Share this page
ta hada ruwan, Aikuwa da na fadawa aya zakinta. Ina nan kwance Sega Nu’aimah ta shigo da kwanukan Abinci, a gabana ta aje ta gaida ni sannan tace “Adda Asma’u, Inna tace Wai ki fada idan kina son wani abu” Kaina na girgiza nace “I’m ok da hakan, kirawo min Rayhana muci” Kanta ta gyada ta fita, kwanukan na bude Abinci Kala uku, kwadon rama da first, ga sachet water me sanyi da Fanta. Rayhana Tazo muka fara ci naji isowar mutanen Adamawa, Umma Falmata da tawagar ta. Babu Wanda ya tashi cikinmu seda muka gama sannan muka je muka gaida ta. Wajen shida muka shirya mukaje gurin kamu. “A Ina zaki kwana? “ Ummaah ta tambayeni bayan an gama kamun, Adda Sa’ada tace “Kiji Ummaah da bata Baki Kema kin sani ai” Dariya nayi nace “Allah Ya bamu alkhairi “ Daga Haka na koma gidan Inna Ade, parlonta duk Anyi shimfida, da yawa mutane sun Fara kwanciya, tsatsallake su nayi cikin dakin, ina zuwa na tarar Inna na sallah babu kowa kan gadonta, kwabe kayana nayi na canja sannan na kwanta akan gadon, ni nasan ba bacci nakeji ba kawai dai hutawa nake sonyi ga Inna idan ta Fara sallah har Se mutum ya gaji da jiranta. A hankali bacci ya Fara cin karfin idona, ban jima da baccin ba naji muryar Adda Fauziyya tana tashina, tashi nayi na zauna raina ya baci nace “Adda na Fara bacci fa” Harara ta tayi tace “Na sani ai, sakkowa zakiyi ki wuce ki samu wani gurin ki kwanta” “Saboda?” Inna ta fada, Ashe ta idar da sallah, Juyawa Adda Fauziyya tayi tace “Inna wallahi bana iya kwana a kasa dole se a gado, idan ba Haka ba da kyar nake tashi” Tsaki Inna tayi tace “Shashanci kenan, ke Kawata koma Ki kwanta, ke kuma Fauziyya kiyi ta tsayuwa amma gadonnan bazaki haushi ba” Kawai se ta Fara kuka Wai Inna bata sonsu, ni take so to itama jika ce, Kaina na girgiza Dan halayen Adda Fauziyya basida kyau. Komawa nayi na kwanta, zuciyata babu dadin abinda ya faru. Washegari aka daura aure, wajen laasar na shigo dakin Inata mika saboda gajiya, wata Hamma na buga daidai shigata dakin Inna, cak hammar ta tsaya saboda abinda na gani a gabana, Yaya Mukhtar yana zaune ya baje yana cin Abinci. Dagowa yayi ya kalleni sannan ya saki Murmushi tareda kallon Inna yace “Inna Fara yar shehu ce haka, Aah yarinya ta girma” Bata rai nayi na karasa shigowa ciki na zauna saman gado nace “Kaima ai ka girma” Dariya yayi yace “Still with the futsara, Ashe baki canja Hali ba” Se kuma nayi dariya na gaisheshi, ya tambayeni Ya makaranta, Inata jin dadi nace na gama secondary dina. Se kuma mukai Shiru, na kwanta inajin yana ta cewa Inna yadda na girma, na zama Yan mata. “Ko dai kana ciki ne Mukhtar? “ Dariya yayi ya mike yana fadin “Inna kenan! “ Ko kwakkwaran motsi kasa yi nayi, zuciyata ta Fara ayyana Ko dai Yana sona da gaske ne? Se nayi Murmushi saboda wani excitement da naji Ya lullube ni lokaci daya. Yaya Mukhtar sa’an Yaya Halifa ne, shi ne Babban yaron Umma Falmata, so a Adamawa suke shiyasa Haduwa dasu ba sosae ba, musamman shi da bai dade da dawowa daga Estonia ba. Mikewa nayi na zauna dan naji fitar Inna, kallon gurin da ya zauna nayi sannan na sake wani murmushin na canja kaya na Kara fita. AyshatuuuAna gama biki muka koma Kano, Abba yasa Yaya Halifa yayi min registration a gateway computers inda zanyi certificate, saboda kada na zauna bana komai. Babu laifi naji dadin wannan shawarar. Ya zamana morning classes ne, 9am to 12noon, da yamma kuma naje islamiyya, so I’m always kind of busy hakanan. Ranar jumaa ina ciwon ciki ko makaranta banje ba, Ummaah ta shigo ta kawo min magani da ruwa nasha, ban wani jima ba bacci yayi gaba dani bani na farka ba se bayan Sallar laasar. Ina tashi nayi wanka na canja kaya sannan na fito parlor. Da mamaki a fuskata ganin Yaya Mukhtar a zaune shi da Yaya Halifa suna hira. Basu lura dani ba seda na zauna Kan cushion din dake gefen Yaya Halifa sannan yace “Asma’u rikici” Dan Murmushi nayi nace “Yaya Ina wuni? Yaushe kazo? “ Kanshi Ya Dan shafa se Murmushi yake yace “Lafiya lau, dazun nan” Kaina na gyada tareda tambayarshi su umma Falmata, sannan Yaya Halifa ya tambayeni saukin jiki. Da daddare Ummaah tana parlon Abba, Se ni daya a parlor, na kudundune kafafuna, dukkan hankalina yana kan kallon da nake, naji sallamar Yaya Mukhtar, dagowa nayi na kalleshi, murmushin nan nashi Yayi min, nima na mayar mishi inajin yadda Wasu knot ke kulluwa cikin cikina, kasa nayi da kaina har ya zauna gefen kujerar da nake, ya aje mug din hannunshi akan center table din yace+ “Me kika kalla haka?” Kallon allon TV din nayi, Kamar ban San me nake kalla ba nace “Uhmmmm! Korean drama ne “ Kanshi Ya gyada yace “I see, amma how do you differentiate between cast din?” “It’s simple ” na fada Ina gyara zamana nace ” Basu kama fa as long as you continue to watch film dinsu zaka gane each of them” Kanshi Ya girgiza yace “I doubt much, saboda komai nasu iri daya ne fa” Murmushi nayi bance komai ba, saboda idan na biye shi I’ll miss some important scenarios. Shima kamar yasan thought din dake running cikin raina bai sake magana ba, Se maida hankalinshi da yayi akan kurbar only God knows what dake cikin mug din. Nima duk se hankalina ya rabu biyu, rabi yana ayyana abinda yazo yi gidanmu, Dan dazun naji Ummaah tana fadawa Baba Zulai zancen zuwanshi, akan a Kara Abinci dashi. Rabin hankalina yana kan kallon da nake. So ba komai na fahimta ba, har episode din ya kare, Se kawai na mayar Aljazira Dan na Kalli news, wannan yana daya daga cikin horon Yaya Halifa a Kaina. Shirun da mukai se yasa atmosphere din ta zama so dull and tense, gashi ina jin idanunshi a Kaina so se na Fara wasa da fingers dina, at least I want to break the silence. But how? Na tambayi Kaina, “Ehn… Yaya Mukhtar so Hutu kazo yi kenan?” Kanshi Ya girgiza yace “I’ve been employed ne” Take faraa ta, ta karu nace “Oh! Congratulations, amma nayi maka murna “ Wink yayimin, Idan da yasan yadda wink dinnan ya taba ni, bana tunanin zai Kara min, ji nayi kamar zanyi melting cikin kujerar, na fada muku how Charming Yaya Mukhtar yake? Kyanshi kadai will make someone fall for him over and over again. Jinin Fulani Dan Mahaifinshi asalin 0 Adamawa ne, so kana kallonshi kaga hakan. “So ya makarantar, medicine dinne? “ Kaina na gyada nace “Shi ne, nayi passing Post UTME kuma score din yayi tallying “ “Mashaaa Allah what a great news, so mun kusa samun Doctor in the family kenan? “ Dan blushing nayi sannan na kalla agogon dake kafe a parlor, idanuna na dan zaro nace “Bari naje na kwanta, its late” Hannunshi ya watsar cikin iska yace, “Oh nima bari naje na kwanta” Daga Haka na juya zuwa daki amma ban kai ga shiga ba naji yace “Asma’u! “ Juyawa nayi na kalleshi, Murmushi yayi min sannan Yayi min waving yace “Sweetest of dreams” Take naji wani blood rush gaba daya jikina, hannuna nasa na dafe cheeks dina saboda wani Hot da naji Sunyi, ban bashi amsa ba na shige ciki, kofar na mayar na rufe sannan na jingina da ita, ji nake kamar faduwa zanyi, tamkar kafafuna bazasu dauki jikina ba, na jima a tsaye a gurin Inata Murmushi sannan na janye jikina Na fada gado, ranar tsabar farin ciki da annashuwa ko addua banyi ba nayi bacci balle canja kaya. Se wajen past two na farka a gigice, seda nayi yadda na saba sannan bacci ya daukeni. Washegari kamar yadda na saba, bayan nayi sallah, wanka nayi na Nemo kaya Marasa nauyi saboda yanayin zafi Ya Fara shigowa. Kitchen na wuce na kwaba batter Banana pancake na Yaya Halifa, baifi 4 pieces nayi ba se abincin su Abba da Ummaah, babu wani Yawa abincin amma har Yaya Halifa yazo cin nashi ban gama ba. “I wonder how you will become a doctor, Dan nasan watarana tabbas kafin Ki yunkura patient zai mutu” Tura bakina nayi Dan wannan furucin kullum se najishi, sede idan banyi wani abu slow ba. Zama yayi ya ci sannan Yayi min sallama Ya tafi office. Ina kammalla breakfast dinsu Abba nayi parlonshi dashi, fitowarsu kenan, na gaishesu sannan na aje komai na koma kitchen Dan dafa noodles, Ina cikin duba wayata naji kamshin Elope, Wanda nasan mammallakin kamshin nan Yaya Mukhtar ne, se na samu Kaina da kasa Juyawa balle mu hada ido. Kaina na gefe nace “Yaya Mukhtar an tashi lafiya? “ “Lafiya lau Princess” Da sauri na kalleshi sede to my utmost amazement Bama kallona yake ba, hankalinshi yana Kan lemun daya shigo dashi, I was kind of disappointed. Amma Se nake ganin Anya ban zake ba, anya am I on the actual and right path? Allah kadai ya sani amma nasan one thing, akwai wani abu da nakeji a gameda Yaya Mukhtar, Wanda a hankali ya Fara gina kanshi cikin zuciyata. Ban taba tunanin ni sokuwa bace Ko kuma nace wawiya Se akan Yaya Mukhtar. Shidai bai taba cewa yana sona ba, sede yadda yake shiga al’amurana is different than any other. Daga ranar tare muke fita, office dinshi a cikin Depot yake amma Se ya kaini har school sannan ya wuce abinshi. Wannan yasa muka saba sosae dashi, indai muna tare kuma mutane suna tare damu to tabbas se Kasan Inada wani special feelings akanshi. Ranar da admission list Ya fito, nayi murna Kamar zan zauce,duk wani me sona seda ya tayani murna na samu Medicine , Rayhana ta samo biochemistry dukka a Bayero. A ranar ina kwance a dakina, nida Adda Meeyna Tazo, Sega Luba me mana Shara Tazo tace Nazo Inji Yaya Mukhtar, ko amsata banyi ba na mike zan tafi, wani fizgowa Adda Meeyna tayimin tace “ke dallah zo, daga ya kiraki ke kuma busy body kin wani tashi, at least take your time mana, kija class dinki. “ Dariya nayi nace “Kaji Adda Meeyna, is not as if saurayina ne fa” Dariya itama tayi sosae tace “Lallai yarinyar nan, wa zaku mayar Yara daga ke har Yaya Mukhtar din, ko makaho ya shafa yasan akwai magana “ Zamana na gyara nace “Dan Allah sona yake? “ Se tayi sakale tana kallona, sannan tace “To Dama baiyi proposing ba amma har kike wannan zakewar. Lallai Asma’u, ki maida hankalinki fa. Ba ayiwa maza haka” Tabe Baki nayi jikina Yayi sanyi, nace “Nifa kawai mutunci muke dashi babu wani abu” “Mutunci ba, ni ban taba ganinki kin saki jiki da mutane kamarshi ba, to ki saurareni Dan abinda jikinki da idanunki ke fada you’re deeply in love with him, ki zauna kiyi sorting out kafin dare yayi miki. “ Bance komai ba na fita kiran amma Kamar an zare min laka haka naji, duk yadda nake daukin abin se naji Ya fita akaina and I found myself questioning myself me nakeyi? Da gaske sonshi nake? Bansani ba tunda gaba daya na shiga rudani. Ayshatuuu*Ok, let’s talk about the plaque that’s threatening the whole globe, the famous Covid- 19. It’s something all of us should know. Precaution is better than curing, wash your hands frequently and pray hard. May Allah Azzawajal ease all our sufferings…..Don’t forget to pray for those Doctors, Nurses, Midwives and all health care team, know that their lives are at stake.* “Congratulations Asma’u! Nayi matukar farin ciki da jin kin samu admission. Ina fatan zakiyi amfani da damarki, kiyi kokari dan Kinsan irin hard journey dake gabanki, I’m sure Kinsan Medicine ba wasa bane” Kaina na gyada nace “Na sani Abba, Inshaaa Allah bazan Baka kunya ba” Murmushi yayi yace “Idan kikayi haka zanfi kowa farin ciki, kuma kin taimaki Kanki, saboda duk abinda kika zama may be bana nan balle na Mora, amma nasan nayi miki Gata, inason kisa a ranki Dan Kanki zakiyi Karatu bawai ni zakiyiwa alfarma ba”+ Kanshi Ya girgiza yace “No! Ni na rigada nayi nawa, na riga na taka matsayin dazan taka, Yanzun filin naku ne. Allah Ya bada saa “ Ya fada yana daukar remote, Amin na amsa mishi sannan nayi masa sallama Dan naje na kwanta, Har na kai bakin kofar parlon, naji yace “Asma’u “ Dawowa nayi tareda zama inda na tashi, “Ahaf kinga na manta, shiga bedroom dina Ki dakko min wata jaka” Tashi nayi na shiga ciki, abinka da Ajiyar wani Se ban gani ba, karshe da kanshi yazo Ya dakko Jakar yana tsokanata Wai na Fara tsufa. Nidai Murmushi kawai nakeyi, sabuwar Apple system da sabuwar Samsung ya bani a matsayin gift. Nafi mintina biyar Ina mishi godiya, saboda Ina son surprise yana kayatar dani. “Se last thing dazan fada miki shi ne Maganar aure, zakiyi aure amma ban yadda ki kawo min wani namiji ba Har Se kin kammalla pre-clinicals dinki, a lokacin I can marry you out in peace. Is that OK? “ Dukda ba haka Naso ba, Dan a lokacin babu wani abu dake birgeni irin naga nayi aure, akwai Wanda muka gama secondary dasu su hudu duk Sunyi aure so I always feel like inama fate dina irin tasu ce. Kuma koda Zaa kashe ni akan dalilin da yasa nake son aure bansani ba, ni dai kawai nayi aure. Bayan sati uku, na gama registration da komai Se Fara attending lecture, Ummaah tayimin sababbin dunkuna, Yaya Halifa ya siyo min dukkan Wasu stationery da nake bukata, in fact kowa supporting dina yake a gidanmu, kowa seda yayi participating in one way or d other. Na gama hada noodles Kamar yadda ya zame min jiki, duk dare ita nake ci as dinner, Ummaah Har ta gaji da fada, Har seda tace Yaya Halifa idan yaje shopping din groceries ya daina hadowa da ita, amma haka zan aika a siyo min a shago, Dan Dama bawai inason in dinga cin brand daya, nafi son Yau naci Cherie, gobe indomie jibi Dangote. Different taste you know! Kan kitchen island din na aje plate din sannan na janyo wata stool na zauna akai na Fara ci, nayi rabi naji isowar Yaya Mukhtar, wani irin race Ya Fara ziyartar jikina, zuciyata tana ta murna jin kamshin turarenshi, idanuna wide open saboda daukin ganinshi, haka kunnuwana sun kagu suji ya furta wani abu. Duk hakan ya faru saboda Yayi sati daya baya gida yaje Adamawa ganin gida, Se yau ya dawo kuma bamu hadu ba, saboda ban wuni a gidan ba naje gurin Adda Maryam acan na yini. Takunshi a nutse ya shigo, amma bai karaso inda nake ba, Se ya tsaya, dukda son kallonshi da nakeyi Naki daga Kaina amma nasan a tsaye yake kuma kallona yake, I can feel his eyes all over me. Ga kamshin turarenshi dake kokarin zautar dani. Spoon dina na aje tareda tura plate din na mike hannuna na rikeda Hot lime juice. STORY CONTINUES BELOW “Asma’u! “ Dagowa nayi a nutse na kalleshi kafin na sake Murmushi nace “Yaushe ka shigo? Yaushe ka dawo?? “ Gyara tsayuwarshi Yayi yace “Na amsa daya bayan daya? “ More like a question, hakan yasa na gyada Kaina ina Murmushi Kamar wata sokuwa. “Dazu da safe Kinje gidan Maryam. Sannan na jima da shigowa amma banyi magana ba” Kaina na gyada nace “Ohhhhhh! I see, ya ka baro kowa da kowa? “ “Dukkansu lafiya” Ya bani amsa a takaice, ko me yayi tunanin kawai se ya fice, so tunanina zai dawo se na koma na zauna, amma nafi mintina goma babu shi babu dalilinshi. Dan Tsaki nayi na fito na tafi daki Inata mita a raina, Raina Ya baci saboda Ina ganin dan me yasa zai fice ba tareda Yayi min sallama ba. Se dana kwanta se naji Kamar anya Inada ounce of hankali a tareda ni? Is not as if Mukhtar yace yana sona ne amma ni me yasa nake wannan abin. Juyi nayi tayi akan gado Inata jin haushin Kaina, tareda tuhumar Kaina akan rashin sanin darajata. Inda kuka ga yadda nayi sorting abin zakuyi tunanin Bazan kara kallonshi ta fuskar so ba amma da safe muna Haduwa wajen gaida Ummaah naji Bazan iya resisting ba, tamkar me zuba min charm a jikina hakan nake ji. ~BUK~ Sabuwar rayuwa kenan dana Fara, level one Dama kowa yasan basics ne, abinda aka koya maka a secondary school ne, though Malaman mu a secondary zasuce, if you go to university, you will go deep. A university ace, this has already been taught during your Olevel no need to go deep. Kunga Kamar kowa yana gudun responsibility dinsa ne. First week dinmu duk ya kare a introduction ne, seda muka shiga second week sannan na Fara karbar citta, kowanne course Se ka cinyeshi tas babu wani compromise, idan ba Haka ba it’s either you change department or you get withdrawn. Shi ne abinda nafi Tsoro a rayuwata, bana son failure bana kaunarta. “Ummaah hostel zan koma” Na fada mata lokacinda na dawo da yamma a gajiye, ga Yunwa Dana kwaso. “Me yasa? “ Kaina na dafe nace “Ummaah wallahi wahala nake sha, kuma na dawo a gajiye Zaiyi wahala nayi Karatu sosae” Kanta ta Jinjina tace “Zanyiwa Abbanki da Halifa magana idan yaso se naji yadda zaayi” Se naji wani sanyi ya ratsa ni at least gwara ayi hakan. Ban kara sati Ina day ba, gaba daya aka tattara na koma hostel, to hakan se yafi min sauki, ga muna tare da Rayhana se na jini safe. Wani yammaci ina kwance a daki, babu lecture din yamma so Karatu nayi, na solving Wasu equation na 1301 sannan na dan kwanta na huta, at least kwalkwalwata ta Dan huta daga wannan charge data dauka. Nayi Shiru Ina bin yan dakin da kallo kowacce tana abinda ya dace. Wayata ta Fara ringing, janyota nayi inajin waye zai takura min ne? Amma ganin sunan Yaya Mukhtar na yawo a sama yasa babu shiri na tashi na zauna ina daidaita kaina, “Assalamu alaikum “ Na fada Ina tabbatar da muryata tayi yadda ya dace, shima amsa ni yayi, se naji tamkar wannan ne Karo na farko dana Fara jin muryar shi “Ina bakin hostel dinku” Ya fada yana katse min tunanina, mikewa nayi zaune nace mishi I’ll be out In a jiffy. Kashe wayar nayi na janyo wani blue black skirt na zura, Dama akwai long sleeve top Fara a jikina, Se kawai na hijab kato na saka sannan nayi waje. Amma zuciyata se kwabata ta take, Tana tuna min da how reckless nake acting. Sede mafi rinjayen Zuciyar hakan yake so sannan Sauran sashen jikina sun amince da hakan. Kuma kowa yasan idan zuciya na son Abu to Tana acting kafin kwalkwalwa ta ankare, to anawa case din Hakane, Se nayi abu se daga baya inxo Inta jin haushin Kaina. A waje Kamar yadda ya fada na iskeshi, yana zaune kan motarshi yana danne danne a wayarshi, Yayi kyau sosae, Dayake shi ba ma’abocin saka kananan kaya bane, yafi ga manyan Kaya, Dan kullum a cikin kaftan yake, ko Dan yasan suna mishi kyau ne Oho! Fuskata dauke da Murmushi na iso inda nake nace “Yaya, Sannu da zuwa” Aje wayar yayi ya kalleni sannan yace “Yawwa, ya lecture din? “ “Alhamdulillah! “ Na fada sannan mukai Shiru, Raina Ina ayyana se yaushe zai ce yana sona ne? Se yaushe, na gaji I can’t wait any longer kuma. Muna ta taba hira har Rayhana ta dawo, dakinmu taje anan akace mata na fita, tasan tabbas ina tareda Yaya Mukhtar hakan yasa ta fito. Tundaga Nesa take tafa hannunta har ta karaso tace “Ikon Allah! Wai ku Meye tsakaninku ne? “ “Me idonki ya gane miki? “ Na fada Ina kauda Kaina amma kafin kalaman su gama sinking cikin kanta ya ce “Babu komai tsakaninmu, we’re just cousins…. “ Bansan nace “Cousins!?” Na fada muryata da rauni a ciki, Murmushi yayi tareda dirowa daga saman motar yace “Zan wuce, akwai sako gurin Ummaah? “ Da kyar na iya girgiza kaina Dan ko amsa balle sallama kasa bashi nayi, na wuce inajin tamkar zuciyata zatayi gobara Haka naji. “Yaya Mukhtar tsakaninka da Allah me Kakeji akan Asma’u? “ Aje wayarshi yayi a vacant seat din gefenshi sannan ya kalla Rayhana yace “Kinsan kina damuna Ko? “ Lumshe idonta tayi tace “Yaya Mukhtar, be serious Dan Allah, kana sonta ko kuwa? “ Kanshi Ya shafa yana Murmushi yace “Amma Kinsan tambayar nan tanada wahalar amsawa Ko? “ “Ka bani amsa, ina maka magana ba Yaya da kanwa ba, ina maka magana matsayin kawar Asma’u “ Dan Murmushi yayi yace “I see, I’m flirting with her, shikenan? “ Kasa Matsawa tayi Kawai tana kallonshi sannan tana nazarin abinda ya fada, can tace “Baka kyauta ba, kuma kusan how reckless wasa da Zuciyar mutum take Kamar kana wasa da ranta ne. Kafi kowa sanin dai Asma’u na sonka, Da har bata iya fahimtar inda kasa a gaba, Dan Haka idan kasan manufarka bata alkhairi bace then allow her and let her be. Kadai tuna Kanada kannai mata! “ Tana gama fadar Haka ta wuce shi a gurin, yayi shiru yana tunanin karfin Hali irin na Rayhana, amma wannan shi ne least abinda zata iya! Ayshatuuu!Assalamu alaikum! Hi pipu. I was in a scenario today, I wanted to leave Kano to Jigawa because of the sudden boarder shut by the states. When I went to park, I spent more than two hours no vehicle, when it came you have to pay one thosand and above, what I noticed is that, people are just waiting for an opportunity su uzzurawa mutane, believe me wallahi in this plaque and Pandemic era, idan baka tausayawa talaja 🎶….So let me be the one and only, can I be your friend and honey, I’ll be your better man………If you’re my girl I’ll take you round the world, I’ll take you places where you’ve never ever been before, so give me your…… 🎶3 Wakar da kullum Lubna se ta jita a dakinmu, amma da yake I’m not a fan of Nigerian music, ban taba fuskantar abinda Psquare ke fada ba se yau, may be hakan yana da nasaba da zafin da zuciyata keyi min, amma jin wakar se naji wani bakon yanayi yana mamaye min jikina, tamkar ana fizgata Ina jin wani tsumammen abu ya karade dukkan zuciyata. That’s Love, a hankali na karasa gadona na kwanta Ina kara nutsuwa da bude kunnuwana inajin wakar, har ta kare. Ta kara maida ita, tanayi tana miming dinta cikeda nishadi. Anty Zubaida itama roommate muke, tana zaune gefen gado tacr “Nikam Lubna shi wannan Hayaty yaushe zai tura ne? Wannan ban taba ganin irin soyayyar ku ba” Idanuna na mayar kan Lubna da ke ta Murmushi amma ta kasa magana, I’m sure tuna shi take. Se naji Kamar nayi kuka, ko se yaushe zanji abinda ake ji? Ko se yaushe zaa furta min, a so ni kamar yadda nake so? It might never happen Kila?+ Shigowar Rayhana a hargitse yasa na dago ina kallonta, zama tayi gefena tace “Zo ki rakani” Mikewa nayi na dauki hijab din dana aje muka fita bayan nayiwa su Anty Zubaida sallama, a kofar hostel muka tsaya, hannunta cikin nawa amma jikinta rawa yake, hakan yasa na dubeta nace “Me yake damunki, jikinki rawa yake fa? “ Kanta ta girgiza ba tareda ta furta komai ba, amma har lokacin jikinta bai daina rawa ba, gaba daya se naji jikina Yayi sanyi, tunda baifi two hours muka rabu ba, amma bansan me ya kada ta haka ba, it’s unlike her saboda ita mutum ce me taurin zuciya, kafin kaga abu ya saka ta cikin Haka zaka dade. Na bude baki da niyyar kara tambayarta se naga motar Abdul saurayinta Yayi parking a gidanmu, hannunta na saki daidai fitowarshi, Ko tsokanar da ya saba min baiyi min ba Illa, bude mata front seat da yayi ta shiga sannan ya bude min yace “Bismillah” Kallonshi nayi Amma Se yayi saurin zagayawa Ya koma seat dinshi, baki daya Kaina ya kulle na kasa tunanin abinda yake faruwa. Shiga nayi na zauna, ina jinshi suna magana kasakasa shida Rayhana, bana jin su hakan yasa na rike wayata gyam a hannuna, and na rigada nayi concluding cewar nothing is right, nothing is in place, dole akwai abinda ke faruwa. Jin anyi parking yasa na dago, se ganinmu nayi a kofar gidan mu, cikin sauri na bude kofar saboda yadda naji wani mugun Tsoro ya shige ni, Ashe banga komai ba saboda kofar gidan iya ganinka motoci ne Anyi parking dinsu, ta karamar kofa na shiga seda jiri Ya kusa yar Dani saboda gawa dana gani cikin makara, a ajje. Waye ya rasu? Na tambayi Kaina Sabida Abba da Yaya Halifa na tsaye sede kallonsu kadai ya isa yasa Kasan cewa suna cikin Tashin hankali. Tsayawa nayi na kasa gaba

Chapter 3 of 18