Sallah itama. Amina zama ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Mama, zazzabin mansura ya dawo, ashe tun dazu tana kwance."
Mahaifiyar Amina bayan ta shafa addu'arta kallan Amina ta yi cikin fara damuwa da lamarin Mansurar ta ce "Amina, Wallahi na fara damuwa da matsalolin yarinyar nan, ace baka da lafiya ka ce Kuma ba za ka sha magani ba Kuma ba za a yi maka Allura ba, to ya take so a yi da ita. Daga ganinta ma dai irin shagwababbun yaran nan ce."
Mansura turo baki ta yi jin mahaifiyarta kamar tana naiman kushe kawartata ta ce "Mama, magani fa ba shi da dadi." Tom ai shi kenan, sai ta zauna ta warke a haka."
Amina ta san halin mahaifiyarta ko itace ta ce ba zata sha magani ba babin takanta za ta yi ba, hakan ya sa ta tashi bata Kara cewa komai ba ta fita."
Bangaran Abba yau da wuri ya dawo gidan, dan yana gidan ma aka yi sallar magariba, bayan ya dawo daka masallaci ya shiga bangaran mahaifiyarsa, ganin bata a falon hakan ya sa ya nufi bedroom dinta.
Zaune ya isketa tana duba majama'ul baharaini. Mahaifiyar Abba na ganin Abba ta rufe littafin, tana murmushi ta ce "Abbana yau 'yar wuri ce kenan?." Eh mama Ina nan ma aka yi Magriba, fatan Kuna lafiya, ya masu jegon."Suna lafiya Lau, ta fada maka kenan." Eh mama mun yi waya."
Abba kallan wayarshi ya yi dake ringing, dagawa ya yi yana kanga wayar a kunne, ban ji mai aka ce ba na ji ya ce "okay gani a gidan ma." Yana fadin haka ya kashe wayarsa.
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce"Lafiya?." Amina ce ta kirani wai zazzabin yarinyar nan ya dawo."
Mahaifiyar Amina cikin takaicin rashin son maganin Mansura ta ce "Ba dole zazzabi ya dawo ba, maganin da ka bata fa in Banda Wanda na bata ta amayar dashi, daga shi ko daya ba ta kara sha ba, to taya zazzabi ba zai dawo ba."
Abba Kai ya jinjina ya ce "Mama ko daya kika ce bata sha maganin ba?." Wallahi Abba, ga zazzabin nan ma ya dawo."
Abba baice komai ba tashi ya yi ya nufi bedroom din su Amina.
Amina na nan zaune ta yi tagumi ta sa Mansura gaba tana kallo, cikin tsananin tausayi, Abba ya yi sallama ya shiga. Kallan Amina ya yi ya ce "Ina laidar magungunan?." Amina dakko ledar ta yi ta mika ma Abba.
Abba sosai ya yi mamakin ganin magungunan suna nan yadda suke. Kallan Amina ya yi ya ce "Me ya sa ba ta sha ba?."
Amina yadda Abba yake mata magana ya sa ta fahimci tuhumarta yake na rashin shan maganin Mansura, bi ma'ana dai tana da laifi.
Abba jin ta yi shiru ya Kuma cewa, "Ba da ke nake magana ba, na ce me ya sa ba ta sha ba?." Yaya Abba, ita ce bata sha ba."
Abba zama ya yi gefan gadon da Mansurar take ya ce ma Amina kawo min ruwa."
Amina da sauri ta je ta kawo ma Abba ruwan. Abba bare magungunan ya yi sannan ya umarci Mansura da ta tashi.
Mansura ta shi ta yi ta zauna tana mai kara kudindine jikinta da bargon, saboda sanyin da take ji.
Abba mika mata maganin hannunshi ya yi da ruwan ya ce "Amsa ki sha."
Mansura kallan Abba ta yi, irin kallan ka tausaya min. Abba babu alamar wasa tare dashi ya Kuma maimata "Amsa ki sha na ce."
Mansura amsa ta yi tana goge hawayanta. Abba ruwan ya mika Mata ya ce "Watsa duka maganin a bakinki."
Mansura watsa duka maganin ta yi, take ta fara kararin amai zata dawo da maganin. Abba tashi ya yi ya daga kanta ya kalli sama, sannan ya amshi ruwan ya tsiyaya mata a baki. Ya ce "Hadiye shi." Ya fadi maganar yana girgiza kanta. Mansura hadiyewa ta yi ba ta shirya ba.
Abba sai da ya tabbatar ta hadiye kafin ya saki kanta.
Mansura nishi ta fara irin na yaran da akai ma dure.
Abba ruwan Allurar ya hada ya kamo hannun Mansura, take hannun Mansura ya kama rawa. Abba Amina ya sa ta rike mai hannun Mansura ya yi Mata allurar, take Mansura ta kama kuka. Amina murza mata hannun ta kama tana cewa "Sannu dear, yi hakuri."
Abba maganin ya mika ma Amina ya ce "Gashi Allah ya sa lokacin shan maganin ya kara yi bata Sha ba, dukkanku ku biyun za ku yi min bayanin dalilin da ba ta sha ba."
Abba na fahin haka ya fita. Wajan mahaifiyarshi ya koma suna fira. Mahaifiyar Abba cikin hirar tasu neka ta ce "Abba Kai kadai ne dana Namiji da nake kalla in ji dadi, kana min duk abin da na ce, sai dai har yanzu ka kasa cika muradina daya tal aduniya. Ba ni da burin da ya wuce Abba kamar in ga ka yi aure, sai yaushe ne za ka yi aure Abba? Yaushe za ka cika burina da na mahaifinka da har ya bar duniya bashi da buri kamar ya ga auranka, tom Allah bai nufa ba, baka yi ba, gashi har yana gaf da cika shekara biyar, har yanzu shiru babu ma wata alamar da kake nuna wa za ka yi aure."
Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Ki yi hakuri mama har yanzu ban samu wadda ta kwanta min bane."
Shiru mahaifiyar Abba ta yi tana nazarin maganar da za ta fada ma Abba. Ta jima kafin ta ce "Abbana na yi maka matar aure wadda nake fatan in sha Allah ba za ka yi danasanin zama da yarinyar ba a yadda na fahimceta."
Abba kallan mahaifiyarshi ya yi cikin rauni, dan duk ba ya jin zabin mahaifiyar tashi zai mai Amma Kuma duk da haka baya jin zai iya bijire ma umarninta. Hakan ya sa ya ce "Mama tun kafin in ganta na aminta da zabin naki." Ma Sha Allah , Allah ya yi maka albarka Abbana, da Alama dai ka gaji mai sunan naka, ba kowa bace na zaba, yarinyar ..... ✍🏻
Fadila Sani Bakori ce.
⭐ABBANA⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Damin samun littafin ABBANA daga faro Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 13-14
Malamarmu Aisha na zaba, yanzu haka maganar da nake yi maka har na yi ma mahaifiyarta magana ma, kuma ta amsa min ta ce ka je ka ganta. Sanin ba za ka yi min musu ba ya sa sai da na fara sanar da mahaifiyarta kafin Kai."
Abba Kai ya daga yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama, in dai ta yi miki Allah ko ban ganta ba ya wadatar, amma duk da haka ki ban address din gidan nasu zan je har gidan."
Mahaifiyar Abba sosai ta ji dadin yadda dan nata ya aminta da zabin ta cikin sauki. Cikin jin dadi mahaifiyar Abba taita zindimo masa albarka tana cewa "Abbana, in sha Allah za ka yi alfahari da wannan zabin nawa. Allah ya yi maka albarka, Allah ya baka duk abin da kake nema duniya da kuma lahira, Allah ya jikan mahaifinka, ya saka masa da alkairi bisa kyakkywar turbar da ya dora min Kai."
Abba sosai ya ji dadin addu'ar mahaifiyar tasa, hakan ya sa cikin jin dadi ya ce "Ameen mamana."
Abba sun jima suna hira da mahaifiyarsa kafin ya yi mata sallama ya koma sight dinsa.
Washegari, Amina da wuri ta tashi ta yi duk abin da za ta yi kafin ta fita. Kallan Mansura ta yi dake ta tsattsakar indomie dake gabanta. Amina dakko maganin Mansura ta yi ta mika mata ta ce "Dear ga maganinki kisha."
Mansura baki ta turo ta ce "Allah bakina fa har ya fara dacin magungunan nan, ni dai gaskiya ba zan sha ba." Amina ido ta zaro ta ce "Ba za ki shaba, baki ji abin da Yaya Abba ya ce ba ne jiya, ni dai dan Allah ki rufa min asiri ki Sha, Wallahi ya zo ya ga baki sha ba har nima ba gyaleni zai yi ba, kina ji dai a gabanki ya ce in mun isa karki Sha, ni dai ki rufa min asiri ki dauka ki sha."
Mansura hannun Amina ta kamo, kamar za ta yi kuka ta ce,"Amina, zan fa babbare sai in zubar kin ga ai ba zai gane ban Sha ba" Uhmmm, Wallahi babu ruwana, idan fa zazzabin ya dawo miki? Yaya Abba da shegan bin diddigi in je ya gano ya ci ubana kila gara ma ke yana ganin bakuwace ya rabu da ke."
Amina kamar za ta yi kuka ta ce "Yanzu ba zaki tausaya min ba?."
Amina ma cikin son fahimtar da Mansura ta ce "Mansura ke ba ki san halin yaya Abba bane, ni dai kawai ki sha dan Allah."
Mansura Kuma kallan Amina ta yi kwalla na taruwar mata ta ce "Amai fa nake ji." Mansura ki sha in Allah ya yadda ba zaki yi ba." Mansura rufe idonta ta yi ta watsa maganin bakinta ta bi da ruwa da sauri."
Yunkurin amai ta fara, Amina da sauri ta fara bubbuga bayanta. Suna a haka Abba ya shigo yi mata allurarta.
Amina gaida Abba ta yi tana mai ci gaba da bubbuga bayan Mansura da har yanzu dafe take da kirji ba ta daina yunkurin amai ba.
Abba kallan Amina ya yi ya ce "Lafiya me ya sa ta yunkurin amana." Yaya Abba daga shan magani." Abba wata farar kwaya ya ciro a ajjihunsa ya mika ma Amina ya ca bata ta tsotsa."
Amina mika ma Mansura ta yi, Mansura ganin magani ne yi ta yi kamar ta je fashi a bakinta taki sha, ta rufeshi a hannunta.
Abba ledar magungunan Abba ya dakko ya hada allurar, Mansura take ta fara yarfe hannu. Abba kallan Amina ya yi ya ce "Reke min hannun yadda ba zai yi rawa ba."
Amina rike hannun Mansura ta yi sosai, Abba daidai zai tsira ma Mansura allurar ta fuske hannunta, by mistake Abba ya caka ma Amina a hannu. Wani uban ihu Amina ta fasa, dan sosai allurar ta shigeta.
Abba cikin bacin rai ya daga hannu ya wanke Mansura da mari. Mansura gigicewa ta yi, dan tun da take ba a taba marinta ba sai yau. Rike wajan ta yi tana murzawa tana kuka.
Mahaifiyar Mansura da tun ihun Amina ta shigo dakin da saurinta har tana tuntube, jin kukan mutum biyu lokaci guda.
Abba kuma daidai ya juya zai fita, suka ci karo da mahaifiyarsa. Mahaifiyar Abba kallan tuhuma take ma Abba, ganin Mansura dafe da kunci tana kuka, ga Kuma Amina rike da hannu itama tana kuka.
Mahaifiyar Abba cikin tausasa murya ta ce "Abbana, ya haka Kuma?." Nan Abba ya kwashe duk abin da ya faru ya labarta mata.
"Allah dai ya kyauta, ni ban ga abin tsoro a Allura ba, duk da ta jijiyar nan na da zafi, amma ya za a yi inda duk zafinta ba takai ciwan ba."
Abba kallan Amina ya yi da har yanzu take dafe da hannun tana kuka, ya daka Mata wata uwar tsawa ya ce"Ba za ki yi ma mutane shiru ba." Abba ya fadi maganar yana kamo hannunta yana ganin inda ya caka mata allurar, sosai ya caketa. Abba murza mata wajan ya yi ya ce "Ki je motana akwai maganin zugi ki sha."
Mansura ko Abba na daka ma Amina tsawa ta yi shiru, tana zare ido.
Abba kallan Amina ya yi ya maka mata wata uwar harara kafin ya ce "Anjima idan na dawo ki zo in miki allurar, dan na gama biyoki nan."
Yana fadin haka ya juya ya tafi.
Mahaifiyar Amina hannun Mansura ta kamo tana liliyawa, kafin ta mai da kallanta ga Mansura ta ce "Shi ya sa masu iya magana suka ce idan ka ga zama ya yi karko wai hali ne ya zo daya. Yanzu me ya acikin Allura Mansura, to Wallahi ki natsu da kyau ki ji Abba ba sauki garesa ba, a haka ma dan har yanzu yana miki kallan bakuwa ne, dan da Amina ce da Kinga yadda zai yi da ita yau a gidan nan. Allura Kuma daga gobe dama an gama inda ya ce min ta kwana uku ce, Kuma kin ji abin da ya ce baya Kara zuwa nan yi miki, daga ya dawo kin ji muryarsa a falo sai ki samesa ya yi Miki, ko Kuma Amina ta rika rakaki bangaransa ya yi miki acan, idan kin natsu har ya gama miki tom,. Idan Kuma baki natsu ba tom babu ruwana, kin ga dai tun yana raga miki sai da kika kuresa."
Mansura dai bata ce komai ba, mahaifiyar Amina ta gama fadanta ta fita.
Amina na fita ta tafi wajan aikinta, mahaifiyar Amina ma ta tafi Islamaiya, ya rage gidan Amina ita kadai, abin da ya faru take ya tuna mata da mahaifinta mai ji da ita, Wanda baya Mata gyara akan duk abin da za ta yi, duk abin da ta yi daidai ne, amma yau ita ake Mata har ana mata faɗa, akan abin da ita bata ga laifi bane.
Mansura kuka ta yi sosai, tana Kiran "Abbana! Wayyo Abbana!!." Kuka take sosai, wanda har sai da ta ji kanta ya fara ciwo kafin ta yi shiru. Abin da Abba ya yi mata Kuma ta barshi dan baya son zamanta gidan ne ya sa ya yi Mata hakan amma aganinta me ta yi mai da zai mareta ,dan ita bata ga abin duka ba, har ana mata tsawa haka. Allah sarki gata kenan, haka dan gata Wanda ba a kwabamawa yake, idan ya je gidan masu kwaba, sai ya ga kamar ba a sonsa ne a gidan ya sa ake kwabame.
Mansura na nan kwance, Sallah kadai ke tada ta, har mahaifiyar Amina ta dawo daga Islamiya. Koda ta dawo ba ta bi ta Mansura ba. Kitchen ta shiga ta Samar masu abin da za su ci.
Mansura na nan kwance har yanzu ba ta bar zubar da hawaye ba Amina har ta dawo. Amina ko da ta shigo bedroom din nasu, kallan Mansura ta yi jin ba ta tanka Mata ba, Amina ta ce "My dear, na yi laifi ne kin ganni kin kauda Kai."
Abin mamaki Mansura kawai sai ta fashe da kuka.
Amina cikin tashin hankali tahau kan bed din tana kamo Mansura ta ce "Mansura, jikin ne, ki yi shiru dan Allah ki fada min?." Amina ta idasa maganar kamar za ta yi kuka. Mansura cikin kuka ta ce "Ba Yaya Abbanku bane ya maran, Kuma mama ba ta yi masa fada ba, ni ta yi ma fada ma. Ni tafiya Zan yi in bar muku gidanku."
Amina cikin tashin hankali, jin Mansura za ta tafi, ta rasa dalili tana matukar kaunar Mansura a ranta, hakan ya sa cikin tashin hankali ta ce "Wayyo dear dan Allah karki tafi, Wallahi Yaya Abba haka yake, ko nima baki ji ba yadda yake min fada, dan Allah ki yi hakuri Yaya Abba ba zai Kara dukanki ba." Mansura da har yanzu kuka take, dan har idanta ya canza kamanni ta ce "Tom ki ce ya ban hakuri, in ba haka ba Wallahi ni gara in tafi."
Amina da kuka itama ba wuya yake Mata ba, fita ta yi daga bedroom din ta nufi falo fa gudu tana kuka. Tana zuwa ta fada kan mahaifiyarta dake zaune tana kuka. Mahaifiyar Amina kamo Amina ta yi tana cewa "Subahanallahi, Amina me ya faru Kuma?." Mama, Mansura ta ce tafiya za ta yi ba zata zauna ba, dan Allah mu je ki bata hakuri, ni dai Wallahi ina sonta bana so ta tafi." Amina ta idasa maganar cikin kuka. Mahaifiyar Amina ganin yadda Amina ke kuka buga Mata bayanta ta fara tana cewa "Shi kenan, Amina ki natsu ki fada min Mana, me ya sa za ta tafi?." Amina goge hawayanta ta yi ta ce "Yaya Abba ne dazu ya kama marinta, dan zai yi mata allura ta goce, Kuma kema mama kika yi ta Mata fada, ni dai Mama ki yi ma Yaya Abba magana dan Allah ya bata hakuri karta tafi."
Mahaifiyar Amina al'ajabi ya sa ta kasa cewa komai. Bata taba tunanin sangartar Mansura takai haka ba, sai yau. Mamakin kalar shagwabawar da aka yi ma Mansura take, wadda ba ta san daidai ba kamar ta haka,. A iya shekarun yarinyar yanzu ai ya kamata ace ta san daidai ta san ba daidai ba.
Amina Kuma jin mahaifiyarta ta yi shiru ya sa ta ce "Mama, dan Allah, kin ga marainiya ce, mu tausaya mata."
Mahaifiyar Abba kallan Amina ta yi ta ce "Shi kenan, Zan ma Abban magana in ya dawo."
Mahaifiyar Amina fadi haka ne dan Amina ta rabu da ita.
Yau ma kamar jiya Abba ya dawo. Yana zaune suna fira da mahaifiyarsa, Amina ta shigo falon.
Bayan ta yi ma Abba barka da dawowa zama ta yi ta yi shiru, tana sauraran ta ji Abba ya ce ta Kira Mansura ya bata hakuri ta ji shiru. Amina, kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama, kin fada masa." Ke baki da baki ne da ba zaki fada masa da kanki ba?."
Amina baki ta turo. Abba Kuma aje wayar hannunsa ya yi yana kallan Amina ya ce "Me kike son fada min, da ba za ki iya ba sai mama ce zata fada mi? Fada min ina jinki?." Abba ya ce yana kallan Amina.
Amina wasa da yatsun hannunta ta fara, da alama dai kamar maganar na naiman yi mata nauyin fada.
Abba dai bai kuma tambayarta ba, amma ya mai da kallansa ga Amina, irin kallan ke nake saurare.
Amina cikin kame-kame ta ce
"Yaya Abba Marin da ka yi ma Mansura dazu ne take ta kuka har yanzu, ta ce tafiya za ta yi indai baka bata hakuri ba. Kuma Wallahi Yaya Abba baka ga fuskarta ba."
Amina har ta Kai maganarta, daga Abba har mahaifiyarsa Amina kawai suke.
Abba dan ya kauda mamakinsa, kallan Amina ya yi ya ce "Ita tace ni sai na bata hakurin marin da na yi Mata?."
"Wallahi Yaya Abba baka ga fuskarta ba."
Abba hararar Amina ya yi ya ce "Tambayar da na yi miki kenan? Na ce ita ta ce sai na bata hakuri.?." Eh, Yaya Abba dan Allah ka bata."
Abba shiru ya yi yama rasa abin da zaice, kila shi ya sa ya kauda maganar ya ce "Ya jikin nata? Zazzabin ya dawo?." A'a, baidawowa ba. Amma ta ce min tunda ka mareta kanta ke ciwo."
Shiru Abba ya yi, kafin ya ce "Kira min ita, ta zo da ledar maganin."
Mansura tashi ta yi ta nufi sight dinsu, Kwance ta iske Mansura kamar yadda ta barta. Amina dafa Mansura ta yi da har yanzu hawaye bai bar fita a idonta ba ta ce "Dear ki yi hakuri haka nan dan Allah, na yi ma Yaya Abba magana yana falo ya ce ki zo."
Amina hannu ta mika ma Mansura ta tashi, da yake tun safe taki cin komai hakan ya sa bata da karfin jiki sosai.
Mansura na bin Amina suka isa har falon.
Mansura zama ta yi kusa da Amina.
Amina kallan Abba ta yi dake dannawa waya da alama kamar bai san sun shigo ba, Amina ta ce "Yaya Abba ga Mansurar."
Abba Kai ya dago ya saukesu akan Mansurar. Abba ko ba a fada mai ba yasan ta ci kuka dan ga idanunta nan sun yi ja. Abba cikin kasa da murya kamar dole akai mai ya yi maganar ya ce "Lafiya me akai miki kike kuka?."
Mansura goge hawayan da ya zibomata ta yi ta ce "Ba Kai bane dazu ban yi maka komai ba kamaran, Kuma har yanzu kunnena ciwo yake."
Abba Kai ya dago sosai ya kalleta, ya rasa abin dama zai ce mata, ya dade yana kallanta kafin ya ce a hankali kamar ance dole sai ya bata hakurin ya ce "Sorry."
Mansura dai kanta kasa bata ce komai ba, Kuma Bata fasa zubar da hawaynta ba, dan ta raina yadda ya bata hakurin.
Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ganin har yanzu tana zubar da hawaye ta ce ,
"Tom ki yi hakuri ya isa sai ki bar kukan haka nan ko?."
Abba hannu ya mika ma Amina alamun ta bashi magungunan Mansurar. Mansura Mika masa ta yi. Amina ta Mika masa magungunan ta yi. Abba lura da Mansura iya gaskiyarta take tsoran allurar ya sa bai bi takan Kuma yi mata allurar ba, ya hada allurar da maganin ya tusa a ajjihunsa.
Mansura ko murmushin farin ciki ta yi, ganin Abba ya tusa ledar magungunan cikin aljihunsa, haka ya nuna ba zai Kuma yi Mata ba kenan, hakan ya sa Mansura cikin jin dadin yau ba za a yi mata allura ba ta tashi za ta tafi. Amina kallanta ta yi, ta ce "Mansura, Abinci fa?." Nakoshi." Mansura ta ce ta juya ta tafi.
Amina tashi ta yi ta bi bayan Mansura, ta ji dalilin da ya sa ba zata ci abinci ba bayan tun safe rabonta da abinci.
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi, ta ce "Abbana, nikam sai inga yarinyar nan kamar tana da wata boyayyar damuwa da ta aje a ranta. Lokuta da dama zaka ga idonta ya yi jajir alamun ta ci kuka, Koda yaushe ina tambayar Amina kodai ta fada mata wani abu, amma sai ta ce min bata fada mata komai ba."
Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Mama, tun farko ba na fada miki yarinyar nan ba gaskiya ta fada mana labarinta ba."
Kai mahaifiyar Abba ta jinjina alamun hakane ta ce "Gaskiya yanzu na fara yadda, saboda idan mutuwar iyayanta ce ya kamata ce ta dangana haka nan, hakika mutuwa na da radadi da Kuma magagi, tom Amma Allah na sa ma mutum juriya aransa, musamman idan aka arba'an, sannan in dai bawa ya yi imanun kowa zai mutu radadin mutuwa da magaginta na watannaine, Allah na sama bawa salama a rai, sai dai ranar da ya tuna ya yi kuka, amma ba irin Wanda nake ganin yarinyar nan na yi ba, kukanta baya kama da na rashi, ya fi yanayi da furgici da gigita. Tom, amma dai inda har yanzu bata nuna mana wani aibunta ba sai mu yi hakuri murungumi kaddarar kasancewa data."
Abba kallan mahaifiyarshi ya yi kafin ya ce "Shagwaba ta yi ma yarinyar yawa da sangarta, bare a fahimceta da kyau, shi ya sa nake ganin ko tsabar shagwaba ne ya sa take hakan?." Tom, kila, zai iya yuwuwa shagwabarce. Yauwa Abba mu bar wannan maganar ma, na ce yau she zaka je ganin jaririn Zainab? Ka ga dai yau kwana biyu da haihuwar."
Abba ido ya zaro da sai yanzu ya tuna da maganar haihuwar, ya ce "Gobe in sha Allah zani."
Mahaifiyar Abba, hararar Abba ta yi ta ce "Kamanta goban mu ka yi da Kai za ka je ganin Aisha, yarinyar da muka yi magana."
Abba shafa kan shi ya yi bisa ga alama ya manta, ya ce "Wallahi na shafa'a, in sha Allah goban sai inje, amma Mama ita ta san da zuwan nawa?." Ta sani Mana, mahaifiyarta ta sanar Mata, ka ga idan kuka daidaita ba sai a hada a yi da na Amina ba."
Murmushi Abba ya yi ya ce "Allah ya kaimu goban sai in je in ganta✍🏻
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Daga Marubuciyar
*Fadeela
*Meenalyn Daddy
*Oga Habib
*Abdurrahim
*In da rai
*So ne sila
*Daga Allah ko dora ma Kai
*Rayuwar Haidar
*Bakin kishi
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
Litafin Abbana na kudi 400 my number 08063830828
P 15-16
Washegari ya kama juma'a, Abba 4 ya dawo aiki, Yana dawowa ya yi shirin zuwa wajan Aisha kamar yadda suka yi da mahaifiyarsa. Abba bayan ya fito da shirin zuwa gidansu Aisha, Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama, zan tafi gidansu Aishar."
Mahaifiyar Abba zaro idanunta ta yi ta ce "Abbana, a haka zaka gidan surikan naka? Haba Abbana wayace maka ana zuwa gidan surikai da k'ananan kaya, ka sa manyan kaya mana."
Abba bata rai ya yi ya ce "Haba mama, kayan nan me suka yi." Ni dai dan Allah ka je
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 15