Share this page
kayannan ki fitar dasu, yarinya kamar ‘yar daji se shegiyar kazanta” Tura bakina nayi na juya na tafi gurin Ummaah, Tana kitchen tana kada miyar dare, “Ummaah kinga Adda Meeyna Gabaki daya ta Watson da kayana waje ko? “ Seda ta kashe Gas din sannan ta kalleni tace “Ba kazanta kike ba Asma’u? Shekara goma sha biyu ace wanka se nace miki kiyi? Wallahi dama kisani ba NTIC kike so ba? Allah Bazaa kaiki ba, Gwaram zaki tafi, yadda ko sunana kikaji se Kinyi kuka, se seniors sun miki dukan da ko cewa akai kiyi kazanta bazakiyi marmarin hakan ba” Ai daga jin hakan na Fara kuka ina bata hakuri amma ko kulani Batayi ba ta tafi daki, komawa nayi dakin Inata kuka, na tsugunna na Fara tsitsince kayan, Adda Maryam ce Tazo ta tayani muka gyara kayan, Wanda basuda guga na kaisu inda ake Tara kayan guga. Marasa wankin kuma na kaisu cikin laundry bin, ni Kaina dana kalla wardrobe din seda naji dadi, saboda yyai kyau. Sallah mukai sannan muka zauna ta tsefe min Kaina Dama kitson guda goma ne, ana cikin combing Adda Sa’ada ta shigo, gefenmu ta zauna bayan ta dage curtains sannan ta kura fanka tace “Wannan se mutum Yayi suffocating saboda warin da Kanki yake” Ni magana Tana min wahala, amma da ina magana nasan tabbas rashin kunya zanyi, so instead of rashin Kunyar sede na murguda Baki, bakin na murguda daidai shigowar Adda Salma, hannunta tasa ta gwabe min bakina tace “Zaki sani, sena fasa fitsararren bakin nan naki” Adda Meeyna dake kwance tayi saurin cewa “Ku kyaleta Dan Allah, kada taji Kamar an takura mata” Dage kafada Adda Salma tayi ta kara Ficewa, wata Uwar harara nabi bayanta dashi, ribbon nasa na tufke kan in a bun, inajin Adda Maryam na mitar gashina baida zuciya. Adda Sa’ada ta wanke min shi tas, tayimin drying sannan tayi min kalba Manya, ta saka nayi wanka ai ji nayi kamar an sakeni, wata fresh air tana shigata ta ko ina a Haka bacci ya daukeni. Duk tunanina zancen zuwa Gwaram wasa Ummaah take, amma bayan sati uku lokacin Zaa shiga sabon session Naga anata shiri, tunda naji Ni Zaa kai nake ta kuka, saboda har ga Allah bana son zuwa. Hatta Abba dake bani goyon baya wannan Karon ban samu ba. The only person that stands for me was Yaya Halifa, shima dalilinshi kada background dina ya lalace amma yadda Ummaah ta dage nasan babu me juyata. Da daddare naje dakin Abba na gaisheshi, Yana ta tsokanata yar boarding, kiran Inna Ade ya katse mana hirar, katsewa yayi ya kira suka gaisa sannan yace mata gani a kusa. Da murnata na karba sannan na mike na fito waje, cikeda murna na gaisheta, Tana tambayata yadda nake, nan kuma na Fara kuka ina fada mata Ummaah bata sona, ta takura min tace Abba ya kaini Gwaram. Dariya Inna tayi tace kada na damu karshen sati tana hanya. Ranar asabar kuwa da sassafe se mukaji isowar ta, lokacin Inata bacci ban tashi ba, Maganar ta yasa na fito, gaba daya ta hade gidan da sababi da kuma fada. Gashi Abba da Ummaah basa nan so babu Wanda ya kulata a cikinsu. Tana zaune naje na zauna kusa da ita nace “Inna kinzo? Sannu ya hanya?” kaina ta shafa tace “Lafiya kalau yar albarka” Mikewa nayi na tafi kitchen na dakko abincin da aka riga aka hada mata na kawo mata, Tana ta saka min albarka, jin dadin hakan yasa duk wannan laziness din nawa naje na bude dakinta na share har da mopping lokacin ta gama cin Abinci, muka koma dakinta ina tayi mata complain akan zaman gidan. Nan kuwa ta hau Tana ta masifa har su Abba suka dawo. Can Ina kwance Tun kayan Dana tashi daga bacci shi ne a jikina, ko wanka banyi ba, ga zafi da ake a gari, jikina Har stinky yake yana bashi amma ina kwance Kamar sarauniya, su kuma sisters dina suna can suna aiki. Sallamar Inna naji hakan yasa na tashi na zauna ina Mata Murmushi Dan nasan zancen zuwa Gwaram ya rushe. Gefena ta zauna tace “Kawata, Ashe kazanta kikeyi? Nidai Allah Ya sani ban tashe ki da kazanta ba, Haka zalika bansan Saude da kazanta ba. Dan Haka ni bana goyon bayan rashin gaskiya, Gwaram zakije ta kodan kiyi hankali” Hannunta na kama ina fadin “Inna Allah zan dinga yin tsafta, Dan Allah Kice Ummaah tayi hakuri” Kanta ta girgiza, wannan shi ne karo na farko da Inna ta juyamin baya, shine sanadin tafiyata GGSS Gwaram! AyshatuuuBayan sati biyu duk wani shiri ya kammalla, I was tired of crying Dan Haka na hakura na zubawa sarautar Allah idanu, Ina ganin ta yadda zaa Fara. Saura kwana biyu na tafi, duk Yan gidanmu suka zo. Adda (Babbar yayarmu) ita ta hada min kayana, kana kallon kayan zai Baka insight din daga gidan Dana fito. Duk fadan da akai min akan tsafta ne, Adda tace min Ummaah tace indai ina tsafta to Zaa canza min makaranta naje dreamy NTIC dina. Ranar Monday very early, Adda Sa’ada da Yaya Halifa suka rakani, Garin Yayi min nisa sosae amma its all sightseeing. Tunda muka shiga na Fara kuka, kuma na lura suma duk jikinsu Yayi sanyi. A office din principal muka shiga, Dama ta rigada tasan da zuwanmu, ina shiga na gaisheta suma suka gaisheta, ta zagayo inda nake ta tsaya tareda shafa kaina tace “Asma’u how are you? “ “I’m fine” na bata amsa da dasashiyar murya, Dan Murmushi tayi ganin ina kuka, zama mukai bayan tayi mana tayin seat, seda tayi cikecike sannan ta tura aka kira VP academic ta hada ni dashi. Nan sukai mata godiya, Har naje kofa tace “I wish you a nice stay kinji”+ Kaina na gyada kawai, a raina Ina ayyana Wanne nice stay kuma a wannan uban dajin. A lokacin ji nake gaba daya rayuwata an gama tarwatsa min ita. Office din VP academic mukaje ya buden student file sannan ya tura SS3 aka kira masa head Girl, Nidai ina zaune babu uhm babu uhmm uhmm, Haka Tazo ta gaisheshi sannan ta gaida su Yaya Halifa fuskarta a sake. “Ga Sister na baki, Dan Allah ki kula da ita” Kai ta gyada tareda nufo inda nake tsaye ta riken hannuna, daga nan mukai sallama bayan su Yaya Halifa Sunyi mata alkhairi sannan aka bata amanata. Tunda naga fitar motarsu nake kuka, tana ta rarrashina ji nayi kamar nayi tsuntsunwa na koma Kano amma babu halin hakan. Haka na bita ta kaini class, gashi makarantar unity school ce, so you got to see different people from different places having different religion, what makes us united is that we’re Nigerians. Kamar munafuka haka na shiga ajin na zauna, se surutu ake, amma wannan head girl din na shigowa sukai Shiru. Seda nayi settling sannan ta koma nata class din. Tunda na zauna ban tashi ba haka kuma bance uffan ba Har aka fita break, kuma Kamar sun hada Baki babu Wanda ya kulani, ina nan zaune duk suka fice se baifi kadan suka rage ba. Durkusar da kaina nayi nayi ta kuka Kamar raina zai fita, na jima a Haka sannan wata Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, ni bansan Wacece Anty Rashida ba but I guess wannan head girl dince. Binta nayi muka tafi, fuskata tayi jawur saboda yadda nayi kuka, ina wucewa anata nuna ni Wai new comer ce. Ana tashi a class muka tafi zuwa hostel nabi ayari, Dutse hostel aka kaini kwanar Anty Rashida, ruwan wanka tasa aka kaimin nayi, ta gyaran kayana, nayi sallah sannan na bita dining, ana Fara zubawa aka zubamin wata taliya, masifar yunwar da nake ji tasa na daure naci, daga nan se prep na yamma, wannan slow slow din da nake har seda aka tareni ban samu sallar ishai ba, aka zanemu kuwa. Har na kwanta ranar kuka nake. A hankali kuma na Fara warewa, sede kafin na ware a kalla nafi sati biyu a Haka, amma daga baya se na Fara yiwa mutane magana Kamar yadda Nima naga suna shiga harkata, ko ina na wuce se Anyi maganata saboda kwatakwata I don’t match with that environment. Zancen tsafta kuwa, ba koda yaushe muke samun ruwa ba, ni a Haka ma Inada Uwar kwana amma dukda haka se nayi kwana uku banda alwala babu ruwan dake zuba a jikina, tunda ba wani amfani take min ba, se nice ma take amfaniwa dani. ga Rana ga wuya da dealing a makarantar da kuma azabar aike. Kafin wata daya farar fatar da duk gidanmu mu biyu muke da ita ta Fara dafewa, na rame Kamar marar lafiya. Lokuta da dama idan naje class banida aiki idan ba kuka ba, na kasa sabawa da rayuwar. Ga duk yammaci da safe se nayi zazzabi to banida Wanda xan fadawa Dan Haka ni daya nake abuna, idanba wata Rumasa’u ba, to Anty Rashida kawai Wayo takeyi min. Ana haka ranar visiting tazo, ana gobe visiting Anty Rashida ta tsefen Kaina ta wankemin tayi min Sabin kitso, Washegari tasa nayi wanka Wanda duk nasan na ganin ido ne. Ta dakko min sababbin check Wanda ban taba sawa ba, na saka take kuma se nayi kyau, idanun nan nawa Kamar na mujiya, Dama girma ne dasu to gashi na rame, hancina ya Kara tsawo, idan aka kalleni abinda ake gani kenan. Muna zaune nida Rumasa’u, class dinmu daya haka dakinmu, so ita ina sakin jiki sosae da ita mun kuma saba. “Asma’u ban taba ganin dariyarki ba irin ta yau, kodan visiting day ne” Dariya nayi Ina rufe fuskata data dashe, kamar banida jini, Haka tafukan Hannayena suma duk Sunyi fayau dasu. “Bazaki gane irin farin cikin da nake ciki ba Rumasa’u” Kanta ta gyada tace “Ai naga alama kam, amma….. “ Bata karasa Maganar tata ba, wata yar SS1 Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, babu yadda banyi ba akan Rumasa’u Tazo muje amma taki, haka na hakura na tafi abuna. Tundaga Nesa na hango Ikhram yarinyar Adda, da wani irin gudu na kwasa, su basu ganni ba Dan Haka babu sanarwa na fada jikin Adda Meeyna, gaba daya suka jiyo suna fadin “Yar boarding, Iyeee! “ Zama nayi gefen Adda Inata Murmushi amma na kasa magana. Duk se naga yanayinsu ya canja gaba daya se bina da kallo suke Kamar irin it’s the first time of them seeing me. “Ummaaah bata zo ba? “ Kafin a bani amsa Sega motar su tayi parking, Yaya Halifa, Ummaah, Abba. Muna hada ido kawai na rufe fuskata Inata kuka, from nowhere naji wata irin karaya ta saukar min. Dukkansu sukai Shiru har nayi me isata na gama, sannann naja Adda Maryam muka Kira Anty Rashida. Ina dawoa na sauka Kan Abinci, duk yadda nake dauki amma haka na kasa cin abincin, su dai basu ce komai ba amma yanayinsu kadai ya nuna min they’re not happy da yadda suka Tarar Dani. Har akai Sallar laasar sannan suka Fara shirin tafiya, Inata daurewa saboda kada nayi breaking, amma seda nayi kuka. Lokacin Abba ya dawo daga office din principal, kallona Yayi yace “Akwai abinda kike bukata a hostel zaki dakko? “ Cikin rashin fahimta nace “Abba? “ Kallon Yaya Halifa yayi yace “Gobe kaje ka samo mata wani admission din, Bazan iya barinta a Haka ba” Maimakon naji farin cikin da nake tuanin ji, se naji zanyu missing makarantar, gaba daya kayana na tattara na bawa Rumasa’u. Muka tafi gida, shima asibiti muka fara tsayawa Naga Likita sannan muka dawo gida. Ina shiga dakinmu toilet na wuce na dinga wanka Kamar zan cire fatar jikina, na fito na kwanta se bacci peacefully and calm. AyshatuuuWashegari ana Fara kiran Sallar farko na tashi, na jima a zaune ina karewa dakin kallo ina kuma godewa Allah, da tuni ina can daji ga sanyin asuba Kamar zai kwashe ka. Kaina na girgiza tareda sakin murmushi na sakko daga gadon na nufi toilet. Nayi alwala sannan na dawo Ina karewa dakin kallo, yadda Adda Salma da Adda Maryam ke baccinsu hankali kwance, a raina na ayyana basu san irin abinda na gani ba, basu san yadda boarding take ba saboda ni daya tal nayi boarding a gidanmu. So I gat the best and weird experience. Seda aka Fara iqamah sannan nasa hannuna na tashi Adda Maryam, ni kuma na tada sallah abuna. Kowa a gidanmu yasan ni da kaunar baccin bayan asuba amma tunda aka kaini Gwaram bana tunanin nayi baccin bayan Sallar asuba sau uku, so har na rigada na saba da hakan. Suna idarwa ko magana bamui dasu ba, suka wuce gado suka sake kudunduna, Nikam Shiru nayi a raina Ina jin tamkar an canja ni, I’m not that lazy Asma’u again, I’m a new person. Kafin bakwai na safe nayi wanka na saka kaya sannan na fito parlor, babu kowa, gidan Shiru kowa baccinsa yake. Se can cleaners dinmu suka zo, kowa ya ganni se Yayi mamakin ganina a gida, sannan Tashin da nayi da wurwuri. Kitchen na tafi dan taya Baba Zulai me yi mana girki aiki. Ina shiga ta juyo da mamaki tace+ “Asma’u yaushe kika dawo? “ Dan Murmushi nayi nace “Jiya, aiki zan tayaki” Seda ta kalleni for some seconds kafin ta amsa min da to, haka Inata tayata tana koya min abubuwa, Dan babu abinda na iya, idan kaganni a kitchen to aiko ni akayi. Wajen Tara naji mutanen gidan sun Fara fitowa, ban leko ba, ina juya Irish din dake cikin mai. Muryar Ummaah naji tana fadin to ina Asma’u zataje da sassafen nan? Kun duba ko ina kuwa? Dan dariya nayi sannan na saki leak spoon din nace da Baba Zulai, bari naje gurin Ummaah, Dan da alamun ita bataji abinda naji ba. Ina lekowa naga Sunyi cirkocirko harda Abba, karasa fitowa nayi Ina gaishesu, kowanne mamaki ne a fuskarshi, Abba yace “Asma’u me kikeyi a kitchen? Kin tsoarata mu, yan uwanki basu ganki ba” Dan Murmushi nayi nace “Abba ina taya Baba aiki ne, bansan zaa nemeni ba” Kanshi Ya gyada yace “If that’s the case, naji dadi “ Daga Haka ya juya zuwa dakinshi, hannuna Ummaah ta kama tace “Ya kika tashi da wurwuri? Keda bakida lafiya “ “Ummaaah ai na samu sauki, kuma a school Baa komawa bacci, so na rigada na saba” “At least, yarinya ta gyaru ko Ba komi” Adda Sa’ada ta fada, kafin muka zazzauna ana ta hira, yawanci su suke abinsu dan ni kawai jinsu nake. Da yammacin ranar Sega Inna tazo, Ashe Abba ne ya kirata, Tana ganina tace Bazan koma ba, Ummaah tace Dama wata makarantar Zaa canja min. Kwananta biyu ta koma Kwalam. Satina biyu na warware gaba daya, babu wani abinda yake min ciwo, da Adda zata tafi tace zata tafi Dani Ummaah ta hana, a cewarta nema min admission ake. Wannan zaman da nayi kowa seda ya lura da transformation din da aka samu a tattare dani. Dukda ko aikin nake amma bana sauri, zan jima ban gama ba amma zanyi, Haka halitta take banida sauri. New horizon college dake Minna nan aka samo min admission, wannan karan babu Wanda Yayi protesting haka aka kaini, nida cousin dita Rayhana amma ita tun Farkon term din aka kaita, so se nayi joining dinta.1 Naji dadin zaman makarantar, Dan aljanna ce compared to inda na baro, ga Karatu both western and Islamic, saboda dama Islamic union suka kafata. Hutuna na farko Daddyn Rayhana ne yazo, munata murna zamu tafi gida, dayazo Ya dauketa ita kadai yace Abbana zai zo ya daukeni, tafiyarsu kuwa ba dadewa Abba da Ummaah sukazo tare, Ashe basa Kano, an tura Abba Delta state wani official assignment na wata daya, shi ne ya taho da Ummaah. Dukkansu sunji dadin ganina da kuma result dina, Haka muka dauki hanya wadda banda bacci babu abinda nakeyi, saboda Daren jiya bamuyi bacci ba, munata hada kayanmu da murnar zuwa gida. A Mobile Base accommodation din yake, flat gida ne da two bedrooms se parlor, toilet da kuma kitchen. Ni na dauki daya su kuma suna daya. Idan ya tafi aiki se nida Ummaah mu danyi hira, muyi aiki Haka muke zama abinmu. Satina daya amma zan iya irga sau nawa na leka kofar gida, ranar Ummaah Kamar an saukar mata da bacci, se bacci take, ni kuma na gaji da zama, kallon ya isheni kawai se na fito na zauna kofar gida, time to time Ina ganin wucewar mutane mazauna Base din. Na jima a zaune naji an kwado min ball a Kaina, da sauri na mike ina sosa gurin saboda ta shigeni bugun. Bakina na turo Ina jujjuyawa dan naga wanene. Wasu maza su biyu suka karaso se haki suke dukkansu sanye da jersey, Babban baifi saan Adda Habiba ba se karamin da baifi saan Adda Maryam ba. Suna zuwa karamin yace ” Ina ball din? “ Ya tambaya yana waigawa alamun nemanta yake, harara na wurga mishi tareda dauke ball din na nufi kofa zan shige gida, saboda rainin Wayo ne, by mere looking sunsan sun buga min tunda gashi ina sosa Kaina amma su ta ball din suke. “Ina zaki Kai mana ball dinne? Bakyaji ne? “ Babban ya fada yana Hararata, wani haushi naji na dauki ball din na wulla mishi, take kuwa ta sauka a kirjinshi nace “Feel the pain! “ Daga Haka na wuce gida na buga kofar tareda jingina a jiki ina maida numfashi, did I seriously hit him? Na tambayi Kaina, kafadata na girgiza na wuce zuwa kitchen na dakko ruwa nasha sannan na zauna ina maida numfashi. Ban kara fita ba Tundaga ranar saboda Ina ganin Kamar idan na fita to zamu hadu dasu. “Ummaah Wai Haka zamuyi ta zama, ba zamu fita ba?” Aje kayan hannunta tayi tace “kin gaji da zama ne?” Kaina na gyada nace “Muje ko cikin gari ne mana” Kanta ta gyada, daga nan ban kara cewa komai ba na maida hankalina kan kallon da nake, da daddare Abba ya dawo yace zamuje gidan abokinshi a cikin Base din, nafi kowa murna, Dan ni na Fara shiryawa na zauna jiransu, a Mota mukaje, gidan sak irin namu. Tun a kofa nake jin muryar maza sunata hayaniya, hannun Ummaah na rike Har muka shiga ciki, Maza ne guda uku suna game ta Chisel, ga board din a gabansu, saboda ihunsu ko sallamar da mukai I’m not sure idan sunji, wata mata wadda bata Kai Saar Ummaah ba, Ta fito daga dayan bedroom din tana fadin “Wai Meye Haka duk kun cika gida da ihu, Iyeee! “ Take duka suka shiga taitayinsu, Se lokacin ta hango mu nida Ummaah a tsaye, yadda ta karbe mu fuskarta a sake ta karaso tana fadin “Ihunsu bai barni naji sallamar ku ba, Dan Allah ku shigo” A take naji ta birgeni, saboda na yadda da bahaushe da yace shimfudar fuska tafi ta tabarma. Bayanta muka bi, Ummaah ta zauna saman cushion ni kuma na zauna Kan carpet nace “Anty Ina yini? “ Kanta ta girgiza tace “Call me Ummiey, ya sunanki? “ “Asma’u” na bata amsa Ina Dan Murmushi, lokacin ne na fuskanci su waye ‘ya’yanta, sune Wanda na bugawa ball last week, bata rai nayi Inaji suna gaida Ummaah, Babansu ya fita ya shigo da Abba, nan aka kafa hira Se ni daya a gefe, su kuwa sun cigaba da game dinsu. Abbansu yace su matsa min nayi nima. A dadare na zauna gefen Babban, na tsakiyan shi ne Wanda ban gani ba ranar, Yana gwada min yadda ake chisel, dashi muka buga Ya cinye ni, aka kara yi yayi winning. Aje king din nayi kan board din nace “Wayo kake min ko? “ Dariya yayi, Juyawa nayi na Kalli Babban yayansu, ya matsa gefe amma idonshi a Kaina. I can say ban taba saurin Sabo da mutane ba irin yadda nayi dasu ba. Matsowa yayi ya dauki king din yasa min a hannuna, dagowa nayi na kalleshi cikin ido shima kallona yake cikin ido and I can swear time stuck, saurin kasa nayi da idona inajin wani discomfort a tare dani, a hankali cikin nutsuwa ya gwada min and take na fahimta, dashi mukayi na cinye dukda nasan he gave me that chance. Kafin lokacin tafiyarmu yayi na ware Duka na saba dasu amma Abu daya na manta shi ne sunayansu, the only name that ring in my head sunan Mamansu UMMIEY! AyshatuuuBamu Kara komawa wannan gidan ba, kamar Hadin baki suma basu zo gidanmu ba, sede naji Abba yace da Ummaah, Ummiey na gaisheta, su Assignment dinsu ya kare sun tafi, duk se naji babu dadi cikin zuciyata, the least thing I should do is to know their names, amma ta Yaya? Babu wata hanya, dan koda mukaje gidan Banji an ambaci sunan kowa ba a cikknsu. Muma a Haka hutuna ya kare aka maida ni Minna, nan muka cigaba da Karatu. Duk Hutu xaazo a dauke mu, sannan visiting sau daya ake zuwa mana a term, so har mun rigada mun saba hakan. A Haka naje SS1, Adda Habiba, Adda Meeyna Da Adda Ummiey Sunyi aure, Adda Salma ma tayi aure dukda bata gama university ba amma Ance ta karasa a gidanta. Gidan Ya rage daga ni se Adda Maryam da Yaya Halifa, Adda Maryam tana Kuwait Tana Karatu, so ko Nazo Hutu sede mu, zauna da Yaya Halifa, muyi Karatu Wanda a gurinshi baya karewa, Har ya samin mugun son karatun, na rigada na saba, hobby dina Karatu ne. “Rayhana Kinsan na kasa karasa Haddar last page din suratul Nisa’i” Na fadawa Rayhana, ina rikeda qurani ita kuma tana zura uniform zamu tafi Quran class dinmu. “Bansan me yasa take baki wahala ba, ki Kara maimaitawa kafin time ya cika” Idanuna na runtse sannan na bude, na tattara dukkan hankalina akan karatun, seda time Yayi ta gama shiryawa sannan muka tafi, gabana se faduwa yake, dan na tsana embarrassment, Allah Ya taimaka ina shiga akace Anyi mishi rasuwa he can’t make it, naji dadi hakan na wuce can extreme din class din nayi ta bita Har ta zauna sannan na dawo gefen Rayhana.+ Lokacinda muka shiga final year, ni nayi applying medicine and surgery, ita kuma Rayhana tayi applying Biochemistry, Kaf class dinmu Rayhana batada na biyu a chemistry, ita ce overall best chemistry student a duka set dinmu, bana jin ba zata iya ba. Munyi graduation gaba daya daga secondary, Yaya Halifa ne yazo ya daukemu daga Minna, Kamar zanyi flying Haka nake ji, ko babu komai nasan at least na taka wani mataki a rayuwata. Straight daga Minna Kwalam muka wuce saboda akwai bikin cousin dinmu da akeyi kuma Duka family dinmu sun hadu. A cikin gida muka sauka, ko Rayhana ban jira ba nayi ciki abuna, da Adda Meeyna na Fara haduwa hannunta dauke da Aarif, rungumeta nayi itama cikeda murna ta rungumeni sannan na karba Aarif nayi ciki. A dakin Inna na tarar dasu Ummaah, kowa yana tayi mana murna, muka gaisa sannan na shige cikin uwardakin Inna, bata cikin dakin hakan yasa na fada gadon Ina Murmushi tuna yarinta da yadda na rayu a dakin, irin bacin da nayi. Ina kwance idanuna a lumshe naji shigowar ta tana fadin “Kawata, kina ina? “ Dagowa nayi tareda riko hannunta nace “Ganinan Kawata, na sameku lafiya? “ “Lafiya lau, ya hanya? “ Fuskata na shafa Dan tun eight muka dakko hanya amma Se Yanzun laasar muka karaso, na gaji sosae. “A gajiye nake Inna” Hannuna dake cikin nata ta saki, tace “Maza sakko kije kiyi wanka, kizo kici abinci. Se Ki huta” “Fauziyya! Fauziyya!! Fauziyya!!! “ Inna ta kwalla mata kira, Se gata ta shigo da ciki a gaba, cousin dinmu ce sannan yayar Rayhana ce tare akai aurensu da Adda Salma, kuma kusan sa’anni ne Dan dai Adda Fauziyya ta bata watanni biyu. “Maza jeki Ki hadawa Fara ‘yar shehu ruwan wanka” Nasan halin Inna Ade, so banyi mamaki ba amma Adda Fauziyya da mamaki tace “Haba Inna Ade, Wanne irin ruwan wanka kuma? “ Kugu Inna Ade ta kama kamar me shirin fada tace “Ruwan wanka nawa ne? Ki wuce kije kiyi abinda na saki, yarinya ta dawo daga makaranta ko tausayinta bakwaji” “Inna wallahi ina fama da kaina Bazan hadawa Asma’u ruwa ba, sede kada tayi wankan. Muma ai ‘ya’ya ne kuma jikoki, amma sede ki ware bi….. “ Bakinta Inna ta buge tana huci tareda fadin “Eh lallai, ni Fauziyya ke yadawa magana, to idan bazaki hada ruwan ba, Uwarki ta hada” Jin hakan yasa nayi saurin cewa “Inna, ni bana jin wanka Yanzun, bani Abinci naci tukunna” Allah Ya taimaka se ta fita kawo min Abinci, Itakuma Adda Fauziyya tasa hannunta ta dada min duka a cinya Sannnan ta fice, bakina na turo Ina sosa gurin, se kuma nayi dariya. Inna Ade Tashin hankali, Yanzu fa tsaf zata iya kiran Anty Hauwa

Chapter 2 of 18