Share this page
ta zuba min idonta, hakan da nayi nasan ta fahimci tabbas akwai wani abu amma Bazan fada ba, tunda I’m naturally introvert. Kasa ce mata komai nayi, se kawai na shiga store na dakko abinda zanyi amfani dashi, bata bar gurin ba Har seda taga tabbas bazanyi magana ba, sannan aikin Yayi nisa kawai se cemin tayi “Koma Menene, kiyi hakuri Allah yana sane dake” Wannan furucin da tayi yasa Wasu hawaye masu zafi suka shigo sakko min, saman fuskata. Ko damuwa in sharesu banyi ba na cigaba da aikin da nake suma tamkar Kara tunkudo su akeyi Haka suka ta zuba, gaba daya hankalin Ummaah ya tashi, tayi ta rarrashina amma kamar zugani take. Karshe cemin tayi STORY CONTINUES BELOW “Koma daki Ki huta, Bari nayi da kaina” Hannuna na wanke na fita ba tareda nayi musu ba, Dan babu bakin musu a taredani, gani nake idan na sake na bude baki to kuma alamari baci Zaiyi. Hijabina naja na rufe fuskata saboda tsoron kada na hadu da Yaya Suleiman. God so kind, ban hadu dashi ba, da kowa ma Har naje daki na kwanta akan gado, kuka nayi tayi kamar Raina zai fita, na kasa tunani saboda Kaina ma a cunkushe yake. Seda na gaji dan Kaina sannan na mike na shiga toilet, har wani jiri nake ji. Fuskata na wanke nayi alwala sannan na fito na tada sallah Maghrib. Ina idarwa naji sallamar Adda Sa’ada, cikeda mamaki na dago ina kallonta, itama ta tsura min idanu se kallona take, hakan se ya karya min zuciya, Wasu hawaye suka shiga sakko min akan kuncina, Dama tuntuni fuskata tayi jawur. Karasa shigowa Adda Sa’ada tayi ta zauna gefena tace “Asma’u! Kiyi hakuri dan Allah, ki daina kukan ai Kinyi da yawa” Hannuna nasa na share fuskata, se naji dan sanyi ya tsirgamin a raina, at least I’ve someone that’s here to comfort me. “Adda Yaya Suleiman yace baya sona, wai shi bai sona” Na fada Wasu hawayen na kara gudu Kan fuskata, Idanunta ta Dan runtse sannan ta bude su akaina tace “Kince mishi kina sonshi ne? “ Da sauri na girgiza mata kaina, nasan banida wani aji daya rage, na rigada na zubar dashi akan nunawa abinda bai sona so, nasan Ina sonshi Kamar raina amma daidai da Rana daya ban taba ayyana nayi splitting masa abinda ke zuciyata ba, koda hakan na nufin zan zauce ne. “To ya akai kika sani? “ Ban daina kukan ba Haka bakina baiyi Shiru na fada mata duk abinda naji, dukda nasan I’m going to have a scolding, tunda ba irin nasihar da Batayi min ba akan na rabu dashi naki, na tabbatar wannan ranar take gudar min, gashi kuma tazo din. “Ki manta dashi, bashi kadai bane namiji a duniya. Nasan Menene so nasan idan zuciyarka tana son abu, mostly Baka ji baka gani, zuciyarka wannan abin kadai take so kuma akwai lokacin da zaki ji zaki iya zuwa kowanne extent dan ki samu abinda kike so. So kenan! Amma ni ban yarda kaje inda baasan darajar ka ba, ban yarda ka zubar da kimar ka a wajen namiji ba, so inaso kiyi hakuri, rabon kwado baya Hawa sama ko ya hau se ya fado. Take heart” Mun jima tana ta bani baki, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na rakata ta gaida Abba sukai sallama da Ummaah ta tafi. Ina dawowa daga rakiyar na iske Yaya Suleiman yana tsaye a parlor alamun yana jiran wani abu, dauke kaina nayi tamkar ban ganshi ba, saboda ji nayi tamkar naje na rufeshi da duka amma babu halin hakan “Asma’u! “ Naji Ya fadi sunana, tsayawa nayi cak kafin na juyo bance dashi komai ba se kallonshi da nake, “Abba yana nemanki” Idanuna na dan zaro nace “Abba? “ Kanshi Ya gyada, fasa shiga dakin nawa nayi na nufi parlon Abba, yana zaune shida Ummaah se Yaya Halifa, muma gefe muka samu muka zauna bayan mun gaida Abba da Ummaah. Gaba daya naji na takura saboda shirun Abba, tunda na gama Year 3 dina nake gudun kebancewa da Abba saboda Ina tsoron yayimin Maganar aure, saboda nasan alkawarin da mukai tun kafin in shiga Medical school. Gyaran muryarshi ya katse min tunanina, dagowa nayi na kalleshi, shima kallona Yayi sannan ya Kalli Yaya Suleiman kafin yace “Halifa ayimana addua “ Take Yaya Halifa yayi opening prayers, wannan ya tabbatar min tabbas Maganar zaayi sede banda insight akan Maganar da Zaiyi amma nasan akanmu ne. “Suleiman, Asma’u! “ A tare duka muka kalleshi, wani irin uneasiness Ya baibaiyeni. Sassauta fuskar shi Yayi, Dan yaga yanayin da nake ciki Kamar ace min kyat na zura a guje. “Naga Dukkanku babu Wanda yake shirin zuwa Yayi min zancen aurenshi, to ni se naga bari na tuna muku. Inason kowannenku zuwa next week ya zomin da kwakwarar Maganar! “ A zabure nace “Abba, next week? “ Kanshi Ya gyada yace “Akwai problem da hakanne? “ Jikina a sanyaye na girgiza Kai sannan nayi kasa da kaina, gaba daya hankalina ya tashi, to ya zanyi ni? Wa xan cewa ya turo tunda ni ko saurayi bani dashi, Tundaga wannan lokacin hankalina ya gushe bansan abinda aka tattauna anan parlon ba dukda ina zaune amma hankalina baya gurin, Yayi nisa, Ya tafi nazarin maganganun Abba. Washegari dana fito seda kowa ya tambayeni abinda ke damuna saboda yadda idanuna sukai zuruzuru, kana kallona Kasan Ina cikin damuwa amma nayi tunanin Dan da kyar bacci ya daukeni saboda Tashin hankali. Ko yadda nake aiki Ka kalla akwai alamar tambaya, komai bana jin dadinshi, kawai dai Inayi ne Dan babu yadda zanyi,. Na gama hada breakfast ban kai ga fitowa ba naji sallamar Yaya Suleiman, Dama tunda mukai wannan abin ba mu sake magana ba, banda kiran da yayi min. Zuciya kenan wani bangaren se yake Murnar ganinshi yayinda wani barin ke kallonshi a matsayin mayaudari, maha’inci kuma azzalumi. “Asma’u Biyani! “ Juyowa nayi na kalleshi, Bazan iya tuna lokacinda naji ya kirani da Asma’u ba, Bazan iya tunawa ba. “Sorry for what? “ Na tambaya ina iyakar kokarin nuna strenght dina, dukda lokacin battling ake internally, zuciyata gaba daya tayi rauni Har tana son affecting muryata. “Nasan Kinji Duka Maganar da mukai nida Khamis jiya akan Maganarki. Bansan kina sona….. “ “Sonka? Ni? “ Na fada Ina nuna kaina da middle finger dina, Kaina na girgiza nace “Meyasa zan soka? Haba Yaya Suleiman Kamar yadda Kake jina matsayin special sister Haka na dauke ka. Ina fata zakai clearing abinda ya cunkushe maka kanka! “ Daga Haka na raba ta gefenshi na fice, a fuskarshi naga disappointment, yaji haushi na fada masa Haka, yafi son nayi ta dakon sonshi bayan shi ba sona yake ba. Tundaga ranar na cireshi a cikin rayuwata, gaba daya na koma masa Asma’u ta da, Bama taba zama muyi Maganar Arziki Ni dashi, naji na tsaneshi bana son ganinshi a rayuwata. AyshatuuuWani irin mugun jiri ne yake neman kayar dani, bansan na damke trolley da aka hada kayan da zaayi surgery ba, take kuwa kowanne ya zube, Haka nima nabi trolley nayi baya zan fadi, amma na bude idona da kyau da suke min wani irin blurred vision, gaba daya head surgeon din, assistant, scrub nurses da Anaesthesist din suka jiyo suna kallona, bakina na bude danyin magana amma na kasa saboda wani baya da na kara yi, daga nan ban kara sanin me ake ciki ba, na suma. Farkawa kawai nayi na ganni an maidani ward, hannuna an daura min drip yana shiga slowaly. A hankali na tashi na zauna ina tuna abinda ya faru, ranar shi ne karona na farko dana Fara shiga operation theater a rayuwata, tunda akace Dani zaayi surgery gaba daya hankalina ya tashi, saboda Ina tsoron jini, bana son ganin jini, amma nasan tunda na zabi yin medicine dolene nayi hakuri nayi adapting. Muna shiga, mukai changing sannan mukai scrubbing aka hada komai, ina gefen surgeon din yana tamin bayanin procedure da zaayi. Tunda ya karba scapel na runtse idona, Ina jin tsikar jikina yana tashi, yana yankawa naji yawu ya cika min Bakina, amma haka nayi composing kaina, har aka shiga deep, ai lokacinne naji jiri Ya fadar dani.+ Kaina na dafe ina ayyana abinda ya faru bayan na fito, yadda na zubar da kayan aikin. Da kaina na cire drip din sannan na tashi na fito zuwa Nurses station, suna zaune dukkansu suna ta Rubutu cikin files din patient. “Kin farka, Sannu! “ Daya daga cikinsu ta fada, zama nayi nace “Yawwa, Sannunku da aiki” Dukkansu suka dubani sannan na koma theater, lokacin sun gama suna lounge suna hutawa na shiga, gaba daya suka dago suna kallona, seda na gaidasu sannan na zauna nace “Sir I’m sorry, I was carried away ne” Kanshi Ya gyada yace “Oh I see! Ya jikin naki Yanzun? “ Ajiyar zuciya me nauyi na sauke nace “I’m feeling better, Alhamdulillah!” Kanshi Ya gyada yace “Kije hostel Ki huta, you eat before coming to theatre. “ Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na dauki kayana na nufi hostel Dan na huta. Wanka nayi sannan na kwanta akan gado take kuwa bacci yayi gaba dani, Dama tunda na dawo daga gida bana samun isashen bacci saboda tunanin yadda zan bulowa Abba nake, ya zanyi da Raina, Ina zan samu mijin da zanyi presenting ma Abba. Shiyasa ko abincin Arziki bana samu Ina ci, ko na Fara ma se Inji gaba daya Ya fita a Kaina. Ina ganin Harda hakan ma yasa na fadi, Dan gaba daya bana cikin nutsuwata. Se bayan Sallar laasar sannan na tashi, wanka na karayi na shirya cikin simple Abaya nude peach nayi rolling da farin mayafi sannan na fito da wallet dita na tafi wani eatery nayi order milk shake da pancake da akai topping dinsa da strawberry. Ina fara ci naji gaba daya an zare min apepite dina, se kawai na jingina da kujerar da nake Kai na lumshe idona Wanda yake kokarin zubar da hawaye. Ban taba kawaowa zan iya shiga Tashin hankali makamancin wannan lokacin ba, gaba daya ji nake an saka min pressure da yawa, dama ace Ina da saurayi it will be better amma banida kowa ina Abba yake son na samu saurayi. Mikewa nayi na fice bayan nayi settling bill din, a hankali naji iska me sanyi tana kadawa, Hatta rigar dake jikina seda ta kadu, yadda iskar keda sanyi Haka nan zuciyata ta Fara sanyaya. Na kusa hostel naji an Kira sunanna “Dr. Shahada! “ Juyawa nayi inda Maganar ta taho, Dr. Ammar ne course mate dina, Dan Murmushi na saki suka karaso shida Dr. Umaymah. Suna zuwa Ammar yace min “Shahada Oga Mansur yace bakida lafiya “ Faint smile nayi nace “I zoomed out a theater. “ STORY CONTINUES BELOW Gaba dayansu suka Fara dariya, nima ina tayasu, nan Umaymah ta bamu labarin yadda tayi nata dake O&G take. Munata dariya muka samu wani bench muka zauna munata hira, yawancin Kan yanayin karatunmu ne da kuma aiki, seda aka Kira Sallar Maghrib sannan muka tafi hostel nida Umaymah shi kuma Ammar ya wuce masjid. Asiya kadai ce a dakin, ta gama dafa noodles, Ina shiga tace Nazo muci, kaina na girgiza tareda yi mata godiya sannan na kwanta akan gado na tunda period nake. Na jima a Haka se naji sallamar Amina Aminu, tashi nayi na zauna dan nasan gurina Tazo, hannunta dauke da handouts dinta ta zauna gefena tace “Kai ashe kin samu sauki, akacemin bakida lafiya “ Dariya na danyi kadan nace “Ki ce an bazani na fadi a theater, shit! “ Tashi tayi ta dakko katon mirror dake kafe a dakin ta kawo min, tareda haska min fuskata gaba daya nayi wata iri Kamar bani ba, duk na rame se haske Dana karayi, fuskata ta kankance. Seda ta tabbatar na gama sannan ta mayar dashi inda yake a kafe ta dawo tace “Asma’u, zan iya cewa tunda nake kawaye bantaba Haduwa da Mutumin da nake so har cikin zuciyata irinki ba, ni ina daukarki matsayin yar Uwa wadda muka fito ciki daya da ita, Ina son halayenki they’re the best so far. Amma sede baki daukeni yadda na dauke Ki ba. Nayi tunanin kawaye sune mutanen da kake zuwa su Baka shoulders din da zakai kuka akai, nayi tunanin shekara hudu da Doriya da mukai daidai da Rana daya zaki cemin Amina gashi wannan abin yana damuna ya zanyi? Sede ni duk abinda ya sameni Shahada ce zata Fara ji….. “ Gaba daya naji kunya ta lullubeni saboda nasan Inada mugun zurfin ciki, bana son fadawa mutane damuwata Ina ganin tamkar na daura musu nauyi ne amma wannan karan Amina Na kaita bango tunda har tayi confronting dina. “Amina Dan Allah kiyi hakuri, ba haka bane, kawai bana son Ina damun mutane da damuwata, se naga kamar zan takura su” Kanta ta girgiza tace “Ko daya Shahada, baki San idan kika fada ba Kamar kin rage tasirin damuwar, ba dole se kin fada min matsalarki ba amma at least ki samu Wanda kike ganin kin yadda dashi ki fada… “ Kaina na girgiza nace “Kai Amina, ba haka bane wallahi Kinsan…. ” se kuma na kasa cewa komai Illa hawaye da suka Fara saukar min akan kuncina, hannuna ta rike tace “Ya isa dan Allah, kada kiyi kuka roommates dinki suzo suna tamabayar ko lafiya. Nasan ke kadai kika san yadda kikeji amma ki sani Allah will always lay a helping hand! “ Daga nan bata kara magana ba se lallashina Har seda nayi shiru sannan na sanar da ita yadda mukai da Abba, nace “Amina banida saurayi balle na tura, kuma Abba is very serious about it, na rasa ya zanyi ki bani shawara! “ Kallona tayi sannan tace “Yaya Suleiman fa? “ Ai se ta kara tunzura ni, nayi ta kuka inajin Kamar zuciyata zata fito saboda zafin da take min, nanma lallashina tai tayi kafin tace “Kun rabu kenan! Wannan kukan said it all. Kinsan wani abu, ni ina daukar aure a matsayin lokaci ne, idan yazo ko ka shirya ko baka shirya ba se kayi, sannan abune da Bazaa ce kayi rushing dinsa ba, ba Kasan hannun da zaka fada ba. Kwanakinnan aure Tsoro yake bani saboda yadda nake ganin anayi yana mutuwa, ana complain se naji Kamar kada nayi Shahada. Yawancin auren soyayya ne amma Se kiga an Kare da Tashin hankali, so Wanda suke son junansu kenan. Shahada tell Abba ya kara miki lokaci, Dan aure ba Nepa payment bane ko gidan haya balle a baka notice. Sannan kada wani pressure yasa ki fadawa unprepared marriage Baki San inda zaki fada ba. I hope I’ve helped! “ Naji dadin shawarar ta, ta saka na warware har tayi mana order aka kawo mana mukaci, mukai Karatu har 12am sannan ta Kara min nasiha ta tafi. Amma Se na kasa samun karfin gwiwar zuwa gida har lokacinda Abba ya bani Har ya wuce, kullum se Munyi waya dashi amma bai taba cemin uffan ba, Haka Ummaah nasan zuba min ido sukai. Kullum idan zan fita se nayi adduaar Haduwa da miji amma Ina ko tareni ma baayi sede ayita kallona Kamar zaa cinyeni amma babu me cewa wani abu. Wata safiya mun gama ward rounds gaba daya mun taho yan team dinmu, Dr. Badamasi wani Consultant nabi office dinshi na consultation ina ganin yadda yake, yana tamin bayanin conditions iriri da management dinsu. Wayata dake cikin clutch dita tayi ringing, kallonshi nayi yace. “Feel free, pick your call! “ “Thank you! “ Na fada sannan na dakko wayar, Sunan Dana gani seda gabana ya fadi, Yaya Suleiman ne, kashe wayar nayi na koma na cigaba da abinda nake amma kwatakwata hankalina yaki zama guri daya, se tunanin dalilin da yasa ya kirani nake, me zai cemin? AyshatuuuKarfe daya na Rana, Dr Badamasi yace na tafi na huta, fitowa nayi tareda kunna wayata na kira Amina Aminu Dan naji inda take, cemin tayi tana Lounge, can na tafi a hanya muna gaisawa da mutane. Naje zanyi kwana na shiga lounge din naga mutum a gabana Yayi min tsaye, dagowa nayi na kalleshi kamar yadda ya tsira min idanu, dauke kaina nayi nace “Ya akai? “ “I need to talk to you “ Kaina na girgiza nace “Sede wani lokacin Yaya Suleiman, Munada lectures “ Daga Haka na juya zuwa inda muke lectures, saboda bana son ya karyata ni ko kuma yaji saboda shi nayi karyar. Biyoni Yayi yace “Asma’u yaushe muka fara yar haka dake, nasan posting kuke ta Yaya zakice min zakije lectures. Kiyi hakuri I know I was a monster, nasan kina sona amma…..” Juyawa nayi na watsa mishi wani kallo na wulakanci nace “Na taba ce maka Ina sonka? Ko na taba turowa nace ace dakai ina sonka? Ko daya banyi ba. Ka isheni ka dameni, ka rabu dani Haka manaa”+ Hannuna yaja har seda muka zauna Kan Wasu concrete chairs, babu kowa a gurin kuma Allah yaso dukkanmu babu lab coat jikinmu. “Naji bakya sona amma wannan ramar da Tashin hankalin dake akan fuskarki na Meye? “ “Ina ruwanka? Dama abinda kazo kaji Kenan? To ni Inada abinyi” Daga Haka na mike zan tafi yayi saurin cewa “Kada ki tafi Asma’u, kawarki nake so, kawarki Nadiya! “1 Bansan yadda naji a wannan lokacin ba, amma kafata kasa dagawa nayi, na tsaya cak inajin yadda kirjina yake wani irin bugawa, Innalillahi wa Inna ilahil rajiun kadai nake ambata a raina, ji nake kamar ana ripping min zuciyata, Kawarki Nadiya na sake maimaitawa cikin kaina. Gabana yazo Ya tsaya yace “Nadiya kawarki ita nake so, inda kin yadda kina sona dazan iya hakura da ita amma tunda perception dina ne Ina ganin gwara nabi son zuciyata” Tunda ya Fara magana nake kallonshi, gaba daya kaina ya kulle na kasa tunanin abinda ya kamata nace mishi, se kawai na saki Murmushi me ciwo Wanda gwara ace kuka nayi tayi, amma tunda nace bana sonshi, ban taba sonshi ba, I’ve to prove myself. “Yau zata dawo daga Yola, gobe Zanje na mata magana. “ Na fada a sanyaye na tafi cikin sanyin jiki, idanuna suka cicikko da kwalla, amma Banason nayi, nafi son Se na kebe Se nayi amma seda ta samu damar zubowa, saurin gogewa nayi na cigaba da tafiya, dakinsu Amina Aminu naje, babu kowa hakan yasa na kwanta gadonta nayi ta kuka, a raina Ina tsinewa Yaya Suleiman da yayi sanadin rabani da farin cikina. Seda nayi me isata sannan bacci yayi gaba dani. Acan gida, Abba da Ummaah Har sun gaji da zuba idon ganin ta inda zan shigo gidan, tunda nayi sati biu Ummaah ke saka ran zuwana amma har nayi uku Ina neman karasa na hudu Bbu alamata. Ta kira Adda Sa’ada tayi mata complain Adda Sa’ada tace ta rabu dani Zanzo da kaina. Abba kanshi seda yace da Ummaah tace min ya janye min Maganar na dawo gida amma Ummaah tace ya barni Zanzo da kaina. Se dare sannan na dawo hayyacina, bayan Munyi Karatu na koma dakinmu, nayi wanka na fito zan shirya kawai naga mutum akan gadona, Nadiya ce “Omo… Omomo! Yaushe kika dawo” Hannnuna taja na zauna tace “Dazunnan Lady, Bazan iya jira Har Se gobe ba” Murmushi nayi nace “Bari nayi sauri na shirya mu fita waje.” Tana ta min hira Har na gama shiryawa sannan muka fito tare, wani secluded area muka samu nayi mana order aka kawo sannan muka zauna. Nayi farin ciki saboda Rashin magana wani lokacin Yayi a rayuwa, da ban kasance marar surutu ba, da tabbas na fadawa Nadiya yadda mukai da Yaya Suleiman, Allah Ya taimaka indai mukai waya se nace mata idan ta dawo akwai magana, Dana tabbatar bazata taba amincewa da zancen soyayya da Yaya Suleiman ba. STORY CONTINUES BELOW “Ma’u duk kin rame, me yake damunki haka, kinganki kamar ba Asma’u ta ba” Murmushi nayi nace “Mhmm, Karatu ne yake cakar Dani, I’m about to start project. “ Been the Nadiya she always is, seta yadda da abinda nace nan muka fada hira sosae anan nace mata “Nadiya Ya Farouq? “ Tabe Baki tayi tace “Ba nace miki Munyi breaking ba, ai tun wannan fadan da mukai muka kasa fixing abin, se naji Ya fita kawai akaina, I can’t continue with someone like him. “ Kaina na gyada nace “Ki dinga hakuri and whatever, Dama ke dashi since from the start you were not meant to be. Yaya Suleiman yace yana sonki kum…… “ Kallona tayi da confusion tace “Yaya Suleiman Wanne? Naki Wai?” Hannunta na kama ina Murmushi nace “Meye kike wani panting saboda nace yana sonki, Eh Yaya Suleiman na gidanmu. Yaushe kike free na rakoki” Tsira min idanu tayi tana kallona tamkar tana son karanto wani abun, kaina na dauke saboda idanuna are weak zasu iya badani Susa naji Kunyar da Bazan manta ba. “Behind wannan smile din naki, Ina hango damuwa a tattare dake, Ki fada min abinda yake damunki mana, ni ce Nadiyanki fa” Murmushi nayi nace “Kinsan talks dinki yana sani kuka ko? Maganar Yaya Suleiman muke. Ya kike ganin. Can you? “ Kallona ta kuma yi, a take na fahimci me take nufi ba girgiza Kai nace “Karkiyi tunannin dating muke da, A’a we were just favourite cousins kin gane? So ni ce babbar kawar Amarya, babbar Aminiyar Ango. How do you see it? Abin Yayi ko? “ Rungumeni tayi tace “Duk tunanina soyayya kuke shiyasa nake hesitating karbar zancen. Ke a matsayin sister dita wacce shawara kika bani? “ Gyara Zamana nayi nace “Ki amince, so far mun jima tare dashi kuma ko a family ana yabon shi. Beside Mamanshi batada matsala. Sede nace all the best “ Bakina na bude tareda kawar da kaina saboda hawaye da naji yana neman bada ni, hura iska nayi tayi har na hadiye hawayen sannan na samu muka cigaba da hirar mu. Da daddare nayiwa Yaya Suleiman text din number ta, address dinta sannan nayi mishi fatan alkhairi, Ina kallo Yayi ticking alamun delivered ai se kawai na Fara kuka, na sadaukar da abinda nake so, na tabbatar kodan wannan Allah zai bani lada kuma ya duba lamurana. Tun Ina tunanin Yaya Suleiman zai Kira har na fitar da rai, se Washegari da yamma ya kirani akan na shirya muje tare, kawai se naji Ya raina min Wayo da yawa hakan yasa nace tutorial Zanje kawai ya tafi. Kamar wasa Nadiya ta kirani tana tamin ihu, Dama Haka Yayana yake, haka ya hadu Haka ya iya soyayya, karshe kasa karasa Maganar mukai nayi pretending network baida kyau na kashe wayar. Ranar da na cika sati biyar banje gida ba, muna ward, Senior Doctor da nake bi yana call so muna tare dashi Sega Amina Aminu tazo, seda ta gaida Dr Mike sannan suka gaisa da Nurses din kafin tace min “Asma’u Kinyi Bakuwa! “ Kallonta nayi nace “Wacece? “ “Zo muje Ki gani” Allah yasa mun gama abinda zamuyi Hakanan na bita muka tafi lounge din da muke, Tundaga Nesa naji gabana yana faduwa, amma ban kara tambayarta bakuwar ba. Ina shiga na tarar da Ummaah a zaune gabanta an aje mata lemu da ruwa, se naji wani dadi ya mamayeni, naji sanyi a raina. Rungumeta nayi ta baya nace “Ummaah! “ Hannuna ta bubbuga tace min “Ai fushi mukeyi dake. Saboda Allah Asma’u sati biyar kina Kano amma Bazan kizo gida ba. Me akai miki? “ Murmushi nayi na zagayo na zauna, tareda kwantar da kaina kafadarta, Murmushi yaki barin fuskata nace “Ummaaah bansan me zance muku ba, amma banida saurayin da zan kawawa Abba shiyasa” Cikeda tausayi na tace “Shiyasa? “ Kaina na gyada nace “Ummaah! “ Kanta ta shiga gyadawa tace “Komai nufi ne na Allah kada Ki takura Kanki, Allah is the perfect timer, so abinda yake naki zaixo sede idan lokaci baiyi ba “ Mun jima munata hira, Tana ta kwantar min da hankali har tace min wani sati zaaje tambayawa Yaya Suleiman auren Nadiya, dukda Nadiya ta fadamin amma seda naji gabana ya fadi, zuciyata ta motsa, nayi saurin kawar da hakan muka cigaba da hiraramu. Ina samun sukuni na tafi gida, kullum ina zuwa daga can, the only time nake kwana cikin asibiti sede idan Munada call ne. Batun Suleiman tamkar da gayya yake Wasu abubuwan duk abinda ya faru tsakaninshi da Nadiya, ni ke Fara sani Tun Ina damuwa Har na hakura, a Haka Manya suka shiga aka saka rana. Ranar nayi kuka Kamar zan fitarda idona, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na hakura, a wannan lokacin muka fara exams na shiga final year. 2 AyshatuuuTunda muka fara exams na maida hankalina kacokan, na share duk Wasu Abu da zasu kawo min tsaiko akan exams din amma dake Allah shi ke handling komai, kuma bazakai cheating nature ba. A karshe dai I break the record, seda na fadi wani course under paeds. Omomomo! Nasha kuka Kamar zanyi hauka, saboda na tabbatar damuwar da nake ce ta sani a ciki. Abba was the only one that supported me amman su Yaya Halifa

Chapter 6 of 18