Share this page
jikina light like a feather, se nake jin sassanyar iskar dake kadawa tamkar zata daga ni sama. Ina jinsu suna kuskus din abinda ya sani nake wannan farin cikin hakan abinda wasu dagacikinsu basu taba katarin gani ba. Ina stepping kafata cikin labor ward naji ana fadin “Kira Dr Shahada matar nan so take tayi parking!” Ni kaina gaba na seda ya fadi, is it a welcome? Na tambaya kaina kafin na cire stethoscope din dake wuyana na mikawa Dr Ruwaida nayi ciki da sauri suka biyo bayana, tana ganina Sister Naima ta saki ajiyar zuciya, gloves na dauka na zura a hannuna sannan na karaso gurin ina fadin “Sister me ya faru?” Tana ta kokarin securing second line tace min “PPH 2• home delivery. Sunce tayi bleeding sosae on their way coming, jikinta ya nuna though on arrival babu active bleeding sede she’s paper white kuma mata kadai suka zo babu maza” Kaina na gyada ina kallon ta nace “Shock zata shiga anytime from now, NASG fa?” Tace “Ana hadowa” Muna tsaye muna jira sega kakarta ce ko babarta no can tell, irin fulanin kauyen nan ne, tana tsayawa tareda kama hannun matar tana mata fullanci nace mata “Baba har yanzun mazan babu wanda yazo” Kai ta girgiza tace “Basu zo ba malama” Na danyi tsaki nace “Mijinta baisan kun taho bane ko ko?” Dariyar yake matar tayi wanda kana kallo is painful tace “Rayuwa ce kawai” Ban kara cewa komai ba tunda Na fahimci abinda take nufi. Baa fi minti biyu ba se gashi an kawo NASG muka shimfuda akan wani vacant bed sannan aka ciccibo ta muka daura ta, tana ta shure shure a haka muka fara kokarin daura mata amma wannan tsohuwar taxo ta rike hannuna tace “‘Yata ki kyaleta da wannan abin kawai bana so” Kallonta nayi nace “Baba wannan shi ne taimakon da zamuyu mata kafin mu samu jini” Matar nan fir taki, muna haka Metron ta shigo nayi mata bayani tace “Kun manta ethics dinku, patient’s right, idan kuma kuna gama sawa ta rasu fa, zata iya cewa abin ya kasheta allow her” Se lokacin na tuna hakan, aikuwa muka kyalleta se mukai waya lab a ara mana jini amma kafin a kawo jinin matar ta rasu, it was touching dan babar tace dalilin da yasa mijin yaki zuwa yace jininta wahala yake kuma shi baisan inda zai samu ba. Mazan kauye kenan basu masan meye amfanin aure ba balle su san darajar auren ko dalilin da yasa ake yinshi. Gaba daya ranar sukuku nayi ta babu wani walwala a tare dani, bawai ban taba ganin mutuwa ba, no amma akwai mutuwar da will stick in your mind forever. Office na wuce dan lokacin da zanyi assignment dina yayi dake ina course na IMCI (Integrated Management of Childhood Illnesses). Glasses dina na saka na bude system dita na fara shigarwa. Wani soft knock naji a jikin kofar hakan yasa na dago tare da kallon kofar, se na tuna cewar ai nayi locking kofar. Dan tsaki na saki tareda mikewa na nufi kofar, ina budewa nayi kyakyawan gani. Yeah kyakyawan gani mana tunda kuwan naga sanyin idaniya ta, naga abinda yasa na saki murmushi a take a gurin. Tsayawa nayi ina maida masa martanin murmushin da yake min. Seda yace min “Rowar office din kike min? Kin tsaya a kofa as if I’m not welcome” Dariya nayi kadan tareda matsawa se ya dage kafadarshi yace “I was passing by nace bari naga yadda kike” Cikin jin dadi nace “Thank you” Kanshi ya girgiza ni kuma na koma ciki bayan naga tafiyarshi. Tunda na zauna na kasa tabuka komai ina tunanin labarin da Doctor ya bani dazun, I’m so curious nasan me ya faru da Izzy, aure tayi ko kuma hanata auren shi akai. Tunani kalakala babu wanda bai zo min ba har tunani nayi kodai Raudha yar shi ce kuma ita ce fruit of love dinsu. Gaba daya na rasa tunanin me zanyi kuma dan kuwa wannan puzzle ne dana kasa solving. Manage please…..No complain Ayshatuuuu🎶Can’t you see? He’s my everything, I’ll wait on him all the days of my life! Can’t you hear? This sweet song he gave? Like cool rain drops falling on a sunny day🎵 Kwanaki a hankali suke shudewa suna wucewa ba tareda saka ran zasu kara dawowa ba, sun tafi tafiya ta har abada. Rayuwar gaba daya is too short wasu abubuwan suna faruwa Amma kwatkwata bamu fahimta, we’re so much engrossed da son kyalekyalen duniya not knowing rayuwar gaba daya ta kusan karewa. A kalla tafiya tsakanina da Dr Abbas tayi nisa mutane da yawa cikin asibiti sun fahimci meke tsakanin ni dashi. We barely hold giggling and grinning idan muka hadu. Akwai wani lokacin banma san me ya faru ba, kawai an kirani naje OT akan wani aiki da zamuyi. Tun daga kofar OT nasan yana ciki saboda bambamin fadan da yake tayi babu kakkautawa, muryar shi was at it’s highest pitch haka. Tamkar kada na shiga dan ni ban taba ganin fadan shi ba hakan yasa naji gaba daya I’m weak. Na juya zan fita kenan naji muryar Dr Lamin yace+ “Asmau!” Juyawa nayi fuskata looking dull na karkaro murmushi nace “Abban Afeeyya, ina kwana?” “Lafiya lau” Ya bani amsa sannan yace “Dan Allah shiga ciki, a patient died on couch, may be idan ya ganki fadan zai ragu” Baki na bude da niyyar protesting se ya riga ni da fadin “Just save them please” Ba yadda na iya haka na shiga ciki, suna tsatsaye a clean area, dukkansu idonsu ya raina fata shi kuma se kumfar baki yake. Banyiwa kowa magana ba kawai na nufi cikin lounge din bayan na tabbatar mun hada ido dashi, kamar minti biyu naji muryarshi yana fadin “All of you should get out of my sight” Ajiyar zauciya na sauke, bayan wasu mintina na fito shi dinma baya nan se chief anesthetist na samu yana ta dariya na zauna kujerar dake facing tashi nace “Me ya faru?” Dariya ya kara yi yace “Kin ceci mutane fa, shigowa office nayi na kiraki nasan ke kadai zai gani wannan temper ta sauka” Kaina Na girgiza dan shikam ya rigada ya san meye tsakanin mu, gashi MD is making it obvious to everyone cewar nidin ni ce farin cikin shi da nutsuwar shi. Mikewa nayi nace “Ba haka bane, kawai na shigo daidai lokacin da zai gama fadan ne. I guess it’s a coincidence” Wani kallo yayi min yace “No, ni ba haka na gani ba, kina shigowa duk wannan fadan dake idanunshi sukai melting especially kin shigo baki kula shi ba.” Dan dariya nayi kadan nace “Oga baka da dama” Yace “Of course, Inata adduar idan mijinki yazo Allah ya baki miji na gari wanda zaki zama sanyin idaniyar shi. Kinsan there’s a great wisdom akan hakuri amma mutane kalilan ke fahimta, kede a rayuwarki kinci ribar hakuri. Ya fada min har manya sunyi magana ko?” Se lokacin na tuna MD ya taba fada min Chief abokin shi ne, like ko sunyi school daya ne i don’t remember gaskiya. A idona Chief yanada matsayi saboda duk lokacin da zanzo OT bai bari na fita bai nuna min cewar aure lokaci bane, no way sede idan aiki yayi mana yawa. Godiya nayi mishi nace “Gobe munada Dialysis so wannan surgery bazaiyi taking place ba se jibi” Kanshi ya gyada tareda min fatan alkhairi na fita, tamkar jirana yake ina fita yana kirana, seda nayi murmushi sannan na kara wayar a kunnena ina fadin STORY CONTINUES BELOW “Allah ya huci zuciyarka” Dariya yayi kadan yace “Me yasa kika shigo lokacin, baki bari nayi knocking senses into their head ba.” Nima dariyar nayi nace “Saboda bana son naji wani abu ya taba maka muryarka, that’s why” “Can i see you? Ko kina aiki ne?” Kaina Na girgiza tamkar yana gaba na nace “Zanzo inshaaa Allah” Daga haka mukai sallama na nufi can a hanya naga anata nuna ni inajin ana cewa ita ce budurwar MD, murmushi kawai nayi na wuce zuwa office dinshi, shi kadai na samu yana zaune akan kujerarshi, idanunshi cikin farin medical glasses wanda ya fito da tsayin hancinshi, dukkan hankali shi yana kan system dan sallamata kawai ya amsa amma bai dago ba balle ya kalleni, zama nayi na maida hankalina kan plasma dake aiki, MBC 2 ce takeyi ana wani program na The Doctor, zamana na gyara dan bana bari ya wuceni ko online ne se na kalla. Ranar akan hyperlipidemia akeyi so yadda na bada attention dina sosae bansan har ya kammalla aikin ba seji nayi dif an kashe socket din, dagowa nayi na ganshi tsaye yana kallona, mikewa nayi nace “Shi ne ka kashe?” Kujerar dake facing dina ya zauna yace “I can’t help naga dukkan hanklainki ya tattara acan kinga dole na kashe.” Bakina na tabe irin nayi fushi dinnan se ya gyara zaman shi tareda daidaita fuskarshi shi wadda ta tabbatar min serious magana zamuyi, na zauna tareda bashi dukkan hankalina. Yace “Asmau kinsan me yake kara miki daraja a gurina?” Kaina na langwabar ina kallonshi with so much love in my eyes Na girgiza kai, murmushi me kyau yayimin yace “Kinada hakuri, ni banida hakura most especially if it’s for me to wait. Kin bani lokaci da yawa kin daga min kafa dukda kullum ina gani kina son na karasa maganar Izzy a idanunki amma kinki tambaya” Na kagu naji amma bana son takura mishi, bance komai ba ya cigaba da fadin “Seda aka daura aure, ban taba ganin ranar da nayi farin ciki irin wannan ranar ba, nayi murna kamar zan tashi sama saboda I’ve got what i waited for all my life. Kinsan me….” Ina kallnshi Na girgiza kai yace cikin rauni “…Kafin na baro inda aka daura aure zuwa family house dinmu aka kiramu Izzy ta rasu…” Mikewa nayi hannuna akan kirjina idanuna a warwaje nace “Innalillahi wa inna ilahil rajiun,! Sorry please, I’m so sorry ya Allah!” Murmushi yayi amma i can clearly see the pain he’s hiding, yace “Wannan shi ne mummunan labarin da ya taba riskata a cikin rayuwata, i felt it dan a take akai asibiti dani, soyayya ta kayar dani na rasa inda kaina yake, meke damuna ? Me ke min ciwo? Me nake bukata. Asmau nasha wahala kafin nayi fighting zuciyata na kara tashi. Nayi kukan rashin izzatu haka tamkar ta tafi da zuciyata se hoto ta bari. Na zama mafadaci very hostile gaba daya na canja, naki nayi aure, soyayyar na tattara na watsar da ita gaba daya. Hajiya kullum nasihar ta nayi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa amna na kasa fahimta gani nake babu mace kamar izzatu kuma ban samu ba tunda na sawa raina hakan. A hankali aka fara hada ni da yaran abokan alhaji ko na hajiya amma ko kallo basu isheni ba se suka kyaleni, a cewar su dan kaina zan sakko and here I’m about to go crazy akanki.” Dan dariya nayi tareda zama nayi masa gaisuwa da jaje amma nasan he’s just faking the smiles, hakan yasa nace “Haka rayuwar yake it’s so unfortunate. Allah ya jikanta” Murmushi yayi yace “Amin. So ina jinki fada min taki side of story din naji. Your love” Kaina Na girgiza komai yana dawo min ina picturing dinsa cikin kwakwalwata sede babu wani labari me dadi ciki amma haka nan zan fada masa especially akan yaya Suleiman. “Taka soyayyar is more enticing than tawa, babu wani jin dadi dana samu se heartbreaks dana samu…” A hankali daki daki na bashi labarin yaya mukhtar down to yaya Suleiman, sede bansan meye dalilin wani rauni da yazo min ba lokacin da nake fada masa ni nayi hooking Suleiman da Nadia, kawai se naji kuka ya kwace min. Kaina na kifar ina kuka a hankali wanda baki daya ya rikita shi fadi yake “I’m sorry, bansan haka kike ji ba , da ban tambaya ba” Seda nasha kukana har fuskata ta canja launi sannan nace “It pains yadda yayi wasa da tunani na Amma it’s all in the past” Hirar kuma duk se babu wani dadi hakan yasa yace naje na huta. Kamar hadin baki weekend din da muka tafi dashi yana sauke ni, Yaya Suleiman na parking, hakan yasa na leka nace ya fito su gaisa dashi, seda ya harare ni kafin ya fito. Yaya Suleiman cikin sakin jiki da sakin fuska ya mika masa hannu shikam Oga ranshi a bace ya bashi suka gaisa ya koma mota Yaya Suleiman ya shiga ciki. Tsayawa nayi nace “What was that face for? You barely smile” Yana bude baki se cemin yayi “I don’t like him!” Da sauri nace “Why? Is not as if kasanshi ko kun taba haduwa” Dariya ya danyi yace “Saboda yasa min wannan idanun sunyi kuka kinga laifina? He played with your heart baby” Rufe fuskata nayi ina murmushi wanda ke ratsa raina nace “Se munyi waya!” Shoulder dinshi yayi shrugging sannan yayimin sallama na wuce ciki ya tafi tamkar na bishi! 2 AyshatuuuuWashegari da daddare Abba ya kirani dakin Inna, ina kallo sakon ya sameni daga bakin Ikhramar Adda Meeyna da tazo mana hutu, mikewa nayi na dauki wani plain veil na dauka ash na yafa a kaina sannan na fita bayan nayi kashedi da babbar murya akan kada a taba min system din. Ina zuwa na same shi yana zaune kan carpet gefenshi Ummaah se Inna akan katifa da yaya halifa shima a zaune. A sanyaye Na zauna dan na san it must be something serious. Seda na kara gaishesu suka amsa inna ta nuna min gefenta na zauna sannan Abba ya fara da fadin “Na taraku anan saboda ke Asmau, ina cikin matukar farin ciki da Allah ya bani iko na sauke nauyin da ke kaina. Last week da kikazo na tambayeki akan maganar Abbas kin amince kin yadda fully zaki aureshi, hakan yasa cikin satinan na zauna da magabatansa na kuma basu aurenki. Alhamdulillah! Kowacce ‘yata haka na mata amd kema hakan na miki sede it’s a condition on no account should you tell me kin fasa aurenshi sede idan babban abu ne wanda ni ne zanyi deciding hakan, there’s no going back. Ina fata kinsan watanni uku kawai aka saka saboda haka sukai requesting. Allah ya tabbatar da alkhairi ya bada fahimtar juna”+ Gaba daya nasan maganar nan kwwai daga bakinshi ne ban ji ba, inshaaa Allah kawai nace sanoda ji nayi tamkar an zuba min ruwan kankara yadda jikina yayi balain sanyi. Koda yaushe ina fatan ranar da zan budu idanu naga aurena amma yanzun se nake jin I’m loving the house more and more. Idanuna se suka cicciko da kwalla inna na tayimin dariyar wai da girmana meye na kuka? Tasan idan nayi auren mantawa da ita zanyi ai fadar haka se na bare baki na fara kukan da baya min wahala, Ummaah ce ta janyo ni jikinta tana rarrashina Abba yana cemin it’s a normal pace for every lady, so su kyaleni nayi kukana. Koda na koma daki gaba daya se na kalli wannan na kalla wancan, na shafa gadon na bude wardrobe na kalla dressing mirror dina filled with kayan shafe shafe a lokacin naji wani irin missing gudan nake. Wayata na dauka na fara dialing “Jewel” kamar yadda nayi saving mishi number nake kuma kiranshi dashi, saboda a ganina yafi karfin silver, darajar sa tafi ta gold haka ta diamond, he’s a priceless gemstone. Yana dauka yace “Cara mia!” Haka yake kirana dashi, at first banma san menene sunan yake nufi ba se wata rana yake cemin it’s means My beloved in russian language. Duk lokacin da ya fada se naji kamar kara min son shi ake. “Jewel!” Na fada muryata cikeda rauni, “Yaya akai? Me ya faru? Muryarki says it all” Kamar yana gabana na turo bakina, dole Abbas ya sami zuciyata saboda kallona idan yayi yasan idan akwai matsala haka idan muna waya kuma bazai taba kyaleni ba se ya tabbatar nayi dariya. “Ni ban gaji da gida ba fa!” Dan dariya yayi yace “Ma’u love! So dama yaya halifa ya fadamin wai na shirya rocking baby, se yanzun Na fahimci menene auren auta! Gidana ma ai is home menene abin damuwa” Kamar yana gabana na fara bubbuga kafata a kasa kamar me kuka nace “Kullum sede ba zan kalla Ummaah ba” “Asmau ai yanzun ma ba kullum kike ganinta ba, ki dauka kamar zakije dutse ne” Kawai se naji hawaye ya fara zuba min, inajin wani irin damuwa a raina. Nasha kuka dakinnan akan banyi aure ba amma see me crying saboda zan bar gidan. Da tsananin mamaki yace “Cara mia are you crying? Menene abin kuka, is not like auren dole zaayi miki, i love you so much and you feel the same. Bawai kuma zakije detentions bane, kinsan duk lokacin da kike son ganin Ummaah I’ll grant you that request. Cara mia dan Allah ki bar kukannan haka, kinsan yadda nake ji haba mana baby? Kiyi hakuri I’ll be everything you need ok?” STORY CONTINUES BELOW “Mhm” Na fada ina share hawayena dan murmushi yayi yace “Smile kinji” And i smiled like a baby daga haka hirar tamu ta cigaba kusan dukkanta akan yadda zamu kasance ne in 3 months dinnan. Daf da zamui sallama nace “Jewel na manta ban fada maka zan tafi minna ba next week” “Minna? Me zakiyi” Gyara kwanciya ta nayi nace “Ka manta can nayi secondary school dina, New horizon?” “Yes?” Ya fada wanting to hear the details” “So zamuje old students reunion” Shiru yayi kamar bai ji ba nima nayi shiru dan na tabbatar yaji abinda nace alamun anya zakije kuwa? Dan tsaki yayi yace “Flight zaki bi, kin sani ko?” Murmushi nayi nace “Awnnnn I love you! Nayi booking ni da Nadia da Rayhana” “Seems good, alright ban gaji da jin muryar ki ba, but kiyi bacci kinji” Kaina na gyada nace “Alright sleep well” 🎵Baby I’m yours I love you much!🎶 Bayan sati daya ranar Wednesday na fara off, tun monday bamu hadu dashi ba and it feels so bad haka nan, bana jin dadi. Gaba daya aiki ya rike shi bashida wani free time haka nima se dan interval da zai samu ya kirani to check on me. Tun dare na hada kayana so muna gama rounds na koma daki nayi wanka na canja kayana zuwa wata loose English gown me kyau color royal blue se touches Na turquoise blue a jiki so se nayi amfani da veil da wani flat clowse half cover me kyau. Fuskata like usual daga kwalli se balm se powder da na shafa. Wayata na ciro nayi dialing number Jewel dan nace masa zan tafi, yana picking yace na sameshi a OT yana can. Mota ta na dauka na tafi bayan nayi parking na shiga ciki inajin kamar na shiga da gudu na ganshi na fada masa how much i missed looking at that handsome face of his. Yana zaune a reception shida Chief gabansu da mug din coffee, bana don wannan coffee din tsakar ranar da yake sha, he’s already addicted to it. Seda na gaida Chief ya dan tsokane ni wai suna missing dina a OT dake na jima banyi surgery ba. Murmushi nayi shikuma yacemun “Let’s go” Bayan shi na bi ya tsaya a inda mota ta take yace “So se tafiya kenan?” Kaina na gyada nace “Yes zan tafi se next week inshaaa Allah” Kanshi ya gyada yace “Safe journey, Allah ya kiyaye se munyi waya” “Amin” na amsa masa na shiga drivers seat tareda fastening belt dina sannan Na kalleshi nayi masa wink, kanshi ya zuro cikin motar yace “Tsokana ko?” Dariya nayi ya zuro envelope gefen seat dina yace “Take care of yourself for me. I love you!” Akwai lokuta da dama da repetition of abubuwa ko magana se ya saka ka gaji, kaji haushi amma banda wannan kalmar ta “I love you” kullum tamkar sabuwa haka take kullum jin ta nake kamar yau aka taba fada min, it’s enticing…. Karfe uku jirginmu ya tashi zuwa niger state, tunda muka boarding flight din muke hira dasu gaba daya secondary school life muke tunawa munata hira so bamu ga lokaci ya ja ba. A school accommodation dinmu yake aikuwa acan muka sauka, muna zama na fara kokarin kiranshi se gashi ya kira, rayhana tace “Tab Ma’u this your Doctor oooo” Hararta nayi na dauki wayar muka fara hira akan tafiyar har suka gama wanka ban gama ba se da Nadia tace “Doctor zatayi wanka” Sannan muka rabu inata mita. Munsha hira kafin washegari akai grand reunion kusan dukkan yan class dinmu sunzo da yayansu baifi mu hudu ne bamuyi aure ba. Se naji dadi saboda bani daya bace kuma gwara ni ina aiki na kama kuma dahir amma ita daya daga cikinsu ma babu aikin babu mijin babu komai a haka take rayuwar. So ka dinga kallon rayuwar wasu nan zaka gane kana cikin niima sosae. Taro ya tashi lafiya washegari muka dauka hanya zuwa airport anan naji message ya shigo min, duk tuannina ya tafi akan may be mtn ne seda na kira Jewel sannan naga wata bakuwar number ce, i didn’t check on the message har seda naje gida nayi wanka na gama wayata sannan na tuna dashi. Wannan message din almost gave me a heart attack ban taba ganin dare me tsayi irin wannan daren ba. I heard zaki aura Dr Kwaccido, do you ever taught of abinda ya hanashi aure. Bari na fada miki he’s a WOMANIZER! 6 Sorry for the late update, y’all should bear with me. Jiki da jini se a slow AyshatuuuuGyara kwanciyata nayi tareda sake bude text message din ina karantawa a iya adadin da bazan iya tunawa ba. Lokaci daya naji wata zufa ta rufeni, makoshina ya bushe se gaba na da ya dinga faduwa kamar zai balla kirjina ya fito. Kallon wayar na karayi na kara nanata message din “A womanizer?” Na tambayi kaina for the nth of time. Kwalkwalwata taki aminta da abinda ta gani haka zuciyata fada min take is not possible, he can never ba amma sede na kasa gaskata su dukka saboda ina cikin wani irin rudani da ban taba shiga irinsa ba. Wayar na ajiye a gefe tareda runtse idanuna a raina ina ayyana me yasa haka ke faruwa dani? Me yasa rayuwa take min haka? Me yasa kaddarata take zuwa a haka? Seda na fara son shi, na gina dukkan mafarkaina tare dashi sannan wannan abin zai kunno kai? Se kawai naji kuka ya kwace min, i was helpless tsoro sosae ya kamani, tsoron kada na rasa shi saboda nasan zuciyata will be shattered jinina se ya kai koluluwan hawa. To amma ai anyi bincike, kuma na tabbatar Abba bazai overlooking wannan abin ba saboda yana son nayi aure, kaina Na girgiza. Ni da kaina na bincika iya yadda zan iya amma me yasa se daga baya naji wannan muguwar maganar, ina zan saka kaina. Haka nayi ta tunani har da wanda bashida amfani na rasa me zanyi a wannan daren ga bacci yace bai san zancen ba.+ Na jima ina kwance, numfashi ne kawai nake fitar dashi a dadin rai amma ko hannuna jinshi nake yayi min nauyin gaske, so a haka dai nake kwance hawaye ya wanke min fuskata. Da kyar na kara mika hannuna na janyo wayar na kara duba message din, se lokacin idanuna yakai kan number, it’s a strange 9mobile number not in my contact, hannuna yana rawa nayi dialing number amma se a cemin my call has been forwarded, bansan iya lokacin da na dauka ina gwada saata ba amma wayar nan bata shiga ba. Jefar da wayar nayi ina nanata innalillahi wa Inna ilaihil rajiun! With the hope akan zuciyata zata rage zafin da tske min zanji afuwa a cikin raina. Kafin gari ya waye idanuna sun tashi saboda rashin bacci da kuma kuka, jikina was very weak da na tada sallah ma nayi tunanin bazan iya ba amma haka na daure nayi sannnan Na kwanta akan carpet dun aikuwa bacci ya daukeni. Bacci marar dadi me cikeda mafarke mafarke duk akan maganar, wai na sameshi akan maganar yace min wai to se me? Da gaske ne haka dai abubuwa iri iri. Amma a haka nayi baccin ban masan ummaah ta shigo ba haka Asiya balle kiran Jewel da yayi tayi se karfe goma Asiya ta shigo ta tasheni da sauri na mike ina fadin “Ya ilahi! Rana haka ta fito?” Da sauri nayi bandaki nayi wanka ina fitowa na shirya cikin lace maroon da blue zani da peplum riga. Veil na yafa na dakko komai sannan na fito, jikina duk a mace komai inayu ne dan ya zama min dole nayi shi. A parlon Abba nayi breakfast pancake da tea shima kawai sha nake da korawa amma it was tasteless gaba daya message din ya tafi da dukkan kuzari na, dukkan farin ciki na and it’s left and empty and emotional Asmau. Sallama nayi dasu na dauki hanya na tafi cikeda kewar su. I zeroed my mind yadda zan samu nayi concentrating akan tukin

Chapter 15 of 18