Yaya Suleiman tabbas ta gama morewa, halayenshi sunada kyau, kuma kowa zaiji dadin zama dashi. Books dina na dauka sannan na fito kafadata sabe da handbag dita na wuce dakin su Rayhana. Tana kwance da waya a kunnenta, na tabbatar Maganar daya ce, Abdul ne.
“Ke Baki jiya da waya ne, kullum ace kuna Abu daya. Haba Dan Allah! “
Na fada bayan na tsaya a kanta, Allah su Rayhana are irritating, kauda wayar tayi daga kunnenta tace min
“Duk ranar da kika Fara soyayya, soyayya da right man dinki, se kin fini sannan zaki gane abinda nake ji. So ya ake ciki? “
Harara na wurga mata tareda sakin Tsaki nace
“Zan tafi, kin fasa zuwan? “
Maida wayar tayi kunnenta, tayi mishi sallama, sannan tace
“Oh Asma’u, Karatu zanyi kije kawai. “
Kaina na gyada na wuce, har naje kofar fita a dakinsu naji ta kwalla min kira, Juyawa nayi nace
“Sauri nake fa”
“Haushi kika ji ne?”
Kaina na girgiza nace
“Ke Wanne haushi, nasan bawai Karatu zakiyi ba, Abdul ne kawai zaizo. Allah yasa nanda 2 weeks kina gidanshi ma huta muma. Amma….”
Tsaki nayi na fice, na rasa wannan jarababbiyar soyayyar tsakanin Abdul da Rayhana, kamar mayu kullum suna waya, abin haushi yake bani, kuma bansan me yasa nake jin hakan ba. Yaya Suleiman na zaune a drivers seat, ya kurawa kofar hostel ido, da dukkan alamu jirana yake yi. Straight inda yake na nufa, fuskata se Murmushi ne akanta, kamar bakina zai yage, is this what I’ve been missing, dama Haka akeji a soyayyar?
“Yaya kayi ta jirana Ko? Sorry “
Murmushi yayi yace
“Anything for Princess, nasan an tsaya yin girls stuff ne ko? “
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi na kuma saki nace
“Kamar ka sani, muje Ko?”
Kanshi Ya gyada tareda yiwa motar key muka dauki hanya, seda muka fita wajen mun hau titi yake tambayata Baiga Rayhana ba, nace Rayhana ta zauna yin ayyuka. Kanshi Ya gyada dan naga shi da ita ba wani good time suke ba, unlike itada Yaya Mukhtar marigayi. A gida muna shiga nasan Yau Inada Babbar Bakuwa, Inna Ade, tamkar yadda na saba haka na shiga a guje Tana parlor tayi daidai, gabanta an cikashi da abubuwa, Abinci ne nama ne and stuffs. Rungumeta nayi nace
“Kawata! Sannu da zuwa”
Itama bakinta ta bude Wanda hakora suka Fara Ficewa sannan ga yadda goro ya rinar dasu. Tace
“Kawata, Karatu ya boye min ke”
Dariya nayi Ina gyara zamana nace
“Ya zanyi kawaliyya? Nasan Kema zakiji dadi ace kawarki Likita ce ko? “
Kanta ta gyada Tana kare min kallo tace
“Wannan haka yake amma se naga kin yi rama, Ina fata babu matsala”
Kaina na girgiza Ina tauna Apple din dana dauka akan table din gabanta nace
“Ko daya, kawai Karatu ne. “
Kanta ta gyada tace
“Allah Ya bada saa, kije kiyi wanka. “
Tura bakina nayi nace
“Kai Inna, wari nakeyi? “
Harara ta tayi tace Hali Zanen dutse. Nayi dariya sannan na tafi na Kai kaina wajen Ummaah, tunda na ganta, naji jikina Yayi sanyi, saboda yanayunta kawai ya nuna min babu lafiya. Zama nayi nace
“Ummaah, Menene? “
Murmushi tayi Wanda ko makoshi bai kai ba, balle ace daga zuciya yake. Tace
“Babu komai, kin dawo? Ya Naga baku taho da Rayhanar ba? “
Kaina na girgiza nace
“Zatayi aiki shiyasa”
Daga Haka na mike na tafi dakina. Inna kwananta biyu amma ni bansan dalilin zuwanta ba Dan babu Wanda ya fada min, sede ni din ba yarinya bace, nasan definitely akwai abinda ke faruwa, amma tunda kowa boyewa yake, Meye nawa na bincike. Se naji Dama ban dawo ba, saboda yanayinsu duka ba cikin jin dadi suke ba.
Ranar Monday mukai sallama da Inna Ade, Dan zata wuce Kwalam, Haka nima zan wuce school. Na tafi abuna. Wajen Karfe biyar na yamma Adda Sa’ada ta kirani akan gata ta shigo cikin school dinmu, Nazo wani eatery mu hadu. Haka na Mike da duk Gajiyata na tafi, ita tayi mana order chilled Fanta, Danni inason Fanta babu ruwana da kakale kakale. Yadda ta tsira min idanu yasa gaba daya na kasa sakewa balle na sha lemun.
“Asma’u kisha mana”
Langwabar da kaina nayi nace
“Adda nasan dole wani abu ya kawoku, Ki fada min Bazan iya sha ba. “
Hannuna ta kama tace
“Ki saurareni da kyau kinji”
Ban bata amsa ba na gyada Kaina, se ta cigaba da fadin
“Kinada saurayi? “
OK, to me tambayar Tazo min a bazata, Abu ne daban yi expecting ba, amma ya zanyi dole na bada amsa. Kaina na girgiza nace
“A’a Adda, wani abu ne? “
Kanta ta gyada tace
“Suleiman fa? “
Shiru nayi bansan yadda zan Fara mata bayani ba, nida Suleiman babu Wanda yace yana son wani amma kuma dukkanmu muna son junanmu, balle ni ai kada wani yaji labari, ina sonshi sosae, son abinda ban taba yiwa wani abu ba. Kuma duk yadda muka zauna da mutum Ko awa ne se ya fahimci shakuwar mu nida shi.
“Kinyi Shiru Asma’u “
Kaina na girgiza nace
“Adda, baice yana sona ba amma…. “
“Amma me? Mistake din da kikayi akan Mukhtar shi kike son kara maimaitawa. Me yake damunki ne Wai? “
Tura bakina nayi nace
“Kai Adda, yana sona ne fa, kawai nasan zai fada idan time Yayi “
Idanunta ta kafeni dasu sannan tace
“Bakida hankali dama Har Yanzun? Wa yace miki ana haka. Ki daina kulashi kina jina ko”
Juyar da kaina nayi bansan yadda zanyi ba, ta Yaya Adda zatace na rabu da only source of happiness dina, kaina na girgiza Se kuma tace
“Kinsan Inna tazo weekend dinnan. Baki San me ya kawota ba right?”
Kaina na girgiza, gabana yana faduwa nace
“Me ya kawota? “
“Zancen aurenki!”
Da mamaki sosae nace
“Ni? Aurena? Haba dai “
Dariya tayi tace
“Saboda Sajida, Nabila da Rayhana dukka sa’anninki ne kuma zasuyi aure, shi ne tazo ta bawa Ummaah da Abba notice. Idan Kinada wani saurayi Ki turashi yayi gaisuwa idan yaso ayi Maganar daga baya. “
Raina a mugun bace nace
“Lallai! Nifa banda saurayi banda Yaya Suleiman sede idan shi zan tura”
Duka ta kaimin Tana fadin
“Dallah rufe min bakinki a gurin, Suleiman ai yafi kowa sanin halin da ake ciki, idan da yana sonki kinsan da tuni yayi magana. Abinda nakeso dake Kiyiwa Allah ki daina grumping fuskarki, ko a samu mashinshini”
Nidai Bance komai ba, Raina Ya baci sosae amma ko daya hankalina bai tashi ba, saboda nasa a raina, aure da mutuwa lokaci ne.
AyshatuuuA hankali na ja kafafuna cikin hostel, duk jikina Yayi sanyi Dan ko sallamar Arziki bamui nida Adda Sa’ada ba. Meye kuma Inna Ade take nufi da rayuwata zatace Ayimin aure, idan na tuna agreement din da mukai da Abba, har Yanzun akwai more than a year zuwa lokacin da ya yarda na kawo mishi mijin aure, but see what this old woman is talking about.
Koda na koma daki, rasa inda zan saka raina nayi naji dadi, gaba daya se nakeji Tsoro yana addabar zuciyata. Alwala naje nayi na gabatar da Sallar Maghrib sannan na dauki wayata na kira Yaya Suleiman. Ringing biyu ya dauka yana fadin
“Ajhumma!”
Se naji na kasa ce masa Ajhussi Kamar yadda muka saba, nace
“Yaya Suleiman, kana ina? “
“Akwai wani abu ne? Ina gida “
Kaina na gyada Banji dadi ba, saboda it’s bothersome nace yazo Ya kaini Unguwa.
“Shikenan kawai”
Kanshi Ya girgiza yace
“Nasan dole akwai wani abu, ko daga muryarki ma, tell me do I have to come over? “
Kaina na gyada inajin bacin rai na yana dan sauka kadan kadan nace
“Gidan Anty Bintu zaka kaini Dan Allah “
Dariya yayi yace
” You don’t have to plead princess, on my way “
Ko godiyar dake bakina banyi ba, ya kashe wayar. Haka na janyo Hisnul Muslim dina Dan nayi azkar. Ina kammalawa yayi min waya na fito, Seda naje zan shiga front seat sannan na fahimci shida wani abokinshi ne, zagayawa nayi na koma baya. Seda ya Fara driving kafin na gaida abokin yana ta Murmushi yana fadin
“A’a dole mutumina, wannan kyakywar yarinya Haka, dole komai kace Asma’u “
Duka Yaya Suleiman Ya kai masa a kafada yana dan dariya kasakasa yayinda naji wani sassanyan farin ciki ya lullubeni. Kenan har Abokanshi sunsan Asma’u, kenan yana labarina cikin friends dinsa? Se na saki Ajiyar zuciya. Hisham sunan abokin, so shima Intern ne a AKTH sede shi ba Doctors bane, physiotherapist ne.
“Asma’u, Kinsan yadda kike kuwa a gurin Yayanki, a asibiti babu Wanda baisan sunanki ba…… “
Steeree Yaya Suleiman Ya buga da hannunshi, hakan yasa Hisham kallonshi kuma Yayi Shiru, Nima daga idanuna nayi Ina kallonshi ta rear mirror, se naga kamar ranshi ya baci ba Kamar zuwanshi ba. To me yasa? Ko baya son na sani ne? Kaina na sunkuyar na cigaba da danne danne a wayata amma badan ina fahimtar abinda nakeyi ba, Gabaki daya hankalina da kwakwalwar Kaina suna wajen Maganar da Hisham yayi, idan kuwa Hakane kuma da gaske ne, babu tantama soyayya ce.
A kalle kalle na, abinda na fahimci soyayya ba se an furta ba, Caring, showing concern, protection shi ne soyayya. Wanene Yaya Suleiman baiyi exhibiting ba, babu shi, so Far zan iya cewa shima yana jin abinda Zuciyar Asma’u takeji.
Anty Bintu last born dinsu Ummaah ce, kuma itace favourite Aunt dina, dukkan wani abu da ya sameni bayan Adda Sa’ada, to ita ce ta biyu da take sani. Tana sona sosae kuma ban taba kaimata kuka na ba, bata lallasheni ba.
Koda naje tana tsakar gida, ta gama kada miyar dare akan murhu, Tana jin sallama ta, Ya’yanta su uku suka yo Kaina, suna murna. Tabarmar da aka shimfida a tsakar gida na samawa Kaina matsuguni munata hira da Yaran. A Haka ta karaso muka gaisa aka zubamin tuwo.
“Wannan zuan Daren nasan dole akwai abinda ya faru da bazai fadi a waya ba Ko? “
Kaina na gyada ina gyara zamana nace
“Anty Inna Ade ce! “
Kawai se naga hawaye ya gangaro min, cikin sauri nasa hannuna na dauke shi amma hakan bai samu ba, Dan take Wasu suka Fara gangarowa, it’s sure unlike me kuka cikin mutane, ni ban yadda wani ya fahimci weakness dina ba, hakan yasa duk halinda nake ciki nafi so nayi kuka ni daya a toilet, amma see this useless tears!
STORY CONTINUES BELOW
“Kanki Inna Ade ta dawo kuma?”
Kaina na gyada nace “Tace Wai Ayimin aure, gaba daya ta dagawa su Ummaah hankali, kuma ni babu Wanda ya taba cewa yana sona, kowa sede yace Inada kyau! “
Kanta ta gyada, wannan Maganar repetition ce, ta rigada taji ta bakin Ummaah da Adda Sa’ada.
“Share hawayenki kijini. Yaushe zaku je bikin nabila”
Hawayen na share Kamar yadda tace, nace
“Kashen satunnan zamu tafi”
Kanta ta gyada tace
“Then zakije Kiyiwa Inna Ade magana, saboda a Yanzun mafitar da kike da ita kenan. “
Nima naji hakan ne ya dace, idan kuma ba Haka ba to tabbas abun ba Zaiyi dadi ba. Mun jima da ita Har nayi Sallar ishai sannan Yaya Suleiman Ya dawo na fita ya maidani makaranta shi kuma ya wuce.
Karshen sati muka tafi Fotuskum, inda anan ake rikon Nabila, kuma saboda karar da iyayenta sakaiwa marikan, aka yanke acan zaayi biki da komai. Da yamma likis muka isa, Dan Haka ina ganin anata shirin tafiya wajen Bridal shower amma naki, saboda Uwar gajiyar dana debo bazata barni na fita ko nan da can ba. Abinci da aka kawo mana naci, nayi wanka sannan na samu guri na kwanta, tun ina jin hayaniyar Yan matan har na koma Se ta Manya kawai.
Dakin da aka bawa Inna Ade, nida ita Zamui squatting, so bayan na yi Sallar ishai na shiga nayi mana shimfida sannan na fita kofar gidan, na zauna wayata a hannuna. A family dinmu, mu hudu ne kawai sa’anni gashi dukkansu zasui aure leaving only I behind. Ina a zaunen Ina hango Yaran dake bayanmu sunata hira da samari, se abin Yayi ta bani mamaki, ni da nake yayarsu bansan wannan ba amma kalle su.
Zama naji Anyi a gefena, of course nasan Yaya Suleiman ne, ko daga kamshin Perf dinsa. Murmushi nayi na kalleshi nace
“Yaya, ya akai ka ganeni? “
Baki ya bude na mamaki yace
“Haba princess, ai ko daga bacci na tashi aka Tara min mata se na ganeki, Kinsan how special kike a gurina?”
Wani sanyi naji cikin raina Ina Murmushi na rasa me nakeji a wannan lokacin, amma abu daya na sani, wannan feeling din bazai fadi da baki ba.
“Ya Postikum din? “
“Not bad”
Na fada Ina karewa gurin kallo, baice komai ba amma dukkanmu Munyi Shiru, bansan abinda yake a zuciyarshi a wannan lokacin ba, but ni tawa tafi farar takarda fari, yanayin iskar dake kadawa a hankali, hankalina a kwance Ina wasa da ganye daya fadi, weather cool and romantic.
Wajen goma da rabi, na koma daki, Inna ta kwanta amma Batayi bacci ba. Shirin kwanciya nayi sannan Nazo na kwanta gefenta, tareda sakin Ajiyar zuciya, jin wani yanayi me dadi, that moment irin dinnan kayi tafiya Ka gaji, kazo ka kwanta, Hatta kashin spine dinka se kaji dadi.
Kaina Inna ta shafa tana fadin
“Asma’u Fara ‘Yar Shehu. Yarinya ta girma. Allah yasa Kema naga Naki auren”
Murmushi nayi a raina na amsa Amin, sannan na ayyana wannan shi ne best moment daya kamaata muyi magana da ita. Gyara kwanciyarta nayi, na riko hannunta nace
“Inna Ade! “
Kallona tayi ta kuma kalli hannunmu da nayi Interwining dinsu, tace
“Ya akayi kawaliyya? “
Kaina na girgiza nace
“Ance min kince na fito da miji Ayimin aure ko? “
Kanta ta gyada tareda tashi ta zauna, nima Se nayi yadda tayi nace
“Inna aure lokaci ne, nasan Kinsan hakan tuntuni. Kuma kinga karatuna akwai matsala idan na tsaya aure. Kuma Abba cewa Yayi se nayi shekara uku sannan zan Fara kula samari”
Tunda na Fara magana ta tsareni da idonta, gaba daya se naji na takura tamkar ba wannan tsohuwar bace Dana saba da ita.
“Na fahimta sun aikoki Ki ja da abinda na fada musu kenan? “
Kaina na girgiza nace
“A’a wallahi Inna, Kinsan ko Maganar bamui dasu ba, kawai naji nayi miki magana ne. Kiyi hakuri “
Murmushi tayi tace
“Shikenan, amma da zarar miji yazo ki kawo shi, Karatu baya hana aure, Haka aure baya hana Karatu. Na fahimci bakida saurayi shiyasa….”
Katse ta nayi da sauri ina dariya, a Haka Maganar ta shiririce har mukai bacci munata hirar Mu. Washegari akai kamu, al’adarsu ta birgeni sosae. The next day akai daurin aure, aka Mika ta gidanta.
Interval din sati daya ne tsakanin bikin Nabila dana Rayhana, muna dawowa muka shiga shiryayen bikin gagaruman Masoya.
AyshatuuuuBan kasance mutum bace me son taro, shiyasa indai ana taro gaba daya se naji an takurawa rayuwata. Gashi kuma Kamar Hadin baki anzo an saka Bikunkuna uku, kowanne interval din kwanaki biyar ne. Tun alhamis muka tafi Faskari, Dan Baban Rayhana Dan can ne kuma acan zaayi bikin. Bana wani doki saboda naje Faskari Har Bazan irga sau nawa ba. Unlike yadda nayi ta zumudin zuwan Potiskum.
“Wai har yanzun Baki shirya ba, Haba ke kuwa Asma’u kowa ya shirya fa “
Kaina na dago daga kan pillon nace
“Ke rabani da wannan event din naku, wallahi na gaji”
Tunda muka zo na samu guri na kwanta Kamar yadda nayi a bikin Nabila, Tun can dama ban fiye son shiga cikin mutane ba, to Yanzun abin yafi tsamari. Hannuna ta ja tace+
“Amma dai Kinsan aurena daban yake dana kowa ko? “
Kaina na dauke saboda na tsani naci, one halin Rayhana kenan. Fita tayi ni kuma na cigaba da kwanciyata ina chatting. Bata jima ba se Gata ta dawo da wayarta a hannu, ranta a bace ta miko min, Babu musu na karba ban duba ba na kara a Kunne na. Muryar Yaya Suleiman naji yace
“Banda musu, bazanji komai ba. Ki tashi ki shirya! “
Cire wayar nayi na mika mata nace
“Jarababbiya kawai”
Dariya tayi, ban dauki wani lokaci sosae ba na gama shiryawa, gidan uncle dinta zaayi cocktail party din. Dake yanada kudi, gidan Babba ne sosae, wajen da swimming pool yake anan akai decorating gurin. Tunda naje na samu gefe na zauna, Ina ta kallon yadda ake ta hidima, amma the only thing da nake so a wannan lokacin shi ne kadaici.
Da daddare Ina zaune Farfajiyar gidan, inda aka Kawata su da concrete chairs, ni daya ce a Hut din, se jotter a hannuna Ina revising mode of action din Wasu Antihelmentics . Wayata ce tayi ringing, daukar ta nayi na duba naga Ummaah ke kirana, dauka nayi tace Nazo naci Abinci. Amsa mata nayi sannan na mike Dan shiga ciki amma wayata ta kara katsemin hanzari, wannan karan Yaya Suleiman, bai samu yazo ba saboda yana call a asibiti. Komawa nayi na zauna tareda kara wayar kunnena nace
“Oppa! “
“Yan mata! Ya Faskari? “
Kallon compound din nayi sannan nace
“Alhamdulillah, ya asibiti? “
Dan Tsaki yayi yace
“Ki Bari kawai, ji nake kamar na gudo. Zakiyi mamakin irin aikin da nasha Yau “
Dariya nayi a hankali nace
“Ayya! Sannu. Hippocratic Oath! “
Murmushi yayi sannan yace
“Zaki ji me ake ji ne, ai Kin kusa kare preclinical dinki. “
Murmushin farin ciki nayi, saboda dadi nake ji idan na tuna wata Shekarar by now, na gama preclinical years dina, at least nayi halfway kenan. Mun jima munata hira dashi Har seda Ummaah ta turo aka tafi Dani sannan mukai sallama.
Kwana biu muka kara a Faskari, muka jiyo gida, Amarya aka kaita gidan Abdul. Tana ta kuka da muka rakata Har seda tasa naji Tsoro ya kamani, a ganina Mutumin dake ihun ayi mishi aure kuma Anyi yana wannan kukan, ni kuma suma zan dinga yi kenan.
A hankali rayuwa ta cigaba da gudana har shekara daya Tazo ta wuce, wata ta shigo cikin hukuncin Allah yadda nake Allah Allah shekarun da zan gama preclinical suzo, sunzo kuma I was successful. Batuna da Yaya Suleiman we’re still hooked sede ni ban fahimci inda relationship dinmu ya saka gaba ba, bansan Menene matsayina a gurinshi ba amma shi yanada Babban matsayi me kuma girma cikin rayuwata, shi ne Mutumin da ko Murmushi yayi se naji gaba daya lokaci ya tsaya cak, se naji Wasu butterflies na yawo cikin cikina. In a nutshell, Ina son Yaya Suleiman kuma banida wani buri a rayuwata irin naga mun zama officially one, Mata da miji. Tun ranar da na fahimci zazzafan son da nake mishi, ranar na Fara adduar Allah Ya karkato min da hankalinshi Kaina.
Akwai wani yammaci yazo school ya sameni, ranar nayi mamakin abinda nayi. Bana kwaliyya saboda looks dina ya isheni, I’m comfortable da yadda fuskata take, dukda mutane na cewa saboda Inada kyau shiyasa Bana kwaliyya. Tunda yace min zaizo na shiga wanka nayi kwaliyya ta ban mamaki, dake is not a usual thing, ba karamin kyau nayi ba. Wani bakin lace na dakko skirt da riga nasa, jikinshi Anyi zanen flowers Fuschia Pink kanana kanana. Yayimin kyau. Seda na dakko matching veil da Takalmi, na feshe jikina da constant turarena na Silent Woman, Dana kalla Kaina se naji kwakwalwar Kaina tana kwaba ta, Tana tuhumata akan zakewa da nakeyi amma dake zuciyata tayi Naam da hakan, haka nasa Kaina na fice inajin yadda roommates dina ke zuzuta kyaun da nayi. Kamar kullum a kan motarshi na sameshi Ya tsirawa kofar hostel idanu yana jiran isowata. Tunda na matso inda nasan tabbas zai ganeni nake tafiya cikin nutsuwa tareda counting takuna. Ina zuwa Naga ko idanunshi Ya kasa kiftawa balle ya dauke, wani farin ciki naji Ya mamaye min Raina,
“Oppa! “
Na fada Ina Murmushi genuinely, Ajiyar zuciya ya sauke yace
“Kinyi kyau sosae fa. Looking stunning “
Hannuna nasa na rufe fuskata saboda Murnar da nayi jin sakona ya isa. Kanshi Ya rausayr yace
“Nasan wannan kwalliyar wani gurin zakije, shiga mu wuce, zanyi magana dake dama”
Se naji Banji dadi ba, shi baisan danshi nayi ba amma zaice Unguwa zanje, shiga nayi duk yanayina ya canza, bai lura ba da yanayina ba, Waka yasa ta Celine Dion I love you! Gaba daya se atmosphere ta zama cool
_I wish I could go back to the very first time I saw you, should have made my move when you look into my eyes, Cuz by now I know that you feel the way that I do…._1
Zuciyata kawai fada min take, the song is for me, Dan ni Ya saka. He’s conveying his heart into mine. Gidan Adda Sa’ada mukaje, dama nasan bata nan, amma dan kar yaji danshi nayi kwalliya kawai se nace muje. Daga nan Grand square mukaje shan Ice cream. Ana kawo mana na Fara sha, shikam hankalinshi baya kan Ice cream din se wayarshi Dayake dannawa, bana fulako indai Ice cream ne, so kan Ya gama danne dannen da yake har na shanye nawa, se kawai ya turon nashi, da farko naki karba amma daga karshe na sha kayana. Seda na gama sannan yace
“Kun taba Maganar aure da Abba? “
Cikin rashin fahimta nace
“Aure? Kamar me kenan? “
“Irin ya taba fada miki lokacinda yake so kiyi aure? “
Shiru nayi Ina tunani sannan nace
“Eh, he mentioned it, lokacinda zan Fara zuwa school yace, idan na gama Year 3 dina Zan iya kawo mishi miji “
Murmushi yayi yace
“Yayi kyau, kinga nanda shekara daya kenan. “
Kaina na gyada yace
“Kafinnan na gama ginin da nake. “
Murmushi nayi naji dadi a raina, Wannan shi ya kara min kaimin Kara sonshi a raina. Tundaga wannan ranar bamu Kara makamanciiyar Maganar ba, naje na fadawa Anty Bintu, itadai bata cemin I should go on ba amma tace na iya takuna, haka Adda Sa’ada ita cewa tayi completely na rabu dashi amma na kasa. A Haka na kammalla 3 years dina, sannan na koma AKTH inda na Fara Clinical years dina.
Ranar Alhamis Nazo gida daga asibiti dake mun Fara Internal medical posting. Wajen laasar Ina daki Yaya Suleiman Ya kirani akan Nazo abokinshi yazo na kawo musu juice suna compound. Hijabina na dakko na fito, Ummaah na fadawa sannan na dakko musu na fita, zan iya kiran abin tsautsayi ko kuma nace ceto amma nasan nayi receiving shockest blow a rayuwata.2
AyshatuuuOne love to you all!
Gaba dayansu sun juya min baya, so babu Wanda yaga tahowa ta a ciki, dukda takalmina yana Kara amma nafi tunanin discussion dinne Yayi zafi da yawa shiyasa basu Ankara da zuwana ba.
“Man kana nufin ka cemin Baka son yarinyar nan? “
“So Kamar Yaya Khamis? “
Yaya Suleiman Ya tambayeshi, banga yanayin fuskarshi ba tunda babu Dama, kawai naji lokaci daya jikina Yayi min nauyi na kasa baya balle nayi gaba, tamkar an dasa ni a gurin Haka na tsaya inajin yadda zuciyata ke bugawa da karfin gaske
“Ka fahimci me nake nufi Suleiman, Dan me yasa zakai haka, Kasan Baka sonta. You should have let her go”
“Ni na tsayar da ita? Bani bane”
“Amma Kasan Tana sonka…..”
Shiru yayi saboda juyowar da yayi ya ganni, wannan shi ne karo na uku da muka hadu dashi, sun Je gurina Ina school sau daya, na biyu sun fito daga Operation su kazo gurina sukaci Abinci, last month kenan. Amma na yaba da halayenshi, he’s a good person+
“Ga juice din “
Na fada Ina aje musu Sannnan nayi saurin Juyawa cikin gida, duk cikinsu babu Wanda Yayi kokarin tsayar Dani, saboda fuskata kawai ta tabbatar musu naji komai.
“Kagani ko? Kaga abinda Kaja ko, gashi taji”
Khamis ya fada yana buga Bumber motar, dauke Kai Yaya Suleiman yayi yace
“Is not as if Dama nace Ina sonta ne, kawai tana birgeni, tana cikin Favorite mutane da nake ji dasu. Ina tunanin tayi mistaken wannan da soyayya”1
“Dukda haka ka cutar da ita, tunda kasan cewa tana sonka, kaga kenan yaudarar ta kayi”1
Hannu ya daga mishi yace
“To Se me? Nace ta soni ne, I’m sorry for that. “
Duk abinda suke fada Ina tsaye Inaji, Dan da nayi gaba ban tafi ba, jikin katuwar pillar dake kofar shiga palor na tsaya Dan nasan bazasi Shiru ba. Bantaba sanin zuciya Tana suya ba se wannan ranar, kirjina tamkar an zuba wuta Haka naji, ga Inata kyafta idanu ko zan samu hawaye su sakko amma hakan bai samu ba, Illa karawa kaina zafi da nayi.
Ina shiga ciki, Ummaah na fitowa daga dakinta, kallona tayi tace
“Asma’u me ya sameki? Meye idonki Yayi ja? “
Kaina na girgiza, da kyar bakina ya budu nace mata
“Tun dazun Haka yake, baki lura bane”
Kanta ta gyada, dakina na nufa Se ta katseni da fadin
“Na zata zaki daura abincin dare ne. “
Kaina na gyada na nufi kitchen, Inaji tana fadin Idan tayi tsami zanji. Tunda na shiga na kifa Kaina akan kitchen Island, ni daya nasan ciwon da zuciyata, Raina da kwakwalwata ke min, gaba daya I was in shock.
“Tashi ki fada min abinda ke damunki? “
Naji muryar Ummaah a tsakar kaina, da sauri a kuma firgice na dago, tana tsaye
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 18