akan kada fa na zake, tayi kuwa nasara haka na basar na tafi daki naci abinci sannan na kwanta, a raina ina fadin aikin ma na yau na fasa bazanyi ba.
Shikam acan a mugun fusace ya isa office dinshi, yana shiga yayi slamming kofar da karfi tareda fadawa kan cushion ya zauna, cushions ne guda hudu tsakiya center table ne me kyau covered with glass baki daya. Zama yayi ya daura kafafunshi akan table din. Wani zafi ne ke karyo masa se gumi yake ka rantse da Allah yana karkashin kwalleliyar rana ne, nan kuwa cikin niimar split yake har biyu a cikin office din. Coat dinshi ya cire ya aje gefe sannan ya sassauta necktie dinshi tareda kurawa kofar idanu yana expecting shigowar Asmau amma har awa daya ta shude babu Asmau babu alamar ta. Mikewa yayi ya fara pacing a cikin office din, me yarinyar nan take nufi dashi yace tazo sannan taki zuwa ta sameshi, kanshi ya girgiza daidai knocking a kofar hakan yasa a sukwane yace
“Yes, come in please”
Kofar aka turo idanunshi a kafe yana jiran ganin wannan farar fuskar tata amma maimakon ganinta se yaga ashe Director Admins and finance ne, se lokacin ya tuna sunada magana dashi. Daidaita kanshi yayi cikin sauri ya koma seat dinshi tareda masa izinin zama, seda suka gaisa kafin ya bude file ya fara briefing dinshi amma rabin hankalin Dr Kwaccido baya gurin tunnainshi kodai mutumin da ya gani tareda Asmau ya gudu da ita ne? Kodai dama saurayinta ne cikin sauri ya matsar da wannan thought din a ranshi, it took him almost 2 months yana bincike a ciki da wajen asibiti akan Asmau, babu inda yaji tana da wani tsayayen magana a kanta….
“Sir, you’re not concentrating, ko mu hadu gobe?”
Kanshi ya dafe cikeda damuwa yace
“I’ll be glad, thank you”
Haka ya tattare kayan shi ya tafi shi kuma ya cigaba da jiran tsamanni amma har yaje azahar ya dawo bata zo ba, sau da dama se ya fara dialing numbers dinta da yayi storing dinsu a kwakwalwar kanshi tun ranar da Dr halima ta bashi ita amma ya kasa, baisan abinda zaice mata ba, zuciyatshi tasha gargadin shi akan wannan kallon ruwan da yake kada wankin hula ya kaishi dare. Ko kuma garin bari ya huce har ya zama rabon wasu, kanshi ya girgiza dan baya tunanin zai iya bari hakan ta faru.
Wajen laasar ya kammalla komai na ayyukan ranar, hannunshi rikeda briefcase da suit dinsa yana waya ya fito, messenger dinshi ya karba tareda kai mishi mota, godiya yayi masa sannan ya wuce cikin motar yana baza idon ganin ta inda zata bullo amma bai ganta ba haka ya tafi dik babu dadi, haka nan yaje gida. Kamar yadda ya saba ganin gidan it was so empty ya zaiyi tunda haka kaddra ta zabar masa kuma hakanan zai karbeta babu yadda zai iya. Straight bedroom dinshi ya wuce yayi wanka yayi alwala sannan ya zura jallabiya brown me gajeran hannu ya dawo parlor ya zauna. Babu jimawa yaji ana knocking wanda yasan ba kowa bae illa sabiu cook dinsa, sunyi waya yace masa ya fita dan yun wata gaisuwa. Shigowa yayi ya risina ya gaisheshi sannan ya wuce kitchen dan hada masa abinci, idanunshi ya lumshe yana bin parlon da kallo, ko ina a share yake, tiles din se kyallin mop suke amma kana kallon yadda komai Na parlon yake kasan babu mace a gidan. It’s obvious kana shiga zaka fahimci hakan, kanshi ya shafa yana jin lokaci yayi da zaiyi uncaging zuciyarshi hakanan, ya kamata ya fito daga dreadful past life dinshi ya cigaba da rayuwa, wannan zuciyar tana bukatar aboki, ya kara kallon katon parlon da hasaso gadon shi, yana bukatar living partner, he sure needs a soulmate.
STORY CONTINUES BELOW
Washegari ranar alhamis, kamar kowanne sati ita ce ranar da muke surgery ni da Dr Kwaccido. So ranar tunda nayi asuba na ko wanka banyi ba Na tafi Paediatric surgical ward, nan patient din yake. Yaron shekarashi biyar yana fama da umbilical hernia. Though condition din is a minor one amma a haka yayi mana booking. Ina zuwa anesthetist din tana zuwa, tare mukai reviewing dinshi kowa yayi documenting abinda ya samu sannan muka rabu. Gaba daya ji nake inama inada excuse din da zan bayar dan bana sam haduwa dashi kwata kwata amma ina na babu wannan, se goma na safe sannan na fito, fuskata tayi yar fayau tsabar fargaba da damuwar da nake ciki idanuna duk sun fada sunken in. Yanayi na ma kawai zaka kalla kasan akwai tambaya. Ina zuwa office na samu kan sofar dake gefe na dan kwanta ai bacci yace idan kaci bashi na se ka biya and it happen.
Bansan ashe har time ya tafi ba, se can naji ana knocking kofar office dina, ko kafin na tattara guntun karfin da ya rage na tashi, tuni kofar was flung open. Wannan kyakyawar fuskar tashi me cikeda haiba da kwarjini tasa nayi saurin tashi ina lalubar veil dina, wannan idanuna nashi that always shine me kamar an zuba musu mai cikinsu ya tsareni dasu, a take naji kamar anyimin duka, yunkurun da nake na daina se kasa da nayi da kaina ina jin an takura ni da yawa. Yana tsaye tareda harde hannyansa a kirjinshi shi bai zauna ba bai kuma nema gurin zaman ba. Kafin na kara yunkurawa naji yace
“Sleeping on duty?”
Da sauri na muskuta tareda girgiza kaina nace
“Sir, banida lafiya ne”
A take naga yanayin fuskar shi ya canja, shigowar shi tamkar wani zaki haka ya shigo ranshi a hade amma yanzun se naga damuwa ta dauke bacin ran dake ciki. Daidaita tsayiwarshi yayi cikin wata tattausar murya wadda babu wani da namiji daya taba amfani da ita wajen yimin magana yace
“Sannu, kinsha magani?”
Kaina Na girgiza nace
“I was about to, se bacci ya daukeni.”
Kanshi ya gyada se kuma ya fita, hakan yasa na sauke nannauyar ajiyar zuciya tareda lumshe idona, ni nasan banda lafiya amma a matsayina ta likita bana tunanin nasan me yake damuna, ban kuma san wanne irin taimako zan bawa kaina ba, nasan kilan tarin damuwar da nasa a zuciyata ce take neman kayar dani…..Soft knock akai jikin kofar, bakina a hankali na bude tareda bada izinin shigowa, shi dinne ya dawo sede wannan karan ya samu rakiyar head of medical department da kuma chief pharmacist. Inata kokarin mikewa ya hanani tareda bawa Dr Mansur damar ya dubani, BP na ya fara dubawa, kawai gani nayi ya cire glasses dinshi yace1
“Her BP is reading 70/40mmHg sir”
Yana fadar haka se naji tamkar an saukar da min symptoms, baice komai ba illa bina da yake da idanunshi me tuhumata akan Me ya faru? Nidai kasa kawai nayi da kaina ina jin ana min prescription sannan aka kira pharmacy suka kawo. Drip aka fara daura min yana fara shiga wani wahallalen bacci yayi gaba dani. Se can bayan wasu awoyi sannan na farka , ina office dina amma ba kamar dazun ba, ina bude idona da kyaftun na fara cin karo tana sallar laasar. Cikin sauri na yunkura inajin karfi a jikina ba Kamar dazun da nake jin jiri ba.
Toilet na shiga nayi alwala sannan nazo na zauna dan har lokacin jikina gashi nan dai, a zaunen nayi both zuhr da asr sannan na kwantar da kaina akan cushion ina lumshe idona.
“Ya jikin Twin?”
Bude idanuna nayi tareda yin kalar tausayi na dubeta har lokacin uniform ne jikinta alamu sun nuna kilan ko ward ba taje ba, ga Afeeyya ‘yar 5 months ta shimfidar da ita a yar corner se baccinta take peacefully.
“Twin Alhmdllh. Yaushe kika zo? Waye ya fada miki?”
Wani kallo tayimin wanda ta saba yimin idan gulma ta motsa, hakan yasa na cuna bakina ina dauke kai. Dariya tayi wadda tasa dole nima nayi sannan ta matso tace min
“Boss ne, da kanshi yazo har ward ya tafi dani, he left here not long ago.”
Kaina na gyada kawai ba tareda nace komai ba, dan bansan me zance din ba. Sake matsowa tayi kamar zata shige jikina hakan yasa na ture ta baya da dan guntun karfin nawa daya rage nace
“Ke munafuka ce”
Shrugging shoulders dinta tayi tace
“Oho! Baby bude baki zakiyi kimin bayani, me yake faruwa. Kinga yadda ya rikice? Ni daya shigo ward dinmu I thought something terrible happened ashe Twin ce babu lafiya”
Hararata nayi nace
“Kede Allah ya sawwake miki, he’s none but my boss and partner aiki na”
Tsareni tayi da idanu irin she needs more, tsaki nayi nace
“Dan Allah ki bani abinci I’m starving”
Hakuri ta bani sannan ta hada min wani tea me kauri, yayi min dadi kodan ina cikin yunwa ne oho, seda na shanye tas sannan tace an tafi a kawo abinci. Bata kara min zancen ba tunda tasan da akwai wani abu da zan fada mata, tsakani na da ita babu boye boye so we still maintain the status. Tunda nayi shiru na fada tunani, anya yadda zuciyata ta adana Dr Kwaccido matsayin shugabana da kuma partner aiki? Ina tantamar hakan, duk wanda nayi aiki dashi zai nuna yaji dadi kuma zaiyi kokarin maintaining dina tun ina house job amma shi nashi salan caring din ya banbanta dana kowa. To amma someone like him…. Sallamar shi yasa nayi saurin bude idanuna, a hankali na amsa wanda iya bakina ne kawai ya motsa, muna hada ido ya sakar min wani murmushi. I swear seda tsikar jikina ta tashi, those eyes of his will definitely not allow me to live in peace sede idan kullum zan kasance ina kallonsu ne.
Gaisawa sukai da kyaftun sannan ya mika mata ledar hannunshi yace abinci nane, gefena ya dawo ya tsugunna yace
“Are you ok?”
Kaina na gyada nace
“Much better. Thank……”
Shush yayi min sannan yayimin murmushi yace
“Kici abinci zanje office”
Se na samu kaina da yi masa murmushi nace
“Allah ya bada saa”
Kanshi ya gyada ya dubi kyaftun dake rike da Afeeyya data riga ta tashi ya bata sallahun lallai naci abinci. Aikuwa yana fita ta fara tsokanata wai wallahi so na yake nidai ban kulata ba dan bazan saka abin a raina ba balle ayi back stabbing dina!
2
Your comments keep me going……..
AyshatuuuuIna kammalla cin abincin naji wani karfi yazo min, duk wannan kasalar babu ita, mikewa nayi na tattara gurin sannan nace da Kyaftun mu tafi gida dan ina son nayi wanka na canja kayan jikina. Babu musu ta tattara kayanta muka fita, bani da wani karfin da zan iya driving hakan yasa kyaftun karbar key din ita kuma Afeeyya na karbe ta, mun saba da ita sosae bata min kiwa dan wani sa’in se tayi ta kallona ni da kyaftun tana tantamar gurin wa zataje tunda kowa yasan nida mahaifiyar ta kama muke sosae, banbanci na da kyaftun nafi ta haske ita kuma ta fini tsayi sannan ita ba a rame take ba, wadda tashin hankali da damuwa yasa na koma hakan.+
Muna shiga na aje Afeeyya na shiga wanka, simple gown nasa ta wani pure cotton yard maroon, free gown ce se stones da aka mata ado dashi. Scarf milk na dakko Na daura sannan na murje jikina da turaren kullum La’eeqa da soft. Lumshe idanuna nayi na dawo na zauna inajin wani daddan yanayi a jikina. Kallon kyaftun nayi da take kokarin hada pap din Afeeyya,
“Ki kirashi kice kin dawo gida, let him not waste his time checking on you a office”
Dan bata fuska nayi tareda fadi
“Is there need for that?”
Kanta ta girgiza tana hararata tace
“Kina da matsala kinsan da hakan? How….?”
Se tayi shiru tareda daukar Afeeyya ta daura ta cinyarta ta fara feeding dinta, wayata dake gefena naji ta fara ringing hakan yasa na kai hannuna na dauka, Adda Sa’ada ce cikin sauri nayi picking dan ta rigada tasan banida lafiya, i texted her though ina tunanin se lokacin ta gani. Ina picking tace
“Fara what happened?”
Dan murmushi nayi jin muryarta duk da damuwa nace
“Ba wani abu bane kawai BP na yayi low”
Ai fa kamar famfo ta fara zuba, tana tamin fada akan tasan na takurawa kaina ne shiyasa hakan ta faru, seda ta gama fadan sannan ta dawo nasiha tana fadin
“Komai da kike gani is a matter of time, da ace tsangwama da takura kai yana sawa kayi abu, da tuni kinyi aure amma shi Allah is wonderful, he’s a perfect timer. Lokaci ne da zarar yazo zakiji it worth the wait!”
What will life be without Adda Sa’ada? Hell na ayyana a raina, bazan iya fadar abubuwan da matar tayimin a rayuwa ba amma she sticks around bata taba nuna min laifina bane da banyi aure ba, Anty Bintu, Yaya Halifa da Adda Meeyna. Banda kamar su. Ina aje wayar kyaftun ta mike tana fadin
“Kada ki zama kina manta alkhairi kuma kada ki bari a golden opportunity like this ya wuce ki. Zan tafi gida, se dare zamu dawo da Daddyn Afeeyya.”
Mikewa nayi a hankali dan bawai malaise din dake damuna ya tafi duka bane, yanzun ma jina nake kamar zan fadi dan dai ina daurewa ne. Hannunta na riko nace
“Ki fahimci abinda nake nufi, i can’t just throw myself on him kamar yadda nayi akan mukhtar (RIP) da kuma Suleiman. I was back stabbed kuma laifin waye? Nawa ne saboda ina ganin dukkan wanda yadan nuna kulawa akaina sona yake. Kina son na kara haka, repeating same mistake is nothing but foolishness”
Zaunar dani tayi dan taga alamar zan iya faduwa ta rike hannuna tace
“Ki fahimci abinda nake nufi nima, ba ina nufin you start chasing him, stalking him and stuffs. Kinsan dai ya miki abin kirki to ko thank you ne he deserves it.”
Kaina na gyada in agreement na dauki wayata and I sent him
Thank you, jiki yayi sauki. Na bar office ina gida
A gurina they were only a plain words amma a gurinshi yayi ta nanatawa saboda dukkan abinda zai fito daga gurina yana daukar abin me muhimmanci. Baiyi min reply ba har kyaftun suka kawo min abinci naci suka tafi na kulle dakin na kwanta tunanin rayuwata yayi min rubdugu, addua a bakina kan Allah yasa Ummaah ta fahimci rayuwa, ta fahimci cewar lokacin zai zo. Da wannan bacci yayi gaba dani se can cikin baccin naji vib din wayata, bansan yaushe rabon da naji an kirani past 10 so da mamaki na bude idona tareda mika hannu na cira wayar, take idanuna suka bude ganin number da take kira, Dr Kwaccido na ayyana a raina at this time, kifar da wayar nayi inajin yadda ilahirin jikina ya mutu, ina ayyana me yasa zai kirani, wata zuciyar tace just to check on you, kaina Na girgiza na ba tareda na yarda da uzurin da zuciyata ta kawo ba. Amma se na samu kaina da kasa nutsuwa, na janyo wayar na kalla 1 missed call, na danyi tsaki ina mitar har yaushe zaayiwa mutum call daya as if baa damu ba. Haka na gama yan mitocina na bude wayata ina kallon pictures dinsu Amalin Adda Habiba sunyi birthday itada Aarif last week.
STORY CONTINUES BELOW
Washegari bayan nayi sallar asuba dake friday ce hakan yasa ban bar kan praying mat din ba har seda na karanta kahfi savoda nasan idan na bar gurin ba lallae nayi ba, ill be much occupied. Ina kammlawa na mike anan wayata ta katse min hanzari, ganin number seda zuciyata tayi fluttering, it kept jumping har hakan ya bani tsoro, but ya zanyi dole nayi picking call din saboda banda uzuri. Dauka nayi murya can kasa nace
“Good morning sir”
Manly muryar nan tashi me saka naji waves electrons cikin jikina ya amsa da fadin
“Morning Asmau”
I can swear akan ban taba jin wani ya fada Asmau so correctly kamar shi ba, kowanne harafi seda aka bashi hakkinshi, har seda naji ina bukatar nayi ta jin shi yana kiran sunan.
“Ya jikin naki?”
Dan murmushi nayi nace
“Yayi sauki, Alhmdllh”
“Alhamdulillah, zuwa karfe biyu zan wuce kano, ki zama ready zamu tafi tare”
Baki bude na tsaya ina tunanin abinda yace min, seda ya kara maimaitawa kafin nace
“Sir zan fara call gobe, so bazan samu damar zuwa ba and thank you”
“Na rigada nayi arranging yadda zaayi, ya kamata ki huta saboda ciwonki stress ne”
Se na kasa musa mishi haka mukai sallama bayan yace zai aiko min breakfast sannan nayi bacci kafin time din. Nidai na rasa tantance me hakan ke nufi na kuma kasa fahimtar inda zuciyata tasa gaba da kuma wanne tarba tayiwa alamarin. 8am na bugawa aka kawo min abincin, cikin basket aka jero shi, messenger daya kawo na bashi 500 yana ta godiya ya tafi. Chips ne cikin bowl se farfesun kayan ciki shima a bowl, tea me kauri cikin wani karamin flask. Gefe leda ce a aje na bude tareda ciro abinda ke ciki, rose flower ce hade da greeting card, mamaki sosae ya kamani na bude greeting card din naga na get well soon ne, a kasa yayi rubutu cikin rubutun da ban taba kawowa ya iya ba kasancewar kowa yasan handwritings din Doctors bashida kyau amma yadda yayi rubutun kamar calligraphy lettering style yayi amfani dashi.1
Come on, get back on your feet and continue that gorgeous smile of yours. Quick Shifaaa Cara Mia!
Shine abinda ya rubuta, zuciyata nasan dama is froze, dan tunda Salis ya betraying feelings dina shikenna na daskarar da ita, ga mamakina wannan kalaman nashi take suka raga raga da wannan kankarar, wani bugu da zuciyata ta shiga yi har seda nayi tsoron kada a samu over extension. Jikina yayi sanyi na kalla rose 🌹 din na shafa na shinshina a karshe na rungume ta a kirjina ina adduar Allah yasa daga shi ne. Greeting card na dauka na kara nanata rubutun ina bin kowacce kalma daki daki, komai na fahimta banda wannan cara mia din kuma babu me amsa min. Abinci kadan naci sega kyaftun tayi ta ihu tana murna tana fadin
“Yarinya kin saka yan maza a gaba fa, kinyi kamun full package”
Se na samu kaina da fara yarda da zancenta, kodai so na yake, ko dai……haka nayi ta tunanin kafin can bacci ya daukeni se wajen 12pm na tashi nayi wanka na hada kayan dazan bukata sannnan na yi sallah na karasa abincin da na rage na wanke na kife kafin na fara neman kaya. Ni dama ba maabociyar kwalliyya bace dan powder ma se kayi da gaske nake siya hakan yasa na zizara khol tareda shafa charpet kan tattausan lebena da ya fara bushewa har fata na neman dagowa. Dana kalla madubi se naga nayi kyau daidai yadda ya kamata. Wani lace na dakko me laushin gaske irin vapers dinnan ne. Background din Coffee ne se designs din suka tashi milk da zaren gold a jiki. Skirt da riga ne nasa na daura dankwali tareda dakko matching veil da takalmi, har na manta last dana nutsu nayi shigar arxiki. 1:50 daidai wayar shi ta shigo akan yana jirana, kara gyara zaman veil dina nayi sannan na dauki abinda zan dauka na fita. Yana tsaye gefen motar yayi shigar da ban taba gani ba, yana cikin farar shadda ta zarce ayi masa coffee aiki, kanshi sanye da zannan bukar yayi kyau very charming. Dake quarters din namu babu mutane yawancin an tattafi weekend masu aiki nayi yasa yake tsaye shi daya. Back seat nasa kayan sannan na shiga gefenshi danshi tunda na kusa karasowa ya koma ciki ya tashi motar. Tunda Na gaisheshi ya amsa ban kara ko tari ba haka shima se gudunshi da yakeyi, seda mukaje wudil ne ya tsaya karbar document ni kuma na samu saken kiran kyaftun na mata sallama. Yana dawowa ya kalleni tareda fadin
“You look disturbed, akwai abinda zan taimaka miki dashi?”
Cikin sauri na karkada kai alamar aa tareda lumshe idanuna ina shakar kamshin turarena nashi da kuma car freshner da ya saka, ga sanyin AC. Yanayin was so romantic. A hankali naji waka ta fara fita cikin speakers din, hannunsa yasa yayi increasing volume din tareda fadin
“Shirin yayi yawa, enjoy please”
🎶I’ve been looking for you everywhere, I’ve been asking god when I’ll found you dear? I know some times last days where you least expect. But I’ll be patient i go wait, wait for you my dear. wherever you are, you have my heart, my darling take me yes I’m. I’ll be loving you from now till i found you my love. I hope say you like me d way i be, i go dey wait for you day and night dear future wife. 🎵
🎤When I need you will you be there my dear? I’ll make silly mistakes please forgive me dear, we have a long a way to waka, hold my hands my dear. Wherever you are you have my heart my darling, I’ll wait for you day and night dear future wife.🎷
1
Tamkar kada wakar ta kare haka naji, idanuna na bude tareda kallon sadhin shi, murmushi ne kwance a fuskarshi wanda tsabar yadda ya kayatar dashi haka na bude baki, hanci ina kallonshi:
“Nayi kyau ne?”
Da sauri na janye idanuna daga kanshi inajin wata kunya ta rufenj kamar na tsaga kasa ta rufe dani.
AyshatuuuuHar kofar gate din gidanmu ya kaini, babu kowa a kofar gidan dama Abba nake tunanin zan samu kasancewar friday ce mostly da yammaci yakan fito da kujera ya zauna yana reading papers. Amma yau se babu kowa hakan yayi min dadi. Yana gama parking na kalleshi nace
“Thank you so much sir, a gaida mutanen gidan”
Wani kallo yayimin wanda yafi kama da harara yace
“Shi bakinnan godiya kadai ya iya yi ne?”
Murmushi nayi tareda sunkiyar da kaina amma bance komai ba, shima murmushin yayi me sauti tareda fadin
“Monday very early zanzo mu tafi”
Babu amfanin musu dan Na lura baya son hakan, se kawai na gyada kaina kurum, daga nan na bude kofar na kara masa godiya nayi cikin gida inajin intense gaze dinshi a kaina da har suka so harde ni. Tundaga parlor na san tabbas yau munada baki dan kuwa ga hayaniyar yara nan, da sallama na shiga inajin yadda kaina ya sara, aikuwa yaran dukkansu suka yo kaina suna ihun murnar ganina, dan da yawansu na jima ban gansu ba. Dukda yadda nake ji haka na daure kowanne na bashi peck a kumatu kafin kuma aka karba kayana aka kaimin daki, ni kuma na wuce parlon Ummaah dan Na tabbatar itada ‘ya’yanta masu aure suna can. Ile kuwa dukkansu suna zaune banda Yaya Halifa.+
Kowannensu ya amsa sallama ta tareda bina da kallo, wasu na mamakin ramar da nayi wasu kuma duhun da fata ta tayi. Gaba daya yadda kukasan an tsotse ni haka na koma wata yar fiyat dani. Gefen Ummaah Na zauna daga kan carpet a dadare nace
“Ummaah barka da gida”
Kaina ta shafa cikin kulawar da aka jima baa bani ba, baa nuna min irinta ba tace
“Yar fara kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga yadda kike rama kamar wata me AIDS”
Kaina na sunkuyar hawaye taf idanuna nace
“Bana jin dadi ne shiyasa na dawo nadan huta”
Dukkansu suka fara min sannu wannan ya rungumo ni tanan har seda hawayen da nake rikewa ya sakko kan kuncina, i can’t remember last time da naga haka.
“Ya A’isha da halima da me gidan?”
Kyaftun take nufi da Afeeyya hakan yasa nace tanan tana gaishesu. Lokaci guda na ware anata hira dani muna kyalkyala dariya, naji wani sanyi cikin zuciyata hade da nutsuwa tareda fatan Allah yasa hakan ta daure na cigaba da ganin hakan. Bayan laasar naci abincin da khairiyya ta kawo min sega Yaya Halifa da Abba nan fa aka fara hira, a tsokani wannan a tskokani wancan se bayan sallar isha kowa ya hada kan iyalanshi suka wuce and i was left in my room all alone counting the numbers of boards that made up the ceiling. Na jima bacci bai daukeni ba inata tunanin rayuwa da yadda take juyawa da makomar rayuwata. Firgigit nayi da tuna ban kira bawan Allah daya kawo ni naji yadda yake ba, ba tareda wani tunani ba na janyo wayata na fara dialing tashi, tana shiga na kwakwalwata ta ankare da abinda nake ta tsayar dani se kawai na kashe wayar ina bubbuga kaina da jin haushin dalilin da zaisa na kirashi. Inata tura baki na tashi na tafi dakin Inna amma na samu tuni tayi bacci. Ina dawowa na tarar da wayar tana ringing and it was him calling, haka nan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 18