kiran Abbana da shi a mafarkinta.....
Duk mai bukatar cikigaban littafin Abbana my number 08063830828
Idan ba siya zaki ba karmu bata ma juna lokaci dan Allah 08063830828
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 15