ga juna ba. Hassana kallan Aisha ta yi da yake Hassana irin masu shegen tambayar nan ne ta ce "Aisha a ina kika san Amina?."
Amina amshe zancan ta yi ta ce "Yaya Abba ya hadamu, Yaya Abba zata aura yanzu haka wata hudu masu zuwa auransu." Hassana Kai ta jinjina ta ce "Ki ce daga yau mu dawo cewa Aunty Aisha mu bar cewa Aisha kaitsaye." Amina kallan Mansura ta yi da har yanzu take kwance bata tashi ba ta ce "Mansura 10:10AM fa dan Allah ki tashi ko wanka fa baki yi ba, yanzu za ki ga Kiran Yaya Abba Wallahi."
Mansura tashi ta yi da sauri ta fada bathroom dinsu. Hassana kallan Amina ta yi ta ce "Amina wannan fa wacece?."
Amina hararar Hassana ta yi ta ce "Wai ke dan Allah yaushe za ki bar wannan halin naki na tambaye-tambaye ne?." Hassana hararar Amina ta yi itama ta ce "Na ji ance tambaya rabin ilimi ce, meye laifin da na yi tambaya akan abin da ban Sani ba."
Cikin jin haushi Amina ta ce ma Hassana "'yar kanwar mama ce."
Amina Kai dubanta ta yi ga wayarta dake ringin tana addu'ar Allah ya sa ba Yaya Abba bane. Amina ido ta zaro ganin Abba ne, gashi tasan babu abin da ya tsana Kamar jira, hakan ya sa Amina na dagawa ta sanar dashi gasu nan fitowa. Amina kallan Aisha ta yi ta ce "Momnyna ku je dan Allah kafin Mansura ta fito idan ba haka ba tafiya zai yi Wallahi."
Aisha kallan Hassana ta yi ta ce "Muje."
Abba na cikin motarsa yana jiran fitowarsu Mansura, su Aisha suka karasa inda ya yi parking.
Aisha gefan Abba ta matsa ta ce "Yaya Abba ina kwana." Abba da farko bai gane Aisha ba sai da ta yi magana dan ta yi mai kyau cikin shigar da ta yi.
Abba babu yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar Aisha da ta Hassana baki daya, yana tsaki tare da dayasanin amsa ma Ahmad da ya yi zai yi jigilar kaisu Mansura duk inda zasu. Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Ku shiga Muje."
Aisha zagayawa ta yi ta zauna a front seat. Abba jan motar ya yi zai tafi Aisha ta ce "Yaya Abba akwai sauran mutun daya." Abba dakatawa ya yi dan dama ya yi mamakin ganin baiga Mansura ba. Shiru-shiru babu Mansura babu alamarta, bunubunu Abba na duba agogon hannunsa, Abba wayarsa ya dauka ya Kira Amina ransa bace tana dauka ya ce "Uban waye drivernku da zaku shanyani ina jiranku?."
Amina hakuri taita ba Abba, Abba ya kashe wayarsa.
Amina Kuma can kallan Mansura ta yi da tasa wata green abaya. Amina cikin jin haushi ta ce "Mansura kina ji fa Yaya Abba ya Kira sai fada yake, amma killi yadda kike shiryawa kamar ba jiranki aike ba."
Mansura kallan Amina ta yi da ta dage sai fada take mata, Mansura turo baki ta yi ta ce "Tom ban ATM cart din naki da pin din."
Mansura da sauri ta fita. Mansura na zuwa Abba ya ja motar gaba daya ransa a bace yake, shi kansa baisan me ya bata mai raiba kawai haka nan ya tsinci kansa cikin bacin rai.
Bayan sun yi dan yi nisa da tafiya kadan, Aisha ta katse shirun da cewa "Hassana Kun ko gaisa da Yaya Abba?." Eh mun gaisa." Aisha cikin son yin magana da Abba ta ce "Ban yadda ba, Yaya Abba wai kun gaisa da Hassana?." Biki ji abin da ta ce bane, ko karya za ta yi miki." Cewar Abba.
Hassana Kuma carab ta amshe ta ce rabu da ita Yaya Abba dan ta tsokaneni ne." Na ga alama." Abba ya ce.
Aisha Kuma turo baki ta yi ta ce "Babu maganar tsokana sanin halinki da na yi ne." Kut, Yaya Abba ka ji wai sanin halina da ta yi ne dan Allah idan a gaban bare ta fadi maganar nan Yaya Abba ba sai a dauka mugun hali garan ba." Abba murmushi ya yi ya ce "A'a babu wanda zai dauke ki haka, ai tunaninka kamanninka." Hassana cikin jin dadi ta ce ma Aisha "Muguwa kinji dai ko."
Aisha murmushi ta yi ta ce "Yaya Abba meye Kuma tunaninka kamanninka, wata irin Hausa ce wannan." Ki tambayi kawarki."
Aisha juyawa ta yi tana kalan Hassana ta ce "Fassara min Hausar Yaya Abba."
Hassana harar Aisha ta yi ta ce sai kin biya." Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba agabanka ake min wulakanci, kana jinta fa wai sai na biya, tom ki rike kalamanki nasan kema ba sani ki kaiba, Yaya Abba zai sanar da ni daga ni sai shi ba za ki ji bama."
Daidai nan Abba ya yi parking ya ce "Mun zo sai ku yi sauri ku sayi abun da za ku siya ko ba a nan zaku yi siyayyar ba?." A'a Yaya Abba a nan ne." Cewar Aisha.
Bude motar suka yi duk suka sauka, Mansura Kuma Mika ma Hassana ATM card din Amina ta yi tare da fata Mata pin din. Hassana da mamaki ta kalli Mansura ta ce "Sister bangane ba kin mikamin ATM card kinki fitowa?." Mansura ya mutsa fuska ta yi ta ce "Sister bana jin dadi kuje dan Allah."
Hassana Kai ta girgiza ta ce "Haba sister kinsan mu mata da kishi Aisha ai ba zata ji dadi ba ta tafi ta barki da wanda zata aura tare." Abba juyowa ya yi yana kallan Hassana ya ce "Inda ta kawo muku uzirinta ku yi hakuri ku tafi Mana."
Shuru duk suka yi sannan Aisha ta kamo hannun Hassana tana murmushi ta ce "Mu je kawata dole mu yi mata uziri inda bata da lafiya."
Suna tafiya Hassana ta kalli Aisha ta ce "Caf dijam, Aisha ki ce kina nan da halin sakarcinki, wannance ta yi kama da mara lafiya, tana sone kawai ta tusa kanta a wajan Yaya Abba ta kwace miki shi, ke baki san yanzu yadda ake tashan kwacan saurayi bane. Baki ji yadda ta yi maganar ba ita aladole ga shagwababba, wai bana jin dadi ne ku je dan Allah. Ke daga jin yadda take magana kinsan makirci ne cike da cikinta."
Aisha shiru ta yi kafin ta ce "A'a inaganin ita fa kamar haka take, yadda na lura da ita kamar bata son shiga hayaniya ne, saboda ranar da muka je gidan suna ma haka tayi, ƙarshe ta tafi ta barmu."Hmmm, ni dai hankalina bai kwanta da yarinyar nan ba." Cewar Hassana.
Hassana duk yadda ta so su yi sauri a cefa nan abun gagara ya yi.
Can bangaran Mansura Kuma suna tafiya ta tusa kanta atsakankanin cinyoyinta. Abba na lura da ita, hakan ya sa ya tashi ya koma inda take, Abba zama ya yi yana dago kan Mansura da ta tusa tsakankanin cinyoyinta. Kallan-kallo suka tsaya yima juna kafin Abba ya sa hannu ya goge ma Mansura hawayan da ke fita a idanunta, Abba cikin nuna damuwarsa ya ce "Ba za ki bar kukanba kenan, ya mu ka yi da ke?."
Mansura fashewa da kuka ta yi tana cewa "Yaya Abba ba fa kuka nake yi ba, nima bansan hawayan na zubarmin ba. Abba bubbuga bayan Mansura yake yi kamar ana lallashin karamin yaro ya ce "Shi kenan na ji ba yadda ba kuka kike ba, ya Isa yanzu ki bar kukan."
Mansura kasa tsaida kukanta ta yi, bisa ga alama ita kadai tasan zafi da kuncin da ke damunta. Abba ganin ya ba Mansura baki ta ki yin shiru hakan ya sa ya ya bude motar zai koma front seat ya rabu da ita.
Mansura rike hannun Abba ta yi ta ce "Na yi shiru Yaya Abba." Ta fada tana jan ajiyar zuciya tana goge hawayanta. Abba gaba daya yama rasa tunanin da zai yi akan Mansura, sun dade shiru kafin Abba ya ce "Daga nan har a yi bikin Aisha idan har kika Kuma yadda na ganki kina kuka tom zan bata da ke bazan sake shiga lamarinki ba inda bakya jin magana."
Mansura tana ƙoƙarin tsaida hawayanta ta ce "Ba zan Kuma ba Yaya Abba." Yauwa yar Albarka." Cewar Abba yana Kuma share ma Mansura hawayanta. Ganin ta bar kukan ya ce "Kina so in Samar miki teaching a school din da Amina ke yi? Kin ga bayan bikin Amina kin huta zama gida ke kadai inda Mama kullum tana Islamiya."
Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai Yaya Abba bana so, ni ba zan iya hayaniyar yara ba." Abba shiru ya yi yana kallan Mansura kafin ya ce "Tom in mai da ke school sai ki ci gaba da karatunki?." Nan ma dai Mansura Kai ta girgiza ma Abba alamun bata so. Abba kallan Mansura ya yi kafin ya ce "Tom fada min me kike so? Ina son in Samar miki wani abin ne wanda zai hanaki zaman gida baki daya." Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai Yaya Abba bana son komai, ni gara in ta zaman gidan ma." Abba da mamaki ya kalli Mansura ya ce "A'a, idan baki son komai sai mu yi Miki aure shi kenan."
Mansura rufe idanunta ta yi kafin ta dago tana kallan Abba ta ce "Tom wa za ku aura min ni da bani da saurayi?." Ni da nake da abokai da yawa, baki ga Mansura bama cikin abokaina zata auri wani, ciki zan samo in aura miki kema."
Mansura bata fuska ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai Yaya Abba bana son kowa, ni ba zan yi aure ba." Ai ko sai kin yi aure, akwai wani abokina ma ina jin zanma Mama magana bayan bikin Amina kema a yi naki." Take Mansura ta fashe ma Abba da kuka dan ta yi tunanin da gaske yake. Abba ido ya zaro yana cewa "Ke ni wasa nake miki aike ba za ki yi aure ba ai na sani duk wanda ya zo ya ce ma yana sonki sai na mishi kus'a." Abba ya fada Yana nushin Mansura a hankali a fuska yana gwada mata yadda zai yi ma duk wanda ya ce yana sonta.
Abin mamaki sai ga Mansura tana dariya... Daidai nan su Aisha suka dawo, da mai baro da ya dakko masu kayan siyayyar da suka yi. Hassana nocking ta yi ma Abba ganin bai kula dasu ba hankalinsa na kan Mansura dake dariyar kus'a din da zai ma wa inda suka ce suna sonta.
Abba fita ya yi yana kallan Hassana ya ce "Sanninku da dawowa." Hassana kallan Aisha ta yi irin kallan gingani ko ai abin da nake ce miki kenan.
Aisha dai ba ta ce komai ba, amma bisa alama ranta ya bace yana yin fuskarta ya sauya.
Abba bude boot din motarsa ya yi mai baron ya loda siyayyar da suka yi a ciki.
Aisha jikinta gaba daya yayi sanyi a haka ta zagaya ta koma wajanta ta zauna.
Abba har ya isa gida babu wanda ya yi magana a motar. Abba bayan ya yi parking umartarsu ya yi da su shiga da duk abin da suka siyo cikin gida. Gaba daya dauka suka yi inda duk suka dauki manya ledoji ban da Mansura da ta dauki 'yar Karama, har ta juya za ta bi su Aisha Abba ya kirata ya ce "Wannan Yar ledar zaki dauka? Zo ga wata in dora miki."
Abba amsar ledar da Mansura ta dauka ya yi ya dora mata wata babbar leda akai. Yana dora mata Mansura ta durkushe har kasa tana turo baki ta ce "Yaya Abba ya fa yi min nauyi Wallahi ban iya tashi."
Abba Kai ya girgiza ya ce "Wa'inna yan kayan ne za su yi miki nauyi, maza ki tashi Wallahi bana son ragonta." Mansura Kuma turo baki ta yi tana durkushe da ledar akanta ta ce "Allah Yaya Abba sun min nauyi." Allah karya ne ba su yi miki nauyi ba." Abba ya fada yana Mika Mata hannunsa ya ce "Kama ki Mike." Mansura kama hannun Abba ta yi ta miki daga durkusan da take.
Bangaransu Aisha ko, suna tafiya Hassana ta ce "Kinga ni ai abinda nake fadamiki, dazu daga gani dama ni nasan lafiyarta Lau, amma ke kika naimi ki kareta wai bata son hayaniya. yanzu gata can tsaye ai suna fira a gabanki ko kunyarki ma bata ji ba."
Fadin gata can din da Hassana ta yi ya sa Aisha juyawa, Hassana ma ganin waigawar ta yi daidai nan Mansura ta rike hannun Abba ta tashi daga durkusan da take, ta yi taga-taga zata fadi Abba ya riketa ya na mata dariya.
Da sauri Aisha ta juyo, take taji wani irin bakin ciki da tsanar Mansura aranta.
Hassana Kuma ta ci gaba da cewa "Wallahi tun kafin lokaci ya kure miki ki sanadar da Amina abin da ke faruwa na kwacan da yarinyar nan ke shirin miki ta take Mata burki.
Aisha dai bata ce komai ba hassalima Kara saurinta ta yi.
Suna shiga da gudu Aisha ta yi sight din Amina jin kukan dake ƙoƙarin kufce Mata. Mahaifiyarsu Amina dake falon da mamaki ta bi Aisha da kallo tana kallan Hassana ta ce "Hassana lafiya me ya samu Aisha haka ta shigo tana kuka." Mahaifiyar Amina ta yi tambayar cikin damuwa."
Hassana cikin tsantsar nuna damuwa ga lamarin ta ce "Gaskiya mama akwai damuwa." Hassana ta fada tana shigewa bedroom din Amina ta bar Mahaifiyar Amina sake da baki.
Can Kuma Aisha na shiga ta fada bed din da Amina take zaune tana chatting ta fashe da kuka. Amina cikin tashin hankali ta wurgar da wayar hannunta tana kamo Aisha ta ce "Mommyna lafiya ya aka yi ke da wa?." Aisha shiru ba amsa sai kuka da take yi.
Amina kallan Hassana ta yi dake tsaye tana kallan Aisha. Amina cikin damuwa ta maida kallanta ga Hassana ta ce "Hassana wai lafiya? Ya aka yi ne ?." Hmmmm." Hassana ta ce ta zauna.
Ana haka ne mahaifiyar Amina ma tashi dakin da saurinta jin sautin kukan Aisha.
Mahaifiyar Amina ganin ba ta ga Mansura ba ya sa ta ce "Ina Mansurar, ko wani abun ne ya s..." Mahaifiyar Amina shiru ta yi jin sallamar Mansura. Mansura da mamaki ta bi Aisha dake kuka da kallo. Mahaifiyar Amina Kuma cikin damuwa ta maida kallanta ga Mansura da ta shigo yanzu ta ce "Mansura wai lafiya ya aka yi ne? Me ya samu Aisha take kuka ne?." Mansura cikin mamaki ta ce "Wallahi mama ban Sani ba, nima tambayar da zan yi kenan."
Mahaifiyar Amina da mamaki ta ce "Batare kuke bane?." Tare muke." Cewar Mansura.
Hassana Kuma dagowa ta yi tana hararar Mansura ta ce "Eh gaskiya fa dole kice baki Sani ba bacin kin manta snatching din saurayi."
Mahaifiyar Amina damamaki ta kalli Hassana ta ce "Kamar ya bangane ba Hassana?."
Mama Mansura soyayya suke da Yaya Abba."
Mahaifiyar Abba da tsananin mamaki ta ke "Wana Yaya Abban?." Mama yaya Abban na gidan nan mana..✍🏻
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 23-24
Mahaifiyar Abba cikin tsananin mamaki ta ce "Wana Yaya Abban?." Mama yaya Abba na gidan nan mana." Cewar Hassana.
Mansura ko tsabar al'ajabi shiru ta yi tarasa bakin magana, tana mamakin shairin da suka kulla Mata.
Mahaifiyar Abba rasa abin da zata ce ta yi dan ita ko magana banda ranar da Mansura ta zo gidan ba ta taba ganin ta hada Mansura da Abba ba, hasalima in ba yanzu ba Abba ba son zaman Mansura a gidan yake ba. Mahaifiyar Amina mai da kallanta ga Hassana ta yi ta ce "Tom waiku me kuka gani da za ku ce haka? Sannan yanzu meye dalikin kukan nata?."
Hassana da ta rasa abin da zatace dan duk surutun Hassana bata da fiye karya ba hakan ya sa ta ce "Mama ki dai tambayi Aishar da bakinta ta fada miki." Mahaifiyar Amina hannun Aisha ta gama ta ce "Tashi mu je ki fada min in ji." Mahaifiyar Amina na rike da hannun Aisha har bedroom dinta, zaunar da ita ta yi kan one hand char din dake bedroom dinta, itama ta zauna, goge ma Aisha hawayanta ta fara yi kafin cikin taushin murya ta ce "Shi kenan kukan ya Isa haka nan, fada min shi Abban ne ya ce miki yana son Mansura?." Kai Aisha ta girgiza.
Shiru mahaifiyar Amina ta yi kafin ta ce " Aisha ki natsu ki sanar dani kin ji zan yi maganin koma meye, Abba bai isa ba ko bayan raina ya wulakantaki ba bare Kuma da raina, fada min ya aka yi?."
Aisha rasa abin da zata ce ma mahaifiyar Abba ta yi, hakan ya sa ta ce "Mama dan Allah ki tambayi Hassana tasan komai Kuma agabanta komai ya faru." Mahaifiyar Amina wayar Amina ta Kira ta ce ta turo mata Hassana.
Hassana koda ta fito falon ba ta ga Mahaifiyar Amina ba, bedroom din mahaifiyar Amina ta shiga da sallamarta.
Mahaifiyar Amina waje ta nuna ma Hassana ta ce "Zauna." Bayan ta zauna mahaifiyar Amina ta ce "Hassana na tambayi Aisha ta ce in tambayeki agabanki komai ya faru, Ina jinki fadamin meya faru bayan tafiyarku?
Hassana Kara gyara zama ta yi kafin ta ce "Mama Kinga Koda muka tafi muka je zamu kasuwa siyayya Mansura kin fita daga motar Yaya Abba ta yi wai bata jin dadi, amma da muka dawo muka iskesu waje daya da Yaya Abba sai fira suke har tana dariya. Yanzu Kuma bayan mun dawo Yaya Abba ya ce mu shigo da kayan da muka dawo dasu, duk maka dako muka taho ita Kuma har ta taho Yaya Abba ya kirata wai ta dawo ta dauki Abba, Wallahi mama Koda muka juyo abinda Aisha ta gani shi ya sata kuka."
Mahaifiyar Amina cikin sanyi ta ce "Me kuka gani da kuka jiyo din." Gani muka yi Yaya Abba yana rike da hannunta suna magana suna dariya."
Ajiyar azuciya mahaifiyar Amina ta sauke. Shiru ta yi dan ta rasa abinda zata ce, sai zuwa can ta ce "Ki kwantar da hankalinki kin ji yayata, Abba bashi da Mata saike, Mansura Kuma duk abin da kika gani ya faru tsakaninta da Abba ki dauka kamar da Amina kika gani, dan Abba kallan kanwa yake Mata, Kar ki kuma sakanki damuwa indai akan haka ne Abba ba soyayya suke da Mansura ba kamar yadda kuka zarga."
Aisha sosai ta gamsu da kalaman surukartata, hakan ya sa ce "Tom Mommy nagode Kuma in sha Allah ba zan sake sa kaina damuwa akan hakan ba." Yauwa 'yar Albarka Allah ya yi Miki albarka." Ameen Aisha ta ce kafin suka fita suka bar Mahaifiyar Abba dariyarsu, suna fita Abba yana shigowa dan har saida suka matsa mai ma. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama Wana albishir din akai miki ne naga kina dariya." Hmmm Abba dole in yi dariya, Aisha ta zo ta dagamin hankali tana kuka wai soyaya kake da Mansura, Koda na tambayi ba asin maganar tasu duk kame-kame ce, daga ji dai kishi take na magana da Mansura da ka yi."
Abba daure fuska ya yi ya ce "Lallai Kam aiki ya sameta." Mahaifiyar Abba gimtse dariyarta ta yi ta ce "Bana son shirme kamar ya aiki ya sameta? Kenan yanzu ka fara magana da Yan Mata a gabanta? Ko me kake nufi?." Abba kai ya girgiza ya ce "Kodaya ba haka nake nufi ba, Amma mama indai dan taga Ina magana da yarinyar can ne ai abin yaban mamaki, tom wata magana muka yi da har zai sa ta ce Haka." Kai rabu dasu shirmansu ne kawai. Dama Abba ina ta so in maka wata magana sai in mata, ka ga dai anci wata kusan biyu kenan da sa ranarka da Aisha, Kuma ni har yanzu banji wata magana da ka yi ba ta shirin biki da kake yi, ko maganar gininka ma ban ji kana maganar karasashi ba."
Abba Kai ya sosa ya ce "Ko jiya mun yi magana da masu aikin, Ina so sai mun gama hidimar bikin nan ne kafin in dora aikin ba tsayawa." Tom Allah ya taimaka." Ameen." Abba ya ce. Sun dade suna tattaunawa da mahaifiyarsa kafin ya fita.
Can bangaran su Amina ko bayan Mahaifiyar Amina ta Kira Hassana, ya rake daga Amina sai Mansura a dakin. Amina kallan Mansura ta yi cikin sanyi ta ce "Mansura wai meke faruwa ne?." Mansura fara goge hawayan da ya zibo Mata ta yi ta ce "Wallahi nima ban Sani ba, da na shigo ne na iske Mommy tana kuka, har zan tambayi lafiya na ji friend dinki na cewa wai na yi ma Mommy snatching din saurayi, wai Ina soyayya da Yaya Abba."
Amina shiru ta yi ta rasa abin cewa, kafin ta ce "Tom yanzu Kuma meye abin kuka anan, ni abinda nake so in Sani me ya faru a tafiyar takune."
Mansura kwashe duk abin da ya faru ta yi ta fada ma Amina. Amina shiru ta yi ta ce "Ki yi hakuri Mansura dan Allah karki dauki aka a matsayin wani abu nasan watarana zaki fahimci halin da Aisha ta shiga dazu, son Yaya Abba take sosai tattare da tsananin kishi akansa, shi yasa ta ji haushin barinku tare gani take Kun yi wata maganar ne, kinsan masoyi yana da zargi." Amina dai har ta gama maganarta Mansura bata ce komai ba. Suna ana haka Hassana da Aisha suka shigo. Shiru babu Wanda ya ce ma kowa komai, Amina ce ta katse shirun da cewa "Hassana Kun gama shigo da kayan ne?." Kai Hassana ta girgiza "Shi kenan ku bari na samu wani yaran ya shigo dasu."
Aisha tashi ta yi tana kallan Amina ta ce "Amina zan tafi sai Kuma ranar daurin aure." Amina marairaice fuska ta yi ta ce "Na zaci kullum zaku rika zuwa nan mu wuni tare dan Allah."
Aisha dai bata ce komai ba murmushi ta yi ta tafi. Hassana ma tashi ta yi ta ce "Nima ai tafiya zan yi jirani." Hassana tashi ta yi suka tafi tare da Aisha. Amina tashi ta yi ta rakasu har wajan get dinsu, bayan sun fitone Amina ta kalli Aisha ta ce "Mommy dan Allah ki yi hakuri abinda ya faru, amma a ainihin sanina Yaya Abba ko magana ba hadasu da Mansura, dan Allah ki yi hakuri zan mata magana." Aisha murmushi ta yi ma Mansura ta ce "Ayyah babu komai ya wuce ai."
Bayan sun Hassana sun tafi Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha kinsan Allah ki ci gaba da sa ido akan yarinyar nan, dan ni ban yadda basa soyayya da Yaya Abba, na fi tunanin dai ko su ne Basu son suna soyayyar ba."
Aisha dai ba ta ce komai, ta yi ma Hassana sallama ta tari Napep ta hau. Aisha ta tafi babu jimawa mahaifiyarta ta zo gidansu Amina.
Mahaifiyar Amina da fara'arta ta tari malamarta, bayan sun gaggaisa Mahaifiyar Amina take sanar da mahaifiyar Aisha, Aisha ma yanzu suka tafi babu jimawa.
Malama kallan mahaifiyar Amina ta yi ta ce "Tun jiya nake cewa zanzo Allah bai yi ba, dama na zo in sanar dake ne na shirya Walima da za mu yi ta bikin Amina a gidan nan, shi ne na ce yaushe za a yi gobe ko sai ana gobe darin aure?."
Mahaifiyar Amina da murnarta ta ce "Kai Malama, wannan babar hidima haka, tom angode Allah ya saka da alkairi, a bari a yi jibi ana gobe biki kenan." Shi kenan Allah ya kaimu.
Malama sun dade suna fira da mahaifiyar Amina kafin ta yi mata sallama ta tafi.
Mansura ranar gaba daya haka ta wuni babu dadi dan tashiga damuwar abin da su Aisha suka yi Mata, ta dauki hakan kamar cikin mutunci ne.
Washagari Abokan Ahmad suka kawo lefan Amina.
'Yan'uwansu Amina da dama duk sun zo, hakan ya sa gidan yanzu ya fara cika, dole ya sa Abba ya bar masu bangaransa ya koma dakin abokinsa da kwana.
Bangaran mahaifiyar Aisha Kuma tana ta shirin shirya masu walimar da za ta yi ta a bikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 15