Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
*ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *wannan shafin gaba daya naki ne LAILA SANI MUH'D (maman teemah) Thnx 4 d love and support* 4⃣2⃣ Mai gadi ne yaji faduwarta ya taho da sauri, tarar da ita yayi ta suma don haka yayi hanxarin lekawa cikin gida ya kira su innah karime ya fada musu abinda ya faru, amma gaba daya suka balbale shi da masifa, suka yi masa korar kare ruwa ya samo ya yayayfa mata, cikin ikon Allah aka samu ta farfado, a hankali ta fara bude idanunta tana salati, hakuri ya shiga bata yana rarrashinta "kiyi hakuri Allah yana sane da halin da kuke ciki, addu'a ita ta kamace ki ba kuka ba" jinta take gaba daya bata cikin hankalinka, a hankali ta karfafa jikinta ta mike, xaunawa tayi don jiri ne ke dibarta, nasiha mai gadi ya cigaba da yi mata,har xuciyarta ta warware daga raunin da ta samu kanta a ciki. yanxu jinta take xata iya karawa da duk wanda ya takaleta da fada, ko ya taba mata mutuncin Amminta, don haka ta mike ta dubi gurin da Ammi take a daure. sunan mai gadin ta kira "malam Ali ina aka jiye mukullin wajen nan, kuma me yasa ka bari aka saka mahaifiyata a ciki" cikin ladabi ya amsa mata "wlh ban sani ba ranki ya dade, su Hajiya ne suka sakata a ciki kuma mukullin yana hannun su" A fusace ta wace gurinsu innah karime ta same su tare da su magaji ana ta hira nuna su tayi da hannunta "abinda ku ke mana ya ishe ku haka, hakuri ba hauka bane, idan tura ta kai bango dan Adam baya jurewa, wane dan iskan ne ya saka min uwa a cikin keji?" dafe kirji innah karime tayi tana mamakin kalaman da ke fita daga bakin Nauwar, gaba daya ta kasa magana sbd bata taba xaton jin hakan daga gareta ba. magaji ne ya mike "wane ne dan iskan a nan, babu wajen da ya dace mahaukaciyar uwarki ta xauna, idan ba xaman turu ba don baxa mu kyaleta a nan, ta bata mana guri da warin kashi ba" bata san lokacin da ta daga hannu xata kwada masa mari ba, rike hannunta yayi. "ko wannan mahaukaciyar uwar taki bata isa tace xata mareni ba, ballantana kuma ke, kuma wlh kin yi na farko kuskure ne idan kika sake yin na biyu ganganci ne, sai kinga yadda xan yi dake a cikin gidan nan, banxa shashasha wacce ubanta bai damu da ita ba" kuka ne ya kwace mata ta fita a fusace ta samu wani katon katako, ta saukewa magaji a kansa, nan da nan ya kamata da kokawa suka rika yi, maigadi ne ya jiyo hayaniya ya shigo ya raba, amma su innah karime cewa suka yi baxa su raba ba, sai ya kasheta su ga abinda xai faru. idanunta a rufe ta fita, gidansu Hamdan ta nufa, kai tsaye dakinsu ta shige ta tarar da momy xaune akan kujera tana isa wajenta ta fada kanta tana kuka, tambayarta ta rika yi. "lafiya Nauwar na ganki a haka me ya faru da ke kike kuka, kiyi hakuri ki fada min matsalar ki" ta kasa fada mata komai sai hawaye gami da ajiyar xuciya da take yi "ki fada min Nauwar dan Allah hankalina ya tashi sosai" cikin kuka take fada mata halin da Amminta take ciki da abinda su innah karime suka yi mata, mayafinta ta dauka suka tafi gidan tare, suna isa ta tarar da Ammi a wannan hali, hawaye ne suka rika xubo mata. "Rehab yanxu kece kika xama haka, kece a wannan halin, gaskiya mahmud yaci amana, bai rike amanar da ya karbo a wajen mahaifanki ba, ya raboki da danginki ya kawo ki wajen da baki da kowa,kuma baki san kowa ba, gaskiya duniya abin tsoro ce" kiran mai gadi tayi tasa ya balle wajen, tunda su innah karime sun hana mukullin, ana budewa tayo kansu da gudu xata dake su,da kyar maigadi yayi ta maxa ya riketa aka shigar da ita daki, gaba dayansu kuka suke babu mai iya rarrashin wani, sbd tausayin Ammi da suke ji. Toilet suka shigar da ita suka canja mata kaya masu kyau, kasancewar tafi sati guda rabonta da taga ruwan wanka, bayan sun dawo da ita daki suka dafa mata abinci mamin hamdan ce take bata,amma da sun bata sai ta furxo da shi ta rika wani ihu kamar na kukan jaki, a haka ta cigaba da bata har ta koshi. mamin Hamdan bata bar gidan ba har sai bayan sallar isha'i Bayan tafiyarta ne Abban Nauwar ya dawo, tana jin karar motarsa ta fito da saurin don ta tarbe shi, amma yana ganinta ya nuna kamar bai ganta ba ya shige bangarensa. bai fi minti biyu da shigowa ba, innah karime ta shiga ta same shi ta xayyana masa abinda ya faru ta hada masa da abinda ya faru da wanda bai faru ba shi kuma ya hau kai ya xauna. A fusace ya fito, yana kiran sunan Nauwar "Nauwar!! Nauwar!! kina ina ne?? jikinta na rawa ta fito don tasan ba alkhairi ne yasa shi kiran sunanta ba. har kasa ta tsugunna, idanunta na kasa tayi masa magana. "gani Abbah" nunata yayi da hannu "kada ki kuskura ki kara kirana da Abbanki ni ba ubanki bane, ni ban haifi wacce xata kashe dan uwanta ba, ban haifi wacce xata ce xata kashe dan uwana ba, daga yau sai yau idan kika kara ikrarin xaki kashe magaji wlh sai na daure ki, sai kin kare rayuwar ki a gidan yari, kuma yanxu yanxu ina son ki tattara kayanki ki fita daga gidan nan, bana son kara ganinku daga ke har mahaukaciyar uwarki" gaba daya ta nemi hawaye a idonta ta rasa, wani daci ne yake taso mata tun daga kasan xuciyar ta, xata bude baki tayi masa magana ya dakatar da ita. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba dayansa sadaukarwa ne ga members na Al-majira fans 1 $ 2 Ina godiya da yadda kuke nuna kulawar ku da kaunar ku ga wannan littafi na gode Allah ya bar xumunci* 4⃣3⃣ Haka ta tashi jikinta a sanyaye ta wuce daki, a hanyar shigarta dakin taci Karo da Habi, bushe mata da dariya tayi Sannan ta dube ta " ba dai ke Mara kunya ba, Kadan kika gani kuma barin gida ya xama dole, sai dai idan rashin xuciya ne xai xaunar da ku" Hawaye masu Xafi ne suka rika kwarara a kan fuskarta, Kai tsaye ta shige daki ta fada kan gado ta fara kuka mai cike da ban tausayi, ta rasa wanda xata ra6a taji dadi ballantana har ta samu damar tattauna matsalarta dashi taji sanyi a ranta. Bugun kofar da ake yi ne yasa ta dawo hayyacin ta a hankali ta tashi don bude kofar dakin,Abbansu ta gani tsaye babu alamar annuri a fuskarsa, suna hada Ido gabanta ya fadi, tasan ba alkhairi ne ya kawo shi ba. Cikin tsawa yake mata magana. "me kike yi har Yanxu baki tattara kayan ki kin bar min gida ba, bana son Ki Kara minti biyu ba tare da kin bar gidan nan ba, Ina nan tsaye Ki hada kayanki Kisan inda dare yayi miki,da ke damu nahaukaciyar mahaifiyarki, bana bukatar na sake bude ido naga giftawar ku a gidana. Fadawa kan shi tayi tana kuka "Haba Abba me Muka yi maka ka tsane mu, idan ka Kore mu ina Kake son mu je, ya Ka ke son mu yi da rayuwar mu ina Kake son mu ra6a mu ji sanyi, bamu da Kowa sai Kai Abbana sai Allahn da ya hallicce mu, Idan kace ka juya mana baya a Yanxu wane hali Kake tunanin xamu fada, na rasa dan uwana, mahaifiyata ta rasa hankalinta,ya zan yi da rayuwata Abbana" ta karasa maganar tana kuka. Saboda tsanin kukan da take yi wasu maganganun ma basa fita.sai da ya gama saurarenta tsaf, ya tureta gefe guda, ya fara mata magana da kakkausar murya. "Ina ruwana da inda xaki, duk inda kika ga ya dace ki tafi mana ba damuwata bace, ai ita duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai sani ba, ku tafi ku girbe abinda ku ka shuka na sharri ke da uwarki" Yana karasa maganar ya fara jefo musu kayan su fall, yana gamawa ya Kira magaji suka fitar da kayan waje Sannan yasa aka jefo Ammi da Nauwar kofar gidan, Sannan ya mayar da kofar gate din shi ya kulle. Kukanta ne ya Kara tsananta Anya kuwa ba mafarki take yi ba, wannan masifa da me tayi kama, ko a mafarki bata taba zaton xata samu kanta a cikin wannnan halin ba, murxa idanunta tayi don ta Kara tabbatar da abinda take ganin ba Gaskiya bane, Yanzu babanta mahaifi wanda yake kaunarsu wanda baya son ganin bakin cikinsu shi ne yayi mata haka, gaskiya asiri bala'i ne, baza ta taba yafewa wanda ya shiga tsakaninta da Abbanta mai kaunar ta ba, kwantawa tayi a kan kayan su tana ta faman kuka, tafi rabin awa tana abu daya, ganin baza ta samu mai taimakonta ba kasancewar dare ya yi, duk makotan su sun kulle gidajen su, wannan yasa ta dago ta fara tunanin nemawa kansu mafita, dagowar da xata yi ta nemi Ammi ta rasa, hankalinta ne ya Kara tashi ta bazama nemanta tana tafiya tana rusa kuka. "Allah ka taimaki rayuwata kaga halin da nake ciki, Allah ka bayyana min mahaifiyata " Tafiya tayi mai Nisa Sannan ta hangota kwance kan wata bola tana tsintar kaxanta tana ci, da hanxari ta karasa ta karbi abinda take ci, dabara tayi mata ta tashe ta daga wajen,suka Kara komawa kofar gidan su ko Allah xai sa Abbansu yaji tausayin su ya bude musu su shigo, abin mamaki tararwa tayi an kwashe kayan da suka Bari gaba daya babu abinda aka bar musu sai kayan jikin su. Haka suka xauna a wajen har xuwa lokacin sallar asubah,yana fitowa ya tarar da su ya sake yi musu sabuwar tijara, maigadi ne ya jiyo hayaniyar sa ya fito don ganin abinda ke faruwa, tunda yasan yanxu gidan ba xaman lafiya ake yi ba. Hakuri ya rika bashi "Gaskiya Alhaji idan aka yi wa bayin Allahn nan haka ba a kyauta ba, kuma ba a yi musu adalci ba, yanxu idan ka Kore su ina xasu je?ka duba fa halin da Hajiya take ciki yanxu gaba daya bata hankalinta, Idan ka koresu Waye xai karbe su, Tunda kaine dolen su, bai kamata kayi musu haka ba, Idan ka kyale su kamar kayi toxarta rayuwar su ne" Tsawa ya daka masa "saurara Malam aikin gadi na dauke ka ko kuma bada Shawara? Bana son munafunci da sa ido, daga Yau ba ruwanka da abinda ya shafi harkar iyalina, ka tsaya iya matsayinka na Mai gadi". Tsugunnawa yayi har kasa "Allah ya huci xuciyar ka Alhaji, na fada maka gaskiya ne Sbd xaman tare bai ce haka ba, Amma kayi hakuri baza a sake ba Insha Allahu" Binsa yayi da harara, wucewa dakinsa yayi ya barshi yana ta balbala fada. Korarsu yayi, sai da ya raka su har karshen layin unguwar Sannan ya dawo. Haka suka wuce suna tafiya Nauwar na kuka tana tuna rayuwa "tabbas duniya abar tsoro ce kuma ba tada tabbas tana iya juya maka baya a kowane lokaci. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *wannan shafin gaba dayansa sadaukarwa ne gareki QUEEN MARYAM (maman surayya)ina godiya da kulawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci ina yinki irin mugun sosai din nan* *♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 4⃣4⃣ Haka suka rika gararanba a cikin unguwa har kusan magariba,duk wanda ya Kalli halin da suke ciki sai ya tausaya musu, ya kuma yi Allah wadai da halin mahaifin Nauwar. Tafiya suka cigaba da yi ba tare da sun tsaya ba, saboda tana gudun kada a samu masu tsaigumi su je su fadawa Abbanta, cewa har Yanxu basu bar cikin Unguwar ba, Don haka tayi gaggawar neman hanyar da xata tsira da mutuncinta da na mahaifiyarta, tana tafe tana kuka ita kuma Ammi na kokarin xillewa ta barta kasancewar yanxu bata gane komai ba kuma ta iya fahimtar komai. Sai da suka yi nisa da Unguwar sosai sannan suka tsaya, bakin kofar wani gida ta samu domin sun gaji da tafiya tana son su huta kuma su Kwana a wajen, idan gari ya Waye kuma tayi tunanin inda ya dace su tafi, domin xaman su a haka ba mai yiwuwa bane. tunanin zuwa Dan batta tayi, sai kuma taga cewa idan taje Dan batta Akwai yiwuwar Abbansu Yaje ya Kore su,don haka ta yanke shawarar tafiya tasha duk motar garin da ta samu, Kawai xasu hau tunda Akwai yan canji a a jikinta. A Yanxu babu abinda ya fi damunta Sama da lalurar Amminta,da rashin wanda xai taimaka mata wajen nema mata magani, tana tunanin hawaye na sauka a kan fuskarta. Wata murya mai sanyi taji ta mata Magana, saurayi ne wanda baxai wuce shekara talatin ba xuwa talatin da biyu yayi mata magana, da dukkan alamu yana da nutsuwa da addini. "Assalamu alaikum yan mata" Dago fuskarta wadda ke cike da hawayen bakin tayi, hanxarin goge hawayen tayi ta dube Shi, cikin ladabi ta amsa masa sallamar "wa alaikumussalam wa rahmatullah " Dubanta yayi yana murmushi. "kin burgeni yan mata kin iya amsa sallama, kuma ba kida wulakanci da girman kai, yadda kike mai kyan nan ya kamata a ce Kina da girman kai amma da yake Kin san darajar dan Adam sai kika amsa min cikin sakin fuska, Allah yayi miki albarka " Amsa masa tayi da Ameen, ya cigaba da surutu. Duk ya cikata da magana ta kosa, ya fadi abinda ke tafe da shi ya bata guri, ta cigaba da dogon tunanin da take yi, domin wannan surutun nasa babu abinda yake Kara mata sai takaici. maganar sa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi. "Da dukkan alamu Kina cikin damuwa Don gashi Ina magana ma hankalin Ki na wani wajen, dan Allah ki saki ranki da ni Ki fada min abinda yake damunki ni kuma na kudiri niyyar taimaka miki da baki mafita a kan abinda ya dameki" Shiru tayi ta kasa bashi amsa sai kalloshi da take yi hawaye na sauka a fuskarta. "kiyi hakuri Ki share hawayen Ki fada min damuwarki dan Allah, ke nake saurare". Cikin kuka take masa magana "baza ka iya fitar da ni daga cikin matsala da kuncin da nake ciki ba, Allah ne Kawai xai iya fitar dani ka kyale ni, bana son na Kara tuna abinda na fara mantawa da shi" Lallabata ya shiga yi a kan ta fada masa matsalarta Amma taki, sai gajiya yayi ya kyaleta. Dubanta yayi sake yi, yana murmushi tunda baxa Ki fada min ba bari na kyale ki, amma yanxu ina Zaki naga kin xauna a nan? "babu inda xan tafi a nan wajen xamu Kwana " Cikin mamaki yake mata magana. "a nan wajen fa kika ce gaskiya baxan bari ku Kwana a nan ba, Sbd gaba daya babu security, kizo xan taimaka muku na baku gurin Kwana Amma fa idan kin amince" Shiru tayi ta tafi dogon tunani,ya za a yi daga haduwa da mutum bata San halinsa ba yace xai taimaka mata, xuciyar ta bata amince da binsa ba "Ki yarda da ni baxan taba Cutar da ke ba, Wlh da xuciya daya nake son taimaka muku don naga halin da kuke ciki " Jin ya yi mata rantsuwa da Allah yasa ta amince xata bishi ya basu wajen Kwana. Don haka ta Mike ya taimaka mata,ta tashi Ammi kasancewar ta fara bacci. Gida ne mai daki biyu ciki da falo sai kuma falle daya sai toilet da kitchen da tsakar gida, gidan ya tsaru sai dai karami ne ba shi da girma.Amma Akwai kayan more rayuwa a cikinsa. Nuni yayi musu da su shiga cikin dakin don haka,suka shiga dakin ita da Ammi, gurin xama suka samu cikin mintinan da basu wuce biyu ba ya xo musu da abinci mai rai da lafiya, Dan ruwa, duk abinda suke bukata shi yake kawo musu,da alama dai gauro ne ba shi da aure, bayan sun gama cin abincin ne ya shigo ya same su, kallonta yayi fuskar sa a sake yana murmushi. "da fatan dai kin koshi kuma gajiya ta bar jikin ku" Kallon shi tayi ta gyada masa Kai alamar "eh" naga alama dai malamar nan bata son magana, Gashi ni kuma sarkin surutu ne da son tambaya kamar dalibi mai koyon aikin jarida Kallonshi tayi tayi yar dariya "tunda kun ci abinci kun huta bari na wuce dakina lokacin bacci yayi, Amma kafin na tafi Ina son Jin Sunan malamar" Kanta a sunkuye ta amsa masa "Sunana nauwar wannan kuma mahaifiyata ce Allah ya jarrabeta da matsalar tabin hankali ne" Cikin tausayawa da kulawa ya yi mata magana "Subhanallah Allah ya bata lafiya, Insha Allah ina da taimakon da xan bata xata samu sauki da yardar Allah" Cikin farin ciki ta amsa masa da Allah ya bada iko. Tunda taji ya ambaci xai taimakawa Amminta ta samu lafiya, xuciyar ta tayi dadi taji kamar an gafarta mata xunubanta, sallama yayi mata ya wuce dakin sa, yana fita tayi shirin kwanciya ta Kwantar da Ammi suka fara bacci cikin Farin ciki. Cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita, a cikin baccin taji kamar tafiya a cikin dakin Don haka ta yi saurin bude ido a tunanin ta Ammi ce xata fita. saurayin nan ta gani daga shi sai singlet da boxers ya nufo inda take, cike da mamaki ta dube Shi lafiya Malam, Kai da ka taimaka mana kuma me ya shigo da kai da tsohon daren nan. Dubanta yayi yana wani shu'umin murmushi " a tunaninki xan taimaka miki haka Kawai ne ba tare da kin taimaka min ba ai rayuwar Yanxu ban gishiri in baka Manda ne sai kin bani xan baki" Kara matsowa yayi daf da ita tana ja da baya tana rokon shi ya tausaya mata ya dubi halin da take ciki ya kyaleta. Murmushin yaudara ya cigaba da yi mata. "yadda kike budurwar nan son Kowa kin wanda ya rasa me yasa xaki cuci kanki, arxiki yana kiranki Kina gudunsa kin fi son ku cigaba da kasancewa a wahala ke da mahaifiyarki, Ki bani dama na shigo cikin rayuwar Ki na sanya Ki Farin cikin da xaki dauwama a cikinsa har Avada, idan kuma kince baki yarda ba, ni baxan miki dole ba sai ki bayani abincina da kika ci min ke da mamanki. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Ba nida Bakin da xan gode muku masoyana sai dai fatan Allah ya bar xumunci* 4⃣5⃣ Hannu tasa a jakar da take adana yan kudadenta ta ciro masa naira dubu biyu ta mika masa. kallonta yayi cikin fushi ya fara mata magana "Sbd ba kida hankali Kudi nace Ki xaro ki bani ko abinda na ciyar da ke,ba Kudin ki nake bukata ba abinda kika ci min xaki baya ni Yanxu" Tsugunnawa tayi har kasa tana masa magiya "ka taimake ni kayi hakuri a Ina zan samo maka abinda xan biyaka Yanxu" Kara matsowa yayi daf da ita ya matseta jikin bango numfashinsa na sauka a kan fuskarta, kokarin matsawa tayi ta xille ta kasa, da sauri yasa hannu ya kamota ya manna fuskarsa da ta ta, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar da yana cikin jaraba "kan ki nafi bukata a Yanxu ba Kudi ko abinci ba, ina so ki biyani ne da abinda Allah ya axurtaki da shi. me yasa kike son yi min rowar abinda kike da shi, me yasa xaki yiwa kanki muguntar samun arxiki, idan kika rabu da gidan nan nasan babu wanda xaki samu ya karbe ki a wannan halin da kike ciki ke da mahaifiyarki, don haka na baki minti biyu kiyi Shawara da xuciyar ki duk abinda kika yanke Ina maraba da karbarsa ,Amma ki sani baxan miki dole ba" Komawa kan kujera yayi yana mayar da numfashi ita kuwa Nauwar sai faman share hawaye take yi, tunda take bata taba ganin bala'i irin wannan ba, kana tunanin mutum xai taimake ka asheba kyakkyawar niyya ce ta kawo shi ba. Tausayin kanta ne ya kamata, komai na duniya ya cakude mata, burinta Allah ya dauki ranta ta huta da jarrabawar da take ciki. Sake kallonta yayi ya mata magana "ke nake saurare Wace Shawara kika yanke idan har baki amince da kudirina ba ki tatttara kayanki Yanxu ki bar min gida, in yaso ko Menene ya same ku ba nida asara" Fadar wannan maganar da yayi ba karamin faranta mata ranta yayi ba, da hanxari ta amsa masa. "Ban amince ba" Cikin mamaki ya dubeta "amma ban taba tsammanin cewa ke wawiya bace sai Yanxu, a ce kina cikin wannan masifar ki qi amincewa da abin alheri, na miki alkwarin xame miki uwa da uba Sannan watsi da damarki kice bakya so, kada kiga cewa dare yayi ko xan daga miki kafa na fasa korarki Wlh Yanxu xaki fita ki bar gidan nan, tunda ba gadonki a ciki banxa shashasha Mara rabo" Bin sa tayi da ido bata ce masa komai ba,tashin Ammi tayi suka fito daga dakin har waje ya rako su yana xaginsu yana cewa Nauwar Mara rabo, sai da suka fita,Sannan ta kalle shi cikin tsiwa take masa magana. "Alhamdulillah na godewa Allah da bai baka damar Cutar da mu ba, macuci maciyin amana, Indai a kan na xauna ka lalata min rayuwa ne gara na rasa rabon duniya gaba daya, don nasan Akwai tanadin da Allah yayi min a lahira" Kallonta ya rika yi ya rasa bakin magana Sbd a tunaninsa bai xaci tana da baki haka ba, mayar da kofar gidan yayi ya kulle, ita kuma ta kama hanya suka cigaba da tafiya, gari yayi shiru ba a Jin komai sai haushin karnuka, kasancewar lokacin karfe biyu da rabi na dare. Bakin wata Makaranta suka samu ta roki masu gadin a kan tana so su bata wajen kwana, ta fada musu su matafiya ne dare yayi musu a hanya, Washe gari su cigaba da tafiya, basu yi musu gardama ba suka basu aji suka kwanta. Gari na wayewa suka taimaka musu da koko da Kosai bayan sun kammala karyawa suka yi musu sallama suka nufi tashar Na'ibawa don su hau mota. Tunanin nauwar gaba daya ya dauke ta rasa motar garin da xasu hau, tana tsaye tana wannan tunanin taji an yi mata magana. "yan mata ina xaki je Kaduna xaki ko maiduguri ga motocin mu nan Saura gurin mutum biyar su cika" Da sauri ta bashi amsa da Maiduguri sbd ta tuna Abbanta a nan yayi bautar kasa inda ya hadu da wasu mutane suka yi xaman mutunci suka xamo tamkar yan uwa har ya taba kai su xiyara mai dugurin dan haka taji dadin samun motar garin. Shiga suka yi suka xauna ita da Ammi, ba a Fi mintuna biyar ba aka karasa cika motar suka dauki hanyar garin mai duguri. Da misalin karfe shida da rabi na yamma suka sauka a tashar garin inda Kowa na motar ya fita ya kama hanyar inda xai je, tun a hanya taga gaba daya garin ya canja mata, ba irin yadda ta san shi a baya ba, gefe guda ta samu ta tsaya tana tunanin Sunan mutumin da zasu je wajensa, cikin ikon Allah ta tuna Sunan wani bawan Allah ta samu xaune. Sallama tayi masa ta tambaye shi ,nawa ne kudin motar da xai kaita unguwar Hausari, cikin kulawa ya fada mata farashin kudin Sannan ya taimaka mata

Chapter 11 of 29