bangajiya kafin ya tafi, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan na fita baki daya daga OT. Ward na koma na karasa ayyukan da suka kamata nayi sannan na tashi gaba daya.
Washegari ranar friday, muna kammalla ward tounds dinmu na shirya dan tafiya kano a raina ina tunanin ya kamata yau ba se gobe ba na fadawa Abba kudirina. Misalin karfe uku na isa gida saboda na biya gidan Adda Maryam da nayi niyyar se yamma na koma gida amma ta bata min rai shiyasa na taho. Ina gidan kanin mijinta wani Nasir yazo, that wasn’t the first time dana hadu dashi a gidan sede baifi sau daya muka taba magana ta minti uku dashi ba kullum daga gaisuwa bamu karawa saboda naga dan raijin wayo me, ni kuwa bana cikin wannan class din. Tunda ya shigo muka gaisa naja mutuncin kaina na cigaba da kallona sunata hira shida Adda, can sega mijinta ya dawo, Yaya Mansur muka gaisa ya zauna yana ta jana da hira dake he’s very jovial to tamu ta zo daya dashi.+
“Kina wuta fa matar nan, nazo kofar gidana naga wata benz, so inata tunanin wa muka samu? Seda na hango wannan ear piece din naku kafin na gane ashe kece”
Dariya nayi dan Na fahimci stethoscope yake nufi, nace
“Babu wani wuta fa Yaya, amfani ake da dama”
Murmushi yayi ya gyada kai yace
“Yeah! Allah ya kawo miji na gari”
Amin na bashi amsa ina murmushi, kallona Adda tayi tace
“Kamar gaske”
Ko kulata banyi ba tashi tayi ta wuce ciki itada yayan, bata jima ba ta dawo hakan yasana wuce kitchen akan na duba abinci dan a daura wani, idan naje gidan sisters dina se nayi musu dinner nake tafiya. Kamar daga sama naji Adda Maryam na cewa Nasir
“Kaima kaki kayi aure kamar Asmau, ko baka da budurwa ne?”
Shiru nayi inason jin amsarshi se yayi dariya yace
“Kai time baiyiba, se an tara tukunna”
Gyara zamamta tayi tace
“Kaga Asmau shes 27 years yanzun, gata medical doctor, babu wani serious magana akanta, bana tunanin tana da saurayi gaba daya so idan tayi maka why won’t you tag along kuyi aure”
Idanuna na lumshe jikina har bari yake na rufe warmer da sauri zan fito kawai naji yadda gayen yake babbaka dariya hakan yasa na tsaya, naji yace
“Kina da abubuwan dariya Antinmu, ni wannan kanwar taki ai ta girmeni ma……in a mocking way ya fada, se naji kafafuna sunyi wani sanyi…..27 kikace? Tabdi! Beside ni fa bazan iya auran health workers ba ke wallahi ko a kafa aka daura min su se na kunce”
Tamkar walkiya haka na ganni a parlon, wani irin mugun kallo na masa nace
“Ai ko maza sun kare nafi karfin na aureka, Adda na gode”
Daga haka na dauki jakata dama veil dina tuntuni yake a jikina nayi waje na barsu baki a sake, mota ta na bude na shiga se kuma nayi shiru ina ganin menene abin fushi har haka? Me yasa raina ya baci dan anyi talla ta, tunda auren yaki zuwa may be kilan ta hakanne zan samu miji. Zuciyata se ta kasu biyu wata na blaming dina wata na tafarfasa tana ganin an raina min hankali ajina ya wuce ayi kamar ana nanawa namiji yana kin karba.
Ina gama parking sega Yaya suleiman, tsayawa yayi yana kallona ni at first ban ma wani lura dashi ba kokari nake na bawa Baba me gadi key din ya shigo da kayan da nazo dasu. Ji nayi yace
STORY CONTINUES BELOW
“Ajhumma!”
Nasan shi daya ke kirana da wannan sunan hakan yasa na dago fuskata a sake na dubeshi nace
“Oppa”
Se naji na tuna da, kamar yadda oppa yake nufin Yaya a korea, yawanci suna fadawa saurayi hakan, tone din da suke using kadai kasan cewar bawai brother yake nufi ba aa sede something else. A wancan lokacin I’m feeling the same, lokacin dana fada se naji wani sanyi a raina but see me today, saying oppa plainly and emotionless rayuwa kenan. Yaya suleiman da naso na kaunace and so much badly wanted na zama mallakinsa amma ya dubi idanuna yace kawata yake son nayi hooking dinsu tare, i felt shattered. That’s then!
“Ya aikin? Kinyi kudi kin manta damu, kullum Nadia tana cigiyarki ko ziyara baki kawo mana”
“Aiki sede godiyar Allah. A gaida Nadia da yara”
Na fada saboda zancen babu ziyara ba mutum daya le zumunci ba both parties keyi, bantaba tunanin zan rabu da raihana da Nadia ba Amma yanzun ni ko numbers dinsu bani dashi. Duk yadda Yaya suleiman yaso na tsaya na nuna masa a gajiye nake dole hakanan yayi hakuri na shige gida. Ummaah Na parlor a zaune itada Asiya na shigo, Asiya ta rungumeni sannan ta bamu guri. Gaisawa nayi da Ummaah tace
“Ina kika tsaya? An shigo da kaya amma ke shiru”
“Nida Yaya suleiman na tsaya”
Bata kara cewa komai ba haka nima se na mike na wuce na tafi dakin Inna, tana zaune kamar kullum ana goga goro. Karba nayi kamar yadda na saba ina gurza mata muna dan taba hira abin mamaki. Hirar arxiki kuma wadda na jima bamui nida ita ba. Tana ta bani labarin ‘yan matancinsu ita da fara yar shehu
“Naso Asmau fara yar shehu ta rayu zuwa wannan lokacin ta ganki. Kawata ce wadda banda kamarta kuma ko bayan data mutu babu wanda ya maye min gurbinta, da yake ita mahaifiyar ta yar Mambila ce to dukkan mu tafi mu kyau, kyakyawa ce ta gaske hakan yasa tun muna shekaru tara aka sakata a lalle, naso kin biyo farin jininta da tuni kina dakinki, da kuma ace shahada da Saude sun barki hannuna da tuni baki shiga wannan kuncin ba.”
Dan murmushi nayi nace
“Inna lokaci ne”
Kanta ta gyada tace
“Da farko nayi tunanin laifinki ne shiyasa na matsa miki, amma a shekarunki na san kowacec so take ta ganta dakin miji. Ina fatan baki rikeni a ranki ba”
Rungumeta nayi da sauri ina dariya nace
“Waye yake fada da kawar shi? Sede idan kawancen bai kai zuci ba”
A wannan na samu sauki, ranar aka tuna da tare muka kwana, Abba nata tsokanar mu wai yau mun hada kai. Da safe nayi dukkan abinda ya dace wanda ya kamata sannan na koma bacci. Wajen sha daya nayi wanka nasan Saturday ce Abba bazai je gona ba, dan baya fita Friday da Saturday he always say they’re meant for rest. Kuma haka yake. Yana zaune shida Ummaah suna kallon Aljazeera, yau mun samu bakuntar yaran Yaya halifa dana Adda ummiey so suma suna parlon se kinji suke. Ina zama muka gaisa yaran suka gaisa se Ummaah ta fita naji dadin hakan sosae a raina dama bana son tana nan bazata bari nayi magana cikin nutsuwa ba.
“Nasan wannan zaman akwai magana, ina jinki”
Abba ya fada yana rage volume din, zamana na gyara nace
“Abba kayi hakuri dukda baka taba magana ba amma nasan kullum yana ranka, nima ba haka naso ba Abba na kai har lolacinnan banyi aure ba”
Murmushi yayi min yace
“Asmau! Ai bake kika hana kanki ba, shima Allah ba hanaki yayi ba he’s testing our faith kin gane?”
Kaina na gyada yace
“So, ki dage da addua Allah baya bacci. Ban taba miki zancen aure ba, bawai bana so kiyi ba ko kuma irin ban damu dinnan ba, ko daya I’m worried, sede ya zanyi idan na takura miki me zai canza?..”
Kanshi ya girgiza yace
“…Nothing my dear, ‘ya’yana takwas kowanne is educated islamically and western, bakwai sunyi aure kowanne peacefully, ke daya kika rage idan na kasa hakuri me nace da Allah? Ban gode bisa abinda yayiwa ‘ya’yana bakwai ba. Kinsan musulinci is wonderful, komai is open sede idan baka sani ba. Aure abu ne me girma, sunnah ce me karfin gaske sede mu bamu dauka sunna bace kawai aure wajibi ne idan bakai ba gani ake kaika jawo amma i know kinsan tarihin Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isah A.S batayi aure ba amma sura kacokan sunanta ne, so bawai se kayi aure zaka samu yardar Allah ba kede ki tuna tarbiyar da nayi miki kawai, ki kare mutucinki da martabarki. I tried as much as i can na zama mutumin arxiki saboda ku, nasan ko bani da rai zaace wannan yaran CP Shahada ce, amma idan na zama mutumin banza akwai matsala abinda zai zama rightfully yours zaa iya denying muku.”
Se naji sanyi cikin raina saboda maganar shi tayi min dadi naji sanyi da farin ciki a raina. Gyara zamana nayi nace
“Abba na samu wata school a America, idan ka yadda ina son zuwa”1
Shiru yayi yana ta kallona har seda yasa na fara jin uneasiness, se yayi murmushi yace
“Zan iya yin tunani da shawara?”
Kaina na gyada nace
“Sure Abba”
“I’ll get back to you”
_I left you guys waiting and I’m so sorry for that. Nayi typing wannan breakfast din for you all, ina fatan I’ll get some mind blowing and awesome comments from you guys as always. Yeah! Ina ganin comments dinku na karanta but replying duka will be hectic y”all know that Nagode sosae Allah ya bar zumunci. Daga yau zanje hutu saboda my friend is getting married, pray please. Is an important biki da bazan iya typing ba har se naga na rakata dakin miji kafin na dawo nutsuwata. I hope zaku min uzuri as usual_
1
_*Yours Truly*_
Ayshatuuuu😍Ban kara ji daga gurin Abba ba akan tafiya ta states, shirun da naji ya tabbatar min it’s a no kenan. Hakan yasa na dangana ba tare da na kara masa magana ba. Wani sati na dawo na tarar da Ummaah ta cika fam kamar zata fashe dama wannan mood din kam ai na saba dashi. Tunda naga haka na kama kaina tareda jan mutumcina. Washegari inadakin inna muna hira ta aiko Asiya akan ta kirani. Ina zuwa na ganta a zaune gefen gado tana ta karkada kafa, zama nayi kan carpet nace
“Ummaah gani”
Key din motarta ta mika min tace
“Dakko hijab dinki zamu fita”
Babu musu na mike hannuna rikeda key din na tafi dakina, dama atamfa ce jikina dinkin skirt da riga so kawai se na dauki hijab coffee dake atamfar da coffee jiki, shoe rack dina na duba na dauki wani flat milk vine se purse sannan na fito , ganin tana jirana yasa ko Inna banyiwa sallama ba kawai na wuce gaba tana bayana. Seda nayi warming motar sannan nayi addua kafin muka fita. Kallonta nayi tana ta danne danne a wayarta nace+
“Ummaah ina zamuje?”
Dago idonta tayi ta kalleni, then ni kuma na rigada na maida hankalina akan titi tace
“Gidan Hajiya Zakiyya zaki kaini”
Seda naji kaina ya sara min baa taba matar da bana so a kawayen Ummaah ba kamar wannan matar, tana daya daga cikin masu zuga Ummaah akaina. Babu yadda na iya haka na dauki hanya amma bakina banda neman agajin Allah babu abinda nakeyi nasan shi kadai yasan abinda nake going through kuma shi zai kawo min dauki. A hanya na tsaya a filling station nayi mata full tank sannan muka karasa gidan. Ina parking nayi wining glasses din sannan muka fito, tana gaba ina baya muka shiga gidan, sunada kudi haka kishiyoyinta uku kuma ita ce ta biyu amma kana shiga zaka san ragamar gidan a hannunta take ita take juya kowa har shi mijin so bana son wannan kawancen. A katon parlonta muka zauna sannan yan aikinta suka cika mana gaba da abinci kafin taxo, tana shigowa tazo ta rungumeni tana fadin
“Daughter da bata zuwa gurin mamanta ko”
Dan murmushi nayi nace
“Aiki ke hanani wallahi amma ai bazan manta Mami ba”
Zama tayi suka gaisa da Ummaah ni kam na bude exotic na tsiyaya na sha bana son tace naki cin komai. Ina nan zaune inaji suna magana kasa kasa se kuma can Mami tace min
“Asmau jeki daki ki jiramu”
Mikewa nayi na tafi dakin tareda crashing akan gadon na dauki wayata ina random searching da ban masan me nake dubawa ba, baki daya hankalina yana parlon. Har nayi waya da kyaftun ta dan dauke min kewa sannan ta kara reassuring dina sannan naji hankalina ya kwanta. Wata Nannyyy ta shigo tace min nazo inji Ummaah. Mikewa nayi na gyara zaman hijab dina sannan na fito kwatkwata idona bai ma lura da mutumin dake zaune ba seda na zauna sannan na ganshi a zaune, mutumin yafi kama da boka gaba dayanshu a birkice yake gashi fal fuskarshi yana zaune se karkada kafa yake, ga wani wari dake tashi kuma nasan tabbas daga jikinshi ne, dan lokacinda muka zo parlon banda kamshin lavender babu abinda yake, i love the scent of lavender so duk inda naji shi se matar ta fado min saboda kamshin gidanta na dindin kenan.
Abu daya da bana tolerating duk kawaici na shi ne wari bana iya jurewa, ko minti daya ban cika ba kawai se naji cikina ya fara kadawa zuciyata tana tashi, i was completely nauseous. Kallon Ummaah nayi zanyi magana kawai naga mutumin yayo kaina gadangadan, fusace na mike tare da ja da baya ina muzurai, instead ya tsaya se naga ya nannada malum malum dinshi yana neman kai hannu jikina,
“Karka taba ni, Ummaah kina kallo?”
Kamar bai ji ba haka ya dinga bina har nakai bango, idanuna na runtse bakina yana ambatar sunan Allah kawai se naji hannunshi yana shafa fuskata, wata muguwar kara na saki tareda zubewa a gurin sumammiya. Bansan me ya faru ba i don’t even know, na dai san daga baya wai ashe me maganin aljanu ne aka dakko shi saboda ana tunanin aljanu ne suka kama ni shiaysa na ki nayi aure. A gado na sameni lokacinda na farka ni kadai, koda na tashi se na fara jin kaurin tukake, tashi nayi na zauna anan naga yadda hayaki ke tashi wai duk ni akewa turare, gaba daya zuciyata tayi min nauyi, kirjina banda zafi babu abinda yakeyi. Tashi nayi zan fita naji an maida ni gadon, se lokacin na lura da Ummaah da Mami da kuma bokan dan a gurina he’s never near Allah wannan mutumin tsubbu yake. Inaji ina gani haka ya kwara min wannan ya zuban wannan, idan nayi ihu se yace aljannun ne hakan yasa kawai nayi shiru. Haka ya gama ya bada wasu layu da itatuwa da saiwoyi da wasu kulle kulle da zaa binne. ita kuma Ummaah se godiya take mishi, kuka ne ya kwace min, kukan takaici, kukan bakin ciki, kukan tausayin kaina, kukan rashin madaga, se naji duk na sare naji kamar ni rahama ta sauka daga kaina. Nafi awa ina kuka tun Ummaah na cewa aljanun ne har naga hankalinta ya fara kaiwa kaina, ganin haka yasa Mami tace nayi wanka, kaina na girgiza ina cigaba da razgar kuka abuna.
Se laasar bayan nayi sallah sannan muka tafi, fuskata tayi jawur kada ma idanuna suji labari. Koda muka tashi tafiya kasa driving nayi saboda yadda jikina ke shaking. Dole haka mami ta bada driver ya kaimu gida sannan ya juya. Dakina na shige na kulle tareda saka key na datse, banma hau gado ba anan jikin kofar na silale a baki na dinga kuka kamar raina zai fita, ban taba tunanin haka ake bakin ciki ba, nayi ta kuka har bansan iyakar lokacin dana dauka a wannan gurin kuma cikin wannan halin ba. Time to time nakan ji ana min knocking amma ko a jikina banma ni da niyyar tashi.
Ban kara fitowa ba se washegari, dake na saba dama ba fitowa nake sosae ba tunda zaman gidan ya zama tamkar a living hell hakan yasa na koma zamana kawai sede aiki ya fitar dani. Ummaah tun daren take kirana a waya amma naki dagawa saboda bansan abinda zance mata ba. Seda nayi wanka sannan na zura wata purple abaya da stones a jiki se walwali take. Comb na dakko na taje kaina na tufike da karamin ribbon sannan na shafa balm a lips dina da yayi ja, kallon fuskata nayi har lokacin bata ware sosae ba ta kumbura saboda rashin bacci da kuka. Ummaah na zaune a parlor hankalinta dukka ta tattara shi akan kofar tawa, ina fitowa idanuna ya sauka a kanta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaisheta nayi ta amsa jikinta a sanyaye ni kuma na wuce kitchen. Ina cikin dama kunu naji shigowar t, kujera ta ja ta zauna sannan tace min
“Asmau kinada hankali kuwa? Kinsan yadda kika tsoratar dani ki shiga daki ki kulle ko a jikinki? Kinsan banyi bacci ba?”
Bance mata komai ba na cigaba da abinda nake, jin nayi shiru yasa ta dawo gabana tareda daka min duka tace
“Bakya ji ne ?”
Na kyafta ido se hawaye, raina a mugun bace nace
“Ummaah me zance miki? Ya kike so nayi? Nidai nasan this wasn’t my mother, uwata ba haka take ba wani ya canja min ke.”
Sororo tayi tana kallona kafin tace
“Saboda na kaiki gurin malami shiyasa zaki fadi haka?”
Kaina na girgiza nace
“Ummaah saboda banyi aure ba shi ne kike kokarin saida imaninki, ke kanki Kinsan wannan mutumin is never near malami, kawai dai kin bi son ranki ne….”
Wani bugu ta kaiwa bakina hakan yasa nayi saurin rufe bakin, fita tayi ni kuma na zauna na dasa sabon kuka.
AyshatuuuuA fragile heart was broken before, i don’t think it could endure another pain, a piece of voice from deep inside that calling you to make you relaxed!
Wannan kwanaki biyun dana kara sun zame min kwanakin da bazan taba mantawa a rayuwata ba, tunda nake addua i was never specific sede nace Allah ya zaba min mafi alkhairi, a ganina hakan shi ne daidai amma tunda naga an fara haka yasa na dukufa adduar Allah yasa nayi aure cikin kankanin lokaci. Ana gobe zan tafi da daddare na dawo daga gidan yaya Halifa saboda gidan babu dadi, daga ni se Asiya se ummaah and I couldn’t, i was suffocating hakan yasa na tafi tun sassafe, Inna ade da Abba sunje umra , jikokin gidan kowa yana gidansu hakan yasa naji zaman ya isheni. Mun jima nida yaya Halifa ina kora mishi bayanin halin da nake ciki. To me zaiyi shi dinma Ummaah ta haifeshi, highest thing shi ne ban hakuri kuma shi din ya bani, ya nuna min Allah yana sane dani kuma komai kaga ya faru to da saninshi. Those words kept me going.
+
Kwana na biyu da dawowa daga kano, na koma aiki na saboda damuwar ma batada amfani. Da yamma ina kwance a daki ba call nake ba so bayan na gama abinda zanyi na fita kasuwa nayo cefane na dawo . Ranar i was craving for dambun shinkafa. Haka na zauna na daura a cikin steamer na koma na fara soya kazar da zanyi pepper chicken da ita. Ina nan zaune na saka wani chilled chapman a gabana ina sha se naji message ping, mikewa nayi da sauri na isa ga wayar tareda tapping message din
A 40year old null para with a diagnosis of ectopic pregnancy and ? Typhoid perforation. booked for ex-lap. Prepare for emergency ex-lap ASAP.
Na karanta yafi sau shida ina kara duba number data turon da mamaki, wannan ai aikin general surgeons ne kuma ma idan ance saboda ectopic dinne I’m not on call. Mikewa nayi na kashe steamer sannan na juye abincin cikin warmer se kadan nasa a plate na saka salad da naman na fara ci. Banma kara komawa takan message din ba saboda a tunanina mistake akai. Seda na gama na gyara dakin sannan naga call din Dr halima yana shigowa, hannuna na goge jikin towel na dauka, ko gaisuwata bata amsa ba tace
“Asmau bakiga message ya shigo wayarki ba?”
“Na gani, I thought mistake ne shiyasa na share”
Cikeda damuwa tace
“This is unlike you, kije yanzun patient din tana Female surgical ward kiyi reviewing dinta”
Kaina Na gyada nace
“Amma bani bace da call bafa”
“Just follow orders kinji, nima order aka bani”
Katse call din mukai inata bubbuga kafa da zumbura baki hakanan dai na samu na dakko kayana na kullum yau pink nasa wando da riga na soft cotton yadi na saba back pack dita na fita. A ward na sameta mugun restless, ciwo yana damunta hakan yasa nayi order a mata allura kafin na kira a kawo ta: daga nan OT na wuce, na samu sun shirya kawai jurana ake hakan yasa na kira dan a kawo patient din. Ana kawo ta na dubi scrub nurse din nace
“Sister, waye zamuyi surgery din dashi?”
Dariya tayi tace
“Baki sani ba dama”
Kafin na bata amsa naji wannan deep voice din tashi, dukda sau daya na taba ji amma hakan baisa na manta da ita ba.
“Evening everyone”
Juyawa nayi da sauri tareda bashi hanya nace
“Welcome sir”
Kanshi ya gyada min sannan ya bawa mazan gurin hannu sukai musabaha ya shiga ciki yayi changing sannan muka fara. Tunda na mika masa scapel yake min tambaya akan conditions din matar, God so kind nima book worm ce so yana tambaya ina amsa shi inda gyara yana min yana kara clarifying min abubuwa. Haka mukai almost 4hours muna abu daya, se bayan maghrub muka gama aka maida ita ward mukai sallah sannan yace a kawo masa folder yayi documenting. Ni na kai masa yace
“Sit please!”
Zama nayi kamar yadda yace, idanunshi ya maida kan folder yana going through hx matar.
“What’s your name?”
Dagowa nayi na kalleshi amma bani yake kallo ba amma nasan dani yake tunda ni dashi ne kadai cikin office din
“Asmau Shahada”
Kanshi ya gyada yace
“A ina kikai training dinki?”
Shortly nace dashi
“BUK, sir”
“Good!”
Daga haka baice komai ba se can ya mika min folder yace nayi rubutun. Zama nayi yana kallo ina rubutawa yana kara guiding dina har na dan saki jikina. Muna gamawa yace min
“You’ve done a good job. We meet some other time”
Kaina Na gyada ya fita ni kuma na koma na zauna ina maida numfashi. Tun daga lokacin shi kenan indai zaiyi aiki kowa yasan I’m his partner tun abin yana damuna har na sake na saba.
Wata Wednesday mun gama ward round, banyi breakfast ba ranar saboda kadan ya rage ban makara ba hakan yasa na tafi cafeteria dan cin abinci. Tsirarin mutane na tarar suna cin abinci, wasu sun gama, seda nayi order sannan na dawo na zaune ina jiran a kawo min. Nayi nisa sosae a cikin wayata ina chatting naji alamar an zauna gefe na. Da sauri na dago wani mutumi ne in his mid thirties ya tsareni da idonshi, the gaze was so intense hakan yasa nace
“How may i help you”
Wani murmushi ya saki yace
“Finally, na samu ganin workaholic Dr Shahada. How far?”
Bansan amsar da zan bashi ba hakan yasa nayi shiru tareda maida hankalina kan wayata, i knew him somewhere amma na rasa a ina na sanshi. Shima bai kara cemin komai ba seda aka kawo min abincin se na maida shi akan ayi packaging ba anan zanci ba. Se naji yayi dariya yace
“Doctor, ya zaki ce ayi packaging?”
Dagowa nayi na kalleshi nace
“Ka takura min”
Murmushi yayi yace
“Tun yanzun, ai abinda zuciya ke so no way ta bar abinnan”
Mikewa nayi naje counter cashier na biya sannan na fice kawai, ashe yana bayana seda nayi nisa sannan yace
“Doctor, you shunning me?”
Tsayawa nayi nace
“Idan abu kake so ina ganin wannan is not right kazo ta haka, dan Allah idan wani abunne follow the right route”
Daga haka na juya zan tafi, to my utmost amazement kawai se ya ruko hannuna cikin sauri na juyo, mamaki kamar ya kashe ni, kafin nayi yunkurin cire hannun se ji nayi ance
“Asmau!”
A tsorace na dago idanuna only to see MD a tsaye ya tsareni da idanunshi da suka kada sukai ja, sunkiyar da kaina nayi tareda kwace hannuna, tuntuni idanuna sun fara kokarin kawo ruwa. Yana isowa gurin yace
“Meet me in my office yanxunnan!”
1
AyshatuuuuTamkar an daddatse min joint dina haka naji, ilahirin jikina yayi sanyi na rasa abinda yake min dadi. Lumshe idona nayi na dubi useless, unreasonable Ashole dake tsaye yana wani irin smirking, idanuna na lumshe raina a mugun bace kawai na juya na tafi. Once in a lifetime kowa yana experiencing such embarrassment, tunda nake ban taba jin kunya irin wadda naji ba. Tamkar anmin duka haka na tafi ina tunanin ta inda zan fara hada idanu dashi. Taya mutum zaiji ace mutumin dake ganin mutumcin ka ace yaga wani ya rike hannunka nasan Allah kadai zao fitar dani.1
Banyi gigin zuwa office dinshi ba saboda bansan wanne ido zan kalleshi ba kawai se na juya na tafi mota ta nayi mata key se gida, dukda hankalina yana kanshi Amma zuciyata gargadi na take
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 18