Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da taga irin wannan abin arxikin har ta manta,a jiye kayan tayi a gefe sannan ta dauki sabulu. jawo kofar dakin tayi ta fito, dan tana jin tsoron ta barta a bude Ammi ta fito a ganta a waje su ci mata mutunci. mai gadi ta samu yana alwala a gefen dakin shi, tambayar shi tayi inda bandaki yake sannan ta roke shi ya bata aron bokitin wanka, nuni yayi mata da hannunshi sannan ya fada mata akwai bokiti a bandakin, cikin nutsuwa ta karasa tana daf da shiga ciki ne, taji tafiyar mutum a bayanta, waiwaya tayi don ganin wanda ya biyo ta a baya, ummy ta gani daya daga cikin kannen doctor tana watsa mata wata muguwar harara, tsayawa tayi ta karewa Nauwar kallon sama da kasa sannan ta fara mata magana. "me xaki shiga kiyi a toilet din mu? daga xuwan ki har xaki fara cika mana shadda" kan Nauwar na sunkuye saboda takaicin da ya cika xuciyarta ta maida mata da amsa, wanka xan yi. xaro da manyan idanunta tayi gami da rike baki, kin xo xaki yi wanka ki goge kaushi, wato ki makalewa dan uwana ko, to wlh baki isa ba yaya babba ya fi karfin ki, kuma baki isa ki shiga wajen nan ba duk masifar ki. kwace bokitin ruwan tayi gami da jifa da shi gefe guda, ta bar Nauwar tsaye a nan tana tunani. karasa wa wajen mai gadi tayi tana masa masifa "daga yau sai yau, kada ka sake barin wadannan mahaukatan su shigar mana toilet sai sun shafa mana cutar hauka ko kuma sun kawo mana annobar ciwon sanyi, duk da bandakin ka ne, ban amince ka bar su suna shiga ba" cikin ladabi da kaskantar da kai ya bata amsa. "Insha Allah xan kiyaye Hajiya." A dai-dai lokacin su feenah da zainab suka yi sallama, suna ganin Nauwar a tsaye suka ci burki suka tsaya, cikin mamaki ta dubi ummy. "wannan kwashen kuma daga ina?" ya mutsa fuska tayi sannan ta basu amsa "yaya babba xaku tambaya don shi ne ya jajibo mana bala'i har cikin gida" cikin masifa feenah ke magana tare da watsawa Nauwar wata shu'umar harara "wai shi yayan nan me yasa yake mana haka ne, sai ya rika taro mana mutane a gida har da gayyar mahaukata, gidan nan fa ba gadon shi ne shi kadai ba, mu ma muna da gado, wlh yau sai wannan yarinya ta fita daga gidan nan dan baxai yiwu mu xauna da mahaukaciya ba" ta karasa maganar tana nuna Nauwar. Ummy ce ta sake dubanta tana murmushin mugunta. " to ai ke baki san wani abu ba, ba ita kadai ce mahaukaciyar ba har da mamanta suna cikin dan akurkin nan a nan aka sauke su" bude dakin suka yi, lekawa suka sai da suka karewa Ammi kallo sannan suka kulle shi. tabdi lallai mun yi sake a gidan nan da har ake mana kwashe-kwashe, kuma wai har shopping yayi mata, saboda tsabar taya bera barna. shiga suka yi dakin suka kwashe duk kayan da doctor ya siyowa Nauwar. wucewa suka yi suka shiga wajen Hajiya, samun ta suka yi tana shirin fita unguwa, yadda ta gansu sun taho gaba daya sai da suka fadar mata da gaba, duk a xaton ta wani abin ne ya afku, jifa zainab tayi da kayan da suka kwaso daga wajen Nauwar bin su tayj da kallo mai cike da mamaki, kafin tace komai har suna sun fara kora mata jawabi. "wlh Hajiya baxa mu yarda ba sai an fitar mana da mahaukatan nan daga gida,haka kawai a kawo mana mutane bamu san asalinsu ba, bamu san yadda suke ba kawai su xaune mana a gida sam baxa bamu yarda ba, ai mu ma muna da hakki a gidan, gashi nan har shopping sai da yaje yayi mata mu bai bamu ba. lallai wannan yaron ya rika, gaba daya yanxu ya canja ya xama mai kunnen kashi, haka kawai muna xaune kalau ya jawo mana jaraba, tuntuni nace a fitar da mutanen nan amma ya kafe saboda baya jin magana,wai shi uban tausayi, nifa yarinyar nan kallon karuwa nake mata,kada taxo har gida ta lalata min yaro, dama da ya bi ta tawa da baxa ma kuxo ku tarar da su a gidan ba, saboda ni yarinyar gaba daya bata kwanta min ba" suna cikin wannan maganar doctor Abdallah ya yi sallama, suna ganin shi suka koma gefe gaba daya suka bi bango saboda kwarjinin sa. cikin bacin rai yake musu magana. Gaskiya Hajiya abinda ku ke yi ke da yaran nan gaba daya bai dace ba, yara basa so a ci arxikin su, Hajiya ki tuna fa yaran nan mata ne baki san irin mijin da xasu aura ba, kuma baki san yadda Allah xai yi dasu ba nan gaba, amma ki xauna kisa su gaba kina koya musu saka da mugun xare,Gaskiya hakan bai kamata ba, ku kuma wlh indai ku ka cigaba da musgunawa yarinyar nan ni da ku ne" Hawa kan Abdallah tayi da masifa dan haka ya fice ya kyaleta. yana fita suka cigaba da tattaunawar da suke yi, feenah ce ta cigaba da magana "wlh Hajiya dole mu takurawa matar nan har sai ta gaji ta kwashe kayanta, ki kyale shi kada ki sake yi masa magana, da kanta xata sulale ta gudu ba tare da ma ya sani ba. kwashewa suka yj da dariya "ai kuwa kin kawo haske feenah haka xa a yi musu duk wankin gidan nan su xasu rika yi, washing machine ya huta, su xasu rika aiki kamar jakuna, hatta inner wears su xasu rika wankewa sun ji dadin wannan shawarar da Hajiya ta bayar, sbd sun yi tanadin kala-kalar axabar da xasu ganawa Nauwar da mahaifiyarta. *Yawan comments yawan typing ehe* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 5⃣9⃣ Tunda suka bar Nauwar a tsaye bayan sun gama yi mata wannan cin mutuncin bata ko motsa daga inda take ba,saboda takaici da bakin cikin da ya mamaye xuciyarta, da kyar ta ja kafa ta koma daki, kifa kanta tayi a kasa,ta rusa kuka mai ban tausayi, turo kofar dakin aka yi tare da sallama, doctor ne ya shigo fuskar shi ba walwala, yana jin xafin wulakancin da ake yi wa Nauwar, tsugunnawa yayi yana fuskantar ta, sai faman kuka take yi bata ma san ya shigo ba. kamshin turaren sa ne ya daki hancinta saurin dago da kanta tayi, ido hudu suka yi da shi, wani kyakkyawan murmushi ya sakar mata. cikin karfin hali ta mayar masa da martani samun guri yayi ya xauna yana fuskantar ta, cikin sassanyar murya tare da kulawa ya fara mata magana. "kiyi hakuri da irin matsalolin da xaki fuskanta a gidan nan, kada ki rika saka damuwar hakan a ranki, domin kuwa halin yaran gidan nan ne raina dan Adam, tunda har kin fahimci haka bana so naga kin kara bata ranki a kan Abubuwan da xasu rika yi miki, kiyi hakuri ki daure wata rana xaki ci ribar hakurin da kika yi" cikin kuka ta dago jajayen idanunta tana masa magana "na gode da kulawar ka gare ni, amma xuciyata baxa ta iya jure cin fuskar da ake min a gidan nan ba, dan Allah ka bani dama na tafi inda xan fi samun sauki, ni wlh har na fi jin dadin rayuwar kasuwar da nake yi a kan dai rayuwar gidan nan, ga shi dai kana girmama ni, amma yan uwanka da mahaifiyarka sun hana ni jin dadi, bana so na xama silar hadaka da mahaifiyar ka, na yanke shawarar yau xan fita na bar gidan nan tun kafin wata matsalar ta afku" cikin tashin hankali ya dubeta "dan Allah ki daina tunanin barin gidan nan, indai kin ga kin fita to na nemo gidan ku da yan uwan ki ne, amma wannan dalilin baxai sa na bari ki tafi ba saboda wahala bata kisa, kuma komai na Allah yana da ka'ida" kuka ta cigaba da yi saboda shi ne kadai abinda xai sanyaya mata xuciya a yanxu, duba dakin ya shiga yi, cikin mamaki ya dubeta "in kayan da na siyo miki" share hawaye tayi sannan ta bashi amsa "an xo an kwashe" "an kwashe kuma? wanene yayi wannan aikin" tsugunnawa tayi har kasa ta fara yi masa bayani "kannenka ne suka kwasa amma dan Allah kada kaje kace xaka yi musu wani abin saboda haka, kayi hakuri ka kyale su, kada hakan ya jawo min matsala a wajen su, ni na yafe musu duk abinda suka yi min" tausayin yarinyar ne ya kama shi, cikin kulawa ya dubeta "ba komai na rabu da su,amma yanxu xan fita xan sake siyo miki duk kayan da kike bukata, kada ki sake bari su dibar miki" godiya tayi masa sannan ya fice, bayan mintuna kadan ya dawo mata da kaya masu yawa, umarni yayi mata da ta boye su gudun kada kannensa su sake kwashewa. kwanan su Nauwar uku a gidan su doctor kullum da irin bakin cikin da take fuskanta, tunda taxo gidan bata samu ta watsa ruwa a jikinta ko da sau daya ba,saboda sun hana ta shiga bandaki dan kada tayi kwalliya ta kwace musu doctor din su. yau da sassafe doctor ya fita saboda yana da aiyuka da yawa a Office, ganin baya nan ne yasa Hajiya ta taho tare da tawagar yayanta, kwankwasa kofar dakin su Nauwar tayi, a raxane ta taso ta bude musu. tsugunnawa tayi har kasa ta gaida Hajiya, wata harara ta watsa mata sannan ta fara magana. "lallai yarinya kin samu sakewa wato har lokacin bacci kike samu, to gidan nan ba na bacci bane.fitowa xaki kiyi aiki tukuru kamar sabuwar jaka, dan baxa ki xauna haka kawai kina cin arxikin mu ba, mu kuma ba ma morar ki" watsa mata kayan wanki tayi a fuska sannan ta jefeta da sabulu "dauki maxa ki xo ki fara aiki, kina gamawa shara na jiran ki, kuma ki shirya jibi xaki bar gidan nan, ko kina so,ko bakya so" ficewa tayi ta barta a tsugunnah tana naxarin irin wannan wahala da kaskancin ta tsinci kanta a ciki. watsi tayi da kayan wankin tana masifa "ba a isa nayi wannan aikin ba, dan nima 'ya ce kamar kowa kuma ina da galihu kaddara ce ta sauka a kaina, dan haka ba katuwar da xan xauna ina yi wa wanki, sai dai idan xa a kore ni a kore ni, dama abinda nafi bukata kenan, tunda rayuwar da nayi a baya bata kashe ni ba, wannan ma ba abinda xata yi min dan na koma kasuwa da kwana" mayar da kofar dakin tayi ta kulle. ta baranda zainab ta hango dakin Nauwar a kulle da gudu ta shiga daki ta fara kwalawa Hajiya kira. "fito ki ga abinda wannan mahaukaciyar tayi" cike da mamaki Hajiya da sauran yaran gidan suka leka suka ga dakin Nauwar a kulle, komawa daki suka yi, kowanne su ya dauki abin duka, cikin masifa Hajiya ke magana. "dole mu dauki mataki a kan yarinyar nan, wato har tayi sakewar da xan sakata aiki taki yi, yau sai naga mai raba ni da ita, wlh yau ko dukan nan xai xama ajalinta kowa sai ya xaneta a cikin ku" bakin kofar dakin Nauwar suka nufa, bugun tashin hankali suka rika yi, a firgice ta tashi ta bude musu, jawo wuyanta Hajiya tayi ta rika duka kamar baxa ta barta da rai ba, sannan yayanta suka dora da dukanta basu kyaleta ba har sai da suka ga ta kai kasa, tana wani irin abu kamar na masu cutar farfadiya. *yawan comments yawan typing, idan an yi comments da yawa na karasa ciko ragowar pages din* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Yan uwa ina jin dadin comments din ku, kuma hakan na kara min karfin gwiwar yin typing da yawa ina godiya sosai* 6⃣0⃣ Duk da yanayin wahala da suka jefa Nauwar a ciki hakan bai sa sun sassauta da dukanta ba, har sai da suka ga ta daina motsi, ganin abinda suka yi mata ne yasa aljanun Ammi suka tashi, nan fa ta shakewa hajiya makoshi ta rika duka ta ko'ina duk yadda yayan nan suka yi su kwaceta suka kasa saboda gaba daya bata cikin hankalinta ,sai da ta gama xane ta tsaf ta sake ta, kan su zainab ta sake yo wa da gudu suka shige daki suka bar Hajiya kwance jina-jina. suna shiga daki suka dauki waya, suka kira doctor, cikin kuka feenah ke masa magana "daga cikin masifar da ka jawo mana, ka kawo mana su har gida, daya daga cikin su ta hau Hajiya da duka, da kyar ne ma idan bata hallaka ta ba" hankalin doctor a tashe ya mata magana "me kike fada min haka feenah, yaushe al'amarin ya faru" Cikin tsiwa take masa magana. "yanxu ne idan kaxo ka ganewa idanunka ni ba ni da lokacin tsayawa na baka amsa ta halin da mahaifiyata ke ciki nake yi" xage-xage su feenah ke yi suna tsinewa doctor saboda ya kawo musu kwai tara tsinana har gida, kokarin fita suke yi wajen Hajiya amma saboda tsoron Ammi ta kasa ta tsare tana jiran fitowar su ta sauya musu halitta. shi yasa suka yi wa kansu fada suka xauna a daki, suna leken halin da ta jefa mahaifiyar su a ciki. cikin gaggawa doctor ya dakko mota, yana tuki yana kiran innalillahi wa inna ilaihi raji'un saboda babban masifa ce ta tunkare shi, wacce kuma idan bai yi da gaske ba sai ta haifar masa da bakin ciki na har abada, a waje ya yi parking saboda baxai iya jira har sai an bude masa gate ya shiga da mota ba, shigar sa gida ke da wuya ya tarar da Hajiya kwance tana numfarfashi, ga Nauwar ita ma a kwance jini na kwarara a kan fuskarta, hawaye ne ya shiga fitowa daga idanun doctor ta ko'ina, yana karasawa wajen Hajiya Ammi ta matsa daga wajen, duk da kasancewar ta mahaukaciya tasan mai kyautata masu. daga kan Hajiya yayi yana mata sannu, bude ido tayi kadan ta dube shi, da hanxari ta xabura xata gudu a tunaninta Ammi ce ta sake dawo wa xata dake ta, cikin nutsuwa tare da rarrashi yake mata magana. "sannu Hajiya, kin ga irin abinda nake fada muku ko, ga irinta nan ai, kun kama karamar yarinya kuna kokarin hallakata ba a kan hakkinta ba, ko da ku ke ganin mahaifiyar ta a matsayin mahaukaciya ita ma tasan ciwon haihuwa, kuma tana jin xafi idan an taba yarta, nasan kuma duk laifin daga wajen ku yake, da baku taba su ba hakan baxai faru ba, yanxu da kun kasheta ai ni ku ka jawo wa masifa " yana Cikin wannan maganar ne gaba daya yayan gidan suka fito suka fara xage-xage, suna cewa ya kawo musu abinda xai kashe su har gida, duk yadda suke tsoron doctor hakan bai hana su fadar duk abinda suka yi niyya ba, shiru yayi ya kyale su saboda a yau dai ba shi da bakin magana tunda aka taba mai gayya mai aiki. daga Hajiya yayi ya komar da ita gefe guda, saboda dakuwar da tayi bata iya cewa komai duk jikinta ciwo yake yi. komawa kan Nauwar yayi inda ya fara bata agajin gaggawa cikin ikon Allah ta farfado, hawaye ta shiga xubarwa shi kuwa doctor sai hakuri yake bata yana lallashinta. Cikin kuka take masa magana. "doctor na gode da taimakon da kayi min, amma wlh baxan sake kwana a gidan nan ba, da kabari da wannan gidan duk daya ne a wajena, tunda naxo bayin Allahn nan basu bar ni na huta ba, na tabbata idan na cigaba a xama wata rana sai sun kashe ni da duka" ummy ce taxo ta tsaya a kansu tana masifa. "ai ni baxan so ki bar gidan nan ba, sai mun gama axabtar da ke mun ramawa mahaifiyar mu abinda Mahaukaciyar uwarki tayi mata, wannan kadan ki ka gani daga cikin axabar da muka fara gana miki" feenah da sauran kannen doctor ne suka shiga dakin su Nauwar suka fara watso musu yan tsummokaran su, xuciyar doctor kamar ta fashe saboda bakin ciki, yasan ko yayi musu magana baxa su fasa ba, sai da suka gama watso kayan gaba daya, sannan suka kulle dakin. cike da rashin kunya suke magana. "mu ga wanda xai xo ya sake bude dakin nan ya saka wasu yan iska a ciki" Hajiya na gama hutawa daga axabar dukan da tasha a hannun Ammi, mikewa tayi ta fara xaxxagawa doctor bala'i. "baka isa na sake kwana gida daya da mahaukaciya ba, yanxu nake so ka tattara ka fitar min da su, idan kuma baxa ka iya ba, xan yi aikina da kaina" hakuri ya shiga bata, tare da nuna mata illar wulakanta bil Adama amma saboda idanun Hajiya sun rufe sai tayi watsi da maganar sa. su feenah tasa suka kinkimi Nauwar suka jefata waje tare da kayanta, ita kuma Ammi tasa doctor ya kamata ya fitar da ita, suka mayar da kofa suka kulle. godiya Nauwar ta yi wa Allah da ya raba ta da gidan bala'i. cikin tausayawa doctor ya dube ta "kiyi hakuri bisa taimakon da na baki wanda ya xamo mana matsala ni da ke, ki kaddara komai ya same ki daga Allah ne, ba a son raina xaki bar gidan ba, amma saboda an fi karfina an rinjaye ni, haka xan kyale ki ba dan ina so ba, kada ki manta da ni a rayuwar ki, duk inda nake xan kasance mai yi miki addu'a Allah ya hada ki da mutane na gari wadanda xasu kula da ke" compliment card din shi ya xaro ya mika mata. "karbi wannna ki rike dan Allah kada kiyi wasa da shi, duk lokacin da kika samu nutsuwa kika koma gida, ki kira daya daga cikin numbers dina, Insha Allah xaki same ni, wannan tafiyar baxa ta yanke alakar da ke tsakanin mu ba, fatana ki kula da kan ki, ki kare mutuncin ki a duk inda kika kasance"ya karasa maganar yana share hawaye. saboda kukan da Nauwar ke yi ta kasa cewa da doctor komai, saboda a dan xaman da tayi da doctor ya matukar shiga ranta. Bayan doctor aka daka, gaba daya suka mai da hankalin su ga wanda yayi dukan, Hajiya ce taja wuyan shi cikin xafin rai take masa magana. "bin ta xaka yi ne uban tausayi, shige mu tafi kafin na tsine maka ka bi duniya, ke kuma ki tashi ki bar nan dan idan na dawo na tarar da ke sai ranki ya baci" doctor na kuka ta ixa keyar shi har cikin gida ta mayar da kofa ta kulle. Tashi Nauwar tayi suka bar kofar gidan, suka kama hanyar tafiya kasuwa. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *masoya bansan da wane kalmomi xan gode muku ba saboda kaunar da ku ke nunawa wannan littafi, ina godia da kulawar ku gare ni, idan da hali xan kira sunan ku daya bayan daya a next post da xan yi* 6⃣1⃣ Har cikin daki ta shigar da doctor, xaunar da shi tayi gami da dukan kansa. "ko xaka yi kuka hawayenka ya kare baxan bari ka bi wannan tsintacciyar magen ba, ni fa lamarinka ma mamaki yake bani Abdallah, daga ganin yarinya baka san abinda ya rabo ta daga gida ba kawai dan ta shirya maka karya da gaskiya, kai kuma ka hau ka xauna saboda rashin lissafi, wa ya sani ma ko su suka yi wa wata asiri abin ya koma kan su, amma duk ka bi ka damu xuciyar ka har da kukan rabuwa da ita, ko dai ba haka ta bar min kai ba???" dago jajayen idanunsa yayi ya kalleta ya cigaba da share kwalla, saboda bakin cikin da ya mamaye xuciyar sa gaba daya ya kasa magana, tunanin Nauwar kawai yake yi da halin da xasu tsunduma bayan rabuwar su, ji yake kamar ya bi ta ya dawo da ita, tsoron tsinuwar Hajiya ne kawai ya hana shi tafiya. kifa kanshi yayi a kasa ya rika kuka tamkar yaron goye, a ranar gaba daya bai rintsa ba, saboda bakin ciki. Yau kusan kwanan su Nauwar biyar da tafiya, gaba daya Hajiya ta rasa kan Abdallah baya kwana a gida baya cin abinci sannan ya daina yi wa kowa magana, sai dai idan yana da abinda xai dauka ya shigo ya biya bukatar sa yana gamawa kuma xai fice,baxai sake dawo wa ba sai wata bukatar ta kawo shi, hankalin Hajiya ya tashi sosai saboda wannan sabuwar dabi'ar da doctor ya bijiro mata da shi. hankalinta a tashe tasa driver ya dauketa ya kai ta Asibitin da doctor yake aiki, tambaya tayi a nuna mata Office din da yake. da sallama ta shiga wajen, samun shi tayi ya dora kan shi bisa tebur hawaye na gangarowa daga fuskarsa, cikin tsananin nuna damuwa ta nemi guri ta xauna, cikin kulawa ta dube shi. "Abdallah wai me ke damunka ne kwana biyu, ko duk a cikin damuwar rabuwa da yarinyar da baka san asalinta bane? ya kamata kasan inda kanka yake, a kan wata shashar yarinya xaka jefa rayuwarka a garari, har ka daina walwala ka bar gida ka daina kula kowa, wato kana nuna cewa yarinyar ta fi mu daraja a idonka ko, to wlh tun wuri ka farka daga bacci mai nauyin da ya dauke ka, kafin na ci maka mutunci, dan baxan yarda da wannan shashancin a gidana ba" Hannu yasa ya share hawayen da ya cika idonsa, cikin sassanyar murya yake mata magana. "baxan taba samun kwanciyar hankali ba matukar ban san inda rayuwar yarinyar nan ta shiga ba, shikenan nan kawai dan kun ga mutum a haka sai ku munana masa xato, ku ka sani ko xaluntar su aka yi, ba su suka xalunta ba, kun yi kuskuren wulakancin da ku ka yi musu, kuma na tabbatar Allah baxai kyale ku ba, dan kaga bawa a cikin wani hali ba shi yake nuna kana da damar da xaka cutar da shi ba, saboda baka san baiwar da Allah yayi masa ba, ni a yanxu baxan iya dawo wa gidan nan ba, alhalin ina ganin dakin da bayin Allahn nan suke ciki, saboda xai rika tayar min da ciwon abinda aka yi musu ne na rashin kyautawa, kawai ku yi hakuri ku kyale ni, dan nasan nima na kusa shiga wani hali, tunda ku ka toxarta su a gaban idona" ya karasa maganar wasu sababbin hawaye suna xuba a fuskarsa. hankalin Hajiya ya tashi sosai da jin maganar doctor dan tasan indai ya furta magana haka take, baya canjawa. cikin rarrashi take masa magana. "Haba yaya babba ya xaka yanke wannan danyen hukuncin, bai kamata a matsayinka na babba ka rika haka ba, shikenan kai baxa ka koyi hakuri ba duk abinda ya faru ba, sai kace sai ka dau mataki, idan kace ka fita daga gidan nan wa ka bar mana ya kula da mu, kuma yarinyar nan nasan yanxu sun kai inda suka kai, a ina xamu nemo ta, ni da ina da halin da xan ganta, da na dawo da ita ko dan cikar farin cikin ka, kayi hakuri ka dawo gida ka kuma dawo da walwalarka kamar da" doctor yaji dadin maganar Hajiya yasan da xai kara ganin su Nauwar ya dawo da su baxa a sake yi musu irin wulakancin da aka yi musu a baya ba. cikin girmamawa ya fara yi mata magana. "ba komai Hajiya ta wuce, amma ki ja kunnen yaran nan da kyau, daga yanxu kada su sake ganin mutum su wulakanta shi, indai suna haka wata rana xasu neme ni su rasa baxa a sake ganina ba" "Ai baxa a yi haka ba yaya babba, yanxu dai yaushe xaka dawo" sosa keya yayi ya dubeta "sai gobe Hajiya" xaro idanu tayi. "Haba yaya bai kamata ka xauna a nan ba har sai gobe kayi hakuri ka dawo yau" "To shikenan xan dawo anjima" farin ciki ne ya bayyana a fuskarta. "yauwa ko kai fa, Allah yayi maka albarka" amsa mata yayi da "Ameen" tashi tayi ta nufi gida, tana xuwa ta fadawa su feenah yadda suka yi da doctor, sannan tayi musu fada sosai, abinci mai rai da lafiya tasa suka dafa masa

Chapter 17 of 29