yashesu, ga abubuwa nan dai da yawa wa inda muke jin labari sanadin taimako." "Mama ba fa duka aka taru aka zama daya ba, Kuma shi kenan saboda haka sai ka ga mutum cikin ƙunci kaki taimaka masa? Wannan dai daga ganinta Mama munsan tana bukatar taimako, Amma ni ba nace dole sai mun taimaka Mata bane, ina naiman alfarmatar mu bata nan da kwana biyu ta dawo natsuwarta koda za mu koreta, dan yanzu ko mun koreta ba lalle ne ma ta san inda zata ba, inda ba cikin hayyacinta take ba." Amina ta isa maganar tana kallan mahaifiyarta.
Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta yi ta ce "Shi kenan, amma ya za mu yi da yayanki? Kin ji dai rantsuwar da ya yi in ya dawo ya isketa a gidan nan."
"Mama sai mu hanata fita falo inda dai Yaya Abba ba shigowa bangaremu yake ba." Amina ta idasa maganar tana langwabe kai, alamun mahaifiyarta ta tausaya Mata.
"Shi kenan Amina, idan za ki iya tsareta ba zata fita falo ba, amma fa ki sani babu ruwana idan yayanki ya Kuma ganinta gidan nan?."
"In Allah ya yadda ma ba zai ganta ba." Amina ta fadi maganar tana tashi ta fita. kitchen ta shiga ta soya doya ta dafa ruwan Lipton ta kaima mahaifiyata, ta zauna suka karya tare kafin ta hada na bakuwarta ta Kai Mata nata.
Da mamaki Amina ta bi Mansura da kallo ganin har yanzu bata tashi ba tana nan a yadda ta barta. Amina hannu tasa tana bubbuga Mansura ta ce "Mansura, ki tashi Mana haka nan." Ido Mansura ta daga tana kallan Amina alamun ba barci take ba. Amina murmushi ta sakar Mata ta ce, "Ki tashi Mana ki watsa ruwa ko za ki ji dadin jikinki, ga abin breakfast na kawo Miki."
"Na koshi." Mansura ta ce a hankali.
Amina da mamaki ta kalleta ta ce "Kin koshi? Jiya ma fa biki ci komai ba kika kwanta, a'a dan Allah, ki tashi ki ci ko babu yawa."
Amina hannun Mansura ta kamo ta ce "Mu je ki yi wanka za ki ji dadin jikinki, sai ki yi breakfast."
Mansura bin Amina ta yi har bathroom din ba tare da ta so ba, Amina hada Mata ruwan wankan ta yi , sannan ta fito ta barta.
Shiru-shiru Mansura bata fito ba, Amina jin shirun ya yi yawa ya sa ta matsa kusa da bathroom din ta ce"Mansura, kin gama wankan ne?."
Mansura da tunda ta shiga tsugunne take tana kuka sai lokacin da ta ji Amina ta kirata kafin ta tashi da sauri ta yi wankan ta fito.
Amina cikin kayan sawarta ta dakko wata goguwar riga ta ba Mansura. Amina da kyar ta samu Mansura ta sha tea din kadan, soyayyar doyar ko ko kallanta ba ta yi ba.
Amina sosai take ƙoƙarin jan Mansura a jiki dan ta ji damuwarta, amma duk abin da za ta ce sai dai Mansura da kalleta da ido. Dole ta hakura ta rabu da ita. A haka Mansura har ta yi kwana uku har yanzu ba su san ko wacece ba, dan jiya mahaifiyar Amina da ta matsata mata da tambaya kuka tasa Mata, hakan ya sa dole suka rabu da ita.
Yau kwanan Mansura uku kenan agidan, Kuma har yau Abba bai san tana gidan ba.
Yanzu haka Abba zaune suke shi da mahaifiyarsa suna fira. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mommy nifa kamar kuka nake ji?" Mahaifiyar Abba da tun dazun take jin kukan, tana sane sharewa kawai take dan kar Abba ya fahimci har yanzu Mansura na gidan, shi ya sa ta yi shiru, dan tasan Mansura ce ke kuka.
Abba jin mahaifiyarsa bata ce komai ba, ya ce "Kai mama, wannan kuka ne." Kallan Amira ya yi ya ce " Amira je ki gani Ina Amina."
"Uncle Abba, ba fa Mommy Amina ba ce ke kuka, bakuwar nan ce wadda mommy Amina ta zo da ita ke kuka, haka take yi kullum sai na ganta tana kuka, mommy Amina da Mama su yi ta bata hakuri amma taki yin shiru.".
Abba da mamaki ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Mama, dama yarinyar nan har yanzu tana gidan nan?." Abba Mai da kallanshi ya yi ga Amira ya ce "Amira Kira min Amina."
Amira da gudinta ta je ta kira Amina. Amina ko dama baki daya a tsorace take, jin yadda Mansura ke kuka da karfi ta San yayanta na gida zai iya ji. Yanzu haka hakuri take ba Mansura tana cewa, "Mansura dan Allah ki rufa min asiri ki yi shiru, Yaya Abba ya dawo yanzu kar ya jiki." Suna cikin haka ne Amira ta shigo ta ce, "Mommy Amina, Uncle Abba yana kiranki." Amina zaro ido ta yi tana kallan Amira, sannan ta ce "Amira Yaya Abba na falo ko?" Eh, Yana falo, shi ne ya tambaya wake kuka, na ce mai bakuwarki ce ke kuka, shi ne ya ce in kiraki."
Tun kafin Amira ta gama Kai bayani Amina ta fara goge zufa, dan tasan yau mai kwatarta hannun yayan nata sai Allah. Amina har zata fita ta kalli Amira ta ce "Amira mama na falo?." Kai Amira ta daga Mata.
Amina da addu'a ta idasa falon.
Can falon ko, mahaifiyar Amina ta dage sai ba Abba baki take tana cewa "Abba, ni na ce Amina ta bar yarinyar nan ta wastsake tukun, Kuma ta wastsake, dan tun ranar da ka ce ta koreta ta yi niyyar zuwa ta sata a mota ta tafi, ganin halin da yarinyar take ciki na ce ta barta ta warware."
Abba dai baice komai ba, dan yasan mahaifiyarsa ta fadi haka ne dan Kar ya bugu Amina. Suna a haka ne Amina ta shigo falon a tsorace. Kafin Abba ya yi magana, Amina ta ce "Yaya Abba, dan Allah ka yi hakuri."
Abba be cema Amina komai ba, sai zuwa can ya ce, "Amina kinsan dai baki taba nuna kina son abu ba naki ko?." Kai Amina ta daga Mai. Ya ci gaba da cewa. " Tun da yarinyar nan ta zo gidan nan bayan sunanta kun Kara sanin wani abu akanta?." Nan ma Amina Kai ta girgiza ma Abba, alamun ba su sani ba.
"Amma Kuma shine ke gaki shugabar masu tausayi duk da haka kina tausaya Mata, ba zaki iya barinta ba ko?" Ya ci gaba da cewa "Yanzu Zamani ya lalace Amina fiye da yadda kike tunanin, wama ya Sani kila wani takashe ta gudu, dan da bakinta ta furta Mana haka, Kuma kin ga in ta tabbata haka ne mun boye mai laifi kenan. In dai baki so mu samu sabani Ina so gobe ki sallami yarinyar nan ta bar gidan nan, ni baki daya hankalina bai kwanta da lamarinta ba."
Abba 10k ya dakko ya ba Amina ya ce "Gashi, ki kaita tasha gobe ki sata a motar Kaduna."
Amina cikin jin dadin ganin yayan nata bai mata komai ba ta ce "Na gode yayana Allah ya Kara arziki." Tana fadar haka ta tashi ta tafi.
Abba Kuma kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama, dan Allah ki yi hakuri idan na saba miki na korar yarinyar nan da na yi."A'a Abbana, baka saba min ba, ni kaina zaman yarinyar ma na naiman samin damuwa, in da dai ita har yanzu taki fada Mana ita wacece, daga sunanta bamu san komai ba game da ita, garama ta tafi, ita wannan uwar masu tausayin na samu in samu kanta."
Haka dai Abba suka kare fira da mahaifiyarsa da sunan washegari za a kuri Mansura.
Washegari Amina da wuri ta tashi ta yi masu abin breakfast, ta kawo ma bakuwarta nata.
Mansura tea din tasha kadan, bread din ko ko kallansa ba ta yi ba. Amina na gamawa ta sa Mansura ta yi wanka bayan ta bata kaya ta sa, Amina ta kalleta ta ce, "Mansura, yanzu zan kaiki tasha ki shiga motar Kaduna ki tafi garinku, za ki gane in da zaki ko?." Mansura mai makon taba Amina amsa sai ta fashe ma Amina da kuka. Sosai ta ba Amina tausayi. Amina dafa ta yi ta ce "Baki son tafiya gidan ne?." Kai Mansura ta daga ma Amina. "Me ya sa biki son tafiya?." Amina ta tambayeta tana mai kureta da ido. Nan Kuma Mansura shiru ta yi bata tanka ma Amina ba. Amina hannun Mansura ta kama tana ja alamar ta zo ta rakata tasha ta sa ta a mota, Amma Mansura taki ta cije tana kuka. Amina babu yadda ba ta yi da Mansura ba ta tashi su tafi amma taki tashi karshe daga zata kama hanunta ita Kuma ta make hannunta taki yadda ta kama. Amina ganin haka wajan mahaifiyarta ta je, cikin damuwa ta labarta Mata abin da ke faruwa. Mahaifiyar Amina da mamaki ta ce "Ka ji min yarinyar, to mu ya za mu yi da ita, yanda Abba ya nuna damuwarsa da zamanta gidan nan ai ba zai yuwu ba, dole za ta yi hakuri ta tafi. Mu je in yi magana da ita."
Mahaifiyar Amina ta dade tana kallan Mansura da ke uban kuka har da majina. Cikin sanyin murya mahaifiyar Amina ta ce "Yata, ki yi hakuri kin ji, Amina ta je ta saki a mota ki tafi gidanku."
Mansura dai babu abin da take sai kuka sosai take kuka har da Majinarta. Amina da babu wuyar kuka ganin haka itama sai ta fashe da kuka. Mahaifiyar Amina Kuma duk sai ta shiga damuwa yadda ta ga Mansura na kuka, hakan ya nuna mata bata son tafiya ne. Mahaifiyar Amina cikin sanyi ta kalli Mansura tana mai dafata ta ce "Shi kenan, ya isa, ki yi shiru, fada min me ya sa biki son tafiyar?." Nan na Maimakon Mansura ta bata amsa sai kuka. Mahaifiyar Amina ta ce "Ai kin ji abinda ke hada ni da ke, ki yi shiru ki fada min me ya sa baki son tafiyar?."
Babu yadda mahaifiyar Amina ba su yi da Mansura ba amma taki Magana sai kuka.
Mahaifiyar Amina hannun Mansura ta kama ita kanta sai ta ji duk ba dadi ta mika ma Amina ta ce "Amina maza ku je ki sata a mota ta tafi."
Amina kama hanun Mansura ta yi suka fita. Suna fita gidan, Mansura ta tsugunna kusa da get din gidan ta tusa kanta a tsakankanin kafafunta tana kuka. Babu yadda Amina ba ta yi da ita ba ta tashi su tafi amma taki, dole Amina ta gaji ta rabu da ita ta koma gida, ta sanar da mahaifiyarta abin da ke faruwa.
Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta sauke ta ce "Amina kin ga dai in da mun samu ta fita daga gidan nan shi kenan, duk da Wallahi duk na ji babu dadi kukan nata, ta bani tausayi sosai, to Amina rayuwarce sai a hankali Kai kanka ba ka gama maganin kukanka ba bare ka yi ma wani."
Amina dai bata ce komai ba ta nufi bedroom dinta ta kwanta, saboda kanta dake Mata ciwo, dan tun jiya ba wani barci tayi ba, kwana ta yi tunanin Mansura. Kasan cewar Amina jiya ba wani barcin kirki ta yi ba, hakan ya sa tana kwanciya barci ya dauketa.
Amina ba ita ta farka ba sai 1:50Pm, ana ta kiraye-kiran Sallah. Tashi ta yi ta fara gabatar da Sallah, sannan ta nufi hanyar fita gidan. Mahaifiyar Amina da ke kitchen Kiran Amina ta yi ta ce "Ina zaki kike sauri haka?." Mama, lekawa zan yi in ga Mansura na nan ko ta tafi."
Shiru mahaifiyar Amina ta yi tana kallan Amina, ta san indai ta je ta Kuma ganin Mansura ba ta tafi ba za ta zo ne ta sa kanta cikin wata damuwar, hakan ya sa ta ce "Bana son shirme me za ta tsayayi tun dazu, ga abincinki can ki je ki ci."
Amina cikin sanyi ta juya ta koma, in da ko tana nan ma babu wani abu da za ta iya Mata, tasan ita ta jawo ma kanta, kila da ta fada masu ita ko wacece ba ta jin yayanta ma zai koreta.
Misalin 80:00PM Abba ya dawo wajan aiki, kamar yadda ya saba dawowa kusan kullum. Da mamaki ya ke kallan Mansura da bai gane kowacece ba, ya ga dai mutum a zaune ta tusa kanta a tsakankanin cinyoyinta. Abba fita ya yi daga motar daboda da kansa ya ke bude ma kansa get ya shiga da motarsa. Da mamaki ya ce "Ke! Lafiya? Me kike yi a nan?." Ya fadi maganar da karfi.
Mansura ko da tun maganar farko ta gane muryarsa cikin tsoro ta tashi ta matsa da sauri ta bar wajan get din nasu.
Abba da mamaki ya bita da kallo dan ya ganeta. Kallo daya ya yi Mata ya fahimci tsoran da ta shiga na ganinshi din da ta yi. Abba Matsawa ya yi har inda Mansura take, tsugunnawa ya yi ya na kallanta, Wanda ita Kuma Bata san yana yi ba, saboda ta tusa kanta a tsakankanin cinyoyinta. Cikin mamaki ko dare bata tsoro Abba ya ce "Me kike yi anan? Biki ji saukona bane ba, na ce Amina ta kaiki tasha ki shiga mota ki tafi garinku ba?."
Mansura cikin tsoro ta ce "Zan tafi." Tana fadin haka ta tashi ta tafi✍🏻
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK
⭐ABBANA⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Daga Marubuciyar 👇🏻
*Meenalyn Daddy
*Oga Habib
*Fadeela
*In da rai
*Abdurrahim
*Daga Allah ko d'ora ma Kai
*So ne sila
*Rayuwar Haidar
*Bakin kishi
Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 5-6
Abba tsugunnawa ya yi kusa da Mansura ,ya ce "Me kike yi a nan, baki ji saukona bane ba, na ce Amina ta kaiki tasha ki shiga mota ki tafi garinku ba?."
Mansura cikin tsoro ta tashi ta ce "Zan tafi." Tana fadin haka ta tafi..
Abba tsayawa ya yi yana kallanta, so yake ya juya ya tafi amma Kuma ya kasa, ganin dare ne, gashi ba garinsu ba ina zata yanzu, hakan ya sa Abba ya bi Mansurar, wadda daga gani tafiya kawai take amma ba ta san inda zata ba. Abba shan gabanta ya yi ya ce, "Muje." Mansura juyawa ta yi ta bi bayan Abba.
Abba da sallama ya shiga falon mahaifiyarshi, inda ya iske mahaifiyarshi da Amina zaune. Amina da Mahaifiyar Amina da mamaki suka bi Mansura da kallo. Abba zama ya yi ya nuna ma Mansura kuda da Amina ya ce "Zauna." Zama Mansura ta yi gefan Amina tana zare ido.
Abba kallan Amina ya yi ya ce ,"Amina me ya sa baki kaita tasha ba kamar yadda nace?."
Amina cikin raurau da fuska ta ce "Yaya Abba, Wallahi ka tambayi mama shirya zan rakata muna fita ta takure a bakin get taki tafiya."
Abba mai da kallanshi ga Mansura ya yi ya ce "Wacece ke? Kuma me ya baro da ke daga gidan iyayanki?."
Mansura kuka ta fara har tana shashsheka. mahaifiyar Amina dafa Mansura ta yi ta ce "Ki yi shiru Yata, ki fada Mana wacece ke?" Mansura dai ba ta ce komai ba, ta ci gaba da kukanta.
Abba ransa fara baci ya yi, ganin kamar tana so ta raina masu wayau, daga tambayeta wacece ita sai kuka, hakan ya sa ya daka mata tsawa ya ce "Wacece ke nace? Ba kuka aka tambayeki ba."
Ba Mansura ba hatta Amina sai da ta tsorata da tsawar da Abba ya yi ma Mansura.
Mansura take jikinta ya fara rawa ta kasa magana, Wanda ita kanta tsoran shirun nata take ji.
Amina a hankali ta ce "Mansura dan Allah ki natsu ki yi magana, Kinga ke Yaya Abba ke saurare. Shirun naki zai jawo ya yi miki wani zargin wajan Yaya Abba, ki yi magana dan Allah."
Mansura cikin sarkewar harshe ta ce"Sunana Mansura, mamana da babana sun yi accident ne suka mutu." Mansura ta idasa maganar tana Kuma rushewa da kuka. Amina sarkin tausayi itama kukan ta fara.
Abba shiru ya yi, kafin zuwa can ya ce "A'ina dangin baban naki suke."
"Ba nida su, babana gudin hijira ya yi, a hanyarmu ta zuwa Kaduna ne muka yi accident din."
Abba kwatakwata zuciyarsa ba ta gamsu da maganar Mansura ba. Amma ganin yadda mahaifiyarsa da Amina suka yadda ya sa bai ce komai ba.
Mahaifiyar Amina cikin tausayin Mansura ta ce "Ki yi hakuri kin ji ba kuka za ki yi ba Addu'a za ki yi musu, Allah ya jikansu, Amina kamaya ku shiga ciki."
Amina hannun Mansura ta kama suka shiga tafi.
Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama ni fa ban yadda har yanzu da yarinyar nan ba, babu wani kamshin gaskiya a kalamanta." Mahaifiyar Abba zuba ma Abba ido ta yi tana mamakin furucinsa, ta ce "Abbana, babu abinda ka rage a halin mahaifinka, tabbas na yadda barewa Bata gudu danta ya yi rarrafe, haka mahaifinka yake shima bashi da yadda, Amma in ba haka ba meye na karyata, ko yana yin halin da yarinyar kadai take na furgici da razana ai ya ci ya sa ka yadda da maganarta. Ni yanzu abin da nake so da kai ka yi hakuri mu barta ta zauna tare damu har zuwa wani lokaci, alabashi idan ta aikata wani abu Wanda ba mu gamsu da shi ba sai mu koreta."
"Tom ba damuwa mama, Allah ya sa mu dace." Abba ya fadi haka yana tashi ya nufi bangaransa.
Haka rayuwar Mansura ta ci gaba da wakana a gidan. Sosai Amina ke bakin ƙoƙarin ta wajan ganin ta jawo Mansura a jikinta ganin ta kauda Mata damuwarta, Amma Ina abin ya ci tura. Amina ko fira ta kawo ma Mansura da ido kawai take binta har ta gama. Amina ganin haka ya sa ta watsar da Mansura. Mansura Kuma ganin Amina ta watsar da ita sai ta dawo tunaninta, duk Kuma sai ta damuwa, dan tasan sosai Amina ke bakin ƙoƙarinta ganin ta sata farin ciki.
Mansura kallan Amina ta yi da ta yi banza da ita, yau tun da suka tashi bata tanka Mata ba, hakan ya sa Mansura ta ce "Amina yau tare za mu shiga kitchen kinsan ban iya girki ba Ina so ki koya min."
Amina da murmushi ta amsa ma Mansura dan tun da ta zo gidan magana mai tsayi ba ta taba shiga tsakaninsu ba sai yau. Hakan ya sa Amina da murnarta ta ce "Tom zo mu je mu yi girkin, dama yanzu nake shirin shiga kitchen din."
Koda suka shiga kitchen din, Mansura da kallo kawai take bin Amina inda ba iya girki ta yi ba, ko in zata dauki wani abun ta mika mata, a haka suka gama girkin. Tare suka ci duk da Mansura ba wani abun kirki ta ci ba.
Da daddare suna zaune babu mai cema kowa koma. Amina datse shirun nasu ta yi ta ce "Mansura gobe zan koma makaranta, hutun mu ya kare, da yake Ina koyarwa.
Yanzu idan na koma ya za ki yi Kinga mama Islamiya take zuwa, ke kadai za a rika bari a gida, ko in yi ma Yaya Abba magana ya sa ki a islamiyarsu mama zata debe miki kawar kadaici, ya fi mu tafi mu barki a nan ke kadai." A'a, ni dai bana so." Cewar Mansura.
"A'a Mansura ba zai yuwu ba a barki ke kadai, kadaici damuwa zai Kara Miki. Ina kika tsaya a school?." Diploma certificate garan.
"Yauwa, tom ko in ma Yaya Abba magana ke ma ko teaching ne ya Samar maki, inga kin huta zaman kekadai"
Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai bana so."
Amina hakuri ta yi ta rabu da Mansura, haka Amina tai ta jan Mansura da hira, har ta ji Mansurar ta yi banza da ita alamun ta yi barci, dama Kuma daga, Eh, sai a'a, Mansura take yi a firar. Amina jin ta yi shiru alamun ta yi barci ya sa itama ta kwanta.
Washegari, Amina da wuri ta tashi ta yi masu abin breakfast. Bayan ta shirya, tada Mansura ta yi ta mika mata wayar ta ce "Dear ga wayata nan ta debe miki kewa." Tana Bata ta tafi.
Mansura ba ita ta tashi ba sai da ta ji yunwa na naiman takura mata kafin ta tashi ta yi breakfast, ta koma ta kwanta. Zaman kadaici sai ya je fa Mansura a duniyar tunani, inda gaba daya tunanin mahaifinta ya fado Mata rai. Mansura kuka ta fara, tun tana yi kadan-kadan har ta fara yi da karfi. tana cewa"Wayyo Abbana, Allah ka jikanka Abbana, Allah ya fe maka. Allah ba dan halina ba ina rokanka Allah ka samin nazuwa a rayuwata. Allah ka cire min damuwa da furgicin da ke damuna. Allah ka dandana min farin ciki koya yake kafin ruhina jikina ya yi ban kwana da gangar jikina nima. Wayyo Abbana." Mansura kuka take sosai da majina tana turje-turje tana Kiran Abbanta.
Abba da shigowarshi gidan kenan, tun kafin ya karaso yake Kiran layin Amina. Amma Mansura da yake kukanta take sha ko ringing wayar ma bata ji ba. Abba jin yadda Mansura ke kuka tana Kiran Abbana, da sauri ya yi bedroom din Amina, dan shi ya za ci ma Amina ce ke kuka. Abba cikin gigita ha hau kan bed din da Mansura take tana bubbuga kadon tun karfin tana Kuma Kiran Abbanta. Gashi Kuma ta kudindi ne kanta cikin blanket din. Abba da gaba daya ya manta da wata Mansura dan tun ranar da ya dawo da ita bai sake ganinta ba, hakan ya sa gaba daya ya dauka Amina ce. Abba da sauri ya kamo Mansura yana cikin tashin hankalin halin da ya ganta ci, ya ce "Amina, lafiya? Me ya same ki? Wa ya taba ki kike kuka haka?."
Mansura da gaba daya ta cukuykuye kanta da blanket , hakan ya Kuma batar da Abba itace, gashi dama kusan kirarsu daya da Amina.
Abba cikin jin haushi ya fara fada Yana cewa"Amina kashe kanki kike son yi ne da za ki cukuykuye kanki haka." Yana maganar yana ƙoƙarin fito Mata da kanta.
Mansura take natsuwa ta shigeta ta hadiye kukanta, ta yi tsit kamar an kashe inji.
Abba da mamaki da yake bin Mansura da kallo wadda idonta ya yi jajir tsabar kukan da ta yi. Abba cikin tausasa murya ya ce "Me akai miki?."
Mansura shiru ta yi tana yin kasa da kanta.
Abba dago kan Mansura ya yi ya, ya Kuma maimai ta Mata tambayar, "Me aka yi miki?."
Mansura goge hawayanta ta yi ta ce kamar za ta yi kuka, bakinta na rawa saboda tsoran Abba take. Cikin shashekar kuka ta ce "Abbana."
Shiru Abba ya yi yana kallanta, kafin ya ce " Ina Abban naki yake?."
"Ya mutu ya barni." Mansura ta fada tana Kuma fashewa da kuka. Abba cikin son kwantar mata da hankali dan ya san yadda mutuwar mahaifi take ya ce, "Ki yi hakuri kin ji, ba kuka ya kamata ki zauna kina yi masa ba. Abbanki bai yi gaggawa ba lokacinsa ne ya yi, addu'a ya kamata ki rika yi masa. Daga yau Kar in Kara ganinki kina Mai kuka, Kin ji ko?." Kai Mansura ta daga tana goge hawayanta.
"Yauwa, good girl."
Abba sauka gadon ya yi ya na cewa "ki shiga kitchen ko taliya inda tafi sauri ki dafa min, zan yi bako, dama Amina na yi niyyar sawa tom na zo Kuma ashe ta yi resume school yau, ki yi sauri dan Allah." Abba ya fadi maganar yana fita. Ba tare da ya bata damar cewa komai ba.
Mansura turi baki ta yi ta ce "Ni ai ban iya girki ba." Mansura ta ce tana sakkowa daga kan bed din.
Kitchen ta nufa, tana zuwa ta samu tukunya ta kusa cikata da ruwa, sannan ta zuba mai ya kusa kwalba, ba soyawa ba komai, ta daddaka tarugu da albasa suma ta wasa. Ruwan ko zafin kirki bai yi ba ta zuba taliyar. Magi ko duk magin da ke kitchen din babu Wanda ba ta sa ba, stone fishi din da ta gani shima ta dauka ta maka a ciki. Ta zauna zaman jiran ruwan taliya ya kone ta sauke taliyar.
Taliya sai da ta zama kamar fate kafin Mansura ta sauketa. Ta dakko Plate ta zuba.
Bangaran
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 15