Share this page
ba, Ummaah tayi fadan ta tareda jadadda min akan next weekend na tabbatar naje kwalam bikin wata neice dita, wannan nasan bazan tsallake ba, dole ne naje idan kuma ba wani problem nake son karawa kaina ba. Ranar sunday muka hadu, Dr lamin, Dr Hafiz, Dr fadima, Dr Habiba, kyaftun dani muka shirya zuwa rock climbing. Tunda na tashi da asuba nayi wanka nayi mana toasting bread sannan na daukar mana drinks. Cikin leggings da knee length top maroon na shirya, nasa hula maroon se nayi rolling veil karami sannan nasa wani black canvas na tsaya a meeting point. Anan na tarar da Lamin da Habiba. Muka gagaisa sega kyaftun da fadima. Dr Hafiz ne ma yadan yi delaying har muka so makara. Garu mukaje inda zamu wani mutumi yazo danyi mana rakiya , tunda muka fara hawa dutse na fara ihu saboda abin ba na wasa bane, a daddafe wani lokacin se an ja hannunmu sannan muke iya hawa a haka dai muka kai karshen gurin. The amazing veiw ever. Aerial view din was wow mukai ta hotuna, nayi farin ciki, nayi dariya wadda take from the bottom of my heart bawai yake ba kamar yadda na saba yi. A wannan lolacin na manta cewar inada damuwa na manta da duk wasu matsalolina na kalla sama saboda yadda nake very high se naga kamr zan taba gajimare. I was so happy.1 STORY CONTINUES BELOW Wajen sha daya muka koma prison dinmu, kowa ya tafi dakinshi, ina zuwa na cika bath da ruwan dumi na shiga da towel na gasa jikina, ina fitowa na sha pain reliever naci pasta sannan n kulle dakin na fara bacci, God so kind period nake bani Na tashi ba se wajen biyar da rabi shima knocking ne ya tadani. A kasalance na mike tareda tambayar waye amma babu amsa hakan yasa kawai na wuce toilet na sake wanka sannan na shirya. Sati na kamawa ranar Friday, muna gama rounds na dauki hanya zuwa kwalam. Lokacin da naje zanyi sallama da kyaftun seda ta cemin nayi hakuri duk abinda zan tarar. Tabbas nasan ba wani abin arziki zan tarar ba, banda tsangwama da kuma nuna ni da zaa dinga yi. Anan sakkowa a massallacin jumaa ina shiga garin. Straight Cikin gida na wuce nidai nasan ba tarbar dana saba gani zan tarar ba a gurin Inna amma dukda haka na rugada na saba, indai nazo kwalam da dadi da babu dadi to gurinta nake zama saboda ko me inna zatayi min bazan taba manta alkhairin ta akaina ba. Wannan rikon da tayi min ma kadai ya isa balle yadda ta fifita ni akan sauran jikokinta. Acan gefe nayi parking sannan na ciro trolley ta na rataya hand bag dita a kafada na doshi gidan. Muna dan gaisawa da mutane har Ikram yarinyar Adda Habiba da Badar yarinyar Yaya Hauwa sukazo suka karba kayan nawa muka shiga ciki. Gidan a cike yake anata kidan kwarya wasu na rawa, gefe ana sauke abinci a haka na kutsa kai ina gaida mutane wasu su ganeni wasu suce ai na girma duk kammani na sun canja, nidai nawa murmushi kawai. A dakin inna na tarar dasu Adda da wasu daga cikin cousins dinmu, sunata shiri zaaje gurin kamu banma shige ciki ba na zauna cikinsu munata gaisawa yawanci na jima banga mutane ba kowa se cewa yake na zama babbar mace nayi kudi aure kawai ya ragemin. Sede inyi murmushi kawai. Adda Maryam ita ta tayimin ankon so gurinta na karba nawa na saka ko Inna bamu hadu da ita ba na tafi. Wajen sallar ishai na dawo a gajiye seda na biya ta gida na gaida Ummaah sannan na taho. Nanma banga Innar ba, babu mutane sosae hakan yasa nayi shirin bacci bayan nayi wanka nazo n haye gadon cikeda kewarshi. Rigingine nayi ina kallon roofing din gadon tareda tuna rayuwar da nayi akan gadon, lokacin i was living peaceful banida wani tashin hankali daya takura min amma yanxun wace ni. Wayata na janyo na bude wani Emdex application ne na drugs, na cigaba da studying magungunan. A hankali bacci yayi gaba dani ba tareda na sani ba dama nayi addua kafin na fara karatun. Na jima da yin baccin kamar daga sama naji ana tashi na, da kyar na bude idona raina duk a jagule saboda i hate it idan aka katse min baccin dare. Inna ce a tsaye tana kallona hakan yasa na tashi daga kwancen da nake tareda gyara zaman hular kaina nace “Inna an wuni lafiya? Ya taro?” “Lafiya lau” Ta bani amsa sannan tace “Asmau wannan gadon da kika kwanta akai ki sakko ki dawo kasa” Kallonta nayi da rashin fahimta nace “Ai zai ishemu mu kwanta ni dake, se kace nayi kiba” Kawar da kanta tayi tace “Kinga Amina da Nusaiba ne zasu kwanta akai saboda kinga su ciki ne dasu, kuma me aure bai saba kwanciyar kasa ba” Kallonta nake sosae, maganar ta dakeni idan tacemin sakko Asmau wasu zasu kwanta saboda ciki, ni ai ba hauka nake ba nasan me ciki need something comfy babu yadda zaayi me ciki ya kwanta dandaryar kasa but meye se ance me aure bai saba kwanciyar kasa ba wato dole se an nuna min ni din banyi aure ba kenan. Kaina na gyada nace “To ni ina zan kwana kenan?” Tabarma dake gefe ta nuna min tace “Ki sakko ki shimfida ta” Wani mugun takaici ya kamani nace “Inna, kinfi kowa sanin bana bacci akan tabarma, ina laifin waccan katifar” Na nuna mata extra katifar ta da take jingine, a hasale tace min “Ke sakko daga gadonnan, idan baki son tabarmar kina iya tafiya wani gurin. Yarinya se tsirin masifa da ruwan ido, dole ki kasa aure” Yadda nake kallonta seda yasa ta dauke kanta naji haushi sosae yadda har bazan iya fada ba, kaina na girgiza tareda sakkowa daga gadon na finciki hijab dina da wayoyina nayi waje amma se na dawo har lokacin tana tsaye bance mata ci kanki ba na janyo trolley na da hand bag dita na nufi kofa se ta biyoni tana fadin “Matsalata dake kawata zuciya, meye abin hada kaya?” Juyowa hawaye ya cika min idanu nace “Aure Allah yake sawa ayu, idan lokacina yayi zanyi, gorinku da duk wani tsangwama ta bazai saka nayi ba.” Kafin na gama tuni wasu daga cikin mutanen dake parlor sunzo suna tambayata me ya faru babu wanda na kula nayi ficewata Allah yasa bankai motata gida ba hakan yasa na bude motar na shiga tare da kifa kaina jikin steer wheel na fara kuka, a raina ina rokon Allah ko aron wucin gadi ne yasa nayi, ko ma wanene kawai Allah yasa nayi aure na huta. Seda na gaji da kukan sannan na kira Adda zannira akan ta bude min gida ina nan tafe. A takaice dai acan na kwana, juyin duniya Yaya Halifa yayi akan na fada masa meye matsalata naki suka hakura suka kyaleni. Washegari ban fita ko ina ba ina daki ina jinyar zuciyata bansan waye yace ma Inna ina gidan ba se gata tazo da kwanuka wai na kari nace mata ni na koshi bazan ci ba, ta kada ta raya naki, ko ji tayi abinda tayimin bai dace ba oho mata dai. Da yamma kuma sega Ummaah itama abin mamaki lallashina ta dinga yi har ta tsareni naci abinci sannan ta tafi. Da daddare mamansu Rahina taxo biko akan na koma can gurin inna amma nace ni sede wata kuma, ba dai aure bane to nayi alkawarin ko dan cocaine ne yace yana sona aurenshi zanyi, na gaji da wannan masifar har ina? AyshatuuuuWayata na kalla a karo na barkatai ina kallon text din da Ummaah ta turo min kusan awa daya data shude , numbers ne har guda biyu na GLO da MTN a kasan an rubuta Barr. Ishaq. Kifar da wayar nayi kawai ina jiran inji kiranta dan tayi min karin bayani amma shiru bata kira ba, nima kuma ba kira zanyi ba saboda ina tsoron abinda zatace min, bana son hooking stuffs dinnan gwara no matter how bad a situation is gwara ace shidin ya fara ganinka yace yana so, dan bahushe yace matar cushe bata da kwarjini. I believe in that also.+ Hakan yasa na mike na cigaba da gyaran daki. Ranar call nake so yamma nayi Na shirya na dauki stethoscope da key din mota da wayoyina na fita. Call room naje Na zauna a gefe ina chatting a wayata ni kadai ce cikin dakin, se can aka kirani a Emergency hakan yasa na tashi na tafi na tarar da wani fatal accident. Tabbas aikin asibiti dole yasa ka kara gaskata iko da daukaka ta ubangiji, mutum ba komai bane a rayuwa duk wannan dagun kai da dagawa amma lokaci daya Allah zai iya reforming halittar shi muga ta karshen girman kai. Mutanen da sukai accident su goma ne cikin wata golf, i wonder yadda sukai squeezing kansu cikin wannan karamar motar. Ina shiga na adana wayoyina da sauran abin amfani, O’C dake duty su uku muka hadu dasu dan ceto ran mutanen, amma uku seda suka mutu babu yadda zakayi, sede you will be contented kayi abinda ya kamata tunda duk munsan death is inevitable. Haka sauran bakwai muka sakasu cikin class din daya dace bamu muka zauna ba se bayan sallar ishai. A matukar gajiye mukai sallah sannan na dawo dan nayi documenting aikin, sannan mukai sallama na koma lounge anan na tarar da missed calls din Ummaah. Ina zama na fara kiranta ta dauka nace “Ummaah inata aiki kika kira, ya gida?” “Lafiya lau” Ta bani amsa sannan tace “Kinga numbers da na turo miki dazun?” Seda gabana ya fadi nace cikin sanyin jiki “Na gani Ummaah, inata son na kiraki” “Ni dana matsu ai na kira, kinsan Hajiya Barira right?” Kaina na gyada kamar tana ganina nace “Eh, Ummin Kaduna ko?” Kawar Ummaah ce irin childhood friend dinnan ce , kowa yasan yadda Ummaah ke ji da ita haka itama indai zatazo kano to se kin ganta tazo gurinta. “Yawwa, wannan Ishaq din danta ne na uku zaiyi aure shine nake son ku daidaita kanku, kinga kema kya samu ki huta da gorin mutane” Se nayi shiru tareda adduar Allah yasa ba nufinta in kirashi ba, jin nayi shiru yasa tace “Baki jina je Asmau?” “Ummaah to me zanyi yanzun?” “Kiranshi zakiyi mana, me kike jira da? Come on ki kirashi kice kece wadda Hajia tayi mishi magna akai” Se naji raina ya baci ni zan kirashi ma bashi ba, ok ya raina ni kenan. Ni na gaji da yadda Ummaah ke hadani da yaron kawayenta suna raina min hankali dan wannan shine third time ana hakan. ” Ummaah, dan Allah karki sani nayi haka, shi ku bashi number ta ya kirani mana amma hakan kamar irin neman kai akeyi dani ne?” Baki bude Ummaah tace “Oh da baki gane ba? Shi ai bashi yake nema ba mu muke nema so mu zamui proposing kingane?” Kaina gaba daya se ya kume, I couldn’t think straight wanne irin ni nake nema ni zanyi proposing? Kawai se nace “Shikenan” Kafin muyi sallama ta tambayeni ni na tura mata kudi nace eh, tayi ta shimin albarka har naji dadi sannan na kashe wayar inajin wani abu ya tokare min kirjina, da kyar nake iya fuzgar numfashi na, idona yayi ja ina fatan Allah ya kawomin dauki a rayuwata, ya kawo min miji nayi aure. Dan nasan bani kadai ce a duniya nakai shekarun nan banyi aure ba amma kowa ya takura min an hanani zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hannuna nasa na rufe fuskata nayi ta kuka kamar raina zai fita ina fatan as my tears cascade down my cheeks, all my worries will be gone and my pains will be ease! Ina gama kukan lokacin already goma tayi ko lunch banyi ba balle dinner, yunwa nakeji amma bana tunanin inada nutsuwar zama naci abinci. Mikewa nayi na fito daidai shigowar kiran kyaftun , se naji wani sanyi cikin raina at least someone cares. Ina dauka ta tambayeni inda nake , ko minti biyar ba ayi ba se gata da basket a hannunta, tunda ta kalleni se naji jkinta yayi sanyi , zama tayi ta hadamin tea ta bani babu musu nasha sannan ta zuba min Arabian sphaghetti tasha vegetables haka naci sannan tace “Wannan kuburin na ido me ya faru?” Lumshe idona nayi ai kamar ance lacrimal glands su sake hawaye se suka wanken fuska, hannuna ta rike batace min komai ba se kallona da takeyi , se can tace “Asmau menene akan aurenne?” Kaina na gyada na fada mata komai daya faru, se cemin tayi “Ki kirashi kinji” Wani kallo nayi mata irin are you mad dinnan? Murmushi tayi tace “Ummaah ce tafi karfin komai, just do it saboda haka Ummaah tace” Haka na kwana ina tunanin yadda zan bullowa koda safe dana fadawa Adda Sa’ada cewa tayi nayiwa Ummaah biyayya hakan kuwa nayi dukda jikina a matukar sanyaye yake haka Na kirashi, tunda ya dauka ko sallamar da nayi bai amsa ba yace “How may i help you?” Duk se naji na muzanta amma haka na daure nace “I’m Asmau shahada, ni ce wadda hajianka tayi maka magana akaina” Maimakon naji tone dinshi ya canja se naji ya kara tamkewa yace “Ya akai to?”1 Na kasa cewa komai se wasa nake da hannuna tareda jin mugun haushinshi kamar na shako shi haka naji, jin nayi shiru se cewa yayi “Kinga idan kin shirya bayanin kanki kya kira but I’ve better things to do!”1 Kit! Ya kashe hannuna na rawa na ciro wayar ina kallonta da gaske yayi hanging, take nayi deleting numbers dinshi daga wayata baki daya inajin tamkar na shake kaina tabbas Ummaah ta gama dani. Da daddare ta kirani akan ko na kirashi na fada mata yadda muaki dashi, tsaki tayi tace na kyaleshi to wannan ya dan sayaya min rai. 1 Ana fara tafiya aikin hajji na tafi nima, i badly want to talk to Allah, lokacinda na ganni gaban kaaaba se kuka na rasa abin roka, se kankame jikina da nayi saboda yadda dukkn tsikar jikina ke tashi. Na jima sannan na samu nayi addua dake lokacin mune daukar farko i got the space. A wannan lokacin alkawarin Allah ya cika kyaftun ta auri Dr Lamin. Bayan na dawo nigeria da hope akan nasan da izinin Allah kukana ya zo karshe. Nasan soonest alkawarin Allah zai tabbata kaina amma shiru har shekara take neman zagayowa, banma kara saurayi ba duk yadda nakejin nakai babu wanda ya kalleni da sunan yana sona, nasha tsayawa gaban mirror na kalli kaina, inga ina nake da makusa. Ni fara ce fari sosae har wani yellow yellow nake, idan nayi mirmushi bayan dimple dake lotsawa a both sides na kumatu na, akwai wata jijiya green dake fitowa rado rado a goshina. Idanuna normal suke kamar na kowa sede eye balls dina manya ne kuma deep chocolate orbs nake dashi. Hancina dogo ne bakina daidai ni da kaina nasan im a beauty, akaina na fahimci kyau baya kawo miji se lokaci yayi. Pressure kam se wadda ban fada ba amma akwai lokacinda nayi wata hudu banje kano ba ina dutse saboda Ummaah kamar ta dakeni idan muka hadu ga inna kamar danni ta koma kano saboda girma, kullum gorin yau daban na gobe daban. So se na daina zuwa gidan gaba daya, sukai cigiyar duniya suka rasa. Ranar wata monday na shiga OT yin Appendectomy, ina fitowa straight dama daki nayi niyyar tafiya dan na shirya zanje wata seminar, da sauri na kalla office din Chief Anaestethist saboda jiyo muryar da Abba da nayi. Banma yi niyyar shiga ba haka na shiga and there i saw him sitting looking at me. Da sauri naje na rungumeshi nace “Abbana” Hararar wasa yayi min yace “Nazo biko ne, tunda laifin wasu ya shafeni” Dariya nayi tareda rufe fuskata , i cant remember ni ina dariya genuinely har haka ba. Ranar se dare ya tafi ko seminar bankje ba, tare mukai lunch a cafeteria se naji ina missing gida sosae. Lallashi na yayi yana nuna min komai zaizo karshe. Haka sati na kamawa naje kano se naga babu wanda ya takira min like always do. AyshatuuuuHannuna na zura cikin aljuhun lab coat dita na ciro wayata saboda jin alamar shigowar message a wayata. Message dinne kuwa daga chief obstetrician dake last month na koma gynae team na bar surgical team na fara residency dina. Kallon metron din nayi nace mata “Mummy, zanje meeting idan akwai matsala a kirani” Kanta ta gyada tareda min fatan alkhairi, inason matar she’s mother figure, a dan zaman da nayi a ward dinta tana yawan bani shawarwari masu amfani tamkar tasan matsalata akan aure take kullum ni da sauran nurses dinta akwai topic din da zaayi discussing akai. Kuma baka isa kace ka zauna bakayi gaining wani abu ba. Office din Dr halima na wuce dake ita ce chief din tamu, na tsaya ni da Dr hafiz se gata ta fito in her usual outfit wato lace gown an daura lab coat akai, irin classy mutanen ne yar gayun gayu sosae. Da sauri na karasa inda take nace “Maam naga message dinki gani” “Yaawa nima yanzun nake shirin kiranki muje meeting zaayi na tarbar sabon MD”1 Kaina na gyada tareda bin bayanta munata dan hira jefijefi, a office din Dr Mahmud anan muka zazzauna akai briefing kowa akan washegari sabon MD da akai posting zai fara aiki , seda Dr Rashida ta ja mana kunne akan kowa yayi watching takunshi saboda baya wasa mutumin idan zaayi aiki ayi dan shi baya daukar kailula. Ta tsoratar damu sosae Amma banji komai ba dana nasan bana barin aiki Na unfinished. Haka muka gama se kuma muka koma office din Dr halima danyin meeting da sauran yan team dinmu. Kafin wani lokaci dukkan asibitin kowa ya shiga hankalinsa ko ward ka shiga se gyare gyare akeyi da fito da sabbabin linens a haka dai ranar ta kare na tafi gidan kyaftun.+ Washegari da safe da wurwuri na gama shirina nayi breakfast dan nasan it will be a busy day i know. Hakanan na fito na shirya cikin coffee wando da riga na soft cotton yadi lab coat na daura ban mayi buttoning ba na rataya stethoscope dina a wuya sannan nayi rolling da karamin coffee veil. Kallon kaina nayi a jikin mirror babu laifi idanuna sun fara dawowa hayyacinsu, wannan zurmawar da yayi ciki duk yadan fito dan hankalina ya fara kwanciya na daina tsangwamawa kaina tunda nasan wannan bashi zai bani miji ba. Gynae emergency na fara zuwa muka gaisa da staffs din gurin sannan aka bani patient din da zanyi reviewing. Ina cikin aikin Dr halima ta karaso mukai rounds sannan muka shiga labor room nanma stable babu wani damuwa sosae a ciki nan muka gama sannan nida ita muka fita. Ko ina cikin asibitin tas yake kowa ya shiga taitayimsa haka kowa yana post dinsa se naji zuciyata tana kwadayin ganin waye wannan sabon MD, naji dadi a raina saboda kowa zai dawo hayyacinsa kowa ya fahimci abinda ya taramu a asibitin. Karfe goma dukkanmu muna tsaye a reception Doctors mu shida daga kowacce cader mutum uku muna tsaye dan tarbarshi, wayata tayi ringing na dauka Dr Ema ne wani house officer ne su na bari a labor room akan duk yadda ake ciki su kirani, seda muka gama magana dadhi sannan na fadawa Dr halima ta fadamin yadda zamuyi kawai se na juya na tafi, ina zuwa na tarar matar tana wani irin massive bleeding babu anyi anyi ya tsaya yaki hakan yasa nabi shawarar da sister ta bayar akan mu cire mahaifar kawai, dole muka tafi OT and that’s how i missed ganin sabon MD. A wannan satin kowa ka kalla cikin asibitin kasan ya dawo hayyacinsa, aiki kowa yake ka’in da na’in nidai bamu taba haduwa dashi ba har yayi wata a asibitin. Kowa complain yake akan ya takurawa mutane, to dama hakane idan mutum yazo yana kwatanta gaskiya tabbas kowa zai tsane shi. Ranar wata litinin nayi aiki na gaji daga nan na tafi Amenity unit wajen kyaftun, mun jima da ita muna hira sannan na tashi n koma lounge. Muna da yawa cikin lounge din masu cin abinci nayi haka wasu na research inda na saba zama naje na zauna bayan mun gaggaisa da Doctors din. Wata Dr hajja watching buddy dita ce ta kawo min wani romantic doctor korean film.1 “Shahada watch this film yayi kyau sosae fa” Bakina na tabe nace “Rabani da wannan romantic films din nasu, ana nuna soyayyar da bata existing gaba daya” Dariya tayi tace “Hooo Anty Asmau i cant wait naga wanda zaki aura, bama romantic din bane ba, surgeries ne kalakala a ciki zaki karu” Da haka tasa na karba film din cikin flash dina, komawa na gyara zamana kan cushion din nayi na fixing wayata a charge tareda dan runtse idona a hanaklai bacci ya fara kokarin fizgata, dama gefena wasu house officers ne mata suna zaune Ina jin dayar tace “Ke kinga sabon MD kuwa” Bude idona nayi a hankali na kallesu amma duk saboda yadda suka zama engrossed ko effect din idanuna basuji ba, dayar tace “Kin ganshi ne ke?” “Sosae ma, though daga nesa ne, ban taba ganin mutumin da fada yake mishi kyau ba se shi, baya murmushi fa amma he’s so cute mashaaa Allah” Ta fada tana rungume fuskarta da palms dinta, se grinning take, se suka bani dariya. Na dauka ni kadai nayi shashancin admiring maza da kuma one side love ashe inada yan uwa. “Awnnnn I’m crushing him already” Wayata ta katse min hanzari da ringing, kaina na kaudar da sauri, tareda sakin siririn tsaki sannan na janyo wayar wata sabuwar number ce, picking nayi tareda karawa a kunnena “Dr Shahada, Dr halima ce” Da sauri na gaisheta se tace min “Kina jina ko? Akwai wata middle age woman a labor room kamar ta samu ruptured uterus, kije yanzun kiyi reviewing dinta in the next 20 minutes zakui mata aiki a OT keda MD” Ambatar MD seda gabana ya fadi me yasa nida MD. Mikewa nayi na tattara kayana na fita cikin sauri, muryar Dr halima nayi min echo a kunnena “Nasan zaki iya, i trust your skills amma ki kula sosae sannan kiyi komai da sauri amma with care, kada ki bari ya kamaki da wani matsala. All the best” Ina shiga labor ward na karanta write up din matar naje nayi assessing dinta sannan na zauna aka shiryata daga nan na wuce OT nayi changing, ranar chief anesthetist din shi zai bamu anesthesia da kanshi sabida wannan shi ne first time da zaiyi aiki a OT tunda yazo. Cikin five minutes suka kammalla komai hakan yasa na kira Dr halima na sanar mata mun kammalla. “Bara na turo miki digits dinsa ki fada masa kun shirya” Idanuna a warwaje nace “Kai dan Allah ki fada masa” Dariya ta danyi tace “Shima mutum ne kamar ni” Daga haka tayi hanging, se na rike wayar sororo ina kallo, aikuwa sega pop din message nata ya shigo, Dr Kwaciddo nayi ta nanatawa kafin da kyar nayi summoning courage na kira shi, muryata a dan rikice nace “Sir I’m Dr Shahada, muna jiranka a OT koami is set.” Cikin stern voice yace “Alright! I’ll be there inshaaa Allah” Sauke wayar nayi tareda sakin ajiyar zuciya, se naji ya burgeni da yace inshaaa Allah. Ina nan tsaye baifi 10 minutes ba se naji shigowar shi. Dogo ne sosae dan idan na karu jikinshi Allah yasa zan kai aljihun gaban rigarshi, nima a mata bana cikin sahun gajeru amma this is to show how tall he’s. Ba siriri bane da ace bashida tsayi kibarshi se tafi fitowa amma dake yana da tsayi se ta shanye kibar. Shi ba fari bane yafi ga a kirashi baki sede not that dark, ga jin dadi se yasa fatarshi take glowing, smoothly tamkar mace kana kallon fuskarsa kaga ta bafullatanni ko ba usul ba amma an samu trait din cikin jini. Wannan shine MD or i can call him Dr Kwaccido. Hannunsa ya tafa yana fadin “Set?” Kaina na gyada nace “Set sir!” Ciki muka shiga bayan mun jira yayi changing, yadda yake aiki will tell you shidin ba na yau bane yasan scalpel scapel tasan da zamanshi. I was extra careful akan aikin har muka gama muka stitching gurin sannan ya kalleni yace “It’s nice working with you” 1 Ayshatuu1″Thank you sir!” Kawai nace mishi ba tareda na bari kalamamsa sun shiga kaina ba, nasan I’m skilled person duk wanda yayi aiki dani komin yadda ya kware to tabbas se yasan nima na maida hankali. Cikin lounge yaje ya zauna aka kai masa folder yayi documenting sannan ya yiwa kowa

Chapter 11 of 18