Share this page
saboda ciwo kwana biyunnan abinda ke damuna kenan ciwon kai. Nayi tunanin stress ne amma it seems kamar akwai wani abu. Fanta nasa aka karbo min na zauna a station ina sha, anan na lura da kafata ta fara kumbura, kallon Metron nayi nace mata a gwada min BP na. Da kanta ta gwada min, na kalleta da mamaki kamar yadda take kallona with amazement tace “Kin gani?” Da damuwa a fuskata nace “I can’t believe it, ya BPna haka?” Kara gwadawa tayi amma reading is still very high, no wonder nake ciwon kai wani lokacin har ina ganin dishi dishi nayi tunanin ciki ne da nake tunanin ya shige ni yasa hakan. Wayata na ciro daga aljihu na jin tana ringing na dauka , Jewel ne “Cara Mia ke muke jira” A sanyaye nace masa ganinan haka na mike babu wani karsashi a tare dani na tafi OT, dukkansu sun shirya so ina shiga nayi changing muka fara aiki. Sosae na daure dan kada ya lura and God so kind bai fahimta ba har muka gama. A ciki na barshi naje na zauna nayi documenting komai sannan na fito daidai lokacin shima ya fito yana gyara hannunsa. Kallona yayi yace STORY CONTINUES BELOW “Ya dai?” Kaina na langwabar nace “Tired” Kanshi ya girgiza yace “You look worried muje” Bayan shi nabi muka tafi office dinshi, seda na zauna sannan ya zauna gefena yace “Ya akai” “BPna ne yayi shooting” Idanunshi ya ware yace “Haba? How comes? Nawa yake reading” “180/110 fa” Mikewa yayi yana girgiza kai ya sake gwada min, glasses dinshi ya cire ya zauna gefe na tareda cuddling dina jikinshi yace “Baby, me yake damunki?” Kaina na girgiza inajin wani rauni a raina nace “Allah babu komai. I dunno!” Se hawaye ya fara saukar min, rungumeni yayi yana bubbuga min baya har Seda nayi shiru dan kaina sannan yace “To meye abin kukan kuma? Kiyi shiru kinji.” Hawayena ya share min sannan ya dinga kwantar min da hankali a haka na hakura. Bai daura ni akan drugs ba kawai se yace bari a fara gano sudden rise din. Da muka koma gida ko girki banyi ba se kyaftun ce ta kawo mana dan da kanshi ya fadawa Lamin. “To kiyi pt mana ki gani ko ciki ne” Kyaftun ta fada min ina cin abinci, kaina na girgiza nace “So nake se lokacin period din yayi idan banyi ba se nayi” Shikenan muka cigaba da hira har dare seda ya dawo sannan ta tafi ita kuma yinin ymin dadi sosae dan na jima banyi irinshi ba. A hankali kuma se yau ya hau gobe ya sauka munata monitoring se daddare yace ya kamata muje ayi pt a gani yana tunanin matsalar daga ni ne. A gida mukayi abinmu and it was positive sede dukkan mu babu wanda yayi murna tunda kuwa yazo da matsala. Bayan munyi sallar ishai muka shiga cikin asibiti don yayimin scanning aikuwa ana yi, ya cemin “Cara mia molar ne” Kallon screen din nayi dama jikina ya bani shinkadai ne zai saka BP ya tashi at early pregnancy bayan munsan normally first trimester ana samun low BP. Tissue yasa ya goge min cikina yace “Sannu kinji” Kaina na gyada kawai na kasa cewa komai, molar gestation? Ni kuma da abinda zan fara kenan. A haka yana ta kwantar min da hankali mukaje gida. Yana ajeni ya fita se gashi ya dawo da ice cream. Kallon shi nayi nace “Is that a bribe?” Kanshi ya girgiza yace “Not at all, inason naga kina murmushi ne” Dariya nayi nace “Gobe se naga Dr halima se ayi booking dina” Kanshi ya gyada yace “Nayi mamaki da kika samu molar bayan yafi zuwa mutane below 20years da kuma above 35years” “A book kenan, Allah a gurinshi it doesn’t matter” Kanshi ya gyada min yace “Yeah!” Molar gestation kamar ciki yake amma tumor ne but non cancerous sede idan baayi da gaske ba zai iya zama cancer din. Mostly yana faruwa saboda anyi fertilizing empty ovum ko kuma sperm cells biyu sunyi fertilizing ovum daya, yaron memakon 46 normal chromosomes zai samu 96 saboda an samu duplicate copy. Scanning ke nuna cewar wannan molar ne. Se terminating dinshi akeyi da zarar ansan shi dinne. Washegari bamu fita da wuri ba se wajen 9am muka tafi, office din Dr halima muka fara zuwa tana ganinmu ta mike tareda bamu guri muka zauna. Seda muka gaisa ya mika mata scanning dina , kamar patient haka tayi counselling dinmu sannan tayi admitting dina a Amenity. Kafin wani lokaci har yan dubiya sun cika na rasa inda zan tsoma raina. Da yamma tazo ita dashi aka kaini OT akamun suction evacuation. Lokacinda muka dawo anesthesia bata sake ni ba inata bacci. Se bayan isha sannan na farka lokacin shi daya ke zaune a gefena. Tashi nayi na zauna bayan ya taimaka min yana ta faman jera min sannu. Abinci ya kawo min bayan nayi brush naci sannan nayi wanka aka shigo serving drugs nurse din tayi sannan tayi mana sallama ta tafi. STORY CONTINUES BELOW Ban tashi da wuri ba se wajen tara na safe, ko ina neat dana tashi so wanka na shiga na fito na shirya cikin abayar da ya aje min sea green se maroon dankwali na daura na zauna tareda daukar wayata na kirashi, yana dauka yace “Kisa hijabi gamu nan zuwa” Ya kashe hijab na janyo na saka tareda daidaita nutsuwata. Sallamar shi ta katse ni ya shigo fuskarshi da murmushi bayan shi duk manyan asibitin ne. Cikin nutsuwa na gaishesu sunata amsawa sannan suka dubani, my God kyauta dai na sha ta. Nayi musu godiya suka tafi sannan ya dawo tareda zama gefe na yace “Na gaji Asmau” “Ka huta kafin ka tafi” Hannunshi ya kai jikina danjin temperature sede all normal se ya mike yace “Bari na tafi kada na hana mutane dubiya” “Aikuwa dai dan kowa yasan kana nan ba zuwa zaayi ba.” Dariya yyai ya fice nasha dubiya kuwan, da yamma akai discharging dina hade da bed rest kawai se muka tafi kano. Se lokacin su Ummaah suka sani, washegari se gata tazo ranar kamar bakina zai yage dan murna bata jima ba sega Hajiya daga hadejia, i was super excited. A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, kamar yadda Allah ya tsara mana. Rayuwa mukeyi cikin aminci da mutunta juna. Na fahimci sosae me rayuwa take nufi me aurenn shi kanshi yake nufi. Akwai lokuta da dama da nake jin kamar na bar gidan, musamman idan muka sami sabani naji kamar wuta ake zazzaga min but dake ni dashi are all matured minds haka muke hakuri mu dangana. Dadin a nawa yafi rashin dadin yawa, so babu abinda zance se godiyar Allah. Shekara biyu nayi inata bari seda nayi planning na five months jikina ya huta sannan na samu ciki. Zo kuga tattalli dama lokacin na gama course dina akan family medicine so kawai se na zama a consultation room nake. Munyi rainon ciki babu kakkautawa wayaga dan Doctor da Doctor? Yasha kulawa scan dinmu na farko ya bani mamaki, it shows triplets yayi ta murna ni kuma ina kuka saboda ina tunanin ta ina zan fara wannan rainon, seda ya gama murnarshi kafin ya zauna yana ta bani baki da nuna min CS ne ba wani abin ba. Aikuwa dake Allah shi ne Allah, babu wani pregnancy complications banda kumburi shi kenan, ina seven months inna ta rasu. Nayi kuka kamar me seda nayi sati a kwalam kafin na dawo, to rayuwar duka nawa ce ma. Da kyar na kai 36 weeks babu pain ko daya aka ce mana kawai ayi CS din zaifi, tare dashi aka shiga aka kaimin sede yana gefe na saboda ba GA bace idona biyu. Ana cirowa ana weighing ana miko masa, first one din namiji ne se mata biyu. Mashaaa Allah kawai. Ana kaini na huta kamar kasa mutane naga soyayya ko nace triplets dina sun gani. Kyaututtuka kam har seda na daina gane wannan na waye. Ranar suna ya saka musu Muhammad, Khadija da A’isha. Ba sunan kowa bane se gidan annabi da ahalinsa. Bayan shekara uku sun girma, duk wanda ya gansu yana shaawarsu not knowing ni irin wahalar dana sha. Shekararsu biyu na dage seda aka kaisu school saboda na gaji, kullum kaina kamar zai tsage ga na patient ga nasu, shidai sede ya kalleni yace I’m his everything, he can’t imagine life without me. Shekararsu biyar muka tafi Ukraine, dukkanmu karatu ya kaimu. Tun daga kansu ban kara samun ciki ba saboda nasan uterus dina is very weak idan na matsa mata zaa samu matsala gwara na huta da kyau. Asabar ce weekend ne, tun sassafe na tashi na shiga kitchen, it’s Saturday kowa yana da damar da zai zabi abinda yake son yaci, wannan shi ne yancin dana basu dukda I’m a very strict mother amma kuma ina wasa dasu dan idan muna wasa bazaka ce ni ke fada ba. List din na duba, Muhammad nasan noodles, Khadija na son strawberry pancake ita kuma A’isha tace scramble egg da bread zataci. In a jiffy na harhada komai, Daddy dani we always have same choice saboda our hearts and soul are connected komai hakan ke so. Gyara gidan nayi sannan nayi wanka har lokacin tara da rabi basu tashi ba, seda na shirya sannan na tada daddy ko ta kansa ban bi ba na tafi gurin yarana, yana ta mitar wai na daina kula dashi nidai bance komai ba se dariya naje, ina zaune sukai wanka na shiryasu muka fito daidai lokacin shima ya fito, da gudu suka karasa suna fadin “Daddy!” “Kiddos” Dariya nayi tateda daukarsu hoto sannan mukai breakfast, muna gamawa aka assignment seda suka gama sannnan na kunnna musu cartoon muka fara namu assignment din. Mun kammallla na kalleshi kamar yadda yake kallona, i imagined him a matsayin mijina, idanuna na lumshe ina tuna rayuwata from lokacinda ta rikice bayan kammalla preclinicals dina, nayi hakuri gashi kuma naci riba, yaran na kalla sunata dariya so peaceful hakan ya kara kwantar min da hankali. A wannan gabar ina kira ga duk wacce batayi aure ba kada ta damu lokaci ne, idan yazo se anyi. We all believe aure habo ne haka wasu kance layin markade ne idan yazo kanka se an markada. Nawa suka aje bucket dinsu aka barar, wasu aka sace, wasu aka saka musu gwalagwaji but still seda aka markada. Ina fatan dukkan yanmata zasui koyu da rayuwata su saka ransu the biggest thing will happen, the patient dog eats the fattest bone! Da daddare muna tsaye ni dashi a gaban balcony, yaran sunyi bacci bayan mun gama video call da yan nigeria, idanuna na daga na kalla sama yadda taurari suka cika sunata haskawa yasa nace subhannallah tareda tabo shi nace “Come on ina son daya” Kalla yayi sannan ya kalleni yayi murmushi nace “Ka kamo min mana” Kallona yayi cikin idanu, wasu molecules suka samu damar ratsa lens din har retina inda ya tafi kwakwalwata ya tarwatsa komai, shi kadai ne a duniyata no one exist again se shi. “I’ve already got my star here” Ya fada yana nuna ni, rungumeshi nayi na fara bashi wani sensual and seductive kiss, da kyar muka koma daki and he gave me something as sweet as honey! Alhamdulillah!!! This piece of work is dedicated to any unmarried lady or a spinster, Allah will make it happen so don’t lose hope my dearies. Wanda Allah ya kaddara naku ne suna nan zuwa and they will for sure take you. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 18 of 18