Share this page
Kamar ya dakeni, yace na zauna wasa abinda banyi a baya ba shi nake kokarin nayi Yanzun, to nasani karatunnan shi kadai ne rufin asiri na. Dama a gidanmu idan kaga ana yaba maka, to sailing Kake successful amma da zarar Ance you failed babu Wanda zai bi bayanka. Naji haushi Dan Hatta Adda Sa’ada wannan karan bamuyi da dadi da ita ba, hakan yasa na dawo hayyacina Naga Meye nakeyi? Kashe Kaina zanyi saboda wani namiji, Wanda ya manta abinda ya faru gaba daya, shi Yanzun house job dinshi Ya gama gaba daya, ya fara residency bayan nan aurenshi Zaiyi, to ni Meye na rike wannan abin cikin zuciyata? Nayi dwelling a rayuwar da ta riga ta wuce. A lokacin na kara fahimtar wani abu da son zuciya ya hanani gani, shi ne Suleiman bai yaudareni ba, ni na yaudari Kaina, ni nayi hurting Kaina, tunda shi baice yana sona ba, yasan ina sonshi to me zai min? Zaice Asma’u daina sona? Bazai yiwu ba. At the spot nayi making mental note cikin kaina akan wannan abin, wannan Maganar ta wuce Har abada sede a hira.+ Nayi Karatu kamar babu gobe, Dama six weeks ne favor din kayi resit, kuma Alhamdulillah Inayi nai making, na zama final year medical student. A lokacin shirin bikin Nadiya da Yaya Suleiman yayi nisa sosae, amma saboda postings, Karatu ga kuma project yasa banyi wani active perticipation a shirin ba, sede duk abinda akai to zata kirani ta fada min, Haka ta bangaren Yaya Suleiman din duk ankon da muka fitar shi ya siya min. Biki saura sati uku aka gama hada Lefe, Ummaah tace Nazo na gani kafin akai, koda zanyi recommending a kara wani abun. Yaya Suleiman yazo Ya daukeni shima bayan Ya gama aikinsa. Tunda muka gaisa bamu Kara magana ba, seda Nadiya ta kirashi tana tambayarshi Ko muna tare ta kirani ban dauka ba, to ya bani, bani Yayi mukai magana sannan nai mata sallama. To wannan ya bashi space din yimin magana, itama random talks ne kawai har mukaje gida. Gidan da mutane sosae, familyn Baban Yaya Suleiman sunzo ganin kaya, dan haka dakina kawai na wuce nayi wanka sannan sun tattafi naje gurin Ummaah, “Ummaah Sannu da gida” “Doctor ta karaso, Sannu ya Karatu? “ Ta fada tana min murmushin dake healing zuciyata, akwatin na janyo Ina dubawa muna hira da ita, seda na gama tas sannan nace “Ummaah, kayannan Sunyi kyau sosae, Allah Ya sanya alkhairi yasa ayi taro lafiya! “ Kaina ta shafa tace “Amin Autar Ummaah, saura naki kuma ko? “ Murmushi nayi Ina maida kayan cikin trolley, amma karkashin raina Amin nake amsawa, gyara zamanta tayi tace “Kinga baifi watanni bakwai Ya rage miki Ki kammalla karatunki ba, kiyi kokari ki saurari masu nemanki, nasan Inna Ade tayi Shiru da Maganar ne amma da zarar kin gama zata dawo da zancenĺ” Kaina na gyada nace “Inshaaa Allah Ummaah” Dan abar Maganar auren kawai se na Fara mata labarin Project dina da nakeyi akan CKD (Chronic Kidney Disease) gaba daya ta bani hankalinta, ina mata bayani tana kara min bayanin Wasu abubuwan. A matsayinta na project coordinator a department dinta. A Haka Abba ya dawo daga gona, mukaje tare na mishi Sannu da zuwa sannnan na barta acan ni kuma na tafi gurin Yaya Halifa. Lokacin biki yazo, dukda ba wani armashi Yayi ba, kasancewar bikin maza ne amma dukda hakan saboda yawan danginmu naji dadin bikin, kusan duk taron a gurin Nadiya nayi shi. Seda aka daura aure sannan na dawo gida, Dan Ummaah tace min Dani zaa dakko Matar Yaya Halifa daga Dutse. A motar Adda Sa’ada muka tafi, munata hira Har mukaje, mutanen suna da kirki, sun karrama mu, muka dakko Sister in-law muka taho da ita kano. Unguwa daya Nadiya da Adda Zannira matar Yaya Halifa, gidan baifi 50miles away ba, haka suke. STORY CONTINUES BELOW Rayuwa tana tafiya da dadi da babu dadi, amma dole duk yadda Tazo Haka zakai embracing dinta. A rayuwata na fuskanci kalubale da yawa daga gurin mutane da dama, Harda Wanda ban taba tunanin hakan ba. A Yanzun idan Bakayi aure ba, mutane kawai gani sukeyi Kaine baka so ba, Kaine Baka maida hankali ba. Ya Ilahil alamin! Ya Zakayi? Zakace dole se kayi aure lokacin bai zo ba, A’a aure da mutuwa lokaci ne, idan lokacin baiyi ba, Baka isa kayi ba. Na kammalla karatuna at a very tender age, gaba daya shekaruna ashirin da uku na karba licence dina under Medical and Dental Council of Nigeria(MDCN, na zama cikakkiyar Medical doctor, ranar da nayi taking Hippocratic oath dina, ranar atttestation nayi farin ciki, nayi murna Kamar zanyi me, na Kalli ilahirin family na da suka zo, ai da kyar bakina ya budu nake karanto oath din. Muna gamawa na fito akai photo session, Yan gidanmu anata rungumeni a Haka muka gama na cire graduation gown din na rataya, cikin yan set dinmu naje mukai hotuna, Dan Wasu ba lallai ku Kara Haduwa dasu ba. Muna komawa gida, na nufi dakin Inna, tana zaune gefen katuwar katifarta, ko sallama banyi ba na mika mata hannu nace “Mun kunce ni dake, har na gama makaranta, na zama cikakkiyar Likita amma baki zo tayani murna ba. Na daina kawar dake. “ Tabe Baki tayi tana bina da wani kallo, Wanda bansan me yake nufi ba tace “To se me Dan banje ba? Da dai aurenki ne da ni ce kan gaba “ Dariya nayi naje na zauna gefenta nace “Kawata ta kaina, Karki damu ina dawowa daga service zanyi aure da izinin Allah” Baki a bude tace “Wani karatun ne kuma, ke Kinci ubanki, so kike se kin tsofe kafin kiyi aure. To babu inda zakije, miji zaki kawo ayi miki aure. “ Dariya na karayi nace “Inna ba Karatu bane, maida wukar, bautar kasa zanyi. Kuma banda abinki aure ai lokaci ne….” “Maganarki kenan kullum, aure lokacin ne, ki kalla sa’annin ki dukkansu Sun yi aure, Rayhana ‘Ya’yanta biyu amma ke kinata gantali” Ta katseni, “Gantali” na maimata, se kawai nayi Murmushi nace “Kawa kenan, ni bana fada da Kawata bari naje, idan kina son wani abu se kiyi min magana” Daga Haka na mike gaba daya raina a jagule, saboda abinda Inna tace, Rayhana sa’a ta ce quite sure, amma lokacinda aka rubuta mana kaddara dole kowa road din da zai bi, daban take. Me yasa mutane basu gane komai MUKKADARI NE ba. Da Ummaah na Fara haduwa dake ta Tara mutane se shiga take tana fita, seda nace ta bari idan an kwana biu ayi walimar amma tace gwara tayi rana daya.1 “Na zata kin shirya, mutane na jiranki fa” Kaina kawai na gyada nace “Yaznun zanyi” Juyawa nayi zan tafi daki Ta kwalla min kira na dawo, kallona tayi tace “Akwai wani abu ne? Naga fuskarki tayi ja “ Taba fuskar nayi sannan na kirkiro Murmushi nace “A’a Ummaah gajiya nayi, Bari naje” Saurin Juyawa nayi saboda jin idanuna sun cicciko da kwalla, Se naji tace min “Today Issa happy day, don’t let anyone destroy it. “ Kaina na gyada na tafi dakin, Adda Zannira ce a kwance da katon cikinta, ta saki fanka, zama nayi gefenta nace “Adda Zanni, duk gajiyar ce” Dagowa tayi ta kalleni tace “Bari dai Adda Asma’u, Babyn ki ya takura min, na kagu Ya fito na Baki abinki. “ Dariya nayi tareda mikewa nace “Kaji Adda Kamar gaske, Se Kinji zafin labor Kice kin fasa” Dariya tayi tayi har na shiga wanka, Ina fitowa na shirya cikin wata red Abaya da Adda Habiba ta kawomin as gift, muka fita bayan nayi kwalliya akai ta hotuna. Se Washegari na samu damar bude gifts din da aka kawo min, yawancin duk gifts din daga yan gidanmu ne, Delivery kits, BP app, forceps da sauransu. Naji dadi sosae, kowa na bishi da text din godiya. Ina kwance a daki sati daya da graduation dina, Inata tunanin Yanzun kuma Ina zaa fada, posting anyishi kuma Anyi posting dina Yobe state. In the next 2 weeks zan tafi. Shigowar Ummaah tasa na mike, kafin nayi magana tace “Dakko Hijab dinki kizo” Zan tambayeta lafiya naga ta juyar da kanta hakan yasa na mike na dauki Hijab din na saka muka fito, tunda naga Munyi dakin Inna Ade naji gabana Yayi mugun faduwa, tunda nake da Inna bata taba zuwa gidanmu tayi fin kwana uku ba, amma wannan karan kwananta goma sha biyu bata tafi ba, hakan ya tabbatar min da she’s up to something kuma tabbas akaina ne, Dan ta dauke min wuta, nima bana son case hakan yasa na tattara ta na watsar da ita. Tana zaune kan katifa, tana murza goro a magogi Tana afawa a baki, nida nafi kowa saninta nasan wata tsiyar zatayi, sallamar da Ummaah tayi yasa ta juyo tana kallona, Nima kallonta nake se ji nayi tace “To Zuwairiyya (Uwarta kenan!) da kikai tsaye dukana zakiyi? “ Da sauri Abba ya juyo yace min “Asma’u come and sit here” Jikina a matukar sanyaye na nufi gefenshi na zauna ina kara tantamar Anya Inna ce, ni tayi addressing da Zuwariyya? Ban gama tunanin hakan ba naji tacr “Ke Asma’u, dago ki dubeni, idan wayannan mutanen sa’anni Ki ne, ni ba Abokiyar wasarki bace, Dan kin Raina mu zaki ce bazakiyi aure ba…. “ Da sauri na katse ta nace “Inna yaushe nace bazanyi aure ba” Abba ne yace “Kar naji Bakinki! “ Shiru nayi amma a raina Ina ayyana ni Asma’u Fara Yar Shehu, Inna take dagawa murya Haka? Bazan iya tuna last time da ta kirani da Asma’u ba, I can even say she never, kawai cemin take Fara ‘Yar Shehu, Ta gaban goshin ko kuma Kawata. Amma yau Inna Ade ke cemin ita ba tsarata bace, kawai se naji hawaye sun Fara min zarya, kaina ya mugun Sarawa saboda bala’in da take. A karshe tace babu zancen zuwa Yobe! 1 Awnnnnnnnnnnnm……. A page is here, to all my followers I say Kumaya! One word for Fara ‘Yar Shehu Inna Ade 1 AyshatuuuHannuna nasa na goge fuskata Dan banga dalilin kuka ba, idan tun Yanzun Ina kuka to nan gaba kukan jini zanyi kenan. Nida Ummaah ta sallama, hakan yasa na mike na fito, kitchen na wuce na fara dama custard Dan inason na Fara sabawa da irin wannan abin, Ummaah ce ta biyoni taga ina kokarin Dama custard amma ya tsinke saboda bana cikin nutsuwata. Hannunta tasa ta dafa kafadata tace “SABR! Asma’u, komai kika ga yana faruwa da bawa da sanin Allah. Kiyi hakuri “ Dan Murmushi nayi nace “Ummaah babu komai, bari naje daki” Tare muka fito da ita, daidai fitowar Abba da Inna, bakinta har kumfa yake saboda balai, Jakarta ce a hannun Abba hakan yasa na karasa na karbi Jakar sannan nace “Inna tafiya zakiyi? “ Kallona tayi sannan tace “Tafiya zanyi Kawa, yaushe zaki zo? “ Kaina na girgiza nace “Babu rana,” Daga Haka muka karasa Mota mukai mata sallama, ta shiga sannan driver ya tada motar se Kwalam. Dukkanmu haka muka tsaya har aka maida gate aka rufe amma babu Wanda ya matsa a gurin, kowannenmu tunanin zantukan Inna ke yawo cikin kanmu, Se can Abba ya juyo Ya kalleni yace+ “Asma’u let’s talk” Wucewa yayi dakinshi, nima na bishi yayinda Ummaah ta tafi daki. Yana zaune a Kan carpet na sameshi, yayi shiru not like my Police Father, duk Yayi Shiru fuskarshi looking pitiful, Se naji na kara takura, naji gaba daya Sauran space din dana bari a zuciyata Wanda Banji haushin Inna ba, baki daya se ya zamana duk ya turnuke ni, har ni kaina haushin Kaina nake ji, at least da nayi auren da ban jawo musu magana ba. Zama nayi gefenshi nace “Abba Dan Allah kayi hakuri, Inshaaa Allah zan kawo maka miji na…… “ Se na kasa karasawa saboda wani irin kuka da ya kubce min, kaina na durkushe Inata kuka, inajin yadda zuciyata ke wani irin zafi, na kasa ci gaba da Maganar seda Abba ya dafa kaina yace “SABR! My Daughter. Ya isa hakan” Sheshakar a hankali ta dauke min, hawayena na share na bude baki zanyi magana ya girgiza kanshi yace “Saboda Bakiyi aure ba se ya zama laifinki? Ba laifinki bane, haka Allah Ya kaddara miki, babu Wanda ya tsallake kaddararshi. Koda zaki kara shekara goma a gidannan Bakiyi aure ba, I’ll say nothing. Bake kika hallici Kanki ba, shi daya halliceki yasan tanadin da yayi miki. So Karki kara kuka akan hakan, zakiyi aure amma se lokacin Yayi. And for Yobe, you have me, you’re your fathers daughter Bazan iya hanaki ba. Inna Ade zata sakko Kinji? “ Kaina na gyada ina Dan Murmushi saboda words dinsa are more of Opoid Analgesic (Pain reliever) a take sukai relieving duk wani bakin ciki da zuciyata ke ciki, a take naji wani karfin gwiwa da nutsuwa ya sameni. Bai barni na tafi muka zauna munata hira, gaba daya hirar yana sighting mini examples ne na rayuwa. Most thing da yayi capturing zuciyata shi ne da yace min “Kinga Asma’u aure ba farilla bane, amma Sunna ce me karfin gaske, a wani gurin saboda Allah yace idan kayi aure tamkar ka cika rabin addininka ne, so kinga akwai falala sosae a aure. Kuma a society dinmu sun daukaka aure sosae da sosae, suna ganin mace is not complete without aure. Eh wani lokacin Haka ne amma kin tuna tarihin Nana Maryam Mahaifiyar Annabi Isah (AS). Batayi aure ba amma a kur’ani Sura guda ce da ita, so kinga zuciya is everything that matters. Ki maida hankalinki akan yadda zaki gyara lahirarki, aure zaizo sede idan lokaci baiyi ba “ Shikenan kuwa na samu lafiya, na wartsake na Fara shirin tafiya Camp. Wani yammaci na tafi gidan Rayhana bayan nayi sallar laasar, ita daya na samu a gidan ta gama aiki ko wanka Batayi ba, Yaran ba sanan sunje gidansu Abdul a sharada. Seda na zauna sannan tace STORY CONTINUES BELOW “Gwara da kika zo dama nemanki nake” Zama nayi nace “Kiyi wankan mana tukunna se muyi Maganar “ Tashi Tayi ta tafi toilet dan yin wankan, tamkar ana jira kawai se wayarta ta Fara ringing, hannuna na Kai na janyo ta, se naga Nabila cousin yana yawo akan screen din, hakan yasa na dauka amma kafin nayi sallama Se naji ance “Haba darling, tun dazun nake jiranki amma baki hau whatsappp din ba, balle na samu naga pictures din ko sa rage min wani zafin, kuma nasan Abdul ai ba yanan” Shiru nayi na kasa fahimtar me ake fada me kuma ake nufi, me yasa nake jin muryar namiji bayan sunan Nabila ne a jiki? Me yasa namiji da ba Abdul ba yake kiranta da darling…. “Baby are you there? Talk to me mana” Ajiyar zuciya na sauke tareda sauke wayar daga kunnena na kashe gaba daya, zuciyata wasu irin wasiwasi take min, Se contemplating nake a Haka Rayhana ta fito, tayi kyau abinta, kamar asalin rayhanata amma se naji Kamar na rufe ta da duka, gaba daya haushinta Ya lullubeni, is she having an extra marital affairs kenan. Tabanin da tayi yasa na dago tareda mika mata wayarta nace “Nabila cousin ta… “ Bata bari na karasa ba tace “Kinyi picking, me kika ji? “ Gaba daya ta gigice hankalinta yayi mugun tashi Wanda hakan ya tabbatar min batada gaskiya, idanuna a kanta nace “Nayi yace yana jiranki ki tura mishi hoton da zai rage masa zafi, ray…. “ Da sauri ta katseni Tana fadin “Ba abinda kike tunani bane wallahi Sister, he’s just a colleague, tare mukai service dashi” “I didn’t ask for all this and yet you are telling me, Rayhana me kikeyi dashi, da aureki da mijinki kike having affairs? Rayhana” Kusa dani ta dawo tare da riko min hannuna tace “Asma’u ki rufa min asiri, nima nasan ban kyauta ba, nasan abinda nake Haramun ne amma na rasa yadda zanyi” Wani kallo nayi mata me cikeda bacin rai, nace “Bakisan yadda zakiyi ba? Is this an excuse. Ke musulma ce and I’m sure Kinsan hukuncin abinda kike aikatawa” Kuka ta Fara tana fadin “Na sani Sis, amma banida option wannan ne kadai abinda nake ganin Zaiyi saving aure na. Idan na kalleki birgeni kike saboda Baki San the hell dake cikin aure ba, baki san bakin cikin dake cikin shi ba, nasha ayyana inama zaai overturning agogo, ya koma baya, I’ll never have chosen Abdul, I regretted that. “ Gaba daya se ta Fara bani tausayi, naji haushinta da nakeji ya Fara wucewa, hannunta na rike nace “Is ok Rayhana, amma ko me Abdul yayi path din da kika bi bamai bullewa bace, halaka zakiyi, kinga kenan kin tashi with nothing, Babu duniya babu lahira even an ounce of pride babu.” Hawayenta ta share tace min “Kinji dadi Bakiyi aure ba, Nazo zan fada miki wannan abin. Tun muna secondary nake son aure, Kinsan Dalili? Saboda I’m thirsty, I want someone to quench that thirst for me, Inada strong sexual desire, zan iya ce miki dalilin aurena kenan. Abinda na fahimta about aure shi ne, Backbone na aure is sex, komai zaayi miki a gidanku amma babu me iya miki wannan se Kinyi aure, the new thing about aure shi ne sex, what about you are deprived of that? Ya kike ganin zaayi kenan? I was innocent and illiterate about it, Abdul tasted that thing to me Se dana saba nasan dadinshi sannan ya nuna he’s not in need, se ya koma a wata, we will have affair sau daya, Ina zan iya, nayi korafin, nayi Maganar, tun ina kunya Har na fito Asma’u nayi mishi barobaro amma yaki fahimta. Aurena zan kashe? Ina ganin Kamar dalilin yayi kadan Yasa nayi hakan, shiyasa na komawa Jabir dina. Nasha zuwa da niyyar fadawa Mama amma se tace, what matters shi ne na rike sirrina, kada na tonawa mijina asiri, kuma no matter what I’ve to save that marriage Dan shi kadai ne Gata na, bata taba saurara ta ba. Kece kadai kika bani hearing ears, Nagode “ Ni Kaina seda hawaye ya zubo min da ta gama fada, hannunta na kama nace “I’m sorry, amma dukda haka baki nemawa kanki solution ba, me yasa a aure akai Waliyyi, run to him, tell him ga matsalarki. Kina ganin sex deprivation Yayi kadan ya kashe aure? Kinyi kuskure Dan a karshe zakiyi dana sani marar amfani, Rayhana quit all this games and tell them, ki fada musu matsalarki, kiyi istigfari, kiyi Tuba, tuba na gaske Wanda bazaki koma laifinki ba, Allah kadai zai daidaita rayuwar aurenki. Kiyi hakuri “ Tunda na dawo gida bayan na baro gidan Rayhana, na kasa nutsuwa, na rasa tunanin me zanyi. Dama idan Kai auren bashi kadai bane karshen matsala, who will ever think Rayhana da Abdul will end up in such a mess? AyshatuuuYOBE, POTISKUM. Abba da Ummaah, su suka rakoni har Potiskum inda anan NYSC orientation camp din yake, bansan yadda Abba ya shawo kan Inna Ade ba, amma nasan ya cika min alkawarin da yayi min akan Zanje Camp, gashi alkawari Ya cika. Tare dasu mukaje akai clearing dina da dukkan Wasu formalities sannan kuma mukai sallama suka juya. Camp life was hectic amma it’s something memorable that happens once a rayuwar mutum. Sati biyu da nayi na rame ga lokacin ana Rana, nayi baki, gani Inada Dan wahalar sabawa da mutane, se ya zamana mutum daya muka saba da ita wata A’isha Kyaftun yar Gumel ce ta Jigawa State. Ita dinma dalili ne ya kawo hakan. Har nayi sati bana shiga harkar kowa, roommates dina dukkansu Christians ne so kullum sede mu gaisa kowa ya kama gabanshi. Ranar Saturday mun kammalla dukkan abinda Zamui naje wani eatery zanci Abinci, Nazo entrance din naji wani yana fadin “Kyaftun! Kyaftun!! “ Ko Juyawa banyi ba, na cigaba da tafiya ta amma se yazo yasha gabana yana fadin “Amma Kinsan tun yaushe nake jiranki? Kinzo kuma kin wani bata rai kin wuce” Juyowa nayi na kalleshi, shima kallona yake, dogo ne sosae Dan duk tsayina se na ganni dwarf a gabanshi, fuskarshi doguwa ce kuma komai dake cikinta Manya ne, ga uban saje daya aje, Wanda zaisa ayi mistaken dinsa a matsayin wani Babban mutum. Gaba daya analysis din nayi shi cikin nanosecond ne.+ “May be you are talking to the wrong person” Na fada masa Ina kokarin Juyawa na shiga ciki amma, Se naji wata murya irin tawa tace “Zayyan! Kana ta jirana Ko? “ Juyawa nayi na Kalli me Maganar, seda gabana ya fadi saboda yadda fuskata take a Kan tata, baki bude nake Binta da kallo haka itama take ta kallona, se shi Zayyan din ne yace “Allahu Akbar! Set of twins from different uterus. “ Kallonshi mukai a tare sannan ta miko min hannunta, take na zura nawa, instead mu shiga cikin Eatery din se kawai muka nufi wani karkashin bishiya muka zauna, Zayyan Ya tafi siyo mana juice. Hannunta ta bani tace “A’isha Kyaftun Ismail, daga Gumel, Jigawa state amma a kano muke” Kaina na gyada nace “Nice to meet you, Sunana Asma’u Shahada Kwalam, yar Jigawa ce ni” Murmushi ta karayi daidai dawowar Zayyan, hannunsa da Fanta biyu, coke daya, ya aje sannan ya zauna yana fadin “Ban taba ganin Kama irin wannan ba, Anya ku din ba Twins bane aka samu akasi kuka rabu” Dariya nayi, Kyaftun tace “Ka Faye surutu matsalata da kai” Kaina na girgiza nace “Ni Kaina nayi mamakin ganinki, ban taba tunanin akwai irin mutanen da Baka hada komai dasu ba amma kana kama dasu Har haka” Kanta ta gyada tace “Seda na tsorata fa Asma’u, I never knew such is real! “ Daga Haka mukai ta hira Har na manta cewa Yunwa nakeji. Daga wannan ranar muka zama kawaye da ita, bacci kadai ne ke rabamu da ita, a gidanmu kowa yasan labarin Kyaftun haka nan nima labarina yaje gidansu. Lokacinda muka fito a camp, munata shiri nace “Kyaftun kada Ki Kira kowa, zaa zo daga gida a daukemu “ Aje Jersey din hannunta tayi ta maida hankalinta kaina tace “To, har Se anzo daukarmu Twin?” Gyada Kaina nayi nace “Eh mana, Bazan iya komawa da kaina ba ai” STORY CONTINUES BELOW Dariya tayi tace “Small Baby, Nan da Kano ai ba big deal bane. Zamubi commercial car ni da kaina zan fadawa Ummaah haka” Bata jira abinda zance ba ta kira Ummaah, har sun saba dan Twin batada duhun kai ko kadan , she’s a wise person sosae. Haka na hakura Washegari muka tafi Tasha Inata jina a takure, Twin se dariya takeyi min tana tsokanata Fathers girl. Seda mukaje Kiyawa sannan Wasu passengers suka sauka, a Dutse aka Kara cika motar. Tunda muka dauki hanya na kwantar da kaina a kafadar Twin na Fara Bacci seda muka shigo Kano sannan ne ta tasheni, wata Ajiyar zuciya na sauke bayan na hango Birni, home sweet home na ayyana cikin raina. Muna sauka muka harhada kayanmu guri guda, Kyaftun taje samo mana Napep. Sallama naji a gefena hakan yasa na juya, tareda amsawa amma a ciki ciki, bakina daya motsa kawai ne zai fada maka nayi magana. “Sunana Salis, ke fa? “ Kallonshi nayi nace “Bashida amfani hakan” Ina fadar Haka na tsugunna ina gyara Trolley Twin. Maimakon ya tafi se ya gyara tsayuwarshi yana fadin “Tunda ni na tambaya ina ganin it’s important, so let me know “ Dauke kaina nayi, zuciyata tana fada min I shouldn’t miss the chance, wannan shi ne lokacinda ya kamata kiyi saurayi, ban gama tunanin ba balle nasan hukuncin da zan yanke Twin ta dawo, kawai Salis Ya juya gurinta tareda yi mata bayanin abinda ya faru, take ta karanto masa home address dinmu, number ta da sunana, Dama tun acan Potiskum ta fahimci banda saurayi, tayi mitar tareda fadin ita ta Yaya zata iya rayuwa babu opposite gender, ai masifa ne kayi sati daya bakaji muryar Wanda yake kallonka as something special ba. Daga Haka muka wuce shi ya bawa me Napep din kudin sannan Twin tayi masa godiya, tunda muka dauki hanya nake mitar ta zubar mana da mutunci, ta bari an biya abinda ya kamata mu biya, Tsaki kawai tayi tace is not like ya siye mune, is just a token of appreciation na bashi access da abinda yake so. Twin kenan duk ta inda na fito tasan yadda zata bullo min, ban taba wining akanta ba, so wannan karan bakina nayi bam dashi. Gida muka fara zuwa Dan Dama alkawarin da tayi min kenan. kowa seda ya Jinjina halittar Allah. Seda muka ci Abinci muka huta sannan na tafi nida Adda Meeyna rakata, har gidansu mukaje, iyayenta masu kirki sede rayuwar gidan is far different from ours, zaka iya saka su a low social class amma kuma irin contented mutane ne, a zamana da ita bazaka tantance wani class suke ba. Allah yasa Nursing tayi abinta, tana da guarantee aiki. Salis Mutumin Ingawa ne ta Katsina state, ko cikin muryarshi zaka dinga jin accent dinshi na yan can

Chapter 7 of 18