Share this page
dashi haka na bude baki, hanci ina kallonshi: “Nayi kyau ne?” Da sauri na janye idanuna daga kanshi inajin wata kunya ta rufenj kamar na tsaga kasa ta rufe dani. AyshatuuuuHar kofar gate din gidanmu ya kaini, babu kowa a kofar gidan dama Abba nake tunanin zan samu kasancewar friday ce mostly da yammaci yakan fito da kujera ya zauna yana reading papers. Amma yau se babu kowa hakan yayi min dadi. Yana gama parking na kalleshi nace “Thank you so much sir, a gaida mutanen gidan” Wani kallo yayimin wanda yafi kama da harara yace “Shi bakinnan godiya kadai ya iya yi ne?” Murmushi nayi tareda sunkiyar da kaina amma bance komai ba, shima murmushin yayi me sauti tareda fadin “Monday very early zanzo mu tafi” Babu amfanin musu dan Na lura baya son hakan, se kawai na gyada kaina kurum, daga nan na bude kofar na kara masa godiya nayi cikin gida inajin intense gaze dinshi a kaina da har suka so harde ni. Tundaga parlor na san tabbas yau munada baki dan kuwa ga hayaniyar yara nan, da sallama na shiga inajin yadda kaina ya sara, aikuwa yaran dukkansu suka yo kaina suna ihun murnar ganina, dan da yawansu na jima ban gansu ba. Dukda yadda nake ji haka na daure kowanne na bashi peck a kumatu kafin kuma aka karba kayana aka kaimin daki, ni kuma na wuce parlon Ummaah dan Na tabbatar itada ‘ya’yanta masu aure suna can. Ile kuwa dukkansu suna zaune banda Yaya Halifa.+ Kowannensu ya amsa sallama ta tareda bina da kallo, wasu na mamakin ramar da nayi wasu kuma duhun da fata ta tayi. Gaba daya yadda kukasan an tsotse ni haka na koma wata yar fiyat dani. Gefen Ummaah Na zauna daga kan carpet a dadare nace “Ummaah barka da gida” Kaina ta shafa cikin kulawar da aka jima baa bani ba, baa nuna min irinta ba tace “Yar fara kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga yadda kike rama kamar wata me AIDS” Kaina na sunkuyar hawaye taf idanuna nace “Bana jin dadi ne shiyasa na dawo nadan huta” Dukkansu suka fara min sannu wannan ya rungumo ni tanan har seda hawayen da nake rikewa ya sakko kan kuncina, i can’t remember last time da naga haka. “Ya A’isha da halima da me gidan?” Kyaftun take nufi da Afeeyya hakan yasa nace tanan tana gaishesu. Lokaci guda na ware anata hira dani muna kyalkyala dariya, naji wani sanyi cikin zuciyata hade da nutsuwa tareda fatan Allah yasa hakan ta daure na cigaba da ganin hakan. Bayan laasar naci abincin da khairiyya ta kawo min sega Yaya Halifa da Abba nan fa aka fara hira, a tsokani wannan a tskokani wancan se bayan sallar isha kowa ya hada kan iyalanshi suka wuce and i was left in my room all alone counting the numbers of boards that made up the ceiling. Na jima bacci bai daukeni ba inata tunanin rayuwa da yadda take juyawa da makomar rayuwata. Firgigit nayi da tuna ban kira bawan Allah daya kawo ni naji yadda yake ba, ba tareda wani tunani ba na janyo wayata na fara dialing tashi, tana shiga na kwakwalwata ta ankare da abinda nake ta tsayar dani se kawai na kashe wayar ina bubbuga kaina da jin haushin dalilin da zaisa na kirashi. Inata tura baki na tashi na tafi dakin Inna amma na samu tuni tayi bacci. Ina dawowa na tarar da wayar tana ringing and it was him calling, haka nan na karasa jiki a sanyaye na dauki wayar tareda karawa a kunnena nace “Barka da dare Sir” “Barka dai Asmau. Ya saukin jikin?” Se dana kalla kaina kafin na amsa masa da sauki se kuma mukai shiru dan nidai bansan me zance msa ba kuma baya son godiya. Hakan yasa nayi shiru. Se can yace “Kiyi bacci and ki tabbatar kinci abinci” Kamar wata doluwa haka na shiga gyada kaina in agreement amma sede bama gani na yake ba balle, seda yace “Huh! Asmau?” Sannan nace “Inshaaa Allah Sir” STORY CONTINUES BELOW Daga haka mukai hanging, wani irin raruma nayiwa wayar taredq rungume ta a kirjina inajin wani farin ciki marar misaltuwa. Murmushi kuwan from ear to ear kamar bakina zai yage. Can kuma na kashe wutar tareda yin addua na kara lula duniyar tunani a haka daddan bacci ya daukeni, it was peaceful dan ko mafarkan da nayi where of love. Dan haka da asuba dana tashi komai lafiya lau jikina ba wannan rashin kuzarin se ma wani karfi da nake ji. Hakan ya bani mamaki amma a kasan zuciyata nasan menene nasan dalili. Ina idar da sallah na janyo babban quran dina na fara tilawa a kalla nayi izu daya kafin nayi azkhar lokacin tuni gari ya waye hakan yasa na gyara dakina na shiga wanka. Ina fitowa na zura wata morning gown ta wani silk purple yadi. Kaina na zura hula sannan na tafi kitchen. Na jima tsaye a jikin working surface ina karewa kitchen din kallo wanda a zahiri kenan amma a badini ina tuannin bidirin da aka sha a kitchen din, tun daga Yaya mukhtar down to Yaya Suleiman. Kowannensu it started at this very place. Ajiyar zuciya me nauyi na sauke ina kara kallon guraren tareda saka hannuna ina tattabawa wasu nayi murmushi a haka na kashe time din da bansan iya adadinshi ba. Se can dana fara jin motsin yan gidan sun tashi sannan na dukufa fara aiki. Na kusa gamawa Mama da Asiya suka zo muka karasa na wuce na gaida Inna sannan Abba da Ummaah. Muna kammalla breakfast na koma daki na dudduba wasu soft copy pages da aka turon akan Breast cancer da Cervical cancer. Ban wani dauki time ba na gama na janyo system dita na fara aikin da na saba wato kallon korean movies, wani Love In The Moonlight. Gaba daya na sakankance ina kallona naji an turo kofar dakin, normally mun saba indai zaka shiga dakin koma waye seka yi knocking da sallama kafin ka shiga. Hakan yasa na dago da sauri tareda pausing film din, mamaki sosae ya kamani ganin Nadia, its been long da naga kafafunta a cikin gidanmu kuma dakina. Mikewa nayi ina sakin murmushi nace “Nads manyan mata, sannu da zuwa” “Yawwa!” Kawai tace min se ban wani damu ba tazo ta zauna nace “Bari a kawo ruwa, yau akwai hirar yaushe gamo kenan” Na fada ina kokarin tashi daga gefenta, hannunta tasa ta rike nawa, hakan yasa nayi saurin kallonta kafin nayi magana tayi beating dina to it tace “Bashi ya kawo ni ba. Kina kallon yanayi na kinsan ba ruwa nazo sha ba. Gargadi nazo nayi miki, mijina Suleiman nawa ne ni daya kinganshi yafi karfin wadda tayi kwantai ta gama aiki cikin kartin maza irinki. Saboda kin kasa auruwa you decided kizo kimin snatching miji? Kul dinki!”2 I was dazed, confused and amazed! Tunda ta fara magana nake kallonta da tsananin mamaki wanda ya kasa boyuwa ya fit baro baro akan fuskata. Tana gama fada ta hankadar da hannuna ta mike da niyyar fita, nasa hannuna na riketa ina kallon idanunta wanda na rasa meye a cikinsu amma nawa firgici ne a cikinsu “Ta yaya zaki fita baki fahimtar dani abunda maganar ki take nufi ba, Nadia ni ce fa” Hannunta ta kwace kamar wata damisa, cikin daga murya tace “Se me dan kece? Ai nasan ke dince shiyasa na sassauta miki, tunda bakiji kunyar kawancenmu kin kai idanunki kan mijina ba bazanji kunyar na miki gargadi ba. Me mijina zaiyi dake tsofe tsofe dake…..” Ban barta ta karasa ba na wanka mata mari ina wani irin huci, i was boiling in, “Kada ki kuskura Nadia…..” Se na dunkule hannuna na kasa karasawa, zuciyata na fada min Nadia ce fa, wannan dinnan, kin manta ta? She doesn’t deserve this. Bana tunanin akwai circumstance da zai zo na manta matsayin rayhana da Nadia a rayuwata, sudai zasu iya mantua amma ni nasan alheri bana mantawa dashi. Ai tana ganin nayi shiru ta fara zage zage wanda ya janyo hankalin Inna da Ummaah dasu Mama, su basu san ta shigo bama dan kowanne na dakinsu. Ummaah tazo tana fadin STORY CONTINUES BELOW “Nadia me ya faru? Me ya hadaku?” Wani mugun kallo tayiwa Ummaah tace “Ki fada mata ta fita harkar mijina, mijina yafi karfin ta shi ba tsaranta bane, idan ba haka ba……” Gaba daya har Inna muka tsaya muna kallonta da tsananin mamaki, kuma shirun da mukai mata baisa tayi shiru ba sema kara daga mirya da takeyi a haka Abba ya fito ya samemu a tsatsaye, Nadia tana ta wulakanci ita me miji. Kallonta yayi yace “Kiyi hakuri ki koma dakinki, ni na miki alkawarin Asmau bazata taba auren mijinki ba, itama nata yana nan tafe da izinin Allah” Kawai tana bude bakinta se cewa tayi “Better!” Ta juya ta fice, tana fita naji wani irin yanayi me wiyar na fada ya lullubeni, kaina kamar zai tsage gida biyu, idanuna da suke neman lumshewa na bude da karfin gaske nace “Abba me ya faru” Ashe yaya Suleiman ya samu Ummaah akan yana sona zai aureni tace masa aa kar ya manta abinda ke tsakanina da matar shi, bai jiba ya samu Inna ita kuwa kowa yasan yana daya daga cikin favorite jikokinta hakan yasa tayi naam da maganar. Kallon Inna nayi kamar zan daketa idanuna se hawaye ke zubowa, gaba daya na manta Inna bata jin turanci nace “For goodness sake, Inna why will you do this? Danme? Kinsa yarinya yar cikinku tazo tayi muku fitsara. Saboda banyi aure ba, kun taba ganin macen da takai age dina bata damu tayi aure ba, in bai zo ba zan fita titi nayi shelar wa yake sona? Waye zai aureni…!” Wani abu naji ya tokaren makoshi hakan yasa na juya dan tafiya daki amma wani mugun jiri ya kwashe ni se gani a kasa, dukkansu suka yo kaina dan tashina amma na mike seda Abba ya rikeni aka kaini har daki daidai shigowar yaya Suleiman a birkice, Abba yace baya son yaji komai kawai yazo ya dubani. Yana dubani ya daura min drip se na lumshe idona kamar me bacci hakan yasa suka fita dan na samu na dan huta amma maimakon na mutsu se kawai na tashi na hada kaina da gwiwa na dinga kuka, a raina ina ayyana yadda rayuwa ta juya, ni Nadia tazo har guda ta ciwa mutunci akan mijinta? Su Ummaah basu tsira ba. Asiya ce ta shigo ta sameni a hakan ta zauna tana ta lallashina har nayi shiru sannan ta dauki wayata dan nace duk wanda ya kira tace banda lafiya. Misalin karfe bakwai na dare nayi sallar maghrib, na dan nutsu ba kamar da safen ba shima Abba da Ummaah suka zo sukai ta lallashina tareda nuna min haka rayuwar take, we must expect worst from life, it’s a trial which are never meant to be easy. Wannan ya karfafa min gwiwa har nasha tea sannan nayi wanka amma idanuna kadai zaka kalla kasan kodai ina cikin damuwa ko banda lafiya. “Yar fara tashi maza maza ki canja kaya kizo parlor kinyi baki” “Baki?” Na maimaita ina kallon Ummaah data bude wardrobe dina da alamun kaya take nemo min kaya, mikewa nayi jin bata bani amsa ba nace “Ummaah su waye?” Juyowa tayi tana kallona kafin tace “MD dinku ne” Idanu na zaro cikeda mamakin abinda ya kawoshi, taba ni Ummaah tayi tace “Tun dazun sukazo so kiyi sauri kisa wani abin kizo” Idanuna Na lumshe ina jin wani mintsini da ale min a cikin zuciyata na farin ciki, kallon kayana nayi ba tareda daukar ko daya ba na rufe na nufi inda Abayas dina suke na samo wata simple royal blue abaya wadda egde dinta aka mata ado da wani silk blue material yayi kyau. Mayafin na yafa bayan na wanke fuskata na fito parlor Amma maimakon na ganshi se wata yar karamar yarinya wadda shekarunta bazasu wuce shekara biyar ba, sanye take da jeans se top an saka mata hula kalar top din. Wasa take da throw pillow din kan cushion din da take kai, gefenta wata middle aged mata ce tana zaune da waya a hannunta amma kamar da suke da wannan yarinyar ta baci. Hakan yasa naji hankalina ya kwanta daga tantamar da zuciyata take. A hankali na karasa inda matar take Na tsugunna a gefenta nace “Barka da zuwa, ina yini?” Da sauri ta dagani Na zauna gefenta tana ta murmushi kamar bakinta zai yage tace “Mashaaa Allah, Alhamdulillah! Barka dai Asmau ya jikin naki?” A kunyace nace “Alhamdulillah!” Dan yadda idanunta ke sparkling daga gani na kamar irin abinda kake jira dinnan shekara da shelaru ne yazo.” “Yayi kyau, Raudha bakiga Anty ba, zo ki gaisheta” Yarinyar tazo tayi hugging dina ta gaisheni , ina murmushi na zaunar da ita kaina naace “Raudha” Kallon Maman ta tayi tace “Amiey, wannan ce Matar uncle Abbas din?” Da sauri na kalli yarinyar dake shafa fuskata sannan na kalli uwar dake kallona with love a idanunta tace “Inshaaa Allah” Kunya ta kamani sosae, zuciyata wani irin bugawa take na kasa tantance a wanne yanayi nake ciki farin ciki ne ko mamaki. Kafin ta kara magana Ummaah da mama suka zo dauke da abinci akan tray, sannan ta zauna suka gaisa inajin tana fada mata su asalinsu iyayensu yan sokoto ne amma dukkansu a hadejia aka haifesu ta jigawa hakan yasa suke indigene tunda sun samu by birth. Nidai hankalina yana kan Raudha da nake feeding tana ta bani labarin Uncle Abbas. Can sega Abba ya shigo, har kasa Maman Raudha ta tsugunna ta gaisheshi ya kirani parlonshi. Tunda nasa kaina nasan Dr Kwaccido na ciki saboda kamshin turaraenshi daya baibaye ko ina Na parlon. Abba fita yayi so daga ni se shi se Raudha data biyoni tana ta tsalle tsallenta. Cikeda damuwa yace “Me yake damunki ne kin kalle ki kuwa? Nasa ki taho gida ki huta amma you are still falling sick. Y kike so nayi ne?” Da sauri na dago kaina ina kallonshi, ya dage girarshi yace “I care of course! My heart flutters whenever I see you or i remember you. Can you do me the favor of marrying a bachelor like me?” 9 Rate the page on a scale of ten 3 Ayshatuuuu ❣️Ban taba jin gidan mu ya isheni ba se wannan karan, seda naji inama nayi zamana a dutse ban dawo ba. Tunda nan din dana dawo dan samun relief kwatakwata abin ya gagara, se ma karin wani tension din da na samu. Washegari, babu kowa gidan dukkansu sun tafi hakan yasa na fito da wurwuri na shiga kitchen dan hada breakfast se na samu Asiya ta fara hakan yasa nayi joining dinta muka kammalla. Ina cikin wanke hannu na cikin sink naji maganar Abba da Yaya Halifa, cikin sauri na fito dan ranar nake tunanin zuwa gidan shi. Suna zazzaune na samesu, gaishesu na fara yi sannan na tambayeshi su anty Zannira yace min dukkansu suna lafiya. Munata hira yawanci shi da Abba ne sede nayi ta dariya a haka Ummaah ta same mu. Gefen Abba ta zauna suka gausa da Yaya halifa sannan na gaisheta nima, amsa min tayi normal kamar ba jiya ta tara min jamaa ba. Nayi tunanin inama wani yayi min abinda Ummaah tayi min, inaga nida shi har abada amma Ummaah Ummaah ce tafi gaban komai, everything she said I consider it as frustration.+ Key Abba ya miko min yace “Auta yau shekararki ashirin da shida, Allah yayi miki albarka. Ga gift dina” Gaba daya na manta da wai yau birthday dina, tabbas girma ya hau kaina I couldn’t believe cewar I’m 26 years already. Kallon key din nayi na mota ne, ai wani ihu na buga ina fadin “Abba mota? Abba nagode Abba Allah ya saka maka da mafificin alkhairi” Na juya gurin Ummaah data tsira min idanu tana kallona, da murana na mika mata key din nace “Ummaah kinga gift din Abba” Maimakon ta karba se cewa tayi “Haba Sir…” Dake haka take kiranshi a matsayinshi na tsohon dan sanda “…ta yaya zaka siya mata mota? Mu da muke son ta kawo miji tayi aure” Gaba daya se naji murnar ta dauke min, dukkan mu muka saka mata ido muna kallonta da mamaki, nidai inajin anya Ummaah ta ce kuwa? Is she really my mom ko wani ke zugata haka? Abba yayi murmushi yace “Madam, meye hadin siya mata mota da samun mijin aure? I see nothing” “Dama baza kaga komai ba amma ai wannan maza tsoron tunkarar ta zasu dinga yi, gata likita ga mota” Dariya sosae Abba yayi sannan ya dubi Yaya halifa kafin ya kara kallonta fuskarta a hade kamar hadari, yace “Halifa, kaji zancen mamanka fa. Can you imagine? What if ta dalilin motar zata samu miji. Kema mutane sun fara miki wannan hudubar? Aure ai nufin Allah ne kuma ko shekara arba’in Asmau ta kai babu miji bazan takura mata ba, saboda abu daya na sani everything lies on it timing!” Daga wannan maganar abin mamaki Ummaah ta fara kuka wai Abba ya fada mata magana sannan wai shi yake daure min wani guri shiyasa naki bada hankali nayi aure. Gaba daya hankali na yayi masifar tashi, na dinga bata hakuri ina lallashi amma ko kallona batayi ba, se na fara kuka nima naji gaba daya tamkar an kifar min da duniyar da nake ciki. Yaya Halifa yasa ni muka fita yana ta bani baki tareda nuna min komai zai wuce. Da yamma naji gidan ya isheni, kamar ana hadamin wuta haka na dinga ji, babu sauki naje nace da Ummaah zanje gurin Adda Sa’ada, bata hanani ba se cewa tayi “Gwara ki dinga fita ko kya samu mashinshini.” Har na tafi ina mamakin Ummaah, mota ta kirar peugeot 206 blue na bude nayi addua sannan na tafi. Adda Sa’ada tayimin murna sosae, da muka kebe na dinga fada mata abubuwan dake faruwa , tayi ta bani hakuri akan lokaci ne sede I’m frustrated na gaji hakanan, bansan yaushe ne har laolacin zai zo ba. Da daddare bayan na idar da sallar ishai na tafi parlon Abba dama seda na tabbatar Ummaah na dakinta sannan naje. Yana zaune ya gama cin tuwo na shigo tareda zama inda ya nuna min. Shiru nayi na rasa me zance masa saboda nauyinshi naji. Can yace “Asmau ya akai ne?” Kaina na girgiza nace “Abba gobe zan koma dutse sa…” “Saboda me? Ba kince min two weeks zakiyi ba, is just five days kawai fa” Se na rasa me zance masa tunda ni dai I’m not used to karya amma bana son ce masa pressure Ummaah ce ke damuna tunda dazun naga sun samu sabani akaina. “Asmau, Rukayya ce ko? Ita take damunki akan aure ko? Kada ki damu kinji ko komai lolaci ne, kada kiji haushinta nata salon kilawar ne. Kibar tafiya dutse ki kara hutawa kinji.” Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na tafi nayiwa Ummaah sallama. Har naje bakin kofa se naji tace “Asmau zo nan” Jiki a sanyaye na koma na zauna kan carpet, gaba daya mun zama sirikai nida ita , idan ina tare da ita se naji wani irin nervousness na damuna. Drawer ta janyo ta fito da wata leda ta aje batace komai ba haka nima se shiru nayi ina fidgeting da hannuna. Asiya babu jimawa ta shigo da wani kasko cikeda ga garwashi, ajewa tayi a gurinda babu carpet saboda kar ya kone. Tana fita Ummaah ta mike tareda min alamar na bita, hakanan babu yadda zanyi na bita, wasu itatuwa ta ciro a ledar ta watsa cikin garwashin take kuwa wani mugun hayaki ya tashi, seda gabana ya fadi. Haka tasa Na tsugunna ta samu wani thick towel ta lulluba min. Na dinga tari ga mugun gumi da ya dinga karyo min Amma Ummaah seda nayi more than 10 minutes a haka sannan ta yayeni. Dana mike se layi har seda ta rikeni sannan ta hada min ruwan wanka shima wasu magunguna ne a ciki amma ko uffan bance ba haka nayi, ina fitowa ta bani mai na shafa sannnan ta sallamrni na tafi. Seda na jera kwana biyu kullum se anyi sau biyu kafin wani lokacin na fita a hayyacina, na rame na lalace nayi duhu. Babu arxiki na cewa Abba tafiya zanyi dan bazan iya zama ba. Shima duk abinda ake ya sani dan tuntuni na fahimci maganin farin jini ko na samun miji akemin, i cant afford losing my iman saboda hakan. Da naje yiwa Ummaah sallama tace min “Asmau akwai bikin Amratu, ina fatan zakizo” Kaina na gyada amma deep down nasan wallahi bazan zo ba dan na rigada na rantse bana son zuwa na zama topic of discussion. Da motata na tafi, wannan shi ne karon farko dana fara tuki me nisa and alhamdulillhi naje lafiya. Dakin kyaftun na wuce bayan na tsaya na zubarda magungunan da Ummaah ta bani cikin incinerator sannan na shiga. Tana zaune ta gama girki kenan na shigo nayi wujigawujiga dani kamar an jefoni. Tace “Twin meye hakan? Me yake damunki?” Zama nayi nace “Bani abinci kede” Babu musu ta zubomin shinkafa da wake da kifi se dressed salad da zobo, nasan gandar kyaftun hakan yasa nace “Kinyi Bako ne?” Fuskarta ta kwabe tace “Dr Lamin ne yayi lunch a gurinna” Kallonta nayi for some minutes kafin na cigaba da cin abinci na , seda na gama tas nayi wanka na dakko zani daga cikin wardrobe dinta na daura hade da top na dawo na zauna nace “Twin, meye tsakanin keda lamin abin yafi karfin kawance sede wani abin” Murmushi ta fara kamar na mata albishor tace “We’re dating har yaje Bama” Idanuna a waje , se kuma na saki murmushi nace “Alhamdulillah, yafi muku ai kun zauna da kuna raina mana hankali” Hakanan mukai ta hira har ta shirya zata tafi night duty sannan taga motar dan bance mata da ita nazo ba da dauki bazai batta muyi hirar ba. AyshatuuuuuuChromic din hannuna na aje sannan aka miko min gauze na rufe muka rufe da plaster sannan na kalli kowa tareda sakin murmushi bayan na cire google din idanuna nace “Alhamdulillah, nice job everyone!” Dukka team din murmushi sukaimin kowa yana kokarin karasa abinda ya kamata, Apron na cire na wulla cikin bin, fitowa nayi tareda cire mask din dake fuskata na danyi mika sannan na tafi lounge dinmu dake cikin OT bayan na karba patients folder a gurin chief anesthetist naje na zauna kan cushion ina documenting aikina. Koda na kammalla banida wani aiki daya rage min hakan yasa na zauna tareda lumshe idanuna kamar wadda take bacci amma ba baccin nake ba, ina naga idon bacci? Matar da ko da daddare se nayi da gaske baccin ke daukeni balle yanzun ido na ganin ido, da dinma guri na samu amma yanzun babu halin hakan, dan damuwar da nake ciki kadai ta isa ta samin insomnia. Bansan adadin lokacin dana dauka a hakan ba se naji an bubbuga min kujerar da nake kai hakan yasa nayi firgigit na bude idona da sukai ja. Dr. Fadima ce tana tsaye ta zubamin ido, zama na gyara tareda kirkiro murmushi nace+ “Doctor yaushe kika shigo?” Zama tayi kujerar dake facing dina se center table dake tsakaninmu, coke ne a hannunta chilled dan kadan ya rage yayi kankara. Tunda nake ban taba ganin coke addict irinta ba, kullum muka hadu se nayi mata fada amma sede tayi dariya kawai tace ai ina exercise ko kuma ace min inada glucometer. Haka dai take tana da kirki tare mukai medical training dinmu a Bayero. “Dr Shahada, me yake damunki?” Dan murmushi nayi nace “Me kika gani? Am I looking terrible?” “More than” Ta fada tana hararata, murmushi na kumayi nace “Kinsan yadda rayuwa take, mutum baa rabashi da matsala sede addua kawai” Gyara zama tayi tace “Amma naki ya fito da yawa, kowa ya kalleki yasan kina cikin damuwa. Kinga yadda kika koma kuwa? Idanunki are all sunken, you hardly concentrate.” Dan runtse idanuna nayi sannan nace “I’m trying” Shi kadai ne abinda ya fito daga bakina, kanta ta gyada tace “Anjima ki shirya tunda baki komai se mu fita, you need a fresh air” Kaina na gyada nayi mata godiya sannan muka koma hirar aiki anan take bani labarin MD ya kusa retire, duk se naji babu dadi dukda bansan shi personally ba amma mutumin yasan me yake, i happened to attend a seminar dashi. Da yamma kuwa muka fita wani hanan hangout, mukai ta hira da ita sannan muka ci abinci danni ko lunch banyi ba, dama kyaftun ke takurani naci, to taje off se ni daya. Sahad mukaje mukai shopping sannan muka koma asibiti. Se naji tamkar ta bani therapy ne. Washegari saturday, kuma shi ne ranar daurin auren Amratu, tun jiya akai kamu da mothers’ eve dama bazanje ba, koda su Ummaah suka kirani nace ai aiki ya cabe min bazan iya zuwa ko ina

Chapter 10 of 18