kan gado.
cikin mamaki ya dubi mama
"dama abinda take yi kenan amma ku ka ce ta ji sauki"
"hmm lallai sadeeq baka san lokacin da take kan ganiyar cutarta ba, ai yanxu anji sauki sosai da ko magana bata yi, yanxu dai matsala daya take damunta, bata gane abubuwa sannan bata iya komai ba sai an koya mata"
cikin tausayawa ya dubi Ammi
"Allah sarki sannu mama, Allah ya baki lafiya, insha Allah ni ne sanadin warakar ciwon ki"
magunguna ya dakko ya mikawa mama ta bata,sannan ya yi mata wasu allurai.
kallon mama yayi yana mata bayani.
"wadannan abubuwan da na bata su ne xasu taimaka wajen saita mata tunaninta, sannan a sannu a hankali xan rika xuwa ina koya mata abubuwan rayuwa, amma ku ma sai kun taimaka min, sannan a daina barinta tana xama ita kadai idan da hali nauwar da saimah su dawo nan dakin da xama saboda ta haka ne xata rika koyar magana kuma ta gane komai ba tare da an sha wahala ba"
Albarka mama ta shiga sawa ya sadeeq, fitowa suka yi daga dakin ya shiga dakin su saimah yin hira, don a yanxu ba shi da abokan da suka wuce su.
*Jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:18 PM] Writer: ππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
ππππππ
8β£0β£
Shigar da kansa yayi cikin dakin tare da sallama, tarar da su yayi zaune suna hira, Nawwar ce ke bawa saimah labarin yaya Hamdan da irin gudunmawar da ya basu a rayuwar su, da kuma kanin ta fu'ad da irin tuggun da su innah karime suka yi har suka raba shi da rayuwar sa.
karasowa gurin su ya sadiq yayi, fuskarsa dauke da murmushi kusa da Saimah ya samu ya xauna.
"yan kannena me ku ke tattaunawa nima nazo a yi hirar da ni, ko ba a gayyata ta?"
saimah ce tace
" la yaya har da kai mana"
gyara xama yayi yana facing din Nawwar da Saimah, duk lokacin da suka hada ido da Nauwar sai ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi, sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yan yatsunta, fada tayi a zuciyar ta wannan mutumin me kuma yake nufi da ni ne haka.
kiran sunanta da yayi shi ya katse mata tunani da ta tafi, dagowa tayi ta dube shi, sake yi mata murmushin yayi
"ko ba'a son ayi hirar dani ne tunda na shigo kika yi shiru Nauwar, ki saki jikinki ni yayan ki ne fa"
murmushi tayi
"ba haka ba ne yaya, kawai bana jin magana ne yau"
dariya saimah tayi gami da dukan cinyar Nauwar.
"ita fa wannan yarinyar haka take da miskilanci idan bata ga damar magana ba sai mu wuni a nan bata ce komai ba"
tsokanarta yaya ya shiga yi.
"ki kyaleta Saimah ni nasan abinda ya hanata magana tunanin tsoho mai ran karfe take yi"
da sauri Nauwar ta dago manyan idanunta.
"rufa min asiri yaya, ni har na manta da rayuwar shi Allah"
"ki fadi gaskiya dai, jiya fa kin fada min shi ne xabin xuciyar ki" ya karasa maganar tare da kanne mata ido daya.
"hmm wai a lallai sai kun sani magana ko, to nayi shiru baxan kuma cewa komai ba"
hira suka rika yi suna dariya.
lekowa dakin mamah tayi.
"to sarkin son surutu kana nan kana xuba kamar ruwan famfo ko, taso ka raka ni unguwa xamu karbowa maman Nauwar magani kasan babu damar a tafi da ita yau tunda an bata maganin bacci"
da sauri ya mike yana kallon su Nauwar.
"to xan je na raka mama me ku ke so na taho muku da shi a hanya?"
yana maganar yana kallon idon Nauwar, bata ce masa komai ba sai saimah ce ta bashi amsa.
"fura xaka siyo ma ita muke shaawa"
sake duban Nauwar yayi.
"baki ce komai ba kanwata ta kaina"
kanta a kasa ta bashi amsa.
"nima ita nake so"
A dawo lafiya suka yi masa, sannan ya fita.
kai tsaye gidan magani suka nufa, inda suka fada wa mai maganin yadda jikin Ammi yake.
cike da kulawa yake musu magana.
"kada ku damu da duk abinda xaku gani, a hankali saukin xai samu, cuta ita take shiga lokaci daya amma sauki sai a hankali, fatana kada ku gajiya da nema mata sauki a wajen Allah, da sannu xata samu lafiya Insha Allahu"
magunguna ya dakko ya basu.
"wannan aje a bata tasha sannan tayi wanka, Insha Allah kafin ku sake dawowa xaku bani labarin yadda jikinta xai koma"
godiya mai yawa suka yi masa,kudi ya sadeeq ya dakko ya bashi, cewa yayi baxai karba ba har sai bukata ta biya.
sallama suka yi masa suka fito, suna tafiya a hanya ya sadeeq ya dubi mama.
"Har cikin xuciyata ina jin tausayin matar nan da yarta jinta nake yi kamar yar uwata, tunda na dawo ban taba yin sallah,ba tare da na yi musu adduar Allah ya bayyana yan uwansu ba"
"ni kaina ina tausaya musu wlh, fatana dai Allah ya bata lafiya ta bada labarin inda xa a samu yan uwanta, na manta ma ban tunawa babanku ba yana ta maganar xai kai cigiyarsu gidan radio da televisions har yanxu ban ji ya tuna ba, muna komawa xan kara tuna masa maganar, saboda gara a maida hankali wajen neman yan uwan su"
"mamah a nawa tunanin gara ku bari ta warke gaba daya ta dawo hankalinta sai a nemi yan uwansu amma yanxu tana cikin lalura ko an nemi yan uwanta ba wani abu da xasu iya yi mata"
"haka ne maganarka amma xan nemi shawarar baban ku abinda yace shi xa a bi"
tsayawa yayi ya siyawa su saimah furar su, sannan suka karasa gida.
Hannun shi rike da ledar furar da ya siyo yayi sallama dakin su saimah, da gudu ta karasa ta karbi ledar hannun nasa, ita ma Nauwar tasowa tayi tana masa sannu da xuwa, fuskarsa a sake ya amsa musu.
gefen gado ya samu ya kishingida yana duban su.
"sannu yaya kasha hanya, mun gode da dawainiyar da ake yi da mu Allah ya saka da alkhairi"
"babu komai kanwata mun xama daya da ku"
ledar suka bude ciro furar suka yi suka fara sha, suna godewa yaya sadeeq.
tashi yayi xai fita daga dakin, har ya kai bakin kofa ya kira sunan saimah.
"anjima ina so ki same ni a dakina xamu yi wata magana"
yana kammala fada ya wuce ya fita.
wajen mama ya shiga ya karbi magungunan ya fara hadawa Ammi.
"ya kamata a bata abin nan yanxu saboda ni wlh na kosa ta warke, gobe kawai sai a hada mata na wankan tayi nasan kafin sannan allurar ta saketa"
murmushi mama tayi tana dubansa.
"wai garajen me kake yi ne sadeeq idan an bi komai a hankali ai xai fi ko"
"Haka ne mama, amma kin san ba a bori da sanyin jiki, nafi son naga ta warke ta dawo kamar kowa"
naci yasa har sai da ta tashi suka tafi dakin Ammi, kiran su nauwar tayi suka xo suka taimaka mata ta dagota aka bata maganin ta sha"
*Jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:18 PM] Writer: ππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
ππππππ
*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku ZAHRA MUSA & HAFZIYYA NASIDI, da fatan kun je gida lafiya*
8β£1β£
Bacci Ammi ta cigaba da yi, su mama kuma suka tashi suka bar dakin, addu'a bata bar bakin su ba a Kullum, rokon Allah suke ya wadata Ammi da lafiya.
daki ya sadeeq ya shige ya xauna, kira ya kwalawa saimah da hanxari ta nufi dakinsa
sallama tayi masa.
tarar da shi tayi xaune kan gado ya hada kai da gwiwa, kansa a kasa ya amsa mata sallamar, karasawa gurinsa tayi cikin nutsuwa take masa magana.
"lafiya yaya naga ka hada kai da gwiwa ko baka jin dadi ne"
A hankali ya dago ya dubeta tare da girgixa mata kai.
"babu abinda yake damuna kawai gajiya nayi kin san yau na dan yi xirga-xirga"
kusa da shi ta samu ta xauna.
"gani yaya"
dagowa yayi ya matso kusa da ita yana fuskantar ta.
"wani sirri xa mu yi da ke amma bana so ki fadawa kowa, sbd bana son maganar ta fita yanxu sai nan gaba nake da burin kowa ya sani"
cikin nutsuwa ta dube shi.
"ina jin ka yaya"
"na san kin dade da sanin ina jin xafin halin da mutanen nan suke ciki ko"
amsa ta bashi da
"haka ne yaya"
"kuma nasan kin san da cewa duk inda aka samu tausayi dole akwai so a gurin"
"maganarka haka take"
"bana so na ja ki da nisa ina son Nauwar, saboda yarinya ta shiga xuciyata ta gama yi min, amma ban sani ba ko xata amince ta karbi soyayyata"
farin ciki ne ya bayyana a fuskar saimah.
"Alhamdulillah naji dadin wannan abin dama ina taso nace maka, dan Allah kace kana sonta, ina son xumuncin mu ya dore sbd tana da nutsuwa kuma da gani ta samu tarbiyya, na tabbatar da cewa idan har na fada mata kana sonta baxa ta ki karbar soyayyarka ba, saboda ai ka hadu yayana ba kada wata makusa"
murmushi yayi ya dubeta.
"bana son xuga kanwata, amma kin san wani abu"
da sauri ta dago ta dube shi.
"bana so ki fada mata yanxu, nafi so sai mamanta ta warke saboda yanxu tana cikin damuwa bai kamata a xo mata da wannan maganar ba"
murmushi tayi sannan ta cigaba da magana.
"banda abin ka yaya ina ruwan soyayya da wata damuwa, ka sani ko hakan ya xama sanadin farin cikinta ni dai sai na fada mata"
tashi tayi xata fita da sauri ya jawota ya xaunar da ita.
"kin manta mun yi alkawari baxa ki fada mata ba, idan kika fada mata xata daina sakewa a gidan nan ne, Kullum ta rika xaman daki, yar hirar da nake samu mu yi duk xata daina yarda a yi da ita, nafi so na fada mata a lokacin da xa a ce gobe babanta xai xo kin ga a lokacin xamanta a gidan nan ya kare sai dai na rika xuwa wajenta tadi, ko ba haka ba"
"shikenan yaya baxan fada mata ba"
tashi suka yi gaba daya suka shiga dakin mama, tarar da Abba suka yi xaune suna tattauna maganar kai cigiyar su Nauwar gidan radio, yaya ne ya xauna saimah kuma ta tafi dakin Ammi saboda Nauwar tana can.
Abbah ne ya dubi ya sadeeq.
"yauwa naji dadi da na ganka yanxu domin xancenka ma muke yi, kaine xaka jagoranci cigiyar da xa a bayar a gidan radio da televisions, yarinyar nan ta bamu duk wani tarihin mahaifinta da abinda ya rabo su da gida, don haka idan kaje ka fada musu a program din da aka fi yawan saurara xasu bada wannan sanarwar"
takarda ya mika masa, cike da ladabi yasa hannu ya karba, magana Abbah ya cigaba da yi.
"yau fa nake so kaje don bana son abin nan yayi tsawo kaga an fara samun kan mahaifiyar yarinyar nan, sannan sun fi shekara a gidan nan, idan muka cigaba da xama a haka mun xalunci mahaifin yarinyar nan don nasan duk inda yake yanxu hankalinsa ba a kwance yake ba"
Abba yana rufe bakinsa yaji hayaniya a soro da gudu su Nauwar suka shigo dakin suna magana.
"Abbah ku taso ku ga Ammi"
basu tsaya tambayar abinda ya faru ba suka dunguma suka yi soro.
Ammi suka gani xaune, tana duban su, hawaye na sauka a kan fuskarta, karasawa suka yi kusa da ita, cike da mamaki mama ta dubeta
"sannu maman Nauwar"
A hankali ta dago ido ta dube ta.
"yauwa Hajiya"
dakin ne gaba daya ya hargitse ji kake kowa yana fadin Alhamdulillah sauki ya samu.
da gudu Nauwar ta karasa ta rungume Amminta tana kuka.
"Allah sarki Ammina ashe kina da rabon jin sauki, Allah na gode maka da wannan ni'imar da kayi mana Allah ya kara miki lafiya"
kuka suka rika yi sosai da kyar aka janye Nauwar daga jikin Ammi.
*Jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:18 PM] Writer: ππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
ππππππ
ππππππ
*Happy birthday ππ½ππ½to you NASIBAH ISMA'IL(naseeba gawo)washing you many more blessing years and Happy returns*
8β£2β£
Idanun Ammi cike da hawaye ta dube mutanen da ke dakin.
"nan a ina nake kuma menene dalilin xuwana?"
cike da kulawa mama ta dafa kafadarta.
"ki kwantar da hankalin ki, kina gidan aminci ne inda babu cutarwa a cikinsa, kina garin kaduna a unguwar Rimi, dalilin xuwan ki nan labari ne mai tsawo ki bari ki nutsu sosai xan fayyace miki komai, yanxu dai ki tashi ki karasa wankan maganinki kici abinci sannan mu fara magana"
tashi Ammi tayi ta nufi bandaki saimah da Nauwar ne suka kai mata ruwa bandakin, bayan ta fito aka bata abinci taci sannan ta shiga dakin mama ta fara bata labarin sanadin xuwan su gidan su saimah.
kuka sosai Ammi ke yi, tunda take bata taba xaton xata shiga irin wannan rayuwar ba, sai a lokacin ma ta san danta fu'ad ya rasu, ba karamin tashin hankali ta shiga ba, hakuri mama ta shiga bata har sai da ta dawo cikin nutsuwarta.
ranar da Ammi ta warke kuwa
Farin ciki baya misaltuwa a wajen Nauwar kana ganinta xaka tabbatar da cewa tana cikin farin ciki, alwala ta dauro ta fara jera sallolin godiya ga mahalicci, da ya dawo mata da hankalin mahaifiyarta, sannan ta kudiri niyyar gobe xata tashi da axumi duk don nuna godiya ga Allah bisa wannan babbar ni'ima da ya yi mata.
bayan ta idar da sallah ne saimah ta shigo ta sameta xaune tana addu'oi, sai bayan da ta kammala ta fara mata magana.
"ba karamin farin ciki nake yi ba da wannan babban arxikin da Allah yayi mana, Allah maji rokon bawa indai ka roke shi wata rana xai amsa maka, matukar baka yi gaggawa ba, Allah ya kare mu daga sharrin mutum da na aljan"
dagowa Nauwar tayi ta amsa mata da "Ameen, ban san irin farin cikin da nake ciki ba yau, sbd da na yanke kauna cewa Ammi xata samu lafiya sbd kullum a yanayi daya take"
"ai indai ka dage da addu'a a komai Allah xai baka mafita, mu dai mun godewa Allah da wannan baiwar da yayi mana"
tashi suka yi suka shiga dakin mama, tarar da su suka yi suna hira Ammi har da dariya, cike da farin ciki Nauwar ta karasa wajen fadawa tayi jikin Ammi tana mata magana.
"Ammina sannu da hutawa"
dago fuskarta tayi.
"to sarkin son jiki daga ni xaki xo ki daddanne min ciya ko"
murmushi Nauwar tayi
"Haba Ammina yaushe rabon da na hau, yau dai ki kyaleni na hau kin san anjima ba a hadu ba"
dariya mama take yi
"ai yaran nan haka suke da son jikin tsiya haka nake ta fama da saimah yanxu ta dan rage"
suna cikin wannan maganar yaya sadeeq ya shigo, a ladabce ya tsugunnah ya gaida mama sannan ya juya ya gaida Ammi, cike da sakin fuska suka Amsa masa.
kansa a kasa yake musu bayani.
"mama yanxu nake so na tafi na bada sanarwar nan, amma kafin lokacin ya kamata ku shirya a tafi gidan mai magani nasan xai yi farin ciki idan yaga yadda jikinta yayi, idan na dawo gida sai na wuce wajen bada cigiyar"
"To shikenan dan albarka"
mayafi suka dauka, sai gidan mai magani, ba karamin mamaki yayi da gani Ammi ba, wajen xama ya basu, fuskarsa cike da fara'a ya dube su.
"Alhamdulillah, Allah maji rokon bawa, sannu baiwar Allah kin sha fama"
murmushi Ammi tayi ta dube shi.
"komai yayi sauki malam yanxu babu abinda nake ji mun gode sosai Allah ya biya maka bukatunka na alkhairi"
hira sosai suka rika yi da Ammi akan rashin lafiyar da tayi, bayan sun gama ne suka yi sallama, kudade masu yawa yaya sadeeq ya bashi, cike da farin ciki mai maganin ya karba, adduar fatan alkhairi ya rika yi musu sannan suka tashi suka bar gidan.
kai tsaye gida yaya sadeeq ya mayar da su mamah sannan ya wuce wajen bada cigiya.
bai dade da tafiya ba ya dawo, tarar da su yayi a tsakar gida suna cin abinci da sallama ya karasa wajen da suke, cikin kulawa mama take masa magana
"sannu da xuwa
saddequ har ka dawo amma kayi sauri sosai"
takalmansa ya shiga cirewa.
" naje na kai mama sun ce Insha Allah xasu bada sanarwar har xuwa lokacin da xa a dace, na bada number wayar da xa a same mu"
Albarka ta shiga saka masa sannan ya shiga kitchen ya dakko abinci.
**********************
A bangaren Abban Nauwar kuwa, sun yi nema har sun gaji don haka suka yanke shawarar komawa gida kawai su cigaba da addu'a don sun san Allah maji rokon bawansa ne.
sallama yayi da Hamdan da Abbansa shi kuma ya wuce gida.
Yana nufo kofar gidansa yaga kofar gidan a bude alamun akwai mutane a ciki, da sauri ya doshi kofar shiga gidan, ihu yaji ana yi ana neman taimako, da hanxari ya shiga gidan don ganewa idonsa abinda ke faruwa.
*Jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:18 PM] Writer: ππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
ππππππ
*Ina yiwa al'umar musulmin duniya Barka da sallah da fatan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ameen*
8β£3β£
cikin fushi ya shiga gidan tarar da kofar yayi a kulle, buga kofar ya shiga yi ba kakkautawa amma ba a xo an bude masa ba sai ihu da yake tashi.
ganin ba a da niyyar bude masa ne yasa ya fita ya bar gidan, kiran me gyara yayi inda ya balle masa murfin kofar ya shiga.
cikin falon ya sa kanshi, ihu dai yake ji amma kuma bai ga komai a ciki ba, dakin Ammin Nauwar ya shiga, da sauri ya ja da baya yana ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un, innah karime ya tarar maciji ya nade mata jiki, ihu kawai take tana neman taimako, jawo kofar dakin yayi ya kulleta, da sauri ya dauki mukullin moto ya fita, kiran masu cire maciji yayi, suna isowa suka shiga dakin da take.
kallo daya mai cire macijin yayi wa macijin da ya nadeta ya ja da baya, dafa kafadar Abban Nauwar yayi.
"Alhaji wannan ba irin macijin da muke cirewa bane, wannan da gani na iska ne, abinda xa a yi kawai turaren magani xan mata, idan ya saketa shikenan idan kuma bai saketa ba sai a yi hakuri, sbd aikin ya fi karfina"
wani gumi ne kawai yake yankowa Abban Nauwar, mamaki yake daga ina ma macijin ya shigo har ya makale mata a jiki bata sani ba.
"shikenan ba komai a gwada yin turaren idan an dace shikenan"
burgima innah karime take yi, tun tana ihu har muryarta ta dashe, turare ya saka a dakin ya kulle sannan suka dawo falo suka xauna.
tagumi Abban Nauwar yayi sbd abubuwan da suke faruwa a gidan sa suna matukar bashi mamaki, a xuciyarsa yake magana.
"mutanen nan sai dai idan wani mugun abin suka kunno ya koma musu kansu, kadan ma suka gani daga aikin asiri"
bayan minti biyar da saka turaren ya tashi ya shiga dakin, tarar da macijin yayi ya sulale ya gudu, gaba daya innah karime ta galabaita ta fita daga cikin hankalinta, a hankali ya dagota, kiran Abban Nauwar yayi da hanxari ya karaso ciki.
"Alhaji abin nan ya illata baiwar Allahn nan saboda duk wata ga6a ta jikinta ya karyata, sannan kuma yayi mata tsattuwa a ido, gaskiya sai tsananin rabo xata samu ta mike, kuma ko ta mike ta rasa idonta biyu"
cikin jimami Abban Nauwar ya dubi mai magani.
"yanxu babu wani taimako da xa a bata kenan"
kallon shi yayi sannan ya mayar masa da amsa.
"taimako daya xamu yi mata shi ne mu bata maganin da xata yi aman dafin da ya xuba mata a cikinta, amma idonta gaskiya ya tafi baxai dawo ba sai dai hakuri"
magana suka jiyo ana yi a falo don haka suka kasa kunne don jin abinda ake fada, Habi ce ta shigo tana shewa.
"innah kina ina ki fito yau nayi ido hudu da gobe da nisa, ya fada min mahaukaciya baxa ta kara samun lafiya ba har abada, kuma shi ma mudi gobe ko jibi xai yi ajalinsa tunda yanxu wulakanta mu yake yi, gara ya hallaka shi kowa ya huta dukiyarsa kuma mun yi alkawarin xamu raba gida biyu mu bashi kaso daya"
duk wannan maganar da take yi a tunaninta babu kowa a gidan saboda bata nan Abban Nauwar ya dawo, shirun da taji ba a amsa mata bane yasa ta shigo cikin dakin, tarar da su tayi tare da mai magani sun yi tsaye suna mamakin maganganun da suka ji daga gareta.
tana ganin Abban Nauwar ta xube kasa tana borin kunya, shi kuwa kallonta kawai yake ya kasa magana saboda mamaki.
mai maganin ne ya buga mata tsawa.
"matsa ki bamu guri munafukar banxa munafukar wofi, kina tsammanin duk maganganun da kika fada bamu ji abinda kika ce bane, to yau karyar asiri ta kare wanda kike yi dominsa yaji komai, yanxu ma da shirin da kika taho da shi ki bani abinda kika karbo kafin na tona miki asiri"
rawar baki Habi ta fara yi.
"wlh ban karbo komai ba Allah ya gafarta malam, babu komai a xuciyata sai alheri"
sake daka mata tsawa yayi.
"xaki bani ko sai na mayar miki da duk asiran da kika yiwa wannan bawan Allahn da iyalansa kan ki"
rufe ido yayi, sannan ya mika mata hannu.
"miko min maganin da ya baki kafin na bude idona"
rawar jiki ta fara yi nan da nan, ta fara kwance gefen xaninta sai ga magunguna nan suna fadowa, a hankali ya sunkuya ya kwashe magungunan.
fuskarsa a daure ya dubeta.
"akwai binne-binnen da ku ka yi,ina so ki hako min shi yanxu ki bani"
sake duban Abban Nauwar yayi.
"wannan matar shaidaniya ce ita da wannan ta kwancen da maciji ya makalewa a jiki, kuma wannan macijin su suka kawo shi gidan nan don ya cutar da kai, sai kaikayi ya koma kan mashekiya, don haka baxan bata maganina ba saboda muguwa ce, gobe kuma xan dawo duk wani mugun aiki da suka yi a gidan nan sai na warware shi, ke kuma" ya nuna Habi da hannu.
"gobe ki shirya duk abinda kika yi na sharri sai na mayar miki da shi kanki, xaki bada labarin illar xalunci da kanki"
faduwa Habi tayi tana rokon shi ya taimake ta ya rufa mata asiri amma ko kallonta bai yi ba ya fice a fusace ya bar gidan.
shi kuwa Abban Nauwar bakin ciki ma ya hana shi magana, kawai wani hayakin bakin ciki ne yake taso masa a xuciyarsa, jiran gobe kawai yake yi ta ga ruwan rashin mutuncin da ya tanadar mata.
*Jeeddahtulkhairπ*
[9/9, 9:18 PM] Writer: ππππππ
*AL-MAJIRA*
ππππππ
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
ππππππ
8β£4β£
Gwiwoyi biyu Habi
tasa a kasa tana rokon shi gafara.
"Dan Allah kada ka bari mutumin nan ya maido min da abinda ba nida hakki a kansa, wlh ba nida wani hannu cikin 6atan yayanka, ban san abinda ya faru ba ka taimaka ka tallafi rayuwata, kasan babu yadda xa a yi a hada baki da ni a cuci iyalanka ko dan alkhairin da kayi mana"
Hawayen takaici Abba Nauwar ya shiga xubarwa ficewa yayi ya barta a dakin tana ta sambatu, sashinsa ya nufa yana shiga dakin ya fada kan gado ya cigaba da share kwallar bakin ciki.
waya ya dauka ya kira baffa, cikin kuka yake masa bayani abinda ya faru.
"Baffa ashe duk halin da na shiga da sa hannun Gwaggo Habi da innah karime"
salati Baffa ya shiga yi.
"Ai dama kaine baka gane ba Mahmud ni na dade da fuskantar hakan, fatana dai kayi hakuri kada ka saka damuwar hakan a ranka kuma ka cigaba da addua komai na Allah yana da iyaka, ya labarin jikat kuwa"
gyaran murya yayi sannan ya fara yi masa bayani.
"wallahi Baffa nayi neman duniya babu labarin su, mun kai cigiya duk inda ya kamata amma har yanxu bamu ji wata magana mai karfi ba, dan Allah ka taya ni da addu'a ina cikin kunci da damuwa ko bacci bana iya yi, xaka yi mamaki idan kaga yadda na rame na fita daga hayyacina"
Hakuri Baffa ya rika bashi yana rarrashinsa har sai da xuciyarsa tayi sanyi, daga karshe Abban Nauwar yake shaida masa abinda ya faru da innah karime, cikin tashin hankali Baffa yake tambayarsa.
"yaushe ita kuma wannan ibtila'in ya afka mata"
"jiya ne Baffa nima bana nan sai dawo wa nayi na tarar da ita a wannan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 29